Kenza eBookz

Gudu da waiwaye bilyn abdul - Chapter 17

Gudu da waiwaye bilyn abdul - Chapter 17

Gudu da waiwaye bilyn abdul Chapter 17: Gudu da waiwaye bilyn abdul Chapter 17. Koda aka idar da sallar isha'i Ahmad gidansu ya nufa, inda ya samu damar…

3,339 words

Koda aka idar da sallar isha'i Ahmad gidansu ya nufa, inda ya samu damar gaisawa da kakanninsa da iyayensa maza, waɗanda yayi mamakin baiji sun rufeshi da faɗan rashin dawowarsaba, dukda yayi tsammanin hakan kuwa, ko baba baice dashi komaiba akan hakan. Yanzun kam har ɗaki ya shiga ya samu gwaggo ya sake gaisheta, duk da bata sake masaba sai da ta jero masa tambayar ya hanya da sauransu. Yaji daɗin kulawarta, dan haka ya amsa yana faɗaɗa fuskarsa da fara'a. Ba tare data kallesa ba tace, "Kai yanzu nan kana ganin abinda kayi mai ƙyaune? Ka tafi kabar ƴar mutane har tsahon wata shidda? Kana ganin inda badan gida bane iyayenta zasuyi shiru su zuba mana idanu?". "Nasan ni mai laifine Gwaggo, amma dan ALLAH ku gafarceni, wlhy inda ALLAH yay zaman nawa mai nisane, sannan harna kwashe kusan watanni uku bana fuskantar komai a sana'ar tawa, saboda bada jari najeba, lokacin ko kuɗin motar dawowa aikine a gareni, amma insha ALLAHU bazan sake kwatanta hakanba, kuma ALLAH ya huci zukatanku, itama zan bata haƙuri na kuma nema gafararta". Shiru gwaggo tayi kamar bazata amsashi, sai kuma zuwa can tace, "Shikenan, ALLAH ya yafe mana baki ɗaya, abu na gaba shine karnaji wani abu daban agareka cikin hidimar bikinnan, babu ruwanka da sabgar yarinyarnan komi zasuyi, ka kama kanka ka kama girmanka, suma su Mudanseer ka sake gargaɗinsu akan karnaji karna gani". "Insha ALLAHU gwaggo an wuce wannan wajen yanzu, babu wani abu saɓanin mai daɗi da zakiji, ni yanzu babu wani abu daya shafeta da yake a gabana sam". "Hakan ya fi". Gwaggo ta faɗa a taƙaice, daga nan shiru ɗakin ya ɗauka babu wanda ya sake cewa uffan a cikinsu, shi dai Ahmad badan hirar ta ishesa bane, haka ita gwaggon, tadaiyi shirune saboda dama tun fil azal babu irin wannan sabon na doguwar hira a tsakaninsu. Kusan mintuna biyar saima ta miƙe ta fice tabar masa ɗakin gaba ɗaya. Sassanyan murmushi yayi yanajin ƙaunar mahaifiyar tasu cikin ransa, maimakon tace ya tashi yaje, shi yaga ta koresa shine ita ta bar masa ɗakin dan kar ace ta saka ɗan fari a ɗaka suna hira. Kai shikam bazai yarda Rumana taima ƴarsa ko ɗansa na fari wannan abunba gaskiya, dan kuwa akwai cutuwa, yanzu shi badan gwaggon ta samu Ayyah mai ƙyaƙyƙyawar zuciya ba da yaya kenan?. Miƙewa yay yaje ya haye gadonta ya kwanta kamar yanda yakeyi a ɗakin Ayyah. Gwaggo dake tsakar gida tana ƴan kaye-kaye saboda ganin hadari sai zuba ido take taga ya fito amma shiru, gashi Ayyah na sashen baba saboda yau itace da girki, yaran kuwa duk sun fice wajen kamu sai Zainab kaɗai a gidan itama tana sashen su Samina. Ɗakin ta dawo dan taga mi yakeyi a ciji da bazai fito ya tafi gidaba gashi har goma tayi, dan taskar labaraima akeyi a redio. Sosai mamakin ganinsa saman gadonta ya kamata, dan sam koda yana yaro ba ɗabi'arsa bace hawar mata gado, sai da ɗakin Ayyah. "Kai lafiyarka kuwa? Wace irin ɗabi'ace wannan?". Dariyace taso kufcema Ahmad dako motsi baiyiba, amma sai ya daure ya haɗiye da ƙyar yana faɗin "Oh gwaggo bakiso na hau sai ƴaƴanki kawai su Mudan? To nima ai suna hawa gadon ɗakinmu idan sun shiga shiyyasa na rama, kuma wlhy ki tambayi Ayyah kiji". Ayyah dake tsaye bakin ƙofa ta kwashe da dariyar shaƙiyancin Ahmad, "ALLAH ya shiryeka ɗan albarka, ammafa kamin dai-dai, maza ka rama mana kuwa muma hawar mana gado da ƴaƴanta keyi ehe". "Yauwa Ayyah ta, shiyyasa kike burgeni akan faɗar gaskiya". Harara Gwaggo ta bankama Ahmad tana cije baki, "Tashi ka fitarmin a ɗaki fitsararren banza kawai". Kasa daurewa Ahmad yay ya sakko yana dariyar yanda Gwaggo ta haɗe gabas da yamma kamar zata makesa, yayinda Ayyah ke tayashi daga waje tana faɗin, "Kaga fito kama tafi gida karta makemin kai daga dawowa". "Aifa ganinan Ayyahna". Gwaggo dai bata tanka musu ba, duk da tana jiyosu suna mata dariya a tsakar gida har su Fa'iza suka shigo. Haɗe fuska Ahmad yay yana kallonsu, dukansu sunsha jinin jikinsu duk sai sukai tsaye suka kasa ƙarasowa. "Daga ina kuke a wannan lokacin!?". Tuni jikin Sadiya ya fara ɓari, hakama Salima uwar tsoro, sai Fa'izace cikin ƙarfin hali tace, "Yah Ahmad wajen kamu". "Kamu?, har zuwa wannan lokacin da yake baku da hankali?". Guri ɗaya duk suka cure saboda tsawar da yay musu. Ayyah tace, "Wlhy nima tun ɗazun abin ya dameni, babanku ma sai faɗa yakeyi, namazo ne nai maka maganar kozaka tura Abu yaje ya kirasune". Sosai ran Ahmad ya ɓaci, yace, "Okey sabon iskancin da yazo muku a kai kenan saboda bana gidan?". "Wlhy A'a yaya, dan ALLAH kayi haƙuri bazamu sakeba". Mudan dake shigowa ta bayansu ya tallare ƙeyar Sadiya dake farko shima yana masifa, "Yah Ahmad karka wahal da kanka ai tun acan saida na basu maruka bibbiyu marasa mutuncin". "Oh kace kainema kaje ka taho dasu?" cewar Ayyah. "Wlhy kuwa Ayyah, tun kusan takwas nake zuba idon ganin sun dawo amma shiru, har tara shiyyasa nai azamar ƙarasa ɗinkin danake nabisu har can, sun miƙe ƙafafu sam basuma da alamar tahowa". Ƙwafa Ahmad da takaici ya isa yayi, ya nunasu su duka yana faɗin, "Wlhy daga yau wanima cikinku ya sake zuwa fatin saina kusa halakashi a gidannan, ƴan iska kuwuce kuba mutane waje kawuna kamar sheƙar angulu". Da gudu suka shige ɗakin Gwaggo dake saurarensu daga ciki, babama duk yana jiyosu, ya kumaji daɗin yanda Ahmad da Mudanseer sukai musu, baida haufi akan tarbiyyar ƴaƴansa, koda baya numfashi su Ahmad garkuwar ƙannen sune.

