Kenza eBookz

Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 1

Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 1

Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 1: Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 1. [5/14, 6:00 AM] Oum khadeejarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

3,045 words

[5/14, 6:00 AM] Oum khadeejarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

By

AyshaNalado

Young talented writers Ass.

YOTA ID NO/15

Kirkirarren labari ne👌

Ina godiya ga Ubangiji daya bani ikon fara sakar mu ku wannan labarin a yau ranar Litinin 13 ga watan Afrilu shekarar dubu biyu da ashirin da shida miladiyya, yadda ya bani ikon farawa lafiya ina rokon yasa na gama lafiya cikin amincin ya ba ni ikon rubuta abin da zai amfani al'umma.

Wannan labarin kacokam ɗin sa sadaukarwa ne ga 'yar uwata Ruƙayyatu (Aunty ummi)

SAKON GODIYA ga shuwagabannin kungiyata YOTA da mambobinta baki ɗaya, ina rokon Allah ya kara hada kanmu mu zama tsintsiya madauri guda.

GODIYA TA MUSAMMAN ga Ayshercool, Amanar cool, Nusy bee, da kawata Oum Nihal bisa jajircewarku da taimakon da kuka bani ta ɓangarori daban-daban kafin fitar wannan labari Ubangiji ya biya ku da gidan aljannah.

Page 1

Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai.

Dare mahutar bawa inji masu iya magana, tabbas haka yake amma ni a gareni wannan daren da na riski kaina a ciki yau, na rasa da mai zan kirashi, kai tsaye zan iya kiran shi da daren baƙin ciki a sauƙaƙe, amma tabbas lamarin yafi gaban haka. Dare ne dana shirya rabuwa ko kuma na ce tserewa daga gaban iyaye na mutane mafi soyuwa a gareni, idanuna sun rufe ruf, zuciyata cike take da kudirin *Daukar fansa* Tsakar dare ne Sakaliya ko ina ya dauki shiru gabas, yamma, kudu da arewa, ko wani bawa a daidai wannan lokacin yana gida dan hutawa, mafi rinjeyen mutane haƙarƙarinsu na a ƙasa suna barci dan huce gajiyar rana, jaruman bayin Allah suna tsaye a gaban mai duka, yayin da wasun su ke aikata akasin hakan. Na kasance ɗaya daga cikin waɗan da ke a ido biyu a cikin wannan dare, kwance muke a kan katifarmu nida ‘yar uwata ɗaya kwalin ƙwal a duniya *Maryoji* Jajayen idanuna a bushe suke ƙamas babu alamar wani abu mai kama da barci zai ziyarce ni,duk da kasancewar sa gwanin iya sata, a hankalina na kai hannuna na dafe saitin zuciyata da nake ji kamar za ta kama da wuta tsabar yadda take yi min 'kuna, wani irin zafi na ke ji a cikinta tare da wani irin tuƙuƙin bakin ciki, so na ke yi hawaye su zubo daga idanuna ko zan samu sauƙin abin da nake ji a cikin zuciya ta amma Ina! Abin ya gagara, lallai zubar hawaye ma rahama ce ga bawa. Juyi nayi tare da kai hannu na dafe marana da nake jin shi yana min ciwo. kamar wacce aka kunnawa majigi haka abin da ya faru a yammacin yau ya shiga dawomin tar a kwakwalwata. Tuno yadda yara harda ma wasu manyan marasa kamun kai, suka ringa jifan Baffanmu suna ja mishi riga tare da yi mishi ihu kamar wani ɓarowa yasa zumbur na mike zaune, tuno yadda baffanmu ya shigo gida a ɗazu da yamma jikin shi butu butu, yara sun jefe shi sun watsa mai ƙasa har sun jimai ciwo goshin shi na tsartuwar jina yasa naji ƙuna da rad'ad'in da zuciya ta kemin ya ninku ninkin ba ninkin, lokacin kuwa da zuciyata ta haskomin , su Talatuwa da su Innan Zainu da kande da sauran matan kauyenmu sun rufa akan innarmu suna mata tijara suna zagin ta har da masu dungure mata goshi, take na ji wani irin kuka ya taho min daga can 'kasan zuciyata, da sauri na kai hannu na dafe bakina saboda kar sautin kukana ya tashi Maryo wacce da'ker ta samu barci b'arawo ya yi awon gaba da ita, kuka na shiga risga bil hakki, kuka mai cike da kaico da ba'kin ciki, nadama tare da danasani, duk wannan cin mutumcin da wulakancin da tozarcin da ake yiwa iyayena ni ce sila,ni ce na janyo musu, iyayena basu cancanci wannan ba'kar sakayyar daga gareni ba, sun soni sun nuna mini gata sun bani tarbiya ingantacciya tare da ilmi na boko dana Mahammadiya, iyayena sun kasance mutane masu kima da daraja a cikin wannan dan 'karamin kauye namu, mahaifin shine limamin wannan kauye yayin da mahaifiyata ta kasance mace mai daraja wacce matan kauyen mu ke matukar girmamawa amma cikin abin da baifi rabin awa ba nasa 'kafa nayi fatali da duk wannan d'aukaka da girma da iyayena keda shi a idanun mutunen yankinmu, tunda wannan lamari ya bayyana Innarmu kullum cikin kuka take babu dare babu rana, ta zama wata sususasciya, gashi tun daga ranar har zuya yau d'in nan Kalmar A bata shiga tsakanin mu ba, da idanu kawai take bina wanda hakan yana matu'kar d'aga min hankali. Har gara daga bangaren Baffa, a ranar yayi min duka, duka wanda ya asma sunan sa duka, duka irin wanda ake yin shi da niyar daukan ran wanda ake dukan, Allah ne kawai yasa kwanana na gaba da babu abin da zai hana na she'ka barzahu, daga ranar kuma ya d'auki gagarumar gaba dani wanda ko kallona bayayi balle har takai ga ya amsa gaisuwata,da kad'an da kad'an ya fara kula ni, wata kila tausayi na bashi ganin yadda na lalace na fita hayyacina a cikin kwanakin da basufi bakwai ba, ranar daya fara jehomin tambaya akan lamarin sai da na saki guntun fitsawa, “Aishatu Wanene shi?” Rana ta farko a tarihin rayutawa da na ji da kunnuwana Baffa ya ambaci sunana gatsau. Innalillahi wainnailaihi rajiun, hankalinsa bai taɓa tashi irin na wannan lokacin ba, ji na yi jikina gaba daya ya dauki wani irin yammm! Tamkar wacce minjirya ya kama, kaina ya yi nauyi tamkar an daura mini kullin kaya, Shin me zancen, wata amsa zan bayar, bayan ni karan kaina ban san shi ba, bansan daga duniyar da yake ba hasalima ko cikakken sunan sa ban sani ba, a cikin a bin da baifi wata biyu ba ya shigo yaruwata yayi mata illar da har duniya ta nad'e bazan tab'a manatawa da shi ba, a hankali cikin shehshekar kuka na furta " *Babangida* ka cuce ni ka cuci rayuwata kaci amanata kaci amanar soyayya, na tsaneka tsana mafi muni tsanar da ban taba yiwa wani mahaluki irin shi a duniya ba, meye laifina dan na mi'ka maka dukkan yardata da soyayyata? A silarka na zama tamkar mujiya a cikin jama'a kowa guduna yakeyi kowa kyamatata yake yi, na zama abin kallo abin nuni a bin zagi da Allah wadai a cikin kauyen mu, hatta a gurun iyayenan ban samu rangwame ba, a gurin mutum d'aya 'kwal nake samun sassauci itace y'ar uwata Maryo. Har gida ake shigowa kallo na, kallo irin na ƙyama, da wukakanci, masu zagi nayi masu tsinuwa nayi. Kuma abin bai tsaya a kaina ba harda iyayena, wad'an da basu ji ba basu gani ba, Baffanmu bai da dama ya fita waje jama'a zasu yi caa akan shi da zagi da habaice habaice, wasu ma har kofar gida suke suke sallama da shi su ci zarafin sa, innarmu kuwa har cikin gida matan kauyen ke biyota su 'kare mata tijara, zagi ta uwa ta uba kwace itace ta aikata abin bani ba, daidai da Maryoji bata isa ta lai'ka kofar gida ba balle kuma ni uwar gayya. Zazzafan numfashi na sauke tare da sa hannu na share hawayen dake gudu akan dakalin fuskata, Ya zama dole na nisanci iyayena domin su samu sassauci. Na tabbata ganina yana 'kara kuntata zuciyar su musamman innarmu wacce gaba d'aya wani irin kallo take bina da shi wanda yafi kama da kallon tsana a duk sanda idanun mu suka had'u, idan bana tare dasu dole zasu manta dani wata rana duk da nasan abu ne mai matu'kar wuya. Lokaci daya naji zuciya ta dake hawaye da ke zubowa daga idanuna ya 'kafe, shawaran da zuciyata ke bani ne keta amsa kuwwa a cikin kwakwalwata, a fili na furta "kuyi hakuri iyayena ya zama dole na nesance ku, domin ku samu sauki da rangwame akan halin dana jefa ku ciki." Kamar wacce ake controlling da remote na mi'ke tsaye cikin azama tare da kunna yar tocilana mai batir na nufi jikin bango inda jakukunan mu na makarantar boko ke rataye, nawa na dauko na dawo a hankali na nemi bakin katifar mu na zauna, fefa na falla, na d'auki biro, na saita domin rubuta wasikar da nayi niyya, kamar almara take hannuna ya kama rawa yana karkarwa kwace da gangan nake girgiza shi, kasa rubuta koda Kalmar A nayi a karshe na ajiye biron tare kife kaina na lula duniyar tunani, shin idan nayi haka na yiwa iyayena adalci kuwa, na jefawa kaina tambaya, wani bangare na zuciyata ne ya bani amsa da cewa, “wannan shine cikakken adalcin da zakiyi musu, koba komai idan basa ganin ki a gabansu zasu manta dake koda lokaci zuwa lokaci, kuma ta haka ne kawai zaki samu damar daukar fansa akan wanda ya tagayyara rayuwar ki, ya jefa ki keda iyayen ki a cikin halin kunci da bakin ciki, tuno wanna kudiri nawa na daukar fansa, yasa naji kamar ana ingizani cikin sauri na shiga rubutu a jikin fefan wanda kafin na gama rubutun gaba daya ruwan hawaye ya gama ji'ka fefan, duk wani bayani da suke nema akan lamarin na rubuta musu, tsab na fede musu biri har wutsiya tare da basu hakuri da neman sanyawar albarkar su a karshe na sanar musu da cewa kar suyi wahalar nemana domin baza su same ni ba na shiga duniya neman Babangida domin na dauki fansa akan shi idan da rabon zamu gana wata rana Allah ya kaddara saduwar mu da alkhairi, ina gama wa na linke shi na ajiye shi a dai-dai inda nake da tabbacin Maryoji zata gani data farka, asusuna na dauka na fasa, na tattare kud'ad'en dake ciki, daga ni sai riga da zani sa'kin dake jikina irin namu na fulani da hula, sai ko yan kud'ad'ena dake ri'ke gam a hannun na, na kwashi y'an takalma na na roba a hannu, cikin sand'a na bud'e 'kofar fita daga d'akin mu, har na zura 'kafata d'aya a waje na juyo na kalli y'ar uwata Maryoji dake kwance tana barci ,jinayi hawaye sun ziraro min a fuskata, a hankali na furta sai "wata rana yar uwa Allah ya 'kaddara saduwarmu da alkhairi." da sauri nasa kai na fice daga d'akin, babu kowa a tsakar gida duk mutanen gidan na d'akunan su, wani baban mayafin Innata da take yawan amfani dashi na gani rataye akan igiyar shanya, janyo shi nayi na yafa a jikina, cikin sand'a na fice daga gidan ba tare da kowa ya ganni ba, har na isa zaure na tura kofar karan da ke a matsayin kofar gidan naji bazan biya wucewa ba tare da na saka Inna da Baffa a idanuna ba, a hankali na juyo na dawo cikin sand'a na isa 'kofar d'akin inna hasken dana d'an hango ya tabbatar da cewa idanun ta biyu, d'an d'aga labulen nayi a hankali na le'ka, tana zaune akan sallaya ta daga hannu sama tana kai kukan ta gurin mai duka hawaye gaba d'aya ya gama wanke fuskar ta, a bayyane take addu'an cikin yaren mu na fillanci wanda shine yaren da tafi ji sosai bisa ga ko wani yare, jin irin addu'an da take yi yasa naji 'kafata na naiman kasa daukar gangar jikina, addu'a takeyi akan Allah ya amshi rayuwarta ta huta da bakin cikin da ni *A'ishatu* na sanya ta a ciki, hankalina naji ya kara tashi, illahirin jikina ya dauki rawa, kuka mai sauti ya subucemin da sauri na saki labulen tare da barin 'kofar dakin, ji nayi bazan iya le'ka Baffa ba, dan shima bansan abin da zan tarar ba, da sauri na fice daga gidan wannan karon ba tare da na sake waigawa ba.

*Mafarin lamari*....

AyshaNalado ✍️ [5/14, 6:00 AM] Oum khadeejarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

By

AyshaNalado

Young Talented Writers Ass.

page 2

*Bayan wasu shekaru....*...

Tsaye take a gaban dressing mirror tana makeup, ta dangwala wancen ta shafa wancen fuskar nan ta ɗauki hoda da jambaki bajau. Matashiyar budurwa ce wacce ba za ta gaza shekara 20 zuwa da biyu ba. Daga bayanta A'ishatu ta tsaya cikin yanayin damuwa ta ce "Oh Allah Salmah mu je mana yamma na ƙarayi fa, kuma sarai kin san idan 5:30 ya yi Ammi ba za ta barmu mu fita ba ko?” Ba tare da ta juyo ba, ta na ci gaba da abinda take yi cikin sauri sauri take faɗin "Sorry Sister dan Allah ki yi hakuri 2 minute, eyeliner kawai ya rage min." Gyara tsayuwa ta yi tana bin bayanta da kallo, a zuciyarta tana mamakin shegen son kwalliyar Salmah, kamar wacce Aljanin kwalliya ya aura, sam bata iya zama da fuska a bushe sabanin ita da ko kwalli da man leɓe, wata rana sai Ammi ta fatattake ta take sakawa. Turo ƙofar ɗakin a ka yi, Salman ya shigo babu ko sallama, a dan fusace ya ce "Zo mu wuce sister, mu bar ‘yar rainin hankalin nan, ita ba kyau ba sai shegen iyayi, ace kullum idan za mu fita sai ta ɓata mata, da wannan fente fenten nata na banza." Ya ƙarashe maganar tare da kama hannun Aysha ya shiga jan ta su tafi, ita kuma ta ɗan tirje. Juyowa Salmah ta yi ta auna mai wata uwar harara da manyan fararen idanunta da ta ƙara ƙawatasu da ƙwale-ƙwalen kwalliyarta “To almunafunfun, ba za ta bi ka ba, sai ta jira ni ɗin, idan ka matsu ka yi tafiyarka, sai mu sa driver ya kai mu." Ta karaso itama ta kama d'aya hannun Aysha ta riƙe, tsaki ya ja ya yi ƙwafa, tare da cewa."Banza mummunan kawai.” Zaburowa ta yi kamar za ta kai mishi duka, a tsiwace tace "Salman ka kiyaye ni." Mari ya kai mata, da sauri ta saki hannun Aysha ta dunƙule ta kare fuskarta, ya sake yin ƙwafa, ya ɗauke hannunshi ba tare da ya isa jikinta ba, yana auna mata hararar tare da faɗin “'Yar banza ga tsoro ga mugun aiki." Jin bai sauke mata yatsun nashi ba kamar yadda ta zata, yasa ta ɗago tana ci gaba da hararan shi tace "Me yasa ka fasa, ai da ka mareni ka gani.” “Mitsssw! Aikin banza kawai.” ta furta bayan ta ja dogon tsaki. Zai yi magana, Aysha ta dakatar da shi a da cewa "Dan Allah Salman ya isa haka, wai yaushe za ku girma ne saboda Allah? Ku kenan kullum cikin tashin hankali sai kace ba 'yan uwa da suka fito cikin mahaifa ɗaya ba. Ku ba yara ƙanana ba balle ace ba ku da hankali, wlh lamarin ku ya fara isana, ni mu tafi yamma na ƙara yi.” Yadda ta yi maganar a ɗan zafafe yasa Salman bai sake tankawa ba sai ya yi ƙwafa ya girgiza kai yana kallon Salmah dake banka mai harara ya ja hannun Aysha suka fice daga ɗakin, Salmah ta rufa musu baya tana ‘yan kungunai.

A falo suka samu Ammi zaune tana kallon Sunnah Tv, tun daga yanayin yadda taga fuskokin twins ɗin nata, tasan an raba hali, lamarin su yanzun ya daina damun ta, idan suna abin su babu mai shiga domin a nan take za su baka kunya, yi tayi kamar bata ga abun da suke yi ba. Sallama suka yi mata, ta yi musu addu'a tare da kashedin cewa karsu kai magriba, idan ba haka ba sun kashe hanyar gobe, har suna had'a bakin gurin cewa "in sha Allah Ammi ba za mu daɗe ba." Tace "Allah yasa." Har sun kai bakin kofa tace "Amm! A'ishatu." Cikin sanyinta wanda ya zame mata wani ado na musamman ta waigo tare da cewa "Na'am Ammi." "ki kula da kanki, ki kula da waɗannan shashashun da kullum basa girma karki bari su raba hali a cikin jama'a kin ji ko?" Ɗan dariya ta yi tare da cewa "in sha Allah Ammi zan kula sosai." Tace "OK bye kowa yamin tsaraba,da abinda na ke so, zan tantanece cikin yaran Ammi wa yafi sanin abinda Ammi ke so yau.” cike da tsantar kulawa da kauna ta yi maganar, Salmah ta ce "Ni zan lashe game ɗin nan domin nafi kowa sanin abinda Ammina ke so, kuma za ki gani." Salman ya auna mata harara tare da cewa "yen yen yen yen! da dogon bakinta kamar Hajiya Saude na gaba tana binta a baya." Duk dariya suka saka mata, aikam ta ƙulu idan da abin da Salmah ta tsana a duniya ace tana kama da kakarsu mahaifiyar Abbbansu wacce suke kira da Hajiya Saude, dalili kuwa, sam kanwarsu bata ciƙuwa waje guda, duk da kasancewar kuwa a zahirin gaskiya kama suke kamar an tsaga ƙara. Ganin yadda suke mata dariya harda Ammi yasa ta kara ƙuluwa cikin fushi ta bud'e kofar falon ta fice da sauri fuuu! kamar zata tashi sama.

A parking lot suka tadda ita jingine jikin motar Ammi wanda a shine Salman zai ja su, ko kallonsu ba ta yi ba ta buɗe bayan motar ta shige, suma basu ce mata komai ba suka shiga, Salman ya zauna a mazaunin driver Aysha ta zauna a gefensa ya tada motar mai gadi ya wangale masa get yana daga mana hannu tare da yi musu a dawo Lafiya. kallo ɗaya Aysha ta yi wa mai gadin ba tare da ta amsa shi ba ta dauke kanta tare da hade girar sama data ƙasa, saɓanin Salman da Salmah da suka amsa mishi a sake cike da kulawa. A haka suka fice daga gidan, tare da daukir hanyar *kangiwa green land* Bayan sun daidai ta akan babban titi, kallo Aysha salman yayi yace "Sister me yasa baki son mai gadin nan namu ne? Ina lura dake baki amsa gaisuwarsa, kuma ko fara'a kike idan ya yi magana sai ki hade rai, alhali yana da mutunci ni banga aibun shi ba, ko wani abu mara kyau ya taba haɗa ku ne bamu sani ba?" Dan kallonsa ta yi tare da ɗauke kai a hankali cikin yanayin ɓacin ran da ba za ta ce, ga musabbabinsa ba tace "Babu abin da ya taba haɗa ni dashi Salman, bana son sa ne kawai saboda sunan sa *Babangida*." Kasancewar shi gwanin barkwanci sai yayi dariya yace "Me sunan *Babangida* yayi banda rigima irin taki, kya ma dai faɗi gaskiya" Dauke kai tayi ba tare da ta bashi amsa ba a haka suka iso kangiwa green land.

Readers Also Read