Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 5
Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 5: Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 5. Da kallo Mother ta rakashi harya ƙulewa ganinta zazzafan numfashi ta…
3,374 words
Da kallo Mother ta rakashi harya ƙulewa ganinta zazzafan numfashi ta sauke, a bayyane tace "A kwai ƙura, an ya ba aljanu ne suka auri Bunayya ba kuwa? Tabbas sune, idan ba haka ba ta yaya yaro daga an yi maganar aure sai ya birkice nan take, idan ba ita din ba ma wa ya isa ya yi mai wannan maganar ya sha lafiya, gaskiya da sake ba su ga ta zama ba kam, ya zama dole su tashi tsaye a kan shi, gobe dole ta kaima Yaya ziyara akan maganar nan." Ta dau tsawon lokaci tana saƙawa da kwancewa a zaune a dining din ba tare da ta ankaraba. Ƙarar doorbell da taji ne ya dawo da ita hankalin ta, ko ba'a faɗa ba tasan Suraj ne, tashi ta yi jiki a sanyaye ta bude mishi ƙofar, ya shigo, kallo agogo tayi tare da maida idanunta kanshi ta tsatstsare shi da su, ko bai tambaya ba yasan laifin shi, da sauri ya rike kunnuwanshi yace "Sorry Mother." Tace "Ina kaje." Cikin in ina yace "Gidan su Salman." Kunnensa ta kama ta Murda da karfi, “Ochhh!” Ya saki kara ya rike kunnen yana ja da baya, “ Karya ka ke yi, yanzu na gama waya da Ammin Salman ta ce min ba ku shigo gidan ba har shi Salman ɗin yawo ko?.” Ya girgiza kai da sauri, ta yi kwata tare da mika masa hannu, musu ya saka mata makullin motar dake riƙe a hannun shi, tace "Punishment ɗinka shine ka shiga kitchen da kanka ka girka abin da zaka ci don na yi kyauta da abincin ka." Cikin ƙasa da murya yace "Father ya dawo ne naga kamar motar shi a parking lot, dan Allah ki rufa min asiri kice ke kika aikeni?" harara ta watsa mai tace "Bai dawo ba Bunayya, ne ya zo." Wani ɗan kayataccen rawa ya shiga takawa, cike da yarinta kasancewarsa gwanin iya juyi, matsayinsa na matashin mai jini a jika wanda yake kan ganiyar tashensa din zai gaza sheda ashirin zuwa da huɗu ba, ya tsagaita ya sake kallonta yace, “Mother yanzu haka kina nufin Yaya B na cikin gidan nan?" "Eh.” ta amsa masa a takaice, "Yeeeee!" ya faɗa tare da kwasa da gudu kamar wani dan 5 years ya nufi hanyar staircase, da sauri mother ta dakatar dashi , ta hanyar cewa "A kull! Ka bari da safe baya cikin good mood, kar kaje ka dame shi da surutu." Dawowa yayi yana taɓe fuska, ya nufi hanyar kitchen, har zai shige tace "Suraj ya juyo." "bani wayoyin ka." Ta faɗa tana mika mishi hannu, kamar ya kurma ihu amma ba yadda ya iya ganin yadda ta tsare gida ba damar wargi, dole yana ji yana gani ya ciro su a aljihu ya miƙa mata, ta amsa tace "idan za ka wuce school gobe ka tuna ka amsa" ya amsa mata da "To Mother." Kamar zai yi kuka, bai ji daɗin tunawa da tayi da batun karbar waya ba wlh, yaso kafin ya kwanta barci ko da bai yi komai da wayar ba, ya ji muryar Salmah, ka da kuwa masifa za ta mai kamar yadda ta saba, amma ba komai gobe zasu haɗu a school ai. Ganin yayi shiru ya tsura mata idanu yasa tace "Da magana ne?" Da sauri ya girgiza mata kai, tace "oya goo." Ta faɗa tana nuna hanyar kitchen, jiki a sanyaye ya juya ya tafi, har ya shige ta daga murya tace "idan ka gama ka karkashe komai ka kulle ƙofa kafin ka kwanta." Daga ciki ya amsa da "OK Mother gud night." Bata tanka shi ba ta wuce nata dakin itama don ta kwanta ta huta...
Anya kuna biye kuwa? Bakwa comment ko labarin bai yi muku bane mu dakata? [5/14, 6:00 AM] Oum khadeejarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀
By
AyshaNalado
Page 6
*A'ISHATU*
Wani irin barci ta yi mara daɗi mai wahala da azabtarwa har na tsayin awanni uku kafin ta farka a firgice cikin mayuyacin yanayi, tana ƙanƙame jikinta tare da dunkulewa waje guda, jikinta ya dauki rawa ga zufa da ke yanko mata ta ko ina, duk da fankar dakin a bakin aiki take, wani irin tsoro da tashin hankali suka lulluɓeta, ta rintse idanuwanta da karfi tana karanta duk wata addu'ar kariyar da ta zo bakinta, a hankali komai ya soma lafawa hankalinta ya fara dawowa jikinta, ta kai tsayin mintuna ashirin kafin ta fahimci mafarki ta yi, wannan baƙin mafarkin da ya kasa barin kyanyarta ta huta, da tana da yadda za ta yi da ta yi domin ta daina tuna wannan yanayin a rayuwarta, amma ta gaza, kuka ta fashe da shi mai karfi tare da daura kanta a pillow, tana kara jin wutar kiyayyar Babangida a zuciyarta, lokaci gudu kudirinta na daukar fansa na kara hauhawa, lokaci daya zuciyarta ta dake, hawayen da ke kwaranya daga idanunta suka ƙafe, take ta nemi ciwon kan da ta kwanta ta farka da shi ta rasa, wayarta ta shiga laluba domin ta duba time bata ji shi ba, hakan yasa ta shiga yunkurin mikewa. Daidai lokacin Ammi ta turo ƙofar ɗakin ta shigo bakin ta ɗauke da sallama, ganin ta a farke yasa ta ƙarasa da sauri ta taimaka mata ta mike zaune, sannu ta shiga jero mata tana dan tattaba kanta zuwa wuya don jin yanayin temperature ta.
Zafin jikin da sauƙi ba kamar ɗazu ba, hamdala ta yi tare da cewa “Sannu A'ishatu kin farka ya jikin?" Gyada kai tayi tare da buɗe bakin ta da take jin ya mata nauyi tace "Da sauki Ammi." "Yanzu meke miki ciwo?" Ɗan ya mutsa fuska tayi tace "ba komai Ammi sai dai bakina ne nake jin ba daɗi, sai kuma jiki na da babu kwari." Ammi tace "kan ya dena ciwo yanzu?" Ta gyada kai "alhmdllh suma sauran a hankali zasu sake ki, yanzu ki tashi na taimaka miki kiyi wanka kici abinci kisha magani, a Kwai alluran da zan miki insha Allah zaki ji daɗin jikin." "Toh Ammi." Toilet Ammi ta shiga ta haɗa mata ruwan wanka, da duk abin da zata bukata, ta zo ta taimaka mata ta miƙe tsaye ta rage kayan jikinta ta daura tawul ta shiga toilet ɗin, koda ta shiga guri ta nema ta zauna mafarkin da ta yi na sake yawo a cikin kanta tana kokarin yakice shi amma ina hoton yanayin ya dade da zama daram a cikin ƙwaƙwalwa da zuciyarta, ta dan daɗe a zaunen kafin jiki ba kwari ta mike ta fara wankan, tun kafin ta gama ta ji wani karfi na kara shigar ta, a haka ta kammala wankan ta fito, tana fitowa Ammi na shigowa ɗakin, hannun ta dauke da cup ɗin tea da kuma plate a rufe, direct gaban mirror ta nufa tana tsane jikinta da tawel, bayan ta gama dan mai ta shafa ta fesa turare a lungunan jikinta, ta saka kwalli a idanunta da su ka yi fari fat, kafin ma ta gama Ammi ta ciro mata kayan da zata saka, dogon rigar materiya mara nauyi ɗinkin buba yadda baza ta takura ba, bayan ta gama shiryawa, umarni Ammi ta bata da taci abinci, tea ta fara shanyewa kasancewar dama babu yawa sannan ta buɗe plate ɗin, indomie ne da soyayyan Kwai a sama da zafinshi sai tiriri yake yi, tana son indomie musamman idan da zafi ,hakan yasa ta shiga cin abincin ka'in da na'in, ganin tana ci yasa Ammi miƙewa ta fice daga ɗakin, kamar minti goma ta dawo hannun ta dauke da magunguna, da ruwan allura da siringi, sai da ta koshi sannan ta ture plate gefe ta rufe sauran.
Bata magunguna Ammi ta yi, ta bata tare da mika mata ruwa mara sanyi a cup, bata kaunar shan magani a rayuwarta da ka bata magani gara ka mata allura, hakan yasa ta riƙe maganin a hannu tana yamutsa fuska, haɗe rai Ammi tayi kasancewar tariga tasan hali, cikin bada umarni tace "oya sha ki bani Kofi." Ganin yadda Ammi ta tsare gida yasa ta shiga hadiya 1 by 1 tana yamutsa fuska harda su kakarin amai, duk Ammi bata kula ta ba sai da ta tabbatar ta shanye , sannan tayi murmushi ta shafa kumatun ta, tace "yawwa ko kefa gud girllll." Ta faɗa cikin zolaya tana jan Kalmar girlllll dole ta saki murmushi itama, Ammi tace "to tashi muyi allura." Ba musu ta miƙe, don bata da matsala da wannan fannin tana da jarumta da juriya sosai kamar ba mace ba, yadda ta tsaya ƙem aka mata alluran babu wani gargada ko dan irin wash ɗinnan, yaba Ammi sha'awa cikin jin daɗi tace "da ace ke namiji ne da soja zaki zama ba yar jarida ba." Dariya tayi Kawai ba tare da tace komai ba, zama Ammi tayi suka shiga dan taɓa hira, Ammi tace "baki tambayeni Salamatu ba" Murmushi tayi tace "Ayya my Salmah nasan ana cen school ana fama da lecture." Ammi tace "yar nema dakyar na samu ta tafi school ɗin fa yau harda hawayenta shaɓe shaɓe wai baza taje ba saboda baki da lafiya,gashi kuma wai suna da test da safen, tun ina rarrashi har raina ya fara baci, kinsan ta da taurin kai kamar kafiran farko, sai da Abie ku ya shirya zai tafi wurin meeting, dan shima suna da meeting da safen a kangiwa palace, shine fa ya rarrasheta kenan ya lallaɓa ta ya kama hannun ta suka fita koya suka ƙare oho." Tun da Ammi ta ambaci kangiwa palace take ta maimaita sunan gurin a ranta, hoton fuskar mutumin nan mai kama da Babangida mamallakin kafuwa greenland ne ya shiga dawo mata, wannan wurin da su Abie suka je meeting kenan yana da alaka da mutumin, dabara ne ya fado mata da sauri tace "Ammi ina ne kangiwa palace kuma? Bayan green land a kwai palace kuma." Murmushi Ammi tayi tace "palace ba kamar green land bane, shima babban gurine mallakin GENERAL IDIRIS AHMAD KANGIWA, guri ne da yayi shi kawai don tattaunawa da mutune." Gyada kai tayi alamar ta fahimta tana sake maimaita sunan general Idris Ahmad kangiwa a zuciyata, mikewa Ammi tayi tana kallon agogo tace "bari na shiga kitchen na haɗa lunch, kinga har 1 ta gota." Tare suka shiga kitchen ɗin da Ammi duk da Ammi ta hana ta saboda jikinta amma ta nace dole ta barta ta ɗan kama mata ƙananan aiyuwa tana yi suna hira jefi jefi tana jeho mata tambaya akan kangiwa cikin tsananin dabara da taka tsantsan, kafin su gama girkin ta ɗan samu wasu information akan general Idris Ahmad kangiwa daga bakin Ammi, a haka suka kammala komai suka shirya a dining zuwa lokacin tuni ta ware dan sosai taji ƙarfin jikinta.
Bayan sun kammala komai sun gyara kitchen ɗin sallama tama Ammi ta nufi dakin su ta watsa ruwa tare da gabatar da sallar azahar tana idarwa kuma ta dawo falo ta zauna tana kallo bata jima da zama ba, Ammi ta fito itama, ta yi wanka ta sake wasu kayan ta tsantsara kwalliya na kece raini, da kallo A'ishatu ta bita aranta tana mai yaba kyan da tayi, Ammi na birgeta sosai macece yar gayu data san sirrin kwalliya uwa uba ga tsabta da kuma iya tattali da tarairayar miji, murmushi suka sakarwa juna, ƙasa daurewa tayi tace "Ammina kinyi kyau sosai." Tace "Allah ko A'ishatu?" Ta kyalkyale da dariya,zama itama Ammi tayi suna kallon tare, zaman su babu daɗewa sukaji alamar dirar mota a compound ɗin gidan, murmushi Ammi tayi a ranta tana mai farin cikin isowar mijin ta lafiya don yanzu suka yi waya yace gashi nan da sunyi sallah zai dawo gida ya huta kafin la'asar su ƙara fita, ƙarar doorbell ya maida hankalin su kan kofar falon,da sauri Aishatu ta miƙe da nufin zuwa ta buɗe, dakatar da ita Ammi tayi, ta mike da kanta dan budewa mijin nata kofa, to her surprise tana buɗewa taci karo da Salmah fuska a haɗe, bata taɓa kawo cewa su bane suka dawo dan sunyi da ita sai 4, ganin Ammi yasa ta kwaɓe fuska sai kuma ga hawaye shar, rasa bakin magana Ammi tayi sai Kawai ta juya ta shige ciki, Salmah ta biyo bayan ta, ganin Aysha a falon yasa ta nufe ta da sauri, itama ta tare ta suka rungume juna, bubbuga bayanta Aisha ta shiga yi tana tambayar ta mekefaruwa, bata kai ga bata amsa ba Salman yayi sallama Suraj na biye a bayan shi, ganin su tare yasa ta ɗiga musu ayar tambaya, ko lura da Ammi bai yi ba ya nufo su yana dariya tare da tambayar Aysha "wai kuka take yi." Harara ta watsa mai ya ƙara kwashewa da dariya yace "yarinyar gobe ma ki kuma." Muryar Suraj daya tsinta daga bayan shi yana cewa "Ammi ina wuni."yasa ya juyo da sauri sai lokacin ya lura da Ammi, da sauri ya karasa ya yi mata side hug yana cewa "oyoyo Ammina." Bata kula shi ba ta cigaba da gaisuwa da Suraj tana tambayar shi Mother da karatu, ya amsa da "duk lafiya kalau." Ta gefen ido ta harare shi, ba shiri ya sake ta, tace "me ya hada ka da yar uwarka?." Tashi yayi daga kusa da ita yana dariya yace "wlh Ammi imarina tayi na rama," Kafin Ammi tace wani abu Salmah ta dago da sauri tace "wlh Ammi karya yake yi, shi ya fara,cemin yake yi ina kama da hajiya Saude, nace bana so yaƙi denawa shine na kwabe mishi baki shine ya mare ni." Taɓe baki Ammi tayi tace "ku dai kuka sani kun fi kusa, yanzu dana shiga fadar ku anjima zaku bada min kasa a ido." Kuje ku kimtsa azo a ci abinci, kallon Salmah , yayi yana mata gwalo, cikin shehsheka tace "wlh bari Abiena ya dawo sai faɗa mai kuma kai da Yaya Anas." Tana gama faɗin haka ta miƙe cikin fushi tayi ɗaki, Suraj ya rakata da ido, fuskar shi dagule, hakan baya rasa nasaba da yanayin da Salmah take ciki don ji yake a ranshi, ya fita jin zafin marin da Salman yayi mata. , sai da ya gama dariyar shi yama Aysha ya jiki sannan suka haura sama shida Suraj dake ta bin Aysha da kallon Sani. Wanda kullum ya ganta irin kallon da yake binta da shi kenan.
Suna barin falon Abie na shigowa, bayan Aysha data rage a falon ta yi mai sannu da zuwa, ɗakin shi dake nan part din Ammi a sama ya nufa, Ammi ta rufa mai baya, ta kuma bar ma A'ishatu sallahun idan su Salman sun fito su haɗu da su yi lunch ɗinsu kawai ita zata yi tare da Abie tunda yana gida, dama indai yana gari breakfast da dinner tare suke yi, lunch dama bai cika yi a gida ba sai jefi jefi, kuma in zai yi ma a ɗakin shi suke yi su biyu, ganin ba kowa a falon yasa ta mike ta bi bayan Salmah, koda ta shiga dakin tana toilet, kwanciya tayi tana ta sake saken ta wanda bata rabo dashi cikin kwanakin nan, fitowar Salmah ya dawo da ita hayyacinta, sai lokacin suka samu daman gaisuwa Salmah ta mata ya jiki, ta amsa mata da taji garau.
Salmah na gama kimtsawa suka fito don cin abinci,suna zama su salman suka fito suma, salmah na ganin su ta bata rai ta shiga yan harare harare tana dan jan tsuki, kujera su ka ja suka zauzauna, Suraj ya zauna kujeran dake facing nata inda zai samu ya dinga kallon ta dakyau, A'ishatu ce tayi serving din su duka, an fara cin abincin lami lafiya, Salman ne kadai ke magana shima jifa jifa, Salmah kam Suraj ya takura mata da kallo duk ɗagowar da zata yi sai sun haɗa ido, ta ko watsa mai uwar harara shi kuma yayi murmushi ya dauke kai, sam ya ki mayar da hankali ya ci abincin sai kallonta yake yi kamar ya samu Tv, haushin shi take ji kamar ta rufe shi da duka, da tana da dama da ta hana shi shigowa gidansu, sai dai ta san ba zai yiwu ba, cin abincin ma don dai ta san Ammi za ta yi fada ne da tuni ta tashi ta bar musu wajen, ba iya abinda Salman ya mata ɗazu bane kadai ya saka ta kuka harda abin da Suraj ɗin ya mata a school da suka fito lecture dazu ya kara tunzurata har ta biye wa Salman suka raba hali a hanya, tana cikin kawayenta ya zo da tarin abokanshi yan bana bakwai kamar yadda take yi musu laƙabi yana nunata, da alamar labarinta ya kai musu su ka nemi son ganinta, tana Ji wani cikinsu na cewa, “Ba laifi she is fine.” wani kuma ya ce, “Ni kuma bata min ba da gani za ta yi hayaniya, amma shan koko kwanciyar rai." Tsabar bakin ciki Salmah kamar ta narka musu ashar, kawayenta sai dariya suke mata, ita Allah ta tuba ko maza sun kare mai zata yi da Suraj karamin yaro abokin Salman ƙanin ta, amma dan rashin kunya yake cewa yana sonta,a rayuwarta bata da sha'awar auren matashi wanda bai haura 30 ba wannan burinta ne ko Ammi ta sani, balle kuma Suraj da take ganin ta girme shi idan ma bata girme shi ba to za su zo tsara, Salmah a kwai son girma ko gyambo ya shafa mata lafiya.
Har suka kusa gama cin abinci fuskarta a daure yake, don ta kudiri aniyar daga shi har Salman din ta daina sake musu, tunda taga alamar ganin hokoranta da suke yi arha yasa har suka rainata haka, muryar Suraj din ne ya katse mata tunani ji tayi yana cewa "Sister Aysha wallahi ina son Salmah!" Ya yi maganar cikin wani sauti mai jan hankali wanda ya janyo daga Aysha har Salman suka zuba mishi ido yayinda Salmah ta maka mai wata uwar harara tana kankance ido cike da masifa tace "Wallahi wallahi Suraj, idan baka fita a ido na ba sai na ci maka mutunci, idan ni sa'ar kace zaka gayamin." Ta kare da jan wani shegen tsaki. Langwabar da kai ya yi abin tausayi ya zuba mata idanunshi da ko makaho ya laluba yasan cike suke da shaukinta na gaske, cikin marainiyar murya ya yace "kin ji ko Eshart wai meye laifi na ne? shin haramun ne soyayya tsakanin babba da yaro, wlh Allah idan ta bani dama zan mata abin da ba za ta samu a wurin babba ba." Kallon shi A'ishatu ke yi cikin tausayawa, lallai iska na wahal da me kayan kara, cikin son ta kwantar mai da hankali tace "kayi hakuri Suraj idan Salmah matarka ce zata so ka kaci gaba da addu'a." Ita kadai ta fahimci halin da yake ciki saboda ita kadai ce a cikin su ta taba fadawa cikin irin wannan yanayin da ƙananun shekarunta. Salmah jin abin da Aysha ke cewa yasa ta miƙe a fusace ta kalle shi tace "ka biyewa mata ta ringa daura ka a keken ɓera dai, kar ka fita idona na rufe, kuma wlh ka sake min irin abin da kamin yau a school sai na yaga maka rigar rashi mutunci tana gama faɗin haka ta bar gurin a fusace." Duk da ido suka rakata, Salman yace "friend na sha gaya maka ba sau ɗaya ba ka fita hanyar salmah ba hankali ne da ita na kaƙi ji." Kamar zaiyi kuka yace "Aboki wallahi ba zan iya ba, ba daga ni bane daga zuciyata ce, ina son Salmah Allah ne shaida soyayyar da ban san adadinta, kuma babu gudu babu ja da baya zan jajurce har na sameta." Salman ya ɗage kafaɗa yace "OK to jiki magayi, ni dai nawa eyes." Sam Salman bai taba daukar lamarin da mahimmanci, Ajiyar zuciya Suraj ya sauke yanabin hanyar da Salmah ta bi da kallo, cikin yanayin damuwa, ya furta, “Salman wasu mutanen ba kai ke zabarsu ba, zuciyarka ce, kuma ko sun ƙi ka kai baka da ikon kin su.” tamkar saukar aradu kalaman suka daki zuciyar Aysha, “ Wasu mutanen ba kai ke zabarsu ba....” kalmar ya maimaita kan shi a zuciyarta lumshe idanun ta yi tana mai sauraren amon wani sauti da ya yi shige da na Suraj a can baya......
Oum Ummeetarh ce😍 [5/14, 6:00 AM] Oum khadeejarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀
By
AyshaNalado