Ganin iskar hadari ta fara tasowa Ayyah tace, "Ɗan albarka maza gida kafin wannan ruwan ya sakko kaji, ka gaida ɗiyar tamu". Sallama yay musu ya tafi, bayan ya leƙa yayma su Iya ma sallama, wadda ta bashi wani abu a robar swan tana faɗin, "Ungo wannan ka kaima Rumana, tashashi yanzu kafin ta kwanta". "To Uwargida ran gida za'a bata ta gode, amma minene haka kamar zuma?". "To shugaban matambaya ba zuma bace, maganin shawarace da naji su Salima nata ƙorafin bata gajiya da kwanciya, shiyyasa na haɗa matashi kartazo wajen taron nan taita langaɓe-langaɓe, tasha kamar kashi ɗaya bisa huɗu". Dariya Ahmad yayi yana cewa, "Oh kajimin iya, kina nufin matata raguwace dai kawai a fakaice?, karki damu nan gaba kaɗan ƙofar gidannan saita mata kasaɗan". "Dako nayi farin cikin hakan ɗan ƙwal uba kawai, kaima ai gakanan ka ɗakko sanwar fara kiban kamar iliyasu". Fita Ahmad yay yana dariya Malam dake kwance yana tayashi.

A waje yay sallama da abokansa dake shirin shigewa gidajensu, ya tari Napep zuwa gida saboda harma an fara yayyafi. A lokacinne kuma motocin su Samina ke isowa, da alama dai lokacin aka tashi daga kamun nasu da yasha banban dana saura. Dan kowa dai yasan da yamma ake kamu tare da dangin amarya, dangin mijima ƙalilan suke zuwa, to ita nata dangin mijin sunfi yawa, danginta ɗaiɗaikune iya ma ƴan uwan mama gaje ne, sai tarin ƙawayenta.............✍🏻

_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_

_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279 _MARYAM SANI_ _ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇 *07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_

Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻 [7/27, 6:06 PM] Sis Hajiyyaye: *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo

*_GDW_*

*(19)*

..............Tun su baba na saka ran dawowar Ahmad a kusa har abin ya fara basu tsoro, dan kuwa gashi ya shiga wata na huɗu da tafiya.

Wata ranar alhamis Ahmad ɗin ya shiga wani shago na masu sai da yari, saboda kiran da mai shagon yay masa zai wanke masa takalmi, dan yanzu ya gama sanin gari ba tare suke yawo da Nura ba, kowa yana fita neman nasane, da yamma su haɗu a inda suke zama, zuwa dare su wuce wajen gadinsu. Tunda Ahmad ya zauna wanke takalmi mai shago ke binsa da kallon ƙurilla, tun Ahmad bai fahimta ba harya fahimci kallon da mai shagon ke binsa dashi. Ɗan ɓata fyska yay, hakan yasa mai shagon yin murmushi, yace, "Na dameka da kallo ko? kayi haƙuri, mamaki nike kamarka fine Boy da wannan sana'ar". Ahmad dai baice komai sai murmushin yake da yay, harya kammala ya tattare kayansa zai wuce mai shago ya mika masa ɗari biyu yana faɗin, "Inda zaka yarda dana koya maka wannan sana'ar tamu ta yari?". Shiru Ahmad yay yana kallonsa cikin nazari, Mai shago ya sake cewa, "Karka zurfafa tunani ƙanina, haka kawai haɗuwar jini ta sakani maka wannan maganar duk da kuwa yauce rana ta farko dana fara ganinka, amma dai kamin kamanni da bakatsinen barume hakanne ya sakamin ƙaunarka ta musamman, idan har ka aminta zakayi na baka dama ka samo jarinka kazo insha ALLAHU zan taimakeka". Kai kawai Ahmad ya jinjina ya fita bayan ya amshi kuɗinsa. Koda ya koma ya sanarma Nura sai yay murna, yakuma bashi ƙwarin gwiwar karɓar tayin Alhajin, dan acewarsa wata damace dasu basu samuba tazo masa dukda bai jima da zuwa garinba kuwa. Amma maganar jari ya jira wanda sukema gadi ya biyasu sai yayi amfani da kuɗin. Ahmad yaji daɗin shawarar Nura, dan haka ya aminta sosai, washe gari yaje ya sanarma Alhajinnan komai, Alhaji ya amsa da babu komai shidai yana jiransa. Kwanaki goma dayin haka suka jira a basu albashi shiru, har haƙurinsu ya ƙare sukaima mai wajen magana, amma ƙiri da muzu ya hanasu yama yi musu korar kare. Wannan abu ya saka su Ahmad a takaici, harya hanasu talla a wannan ranar sukai yinin baƙin ciki. Da abokansu suka dawo daga tasu sabgarsu suma sai suka sanar musu, suma ransu ya ɓaci, nanne wani ke basu shawarr idan zasu iya aikin sauke kaya suzo suje, shi mutumin kullun yake biya adadin kuɗin aikin da kayi. Da farko Ahmad ya musa, amma da Nura ya lallashesa saiya yarda washe gari sukaje. Wajene kamar kamfani, ana kawo kaya sukuma za suke jigilar saukewa daga motar zuwa store. A sati ana sauke kayan sau biyar ne. Duk da wahalar dake cikin aikin haka Ahmad ya dage, bayan sun kammala na ranar kuwa aka biyasu haƙinsu, sunsha ciwon jiki saboda rashin sabo, dan daƙyar sukai barci ranar, amma daɗin kudin da aka biyasu ya saka washe gari suka sake komawa. A hankali sai gasu sun zama ƴan gida, dan kuwa harma sun saba komai anayi dasu na harkar dako a ma'aikatar. Duk kuɗin da suka samu Ahmad kan kai nashine wajen Alhajin nan yana tara masa, a randa suka cika sati na huɗune kuma sai kawai ogan wajen ya basu sanarwar duk wanda yazo gobe yaga sunansa an kafe to karya sake zuwa aiki, an koresa kenan Hantar cikin su Ahmad ta ɗuri ruwa, dan kuwa suna samun alkairi a wajen babu laifi. Washe gari duk a cikin damuwa sukazo, sai yazam gaba ɗaya waɗanda aka cire hausawan ne, kukane kawai Ahmad baiyiba, suna shirin tafiyane kuma matar mai gidan ta dakatar da Ahmad, acewarta wanan ƙyaƙyƙyawan babu inda zaije, dole ogan ya maida sunan Ahmad kuwa. Duk da yaji dadi ya nuna damuwarsa na rashin Nura, haka ya cigaba da aikin har tsawon sati huɗu sannan ya bari saboda yaga dai Alhmdllh yaɗan tara wani abu da zai ishesa jari. Lokacin da zai wucene sai matar ogan ta nuna rashin jin daɗinta, hakan yasa tai masa tayin gadi a gidansu, zasu kuma bashi ɗakin mai gadi ya zauna. Nanma bai bata amsaba sai da yazo ya shawarci Nura, Nura kuwa ya bashi kwarin gwiwa akan hakan. Ahmad bai amsa zaiyiba sai da ya koma wajen Alhaji aka fasa asusun kudinsa na dako da ya tara Alhaji ya haɗa masa kwabar ƴan kunne ta hannu, aka zuba kaya dai-dai kuɗinsa sannan, ya bashi tare da sanar masa dabaru akan sana'ar. Daganan kuma ya koma ga ogansa ya sanarma matar zaiyi gadin, amma zaike zuwa sana'arsa da rana. Babu musu suka amince, a cewarsu aiba zaman gidanma sukeba da ranar. Tundaga wannan ranar rayuwa ta sake sauyama Ahmad, dan kuwa a cikin watannan gaba ɗaya saiya cinyesa a yawon tallar ƴan kunne da gadi, koda ƙarshen wata yay yaga yaɗan farfado sai ya fara tunanin zuwa gida, lokacin yanada wata shida cif a garin porthercout. Babama har yayi fushi da rashin zuwansa ya haƙura yabar masa magaba. Tun daga randa yay aniyar zuwa gida yaɗan fara sayen tsaraba yana ajiyewa wadda zai fuskanci gida da ita, haka kawai kuma sai yakejin ɗokin ganin Umm-Rumanan sa.

_________________________________

Zuwa wannan lokacin maganar Ma'aruff ta shiga gidansu Samina, yayinda alakarsu ta sake ƙazanta sosai, dan tunda aka tsaida bikinsu wata biyu kacal sai yazam babu abinda Ma'aruff ke burin samu daga gareta sai jikinta. Har takai dai yau yaci galabar rabata da budurcinta a gidan gonarsa, tasha kuka iyakar iyawa, shiko ya katsatstsareta da lallashi da daɗin baki akan ai babu komai tunda shine zai aureta, kuma bikin nasu duka saura wata ɗaya ne kacal ai. Tun tana kuka da ƙarfin zuciya har ta aminta da daɗin bakinsa, ya tainaka mata ta gyara jikinta, tare da saka abokinsa ya kawo mata magunguna da allurar rage raɗaɗi, ya kuma kaita Shop rite yay mata shopping na hauka da bai taɓa mata irinsaba, ya maidota hargida tare da bata maƙudan kuɗi. Mudanseer dake shago Shi da Abu yana kallon yanda Ma'aruff keta saukema Samina kaya niki-niƙi, baki kawai ya taɓe ya ɗauke kansa danshi yanzu babu abinda ya damesa da ita. Maimakon lokacin da aka shiga da kayan Mama gaje ta fahimci halin da Samina take ciki sai idonta yafi karkata ga manyan ledojin. Duk uwa mai hankali aka taɓa mata yarinya, kuma yarinyar ta dawo gareta a randa abin ya faru dolene ta fahimci akwai matsala, dan duk macen da aka raba da budurci komai tsahon shekarun da take dashi babu aure wlhy sai taji daban, idan ko babu aurene fargabar fara yinta bata hanyar daya daceba koda itace takai kanta saikin sameta tattare da ita, iyaye kalubale ne agareku, dan yanzu har sai ƙaton banza ya gama lalata miki ƴa a waje ta ɗau ciki ta zubar bama ki saniba saboda sakaci da sakarci kosan duniya irin namu. Da wannan damar rashin kulawar tamu samari keta lalata yara ta yanar gizo da zahiri ba tareda kun fargaba, damuwarki kawai ki gyarama mijinki kanki dacin kwalliyar tafiya biki domin ki birge mata ƴan uwanki, idan kishiyace dake hankalinki na kanta, saikiga ƙanin uban yarinya ko ƙaninki ko wani na kusa daku ya gama warware tufkar tarbiyyar da kukayi kina nan shatata da baki, sai rashin mutunci ya saka saurayi sakin videon baɗalar da yay da ƴarki a yanar gizo ki haukace har takaiki da faɗawa wani hali ki kamu da ciwon hawan jini kona zuciya, bayan kuma kinbar gini tun ran tubani. A tunanina duk uwa datasan ƴarta budurwa nada wayar yakamata tazam mai saka mata idanu akan wayar, kodama bata da ita ki saka mata ido tunda akwai ta ƙawaye. Tanan suke shiga yanar gizo su haɗu da ƴan iskan facebook, ko istagram, ko litatafan batsa dake yawo a kowacce irin kafa ta yanar gizo, ko ƙawa ta sakata a group da sunan group ɗin matan aure wanda idonsu ya rufe basajin tsoron ALLAH duk abinda yake haramun shine abun kallonsu, wanda yake haramun shine abin furtawarsu da jinsu a zuwan wai koyan rayuwar aure, ke wane kidahumancin ya baki tunanin sai an ɗakko shaiɗancin tsiraicin wani kin ganine zakisan yanda zaki rayu da mijinki?, wlhy matan aure kaiconku da wannan wawancin mai toshe ƙofofin hasken zuciya da kashe gani. Ƴammata da yawa daga shiga irin waɗannan groups suna canja suna komai ke fara tabarɓare musu, idan k uwa baƙya bibiyar lamarinta daga haka sai kiga komai da kika gina ya tarwatse. Wlhy kuzama masu kulawa kafin ku riski ranar kuka da nadama akan ƴaƴanku, domin sai ALLAH yay miki tambaya dalla-dalla akan tarbiyyarta. Wannan sakacin ne ya hana Mama gaje fahimtar komai akan Samina har Ammin su Umm-Rumana ita ta lura, ba ƙaramin ruɗani ta shigaba, sai dai tana tsoron tace wani abu aga zaƙewarta. Samina kuwa kwanciya tai wahala ta sakata barcin dole, bata tashi farkawaba sai bayan sallar magriba, agaban mama gaje ta dafa ruwan zafi taje tai wanka dashi ta sake gasa jikinta kamar yanda taga ana cewa a novels, koda ta fito sama-sama taci abinci ta sake kwanciya, kobi takan kayan da mama gaje ta baza a ɗakin bataiba saboda ita tasan wahalar da taci kafin ta samo kayan.

