Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 3
Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 3: Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 3. A yadda take kwance haka Ammi ta sameta idanunta a runtse ta yi nisa…
2,614 words
A yadda take kwance haka Ammi ta sameta idanunta a runtse ta yi nisa cikin kogon tunani, har Ammi ta zauna kusa da ita bata da masaniya, sai da ta saka hannu ta kwashe mata gashin daya zubo ta gaba ya rufe mata fuska, sannan ta gane a kwai mutum a ɗakin, ba tare da ta buɗe idanu ba tace "Salmah wanene shi ?." Don duk a tunanina salmah ce ta shigo, gyaran muryar da Ammi ta yi ne yasa ta yi saurin buɗe idanunta dake rintse akan fuskarta ‘Ya zama dole na boye musu damuwata, ya zama dole na san yadda zan yi na kauda hankalinsu akan zargin abin zargi, bai kamata susan komai yanzu ba, a kwai aiki tukuru a gabana wanda ni kadai zan tunkare shi ba tare da sani ko taikamon wani ba,idan ma za su sani to tabbas sai naci karfin aikin’ a zuciyarta take wannan batun yayinda suka tsurawa juna idanun da Ammi kowannensu da abin da yake saƙawa a zuciyar shi, can kuma ta yunkura ta miƙe zaune tana sakarwa Ammi murmushin yaƙe, a ƙoƙarinta na boye halin da take ciki, martanin murmushin Ammi ta mayar mata, ta miƙa hannu ta shiga tattare mata gashinta, ta kama mata shi da ribbon tare da daura mata ɗankwalinta, ita kam sai bin ta da kallon take yi kamar ta samu wata sabuwar halitta, zuciyarta a cunkushe, kallonta Ammi ta yi tana sakin murmushi ta dafa kafaɗarta tace "Ki tashi ki yi sallah A'ishatu ga magriba nan ana ya kira, yanzu ba lokaci ba ne da mutum zai ba shaiɗan dama har ya jefa shi cikin irin wannan yanayin da kika tsinci kanki, lokaci ne da ake bukatar mutun ya yawaita istigfari domin samun yafiya a gurin ubangiji, ki tashi kiyi alwala za ki ji sanyi idan kuma kika yi sallah ki yi addu'a ki karanta alkur'ani mai tsarki, koma menene Allah zai kawo miki sauƙin sa kin ji ko?" Gyaɗa kai ta yi tare da sakin murmushi wannan karon murmushin gaske bana yaƙe ba, kalaman Ammi sun dan samar mata da natsuwa kaɗan har take jin ta ɗan fara dawowa cikin hayyacinta, miƙewa Ammi ta yi tace idan kin idar da sallan isha'e ki same ni a ɗakina, bayan fitar Ammi miƙewa tayi ta faɗa toilet ta dauro alwala tare da gabatar da sallan magriba, ta daɗe tsna kwararo addu'a a cikin sujadarta ta karshe kafin na sallame, bayan ta idar hannu ta ɗaga sama ta shiga kwararo addu'a tana yi ina hawaye, gaba ɗaya hankalinta ya tattara ya koma gaban ubangijinta, har Salmah ta shigo ɗakin ta nemi wuri ta zauna bata da labari, sai da ta dauki dogon lokaci sannan ta shafa, ba laifi ta ji sauƙi sosai a zuciyar ta dan zafin da take mata ya ragu kashi ashirin cikin ɗari, kallon juna su ka yi da Salmah, suka sakarwa juna murmushi, wanda ita nata na yaƙe ne da hausawa ke cewa yafi kuka ciwo, Salmah tace "Ɗazu kin firgitani sosai wlh A'isha, hankalina ya tashi amma yanzu tunda naga kin dawo daidai hankalina ya kwanta." Murmushi ta kuma sakar mata ba tare data amsa ta ba, Salmah bata damu ba dan in dai wannan dabi'ar ta Aysha ce ba baƙon abu bane a gareta, za ta iya mata magana sau biyar ma ba tare da ta bata amsa sau ɗaya ba wani lokaci, tun tana damuwa har ta ware ta saba da yanayi da dabi'arta, wayarta ta mika mata tace "Gashi Yaya yana son yin magana da ke tun ɗazu yake damuna na kai miki waya,wai ya yi ta kiran layin ki baki daga ba." karbar wayar ta yi yanzu ma ba tare da ta amsa ta ba, tana karɓa kamar jira ya ke sai ga kiran shi kuwa, bin screen din wayar tayi da kallo gabanta na faduwa, *Sweet bro* shine sunan da ke yawo a saman screen ɗin wayar, ta rasa mai yasa a duk lokacin da Ya Anas ya buƙaci yin magana da ita a waya take tsintar kanta a cikin yanayi na rashin natsuwa da faɗuwar gaba, ganin yadda Salmah ta tsatstsare ta da manyan idanunta yasa ta haɗiyi wani busasshen yawu tare da daga wayar ta kara a kunnenta, Ajiyar zuciya Salmah ta sauke tare da sakin murmushi sai kuma ta miƙe ta fice daga ɗakin.
Daga can bangaren Anas shima ajiyar zuciyar ya saki, sannan cikin dakakkiyar daddaɗar muryar shi yace "Assalamu Alaiki ƴar ƙanwata." Gwauron numfashi Aysha ta sake cikin sanyin murya tace "wa'alaikas-salam ."duk shiru su ka yi suna sauraron numfashin juna, shi ya fara katse shirun ta hanyar cewa "A'ishatu ba gaisuwa."Kunya ta ji ya kamata, da sauri tace ta ce "Ina wuni Ya Anas ya aiki ya karatu." Yace "Ba zan amsa ba tunda sai da na roƙi gaisuwar." A kunyace ta ce "Ka yi hakuri dan Allah wlh hankalina ne yayi nisa." yace "Na yi, , ina gajiya karatu da aiki Alhmdllh." Ta ce "Ma sha Allah." Duk shiru su ka kuma yi, ta rasa mai za ta ce mashi, har yau ta kasa sakin jiki da Ya Anas, kunyar shi take ji sosai duk da yana deɓe mata kewa sosai da daɗaɗan kalaman shi, yadda yake nuna kulawa sosai a kanta yana mata daɗi, tunaninta ne ya katse lokacin data ta tsinci muryar shi yana cewa "Ya kewana, koda yake nasan ba ki ji ko?." Girgiza kai tayi kamar yana gabanta tace "ina ji." Yace "ban yarda ba." Shiru ta yi bata bashi amsaba saboda har yanzu zuciyarta bawai ta gama daidai ta bane tana yin komai cikin karfin hali ne da kokarin danne damuwata, shi kanshi ya fahimci yau bata cikin walwala, dan haka hira ya shiga janta dashi cikin barkwancin sa, yanayin shi daya sak da Salman kusan komai masu yana kamanceceniya, sosai hirar yayi mata daɗi kuma ya ƙara samar mata da nutsuwar zuciya duk da ba wani amsa shi take yi ba rabi da kwatar hirar shi yake yi, ita dai kawai daga eh sai a'a ne nata sai ko murmushi.
Sai da yaji ana rangaɗa kiran sallan isha'e ta cikin wayar a masallacin gidan nasu sannan ya mata sallama domin ya bata damar yin nata sallar, duk da shi a inda yake yanzu tsakar dare ne lokacin da kowa ke kwance yana hutawa.
Tana ajiye wayar Salmah na shigowa ɗakin, cikin son danne damuwarta, ta watsa mata hararar wasa tare cewa "Hala laɓe kike min?" Ta kwashe da dariya ta ce "A'a leƙe nake miki ba laɓe ba." "Ai za ki aika indai keɗin da na sani ce." Cikin dariya ta ce "Bani wayata ni, zan yi abu mai mahimmanci dashi kuma ki ta so muje mu yi dinner Abie ya dawo yana tambayar ki." Miƙa mata wayar ta yi ta ce "Umm! soyayya manya, da alama yau Surajo na cikin alheri.." Take duk wata fara'ar dake kan fuskarta ta dauke dif, ta sake baki ta yi tana kallon Aysha irin kallon nan na mutum ya rasa abin cewa, ita ko dariya ta shiga kwasa sanin cewa ta kai ta bango, a duniya idan da abinda Salmah ta tsana bai wuce a dangantata da Suraj ba. "Allah ya isa tsakanina dake A'isha." Ta furta a kule kafin ta juya fuuu ta fice daga dakin, Salmah akwai sauran fushi sai dai kuma a take take saukowa,. Cikin dariya Aysha ta ce "Sorry lovely Sister jira ni mu je tare." Ko kallonta bata yi ba ta fice abin ta. Tana ficewa ta gimtse fuskarta dama duk abinda take yi karfin hali ne, tasan idan taci gaba da nuna dumuwarta a fili tabbas za su shiga damuwa a karshe su na iya danganta hakan da abinda ya faru dazu, garin haka har kilu ta jawo bau, wanda baza ta so haka ba, miƙewa ta yi ta gabatar da sallar isha'e, ba don ta so ko tana jin yunwa ba ta fita yin dinner, sai dan ta ƙara kwantar musu da hankali su tabbatar babu wata damuwa a tare da ita. Ko da ta fito duk suna kan dining, Abie, Ammi, Salman da Salmah, sai sauran empty sit guda biyu, tana fitowa duk da kallo suka bi ta, direct gun Abie ta nufa cike da ladabi ta tsuguna har ƙasa, da sauri ya ɗago ta cikin kulawa yace "A'a A'ishatu nasha gaya miki bana so." Murmushi tayi ta zauna a kusa da Salman, ta ce "Abie ka dawo lafiya ya hanya." "Alhmdllh Aisha." "Masha Allah, Allah ya huce gajiya ya bada sa'a da nasara akan abin da a ka je nema." Duk da amin suka amsa, Abie yayi murmushi yace "Nagode sosai da addu'a A'ishatu, shi yasa na ke son ki kina da hankali wlh, kin fi su O'o Hankali gashi dai nike ga kamar zasu iya girme miki a shekaru." Ammi ce ta karɓe zancen da cewa "Ai A'ishatu ta musamman ce,Allah yayi mata tarin baiwa da ba kowa ke iya gani da ganewa ba sai wanda ke tare da ita kullum zai gane qualities ɗinta." Murmushi Abie yayi yana hasaso wani lamari mai girma game da ita a zuciyar shi, , Ammi ce ta yi serving din kowa abin da zai ci sannan suka nutsu kowa ya maida hankali kan abincin shi, Salmah ce da bakin ta bai iya shiru ta shiga bama Abie labarin ganin da suka yiwa Mr AA kangiwa ɗazu a green land, cike da shauki take bashi labarin, haduwar shi da ƙasaitar shi kyawun shi da irin tarin dukiyar shi yadda mutane suka ruɗe da ganin shi da dai sauran abubuwan da suka ja hankalinta, Salman ma yana gefe yana saka mata baki jefi jefi, Abie yace "Umh! lallai kun taki sa'a, Mr AA kangiwa da ke da wuyar gani shine kuka ganshi yau a arha ɓagass haka, to komu da muke makusantar mahaifin shi, sai mu kwashe sati muna son ganin shi bashi da time, mutum ne da yasan mahimmanci lokaci. ga cika alkawari, Duk yadda a ka yi wani kwakwkwaran abu ne ya fitar da shi zuwa wurin nan a daidai wannan lokacin." Tunda aka fara magana akan shi gabanta ya shiga faduwa, shiru ta yi tana nadar duk bayanan da Abie keyi akan shi, wanda take da tabbacin za su mata amfani a cikin abin da ya tunkaro ta, ‘kenan Abie yana da wani ɗan kusanci da ahlin kangiwa? Ta jefewa kanta tambaya, ji ta yi abincin ya kasa wuce mata lomar data kai na karshe daƙer ta iya haɗiyewa, saboda dacin da zuciyarta ke mata, dabara ce ta faɗo mata, ta ajiye cokalin hannunta ta miƙe tana yamutsa fuska tare da riƙe ciki, har suna haɗa baki wurin tambayarta lafiya menene, "Cikina ne na ke ji yana yamutsamin zan shiga toilet ne." Ba tare da zargin komai ba Ammi tace “ Ayya sannu, Allah ya sauwaƙe." Ta yi gaba da sassarfa tana faɗin “Amin Ammi.” ɗakinsu ta nufa ta faɗa kan bed shiga sauke nurfarfashi.
Aysha Nalado✍️ [5/14, 6:00 AM] Oum khadeejarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀
By
AyshaNalado
Page 4
Bata san iya adadin lokacin da ta ɓata a kwance cikin wannan yanayin ba, zuciyarta na zafi ga wani irin bugu na wuce ƙa'ida da tun da Salmah ta ambaci sunan wanna mutumin mai fuskar Babangida bai sarara mata ba. Hakan ke kara tabbatar mata da cewa tabbas lokaci ya kusa, addu'arta ya karbu, kuma hakar da ta kwashe shekaru tana yi a duhu yana daf daf da ruwa, wanda zai ba ta damar komawa ga farin cikinta wato iyayenta. Rintse ido ta yi tana hasaso fuskar Baffanta, mutum mafi soyuwa a zuciyarta, da Inna, mahaifiyarta wacce su ke yi wa juna wani irin so, wanda zuciya da zuciya kawai ke aiki wajen fallasuwarta, sai kuma Maryo wacce kai tsaye ta bata matsayin rabin jikinta. Murmushinta mai kyau ta saki saboda wani yanayi mai dadi da take tunawa wanda ya shuɗe a baya, sai kuma nan take ta gimtse fuska tana fesar da wani irin wuci mai zafi tare da taune lips ɗinta da karfi, take fuskarta ya bayyana yanayin da zuciyarta ta shiga na tsantsan bakin ciki.
A haka Salmah ta doko sallama tare da shigowa ɗakin, wanda ya dawo da ita hayyacinta, ta buɗe idanunta da suka dan sauya launi, tare da sakar mata murmushin yaƙe, tana miƙewa zaune, Salmah ta ɗan yi jim tana kallonta, kafin kuma ta tako ta ƙaraso cikin ɗakin tana faɗin “Daga shiga toilet sai mu ka ji ki tsit." Dan yamutsa fuska ta yi tana dafe cikinta tace “Cikin nawa ne ban ji daɗin shi ba, shi yasa ban dawo ba." Tace "Ayya sannu ko da na ji dama, bari na duba miki ɗakin Ammi ko akwai flajin sai ki sha." Da sauri ta girgiza mata kai tace "ki bar shi kawai, na ɗan ji dama." Harara Salmah ta watsa mata tace "Ai dama ba son shan magani kike ba nima da gangan na faɗa." "Tunda kinsan da haka meye na wahalar da kanki wajen tambayata.” Ta taɓe baki, tace "ke dai ki ka sani." Ta kai karshen maganar tana shigewa toilet. Bayanta Aysha ta ƙurawa ido, tana tufka da warwara a zuciyarta na yadda za ta bullowa lamarin da ya taso masa bagatatan, ba za ta taɓa wasa da wannan damar ba wanda take da yakinin zai iya kaita ga cimma burin zuciyarta na abinda ta ginata a kai wato ɗaukar fansa, tsawon shekaru ta kwashe tana bulayin neman wannan damar tare da addu'a ba dare ba rana. Minti goma Salmah ta ɗauka a toilet, ta fito ɗaure da tawel da alama ruwa ta watsa, Aysha na kwance tana kallon ta har ta gama shiryawa cikin kayan barci karamar riga da dogon wando masu taushi, ta shimfiɗa pray mat ta kabbara sallar shafa'i da wuturi, har ta yi ƴan addu'o'inta ta shafa, idanunta a kanta kamar zata cinyeta da ido, sai da ta gama ta ninke sallayar ta mayar ma'ajiyar shi, sannan ta ta juyo ta kalle ta ce " yau na shiga uku da wannan mata kallo haka kamar wacece ta warke makanta." Murmushi A'ishatu ta yi tace "Hmmm wlh mamakin ki na dazu na ke yi." Taɓe ba ki ta yi tace "Ɗazun da na yi me kike mamakina, ke dai baki rabo da tsarabe tsarabe." Eshart Tace "Allah ba wasa na ke yi ba ɗazu a green land yadda na ga kin wani ruɗe da zuwan wannan mutumin da naji kuna ta kira da, Mr AA kangiwa, Allah abin ya ɗaure min kai shi ba sahabi ba shi ba ba tabi'i ko tabi'id tabi'ina ba." Wani irin zaro ido Salmah ta yi tace "keee! Kinsan wanene Mr AA kangiwa kuwa?" Ta karshe maganar tana rike haɓa, kallon ta A'ishatu ta yi a zuciyar ta tace "anzo wajen." Miƙewa ta yi zaune ta gyara zama cikin alamar ɗokantuwa da son jin labarin Shi tace "Ina kuwa zan sani Sister." Salmah tace "Haba shiyasa kike wani cewa kaza da kaza akan shi, Allah da kinsan wanene AA kangiwa da sai kin fini ruɗewa, hmm ke ba ki ga yadda kowa ya ruɗe dajin sunan shi kawai ba, kai Mr kan giwa ya haɗu ta ko ina ga kuɗi, gayen ga mulki, ƙasar nan baki ɗaya tasu ce,ga kyau uwa uba kyakkyawar zuciya,wlh ina son guy ɗinnan kamar na zauce ni ko da gaisawa dashi na samu na yi sau daya na more." Ƙur A'ishatu ta ƙurawa bakinta idanu tana kallo, duk wannan lissafin da take yi,ita ba shi take son ji ba, Kawai abin da take son ji shine wanene shi?, Ɗan waye? Cikakken sunan sa? Da kuma matsayin sa a Nigeria? Amma ta ina zata fara jeho mata waɗannan tambayoyin ba tare da ta kawo zargin wani abu a ranta ba.