Kenza eBookz

Gurbin ido huguma complete - Chapter 26

Gurbin ido huguma complete - Chapter 26

Gurbin ido huguma complete Chapter 26: Gurbin ido huguma complete Chapter 26. Hannu ya daga masa ya qarasa cikin coolness dinsa ya sanya hannu zaya bude…

4,489 words

Hannu ya daga masa ya qarasa cikin coolness dinsa ya sanya hannu zaya bude gidan gaba,a dai dai lokacin ta qaraso cikin shigar wata irin gown da aka mata wani dinki,kanta yane da qaramin mayafi,yayin da fuskarta ke dauke da wani makeken sun glasses da yayi shigen kala da kayan jikinta,wani babban bangul ne a hannunta ke zobe guda daya,sai hig hill shoes data sanya a qafarta,mahadin figigiyar hand bag dinta,ta fito a unaisarta sak,unaisar shekarun baya,diyar gidan minister,shigarta gaba daya batayi kama da shigar wadda zata gidan surukanta ba,ga mutumin da ya fara ganinta yanzu,zaiyi zaton wani taro daya shafi siyasa ko kuma jiga jigan 'yan boko zata je.

"Good morning" ta fada cikin salo,idanuwanta na kan ja'afar,wanda tuni ya bude gaban motar yana yunqurin shigewa

"Morning" ya amsa mata a taqaice,sannan ya zura jikinsa a hankali kafin ya dauke qafafunsa dake saye cikin wani lafiyayyen half cover shoe na kamfanin louise vuitton,hannunsa dake daure da wani lafiyayyen gogon kamfanin Blancpain ya zura da niyyar rufe murfin motar,unaisa tabi hannun da kallo bayan ta gama qarewa takalminsa kallo,take ta sake sallamawa,da gasken gaske dan gayu ne shi din na qarshe,wanda yasan sirrin kwalliya tare da ta'ammali da designers kayayyaki,bata sake cewa komai ba itama,saiya bude back seat amma ta saitinsa ta shige,tana dora idanuwanta kan fuskarta da take iya hange ta madubin gaba,wanda tuni ya bude news paper ta safiyar ranar da drivern sa ya miqo masa,yawanci dukka safiya yakan dudduba jaridan data fito a safiyar,musamman page din da suke wallafa al'amuran da suka shafi kasuwanci.

Tana so ta tambayi wanda suke jira amma wani irin kwarjininsa daya cika motar ya hanata cewa komai,sai ta fidda wayarta ta bude watsapp dinta,ta hau turawa anty talatu saqo,abinda ya dan janye hankalinta kenan,saboda maganar da suke da anty talatun nada matuqar muhimmanci.

Karo na uku kenan ya daga kansa yana duban hanya da niyyar idan bata fito ba zasu wuce kawai,ta biyosu daga baya,har yadan fafa hasala,saidai bai nuna ba kamar yadda ko sau daya baiyi qorafi ba,kasancewarsa mutum ba mai yawan magana ba,saidai a cikin sa'a ya hangeta tana tahowa.

Glass din fuskarsa da yakanyi amfani dashi lokaci lokaci ya zare a hankali tare da qoqarin kau da idanunsa daga sashen da take tahowan,bawai don yana tunanin tana ganinsa ba,a'ah......daya daga cikin dressing na shaheeda tayi,dressing din da kusan zai iya cewa ita daya ce macen da yasan tana yinsa,kuma har yau shi dai bai sake ganin wata da irin shigar ba sai ita....bai sani ba,ko don idanun gaske dana zucin ma gaba daya tare da hankalinsa kacokam basa tare da kowacce mace?.

Shigar lafaya tayi blue black me adon gold a jiki,ko ba'a fadi ba kalar tana daya daga cikin kalolin dake haska farar fata ainun,rashin sabo da yanayin shigar ya sanyata take jin kamar zata harde,wannan ya sabbaba mata taku cikin nutsuwa da takatsantsan,abinda ya zame mata kamar ado,kamar wadda ke yin tafiyar da gayya da kuma wata manufa ta daban.

Dukka cikin sakannin da basu haura goma ba ya gama kallonta kafin ya zare idanunsa ya maida kan news paper din nasa,dai dai lokacin da ita kuma unaisa ta daga kanta da xummar gyara zamanta,idanuwanta sukayi kyakkyawan ganin da ya sanya tunaninta qwacewa na wasu daqiqu

"Damn it" ta fada can qasa,tana jin wani abu me qarfi yana fusgarta,kishinta ya soma huda zuciyarta yana ratsata da gasken gaske,bata iya dauke idanuwanta ba,har zuwa sanda ta iso dab da motar.

