Kenza eBookz

Gurbin ido huguma complete - Chapter 38

Gurbin ido huguma complete - Chapter 38

Gurbin ido huguma complete Chapter 38: Gurbin ido huguma complete Chapter 38. Tunda suka shiga motar ko sau daya bai sani hannunsa daga cikin nata ba,yana…

4,481 words

Tunda suka shiga motar ko sau daya bai sani hannunsa daga cikin nata ba,yana riqe dashi gam yana murzawa a hankali,ya dameta kan ta fada masa me yasa tadan rame ba kamar yadda ya dawo da ita ba?,ko akwai mai matsa mata?,ko makarantar babu dadi?" Tsaf ta boye idanunta cikin hijab,taqi kuma cewa komai dashi,sai ya sakar mata lallausan murmushi

"Ni bari na gaya miki....tunda ke kina boyemin,kada nace kina sona ko?" Curewa ta sakeyi waje daya dariya mai dan siririn sauti tana qwace mata,abinda ya sake jan hankalinsa a kanta kenan,ya saki murmushi shima me sautin

"Bana iya baccin,bana iya cin abinci,Allah kinji nace miki Allah,tunda kika tafi kika tafi da dukka farinciki da walwalata,har na dinga jina kamar marayan da babu uwa babu uba" kanta ta daga a hankali,bakinta ya subuce tace

"Kamar ni kenan?" Idamunta na nuna alamun rauninta,tausayinta ya tsarga masa sosai, cikin ransa yace

"Kin kusa yin dariya in sha Allah" amma a fili saiya riqe hannunta dakyau,ya jashi zuwa qirjinsa saitin zuciyarsa

"Ki daukeni kamar uwa da uba a wajenki,nayi alqawari zan cike miki dukka wani gurbi da gibi da kike dashi a rayuwarki" idanunta ta maida ta lumshe,tana jin kewarsu,maganarsa ta ta katse mata tunani

"Wannan zafin jikin tun yaushe kika fara shi?"

"Last week ne"

"Ya kamata kiga likita kenan,don kada yaci gaba" ya fada tana sanya signal a motarsa,kanta ta girgiza tana bin titin da zai kaisu gidana abbi da kallo

"Yana sauka.....amna nakeson ka daukomin,tunda na dawo ban ganta ba" fuska yadan kwabe kamar yaro qarami

"Noooo......so nake mu shiga duniyar da zata bamu nutsuwa,wadda babu kowa a cikinta daga ni sai ke" yadda yayi maganar yana rage gudun motar ya kuma sanya idanunsa cikin nata sai wani nauyin ya kamata,ta maida kanta baya ta jinginar tana rufe idanuwanta.

A parking lot na gidansa dake government road ya tsaya,sannan ya kirayi me gadin,ya gaya masa ya rufe masa gidan,idan anzo nemansa yace he's not available😂,kasaqe mai gadin yayi yana maimaita kalmar

"Yallabai kamar wani layin waya?" Ya fada a ransa

"Jeka" ja'afar din ya fada yana sallamarsa,sai ya amsa da to yana komawa bakin aikinsa.

Yanxun ma daukar abarsa cak yayi har zuwa sassansa,tare sukayi alwala sukayi sallar la'asar data kubce musu su duka,ya waiwayo yana dubanta a hankali bayan sun isar,sai ya zame ya kashingida yana tokare jikinsa da jikinta,idanunsa a qasa

"Me zakaci?" Ta tambayeshi saboda tunawan da tayi yace bai iyacin abinci

"Anything angel,indai daga gareki ne zanci,amma for now dai barci nakeji" ya fada yana zamewa a hankali,ya aza kansa saman cinyarta kwanciyar rigingine yadda yake ganin fuskarta fes,yana kafeta da wani irin kallo,idanuwansa suna lullumshewa.

Hannunsa ya sanya ya zare tafin hannunta data rufe fuskarta dasu,muryarsa da matuqar rauni yace

"Noooo.....don Allah please ki barni na more,don Allah,badon ni ba" sai ya maida hannuwansa ya harde a qijinsa yana ci gaba da kallonta,idanuwansa na masa nauyi,wani irin barci na rinjayar idanuwan nasa,a hankali yana kallonta suna rufewa,har suka rufe gaba daya,wani daddadan baccin da ya manta rabonsa dashi yayi awon gaba dashi.