Haka Samina taita jiyyar jikinta har kwana biyu, ko ɗaga wayar Ma'aruff batayi idan ya kirata saboda haushinsa da takeji, amma taji daɗin yanda ya nuna damuwarsa a kanta, sai turo mata massegea yake kamar hauka, wannan yasa a cikon kwana na huɗu ta kulasa. Yako kalailayeta da daɗaɗan zantuka ranar, haryaci galaba a kanta tafito makaranta taje Office ɗinsa ta samesa, acan yakuma lallaɓata ya ƙara na biyu, ranarma taci kuka dan tasha wahala, amma daya lallaɓata da mayaudaran kalamanasa saita goge hawayenta saboda ta yarda dashi. Tun daga wannan ranar ya maidata kamar wata matarsa, a gefe kuma yanata sakar mata kudi itada ƙawayenta suna shirin biki. Sati na biyu da kauda mata martabarta aka kawo lefenta daga gidansu ma'aruff akwati ashirin da huɗu cif, tare da katuwan jakkuna uku manya-manya, ɗaya na babanta, ɗaya na Mama gaje, ɗaya na danginta. Ranar dai kam su Ayyah sunsha kallo, sun kumasha gori wajen mama gaje da danginta, ƴan anguwa kam ai kamar sa fasa gida kallon kaya, harda ƴan gayyar soɗi, dan ko su Maman Ama sai gasu sunzo ganin ƙwaf daga jin su Salima na sanarma Umm-Ruman cewar gobe za'a kawo lefen Yaya Samina. Shine mutanenku sukai shiri Rumana bata saniba sukazo wai yimata kara tunda ita har yanzu bata fara zuwa gidaba baba Yusha'u ya hana, yace tai zamanta har Ahmad ya dawo ya bata izinin hakan, makaranta kawai take fita, shima kuma jarabawama suke zanawa ta ssce. Ranar su Nafy ƙawayen Samina haka sukaita yawo da wannan lefe a social media, yayinda ya tadama ƴammata da yawa hankali da fatan suma sai an musu irinsa koma wanda ya fisa. Harda masu takaicin inama sune, irinsu Kausar. Koda sukaje suna bama Rumana labari tasha mamaki, dan ita bama ta kawo can sukajeba, amma sai batace dasu komaiba akan hakan dukda taji haushi.

_________________________________

Baba ne ya gindayama Ahmad sharaɗin ya tabbatar yazo gida anyi bikin Samina dashi, tunda shine namiji babba a gidan bai ƙyaitu ace baya nanba. Dukda baiso hakaba dole yabi umarnin baba, tunda yanzu dai Alhmdllh, duk da bawasu maƙudan kuɗi ya samuba babu laifi tafiya tai riba, dama kuma ya gama shirinsa tsaf.

★★★★★★

Umm-Rumana duk da bata da tabbacin zuwa gidan bikin haka ta wanke kanta Salima ta yarfa mata kananun kitso, suka kawo ƙawarsu har gida tai mata ƙunshi mai ƙyau, haka kawai ta tsiri juya fasalin ɗakinta. Tako tsare su Fa'iza suka tayata, komai suka canja masa muhalli ya koma kamar wani sabon ɗaki, aranar kuma su Samina ke shirya fatin ƙunshi a wani haɗaɗɗen hotel tsadajje. Su Fa'iza duk sun gudu sunbarta ita kaɗai a gidan, dan haka bayan tai wankanta tai kwanciyarta tana kwasar barcin gajiyar aikin da sukayi.

★★★★★★

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull