Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 2
Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 2: Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 2. *kangiwa green land* fitattace ne kuma sanannen babban shopping mall…
2,663 words
*kangiwa green land* fitattace ne kuma sanannen babban shopping mall wanda sunan sa ke amsa kuwwa aciki da wajen birnin Kaduna. Wuri ne da ba ko wane irin mutum kara zuɓe ke iya zuwa domin yin siyayyaba sai wanda yaci ya tada kai da masu gida rana. Wuri ne da yan mata da samari 'yan hutu y'ay'an manya dama y'ay'an y'an uwana talakawa y'an karyan nera ke karakainin zuwa domin shakatawa da kuma siyayya musamman da yammci idan kaje gurin wurin zaka same shi cike da matasa, har ma da manya dama ƙananan yara jefi jefi. Kamar kullum yau ma wurin cike yake taf kowa na harkar gaban shi, a daidai wannan lokacin, Salman ya yi parking a farfajiyar wurin, fitowa su ka yi suka nufi cikin wurin domin yin shopping wanda dama shine abin da ya fito da su daga gida, kowannen su daukar basket yayi suka fara tsintar abin da su ke so tun suna yi a tare har takai ga sun rarrabu kowa yayi nashi ɓangaren. Mintuna 30 bayan rabuwarsu Aysha ta kammala sayayyar duk abin da take bukata harda na Ammi da tace su siyo mata, tunanin ta inda zata fara neman su Salmah ta shiga yi dan a zahirin gaskiya kangiwa green land, babban wajene na bugawa a jarida, kamar daga sama ta jiyo sautin gudu daga bayanta tare da dan hayaniya da sauri ta jiyo, su ɗin ne ke tafe kamar yadda tayi tsammani, tsayawa tayi ta riƙe kugu tana hararar su, wannan lamari na tagwayen Ammi na ci mata tuwo a kwarya, sam basu kula da yanayin da take ciki ba sai ma Salmah dake gaba ta ƙaraso bayanta tare da ƙamƙameta tana cewa "Sister ki boye ni Salman zai dukeni." shiko Salman ƙokarin kai mata cafka yake yi tana dojewa tare da tura Aysha dake kokarin hanashi dukan nata har hankalin wasu daga mutanen wurin ya fara dawowa kansu, suna cikin wannan yanayi kamar daga sama su ka ga an canja hasken wajen ya koma wani irin launin wuta mai kala kala tare da bada wani sauti ɗin! ɗin!! ɗin!!! kafin su gama mamaki su ka ji sufikun dake maƙale a kowani kusurwa na wajen sun d'auki kururuwa da shelar cewa ana ba kowa da kowa umarnin da ya ajiye duk abin da yake yi ya fita an ba kowa five minutes, a tsorace suka shiga tambayar juna mekefaruwa, sai dai cikinsu babu wanda zai iya baiwa wani amsa, tuni firgici ya gama bayyayana ƙarara a fuskar Aysha domin tamkar farar kura take wajen tsoro. Kafin su dawo daga wanna shock ɗin suka tsinkayi muryar wasu manyan y'an mata daga gaban su, cikin farin ciki dayar ke cewa ɗayar "ke Hafsa kamar Mr AA kangiwa ne fa ya kawo ma wurin ziyarar bazata." , cikin zaro ido wacce a ka kira da Hafsa ta ce "kice wlh." "wlh kuwa haka na ji yanzu ana ta fad'a." Ihun murna Hafsa ta saka tare da rungume kawarta cikin wani irin matsanancin farin cike take cewa "finally yau zan ganshi ido da ido wayyo daɗi kashe ni." Sosai Aysha ta cika da mamakin halin da y'an matan nan suka shiga, sai dai bata kai ga jefawa Salman tambayar da ke sakadar zuciyarta ba, taji Salmah da ke kusa da ita ta kurma wani uban ihun murna tana tsalle a rude take cewa "Mr AA kangiwa Innalillahi Salman where is my phone, a she da rabon zan ganshi ido da ido wata rana wayyo ni salamatun Ya Anas yau ina cikin Alheri" Shima Salman ɗin duk a ruɗe yake da farin ciki jin wai Mr AA kangiwa yazo wajen , kan Aysha gaba ɗaya ya gama kullewa, Mr AA kangiwa, Mr AA kangiwa, haka ta yi ta maimaita sunan a zuciyarta kamar mai bitar hadda, tabbas tasan sunan, ba yau ne karan farko data fara jin sa a bakin mutane ba. Shin wanene shi? Wani matsayi gareshi haka da kowa ke rawar 'kafa dajin sunan shi, shiba sahabi ba, shiba wani shahararren malami ba, Hannunta da Salman ya figa da sauri ya jata su ka yi haryar fita daga wurin shine ya katse mata tunani, a guje Salmah da duk ta wani susuce ta rufa musu baya. Rige rigen fitowa suka samu anayi kowa ka gani Kalmar Mr AA kangiwa ke bakin shi, jikin Aysha bai 'kara yin sanyi da lamarin ba sai da taga yadda manyan y'an mata masu ji da kansu y'ay'an masu kuɗi suka ruɗe, da jin zuwan wannan d'an taliki da sunan sa ke amsa kuwwa a kunnayenta, kuma abin mamaki baga yan mata kawai ba harda ma zaratan samari masu ji da kansu dake wurin, fuskar kowa cike da farin ciki tare da zaƙuwa da ɗokin son ganin mamallakin wannan suna, mamaki bai kara kasheta ba sai da suka fito harabar wurin taga cincirundon y'an jarida, gidajen redio dana talabijin babu iyaka ga polisa summa wajen kewanya. Wai ashe ma duk wannan karakainin da a ke yi kan jirgin bai riga ya ƙaraso wajen ba labari kawai aka samu yana hanya shine fa duk wuri ya ruɗe, duk da ba ta san wanene shi da kuma matsayin da yake dashi a wurin mutane ba, tana da tabbacin shi ɗin na musamman ne, haka kurum ta tsinci kanta da son ganin koma wanene wannan mutumin ɗan baiwa mai dubun masoya haka. Salmah ce ta dinga kutsawa dasu gaba gaba inda za su samu su ganshi da kyau, tuni wurin ya kara haɓɓakewa da mutane , da alama ba iya waɗan da ke cikin wurin kawai ba ne ke dakon jiran isowarsa harda wad'an da suka samu labarin zai zo suka taso takanass dan ganin shi. Polisawa sai aikin kakkare mutane su ke yi domin samar mashi da hanya, Aysha dai na tsaye kusa da Salmah da duk ta gama rud'ewa sai wani rawar jiki ta ke yi tana jiran ganin ikon Allah, tsayuwar su kamar da minti ashirin, suka fara jiyo wani irin jiniya mai masifar ƙara, wurin ne ya dauki hayaniya masu ihu nayi masu cewa gashi nan ya iso nayi kowa na fad'in albarkacin bakin shi, Sosai Aysha ta zuba wa hanyar da take da tabbacin tanan nake jiyo 'karar jiniyar ido. Da wani irin mahaukacin gudu wasu zafafan motoci masu mugun tsada suka shiga shigowa wajen a jere, a tare suka shiga yin parking cikin wani salo na gwanancewa, take wurin ya kara daukar sowa da tafi, yanayin shigowar motocin da yanayin parking d'insu ma kawai abin birgewa ne ga mai kallo balle kuma batun kyawu da tsadar motocin, motocine guda goma sha daya reras, gaba dayan su bakake sai guda ɗaya tal na tsakiyar su wanda ya kasancewar fari sol sai daukar ido ya ke yi kwace da diamond a ka ƙera shi. Kusan mintuna biyar suka dauka kafin a hankali murafen bakaken motocin su bud'e a tare a lokaci guda, wasu irin zaratan majiya karfin escort suka shiga fitowa daga cikin motocin sanye da bakaken suit fuskokin su sanye da maka makan space irin no respect d'innan tsit kake ji wuri ya dauki shiru kamar ba shi ba ne yanzu kamar zai fashe da hayaniyar jama'a, d'aya daga cikin escort d'inne ne ya 'karasa gaban farin motar ya bud'e kofar baya tare da matsawa gefe d'aya ya kame kamar gunki, sai da ya share mintuna biyu sannan ya zuro 'kafafunsa dake sanye cikin wasu arnayen ba'ka'ken takalma sawu ciki masu masifar kyau waje, zuru kowa yayi ana jiran ya 'karasa fitowa masu yin video irin su Salmah tuni dama suka fara kwasa abinka da zamani na social media, abin watsawa baya kadan to balle baiyanar AA Kangiwa da ranar Allah ai abin kallo ne ga jama'ar Kaduna kai jama'ar Nigeria ma gaba ɗaya, wasu ma live su ke daurawa, sai da ya kuma kwashe wasu mintuna uku kafin ya zuro sauran jikinshi gaba d'aya waje, yadda lokaci d'aya gurin ya d'auko wani irin sowa da tafi sai da Aysha ta firgita, inda kasan wad'an da aka ba umarni a tare kamar irin a fillin ball din nan anci kwallo, yana fitowa escort ɗin shi guda shidda suka layu a bayan shi yayin da sauran ke tsatstsaye a inda suke suna muzurai, ba ta gefen da su Salmah suke ya fuskanta ba ya juyo musu baya, hakan ya yi musu shamaki da ganin zahirin fuskarsa. Tun da Aysha ta sauke idanunta a kan faffadar bayan shi dake sanye cikin wasu irin zafafan suit black masu mugun kyau da masifar tsada, wanda akalla kudin da aka siyen su ya ishi talaka zama karamin attajiri gabanta ya yanke ya yi mummunar faɗuwa haka siddan. Wata tsayuwa yayi irin ta zaratan matasa majiya karfi, ba ta san lokacin da ta furta, "Ya subhanah!." A bayyane ba. A tsaye yake ƙem dogo mai kirar cikakkun maza, sumar kanshi ma kawai abin kallone, gashin baki ne sidik saisayayyen irin tamu ta baƙar fata, sai dai a cike take da kan an yi mata askin zamani irin ta matasa masu aji, ga taushi wanda mutum zai shaida hakan ko a ido, sai sheki take tana daukar ido da gani ba karamin maƙudan kudi yake kashe mata ba. kwarai ta zaku da son ganin fuskar koma wanene wannan mutumin, bata dawo daga duniyar begen shi data lula ba, taga ya fara wata irin tafiya mai cike da ƙasaita da nutsuwa tamkar wani basarake, ya durfafi main entrance na mall ɗin, escort din shi biyu suka rufa mishi baya, yayin da sauran ke tsaye a inda suke kamar an dasa su, ji ta yi bazata iya bari ya shige wurin nan ba tare da ta samu nasaran ganin fuskar shi ba, tunanin ta yadda za ta samu damar ganin fuskar shi ta lalu, ƙur ta kurawa bayan shi idanu kamar zata hango fuskar shi a bayan nashi, Salmah ce ta katse mata tunani da cewa "Oh shirt! Sister Eshart mun tsaya ta bayan shi gashi bamu samu ganin fuskashi da kyau ba, zo mu kutsa ta can mu samu muje ta gaban shi kafin ya shige ciki." Kamar daga sama ta tsinci maganarta jin abin da take cewa yasa ta zabura ta damƙi hannunta da mugun sauri ta ringa janta suna rasta mutane suna kutsawa, burinta bai wuce tayi arba da fuskar shi ba, dai-dai sun iso ta gaban shi yana gaf da shigewa cikin wurin, cak ta tsaya tare da wani irin zaro idanu waje lokacin da idonuna suka yi arba da fuskarsa, fuskar da ko mutuwa tayi ta dawo ba ta jin zata bace a idanunta, a matukar dimauce ta furta *Babangida*
Rikita rikita shin da gaske Babangida Aysha ta gani a matsayin AA kangiwa ko kuwa gizo ya ke yi mata. Shin wai menene haɗin Shatou ɗiyar Baffa da Babangida ne? Yaya haɗuwar ta kasance? Tafiyar mai tsabta ce, nishadi kyauta, za a wasa kwakwale, zuciyoyi sa su yi laushi, dambarwa iya dambarwa let's go ma fiful wannan dai matashiyar marubuciyar ce da ta nishadantar daku da labarin DAMA TA BIYU, sannan ta sake gwangwaje ku da JOY kun dai san hannunta, to wannan tafiyar tasha banban da ta baya kar ku bari a yi babu ku.
Aysha Nalado 09116099486. [5/14, 6:00 AM] Oum khadeejarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀
By
AyshaNalado
Young Talented Writers Ass.
Page 3
Yadda ta taka wani irin wawan birki ya sa Salmah saurin juyowa ta kalle ta. Kafin ta yi wani yunkuri ya gama shigewa cikin wajen gaba ɗaya, take kanta ya fara juyawa, ƙafafunta na neman su gaza ɗaukar gangar jikinta, jiri ya shiga kwasarta, da sauri ta riƙe Salmah dake kusa ita gam, zuciyata na sake hasko mata hoton fuskar shi.
A gigice Salmah ke faɗin "Menene Aysha mekefaruwa?" gaba daya ta ruɗe ganin yanayin da ta shiga cikin abin da baifi kiftawar ido ba. Kasa bata amsa ta yi sai wani irin numfashi da take fesarwa mai zafin gaske, ji take yi zuciyata kamar tana ci da wuta.
Sannu Salmah ta shiga jero mata, duk da bata san asalin abin da ke damunta ba, ɗagowa ta yi ta sauke mata idanunta da suka rine lokaci guda, da murya mai kaushi tace "Salmah mu bar wurin nan." Da sauri ta amsa mata da "to." Tare da lalubo lambar Salman ta danna masa kira, ta sanar mishi abin da ke faruwa, bai bata lokaci ba ya iso inda suke yana jero wa Aysha tambayoyi a ruɗe, maimakon ta bashi amsa sai cewa ta yi "Salman ka kaini gida, zuciyata ciwo." Ta faɗa ta na nuna kirjinta, Yace " Subhanallahi gida ko asibiti, idan ba ki da lafiya asibiti ya kamata na kai ki." Ganin yana bata mata lokaci yasa ta ɗago a masife tare da daka mai tsawa "Salman nace ka kaini gida ko!" Yasha mamakin jin wai yau A'ishatu ce take daka mai tsawa haka, yarinyar da magana da karfi ma bata iya ba, ya tabbata a kwai wani baban al'amari dake faruwa, bai sake musa mata ba sai cewa yayi "is okay na ji muje na kai ki gida, kiyi hakuri, ke yar uwata ce shi yasa na damu da lafiyar ki." Yanayin yadda ya yi maganar a sanyaye ya sanyayyar mata da nata jikin, duk da halin da zuciyarta ke ciki a lokacin sai da ta ji babu daɗi akan abin da ta yi wa Salman, kamata yayi ta bashi hakuri a lokacin don daga yanayin kalaman shi, ta fahimci kamar ranshi ya sosu, amma a halin da take ciki ba za iya ba, ko a mota zaman kurame su ka yi, kowa da abin da yake tunani a ransa, cikin ƙanƙanin lokaci suka iso gida, yana yin parking ta fito ba tare da ta tsaya jiran ɗaya daga cikin su ba ta nufi apartment ɗin Ammi wanda a nan ne ɗakin su yake , cikin sa'a Ammi bata parlour hakan ya mata daɗi, dakin su ita da salma ta zarce, tana shiga ta yi wurgi da ɗan karamin mayafin dake jikinta ta zame dan kwalin kanta tare da zare ribbon ɗinta take dogon gashinta mai laushi irinta fulanin usuli ya barbazu har kan kafaɗunta, faɗawa kan bed ta yi, ta kwanta rigingine tare da rintse idanunta, hoton fuskar shi na sake yawo a kwakwalwarta, tana bukatar nazari, tunani da kuma dogon bincike akan wannan mutumin, tabbas kamannin Babangida ta gani kwance akan fuskar shi, amma shi ɗin yafi Babangida girma, zati, cika ido da komai, shin wanene wannan mutumin mai kama ɗaya sak da Babangida?
A can parking lot kuwa da kallo su Salmah suka rakata har sai da ta kulewa ganinsu, lokaci ɗaya kuma suka kalli juna zuciyoyin su cike da al'ajabi, ba su taɓa ganin Aysha cikin wannan yayin ba tun tasowar su da ita, shin meke faruwane? Jiki a sanyaye su ka ƙaraso ciki suma, babu kowa a falon, Salman ɗakin shi ya nufa saboda gabatowar magriba da ake ta ƙira, Salmah kuwa ɗakin Ammi dake upstairs ta haura domin ta sanar mata da dawowar su.
Yadda Ammi ta ganta jiki a sanyaye yasa ta mai da dukkan hankalinta gareta, ganin salmah a irin wannan yanayin yana kayar mata da gaba dan yanayi ne da take shiga idan bata da lafiya ko kuma take cikin tsananin damuwa, ƙureta da idanu ta yi har ta ƙaraso gabanta ta zauna tare daura kanta akan cinyarta, hannu Ammi ta kai ta taba jikin ta, ta ji sanyi kalau babu alamar zazzabi, cikin sanyi tace "Mekefaruwa ne salamatuna waya taɓa ki? ko Salman ne?." Sai da ta sauke wani gwauron numfashi' sannan ta dago ta kalli Ammi tace "Ammi sister Eshart ce." Cikin mamaki Ammi tace "A'ishatu kuma? meya haɗaku, ina kuma ita A'ishan?" Amsa ta tayi da "Ammi babu abin da ya haɗamu." Take ta labartawa Ammi abinda ya faru. Shiru Ammi ta yi na wasu yan daƙiƙai tana maimaita sunan Babangida a rantads tunanin in da ta taɓa sanin sunan, kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Yanzu ina A'ishatun take?" "Ta rigamu shigowa wata ƙila tana ɗaki." Miƙewa Ammi tayi ta fice daga ɗakin.