Gurbin ido huguma complete - Chapter 25
Gurbin ido huguma complete Chapter 25: Gurbin ido huguma complete Chapter 25. "Kiyi haquri baba,baice yana buqata ba"
4,457 words
"Kiyi haquri baba,baice yana buqata ba"
"Kin taba nuna damuwa ko gwada kaiwar bare ki Fatima hakan?,bari na fito miki a mutum maimunatu" baba tabawa ta fada tana gyara zamanta,abinda ya sanya maimunatu tattara hankalinta waje daya
"Gaba daya na fuskanci inda zaman aurenki ua dosa,bansan na abokiyar zamanki ya yake ba,a gajarce zan gaya miki,ba'a yankewa mutum hukunci ba tare da ka ma'amalanceshi ba,ki sauya,ki zama kamar kowacce mace a gidanta,ki sauke naki hakkin da nauyin,ko meye zai taso a gaba....ko meye zai biyo baya zaki fita a ciki,kiyimin alqawari daga yau zaki canza,inason ganinki kamar kowacce macen auren maimunatu,ina miki sha'awar hakan,na san ja'afar,yana da zuciya me kyau wani abune daban ya canzashi,kuma ina kyautata zaton duk wanda ya aro wani hali da ba nashi ba,rabashi dashi abune me sauqin gaske,zaki canza maimunatu?" Kai ta gyadawa baba tabawa a hankali,tana sake jin nauyi,saboda tana ji a ranta da gasken butulci take son tayi,tana qasan inuwar alfarmarsu,ta samu rayuwa me kyau me cike da gata,sannan ta kasa ciyar da dansu abincin da shine ya siyo shi?,bayan duka duka bata zaman wata biyu ma cikin gidan?.
Da kanta baba tabawa ta shirya abincin cikin wasu sababbin warmers masu kyau
"Dauka maza kikai masa,daga yau babu ruwanki da abokiyar zamanki,duk sanda kika fuskanci yana da buqatar abinci kuma bata nan,bata kuma bashi ba,koda ba ranar girkinki bane dauka ki bashi,ke Allah zai bawa ladan".
Daki ta koma,ta zabo hijab cikin hijabs dinta ta sanya,ba abinda hijab din keyi sai qamsin turaren wuta na kaya,ya kuma amshi fatarta qwarai,kalar blue black,da kallo baba tabawa ta bita sanda ta fito,kamar tace mata ta canza mayafi a maimakon hijab din,amma sai kuma ta canza shawara ta qyaleta.
A hankali ya sauke ajiyar zuciya,sannan ya tura hannunsa cikin sumarsa yana yamutsata,hakanan yaji kawai komai baya maaa dadi,sai yakai hannunsa guda daya ya rufe system din dake gabansa ba tare daya damu da yayi shutting down dinta ba,duk da muhimmancin hakan,sai ya koma a hankali ya jingina bayansa da kujerar da yake zaune,ya kuma hade yatsunsa waje daya yana lumshe idanuwansa.
Wani irin bugu zuciyarta take sanda takai step din qarshe na benan,tana ji kamar ta koma,amma kuma idan tayi hakan bata kyauta ba,kamar ta wofantar da maganar baba tabawa ne,ci gaba tayi da takawa cikin tsoro da fargaba,tana tafiya kamar ba zata kai qofar da zata sadata da ainihin falon ba.
Sanda ta isa qofar sai taja ta tsaya cak,ta runtse idanunta da qarfi,a karo na farko zata fara taka sassansa,batasan da wacce fuska zata kalleshi ba,tsoronsa yana nan fal cikin zuciyarta,tanason baiwa kanta qwarin gwiwa,ta dora hannunta saman handle din,ta runtse idanunta gami da dauke numfashinta sannan ta tura ta sanya kanta.
Daga inda yake zaune miqe da qafafunsa saman table din gabansa idanunsa a rufe yaji an motsa qofar,saidai duk da haka hakan bai sanyashi motsawa ko bude idanunsa ba,a zatonsa unaisa ce,wadda ta gaza haqurin zuwa wajensa da ziyartarsa lokaci lokaci,bayan ya riga daya tabbatar mata gaskiyar abinda ke ranshi gami da bata zabi.
A hankali sassanyan qamshin da ya hanashi sukuni wunin yau,ya kuma wuni dashi cikin jikinsa ya fara cika masa hanci,ya kuma gauraye da sallamarta cikin siririyar muryarta din nan mai dauke da wani amo na musamman,ba tare daya shiryama faruwar hakan ba ya soma bude idanunsa da suka sauya launi saboda mintunan da suka dauka a kulle.
Fes ya sauke idanunsa a kanta,cikin shigar da yawanci shaheedansa ke yinta,shigar da yakan tsokaneta da ita zamanin da suna raye
"I want to see my wife gani na haqiqa..... please madam, remove it" murmushi take jifansa dashi,sannan ta zare din tana fadin
"Am all yours,and belongs to you".
Haka kawai ya samu kansa da gaza dauke idanunsa daga kanta,wani abu na masa yawo tsakiyan kai kamar ana yamutsa kwanyarsa,duk da cikin hijab take amma hoton dazu ke masa yawo cikin idanunsa,ya qureta da kallon dashi kansa yasan idan da ace ita din ba halaliyarsa bace ya kauceea koyarwar addini,baisan me ya sanya masa qulafucin kallonta haka ba.
cikin matuqar juriya da kuma dauriya take bawa kanta confidence,abun dazunke tabata,tana jin kakar qasa ta tsage mata ta shige,ko kuma tayi fiffike ta fice a dakin,ta iso gab dashi kana ta sulale a gabansa ta tsugunna,abinda ya bawa turarenta damar isa gareshi da kyau
"Barka da dare" tayi maganar da wani irin tune,sai ya tashi ya zauna sosai yana sauke sambala sambalan qafafunsa daga saman table din zuwa qasa
"Barka" ya amsata a taqaice,bata tsaya jiran cewarsa ko wani abu ba ta fara fidda warmers din,ya bude baki kaman zaiyi magana kiran jabir ya shigo wayarsa,sai ya maida hankalinsa ga amda wayar,inda ita kuma hakan ya rage mata wani mugun nauyi da takeji an aza mata tun farkon shigowarta falon,rawar da hannayenta keyi suka ragu,ta fidda koma ta kuma yi serving dinsa ta jera komai cikin nutsuwa,sai ta miqe ta fara takawa zata bar falon,cikin ranta cike da fata da addu'ar kada wani abu ya tsaidata.
Dan binta yayi da kallo kadan yana karantar tafiyartata duk da amsa wayar da yakeyi,tamkar wata me tafiya saman rairayi ko yashi mai laushi,duk da bai iys ganin qafafunta saboda hijabin da ya saukar mata,amma kuma yanayin tafiyarta kawai zai gaya maka qafafunta akan tsari suke,janye idanunsa yayi yana jan dan qaramin tsaki,tsakin da ya bayyanarwa jabir ta cikin wayar
"Lafiya?" Ya tambayeshi a taqaice
"No... it's not a matter,ina jinka" yayi maganar yana sauke dubansa ga abincin,wanda tuni yaja ra'ayinsa,bai kuma iya gama wayar ba ya zamo a hankali daga saman kujerar,ya sanya spoon din data ajjiye masa ya diba ya fara ci.
Har cikin ransa yaji nutsuwa da abincin dari bisa dari,dama baba tabawa zabinsa ce akan abinci,don haka duk wani tsohon cinsa ya tashi,yaci abincin sosai fiye da kima,ya kuma kwantar da tsohuwar yunwarsa,haka nan ya dinga jin wata nutsuwa na saukar masa,ba shakka samun abinci gamsashe ma rahama ne,duk wata gajiya da kasala da yake ji fiye da rabinta ta kama gabanta,sai ya samu kuzarin yin aikinsa fiye da dazun,ya sake kunna system dinsa,yaci gaba da nazarin meeting dinsu na dazu wanda tuni PA dinsa yayi documenting komai ya aiko masa,ya dinga cire kusakuran da yayi a dazun,lokaci lokaci yana dan jan tsaki,baisan ya akayi gaba daya dan qanqanin abu irin wannan ya dagula masa lissafi ba,saidai duk da hakan a yanxun ma idan ya tuna sai yaji tsigar jikinsa tadan zuba,yakan dan lumshe idanunsa kadan kana ya bude ya ture komai yaci gaba da aikinsa.
Binta da kallo baba tabawa tayi lokacin da tayi sallama take shigowa falon,sai taci gaba da kallonta baki bude,har ta iso tana zubewa saman kujera
"Wash" ta furta ba tare da tunanin komai ba,ta fadi kalmar ne saboda yadda taji kamar an bubbuge mata gabbanta,uwa uba kuma gudun zuciyarta daya qaru wanda sai a yanzu take qoqarin sai saita kanta.
Hijabinta ta zare ba tare data lura da kallon da baba tabawa ke binta dashi ba,ta isa ga fridge ta bude,ta fidda ruwa me sanyi saboda yadda takejin maqoshinta ya bushe sosai,bata buqaci cup ba ta balle murfin ta fara sha a hankali,idanunta na hango mata shi cikin falon nasa da bai fiya haske ba,cikin wata abaya ta maza
"A haka he's very calm and quiet,amma macijin sari ka noqe ne" ta fadawa kanta da kanta tana cire robar daga bakinta,ta dora ragowar saman fridge din sannan ta juyo.
Sai a sannan ta lura da kallon da babab take mata,ta kuma tsargu,amma kafin ta tambaya ita ta rigata
"Har me?,wai har kin dawo?" Kai ta gyada mata tana neman wajen zama,hannu tasa ta kama baki,sai kuma ta kada kai
"Nidai nasan ba'a ajewa miji abinci a taho a barshi dashi"
"Aiki yake baba,kuma waya ma yake amsawa,so yana buqatar space,may be wayar ta sirrice" ta fada har zuciyarta,saidai ita baba tabawan ta kalli hakanne da sunan bawa kai kariya kawai
"To Allah ya kyauta" yadda baban tayi sai duk maimunatu taji bata ji dadi ba,saboda itama baban kamar bataji dadin yadda tayin ba,to amma kuma ta yaya zata iya zama dashi a muhalli guda?,ko abincin data kai din kawai tasan karambani tayi da kuma bin umarni,tana da yaqinin zaiyi wuya yacu,ta fahimci kamar yana da jin kansa,izza da kuma qasaita,bai taba neman wani abu daga garesu ba cikin gidan dai dai da ruwan sha kuwa,sai taja wayarta kawai ta kunna data tahau sabon Whatsapp dinta,ta kuma fara da yiwa qawayen nata guda uku sallama.
Taci sa'a kuwa ta samu afrah a online,cikin mamaki take tambayar da gaske itace,sai suka zarme da hira,wadda ta daukesu lokaci mai tsaho,daga bisani sukayi sallama bayan ta bata labarin latest Korean dramas masu zafi da suka fito.
Kai tsaye ta wuce Vidmate ta saukesu masu yawan gaske,saidai tana tunanin yadda zata kallesu a nutse ba tare da sun hanata bitar karatuttukanta na makaranta ba. [11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 49
A kasalance yabar sashen nata zuwa nasa,gaba daya ta sakarwa jikinsa wata irin kasala,ya rasa dalilin da ya sanya duk sanda incident irin haka zai faru tsakaninsu sai haka ta kasance.
Sam bai kula da wanzuwar mutum a wajen ba,har ya kama stairs zai hau yaji an kirayi sunansa a tausashe,sai ya tsaya cak,ya kuma waiwaya a hankali.
Unaisa ce tsaye,sanye da wata fatar gown,kanta babu dankwali sai qaramin vail data yafa a kanta me shara shara,idanunta a kansa,tana dubansa cikin wani irin kallo wanda ya nuna yadda tayi laushi har cikin idanunta,qasan ranta tana jin wani irin qaunarsa tana fusgarta,zuwa yanzu takai maqura,hakanam tana jin haqurinta yana neman gazawa,tayi iya matuqar qoqari a irin yadda ta saba rayuwarta,sai ta sake sassauta fuskarta tana fatan ya duneta da idanun tausayi,bata taba kawowa cewa izzarsa miskilancinsa da kuma jin kansa sunkai har haka ba,tayi tunanin a kurkusa zata tagi da imaninsa kamar yadda yake tafiya da imanin duk wani da namiji,fara takowa tayi a hankali,yana biye da ita da idanu,har zuwa sanda yaga tana shirin wuce iyakar da yakega ya kamata ta tsaya
"Stop there" ya fada da muryarnan tasa dake dauke d wani irin amo,ba zato babu kuma tsammani sai jinta yayi ta fada jikinsa gaba daya,ta kuma sanaya hannunta ta qanqameshi da kyau idanunta yana tara qwalla.
"Meye haka?, what's this?" Ya fada yana yunqurin tureta daga jikinsa,saidai hakan bai samu ba saboda yadda ta sake cukuikuyeshi tana fadin
"Na gaji.....na gaji,am going to kill my self indai ba zaka saurareni ba" furucin nata yayi masa banbarakwai sosai atsakiyan kansa,diyar musulmi ke zance aikata ta'addanci a karan kanta?,bawai don ya damu ko kima ya tsorata da furucinta ba yace
"Okay,okay......sakeni tukunna" kamar ba zata sakeshin ba sai kuma ta sakeshi,ta kuma ja da baya tana dauke qananun qwallar fuskarta,hannyensa ya shiga yarfewa kamar wanda wani abun qi ya tabawa fata,fuskarsa ya sake hadewa ya tsare gida sosai yana dubanta
"Am all ears" ya fada yana goye hannuwansa a qirji,idanunta tadan watsa bangaren sasan maimunatu,ta yaya zatayi irin wannan maganar dashi a waje.irin wannan,by mistake yarinyar tazo guftawa ta jisu?,ta tabbatar idan haka ta faru ajinta ya gaba zubewa a idanunta har abada
"Am not comfortable here......i need privacy" kamar bazai amsata ba,sai kuma ya juya ya soma takawa zuwa saman a nutse cikin takunsan nan na daban,ta bishi da kallo tana jin wani abu yana tsarga mata,kafin daga bisani ta soma bin bayansa,tana qiyasta irin kalmomin da zatayi amfani dasu wajen ganin tasha kansa.
Suna isa tsakar falon idanuwanta na sake sauka ga hotunan shaheeda,yadda ta tsani mutuwarta haka ta tsani bude idanu taga wadan nan hotunan,asalima tana kishinsu fiye da yadda take jin kishin maimunatu,tunda a yanzun maimunatu bata tsare mata komai ba,bata ma.kallonta a matsayin matsala gareta,saidai tana jin haushin amsa sunan matar mijinta da tayi,harara ta jefi hoton dashi,wanda ja'afar dake qoqarin ganin ya saurareta idanunsa suka shaida masa hakan,wani abu me kama da mamaki ya saukar masa
"Harara?,for what?" Maida idanunsa yayi ga sassan da hoton shaheeda ke maqale,dai dai sanda ya dauke dubansa zuwa ga unaisa,itama dai dai sannan ya dauke idanunta zuwa kansa,sai suka hada idanu,kamar an zare wani abu daga zuciyarta taji,bataso ya ganta ba,amma ita ba wannan ne damuwarta ba,damuwarta ta fidda wadda ke cikin hoton daga zuciyarsa gaba daya,kamar yadda ta five a filin duniya,ita kuma ta maye gurbinta
"Uhmm.....go on" takowa ta soma yi tana sake nufoshi,ta dora dukkan wani yanayi da zai baka tausayi a kan fuskarta,saidai tana zuwa gab dashi ya sake dakatar da ita
"Don't do it" ya fada calmly gami da yi mata nuni da hannu kan yana saurarenta,bata da wani zabi illa fashewa da kuka harda sheshsheqa,abinda ya bashi mamaki ganin cewa shi din bai aikata mata komai ba,fuska ya hade sosai yana dubanta,sai kuma ya kau da kai yana jan tsaki can qasan ransa
"Bansan meye laifi na,ban kuma san me na aikata maka ba,don kawai nace ina sonka ja'afar?,ta yaya da hakkina a kanka tsahon shekara kusan guda ka takemin kamar bakasan da wannan ba"
"Anzo wajen" ya fada a ransa yana jin tana sake ficewa daga ransa,ta yaya yarinya mai cikakkiyar kunya da nutsuwa zata iya duban idanun da namiji.....duk da kasancewarsa mijinta,amma a matsayin budurwa ta gaya masa hakan?,well.....batayi laifi ba,tunda hakkinta ne kamar yadda ta fada din,amma bayajin koda danneshi akayi zai iya aikatawa,hes not in the mood gaba daya,bayajin wani feelings a yanzu a kanta ko dis.
Kujerar dake daura dashi ya qarasa ya zauna a hannun kujerar,yaci gaba da dubanta hankali kwance sanda taketa kukanta tana sake qara ma kukan salo a fatan da take na samun nasara a kansa,can qasan zuciyarsa yake qissima ta yadda zai raba kansa da wannan matsalar.....eh.....matsala mana,zuwa yanzun yana jin unaisan ta zame masa matsala,babu abinda take haifar masa banda kwasarwa kansa zunubi,bayan yana da tabbacin abune mai wahala ya iya karbarta cikin rayuwarsa,zuciyarsa wata irin zuciya ce mai wahalar sha'ani
"I already told you,zamanmu abu ne mai wahala da ban hango yiwuwarsa,ni am ready to dismissed you,the choice is yours.....karki sake tara ta da irin wannan shirmen" daga haka ya miqe ya nufi bedroom dinsa,ta yunqura zata bishi,saidai ko kafin ta isa ya maida qofansa ya rufe,ta daga hannu kamar zatayi knocking sai ta sauke,ta fahimci wasu daga cikin halaye da kuma dabi'unsa,idan ta sake tayi knocking masa qofa,batasan me zai biyo baya ba,sai ta juya da gudu gudu tana sauka daga stairs din kuka yana kufce mata,ta gaji gaskiya,ta kuma kai maqura,tana jin ta iso geji,batason kuma ta bata dukkan wani tanadi da tayi masa,zata dauki mataki na gaba itama da takeji har cikin ranta da zuciyarta shine dai dai.
°°°°°°°Ta tabbatar idan har ta zauna a wajen baba tabawa babu abinda zai hanata cewa taje takai masa abincin dare,wannan shine worst abu da zata sanyata,bata jin zata iya hada idanu ko muhalli dashi,gaba daya ya ajema ranta da zuciyarta wani abu,wani irin nauyi da kwarjininsa daya qaru cikin idanunta,gefe guda wani abu me kama da haushinsa da take ji,gaba daya halayyarsa batayi mata ba,hisham ya fishi sauqin kai kirki fara'a da iya mu'amala da mutane,komai nasa cikin tsumewa da tsare gida?.
Leqawa kawai tayi ta duba baba tabawan don tasan ta tashi kuma lafiya take,don ko ita tayi mamakin jimawar da tayi tana bacci
"Zan koma na kwanta baba,jikins yau banajin qwarinsa"
"Ashsha.....amma dai ba ciwon bane ko?,yana shirin dawowa ina shirin tattara komatsaina na koma inda nafi wayo?" Dubanta da kyau maimunatu tayi,gabanta ya fadi,sai taji an cire dukka sauran walwala daga zuciyarta,komawa tayi ta zauna a maimakon tashi da tayi dazun
"Tafiya kuma baba?" Kai ta gyada
"Eh,ai gwara na koma gida hakanan,tunda naga jikin naki ai yayi kyau,banda tsautsayin da ya faru yau ma ai da yau din a gida zan kwana" gaba daya jikinta ya gama mutuwa,batason tafiyar baban,saboda tasan ba komai bane zai faru sai zaman kadaici kara dadi,wanda a yanzun ta fara sabawa da rayuwa da mutane,daya daga cikin dalilan da ya sanya ko hutun makaranta bata fiya son ayi ba,banda tanason tazo taga anni wasu lokutan.
"Don Allah baba ki bari sai zuwa wani lokaci,ko kuma idan zan koma hutu,saura kwana ashirin gaba daya mu koma" kai ta girgiza
"Banda abinki maimunatu ta yaya zan zo cikin yara gotai gotai dani na zauna banda ma lalura ta rashin lafiyar?,ai gwara na tafi,kema kyafi sakewa kiyi bautar aurenki yadda ya kamata" daga qarshe ta shagwuba mata magana,wadda ta sanya bata sake cewa komai ba,sai tayi qas da kanta.
Bata sani ba ko kewar baban ta fara, yadda ta tsara guduwa daki batayi hakan ba,sai ta zauna suna fira sama sama,yayin da baban tayi amfani da wannan damar tana sake jan hankalin maimuntu a fakaice akan rayuwar auren nata.
Washegari gaba daya bata fito a daki da wuri ba,tana qiyasta lokacin da zai shigo gaida baba tabawa,ta kuwa qiyasta dai dai,don kuwa ya shigo gaida ita din,saidai a gurguje,don yana sauri zashi gida karbar kudin auren salma hafsa da kuma nadiya,harma da laila,sosai baba tabawa taji dadin labarin,bayan kuma maimunatu ta fito ta shaida mata.
Tun a waya ta kira laila tayi mata murna,saboda tasan yadda take son auren,don babu wanda ya zaci ma za'a karba harda nata,ta kuma dan tsokaneta,baba tabawa na zaune tana jinsu tana dariya,ko bayan ta gama wayar ma hirar familyn dr marwan din suka shiga,wanda duka baba tabawan ce ke bata labarin yawan zuri'ar khalidu akko,da kuma karamcin mutan gidan dr marwan din,wanda ita kanta maimunatu shaida ce,bata taba zaton a duniya akwai mutane irinsu ba,sun samu dukkan wata dama ta rayuwa,amma hakan baisanya sun wulaqanta kowa ba,ko kuma sun dauki kansu a wani abu ba.
***********Washegari tun safe maimunatu tana dakin baba tabawa,gaba daya yau din ranta babu dadi,tare sukayi abincin safe,baba tabawan ta dora na dare da wuri,saboda da yamma sukayi da driver zaizo ya dauketa,ko mai maimunatun takeyi cikin kasala da rashin dadin rai takeyinsa,tana jin inama ace zata iya hana baban tafiya,inama zata yarda suyi zamansu tare,saidai tasan hakan ba mai yiwuwa bane.
Suna gama girkin ta wuce dakinta,tayi wanka,sannan ta shirya cikin wata chiffon gown da aka fidda mata desin me kyau,ta bude sosai daga qasa,ta gyara kanta,ssnnan tayi rolling vail din da tazo dashi shima na plain chiffon mara ado a jiki,jikinta na fidda sassanyan qamshin turaren burberry london,bata saka komai a fuskarta banda powder da lip balm,saidai fuskar tata koda yaushe fresh take,saboda hutu data samu sosai,uwa uba fatarta me kyau ce,babu wani qurji ko pimples ko daya,yan makarantarsu da yawa suna zaton tana shafa wani.mai ne na musamman,saidai ko kadan,haka fatarta yake naturally,ta dauki wayarta,ta sake fitowa wajen baban.
Zuwa la'asar din baba tabawan ta kammala komai,ta kuma dauko jakarta zuwa falon maimunatun,yayin da take biye da baban dauke da wata leda data cika mata ita da kayayyakin da tasan zataji dadinsu,fuskarta gaba daya a narke take,tana riqe da ledar har zuwa sanda suka fito babban falon gidan,sai baba tabawan taja ta tsaya
"Af....niko nace bai kamata na tafi bamu gaisa da abokiyar zamanki ba,tunda nazo banga fuskarta ba"
"Gaskiya kam" maiminatu ta fada tana dan kallon sassan nata,bata manta when last data shiga sassan nata ba,tun daga ranar itama bata sake sanyata a idanunta ba,sau daya tak dai ta hangota a parking lot na gidan zata fita cikin motarta,saita amsa jakar baba tabawa ta riqe mata,don batajin xata iya shiga sassan matar.
Ko minti uku cikakke baba tabawa batayi ba ta fito,fuskarta babu yabo babu fallasa,bata dai ce da maimunatu komai ba suka wuce inda mota take jiranta.
Maimunatu bata bar gaban motar ba sai da taga fitarsu daga gidan,ta sauke ajiyar zuciya tana jin jiki da zuciyarta babu dadi,ta juyo a hankali ta soma takawa zuwa cikin gidan,tana wassafa zaman kadaicin da zatayi na kwanaki ashirin,har zuwa sanda zata koma makaranta.
Tun kafin maimunatun ta qaraso ita ta ganta,ta zuba mata idanu sosai tana kallonta, yadda ta fahimci ita bata ganta ba ya bata damar kallonta yadda taso,suna sake kusantar juna wata irin fargaba ba ratsa zuciyar unaisan,wanne irin kyau da canzawa yarinyar takeyi?,ba haka tasan fuska da jikinta ba,lokaci guda taga kamanninta na juyewa,tana tashi daga maimunatu 'yar ruga zuwa wata balarabiya daga yankin qasashen larabawa,brown mayafin data yane kanta dashi ya sake taimakawa wajen fidda haske da kuma kyanta,wani dunqulallen abu me tauri ya daki zuciyar unaisa,tayi qoqari qwarai wajen ganin ta dauke idanunta sanda suke gab da juna,ko don gudun kada maimunatun ta ganta amma kuma ta kasa,matsowar nata kusa da itanne ma ya sake haifar mata da wani ciwon a zuciya,kyanta ya sake fitowa fes ga idanunta,lallausan qamshi me aji dake fita daga jikinta,sai taja wani tsaki mai qarfi sanda taga yarinyar ta wuceta ba tare data ko nuna ta ganeta ba bare tayi yunqurin gaidata.
Wani abu ne yazo ya tsaya mata a wuya,me yarinyar ke nufi?,tana nufin wuyanta yayi kauri kenan?,ko tana nufin zata goga da ita ne?,zata amsa sunan kishiyarta?,anya kuwa babu wani abu daya taba ratsa gsakaninta da ja'afar wanda ya sanya faduwar darajarta a idanun yarinyar da har zata iya gotawa bata gaidata yadda ta saba ba?,idanunta ta kulle da qarfi tana girgiza kai,bata fatan ya santa kafin yasan yarinyar,wannan shine abu mafi muni a gareta,indai hakan ta kasance ta tabbatar akwai gagarumar matsala,dole ta samawa kanta mafita da kuma 'yanci,don haka sanda ta bude lafiyayyar motar tata ta shiga,sai ta zaro wayarta tahau kira,a maimakon ta kunnata ta fice kamar yadda tayi niyya da farko. [11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 50
Itako maimunatu ko daya ta manta da sha'anin unaisa,tunda ta wuceta ta isa sashenta,sai ta kulle falonta abinta,da farko ta rasa me zatayi,don babu wani aiki da zai debe mata kewa,daga bisani ta tashi ta debo litattafanta na makaranta ta soma dubawa,don tunda ta dawo rashin lafiyar da tayin bata barta wannan karon tayi karatun kirki ba.
Bata bar kan litattafan ba sai da aka kira sallar magrib,bayan tayi sallar ta kuma ci abinci sai ta jawo wayarta tahau watsapp,shaf tama manta dashi,kasancewar bata wani saba ba,ya kuwa debe mata kewa sosai,don bata sauka ba sai da aka kira isha'i,tayi isha'in,ta kashe dukka wutar dake falo ta wuce dakinta,kayan bacci ta canza,ta haye gado,sannan ta duba last episode data tsaya a drama dinta ta kunna abarta ta dora daga inda ta tsaya.
Karfe tara harda mintuna ya shigo gidan,ya jima sosai yau a office fiye da yadda ya saba,duk da cewa dama lokaci irin wannan da suke soma shirye shiryen lissafin shekara da kuma tafiya hutun qarshen shekarar yana dan samu jimawa a office din fiye da ko yaushe.
Daga yanda yake takowa kadai zakasan ya gaji tubus,ya tura qofar falon ya shige kansa tsaye,don yasan babu wanda zai samu a falon,sannan ya soma haura samansa kai tsaye,yadan dubi sashen da qofar falon sassanta yake,yadan sasssuta saurinsa kadan kamar xai tsaya,sai kuma yaci gaba da tafiyarsa zuwa saman da dan sasssarfa.
Fridge ya fara isa ya ciro ruwa mai madaidaicin sanyi,sannan ya dawo saman daya daga cikin qawatttun turkish chairs din da suka qawata falon ya zauna,ya bude murfin gorar ruwan ya kafa bakinsa,yanajin yadda sanyinsa da baiyi yawa ba yana ratsa hanjinsa,rabi kawai yasha ya dire robar,ya sunkuya yana sabule takalmi da socks na qafarshi hadi da janyesu gefe,sannan ya miqe yana dauke briefcase dinsa,daya hannun nasa kuma yana sassauta tie din wuyansa,don burinsa shine kawai yayi wanka a yanzun,ko qafafunsa da hannayensa da suka sage zasu samu sassuci
"Oh shit" ya furta a hankali sanda wayarsa ta dauki daddadan sautin ringtone,ya murda handle na bedroom din nasa ya tura ya shiga gefe guda kuma yana qoqarin ciro wayar ya duba me kiran.
"Anni kuma?" Ya fada da dan mamaki a ransa,don yasan ko dazun sai daya biya ta gida,jakar ya wulla saman gado ya soma rage suit din jikinsa,sannan ya danna alamar kore na amsa kira,ya kuma dora wayar saman qawataccen dressing dinsa ya sanyata a hands free.
A kasalance yayi mata sallama,saidai yanayin yadda ta amsa sallamar yaja hankalinsa,har ya maida dubansa ga madubi yana kallon kansa da kansa,tare da jiran jin abinda zata fada
"Kana jina jafaru?" Ta fadi a kausashe kuma kanta tsaye,idanunsa ya lumshe ya kuma bude duk a kusan lokaci daya sannan yace
"Ummm"
"Idan kaga ma ba zaka amsa ba duk bazanyi mamaki ba,tunda dai xuwa yanxu wuyanka ya isa yanka,sannan kayi sama da haka ma......inason a gobe kafin ka wuce wajen neman kudin daka maidashi ibada sama da komai,ka tattaromin kan matanka ka kawomin su dakai kanka,dukkanku inason ganinku" qit ta kashe wayarta,sai ya aza idanunsa akan wayar tasa ba tare da yace komai ba,kwanyarsa na masa bita yanayin sautin muryar anni da kuma abinda tace masa goben yayi
"Matansa?, what's happening?" Ya yiwa kansa tambayar da bashi da amsarta,sai kawai ya zabi jefa damuwar samun amsar tambayar a bayan damuwoyinsa,ya dage kafafa in i don't care manner,yaci gaba da zare kayan jikinsa ya kuma wuce toilet ya hada ruwa me zafi yayi wanka,wannan kusan dabi'arsa ce,ba kowa ne zai iya wanka da ruwan da yake wanka dashi ba saboda yayi zafi da yawa.
Daya fito yana sharce sassalkar sumarsa dake jiqe da ruwa,qugunsa daure da towel wanda ya bayyana dukka wata kyakkyawar qira ta jikinsa,gefe guda maganar anni na dawo masa,sai ya janyo wayarsa a hankali sanda ya tuna voice note din da amna tace tayi masa ta wayar khadim,ya lalubo number dinsa ya shiga,ya kunna na farko yana samun waje ya zauna yana ci gaba da goge jikinsa.
A hankali tsadadden murmushin nan nasa ke fita a fuskarsa,abune me mugun wahala ka ganshi ga fuskarsa,duk da yadda yake qara masa mugun kyau,sai daya gama ji tsaf sannan ya jawo wayar yana kasheta,can qasan ransa yace
"You deserve my time amne na,i promise you,i will make you happy ending month in sha Allah".
Sai daya gama shiryawa sannan ya tuna bashi da abinda zaici,ya sani yau baba tabawa ta koma gida,it means zaici gaba da bulayin neman abinci?,anya ba cook zai dauko ba kuwa ya aje cikin gidan?,sam ba girmansa bane a dinga ganinsa a eatery da sunan siyan abinci,bayan yana da komai,Allah ya mishi komai,yana da arziqin da idan abincin wata qasar yakeso yaci kullum to fa zai sameshi,sai ya miqe yana fita zuwa ga fridge din falonsa ko zai zamu wani abu da zai iya ci,gefe daya yana tunanin yadda zai gaya musu su shirya goben zasu wajen annin.
**********Karfe goma na safiyar washegari,wata safiya da aka tashi da haduwar gajimare wanda me dan duhu,cikin abubuwan dake alamta fara saukar damuna kowanne lokaci daga yanzu.
Tsaye a gaban daya daga cikin motocin dake fake a harabar gidan yake,sanye da wata shadda sky blue me matuqar kyau da daukan hankali,anyi mata dinkin zamani wanda ya dace da yanayin qirar jikinsa,ya kuma tafi da structure na jikinsa a matsayin cikakken namiji da ya amsa sunansa,mai haiba cikar kamala da kuma zati.
Qarasowarsa wajen kenan,cikin hanxari drivernsa ya fito yana karbar jakar hannunsa,gami da qoqarin bude masa seat din baya kamar yadda suka saba duk sanda xasu fita.