Kenza eBookz

Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 4

Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 4

Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 4: Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 4. muryar salmah ta tsinta tana cewa "kinsan kuwa wanenen Mr AA kangiwa?" Da…

2,893 words

muryar salmah ta tsinta tana cewa "kinsan kuwa wanenen Mr AA kangiwa?" Da sauri ta dawo haiyacinta tare da girgiza mata kai, Salmah tace "hmmm zan gaya miki amma ba yau ba dan wlh yanzu barci barci nake ji, kuma gobe inada class din safe." Ta ƙarashe maganar tana sakin hamma tare da fara lumlumshe idanu alamar dai barcin takeji da gaske. Innalillahi! A'ishatu ji tayi kamar Salmah ta ƙwada mata ƙaton sanda a tsakar ka, ji tayi gabanta ya shiga wani irin ɗuka da sauri da sauri, zuciyar ta ce ya shiga bata shawarwari kala kala, ta riga tasan halin Salmah da kafiyar tsiya tunda ta furta ba yanzu ba,to kuwa baza ta faɗa yanzun ba, wata zuciyar tace ki fito fili ki gaya mata wacece ke da kuma abin daya fito dake daga kauyenku har kika faɗa hannun iyayen ta, wata ƙila zata ji ƙarfin taimaka miki, wata zuciyar ce ta ƙwabeta da cewa Ahir ɗinki yar Baffa wannan ganganci ne wai haihuwa da damuna kinfi kowa sanin wacece Salmah bakin ta baya haila, bacin haka kin shirya baiwa wani labarin rayuwarki ne? Idan ma kin shirya ba Salmah ba, domin bata da nutsuwar da zata iya daukar nauyin ruɗanin dake cikin labarinki a kanta, kiyi hakuri kibi komai a hankali, sannu ai bata hana zuwa, kuma in kere na yawo zabo na yawo wata rana za'a jone, indai baki da haƙƙin Babangida to kuwa Allah sai ya saka miki akan zalincin da ya miki. Bata san ta lula dogon tunani ba saida ta tsinci saukar numfashin Salmah a kunnenta alamar tama yi nisa cikin barcin ta, jiki a sanyaye ta miƙe ta faɗa toilet itama, wanka tayi wanda ya zame musu jiki a gidan wankan dare kafin barci sun dauke shi kamar wani farilla wannan kuma tirenin din Ammi ne kasancewar ta mace mai matukar tsabta. Alwala ta d'auro bayan tayi wankan ta fito ɗaure da tawel, kayan barci ta sanya itama ta gabatar da shafa'i da wutiri, ta daɗe tana addu'o'in samun nasara akan abin da tasa gaba kafin ta miƙe ta maida pray mat, ta kashe wutar d'akin sannan ta lallaɓa ta kwanta kusa da Salmah, tare da ja musu bargo. Ƙamas haka take jin idanunta a bushe babu alamar wani abu wai shi barci, tafi awa d'aya a kwance tana saka da warwara, ji tayi daren yayi mata nisa. Sabo fil haka taji tabon da Babangida ya bar mata a zuciya ya dawo, ƙudiri da muradin daukar fansarta yana daɗa ninkuwa, taso koda cikakken sunan wannan mutumin ta sani, duk da bata da tabbacin shine Babangida, amma ai yadda suke da tsananin kamanceceniya bazai rasa nasaba da shi ba, me yuwuwa ɗan uwansa ne na jini, jin barci baida niyar kawo mata ziyara yasa ta mi'ke zaune tare da lalubar wayar ta, Karfe goma sha biyu da ƴan mintoci na dare, data ta kunna take kuma ta shiga tunanin ta ina zata fara, direct Facebook ta shiga wurin searching, ta rubuta *kangiwa* take ya nuna mata sunaye masu ɗauke da kangiwa bila adadi, zuru tayi tana binsu da kallo, ta rasa ma me zatayi, zuciyar ta tace ta bata shawara da cewa ki bisu da ɗaɗɗaya ki duba sunan Babangida kangiwa, hakan ko tayi, har ta gama zageyen ta ta sake babu wani suna mai kama da Babangida a cikin jerin sunayen, bata haƙura ba haka taita research daga wancen manhajar zuwa wancan, amma babu alamar nasara, ta kwashe kusan awa biyu tana abu daya , dare ya tsala sosai tuni barci barawo ya shiga kawo mata farmaki, tana dojewa batasan sanda yayi nasara a kanta ba sai tsinkayar kiran assalatu tayi a kunnenta, lumshe idanun ta da sukai mata mugun nauyi tayi ta buɗe akan fuskar Salmah dake ɗan motsawa, so take ta mike amma jikinta babu kwari, gefen kanta taji ya fara sara mata, tana jin sanda Salmah ta mi'ke tana da karanta addu'ar tashi daga barci, makunnan wuta ta laluba ta kunna wuta take dakin ya gauraye da haske kamar da rana, toilet ta shiga tayi uzirorinta tare da dauro alwala ta ta fito, duk abinda take yi tana jin ta, kin tashi tayi sai da Salmah ta shiga dan bubbuga ƙafar ta tana kiran sunan ta sannan ta buɗe idonta daya mata wani irin nauyi dakyar , suna haɗa idanu ɗan zaro ido Salmah tayi tace "subhanallahi sister Eshart ya naga idanun ki kumbura sunyi ja kamar baki samu isasshen barci ba?." Cikin basarwa tace "ina ganin ciwo suke min." Daga haka ta samu ta yaki zuciyarta ta miƙe dakyer tana layi ta shige toilet, koda ta fito akan pray mata ta samu Salmah hannunta riƙe da dan ƙaramin Qur'ani tana bitar haddanta a zuciya, wani daddumar ta shimfiɗa itama tayi nafila tare da daukar nata Qur'anin itama da nufin yin bitar amma ina ji tayi idanunta na mata wani yaji², a haka har aka ta da sallah a masallacin gidan duk mikewa sukayi suka bi jam'i kasancewar tangararau suke jin kiran sallar kamar a cikin ɗakin nasu akeyi.

Suna idarwa ko addu'a bata tsaya anyi da itaba ta mike ta fada kan gado, ragwab! tun cikin sallar taji wani matsanancin ciwon kai ya ziyarceta a lokaci guda tare da wani irin barci mai nauyin gaske, Salmah kam baki ta sake tana binta da kallo, a cikin kwanaki biyu nan lamarin Eshart ya fara ɗaure mata kai yanzu zata ganta normal anjima ta ganta a birkice, bata ce mata komai ba saida ta gama addu'o'in ta, miƙewa tayi taje ta gabanta ta leka fuskarta ta, gani tayi tana sauke numfashi alamar barci yaci karfin ta, a fili tace "oh ni Salamatu meke shirin faruwa ne haka, anya kuwa sister Eshart tana ƙalau." Sake leka fuskarta tayi tare da kai hannu ta ta'ba goshin ta, Aiko ya dau zafi zau ga jijiyan kan sun fiffito da alamar kan na mata ciwo, cikin sauri ta fice a ɗakin don gayama Ammi abinda ke faruwa.

*KANGIWA ESTATE*

Babban estate ne wanda zan iya cewa babu irin shi a ciki da wajen birnin, gidaje ne a cikin shi tsantsara tsantsara masu fasali irin ɗaya sunfi guda ɗari, sai dai wani yafi wani ƙayatuwa da wasu ababen na more rayuwa, hakan ba zai rasa nasaba da yanayin aljihun mabanbantan mutanen da ke zazzaune a cikin rukunin gidajen ba. Dare ne da misalin Karfe 9 wata falleliyar mota mai mugun tsada kirar yayi baka ƙirin sai walwali take yi, tayi horn a bakin makeken get ɗin estate ɗin, da sauri biyu daga cikin sosojin dake gadin get din suka leƙo, ganin falleliyar mota ba bakon abu bane a garesu dan a cikin estate din a kwai manyan yan siyasa da yan ƙasuwa da ma ma'aikan gwamnati masu ji da naira a kwai kuma takawa masu karamin karfi. Doka ce sai sun duba koma wanene ya zo kafin a bude mishi get ya shiga, daya daga cikin su ne yayi knocking din motar, ba'a bude ba sai da aka kwashe kusan mintuna biyu, sannan a hankali glass din gefen direba ya fara zuwa kasa kusan a tare suka leka ciki motar, ganin wanda ke zaune cikin motar yasa jiki na bari suka shiga rige rigen buɗe get din,sai da suka gama buɗewa sarai, sannan motar ta fara tafiya zuwa ciki, duk kamewa sojojin nan su ka yi alamar girmama ga mamallakin wannan motar, tsayawa motar ta yi a daidai wurin su, a hankali ya miƙo hannunshi ya yafito babban cikin su, jiki na rawa ya ƙarasa tare da sara mai, sannan ya duƙa daidai windon. Shi kaɗai ne cikin motar sanye cikin ƙananan kaya kanshi sanye da P cap fuskar shi sanye da wani irin facemask wanda ban taɓa ganin irin shi ba,mai faɗi ne wanda ya rufe fuskarshi sosai har ta ƙasar haɓarsa, idanunsa sanye da wani siririn glass baƙi wanda yayi masifar yi mishi kyau, a hankali cike da tsabar madaran miskilanci, cikin bada order yace "kada kowa ya san na shigo estate." Da sauri ya sake ƙamewa tare da cewa "yes sir." Da wani irin masifafen gudu ya ja motar ya harba kan shimfiɗaɗɗen kwaltar da ta mika zir har karshen estate ɗin. [5/14, 6:00 AM] Oum khadeejarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

By

AyshaNalado

Page 5

Dai-dai wani tamfatsetsen get hause no 32, ya tsaya tare da danna horn, da sauri mai gadi ya wangale get, da alamar tsaye yake yana jiran isowar shi, koda yayi parking sai da ya kwashe kusan 2 minute kafin ya fito. Compound din gidan yalwace yake da hasken fitulun solar ta ko ina tar-tar kamar rana, hakan yasa ya kara jan P cap din shi gaba da kyau ya kare fuskar shi, kafin cikin takunsa mai cike da nutsuwa da kasaita ya nufi kofar shiga kayataccen ginin upstair ɗin da ke nan kalli ɗaya tal a cikin gidan. Danna doorbell yayi sau ɗaya yaja ya tsaya, kusan minti biyu ba'a buɗe ba, dan guntun tsaki yaja yana mai kallon agogon dake daure a tsintsiyar hannun shi, sake danna wa yayi a karo na biyu, wannan karon yana danna wa ana buɗe wa, dattijuwar macece wacce a kalla zata kai shekaru 40+ da haihuwa ba, ganin wanda ke tsaye bakin kofar yasa ta zaro manyan idanunta a tsorace, ba ta taba zaton shi ba ne, duk tunanin ta Suraj ne, da yace mata yana zuwa shiyasa ma ta buɗe kofar gabanta gaɗi, da sauri kamar wata mara gaskiya ta kamo hannayen shi ta janyo shi ciki, ta maida kofar ta rufe tare da murza key, koda ta juyo kan sofa ta ganshi yayi wata irin zama yayi balance ya cire P cap ɗin kanshi ya ajiye a hannu kujera, ƙarasawa ta yi gaban shi ba tare da ta ce ma shi komai ba ta saka hannu ta cire facemask ɗin dake fuskar shi tare da zare siririn glass din daya toshe kwayoyin idanun shi da shi.

Ajiye mai tayi kusa da P cap ɗin, ta juya zata bar falon still bata ce mai kala ba, da sauri ya riƙo hannun ta, tsayawa ta yi, ba ta tafin ba shi ma bai sake hannun ba, tasan me riƙo hannun ta da yayi yake nufi, haka zalika shima yasan me shirun ta yake nufi, ba tare da ta juyo ba tace, "Nasha gaya maka Bunayya, bana son kana fita kai kaɗai riski ne ga rayuwarka, balle ma a irin wannan lokaci na duhun dare. So kake su kashe mana kai? Idan kai baka son rayuwar ka mu muna son ka." Shiru yayi ba tare da iya cewa komai ba, dama ya shiryawa hakan don yasan dole za ta kasance.

Ganin bai da niyyar yin magana yasa ta fisge hannuta daga riƙon da yayi mata ta ci gaba da tafiyar ta, bata san tasowar shi ba sai dai Kawai ganin shi tayi a gabanta, dakatawa tayi ta daga kai kasancewar yafi ta tsawo sosai ta zuba mai idanu tana binshi da wani irin kallo mai cike da zallar madarar so dà kauna, hannu ya kai ya riƙe kunnuwanshi, tare da yin narai narai da idanu, a hankali cikin muryar shagwaba kamar ba wannan zankaɗeɗen murdadden saurayin mai cike da miskilanci ba ya ce " I am sorry mother ba zan sake ba in sha Allah " hararar shi tayi ta ce "sau nawa kake cewa haka kuma da anjima ka sake." Ya ce "kiyi hakuri Mother tsananin kewa da bagen son ganinki ne suka addabi ruhina, zuciyata ta dinga azalzalata a kan na zo na ga sanyin idaniyata." Hannunta ta daura a kumatunshi dake dauke da gewayyayyen saje mai taushi sassayayye da ya kara fito da kyawu da kamalar fuskar tasa ta shafa, tare da cewa Na hakura Bunayya, kasan ba zan iya dogon fishi da kai ba shi yasa ka ke yin abin da na haneka a duk sanda ka ga dama, saboda kasan lago da hanyoyin tankwara zuciyata, amma zan yi maganin ka soon." Tsadadden murmushin shi ya saki tare dà kamo hannunta dake kan kumatunshi, ya kai saitin bakin shi ya sumbata, tare da cewa "Thank you, mother like no other." Murmushi ta saki tana zame hannunta daga nashi, yace "Mother yunwa na ke ji tun safe ban ci komai ba." Zaro ido ta yi tace “Tun safe fa kace?" Ya langwaɓe mata kai yana taɓe baki kamar zai yi kuka, tace "Innalillahi Bunayya wai me yasa kake min wasa da rayuwarka ne haka for god sake." Bata jira jin amsar shi ba taja hannun shi zuwa dinning area, ta ja mishi kujera ya zauna kafin kace kwabo ta cika mishi gaban shi da abinci kusan kala uku, ta tsiyaya mai ruwa da zobo a cup, ta tura mai ta miƙe ta buɗe fridge ɗin dake angle ɗin wajen ta fito da dammammiyar fura mai sanyi a cikin wani dan bowl ta tura mai gaban shi, kasancewar tasan yana masifar son fura musamman ma wanna da take dama wa, wanda takanas take sanya makociyarta ta yi mata shi na musamman, so da yawa saboda shi take yawan ajiye damammiyar fura, duk wannan abubuwan da take yi tana yi tana mai faɗa akan wasa da rayuwar shi da yake yi, cikin faɗa faɗa amma a hankali kasancewar tasan shi mutum ne da baya son hayaniya take cewa “Yanzu menene amfanin ace mutum ya wuni bai ci komai ba, gaskiya kar ka sake maimaita irin wannan kuskuren, kai kenan baka da cikakken lokacin kanka kullum cikin aiki, kuma ma wannan abin harda laifin, Aunty Rukkayya itace bata kula da kai da cikin ka yadda ya kamata zan kai karar ta wurin Yaya, sannan mai babban laifin Kaine Bunayya na ce ka fitar da mata kayi aure kaƙi yanzu inda kana da mata ai ba za ta barka haka a gantale ba, cikin dubban yan matan da ke kara kaini kaunarka, ka fidda ɗaya dan Allah koda cikin Ahlin kangiwa ne ka zaɓa muna da ƴan mata birjit a zuri'ar mu. Ko huɗu kake so kana da halin, auren su a rana ɗaya, kana da inda zaka ajiye su kuma ka kula da bukatun ko wacce ba tare da ka takura ba, mahaifinka bashi da buri kamar yaga ka fitar da matar aure, kana tuananin idan haƙurin shi ya ƙare bazai aikata abin da ba zai maka daɗi ba kuwa? kasan fa mutum mai haƙuri kamar Yaya bai iya tunzura ba,muna saka ran nan da yan wasu watanni za ka taka babban matsayi a kasar nan, shin a haka kake so ka zama jagoran biliyoyin mutane, shi fa aure yana cika mutunci da kimar mutum ne, kai tsaye ma a addinance yana cike rabin addinin mutum, matashi mai shekaru kamar naka kamata yayi ace yana da mata har da albarkar ƴaƴa, ka duba abokinka Usman dan gidan Yaya dattijo tare a ka yi goyon ku, kama girme mishi a haihuwa amma yanzu ƴaƴan shi biyu matar shi nada cikin na uku kai kana nan har yanzu baka kama dahir ba."

Duk wannan bambamin faɗan da mother ke yi yana jin ta bai tanka ba sai ma buɗe ciki da yayi yana ta kai lomar abinci, sai da ta yi mai isar ta, sannan kuma ta sausauta murya ta koma rarrashi, cikin raunin muryar ta ci gaba da cewa" shin me yasa ba za ka fitar da mace ka aura ba Bunayya? Idan ma ba za ka iya zaɓe ba ka bani dama ka faɗi irin wacce kake so wlh zan nemo maka ita a duk inda take. Idan kuma kace ka bani dama wlh na riga na tanadar maka mata nitsatsiya yar mutunci uwa uba kuma kyakkyawa ta karshe ga ilmi wacce zaka iya shiga ko ina da ita a faɗin duniya ba za ka ji kunya ba, ka yi tunani a kan maganata son dan Allah ka amince min kodan Yaya da damuwar da yake ci akan lamarin ka fitar da mace ka yi aure."

Kadan yaci abincin ya dauki damammiyar furan data ajiye mai ya shiga shiga sha yana ji kunnen shi kamar zai tsinke dan santi sai da ya shanye tass, sannan ya ajiye spoon ɗin yana lashe baki, kallon shi mother ta yi tace "Baka ce komai akan magana ta ba Bunayya." Shiru yayi ya zuba mata idanu yana tunanin amsar da zai bata, can kuma ya buɗe baki dakyar yace "kiyi hakuri mother a kwai lokaci." “Wani irin lokacin ne wannan da yaƙi zuwa har yau, kullum idan magana makamancin wannan ya haɗa ni da kai amsar da kake bani kenan, kiyi hakuri mother a kwai lokaci, to yau dai dan Allah ina bukatar jin wata amsar sabanin wannan, na gaji da jin wannan." Ta karshe maganar a ɗan kausashe da alamar abin yana cin ranta matuƙa, ta kuma tsare shi da idanu alamar tana jiran ji ta bakin shi, ƙasa ya yi da kai domin baya jure irin wannan kallon daga gareta. Shiru ne ya ratsa wajen na mintuna har ta cire rai da jin amsa daga gare shi, ta tsinci muryar shi cikin sanyi yana cewa “ Ki yi hakuri Mother, zan yi aure in sha Allah, ku ci gaba da yi mini addu'a, i need to rest, zan dan kwanta." Yana gama faɗin haka ya miƙe idanunshi sun rine, da alama yayi babban fami a zuciyar shi, cikin sassarfa ya haura upstairs, ɗaya daga cikin ɗakunan dake saman ya buɗe ya shiga tare da maida ƙofar garam.

Readers Also Read