Saukar numfashin sa cikin nutsuwa ya tabbatar mata baccin yakeyi da gaske,a hankali ta sauke idanuwanta kan fuskarsa

"Ma sha Allah,fatabarakallahu ahsanul khaliqin" ya fita a bakinta,asalin kyau ta gani dab da ita cakude cikin fata chocolate color.

A hankali take qare masa kallo,kwantacciyar sumar fuskarsa mai santsi baqa sidik data sake qwawata fuskarsa,wani irin gyaran fuska yakeyi,kamar na jaruman fina finan qasar hindu,koma waye yake masa aski tabbas expert ne,ya kuma san aikinsa,bata taba damuwa da aski ko sanin me askin maza ke ciki ba,amma a yanzun askin ya burgeta sosai.

Yatsanta guda daya ta sanya tsakanin gashin girarsa masu laushi tana zagaya girar,caraf taji ya kama hannunta,ya riqe da kyau cikin tattausan tafin hannunsa,cikin murya dake cike da mayen bacci yace

"Am sorry angel,hannunkin nan mai laushi da yawa zaya hanani yin bacci,har gwara kici gaba da kallona,na baki dama,ina jinsa kamar garkuwa ne a tattare dani" yana gama fadin hakan ya sanya hannuwan nasa qasan kuncinsa yayi filo da tafin hannun nata,yana kuma sake gyara kwanciyarsa sosai cikin jikinta,kamar qaramin yaron dake jin rigima ya samu mamarsa ta dorashi kan cinyarta.

Kunya da mamakin yadda baccinsa ya katse,ya kuma fahimci kallonsa takeyi ya kamata,sai tayi shuru kawai tana murmusawa kadan kadan,har zuwa sanda itama nata baccin ya iso,ya rinjayeta,sai gashi a hankali ta kifa fuskarta a tasa,sannu a hankali suka fara musayar numfashin juna.

Shi ya fara farkawa,amma sai ya gaza motsawa saboda yadda tayi masa rumfa,cikin jikinsa ya dinga jin wani abu yana shigarsa yana ratsashi,ya dinga sauke murmushi shi kadai,zaiso su tabbata a haka,saidai kuma yana dan motsawa kadan itama ta farka,ta kuma tashi da sauri cikin kunya da mamakin yadda gaba daya tayi male male a jikinsa,daga kanta zuwa qirjinta.

Juyowa yayi sosai yana fuskantarta kamar dazun da idanuwansa da suka dan kada kadan sabida baccin daya tashi a shi

"Yunwa nakeji,please ayimin taimakon gaggawa" kai ta gyada masa tana murmushi dake nuna zallar kunya

"Uhmm madam,a taimakeni,tsohuwar yunwa ta tashi" da ido tayi masa nuni kan ya dagata,bai dagata ba ya tsareta da ido amma girki yakeso,mirginawa gefe yayi da sauri yana cewa

"Ya salam.....afwan" abinda ya bata damar tashi kenan,ta dauki ribbon dinta daya zame yayi nasa waje ta tattare sumarta mau santsi waje daya sannan ta tashi,yana kwancen har yanzu cikin mutuwar jiki yana qare mata kallo,idanuwansa suna lullumshewa,shi daya yana sake tsumuwa da ganin surarta,kasancewar yanzu babu hijabi a jikinta.

Har takai qofa taji yace cikin wata irin murya daya cika taushi da yawa

"Angel moon" sai ta tsaya cak ta waiwayo,murmushinsa shine abu na farko data fara gani sannan ya motsa bakinsa,cikin wani slow ya furta

"I love you"....." Wani kunya ya bata yadda ya furta mata maganar,da kuma yadda ya kafeta da idanu,sai ta juya da dan sassarfa ta fita a dakin,bata tsaya ba sai datakai kitchen,sai ra jingina da freezer din cikin kitchen din tana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya gami da murmushi mai taushi,ko wanne second da zaizo ya wuce mamaki J yake bata,completely ya canza,wai dama haka yake?,sai ta tuna wani hira da suka taba yi da afra,a sannan ta dauka sharrinta ne,bata gasgatata ba sai yanzu

"Hmmm,rabu da miskilallun na masu jin izza da isa,da yawansu idan kikaga yadda suku sukurkucewa akan soyayya sai sun baki tausayi,Allah saiki rainasu inda xaki gansu gaban macen da suka matowa,amma suna fitowa waje sai suyita wani izza suna muzurai" saita sauke wani sabon murmushin,ta taka zuwa tsakiyar kitchen din,kwanyarta na mata searching,cikin abubuwan data karanta a dairy din shaheeda a favourite food nashi,wanne ne mai sauqi da zata dafa masa.

Rub da ciki yayi bayan ta fita,ya jima a haka yana hasashen yadda yakeji a jikinsa akan maimunatu,da yadda soyayyarta tayi masa wani irin kamu,yana jin buqatuwa sosai zuwa gareta,saidai yanason ya bata space,kada ta dauka jikinta kawai.shine abinda yake buqata.

Toilet ya shiga yayi aswaki da miswak na Aarak,wanda indai yayi bacci irin hakan yakeyinsa,ya fesa mouth fresh a bakin nasa bayan ya daura alwala sannan ya fito,yanason ya qarar da dukka lokacinsa tare da ita.

Sam sam bataji shigowarsa ba,sai tsintar kanta tayi jingine a qirjinsa,ya zagaye ta ta qugunta,ya sanya hannuwansa saman plate tummy dinta,ya kuma dora kansa saman kafadarta yana leqen abinda take dafawa,da muryar dake wanzar da soyayya a zukata ya fara magana

"Shine kika gudu?,bayan ko kwatar abinda yake raina ban gaya miki ba?,lemme tell you one to two reasons that make me love you" sai ya sake mannata cikin jikinsa sosai kamar xai maidasu abu daya,ya sake qas da muryarsa

"I love you because you make me feel again that am worth something.....i love you because you make me smile when I almost forgotten how to.....i love you angel for so many reasons" gaba daya kalamansa sun kashe mata jiki,kawai saita kasa ci gaba da yanka dankalin da takeyi akan chopping board,tana riqe dai da wuqar kawai a hannunta.

Sakinta yayi daya lura da haka,sai ya zame ya dawo gabanta,ya karba wuqar ya fara yayyanka mata da sauri da sauri,har yadda ya iya ya bata mamaki,yana yankan yana daga kai yana kallonta kamar zata bace masa,hakan ya sanya saura kadan ya datse hannunsa,don haka ta karba aikinta tace ta gode

"Ko kin koreni ba inda zani" narai narai tayi da fuska,zuciyarta cike fal da saqonni amma kuma nauyi da kunya hadi da rashin sabon da har yanzu basuyi ba ya hanata furtawa,ya gama karantar qwayar idanunta da kyau,don haka murmushi kawai ya saki

"A juri zuwa rafi da tulu diban ruwa" ya fada a ransa.

Kusan shi ya tayata dukka aikin sukayi suka gama tare,tun cikin kitchen din ya zuba ya fara kaiwa cikinsa,itace mutum ta uku a duniya da yakejin dadin abincinsu fiye ma da yadda ransa yakeso,da qyar ya iya kaiwa falo ya zauna tayi serving nashi.

Dadin sai ya masa yawa,ya dinga jinsa yana yawo a wani gajimaren farinciki,yana ci yana kallon fuskarta har ya kammala.

Daure da babban towel ta fito a wanka bayan ta baroshi a falo yana waya,awa kusan daya kenan,a nutse ta qarasa walking closet dinsa tana dudduba kayan da zata saka,saidai babu wanda zai mata,hasalima gaba daya an kwashe sauran kayan da sukayi ragowa na mata,taja tsaki yafi a qirga,dole daga baya ta fara lalube cikin trouser dinsa ta samo daya ta saka,ya mata mugun yawa,saita tsugunna ta lanqwashe qasansa,sannan ta shiga dubawa cikin rigunansa ko zata samu wanda zata saka a jikinta. [11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 79

Weekend na musamman suka sakeyi kamar yadda ya shirya musu,don wannan karon daga makaranta kai tsaye airport suka zarce,already ya siya musu ticket zuwa kano,akwai aikin duba ginin company dinsa da yakeyi,cikin 'yan awanni ya gama dubawar suka sauka a Bristol palace,a nan suka more amarcinsu sosai,kwanaki biyun da sukayi ta sakar masa zuciyarta harma da gangar jikinta,wani sabo da shaquwa ne sosai suka shiga tsakaninsu.

Ta dauka Sunday ko Monday da sassafe zasu wuce,amma sai taji baice komai ba,itama kunya da nauyinsu take ji shi yasa bata tanka masa ba,ta fuskanci makarantar takai masa ko ina,kawai lallabawa yake yana ma anni kawaici.

Da wani yammaci tana zaune a balcony din dake gaban dakinsu,saman wani table dan qarami mai kujeru guda biyu,gabanta littatafanta data taho dasu saboda assignment da aka basu wanda yake a mazaunin test.

Sosai hankalinta yayi gaba tanata rubutu,yana tsaye a bayanta bata sani ba,hannuwansa cikin aljihun trouser dinsa,yana sanye da slim fit shirt mai gajeran hannu,wadda ta zaune ta lafe a jikinsa,ta kuma fidda qirarsa na cikakken namiji.

Murmushi yadan saka sanda ta daga hannunta tadan yarfeshi kadan,alamun ta gaji da rubutun,ji yake kamar ya dauketa.ya hadiyeta,wani irin zazzafan so ne nata yake shigarsa zuwa kowanne sashe na jikinsa,sai ya fara takawa sannu sannu har zuwa bayanta,ya tsaya sannan ya miqa hannunsa ta gefan kafadarta ya ranqwafa faffadan qirjinsa yana gogar bayanta,ya sanya tafin hannunsa ya rufe rabin littafin.

Duk sanda ya kalleta ya tuna alkhairin dake shirin fuskantar rayuwarta sai yaji wani madaukakin farinciki yana ratsashi,yaya zata dauki lamarin?,zuciyarya zata samu wannan juriyar kuwa?,wannan shine tambayar da yakema kansa.

Cak ta tsaya da rubutun,murmushi na tashi akan fuskarta,sai ga cira kai a hankali ta waiwaya tana dubansa,take idanuwansu suka sarqe waje daya, fuskokinsu gab da juna,numfashinsu ya fara gauraya waje guda,kusan lokaci daya kuma a tare kowannensu yadan lumshe idanunsa kana ya bude, ja'afar din baice komai ba,sai ya sanya daya hannun nasa ya zare biron dake tsakanin yatsunta ya aje,sannan ya saka hannuwansa biyu ya dagata cak ya ture kujerar ya kuma dorata saman table din,sannan ya sake jawo kujerar gabanta,ya zauna a kai,ya kuma matso da ita dab da ita kamar zai shige cikinta,ya kwashi qafafunta ya dorasu saman qafarta.

Da kallo yabi qafafun nata,farare sol babu digon komai a kai,sai na baqin lalle sidik sake saman faratan yatsun nata,wanda hakan ya zama musu wani ado na musamman.

Hannu yasa ya fara mata tafiyar tsutsa a qafar tata,sai ta qyalqyala dariya tare da qoqarin janye qafartata tana jin wani iri

"Ka bari......don Allah"

"Don Allah wa?" Ya tambayeta yana kallon fuskarta,wani irin murmushi mai cike da shauqi kwance saman fuskarsa

"Nidai don Allah"

"Nace don Allah wa ?,yau sai kin fada,idan ba haka ba?,....... tom" sai yaci gaba dayi,wannan karon har saman qafarta zuwa qaurinta

"Don Allah my baby,my hot baby........my life line.....my hubby.....my other half.....my moonlight" dukka ta hada ta fada tana dariya tare da son ya cikata,cak ya tsaya yana lumshe idanu

"Wow......wow..... great!" Ya fada yana sakin murmushi sannan ya dubi idanunta da wani irin taushi

"Fantastic I really enjoy these names moon angel.......,you have the best gift ever let me give it to you" bata qara wani tunani ba ya miqe tsaye ya sunkuceta,ta cikin balcony din ya buda qofar Glass din suka zarce bedroom dinsu.

Wani irin hot romance ya dinga aje mata da wasu kisses masu zafi,wani saqo me nauyi da tsayawa a rai ya dinge ajema kowacce gaba ta jikinta,sun jima a haka kafin su nutsa duniyar ma'aurata,wadda suka jima da tsarata hadi da killaceta da wasu irin abubuwa masu sanya abokin rayuwarka ya tsaye maka a rai.

Tana saman mirror yana busar mata da kai da band drayer,daure take da towel wanda ya dan zame kadan yana nuna fararen qirjinta da kuma tudunsu ta sama,abinda yake yawan tafi da hankalinsa kenan,shima din towel din ne daure a qugunsa,yana busar mata da kan idanuwanta na saman gargasar qirjinsa da ko yaushe taje burgeta,tana daya daga cikin abubuwan dake sanya mata nishadi,tana da laushi sosai,hakanan wani qamshi take bayarwa na musamman

"Yaushe zamu koma,akwai assignment da yawa a hannuna a satin nan" ta fada a hankali da muryarta mai taushi,duk da can qasan ranta tana jinne kamar zai maidata kurkuku.

Ajiyar zuciya ya sauke,sai ya juyar da ita tana fuskantar madubi sosai,idanunsu cikin na juna,ya motsa labbansa a hankali

"Angel.....na tsani makarantar nan totally yanzu...... you are my perfect place to go when my mind searches for peace,ta yaya zanso rabuwarmu kota second daya?,.....you are my world angel,if i could have one wish.....i would wish to wakeup every day to the thousand of your breath on my neck,the warmth of your lips on my cheek,the touch of your fingers on my skin and the feel of your heart beating with mine,ba abinda yafi min wannan dadi a rayuwata" ya qarashe fada yana nutsa yatsunsa cikin gashinta don ya tabbatar ko.ina ya bushe, idanuwansa kuma cikin nata,sai taja numfashi sosai,ta kuma lumshe idanunta,hannayenta ta bude gaba daya,ya saki tattausan murmushi shima ya bata dama tayi huggin dinsa sosai,a hankali tace

"Ka sakani jin cewa ni wata mutum ce ta daban,ka saka duniyata cikin nutsuwa ka sani inajin cewa am protected tako ina kuma am loved,i don't ever want to live my life without you by my side"

"Don't kill me please babe" ya fada yana dariya

"Abun zaimin yawa,ga huggin da wadan nan kalaman masu zaqi?" Sai ya bata kunya ta cukuikuyeshi da kyau, shi kuma yana dariya abinsa,kafin a hankali ya rage sautin murmushin da yake yi din

"Oya,sauko ki shirya,don idan naci gaba da ganinki a haka komai yana iya faruwa,ni kuma so nake kiyi alwala.kiyi salla raka'a biyu,ki godema Allah,akwai muhimmin al'amarin da yake shirin tunkaroki" daga kanta tayi a hankali gabanta yana faduwa tana dubansa

"Menene?" Murmushi ya sakar mata saboda ya hangi tsoro da karaya a tattare da ita,sai yasa yatsansa ya lakace mata hanci

"Matsoraciya,khairan in sha Allah" shuru ta sakeyi,sai ya riqeta sosai

"Baki yarda dani ba?"

"I trust you"

"Oya.....do what I said to you" saita jinjina kanta,ya riqe mata hannu ta zamo a hankali qasan mudubin.

Duk yadda taso ta manta da abinda yace matan ta kasa,tayi sallar harma sun wuce raka'o'in da yace mata,haka kawai takejin kasala da mutuwar jiki,gefe guda kuma kamar zazzabi zai kamata.

Wayarta dake gefanta ce ta fara haske ba tare da fitar sauti ba,duk sanda suke a tare ita dashi irin hakan wayoyinsu dukka a silent yake sanya musu idanma anci sa'a bai karba ya kashe ba,yakance basa buqatar kowa basa kuma buqatar komai,daga shi sai ita,duniyarsu ce wannan so basason kutsen kowanne abu.

Dubawa tayi sai taga afra,ta shafa addu'ar da takeyi ta janyo wayar tana amsawa,bayan sun gaisa tace mata

"Kin ganni a hanyar gida daga makaranta,zanje na duba jikin daddy,jiya muslim (qaninta) yacemin basuyi barci ba,jikinsa ya motsa,wai amma hajja ke boyemin don kada nazo,ta yaya zan iya zama maimoon?,ko tsanani jikin yayi basu gayan ba oho" cikin sigar lallashi da kwantar da murya tace

"Kai haba,bana jin haka,ki kwantar da hankalinki ba komai.in sha Allah" ta bata qwarin gwiwa sosai kuma afran ta samu qwarin gwiwar,sannan sukayi sallama tana cewa

"Ki gaida hajjan da daddyn duka,Allah ya qara afuwa" jikinta a sanyaye ta ajjiye wayar bayan sunyi sallamar,aai tadan fada tunani kadan,kafin J ya shigo ya kore kowanne tunani da fargabar da taketa tsintar kanta a ciki.

Bayan sunyi sallar isha'i motar hotel din ta daukesu zuwa shoprite,yace tayi siya duk abinda take so,kusan su amna amma dasu anni da kuma su laila ta yiwa tsaraba,sai ya tsaya yana kallonta kafin yadan ranqwasheta a tausashe

"Kin manta dani?,su anni kawai kika sani?" Ya fada yana narke fuska kamar qaramin yaro,sai abun ya bata dariya har haqoranta suna bayyana

"Ta yaya zan manta dakai?" Ta fada tana janyo daya cart din dake gefanta.

Luxuries undies ne masu kyau da tsada na maza a ciki,handkerchief perfumes da pyjamas masu shegen kyau,sosai yaji ta burgeshi qwarai, sai ya danyi hugging dinta ta kafadarsa

"Thank you,thank you my angel moon"sai kuma yace

"Amma banga taki siyayyar ba da kuma ta baby na"

"Ka wadatani da komai,bana buqatar komai.....baby kuma wanne bayan amneee na?" Fuskarta ya daga da yatsunsa yana kallonta,kamar mai rada ya rage murya can qasa

"Baby unborn" ya fadi yana shafar cikinta da hannunsa,turesa tayi tana turo baki hadi da sakin murmushin jin kunya,dariya ya saki yana sake jawota jikinsa

"Am serious,bana aikin banza,jikina yana bani very soon amneee zata samu brothers and sisters" ido ta fiddo

"Bama brother ko sister ba?,harda qari?" Kai ya jinjina

"Yeah,i trust my self cikin ikon Allah bana bada iri guda daya,ga example akan amna.....niba rago bane,sannan Allah na na sona,yasan inason yara da yawa" dukansa ta soma yi cikin wasa tana sake tureshi

"Nidai ka daina fada please"

"Zaki sani ne,na riga na bada ajiya kuma an karba,so sai randa zan karba kayata in sha Allah kawai nake jira" ta fuskanci yau din yan tsokanar suna kusa,dibanta kawai zaiyita yi,dole ya haqura ta barshi kawai,saidai kuma maganarsa tayi ta sakata murmushi ita kadai

"Ni ba rago bane.....yes,ta shaida haka" ta fadi a ranta,sai kuma taji kunyar kanta da kanta,ta saki murmushi kawai. [11/25, 7:22 AM] Safiyyatulkiram: 80

Tun cikin airport din malam aminu kano dake kano tana maqale dashi kamar yadda ya saba,ba ruwansa da idanuwan kowa,ta fuskanci shi din kaifi daya ne,bashi da kwane kwane ko nuqu nuqu,baya kuma iya boye abinda yake cikin zuciyarsa.

Duk yadda yayi qoqarin janta da wasa da hira don ta sake sosai amma kuma ta kasa,batasan me yasa ba gaba daya jikinta a matuqar sanyaye yake,sai faduwar gaba da takeji lokaci lokaci,a haka har jirginsu ya daga zuwa gombe.

Mota daya rak ce tazo daukansu,sanda suna cikin motar ma hannunsa na cikin nata,kanta na saman kafadarsa,idanunta na biye da titi,bata ankara cewa ba hanyar gida sukayi ba sai daga bisani,batace komai ba,duk da cikin zuciyarta zata so ace gida suka nufa ta kwanta ta huta,don wata irin gajiya takeji,kamar wadda sukayi tafiyar mota.

Tafiyar minti kusan arba'in sukayi,lokaci lokaci tana jinsa yana amsa waya,saidai batasan me yake fada ba,har suka isa wata unguwa,motar tasu ta gangara jikin wani dan symbol dake dauke da sunan street din.

Kofar wani gida suka tsaya,ta daga kanta a hankali tana duban gidan,babban gida ne da ya amsa sunansa,yana dauke da katafaren gini manyan katangu da kuma tsayayyen bene na alfarma,sauke idanunta tayi dai dai sanda security ya leqo,ba tare da yace musu komai ba kaman yasan da zuwansu ya dage musu gate suka wuce zuwa ciki kai tsaye,ya qarasa parking lot dake gefe daya na gidan can nesa kadan da gate,ya tsaida motar.

Dagata kadan ja'afar yayi yana kallonta,ya sakar mata murmushi, muryarsa a hankali yace

"What's happening, ?" Ya tambayeta a tausashe,kawai sai ta fara tara hawaye amma kuma sai ta girgiza masa kai

"Nothing,ba komai"hannuwansa ya sanya ya kama fuskarta,ya sanya idanuwansu sosai cikin nata yana bata wani qwarin gwiwa wansa ta jishi cikin jikinta sosai,hawayen data tara suka fara shanyewa suna komawa ciki,sai da yaga ta nutsu sannan ya bita da wani murmushi mau narkar mata da zuciya

"good, everything will be fine" ya furta yana manna mata wanu kiss mai taushi a goshinta,sannan ya buda motar ya fita,ya zagaya ya bude mata,a hankali ta sauko,sai sannan ta sake kallan gidan da kyau,lallai babban gida ne

"Ki shiga ciki,yanzu zan shigo sai mu wuce gida,zaku gaisa dasu ne" kai ta gyada masa a sanyaye,tana mamakin wanne irin muhimmanci ne da mutanen har haka, wanda kai tsaye daga airport sai wajensu?,bazai bari suje gida su huta ba?.

Binta yayi da kallo sanda take takawa,cikin tafiyar nan tata kamar tana rangaji,qafafunta akan tsari,cat walking din nata tana burgeshi sosai,idanunsa basu taba ganin tafiya irin tata ba,a hankali har zuwa sanda yaga ta isa babbar qofar falon,ta bude ta shige,sai ya sauke ajiyar zuciya me nauyi yana furta

"Alhamdulillah" cikin sanyi yana kuma lumshe idanunsa,tare da jiran abinda zai biyo baya.

Cikin muryarta dake cike da sanyi tayi sallama a babban katafaren falon,dukkan mutanen dake falon suka daga kansu,banda wani babban mutum ma'abocin furfura tsalli tsalli a saman kansa dake zaune saman kujera hannunsa riqe da waya,da alama akwai wani abu me muhimmanci da yake kallo.

Da idanu ta bisu da kallo kamar wadda aka kafe daga bakin qofa,umma sa'ada ce sai anni da baaba tabawa,gefe daya dr marwan ne wato abbi a zaune,sai kuma wata dattijuwa dake zaune itama dab da babban mutumin.

A hankali ta maida dubanta ga mutum na qarshe wanda idanuwanta suka sauka a kansa,wata mummunar faduwar gaba ce ta ziyarceta,lokaci daya taju gaba daya kwanyarta da tunaninta sun birkice,ta fidda idanunta da kyau taba qare masa kallo kamar idanuwanta zasu fado,bakinta da jikinta dukka suka fara rawa,komai dadewar zamani,komai shudewar lokaci idanuwanta da zuciyarta ba zasu taba mantawa dashi ba

"Abbuuu" ta kirayeshi da sunan da duk duniya ita daya ke kiransa dashi.

Tamkar wanda aka fusgeshi ya daga kansa da sauri,take kowanne sashe na kwanyarsa ya fara motsawa yana qoqarin dawowa saiti tare da son komawa bakin aikinta bisa tsari da doka.

Miqewa tsaye yayi bakinsa yanata motsawa,da alama akwai abinda yakeson furtawa amma kuma ya kasa cewa komai din

"Diyammm" cikin wata irin fusga ya fadi sunan,abinda ya sanya maimunatu rushewa da kuka tana sake kiran sunansa,sannan ta diba da mugun gudu tayi inda yake tsayen,saidai kafin ta qarasa ya dafe kansa da yaji kamar an balla masa qashin kansa,ya tafi luuu zai fadi,abbi da yafi kusa dashi yayi hanzarin tarbarsa,saidai tuni ya sume

"Abbuuuuu" ta sake fada da qarfi ganin ya fadi,wani irin tsoro da fargabar suna shigarta,kawai sai taji itama jiri ya kwasheta,kunnuwanta kuma suka toshe idanunta suka fara ganin gilmawar duhu,take qafafunta suka gaza daukarta,ta tafi luuu zata fadi,umma sa'ada data fisu quruciya ita ta cimmata ta tareta tana kiran sunanta da qarfin gaske,kiran da yaja hankalin ja'afar dake tsaye,ya bude idanunsa a hankali,kunnuwansa na sake isar masa da saqon kiran kunan maimunatu da akeyi,bai jira komai ba cikin wani irin hanzari da zafin nama ya nufi cikin gidan kai tsaye.

A hannun umma sa'ade ya sameta tana jijjigata gami da kiran sunanta,yana zuwa ya karbeta idanuwansa akan fuskarta da jikinta daya saki gaba daya,da alama ma batasan me ake ba

"Angel!" Shima.ya fada hankalinsa na neman gushewa daga jikinsa,ba abinda zuciyarsa ke hasaso masa sai rasata zaiyi,abbi ya kula yana neman ficewa a hayyacinsa ne,don ba abinda yake sai girgizata da kiran sunanta,da alama komai ya kwance masa

"Ja'afar!" Abbi ya kira shi da qarfi sosai,kiran daya dawo dashi hayyacinsa

"Ka dauketa ka sakata a mota,idan ka fita kace auwalu yazo yanzu yanzu mu miqasu asibiti gaba daya" cak ya dauketa kamar 'yar tsana,yana tafiya yana kallon fuskarta,kamar idan ya daina kallonta da second daya zata mutu ne.

Cikin qasa da minti ashirin suka isa asibiti guda daya gaba dayansu,suna isa din aka karbesu aka shiga basu taimakon gaggawa gaba dayansu,abbu dai sai da aka kira likitansa da yake dubashi tsahon shekarun ya shiga dakin da aka bashi,yana da kyakkyawan hope din lafiyarsa ta dawo,tsahon shekarun dama abinda suketa lalube kenan,abinda zai tuna masa da wani.lamari daya shude a baya.

*_BAYAN AWA DAYA_*

Shuru dakin yake,babu motsin kowa duk kuwa da cewa kusan su biyar ne cikin dakin,daga saman gadon maimunatu ce kwance a miqe saman gadon,hannunta maqale da qarin ruwa,ja'afar na tsaye gaban gadon ya sanya tafin hannun da ake qara mata ruwan cikin nashi,kamar zaya koma cikinta ko kuma ya maido ciwon jikinsa,sam.ya kasa zama,baya jin nauyin kowa a lokacin,burinsa kawai shine maimunatunsa ta farka da cikakkiyar lafiya a jikinta.

Anni ammi(shiyar maman ja'afar din)baba tabawa da umma sa'ade duka suna tsaye,kowanne zuciyarsa cike da tunani iri daban daban.

Dai dai lokacin da liktar data gama dubata dazun ta turo qofar ta shigo.

Dr noor,family friend din ja'afar ce,hakanan tare sukayi primary to secondary school,yanzun haka tana da aure harda yara uku,a nutse suka gaisa dasu anni a yanzun,ba kamar dazun dako damar gaisuwar ba'a samu ba,sannan kuma kai tsaye ta wuce kan maimunatu ta dudduba file da drip din dake sauka a jikinta,tayi dan rubuce rubuce sannan ta dubi ja'afar

"Ba wani damuwa captain,komai ya dai daita,ta koma normal,tana tashi a barcin nan zakuga kamar bata yi ba,saidai idan kunga da wani matsala sai a sakemin magana,ina office dina daga nan har zuwa 10pm"

"Okay,thank you" murmushi tayi "Babu komai captain,ba wucewa zatayi ta barka bafa" kadan ya motsa bakinsa alamun murmushi,sai ta juya wajensu anni,kafin ta sake magana hajja ta shigo,jajirtacciyar tsohuwa mai yawan tawakkali da daukan qaddara da jarrabawar rayuwa,dukka al'amuran nan sun bugeta sosai,to amma tayi qoqarin jurewa,duk da fuskarta ta nuna zallar tashin hankali,tun dazun ita da abbi da alhaj bello qani ga abbu suna can bakin qofar dakin da likitoci ke kansa,duk suka maida hankalinsu a kanta sanda tayi sallama tana nufar gadon da maimunatu ke kwance,idanuwanta a kanta,tana jin wata qaunar jikartata da ta kwashe tsahon shekaru tana addu'a a kanta,tana fatan Allah ya bayyanata,ubangiji ya zama gantanta,jikanyar tata data jima dauke da qauna da soyayyarta a cikin ruhinta,saidai batasan a inda zata cimmata ba,bare ta nuna mata gata soyayyar da kuma kulawa,har sai yau da buwayin sarki ya yanke komai.

"Hajiya,ya jikin alhajin"

"Alhamdulillahi anni,sun gama iyakacin qoqarinsu,sun kuma bada tabbacin da yardar Allah komai nasa ya koma saiti yadda yake,da zarar ya farfado zai iya tuna komai da komai"

"To alhamdulillah, Alhamdulillah" suka kusa hada bakin wajen furtawa dukka su ukun.

Dr noor ta jinjina kai itama

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull