Kenza eBookz

Gudu da waiwaye bilyn abdul - Chapter 18

Gudu da waiwaye bilyn abdul - Chapter 18

Gudu da waiwaye bilyn abdul Chapter 18: Gudu da waiwaye bilyn abdul Chapter 18. Ƙarfe kusan huɗu su Ahmad suka iso cikin garin kano, ya jigatu sosai saboda…

3,372 words

Ƙarfe kusan huɗu su Ahmad suka iso cikin garin kano, ya jigatu sosai saboda tafiyar dare sukayo, tun a tasha sukai sallama da Nura da shima yazo ganin gida, ya loda kayansa a napep ɗin da yay shata suka nufi gida. Ƴammatane danƙam da ƙofar gidansu, ga galla-gallan motoci sun jeru domin kwasarsu zuwa wajen kamu. Mai napep ya samu ɗan wajen maƙalewa yay fakin. Kallo ɗaya Ahmad yayma motocin ya ɗauke kai, dan koba a faɗa masaba dai yasan ƴan bikine. Yana fitowa idon Mudan dake ɗinki a shago ya sauka kansa, cikin matuƙar mamaki ya fito, dan babu wanda yasan da dawowar Ahmad ɗin sai baba. "Yah Ahmad!" Abu ya faɗa da ƙarfi shima tare da sakin butar da ya ɗeboma Mudan ruwa daga cikin gida, sheƙawa yay da gudu ya koma dan kai rahoto. Kafin kace mi yara sun zagaye Ahmad anata murnar ganinsa suna kwasar kaya zuwa cikin gida, hakan ne ya sakashi farin ciki, inda kuma hankalin ƙawayen Samina ya dawo kansa, dan kuwa su Nafy tuni sun fara rattafo labari akan da shine zai auri Samina ai. Da yawansu ƙyawunsa ya ɗau hankalinsu, sai dai sunce rashin ƴan canji ya kwafsa masa. Ahmad da baisan mi sukeba tuni ya nufi cikin gida riƙe da hannun Mudan suna dariyar tsokanar da mudan din ke masa akan yayo ƙiba kamar ba shiba. A ƙofar soro sukai karo da Samina da taci ado cikin wani arnen farin les, ƙawayensu kusan biyar na tare da ita, da alama dai zasu fita ne domin a kaisu wajen kamun. Kallo ɗaya Ahmad yay mata ya ɗauke idanunsa yana cigaba da murmushinsa da ya ƙara haska choco color ɗin fatarsa mai ƙyalli ta asalin rumawa. Haka kawai Samina ta samu kanta da faɗuwar gaba, tuntuɓe tayi zata faɗi ƙawayentan sukai saurin tarota, da kallo ta bisa har suka ɓacema ganinta, sosai taga ya canja mata duk da ma babu kwalliya tare dashi, dan wandon jeans ne da t-shert mai gajeren hannu a jikinsa, duk rigar ta yamutse alamar sunsha zaman mota. Siririn tsaki taja tana faɗin, "Ɗan wahala kawai" a fili. Mutum biyu a ƙawayen nata da sukasan komai suka kwashe da dariya kuwa, suma idonsu a kansa, sai daifa harga ALLAH sun yaba da wannan ƙyaƙyƙyawar halittar. A cikin gida kam an rikice da dawowar Ahmad, harma ya rasa sannu da zuwar wazai amsa, ƴan uwansa da yaran anguwa duk sun zagayesa, kunsan yaro dason adawo daga tafiya a bashi tsaraba koda ta biredi ce😂. Fahimtar hakan da Ahmad yay ya sakashi jan ledar biredi ɗaya ya miƙama Sadiya data ajiye masa ruwa yace ta raba musu. Aiko kowa yana samu aka bashi sai ya fita cike da ɗoki kai rahoto gidansu. Bakin Ayyah gaba ɗaya yaƙi rufuwa, ta kasa zaune ta kasa tsaye, Gwaggo kuwa babu mai cewa ga yanayinta, sai dai cikin ranta ita kaɗai tasan sanyin da takeji na dawowar Ahmad ɗin. Bayan yasha ruwa suka gaisa da mutanen da suka shigo ƴan biki masa sannu, wasuko dai ƴan son ganin ƙwaƙwaf ne. Bayan an gaggaisa suka fita, shima sai ya samu gaisawa da nasa iyayen da ƙannensa. Yana shirin kishingiɗawa a tabarmar da aka shimfiɗa masa Ayyah tace, "Ɗan albarka badai anan ba, maza tashi ka wuce wajen matarka ka huta acan". Cikin shagwaɓa ya narke murya yana faɗin, "Kai Ayyah na, nifa kamarma kin daina sona nake gani?, yanzu abincimafa kince bazaki bani naci ananba". "Aiko wlhy ban baka, gashi dai zan zuba a kwano auta tazo ta bika dashi gida kaci acan, maza tashi, baiwar ALLAH ai tayi haƙuri ƴarnan". "To Ayyah zan tafi, amma ki bari mu gaisa da baba to". "A'a idan ka dawo anjima kwa gaisa, dan malam ma baya nan kusa yaje Dawanau ne". Dole Ahmad ya miƙe domin bin Umarninta, jakkar kayansa kawai da jakka ɗaya da leda ya ɗauka, sauran kayan kuwa duk nan aka barsu a ɗakin Ayyah kamar yanda yace su Sadiya su shiga dasu. Shi kuma Mudanseer ya ɗauka kayan ya fito ƙofar gida domin tarar napep. Su Samina amare har an wuce, sai abokan Ahmad dake jiran fitowarsa. Nanma fa wata sabuwar murnarce ta sake kacamewa a tsakanin abokan amana tun ƙuruciya, da ƙyar Ahmad ya ƙwaci kansa akan zaije ya kimtsa ya dawo. Ya shiga napep ɗin da mudan ya saka masa kayansa suka wuce.

Cikin barci naji muryar Zainab na faɗin, "Yaya Rumana ki tashi ga Yah Ahmad ya dawo". Da ƙyar na iya buɗe idanuna saboda ba ƙaramin barci nayiba ashe, ganin Zainab zaune kusa dani ya tabbatar min da ba mafarkin dana saba yi bane. Tashi nai zaune sosai, sai kuma na miƙe zumbur jin muryar Yah Ahmad dake amsa gaisuwar su maman Ama. Kasa haƙuri nayi, na nufo ƙofa domin tabbatarma kaina. Sai dai ashe ya kawo jiki zai shigo sai mukai karo harna bige kaina a ƙirjinsa, nai baya zan faɗi yay saurin ruƙomin hannu..............✍🏻

_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_

_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279 _MARYAM SANI_ _ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇 *07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_

Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻[7/28, 1:22 PM] Haleemat M Musa: https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo

*_GDW_*

*(27)*

..............Jini sosai ya ɓallema Samina, abinda ya tsorata su Ma'aruff kenan suka ɗauketa zuwa asibiti, gaggawar fara ƙoƙarin shawo matsalar Aliyu ya farayi, da ƙyar aka samu komai ya dai-daita bayan baƙar wahalar da yasha. Ma'aruff sai jan tagwayen tsaki yakeyi, ya kasa zaune ya kasa tsaye har sai da Adam ya fito sannan. Kwantar masa da hankali yayi akan an samu dai-daiton komai, yanzu haka zasu kai Samina ɗakin hutune. Numfashi ya sauke a hankali, sai lokacinne ya tuna da batun aikinsa, waya ya ciro yay kira Mama gaje ya sanar mata akan tazo asibitin ta samesu. Hankalinta ya tashi sosai, da yake batasan ina zata gano asibitinba saboda private ne sai ta tasa ƙanin Rumana gaba Kamalu suka tafi dan ya rakata, bata sanarma kowaba saboda a ƙofar gida ta gamu da Kamalun ta iza ƙeyarsa suka tafi. Koda suka iso suna gaisawa da Ma'aruff ya kaita ɗakin da aka kai Samina sai yay mata bayanin ɓari Samina tayi, daga haka yay musu sallama ya tafi akan shi zaije Office ne saiya dawo. Yanda Samina ta rame ya tadama mama gaje hankali, amma data tuna ɓari akace tayi saita danganta ramar da kwaikwan ciki, sai dai a ƙasan ranta tana mamakin miyasa Samina bata taɓa sanar mata ta samu cikiba koda wasa? Yanzu kuma auren sati uku ne har an samu cikin da zai iya zubewa?. Batai zurfi a wannan tunaninba ta watsar da shi gefe kawai ta ɗakko wani. Kamalu shine ya koma gida ya sanar musu Samina na asibiti babu lafiya, kowa yasha mamaki, amma da yake ba biyema shirmen mama gaje sukeba sai sukai shirin zuwa su dubata. Yayinda yaran gidan suka fara tafiya kaima yayyensu na ma'auri labarin.

Harsu Ayyah sukazo duba Samina asibiti tana barci bata farkaba, kowa yayi mamakin ganin ramar da Samina tayi a sati uku da aure kacal, hakama zancen ɓarewar ciki ya tsayama kowa a rai. Ammi ce kawai data daɗe da fahimtar Samina nada shigar ciki tun tana gida abun bai bata mamakiba, sai dai tana tausayin mama gaje akan ƙarancin rashin kulawa da saka idanu akan yaranta. Basu baro asibitinba sai gab da magriba, har zuwa lokacin kuma babu ko ɗaya daga dangin mijin Samina daya leƙo, shima kansa Ma'aruff ɗin bai dawo ba, sai Inna mari da Iya da sukaje, sai ko dangi ɗai-ɗai irin na kusa da labarin yaje musu suma suka ɗan lalleƙo. Har zuwa lokacin kuma Samina nata barci bata farkaba, su dai sallama sukai musu suka taho akan sai kuma gobe idan ALLAH ya kaimu, dan malaman asibitin sun fara maganar sunyi yawa, da sun tsaya har sai Saminar ta farka suma. Bayan dawowarsu gidane suma su Baba suka tafi duba Saminar, sun isa babu jimawa ne ta farfaɗo. Da ihu da fisge-fisge Samina ta farka, sai ambatar sunan Ma'aruff take akan itafa tanason cikinta karsu zubar mata, babu wanda bai shiga ruɗaniba, su sam sunma kasa fahimtar mi Samina ke faɗa. Dr Adam yace duk su fita daga ɗakin Please. A daidai wannan lokacinne kuma Ma'aruff ya dawo, daka gansa zaka san hankalinsa kwance, kuma daga gida yake, dan bakayan ɗazun da safe banema a jikinsa, babu tausayi ya wankama Samina dake cikin halin rashin sanin mi takeyi mari, "K dan ubanki duniya kike faɗama yanda aikai ne?" Da sauri Adam ya janyesa yana masifa, "Wai kai MJ mike damun kankane? Yarinyar dama batasan ina a hankalinta yakeba kakema wannan Marin? Kaji tausayin halin da muka sakata mana, wlhy badan tanada sauran shan ruwaba a ɗazun zata iya rasa ranta, kai baka da wani abin birgewa sai dukan mace? Wannan fa matarkace ta sunna ba matan banza daka sabama wannan rayuwarba, Mtsoww, baka sha giyarba ma rasa hankalinka ake......" A fusace Ma'aruff ya dakatar da Dr Adam, "Malam karka faɗamin babu daɗi mana, bansan shishshigi kaima ka sani". Banza Dr Adam yay masa, ya shiga ƙoƙarin ganin Samina da numfashinta ke fita da ƙyar bama taimakon gaggawa, dole dai allurar barcin ya sake mata saboda sam bata a cikin hayyacinta, a ƙasan ransa yana dana sanin biyema Ma'aruff akan wannan aikin. Acan waje kuwa su mama gaje na iya jiyo hayaniyar su Ma'aruff, sai dai basajin mi suke faɗa, tuninsu ma duk ruɗewar halin da Saminar ke cikine ya jawo hakan, hakan yasa suma suka sake rikicewa ainun. A fusace Ma'aruff ya fice daga ɗakin, ko kallon su Baba dake wajen dasu mama gaje baiyiba balle su sami mutuncin a gaishesu, su duk ganinsu halin da matarsa ke cikine ya sakashi a ruɗani🥺. Basusan ma yana fita daga asibitin zuwa yay ya tanaji giyarsa ba tare da tsaleliyar budurwa suka nufi gida, tunda yau babu Samina a cikinsa anan zai warwasa abinsa😢.

★★★★★★★★★★★

Ina bakin rijiya zaune ina wankin ƙarfin hali saboda kaina dake mani wani azabar ciwo, gaba ɗaya kwanakinnan haka nake fama da wannan ciwon kai, abinda kawai nasaka a raina basir ne yaymin mugun kamu da malleriya, sallamar yaran gidanmu ta sakani ɗago idanu na kallesu, ni kaɗaice dama a gidan, Kausar taje asibiti wai yaron cikinta na dawo mata a ƙirji, maman Amatullah kuwa tana gidansu sunan ƙanwarta data haihu, su Fa'iza kuwa tun da safema suka tafi gida yau. Sallamarsu ta amsa fuskarta dai babu walwala. "Ku kuma daga ina? Da wannan tsakar ranar khadija?". "Yaya Rumana daga gida mukefa, Yaya Samina ce bata da lafiya tana asibiti". Ajiye hijjab ɗin danake cuɗawa a cikin ruwan kumfar nai ina faɗin, "Ya salam, miya sameta haka?". "Muma bamu saniba, amma dai su Ammi ma duk sunacan sunje dubata". "Wayyo, to ALLAH ya bata lafiya, zan kira Yah Ahmad kuwa nasamu zuwa anjima naje na dubata". Haka Rumana ta cigaba da wankinta su khadija na tayata da hira, duk da ma ita ba saka musu baki takeba dan kanta dake ciwo, da yake wankin baida yawa dan danan ta kammala, tana share ruwan wajen Kausar ta shigo tana ɗaga ƙafa da ƙyar saboda ciki, duk da yanzu bata min magana hakan bai hanani mata sannu ba. "Uhumm" kawai tace min ta buɗe ɗakinta ta shige. Ban damuba, nima na haɗa robobin danai wankin na nufi nawa ɗakin, muna shiga na bama su Khadija kantu daya rage a kayan sana'ata nace suje gida kar'a nemesu, dan nagaji da surutunsu nikam. Da murna suka amsa suka wuce, nikuma na shiga duba magani dan nasha sai dai ma ashe ya ƙare, ƙaramin tsaki naja na haye gado na kwanta kozan samu sassauci.

Ring ɗin wayartane ya tasheta daga nannauyan barcin datai nisa a ciki, ta kai dubanta ga agogon ɗakin tana ƙoƙarin lalubo wayar a ƙasan filo. Ƙarfe biyar na yamma, agogon ya nuna, tashi nai zaune a rikice dai dai na gama ciro wayan, Yaya Ahmad ne, kafin na ɗagama ta tsinke. Ina ƙoƙarin sakkowa ya sake kira, dakatawa nai na ɗaga ina kaiwa kunne. "Kina lafiya kuwa? Tun ɗazun nake kira amma babu amsa". Cikin yanayin wanda ya tashi a barci nace, "Kayi haƙuri Yaya, wlhy barci nake". Daga can yace, "Barci kuma? Lafiya dai ko?". "Lafiya ƙalau, kaina ne kawai kemin ciwo dan wankima na gama".. "Na rasa wannan ciwon kai na miye haka? Kusan kullum yanzunfa sai kinyi?". "Wlhy kuwa Yaya, amma karka damu inaga basirne, zan aika iya ta bani magani". "ALLAH ya ƙara sauƙi, yanzu kinsha magani ko?". "A'a maganin ya ƙare, jira nake anjima idan Yah Mudan yazo sai ya sayo mani". "Bara kawai na kirashi sai ya kawo miki yanzun, ina zama da ciwo yaga daɗi". "To Yaya na gode, itama Yaya Samina ma bata da lafiya". Shiru yay kamar bai jitaba, hakan yasa tai tunanin baijinba ta sake maimaita masa. Cikin halin ko in kula yace, "ALLAH ya ƙarama kowa lafiya". "Amin yaya, ammafa abin serious ne fa, dan tanama asibiti, na shirya naje na dubota dan ALLAH?". A hasale yaja tsaki yana faɗin, "Malama kiji da naki ciwon kinji, inada abunyi sai anjima" ƙit ya kashe wayarsa. Shiru nayi a wajen tamkar ruwa ya cinyeni, na zame wayar a hankali ina kallonta kamar zan hangosa ta ciki, dama tun jiya nasan haushina yakeji saboda su Fa'iza sunce zasuje gidan Yaya Samina, nima saina tambayesa dan naje nagano ɗakin amarya daga nan mu wuce gidan sunan ƙanwar maman Ama da akeyi. Aiko naci masifa, dan Yah Ahmad na asali dana sani ya komamin, tamkar zai jawoni daga wayar ya daka, daga ƙarshe ya kashe wayarsa ma baki ɗaya, na gwada kira yafi sau hamsin amma switch up, ni kuma yanzu sam banyi zaton abin zai ƙara ɓata masa raiba tunda dai ciwo akace. Damuwa fal raina na tashi na fita, dan ko sallar la'asar banyiba, tsakar gidan shiru kamar babu mutum, dama dagani sai Kausar ne, mai raya gidan maman Ama ce kodan saboda ƙiriniyar yaranta. Bayan na idar da salla na ɗauki waya na kirashi, amma harta yanke bai ɗagaminba, na kuma kira ban gajiba, sai da na jera masa kira goma sannan ya ɗaga. A hasale yace, "Ke wai bakisan ina kasuwa bane? Idan kika takura min da maganar nan zan ɓata miki rai wlhy". Bai jira ma mizan ceba yanzun ma ya sake yanke min wayar, hawaye masu ɗumi suka shiga rige-rigen fitowa a idanuna suna silalowa bisa kumatuna, ni bansan lokacin da ya farama Yaya Samina irin wannan baƙar tsanarba? nima dai na shagala wajen mantawa murɗaɗɗen halinsa ne, darajar aurenmu yasa na fara ganin haƙoransa a waje, suma ɗin a wannan zuwan. Zamewa nai na kwanta ina cigaba da hawayena.

Sai bayan isha'i yau su Salima sukazo, dan sune ke a gidan saboda su Ammi sunje duba Yaya Samina a asibiti. Yanda suke bani labarin halin da Yaya Saminar take ciki sai tausayinta ya kamani, na mata addu'a dan nasan tunda yace bazan jeba to bazanje ɗinba, dan sunan ƙanwar Maman Ama da yace bazanjeba jiya gashi banje ɗinba. Sai da zan kwanta ne danaga har lokacin bai kiraniba nai masa text message na ban haƙuri da kalamai masu sanyi na tura masa. Haka na kwanta cikin damuwa, da ƙyar barci ya ɗaukeni kuwa, dan ya sabamin duk dare ko bazamuyi hira mai tsaho ba dai zamu gaisa yaji lafiyata naji tashi kafin na kwanta.

Da safe ko da su Fa'iza sukace na shirya muje dubota, canai musu suje kawai banajin daɗi, danma karsu zargi wani abu sai nace jiri nake gani. Sannu sukaita jeramin kafin su wuce, nace suce ina gaisheta dan ALLAH. Bayan wucewarsu na ɗauki wayata na sake dubawa, a zatona ko zanga reply ɗin Yah Ahmad, amma sai naga wayam, tagumi nayi na zubama wayar ido kawai. Duk da motsin Kausar da nake jiyowa a tsakar gida ban fitaba sai da zanyi sallar zuhur, dan kafin su Salima su wuce komai sunmin har ɗibar ruwa. Banga Kausar a wajeba yanzun, ta shige tuni, na laru dai batajin daɗi kwana biyunnan, ɗakinta na nufa nai sallama, sai da nayi kusan uku sannan ta amsa min, ban damuba na shiga ciki, kwance take a ƙofar ɗaki, ɗakin kaca-kaca babu gyara, na zauna a kujera ina mata sannu da tambayarta yaya jikin?. Nanma da ƙyar ta amsamin cewar da sauƙi. Duk da nima ba ƙarfin nakeji ba haka na tashi na fara kimtsa mata ɗakin, dan yayi datti da yawa, da alama dai tama daɗe batai gyaransa ba, wanke-wanke kansu cike da babbar robarta ta tara, bayan na gyara gadon nace ko zata koma can. Bata musaba ta yunƙura zata tashi amma ta kasa, taimaka mata nai ta miƙe ta koma saman gadon, nikuma na ƙarasa kimtsa ɗakin harda morping duk nai mata, na kwashi wanke-wanken na fita dasu. Har la'asar ina ma Kausar hidima, sai da naga komai yayi fes sannan nace mata ta daure tayi wanka zataji ƙarfin jikinta, kanta ta ɗagamin kafin ta fara jeramin godiya. Nai murmushi da faɗin babu komai karta damu, koda na fito nai alwalar la'asar ɗaki na koma, ban sake fitowa ba sai da Maman Ama ta dawo gab da magriba. Sannu da zuwa nai mata tare da ALLAH ya raya, na kuma bata haƙuri akan rashin ganina da bataiba. Ta ɗanyi dariya tana bina da kallon ƙurulla, "Babu komai Amarya, ai dole nai miki uziri tunda ban saniba ko ogane ya murɗa kambunsa, dan ba kasafai suke son yawan fitarba". Murmushi nai nace, "A'a bama shi bane, kawai dai jiya na yini ne da ciwon kai wlhy". "Ayyah, to UBANGIJI ya ƙara lafiya". Da Amin na amsa ina tsokanar Amatullah dake cin biscuit.

________________________________

Ɓangaren Samina kam sai washe gari ta farfaɗo cikin hankalinta, taƙi magana wa kowa sai hawaye, hakan ya saka Inna mari fara mata masifa akan ai ba kanta aka fara ɓarin ciki ba, idan tayi haƙuri ALLAH ne zai bata wani. Ita dai batace uffan ba, sai da taga ƴan dubiya nata zuwane sannan ta daurema ranta ta daina kukan, sai tsoro ya kamata sosai da lamarin mutane, dan wasu idan akace ɓari tai sukan jinjina maganar, harda masu cewa ikon ALLAH, yanzu cikin sati uku har yakai ai ɓarinsa?. Wannan furuci da mutane ke yawan yi sai ya fara ɗarsama mama gaje da inna mari shakku suma a ransu, ga mamakin rashin dawowar Ma'aruff asibitin, tun daren jiya daya fita cikin fushin abinda Aliyu yay masa su kuma suka ɗauka damuwar halin da matarsa ke a cikine, sai kuma rashin ganin danginsa da basu zo duba Samina ba. Koda mutane suka tsagaita zuwa yamma inna mari kasa haƙuri tai sai da tai maganar rashin dawowar Ma'aruff ɗin da rashin zuwan danginsa. Uffan Sanina dake kwance bata ce ba, duk da kuwa taji mi Inna Mari ɗin ta faɗa sarai. "Wai Samina bakiji mina faɗa bane halan?". Kallo ɗaya Samina tai mata ta janye idanunta gefe, "To idan najiki mizance Inna mari? Naga dai kwance nake anan ta yaya zansan lafiya ko saɓanin hakan". "Kefa dama baki da kunya Samina, daga tambaya minene namin baƙar magana dan rashin arziƙi". Shareta nanma Saminar tayi, saima ta rufe ido kamar mai shirin barci. Har suka kwanta babu Ma'aruff babu dalilinsa..........✍🏻

_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull