Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 6
Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 6: Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 6. Page 7
3,360 words
Page 7
Tsit wajen ya ɗauki shiru tamkar mutuwa ta gifta, daga Aysha har Suraj babu wanda ya sake daga cokali da nufin kai abinci bakinsa, sabanin Salman da ya dukar da kai ya ci gaba da cin abincinsa yana danna waya hankalinsa kwance, don ko kadan kalaman Suraj ba su wani ratsa shi ba, shi dai tunda ya fita haƙƙin sa a matsayin shi na abokin sa ya ba sa shawarar da ta dace, to yasan ya fita har a gaban Allah, sai dai ya yi nak sanna ya mike yana kallon agogon dake daure a hannushi, ya kalli Suraj ya ce Romeo Baban Soyayya mu je ko it's almost time to pray. Bayan fitarsu jiki a sanyaye Aysha ta mike zuciyarta ya yi mata nauyi yayinda kalaman Suraj na karshe ke ta amsa kuwwa a kunnuwanta, suna neman su rijita mata ƙwaƙwalwa su jefa ta a yanayin da zai hanata ta rintswa a daren yau, kuma bata fatan hakan, rintse idanu ta yi da karfi, ta fesar da numfashi, kafin ta sa dukkan karfin da zuciyarta ke da shi ta yi facali da su, sannan ta nufi dakinsu don gabatar da nata sallar la'asar ɗin,, a kwance ta samu Salmah rigingine riƙe da waya a hannunta, tana karatun littafin Gaba da gabanta na Ayshercool, saboda yadda labarin ya dau hankalinta ko ɗagowa ta kalli Eshart ta kasa, idon ta akan waya ta amsa mata sallama, A'ishatu ta ce "Master a nan ana ta Sana'a." Still bata ɗago ba ta ce "Umm." Taɓe baki ta yi ta rasa daɗin me Salmah ke ji a karatun novels musamman na Hausa, kullum sai ta yi shi kamar farilla, ta ce "To sai ki tashi ki haka ki yi sallah gashi nan ana ta kira." Kicin ƙosawa da katse mata karatu da take yi ta ce "tohhhh." Riƙe haɓa ta yi ta ce "Allah ga kayanka, Allah ka shirya." Wannan karon kam bata samu amsa ba, ganin haka yasa ta shige toilet don yin alwala, tana fitowa , ta tarad da Salmah ta kife wayar tana miƙa sai murmushi take saki ita ɗaya, hararar ta A'ishatu tayi tace "Ai na ɗauka ba za kiyi sallar ba ne." Ta ce "Sister ba za ki gane bane novel ɗin ya haɗu ne over wlh, duk fushin da na kwaso da takwaicin wancen yaron ina hawa online na ga ta yi posting, baki ji daɗin dana ji ba, ji na yi kamar an wanke min zuciya da ruwan sanyi." A'ishatu da ta gama shimfiɗa pray mat ta saka hijab ta ce " To madallah ina zuwa ki ga." Tana gama faɗin haka ta kabbara sallarta, ganin haka yasa ita ma ta mike ta yi toilet don dauro nata alwalan, bayan sun idar kasancewar ranar alhamis ne babu islamiyya yasa suka zauna a ɗaki suna taɓa ƴar hira,Salmah na bata labarin abin da Suraj ya mata yau a school, sai dariya A'ishatu ke mata, ita ko sai masifa take tana tsigale shi kwace yana gurin, Cikin da dabara A'ishatu ta sa ko maganar kangiwa Cikin hirar tasu, aiko nan Salmah ta shiga yabon shi tana kuzuzuta shi, tare da faɗin irin nagartar shi, gyada kai ta yi tace "Lallai mutumin nan karshe ne har na matsu naji cikakken sunan shi." Salmah tace "Cikakken sunan shi, AHMAD IDRIS AHMAD KANGIWA Dam! Zuciyarta ta buga da karfi kamar fashewar nakiya, Ahmad.... Idris.... Ahmad ta maimaita sunan a ranta tare da lumshe ido ta bude a hankali, sai kuma ta saki murmushin yaƙe ta ce "Umm.. ka ji special name sunan manya."
Salmah ta ci gaba "Mahaifin shi, shi ne General Idris Ahmad kangiwa. Tsohon soja ne mai matakin general, mutum ne nagartacce wanda yake da tsananin tausayi da taimakon talakawa da son tallafawa rayuwar su, hakan yasa ya kasance mai farin jina a cikin al'umma, bayan yayi ritaya Kawai sai na kusa da shi suka bashi shawarar ya faɗa harkar siyasa ta nan ne kaɗai zai samu ya taimaki talakawa wanda wannan ne babban muraɗin shi, Allah ya saka mishi kishi da tausayin talakawa a ranshi tun bai san kanshi ba, bai yi kasa a gwuiwa ba ya tsunduma harkar siyasa. Shigar shi siyasa ya girgiza zukatan magauta, don mutum ne shi na mutane yana da wani irin farin jini mai ban mamaki, fitowa ta farko jam'iyar shi ta TBA ta tsaida shi a matsayin dan takaran gwamna, kasancewar shima mai arziki ne sosai kuma sananne na mutane, wannan abu ya matukar ja mishi bakin jini a gurin daɗɗaɗun jam'iyar wanda suke ta harin wannan damar ba'a basu ba, shi karan kanshi bai so ba don shi da yaso ne ya fara daga ƙasa kamar Senate haka, amma tunda sunga cancantar shi sun daura shi dole ya karba, tun kan a kai ga yin zaɓe ma wasu daga Cikin jamiyoyin adawa suka shiga zame wa, suna janyewa, don sun tabbatar baza su kai labari ba, ranar kuwa da a ka yi zabe tun kan akai ga yin announcing kowa ya tabbatar da cewa shine ya lashe zaɓe, yayi mulkin garin nan a shekara ta dubu biyu , lokacin da yayi mulki bani da wayau, amma a labari ance har yau ba'a taba samun managarcin mulki kamar lokacin mulkin shi ba, duk da yasha gwagwarmaya sosai da sosai da mutane mabanbanta, yayi yaƙi sosai da mabarnatan ƙasar nan, bai bari an yi wasa da dukiyar talakawa ba, aiki tukuru yayi, a lokacin shi talakawa sunji daɗi sosai,a haka yayi mulki shi har na tsawon shekara takwas, kafin ya sauka, inda a zabe na gaba aka sake tsaida shi dan takaran Senate, shima alhmdllh yayi nasarar lashewa inda ya sake wasu shekaru 8 din akan mulki, bayan wannan matakin ance ya rike matakai da yawa masu karfi a mukamin gwammati, har kawo zuwa yanzu da yake a matsayin mai baiwa shugaban ƙasa shawara na musamman a kan harkokin tsaro da zaman lafiya a kasa. “Gyada kai A'ishatu da ta buɗe dukkan kunnuwanta tana shan labari tayi, jin salmah ta dasa aya, Cikin mamaki tace "Duk a ina kika samo wannan labarin haka." Murmushi t ayi ta ce "a Gurin Abie kinsan Abie yana ɗaya daga Cikin manyan lowyoyin shi a halin yanzu, kuma suna tare tun da daɗewa don shima Abie dan siyasa ne, tun yana matashi kuma koda ya gama karatu ya samu aiki bai bar siyasa ba, to a haka suka haɗu da general Idris kangiwa har ya zama ɗaya daga Cikin lauyoyin shi." A'ishatu tace "Masha Allah, lallai an sha daga, dama malam bahaushe ya ce in ka ji wane ba banza ba, Allah ya ja zamani." “ kwarai kuwa kuma har yanzu ana sha domin a halin yanzu babban ɗanshi ne ke siyasa, gwamnan mu na gobe da yardar Allah, Mr Ahmed I Ahmad kangiwa." Ta kàrashe maganar cike da shauki, cikin da tsagwaron mamaki A'ishatu ta ce "kina nufin Mr AA kangiwa." Salmah ta ce "kwarai kuwa shi nake nufi fari mai farar aniya." So take ta jeho ma Salmah wata tambaya amma kuma tana tunanin ta yaya, kafin takai ga ƙara cewa wani abu, Ammi tayi sallaman ta shigo ɗakin, hannunta rike da wayarta, ko sannun da suke mata bata samu amsawa ba ta ce "ku shirya yanzu pls na aike ku, gidan hajiya turai ku kai mata saƙo, gobe da safe za'ayi tafiya dashi wlh na sha'afa sai yanzu ta ke kirana, na tuna, na nemi salman ban ganshi ba na ta kiran shi a waya ma bai dauka ba." Da to Ammi suka amsa,ta juya ta fice tana cewa "ina jiran ku a ɗakina." Sharp sharp suka shirya Salmah ta saka wando falazo da riga mai dan kauri ta dauki hijab din ta Jalbab dogo har kasa ta saka bayan ta ɗan yi kwalliya mai sauki a gaggauce, ta saka takalmin ta hill, ita kam A'ishatu, dogon rigar atamfa ta zura ta yafa gyale medium, wanda ya shiga da kayanta, bata daura dan kwali a kanta ba saboda ita ba ma'abociyar daurawar bace, lip gloss fari ta shafa a pink lips ɗinta, ta zura takalma plat a kafarta suka fito sai kamshi su ke bazawa, a tsaye a falo suka samu Ammi riƙe da wani babban leda mika musu tayi tace "oya kuyi sauri, kuje ku dawo, kar ku zauna kuna kaiwa ku juyo kunji ko." Har suna hada bani wurin cewa "to Ammi." 2k ta mika musu ta ce "gashi ku dauki drop din napep ya sauke ya jira ku ya dauko ku, bazan ba ku mota ku tuka da yamma ba, dama salman na nan ne sai ya tuka ku, kuyi maza da kun kai mata ku dawo kuce ina gaishe ta." suka amsa mata da to, tare da saukar saƙon suka fito, basu sha wani wahala ba, wurin samun adaidaita,ko ciniki basu yi ba suka shiga tare gaya musu inda zai kai su, da kwatance ya kaisu har kofar gidan , sai da suka sauka salma kemai bayanin ya jirasu ya maidasu sai su bashi kuɗin gaba ɗaya, hakuri ya basu kan cewa yana da uzuri, mai karfi su sallame shi Kawai, ai da sun gaya mai haka tun farko da bazai zo ba, Salmah tace "Oh ohh yanzu ya zamuyi gashi ko daga nan zuwa fita titi baban aiki ne, ga yamma Mallam ka mana hakuri mana ko titi ka fidda mu." Ya ce "malama nima kumin hakuri uzirin gaggawa gareni ku sallame ni dan Allah, kudin ku Dari shidda."Salmah zata kara magana A'ishatu ta dakatar sa ita tare da mika mishi dubu daya ya basu canji ya juya abinshi. Shiga get ɗin tamfatsetsen gidan su ka yi, kasancewar me gadi yasan da zuwan su yasa basu wani tsaya dogon bayani ba ya buɗe musu. A falo suka tarad da ita zaune, hamshakiyar macece yar gayu, tana ganin su ta shiga sakar musu fara'a suma murmushi suka shiga yi har suka isa gabanta, suka ɗuka har ƙasa suka gaishe ta a tare, amsa wa tayi tana ɗago su , ta ce "oh ikon Allah ni turai girman ƴa mace babu wuya yanzu Salman da A'isha kune haka kuka kara zama zankaɗa zankaɗan yan mata, a lallai bari na fara shiri a Kwai gagarumin biki a gabana." Duk dariya suka saka cike da kunyar maganar ta, macece mai fara,a da yawan barkwanci hajiya turai akwai kirki kawar Ammi ce tun ta kuruciya, miƙa mata saƙon A'ishatu ta yi,karba tayi tace " yawwa dama yanzu nake son na sake kiran ta Ashe ma kuna cikin gidan, ya kuke yarana ya karatu." Suka amsa da alhmdllh, tace to ku zauna bari nasa a kawo muku ruwa, har suna haɗa baki gurin cewa "A'a hajiya mungode." Hararar su tayi daga inda take zaune ta shiga kwala kiran sunan yar aikin ta, da sauri ta iso tana cewa "gani hajiya." Ta ce "ki kawawo yarana abun taɓawa." Kan kace kwabo ta cika musu gaban su da kayan maƙulashe, ba yadda su ka iya haka dole hajiya Turai ta saka suka tsatstsakura, tana tare dasu tana musu fira cikin barkwancinta, suko sai dariya su ke yi idan ta faɗi abin dariya. Wani masifeffen ƙamshi ne ya turnike hancinsu, kafin su gama tunanin daga ina kamshin nan ke tasowa ya bayyana a falon Cikin gayun shi, matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, da haihuwa kyakkyawan gaske wankan tarwaɗa dan gaye na nunawa sa'a, tunda ya shigo falon idanunshi ke kan su, yana binsu da wani irin mayen kallo musamman A'ishatu data fi daukar hankalin shi, zama yayi a ɗaya daga cikin kujerun falon, idanunshi a kansu ya ce, "hajiya baƙi ki ka yi ne?" Ta ce "Baƙi kuma ƴan gida, baka gane su bane." kafin yace komai suka shiga gaishe shi, don su, sun gane shi sarai ɗan ta ne, Ammar abokin yaya Anas, amsa su yayi yana kare musu kallo don son lallai gano ko su waye, hajiya turai tace "Da gaske baka gane su ba." Ya girgiza kai, "Aiko dai anji kunya ƙannen Anas ne fa, Salmah da A'ishatu." Zaro ido yayi cike da mamakin girman yaran, yaran daya Sani a yan kwailaye sune suka zama haka, cike da mamaki yace "ikon Allah, yanzu salmah ce ta girman haka." , Shi sai yanzu ma yake gane ta, hajiya turai ta ce "ba kun watsar da zumunci ba, ai ga irinta nan, yanzu da a hanya kuka haɗu sai dai ka wuce su wace ko? Ni bana ma jin tunda ranar da Anas ya bar ƙasar nan kaje gidan nan." Sose keya yayi cikin rashin gaskiya, ta ce "naga kamar fita zakayi pls ka biya ka sauke min su daga nan ma ka shiga ka gaisar da hajiya Rabin." Da sauri ya ce "OK ba damuwa muje bari na kaisu." A ranshi yaji dadin wannan lamarin don shi faduwa ce tazo mishi daidai da zama......
09116099486 [5/14, 6:00 AM] Oum khadeejarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀
By
AyshaNalado
Page 8
“Yawwa to bari ina zuwa na ba su saƙo.” Hajiya Turai ta faɗa tana miƙewa zuciyarta cike da mamakin Ammar, saboda yadda ya yi saurin amsawa babu wani jan aji ko ƙorafin da ya saba, gashi ta lura tun ɗazu sai bin ƴan matan da kallo ya ke yi kamar zai haɗiye su da ido, murmushin manya ta yi zuciyarta cike da zargin wani abu, tasan dai banza ba ta kai zomo kasuwa, ta fi kowa sanin Ammar da ƙyuyar masifa, ko yanzu ma ta faɗa ne kawai don ta ji bakinsa, ba don ta saka rai da amincewarsa ba. Shigewar Hajiya ya bashi damar samun waje ya zauna a kujerar da ke kallon nasu, ya zuba musu shanyayyun idanunsa masu kyau da kwarjini. Duk sun taƙura musamman Aysha da ba ta cika son kallo ba, dauke kai ta yi daga gefen shi, amma duk da haka tana jin idanunshi na yawo a jikinta. Salmah ya shiga ja da hira yana mata tambayoyi akan karatu da mutanen gida, tana bashi amsa. Sosai haushin Salmah ya cika ta jin yadda ta sake tana bashi labarin gidansu, har da wanda ba a tambaye ta ba, abinka da mai bakin tsiya. Shi kuma bini bini ya sako ta cikin hirar tasu, basar da shi ta dinga yi tana amsawa a takaice, wani kuma ta share ta yi kamar ba ta ji ba. Gajiya ya yi ya ce "Salmah hala Sistar ki bata magana?" Kallon ta Salmah ta yi ta ce "Tana yi, amma ba sosai ba, kuma ba a ko ina ba." Gyada kai yayi tare da ce wa "Very good." Yarinyar ta birge shi jan class ɗin ta ya ƙayatar da shi uwa uba kyaulwunta ya matukar fusgar shi, cikin son ta kula shi ya ce "Ki saki jiki dani fa Aysha ni yayan ki ne, nasan baki waye ni sosai ba kamar Salmah, amma abinda yayi Anas shi yayi ni ki dauka cewa ni Anas ne." Rasa yadda za ta yi da wannan nataccen mutumin ta yi, kafin ta tattaro amsar da zata bashi, Hajiya Turai ta dawo falon hakan ko ba ƙaramin dadi ya mata ba, karasowa Hajiya ta yi tana ce wa "Ayya daughters ku yi hakuri na barku jira, wlh kunnen nawa ne da shegen mantuwa, manta indai na ajiye abin na yi." Ta ƙarkare maganar tana miƙawa Salmah wani leda mai dan girma mai dauke da rubutun Arabic da tambarin wani kamfani da ke nuni da cewar ta kasashen larabawa ce. Bayan Salmah ta amsa, sai taci gaba da ce wa "ƴan kayan kwalliya ce ta mata nace bari na baku kwa ƙara." A tare suka shiga godiya, magana Ammar ne ya katse su, "Hajiya ai da kinbar shi, yanzu in mun fita sai na biya dasu na siya musu." "Nawa dabam, naka dabam ko yanzu ma bata baci ba ƙari ai yafi ƙara." Murmushin ya yi ya ce "To shikenan yau zan fanshi abokina." "Ai kuwa dai da ka kyauta, Salmah, Aisha ku tashi ku je yamma na yi nagode Allah ya muku albarka ku gaishe ta da kyau." Kusan a tare suka miƙe Ammar yayi waje suka rufa mishi baya har gurin motarsa, suna zuwa Aysha ta yi saurin buɗe baya ta shige, don karma tsautsayi zama a gefen shi ya kama ta, don kwarai ta takura da mayen kallon shi. Fuskar shi ta gwada rashin jin dadin hakan, amma ba yadda ya iya, Salmah kam bata fahimci abinda ke faruwa ba ta buɗe gidan gaba ta zauna shima ya shiga ya ja motar suka bar farfajiyar gidan.
Ko a hanya shiru ta yi ta maida hankalinta kan wayarta, ta na dai jiyo sautin hirar shi da Salmah sama sama , amma kai tsaye ba za ta iya cewa ga abin suke cewa ba, jin motar ta yi parking yasa ta dago da sauri,tasan dai a ƴar tafiyar nan da su ka yi bai ci ace sun iso gida ba, tasha mamakin ganin ya faka ne a farfajiyar babba katafaren sabon gurin cin abinci da makulashen nan dake tashe wanda babu kamarsa duk faɗin garin, *Dausayi food's & snack's* a ruɗe tace "Salmah me ya kawo mu nan?" Salmah ta ce "ki tambayi, Ya Ammar." Juyawa ta yi ta banƙawa keyarsa harara, caraf idanunshi ya haɗu ta mirror, murmushi ya sakar mata da sauri ta dauke kanta, ya ce "Oh sorry Aysha ban gaya miki ba, na ɗan biyo daku ta nan ne, ku sai abin kwalama." Cike da jin haushinsa tace "Bama jin yunwa kuma a gida ance karmu daɗe Ammi za ta yi mana faɗa idan muka koma." Ƙarara muryarta ya nuna ɓacin ranta, duk shiru su ka yi kafin Ammar ya sauke numfashi ya ce "karki damu ni da kaina zan kai ku har gaban Ammi na kuma gaya mata nine na daɗar daku." Share shi ta yi dan har ga Allah ranta bai ya so, kuma ga wani tsitsinkewa da take ji zuciyar ta na yi haka kawai, gabanta ya shiga faɗuwa. Buɗe motar ya yi ya fita Salmah ma ta fita, ita kam gyara zamanta ta yi ta haɗe kanta da kujera tana ambaton sunan Allah saboda bakon yanayin da ya risketa nan take, ganin shiru shiru bata fito ba yasa Salmah dan leƙawa ta window ta ce "Sister fito mana." Ba tare da ta dago ba ta ce "ku shiga kawai, zan jira a nan." Muryar ta kadai ya shaidawa Salmah cewa ba wasa take yi ba, jiki a sanyaye Salmah ta kalli Ammar ta ce "Yaya Ammar wai mu shiga kawai." Shi karan kanshi jikin shi ya fara sanyi da lamarin yarinyar da alamar dai ko zai samu kanta sai ya sha baƙar wuya,amma ba komai zai jure, don ba zai wasa ya rasa wannan zukekiyar ba. ba dan yaso ba suka barta a mota suka shiga ciki shida Salmah.
Jin sun tafi yasa ta dago ta maka wa bayan shi harara tare jan tsuki, ta riga ta gama fahimtar takun shi tsaf, ,so yake ya samu fuskarta ta yadda zai iya gaya mata wani shirmen bazan shi, ta sha haɗuwa da maza kala kala da suka nuna muradansu a kanta, ta riga ta lashi takobin cewa har ta mutu baza ta taɓa ba wani ɗa namiji dama ya shiga zuciyarta ba, ta riga ta yi na farko, kuma na karshe, indai soyayya ce wannan alkawari ne.
Tana cikin wannan saƙe saƙen wata jar mota mai matsakaicin tsada amma sabuwa ce dal tayi parking a kusa da motar Ammar, bata san mai yasa ba amma haka kawai ta tsinci kanta da son ganin su wanene a cikin motar, ƙurawa motar idanu ta yi ba tare da ita ma tasan dalilin yin hakan ba amma koma mai tayi umarnin zuciyarta ne, anfi minti goma kafin a buɗe murfin motar, sai da aka kuma kwashe minti biyu , kafin da sauri taga wani mutum dogo ya fito daga motar, fuskar shi sanye da facemask idanunshi toshe da bakin gilashi kanshi sanye da face cap, ya jawo cap ɗin kasa sosai ya kare fuskar shi, hannun shi kuma rike da dan ƙaramin jaka mai zubin akwati, da wani irin sauri ya fito daga motar yana waige waige kamar mara gaskiya kafin ya yi wuf ya shige cikin wurin kamar walkiya cikin takun shi na majiya karfi.