Batasan waye da waye a ciki ba,don haka tadanyi knocking kadan,drivern ya motsa da niyyar fita ya bude mata kamar yadda ya yiwa unaisa,sai ya cira kansa a hankali daga cikin news paper din

"Ummm ummm", ya fadi a taqaice,sai ya waiwayo ya kalleshi,yayi masa alama da ya zauna,a ladance ya amsa masa,ya ajjiye news paper din,sannan ya kama handle na motar ya bude,ya zuro qafarsa waje guda daya.

Kusan a tare suka hada idanu ita dashi,dukkansu cikin gaggawa kowa ya killace ganinsa,cikin dakakkiyar muryarsa ya magantu

"Bana iya zaman jiran kowa....wannan ya zama shine lokaci na qarshe da zaki aikata hakan" ya qarashe fada da muryar warning gamida da kausasa maganar tasa.

Sauka idanuwanta sukayi kan unaisa,wadda tadan rage glass din xuwa qasa kadan saboda ta samu damar jin a inda zasu fada,ita unaisar ke kallo,sai da suka hada idanu kuma sai ta tabe baki ta kuma janye idanun nata daga kansu ta mayar ga wayarta,a hankali maimunayu ta dauke idanunta daga wajen itama,tana jin yadda idanun nata suka cika da qwalla,cikin muryar nan tata dake cike da rauni....wadda ga wanda bai snata ba zai kira hakan da zallar shagwaba tace

"Kayi haquri" lafazin suka fita da sanyi da kuma zaqun muryarta,bashi ba,hatta da unaisa sai da salon da tayi maganar yaja hankalinta,ta sake maida idanunta kanta ba tare data shirya ba,tana jin kamar ta samu abu ta boye maimunatun,idanu su daina kaiwa zuwa gareta.

Sai daya lumshe idanunsa kana ya bude duka kusan lokaci guda,ya sake zube dubansa akan fuskarta,yana kallon yadda idaninta keta qyalli saboda ruwan hawauen da sukayi guzuri,yana mamakin saurin kukanta....me yasa ita din bata da tsayayyar zuciya,saurin bada haquri saurin kuka da kuma shagwaba kamar wata yayayya.

Qaramin tsakin da ita daya ta iya jinsa yaja yana maida jikinsa cikin motar

"Shiga mu tafi" ya fadi s gajarce,sai tasa hannu ta buda murfin motar ta kuma shiga bakinta dauke da sallama,driver ya amsa,yayin da da bakin J din yadan motss kadan alamun amsawa,ta fannin unaisa kowa ko uffan bata ce,can qasan ranta a mugun quntace.

Kaf maganganunta na jiya bata ga inda ta sanyo maimunatun a ciki ba,don me xa'a tafi da ita,ta maslahar aurenta ita daya kawai takeyi,bata qaunar ganin kowacce mace ta giftawa wannan buri da muradin nata.

Sosai qamshinta ya cika motar,har yaso yayi gogayya da nashi turaren,ya rufe news paper din a hankali ya ninketa gida biyu yana jan numfashi sosai wanda ya cika da qamshin nata,yana fesarwa kiran anni na shigowa wayarsa,ya dubi fuskan wayan bayan yayi kamar bazai dauka ba

"Am on my way" ya fada a taqaice,ya zame wayar daga kunnensa ya maidata inda ya dauko ya ajjiye,gefe daya na zuciyarsa yana cike da mamakin kiran meye haka anni ke masa da har ta qagu su iso,tabe bakinsa yayi,baisan da wacce rigimar zata zo masa yau ba,don bata rabo da rikici,amma koma dai meye...... he's ready akan duk wata rigima da takeji da ita,don yayi mata iya abinda zai iya,duk da ransa da zuciyarsa basa so.

[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 52

Fuskar anni kadaran kadaham sanda yake gaidata,duk da ba wani kallonta yayi can can ba,amma kuma jiki da zuciyarsa sun gaya masa lallai akwai wata a qasa,maida idanunsa yayi ga haj munubiya,matar da tun da can ba wani yi masa tayi ba,dama babu wani jituwa sosai a tsakaninsu,duk da ba wani abu bane yake shiga tsakaninsu ba,amma jininsu bai hadu ba.

Tata gaisuwar mai guda daya ya miqa mata,ta amshe da sauri tana cewa

"Lafiya qalau manya,ya ayyuka ya iyali?"

"Alhamdulillah" ya amsa mata a taqaice idanunsa akan qafafun anni dmda aka shafawa magani,ta kuma miqesu,da alama ciwonsu ya motsa

"To Allah ya taimaka,ya kuma dafa mana" bai maida hankali kan amsa addu'arta ta qarshe ba,cikin muryarsa me taushi da wani lokaci kan fito da wani amo da nauyi yace

"Anni,har yanzun duka tarin magungunan da kike amfani dasu basa aiki?" Dan duban qafar tayi kafin ta maida dubanta gareshi

"Abunne kasan dacewa ne,anata yi dai,sai sanda Allah ya dauke"

"Bare ciwo,kasan idan ya hadu da girma sai haquri" haj munubiya ta tsoma musu baki,ba tare da yabi ta maganarta ba ya zaro wayarsa,ya budeta,yayi kiran waya sannan ya sanya ta a kunne.

A hankali ya fara magana cikin yaren da maimunatu taji yana magana dazun,sai kuma yadan miqe a nutse yayi gaba dasu kadan can wajen dining din annin yana ci gaba da yin wayar,dai dai lokacin da khalid yayi sallama cikin falon.

Kan maimunatu idanunsa suka fara sauka,zuciyarsa tadan motsa,ya dan kafeta da idanu yana qarasowa cikin falon,sanye da qananun kaya,ya cusa hannunsa guda daya a aljihun jeans dinsa,daya hannun kuma riqe da key din motarsa yana dan kadawa

"Har ka dawo?" Haj munubiya ta fada,don ba haka taso ba,bataso dawowarsa a yanxun ba,saboda tana son fara aiwatar da shirinta,maganarta tasa ya dauke dubansa ga maimunatun zuwa kanta

"Eh,naji kince sauri kike ko?"

"Eh.....bawai wani sosai ba,dama abinda yasa nace kayi saurin kazo mu wuce,hafsat tacemin zata shiga makaranta,to kuma yanzun naga tex dinta ta fasa fitar,kuma na dan kwana biyu ai banzo gidan ba,ya kamata nadan zauna kadan mu gaisa sosai,don ko wajen yaaya marwan din ban shiga mun gaisa ba" anni dake sauraronta baki ta tabe tana kauda kanta gefe,a dan zuwan da take jifa jifa bata taba ganinta ta shiga sashen marwanun haka siddan ba,saida dalili,saboda haka kawai ta dorawa aishatu amma tsangwamar da babu dalili,face zallar faccalanci,amma yau abun mamaki wai ita ke zancan bata shiga sun gaisa ba,kafada ya daga yana maida kallonsa kan maimunatu kamar da ita suke maganar

"Well.....shikenan,zan koma ni,driver ya maidake gida kenan?"

"Eh zan kirashi,ko zuwa azahar ne sai na koma".

"Ina kwana" maimunatun ta fada sanda ta fahimci sun gama maganar,fadada fuskarsa yayi da fara'a yana amsa mata tare da tambayarta gida da kuma karatu,sai tayi mamakin yadda akayi yasan tana makaranta,amma tadai amsa masa da

"Alhamdulillah" dai dai sanda ja'afar ke saukowa yana shigowa cikin falon,idanunsa duka akan khalid din,tunda ya shigo yana karance dashi,yana ganin kuma kome dake wakana cikin falon,wani dan zafi yake ji a qirjinsa da baisan dalili ba.

Waiwayowa khalid din yayi sanda yaji muryarsa yana fadin

"I will call you back later" cikin wayar,sai ya tako a hankali yana miqa masa hannu cikin sakewar fuska,ja'afar na daya daga cikin mutanen da yake burin inama ace shine su,abubuwa da dama masa suna burgeshi,saidai girman kan da yake dashi yasa yake dannewa tare da hudubar haj munubiya dake nuna masa cewa gaba yake da ja'afar din a wajenta,kada ya sake ya nuna masa shine sama dashi.

A daqile ya bashi hannun sukayi musabaha,haka kawai yakejin zafin har yanzun a cikin ransa,idanuwansa kuma ya kasa kaudasu tsakanin maimunatu dake zaune properly waje guda,bata ma san meke faruwa ba,don dukka idanunta ta tattarasu kan wayarta ne

"Ba zaki sake amfani da kowanne irin magani ba,nayi magana da wani qwararren asibiti a turkey,zan qoqarin nema miki visa in sha Allah" ya fada muryarsa na dauke da wani irin amo kamar wanda yake fushi.

Sak hajiya munubiya tayi,cikin ranta tana debowa ja'afar tsinuwa,dan rawar ganin da yaronta yakeyi take taqama dashi,iyayensa maza ke yabonsa yana kula da mahaifiyarsu shine wannan shegen yaron me kafirin izza da jin kai zai soke?

"Amma.......naga a nan akwai likitan da nake turata abuja tana gani" khalid ya fada yana jin ba dadi cikin ranshi,kai tsaye ya kalla khalid din

"I know......."ya bashi amsa,gyara tsaiwa khalid din yayi,yana jin shima namiji ne kamar ja'afar din,kuma yana da say akan annin kamar yadda shima yake ganin hakan

"To inaga a barta zuwa wani lokaci mana"

"Ciwon yaci gaba da cin jikinta har sai ta daina tafiya?,banga wani ci gaba ba" ya fada hakan bayan yaja dan qaramin tsaki.

Idanu anni ta zuba masa tana karantarsa tare da son lalubo dalilin wannan fushin da kuma inda ya deboshi bayan ba haka ya shigo ba,dole ta tsoma baki,don kada ja'afar din ya sake fadin wani abu da bazaiwa munubiya dake zaune tana kallonsu dadi ba,batason kuma wani sabani ya dinga giftawa tsakanin jikokinta,bata jina da kashe case din khalid din da hisham ba,kada kuma wata sabuwa ta danno kai

"Shi ciwo fitarsa aisai a hankali,kuma shima likitan inajin dadin maganinsa sosai,kwana biyu ne da naqi komawa lokacin da yace abun ya dawomin" bai sake cewa kowannensu komai ba,sabida ya riga daya qudurce a ransa abinda yayi niyya,bazai kuma fasa ba.

Sallama khalid din yayi musu,sai haj munubiya ta miqe tabi bayansa,don tana son tace wani abu dashi,tanason kuma kafin taje ta dawo su gama abinda zasuyi itama ta dora nata

"Bari na shiga mu gaisa"

"To" anni ta bita dashi,don dama wajen takeson ta fita ta basu.

Falon ya dauki saiti shuru ba wanda yace komi,cikin zuciyar unaisa fal haushi,ita ba wannan ya fiddota gida ba,so take kawai a fara maganar da data tarasun.

Duban unaisa anni tayi,tana sane tace

"Shiga kitchen unaisa ki hadowa mijinku abinci" don ta sani sarai bai karya ba,don ba sanin jiya ko yau ta yiwa ja'afar din ba,kai ya girgiza

"Coffee kawai is okay" ya fadi a hankali yana rage kaifin idanunsa,har yanzun yana jin ransa yana suya.

Haushi ya sake qume unaisa,itakam meye hadin zuwansu nan da shiga kitchen ne?,ita tsakaninta da coffee ai saidai tasha,batasan takan yadda zata hadashi ba,to amma ba yadda zatayi,sai ta ajjiye maqallaliyar jakarta ta miqe ta nufi inda anni ke nuna mata.

"Bakwa bawa mijinku abinci ne maimunatu?" Anni ta jefa mata tambayar kai tsaye,sai maimunatun tadan rude, saboda bata tsammaci zuwan tambayar a sannan ba,ta daga kai ta kalli anni,sai kuma ta mayar ta sunkuyar ba tare da tace mata komai ba,ta yaya zata amsa mata?,tace mata batasan lokacin tashinsa da fitarsa ba?,ko kuwa tace batasan dawowarsa da lokacin buqatar abincinsa ba,ajiyar zuciya annin ta sake ta share maganar itama bata sake cewa komai ba.

Bata jima ba ta dawo dauke da mug a hannunta,ta ajje masa a gabansa tana sauke numfashi,sannan ta koma inda ta tashi ta zauna tana baza kunne.

Kurba daya yayi masa daci ya gauraye masa baki,sai ya maida ruwan coffee din cikin cup din yana duban unaisa da batasan ma me ake ba,saidai duka anni tana ankare dashi,ransa yaji ya quntata,ya dire cup din yana cewa

"Baaba tabawa fa?"

"Taje a lallabe mata kanta" bai wani san lallabewa ba,sai kawai ya lumshe idanunsa ba tare da yace komai ba

"Ko a canza maka wani?" Ta tambayeshi,kai kawai ya kada idanuwansa na a lumshen,tunda unaisan ta kasa hada coffee yayi dadi ina ga maimunatun haihuwar shekaran jiya?,qilan ma har gwara na unaisa akan nata.

"Ku bani hankulanku nan" anni ta fada tana saka seriousness cikin muryarta,dukka suka maida hankalinsun nasu a kanta,jaafar din shima ya bude nasa idanun ya zubesu akan annin

"Maimunatu" ta kirayeta kai tsaye,gaban maimunatu ya fadi,ta amsa mata cikin sanyi

"Akwai cutarwa a zamanki da ja'afar?,ko akwai wani abun qi da yake miki?" Tirqashi,girman tambayar da taji a tsakiyar kanta ya wuce yadda zata misalta,wannan shi ake kira da 'yar tinqe,me anni take son tace?,me takeson ji daga gareta?

"Uhmmm,ina jinki" anni ta fada tana kafeta da idanu,kamar yadda ja'afar shima ya kafeta da nasa,mamaki da kuma son gano manufa ko kuma ma'anar tambayar na masa yawo a kwanyarsa.

A hankali ta girgiza kanta,don itakam bata data cewa,to me take buqata daga gareshi?,bata taba rasa ci sha suttura ko magani ba,meye ya rage mata

"Kin tabbatar?,banda ci sha da suttura komai ma kina samu?" Anni tayi tambayar cikin fillanci ba tare data bayyana komai ba,sai ta sake gyada kanta tana tabbatarwa anni.

Dauke idanunta anni tayi daga kanta tana sake jin girma martaba da darajar maimunatu na ninkuwa a idanu da zuciyarta,ba zata iya fitowa kai tsaye ta fadi laifi ko aibun jikanta ba gaban idanunta,kunya kara da yakana suna tattare da jininta,tasan yadda komai ke wakana tun dawowar baba tabawa data matsa sai taji,tun kafin ma unaisa ta daga waya ta kawo mata qararsa

"Kefa unaisa?"

"Bani da matsalan wannan duka,saidai......" Shuru tayi tana dan jin nauyi ita kanta na fadin abinda ke ranta yake kuma damunta

"Uhnnnn......fadi matsalarki,ai dama dalilin zaman namu kenan"

"Ban taba kwana a dakinsa ba,shima kuma bai taba kwana a nawa ba" ta qarashe maganar tana baiwa kanta qwarin gwiwa da taimakon qarfafa mata gwiwa da anty talatu tayi kan ta fadi maganarta kanta tsaue,saboda indai aka dace aka shawo kansa to wannan abun shine hanya guda daya tilo da zata mallakeshi,kuma hanya mafi sauqi da zata ja masa zarenta yadda take so.

Wani abu mai nauyi ne ya sauka saman kansa,sai ya rufe idanunsa,zallar mamaki da takaici suna cin zuciyarsa,kan unaisan daya kuwa?,da zata furta wannan maganar wa anni,bayan kowanne mai hankali kai tsaye zai fahimci abinda take nufi.

Waiwayawa anni tayi ga maimunatu

"Karya kikamin kenan?" A rude maimunatun ke girgiza kai,don gaba daya ta rude,mamaki da al'ajabin unaisa ya cikata,kunya kamar zata kasheta

"Ba gashi abinds 'yar uwarki ta fada ba?,kuma ni nasan hali,sanin hali kuma yafi sanin kama,sannan nasan abinda yaci doma bazai bar awai ba" saita maida dubanta ga ja'afar,ta kuma kira sunansa da kakkausar murya,a nutse ya bude idanunsa yana kallonta,kallon da anni ta tsani ya mata shi,saboda zaka haqiqance ne kana fada,amma sai kaga fuskarsa na nuna hankalinsa kwance yake,ya zuba maka ido yana kallonka kamar wani kurma har kayi ka gama

"Kalleni da kyau,kuma kayi ta kanka wallahi kafin nayi maka mai dungurungum,su yaran da aka kawo maka ka zubesu kana dirka musu abinci ce maka akayi auren yunwa sukayi?,ko babu abinci a gidajensu?,shi kadai aka kawo maka su ka basu?" Kamar ga maimunatu tayi tambayar,sai gata ta miqe cak tsaye,annin ta saurara tana kallonta

"Ina zaki?,zauna"

"Toilet zani,fitsari nakeji" jin abinda ta fada sai anni ta barta ta maida dubanta ga ja'afar,kamar wadda za'a kama haka maimunatu ta nufi sassan da zai sadata da toilets na sashen.

Tana shiga ta maido qofar ta rufe,ilahirin jikinta rawa yakeyi,gaba daya maganar ta birkita mata kwanya,ga wata irin kunya da taji kamar qasa ta tsage ta shige,yanzu fisabilillahi banda abin anni me ya kawo wannan zancan ana zaman lafiya?,ina zasu kai ja'afar?,wannan abun me shegen wahalarwa annin ke kira musu?,bayan a drama din da take kallo,da karance karancen da afrah ta koya mata tana ganin yadda ake jin jiki,duk da wadanda take kallo da karantawa ba kai tsaye suke nunawa ko fadi ba,amma ai alamun qarfi yana ga me qiba.

Minti kusan goma harda doriya ta kwashe kafin ta dage zaninta tayi fitsarin da ya cika mata mara tun sanda anni tayi mata tambayar farko,sai data daura alwala ko zataji dai dai,ta goge fuskarta ta kuma gyara daurinta sannan ta fito. [11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 51

Shuru ne ya biyo baya cikin motar,tsakanin unaisa da maimunatu babu wanda ya cewa da dan uwansa uffan,sai ogan daketa amsa waya cikin wani yare da dukkansu basu gane wanne ba,daga bisani unaisa ta fahimci turkish language ne.

Girman kai da shegen son girma yasa unaisa taji zafin yadda maimunatu ta shareta,a ganinta maimunatun bata isa tayi mata haka ba,yarinyar gaba daya nawa take?,sa'annan kuma wace da ita?,banda martabar aure da ja'afar din daya hadasu qarqashin inuwa guda,bata jin maimunatu takai koda matsayin 'yar aikinta ma bare zaman kishi,amma zata nuna mata ita din ba komai bace,sannu sannu bata hana zuwa ai,muddin ta samu ja'afar a hannunta sai ta gane shayi ruwa ne.

Itakam maimunatu gaba daya hankalinta na kan wayarta,chart suke da afrah tana bata labarin ahmad dinta,a zahiri gwasale afran take,amma a badini yadda salon soyayyar tasu take shine yake burgeta,abinda ya sanya murmushi kenan saman fuskarta lokaci lokaci,har bata maida hankali ga unaisa dake gefe tana ji da girmanta ba,bare ja'afar dake amsa waya cikin yaren da batasan wanne bane,saidai lokaci bayan lokaci idan yayi wata maganar lallausar muryarsa na ratsawa cikin hankalinta da yayi nisa a wajen jin labarin da afra ke bata.

Karamin tsaki unaisa taja,har cikin ruhi da zuciyarta tana sake jin zafin shariyar maimunatu,gefe guda kuma yadda yarinyar ta canza ya tsaye mata a rai,ta lura idan ta tsaya wasa sai wankin hula ya kaita dare,dole tayi amfani da dukka wayewarta da kuma iliminta da kuma gogewarta tayi abinda take ganin shi ya kamata.

Qaramar ajiyar zuciya ta sauke sanda motarsu ta tsaya a babbar mashigar gidan dr marwan,drivernsu ya saki horn me gadi ya taso ya bude musu,cikin girmamawa yaja da baya kana ya rusuna musu har xuwa sanda motar ta qarasa shigewa yaja gate din ya kulle.

Tun kafin motar ta tsaya suka hangi abbi shi da ammi,tana riqe da briefcase dinsa da alama rakiya tayo.masa zaya fita,wannan kusan dabi'ar dukka matan gidance,girma ko shekaru basu sanya sun canza ba,abbi din yana riqe da hannun amna,wadda tayi kyau cikin dinkin atamfa straight gown,kanta babu dankwali saidai a taje yake cikin band da aka matse mata yalwataccen gashinta dashi,ta noqe kanta a kafada,da alama rigima take tabawa.

Dukka hankalinsa nakan yarinyar tasa,don haka yayi sallama da wanda suke magana a wayar ya kashe yana sanya wayar cikin aljihun rigarsa,dai dai sanda motar ta tsaya ya bude yana fitowa kamar yadda suma su maimunatu suka fito,dukka suka dunguma zuwa inda abbi da ammi suke tsaye,wanda hankulansu yayi wajen motar tun tsaiwarsu.

Idanu amna ta fiddo sanda ta hangi daddynta ta kuma hangi anty maimoon,da sauri ta zame hannunta ta manta da rigimar ma da take wa abbi ta nufesu da matuqar sauri,saidai tana isa dab dasu ta yanke ta nufi maimunatu wadda ta bude mata dukkan hannayenta fuskarta fadade da wata lallausar fara'a da murnar ganin yarinyar,ta dauketa cak suna dariya su duka

"To alhamdulillahi,shikenan rigima ta qare,an fansheni" abbi ya fada sanda suke sake qarasowa wajensa,ammi da maimunatu suka saki murmushi,banda ja'afar da ya dauke kansa daga kansu,karon farko da amna ta taba ganinsa ta wuceshi,koda waye ta gani kuwa shine mutum na farko da take fara zuwa wajensa kafin kowa,sai kuma unaisa da wani haushi ya saukar mata,wanda ya bayyana har saman fuskarta,ta kuma kasa danneshi.

Maimunatun ce ta fara isa gabansu,ta zube tana gaidasu,cikin nuna kulawa suka amsa,tadan miqe dauke da amna a hankali sanda ja'afar ya iso shima ya sunkuya yana gaidasu,bata tsaya jiransu ba tayi gaba abinta da amnan zuwa sashen amma,amna nata zuba mata zance yadda ta saba,ita kuma tana biye mata suna dariya,har suka isa sassan amma.

A falo suka gaisa da masu aikin amma cikin mutuntawa,suka shaida mata tana wanka,amma dab take da fitowa,sai ta zauna saman carfet tana dakon fitowarta.

Sallamar da akayi cikin falon ta sanyata daga kanta,hisham ne ya shigo,sanye da jallabiya, da alama yau din bashi da niyyar fita kenan,duk da ranar ranar aiki ce bawai weekend ba

"Matar babban yaaya" ya fada cikin dan zolaya yana wucewa gaban freezer din amma dake falon ya bude yana duba abinda ya shigo dauka din

"Barka da safiya" ta gaidashi cikin mutuntawa da kuma jin nauyi

"Barka kadai yayarmu.....jiki yayi sauqi kenan?"

"Alhmdlh ya hisham na warware"

"Allah ya qara afuwa......rigima'u,yau kuma me aka tashi dashi?,wa kike juyewa rigimar safiyar alhamis din?" Yayi maganar yana duban amna dake zaune gefan maimunatu,saidai ta kanainayeta gaba daya,duka gwiwoyinta na kan cinyarta,kamar jira take ta miqe ta isa gareshi,da niyyar fita ya shigo,amma dole amnan ta tsaidashi ya samu waje ya zauna a nan,ya ballowa kansa ruwa kenan.

Maimunatu na daga gefe tana murmushin jin yadda rigima ta barke tsakanin hisham din da amna,sauqin kansa da yadda ya iya tafi da rigimammun yara yana burgeta,gaba daya ya maida kansa shima kamar amnan,dai dai lokacin da ja'afar ya sako kansa zuwa falon.

Akan fuskarta idanuwansa suka fara sauka,fuskar dake cike da fara'a,jerarrun fararen haqoranta da suka bayyana,da wata lobawa ta musamman dake tsakiyar habarta,hasken fatarta ya sake fitowa sosai ta tsakiyar fuskar hijabinta,tana gab da dago idanunta don amsa sallamarsa ya kauda kansa,ya maida dubansa ga amna,wannan karon sauri tayi ta sabule daga gefan hisham da take zaune,ta nufoshi da sauri tana wara hannuwanta

"Dadddyy" tana isowa ya dauketa cak a hannunsa yana kallon fuskarta dake matuqar kamanceceniya da tasa,yasa yatsuntsa guda biyu yaja kumatunta,cikin low sound wanda ita daya zata jishi yace

"Naqi wayon,babu wani daddy,tun dazu ba'ayi welcoming daddy ba sai yanxu?" Wuta ta langabe masa fuskarta a narke

"Sorry....sorry dad" ba tare da ya shirya ba murmushin gefan baki ya kubce masa,yadda tayin sai ya tuna masa da maimunatu dake zaune a gefe,kamar ita,koda yaushe aka kamata ko ake tuhumarta da laifi ko aka ritsata haka fuskarta yake komawa,yayi kaman zai kalleta sanda yaji hisham na magana da ita amma sai ya dauke kansa,saidai kunnensa na sauraren hirarsu,yana mamakin yadda take dan sakin jiki haka da hisham din.

Yana qoqarin zama amma ta fito,maimunatu ta dubeta cikin girmamawa tana mata sannu da fitowa,fes ds ita cikin atamfa super exclusive,kai baka ce itace ta haifa kamar ja'afar ba saboda tsabar gayu da gyara.

Waje ta samu ta zauna lokacin hisham ya kama hanyan ficewa

"Me yasa ne baka tafi ba hisham?" Amma ta jefa masa tambayar tana zama,fuska yadan yatsina yana satar kallon ja'afar,suka hada idanu kuwa,ja'afar din ya watsa masa harara,sai yadan saki dariya hisham din,kafin ma yace komai amma tace

"Kada ka daka ta tashi,dama ka sani ba zuwa yake ba,tun can baya ma sai na matsa sosai yake zuwa,yanzun ma ya daina gaba daya" gyara tsaiwarsa yayi

"Taron family dinne anni..... sometimes kawai gulma ne da kuma daukan bangaranci,ga yarinyar can fawwaza.....ta cika naci wlh,idan ma naje ba barina zatayi na sake ba" ya qarasa maganar yana sanya kansa wajen,dauke dubanta amma tayi daga kansa tana cewa

"Allah ya kyauta" sannan ta maida kallonta ga ja'afar

"Ya kamata ku dinga daurewa kuna zuwa koda ba zama zakuyi ba,ba zai yiwu ace ko da yaushe saidai matan suje ba,nima banda yau na tashi banajin dadin jikina ai babu abinda zai hanani zuwa"

"Me ya sameki amma?" Ja'afar din ya fada da sauri cikin nuna tsantsar kulawa,tafin hannunta ta murza kadan

"Ba wani abu serious bane,kawai nauyi naji jikina yayimin" motsawa yayi yana miqewa

"Noo,bai kamata ace kin zauna ba bakiyi checking me yake faruwa ba,dauko mayafi amma muje a dubaki" qaramin murmushi ta sauke,ta jima da sanin irin soyayya da kulawa da ja'afar ke mata ta dabance ko cikin yaranta,shi yasa komai nasa itama ya fita daban cikin zuciyarta,duk da tana qoqarin dannewa

"Ba komai fa,jiki ne da jini,dama ba za'a yita zama haka ba ba'a taba lafiyarka ba,yanzu ba gani a zaune ba muna magana" duk yadda yaso suje amma tace masa aah,dole ya haqura ya zauna,saidai dukka hankalinsa yana kanta

"Ina fatan kuna lafiya" amma ta fada,tambaya ce guda daya,amma tana dauke da ma'anoni,kara ya hanata buda tambayar,kai maimunatu ta gyada kanta a qasa cike da kunya da kuma surukuta,yadan saci kallonta,yadda takeyi din kamar yadda shaheeda kema amman,can qasan ransa yaja tsaki,me yasa yake yawan kwatanta da shaheeda bayan ba ita bace?,sai ya miqe yana fadin

"Zan shiga wajen anni"

"To ba laifi,ki shiga ku gaisa maimunatu" ta fadi don tasan yawanci direct nan suke fara yowa sai sun gaisa suke wucewa sassan annin.

A hankali suke takawa zuwa sassan annin,yana gaba tana biye dashi a baya,tamkar wata maras gaskiya,jifa jifa take satar kallonshi,yadda yake takawa majestically,cikin aji da izza,ba zato taga ya ja birki ya kuma waiwayo,ta daga idanunta a hankali tana duban inda yake tsaye ba tare data iya kallon qwayar idanunsa kai tsaye ba,nuni yayi mata da hannu kan ta wuce gaba,sai ta tako a hankali tazo ta giftashi,ta wuce kamar yadda ya buqata,lumshe idanunsa yayi sanda iska ta kwaso masa qamshinta,wannan qamshin dake maqale a wani bangare na kwanyarsa tun a wancan lokacin,sai ya rufa mata baya,suna ci gaba da takawa daya bayan daya.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull