Kenza eBookz

Gudu da waiwaye bilyn abdul - Chapter 16

Gudu da waiwaye bilyn abdul - Chapter 16

Gudu da waiwaye bilyn abdul Chapter 16: Gudu da waiwaye bilyn abdul Chapter 16. Kowa yasan zuwa yanzu idanun Samina sun ƙara buɗewa, ta fetsare sosai, dama…

2,760 words

Kowa yasan zuwa yanzu idanun Samina sun ƙara buɗewa, ta fetsare sosai, dama karatun islamiyya kam ta ajiyesa gefe, na bokonma da take fakewa dashi yanzu bayi takeba, tunda da taje Ma'aruff ke zuwa ɗaukanta, wani lokacinma ko cikin makarantar bata shiga, kai tsaye gareshi take tafiya, abun yakai har Company dinsu Ma'aruff Samina zuwa take Office ɗinsa susha sha'aninsu. Gaba ɗaya ta manta da wani halitta Ahmad balle rayuwarsu ta baya da ƙoƙarin gina rayuwarta da yayi, gaba ɗaya ita a dole yanzu ta zama babbar yarinya, budurwar babban yaro da ya fi mijin novels komai. Abinda yasa Samina taƙi yarda ta bama Ma'aruff kanta 100% saboda tana tuna yanda marubuta kansa amarya tasha gata wajen minjinta a daren farko saboda budurcinta daya samu, amma yanda yasha kawo farmakin amsa da tuni ta bashi. To tanason dai itama taga wannan gatan shiyyasa.

_________________________

Rayuwa a wannan gida a yanzu babu abinda zance kam, dan bazance ina a ƙuntace ba bazance kuma inajin daɗiba. Sauƙina ɗaya yanzu tunda safe damunyi kari muka gyara ko ina makaranta muke nufa, bayan na saka Uniform nakan saka hijjan dina har ƙasa da niƙaf, ba ruwana da malamanmu, harma wani girma suke bani, hakan kansa ƴan ajinmu suyitamin shaƙiyanci, iyakata dariya kawai, sai ko su Salima dakan taremin. Idan aka tashi daga can gida su Fa'iza suke wucewa, nikuma na wuto gida nima, nakan tadda su maman Ama a ɗaki ɗaya zaune suna hira, ko a tsakar gidan wadda na tabbatar bata wuce gulma ba, dama ni tunda na sanar musu zan koma makaranta suka dasa yi dani, nakanji har dariya suke wai tundafa miji ya rainani ai dole ya maidani cikin ƴammata, tunda bani da maraba dasu. Da farko bana fahimtar zancen, amma a hankali saina gane manufarsu, sam ban damuba dan kuwa ni abinda suke nufin ba shine damuwataba, koda zamu shekara goma Yah Ahmad bai nema komai daga gareniba bazan taɓa ɗaukarsa komaiba. Dan laulayin ciki da kausar ta farane ya kan kawo a zauna anamin shaguɓe a kansa, tunma bana fahimta harsu Fa'iza suka ankarar dani, banji komaiba a raina, sai ma mamakin rashin ya kamata irin nasu maman Ama nake gani, su miye damuwarsu dan yaya Ahmad bai taɓa mu'amulantata a shimfiɗaba to?. Zanyi ƙokarin mana girki nasa a kula, la'asar nayi zan shirya na wuce islamiyya, daga can muke haɗuwa mu dawo gida da su Salima idan an tashi. Ko mun dawo kuwa muna ɗaki abunmu, idan kinga mun fito kuwa ban ɗaki zamuje ko yin abu mai muhimmanci, hakan ya saka su Kausar sake maidani naman cinsu, duk da a hakan kuma suma basubar junansu ba. Yanzuma likafa ta cigaba har gidan maƙwafta suke zuwa suma suna zuwa nan. Babu ruwana da kowacce mace bayan gaisuwa.

Lamarin Yah Ahmad kuwa bai cika damuna ba, duk da bawata waya mukeyi da shiba, tundama ya tafi baifi sau uku na taɓa waya da shiba a wayar Yah Mudanseer. Duk abinda na buƙata Yah Mudan na ƙoƙarin kare mani mutunci ya saya mani, idan kuma yafi karfinsa zai sayo dai-dai ƙarfinsa. Nima bamma faɗar wanda yafi ƙarfin nasa sam. Zuwan Ayyah gidan biyu dan taga yanda muke, hakama Yaya Maryam da yaya Sakina da Raheenatu, suma duk sunzo mani harma da yaya bintu yayar Samina. Suma duka zuwansu ya sakani farin ciki, duk wanda ya ganni kuma zai shaida hakan a fuskata. Kullum dai nakanbi mijina da addu'ar fatan alkairi da kariyar UBANGIJI aduk inda ya tsinci kansa, ALLAH kuma ya azurtashi da halalinsa komai kankantarsa, ya tsaresa daga haramun komai yawanta da ribar da zaici a cikinta. A farkon tafiyarsa naji kewarsa, amma zuwa yanzu sam babu hakan a raina.............✍🏻

_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_

_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279 _MARYAM SANI_ _ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇 *07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_

Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻 [7/27, 6:06 PM] Sis Hajiyyaye: *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo

*_GDW_*

*(20)*

...............Sassanyan numfashi na sauke jin ALLAH ya taimakeni bansha ƙasaba, sai dai jina a jikinsa saboda jawonin da yayi ya saka gabana faɗuwa nai saurin son matsawa bayan again. Sakinta Ahmad yayi saboda ganin Zainab a ɗakin, shima jinta da yay jikinsa ba ƙaramin bugawa ƙirjinsa yayi ba, ya raɓa ta gefenta zai wuce murya na Rawa tace, "Sannu da zuwa Yaya". Idanunsa ya ɗan lumshe yana ƙoƙarin zama a bakin gadon, ya ɗago ya kalleta sosai murya ƙasa-ƙasa ya amsa da "Yauwa, kema sannunki". Ruwa Umm-Ruman ta ɗibo a kofi bayan ta ɗauraye, ta kawo gabansa ta ajiye tare da durƙusawa tana sake masa sannu da zuwa, tana a duƙen take gaishesa cikin girmamawa. Daƙyar Ahmad ke ƙoƙarin amsawa dan sosai Rumana ta canja masa, sai yaga ta sake girma, ko dan dai kafin tafiyarsa ba wani kallon ƙwarai yake mataba, sannan bata yarda ta zauna babu hijjab, yau ko ya rutsatane babu hijjabin. Sanye take da siket da riga na wani yadi mai kama da atanfa, siket ɗin 8-fisis akai masa, hakan yasa ya matseta kaɗan daga sama ya buɗe sosai a ƙasa, ga rigar fitet ita kuma, sai hannunta ne daya buɗe sosai daga ƙarshe. Mudanseer ne yay musu ɗinki, a lokacin har Ahmad ɗinma na faɗan yanda Mudanseer yay wulaƙanta kayan da ɗinkin manyan gayu. Yadin bai kai sun sami ɗan kwaliba, sai wani kalan suka saya, itako Rumana bata cika son ɗan kwali mai santsiba, shiyyasa ko yanzu gyalen jallabiyane ta yana akan nata, hakanne ya bayyana haɗaɗɗen kitsonta ta gaba, sai jelar da yake iya hangowa kaɗan idan ta duƙa saboda tanada tsahon gashi, kusanma duk yaran gidansu ALLAH ya basu suma harsu mazan. Duk da yasha ruwa a gidansu baiƙi shan wanda ta kawo masaba, dan ganinta ya haddasa masa wani sabon ƙishirwan. Yana cikin shan ruwanne Zainab ta miƙe saboda gargaɗin da Ayyah tai mata akan tai maza ta dawo karta zauna. "Uhm Yaya Rumana bara naje gida, Ayyah tace karna zauna saboda magriba ta kusanto". Ji Rumana tai kamar ta hana Zainab wucewa, dan kallon da Ahmad ke mata duk ya sakata ruɗewa, kamar zatai kuka tace, "Ki zauna su Fa'iza su zo mana, ƙilama Yah Madan yazo anjima saiki bisa". Zainab taɗan ƙwalalo ido waje tana fadin "Kai, Yaya Rumana ALLAH Ayyah dukana zatai, gara dai na tafi, gobe zan dawo". Ahmad dai duk yana jinsu amma uffan bai ceba, yama ajiye kofin ruwan ya koma latsa wayarsa daya sake, dukda ba sabuwa bace tayi ƙyau dan batasha wahalaba sosai. Hamsin Rumana ta bama Zainab, "Tunda kinƙin Zee shikenan, gashi saiki hau napep". "Kima barshi Ayya naira sittin ta bani kuɗin zuwa da komawa, kin gani" zainab ta ƙare maganar da nunama Rumana sauran talatin ɗin tana ƙoƙarin fita. Ba yadda Rumana ta iya dole a gaban idonta zainab ta wuce.

Kanta a ƙasa tanata faman gyara gyalen danya rufe mata ƙirji ta maida hankalinta ga Ahmad da har yanzu bai daina latsa wayarba. "Yaya a saka ruwan wankane ko zaka fara cin abincin?". Ba tare da ya bar abinda yakeba yace, "Sakamin ruwan, dan zafi nakeji". Da "To" ta amsa, ta sanshi dason wanka da ruwan zafi dan haka ta ɗakko na filas data saba ajiyewa ta juye a botiki ta fita danta sirka masa.

Da sauri Maman Ama da Kausar da suka haɗa kai suna gulma a ƙofar kicin suka hau washe baki kamar gaske. "A, Amarya barka fa ƴan tafiya an sauka lafiya". Umm-Ruman ta amsa da "Yawa, ngd". Tasan dai gulmarta sukeyi, tunda kullumne babu fashi, har maƙwafta surutu suke zuwayi akan wai Yah Ahmad ya watsar da ita tsahon wata shida yaƙi dawowa, ƙilama ya gudune, idan iyayenta sukaji zasuzo su kwasheta itada kayan tunda mai gidan haya dai ba lamuni zaiyiba idan shekara ta ƙare. Yanzukam gulmarta suke akan wai ashe tasan mijinta zai dawo shiyyasa taketa ɓare-ɓaren gyara jikin tarbarsa, amma da suka tambayeta sai tace kwalliyar bikice. Kausar harda cewa, "Yo kwalliyar iyakar fatar ido dai zata tsaya tunda ba wata uwa zai iya mataba". Sosai maman Ama taita dariya da faɗin, "Wa yaga lagwani" shinema Rumana ta fito ta ritsasu.

Sai da taɗan sake ɗauraye masa bayin sannan ta ajiye ruwan ta fito. A ƙofar ɗaki ta iskesa zai fito, hannunsa riƙe da abin wanka da brush da ya sakama makilin, ta matsa ya wuce bayan ya ajiye takalman daya fiddo na silifas. Aiko harya shige banɗaki su maman Ama na binsa da kallon ƙurilla, so suke suga abin kushewa a samu nayi, sai basu ganiba, dan saima wata ƙiba data ƙara masa cikar zati da kwarjini ya ƙaro. Sai suka koma faɗin, ba dole ya narko ƙibaba yanacan yanacin daɗinnsa ya bar Rumana anan cikin wahala daga fara da mai sai wainar filawa. Karaf sai zance a kunnen Umm-Ruman data fito ɗauraye filet ɗin da zaici abinci. Kanta kawai ta girgiza tana mamakinsu ta koma ɗaki abinta dan gulma ta rufe musu ido basuko farga da itaba. Koda Umm-Ruman ta koma ɗaki sai ta ɗauki turaren tsinke ta sake kunnawa, duk da dai da safema ta kunna, kuma Alhmdllh ƙamshin ya kama ɗakin saboda nacin saka turaren da takeyi ga firishina ta haɗawa da yaya maryam ta kawo mata mai ɗan yawa, tanata ɓoyen abunta sai kaɗan- kaɗan take sakawa har turaren wutarma, na tsinkenne dai kullum saita kunna saboda da yawa aka kawo mata su.. Tana ƙoƙarin kunna fitila saboda duhun magriba da garin yayi Ahmad ya shigo ɗakin da sallama, Amsawa tai ba tare data juyi ta kallesa ba saboda kunya, duk da tasan akwai jallabiya a jikinsa kuwa. Batai auneba taji hucin mutum a bayan, cikin ɗan hanzari ta juyo, Ahmad dake tsaye a bayanta ya miƙa hannu zai ɗauki robar mai dake saman madubin, gefe Rumana ta matsa, duk da hakan kuma jikinsa na taɓa nata saboda lungun wajen baida girma sosai. Baice da ita komaiba, duk da ya lura da yanda taketa zare idanu, ya ɗau mansa ya zauna abakin gadon danya shafa, ganin taƙi wucewa ya ɗago fararen idanunsa ya ɗan kalleta. Saurin raɓashi tai ta fice, ya bita da kallo kawai yana girgiza kansa. Tana alwala a bakin rijiya yazo ya wuce zai fita massalaci, ta shaƙi ƙamshin turaren daya saka tana binsa da kallo, sosai taga canji daga garesa, sai taga kamar an wani canja matashi, dan yanda jikinsa kawai ya murje zai baka amsar tafiya tayi riba. Da wanna tunanin ta shiga ɗaki itama ta kabbara salla.

Ana idar da sallar magriba sai gashi ya dawo, a bakin gado ya zauna dai-dai tabarmar data ɗora kayan abincin, waya yakeyi, dan haka ta matso ta fara zuba masa abincin a filet, harta kammala zubawa yana wayarsa, sai dai idonsa na kanta kamar ya samu talabijin, dukda tanajin yanda idonsa ke yawo a jikinta tunɗazun ita bata yarda ta kallesanba. Kauda kwanikan tayi gefe yanda zaiji daɗin sakewa a wajen sosai, ta yunƙura da niyyar ta miƙe kawai babu zato taji ya ruƙo mata hannu, kafin ta gama tantance gaskiyar lamarin ta tsinci kanta ɗare-ɗare bisa cinyarsa. Kasa magana tayi dan matuƙar al'ajabinsa, ga jikinta sai wani yamm yakeyi, Ahmad ya ajiye wayar gefe tare da kallonta sosai, yanda yake kallon fuskarta babu wani alamun jin ba daidaiba ne ya sakata kasa jurewa ita, gashi fuskarsa sam babu walwala, kamar dai yanda ta saba ganintane acan baya. Hannu ya saka ya ɗago da haɓarta yana ƙoƙarin zare hijjab ɗin, bata hanashi ba, dan batagama fuskar yin hakan daga garesaba, sai sake matse hannayenta take waje ɗaya illahirin jinin jikinta na gudu cikin kowacce jijiya da sauri. Ya ajiye hijjab ɗin saman gadon ba tare daya tankaba, goshinsa ya ɗora saman nata, mutuniyarku saita sake ruɗewa, cikin in ina tace, "Ya..ya a...b in ....cin za..i zai huce fa". Ahankali ya furta "idanma ya huce bakece kika ja ba?". Babu shiri ta ɗago idanunta sai suka afka cikin nasa, dan har yanzu goshinsa nakan nata, hancinsu gab da juna suna musayar numfashi, hakama bakinsu babu wata tazara duk da ita Rumana taɗan duƙar da kantane ba kamar yanda nasa yake daret ba. Ƙasa ta sake maida idanun dan bazata jura kallon cikin nasaba, cikin muryar da ita kanta batasan tana da itaba tace, "Yaya ni kuma?". Ahmad da muryar Rumana ta saukar masa da kasala yace, "Uhum mana, ke haka aka koya miki tarbar miji ne? Wata shidda bama tare amma sam banga wani murnar ganina ko kewata a tare da keba". Karon farko da kanta ya kasa ɗaukar kalamansa, domin batai tsammanin wannan furucin daga garesa ba. Saita kasa bashi amsa, wasa dai taketayi da hannayenta dake bisa cinyarta, itako tana saman tasa zaune ko nauyinta bayaji. Hannunsa dake zagaye da ƙugunta ya janye ya kamo hannayenta da taketa cuɗawa waje ɗaya. Sosai jan lallen da akai mata wanda ya gaurayu da zanen baƙi yayma choco fatarta dake kama da tasa ƙyau, ya janye kansa daga goshinta yana sauke sassanyan numfashi tare da murza yatsun hannun nata duka cikin hannayensa. "Tunda bakiyi murna da dawowar tawa ba, ɗagani na koma inda na fito". Da sauri ta girgiza kanta idonta na cikowa da ƙwalla "ALLAH yaya ba haka baneba fa, nayi murnar dawowarka mana". Tsura mata ido yay, yanda idanunta suka kawo ruwa suna fidda wani ƙyalli saboda hasken fitilar sun ƙayatar dashi, ɗan yatsa ya ɗora kaɗan ya dangwalosu yayinda suka gangaro kaɗan saman furkarta, "Har yanzu kina nan a shashasharki dai?". Baki Rumana ta kumbura kaɗan wai ita dole taji haushi ya cemata shashasha. "Haushi kikaji?" Yay maganar cikin kunnenta yana sunsunar dokin wuyanta dake kamshin khumrar data shafa. Da sauri ta sinne kai ƙasa, jikinta na ɗaukar ƙyarma saboda sabon al'amarin da yakeyi mata. Baki yaɗan taɓe yana saka hannu ya ɗago haɓarta suka kalli juna, "Oh jan ajine komi?". Kasa jure kallon tayi tana janye idanunta, "A'a kawai dai banyi zaton dawowar taka bane ba yanzu". Tai maganar cikin sarƙewar halshe. Karon farko yayi murmushi har haƙoransa na bayyana, ya yunƙura tare da miƙar da ita shima ya miƙe, harkan tabarmar suka isa hannunsa riƙe da nata, ita dai ji take tamkar ta tsilla da gudu, sai da suka zauna sannan ya saki hannun nata, yakai hannu ya jawo filet ɗin abincin gabansa ya faraci ba tare da ya sake cewa komaiba. Rumana dai na zaune duk a takure, addu'a take ALLAH ya kawo mai belinta yanzun nan, sai dai addu'ar tata bataci ba, dan kuwa har ya kammala cin abinci babu wanda ya shigo, sai motsin matan gidan da suke jiyowa daga tsakar gida. Shikam Ahmad yanacin abincine idonsa akanta, musamman ma ƙushinta data gama tsole masa idanu tun shigowarsa gidan, amma da yake jarumin dakewane bazaka taɓa fahimtar hakan akan fuskarsa ba. Ya kammala cin abincinsa tsaf sannan yasha ruwa yana yin hamdala, dai-dai nan aka fara kiraye-kirayen sallar isha'i. Wayarsa ya ɗauka yay kiran wani da taji yana ambata da Nura, kusan mintuna biyu suna wayar sannan ya kashe, miƙewa yay tsaye yana zira wayar cikin aljihun jallabiyarsa, "Bara naje salla, daga can zanje gidan dan bamu gaisa dasu baba ba". Kan Rumana a ƙasa tace, "Saika dawo a gaishesu". "Uhum" ya faɗa yana ficewa daga ɗakin.

Sai da Rumana ta jiyo fitarsa daga gidan gaba ɗaya sannan ta sauke numfashi tana murmushi, ta kalli hanunta sosai da yasha murza a nasa ta lumshe ido, wai yau itace bisa cinyar Yah Ahmad zaune ɗane-ɗane, yana mata magana cikin taushin murya da sanyi. Duk da tasan ba sonta yakeba hakan ba ƙaramin daɗi yay mataba, salla ta miƙe ta gabatar sannan ta zauna ta cinye sauran abincin da ya rage a filet ɗin tana mai jin wani tsagwaron nishaɗi...

★★★★★★

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull