Kenza eBookz

Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 7

Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 7

Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 7: Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 7. Dam dam dam zuciyarta ya ci gaba da bugawa da sauri, haka kurum ta ji…

3,171 words

Dam dam dam zuciyarta ya ci gaba da bugawa da sauri, haka kurum ta ji bata yarda da mutumin nan ba domin ta tabbatar bugun zuciyarta yana da nasaba da shi, ya yi kama da mugun, duk alamun rashin gaskiya sun bayyana a tare da shi, ‘ko dai irin masu dasa bom ne a cikin al'umma don su hallaka muminai waɗan da ba su ji ba ba su gani ba? Zuciyarta ya yi mata wannan tambayar cikin firgici, zumbur ta dago kai tana zare ido, tabbas zai iya kasancewa musamman yadda taga yana ta kaffa kaffa da akwatin nan tasan ba abin arziki bane a ciki, kuma hakan ba wani abu bane a wannan karni da suke ciki na yanayin rashin tsaro, ko sati ba a rufa ba da irin hakan ya kasance a tsakiyar kasuwar tudu har yanzu cikin jimami da alhinin abin jama'a suke.

Innalillahi wainnailaihi rajiun! Ta shiga maimaitawa a bayyane, yanzu ya za ta y?, ba za ta iya tafiya tabar salmah a cikin wurin nan ba, dole ta shiga ta ceto rayuwarta koda hakan na nufin zasu rasa rayuwar su baki ɗaya ne, lokaci guda ta fice daga cikin hayyacinta, musamman da zuciyarta ta ci gaba da hasaso mata hoton mutumin har ya riga ya dasa bom ɗin, da wani irin mahaukacin gudu ta balle murfin motar ta fito, waige waige ta shiga yi babu salmah babu alamar ta a farfajiyar wurin, da alama har zuwa yanzu basu fito daga ciki ba, da gudu gudu sauri sauri ta nufi cikin wurin, hankali a tashe kallo ɗaya zaka san bata cikin hayyacinta ita kadai tasan halin tashin hankali da take ciki, sai bangaje mutane take yi ba tare da ta tsaya ta saurare su ba, security dake bakin ƙofa ne suka rufa mata baya suna “Hee heee! Amma , ko su ɗin bata saurara ba taci gaba da kutsawa tana waige waige, wuri ne babba don gidan sama ne me hawa biyu yadda saman yake haka exactly ƙasan yake, kuma cike yake da mutane , tuni hankalin mutane ya fara dawowa kanta, take wasu daga cikin mutanen dake wajen suka shiga binta, don duk tunanin su sata tayi shi yasa security ke binta tana gudu, duk bata san su na yi ba, burinta bai wuce tayi tozali da salmah ta jata subar gurin , sai dai duk iya waige waige da duɓe duɓenta bata ga salmah a ƙasa ba,da alama suna sama kenan, da mugun gudu ta nufi saman, ganin haka yasa wasu daga cikin masu binta suka zagaya ta daya hanyar don yi mata zobe su ritsa ta.

Ya juya baya yana tafiyar shi cikin sassarfa sauri yake yabar gurin kafin mutane su ankara da shi so yake yayi ya gabatar da abin da ya kawo shi wajen, cikin gaggawa ya tafi domin yana da wani meeting da zai shiga immediately 6pm yanzu gashi 5:40 hawa stairs ɗin yake yi cikin sassarfa, yayin da ita kuma take bin bayan shi a guje ba tare da ta lura da cewa mutumin da dakewa gudu bane a gaban ta,don idanunta ya rufe bata ko ganin gabanta, burinta ta ja salmah su bar wajen kafin mai afkuwa ya afku. Ta iso daf dashi ba tare da ta san shi bane ta dai san a kwai mutum a gabanta wanda burinta idan ta cimmi shi bai kauce ba ta bangaje shi ta wuce kamar yadda take wa duk wanda ya tsaya mata a hanya , shi kuma jin alamar ana biye da shi da gudu, yasa ya dakata tare da juyowa a shirye don duk tunanin shi daya daga cikin masu harin rayuwar shi ne da basu rabi da bibiyarshi duk in da yasa ƙafa, dan sun sha kawo mishi irin waɗan nan harirrukan duk da futa ce yayi ta sirri cikin ɓadda kama.

Ba ta san wanda ke gabanta ya tsaya har ya juyo ba sai da ta ji ta gwabza wani irin mugun karo dashi, wanda saida yayi saniyar cirewar glass ɗin idon shi da face cap ɗin kan shi a lokacin guda,ita kam taga taga tayi baya zata fadi da sauri yayi wurgi da box ɗin hannunshi ya taro ta da gaba ɗaya hannayenshi, yayi haka ne kuma ganin idan har ya bari ta faɗi a gurin zata raunata sosai, duk da baisan wacece ba hasalima bai san shi take ma gudu ba, dai dai kuma lokacin masu binta suka ƙaraso wajen ciki harda salmah da Ammar, duk cirko cirko mutane suka tsatstsaya ganin abin da ke faruwa, ita kam idanunta a rintse yake don ta sadakar ta fadi, jin an taro ta yasa ta shiga sauke ajiyar zuciya da sauri da sauri, sun kwashe kusan 1 minute a haka, bata gama dawowa cikin hayyacinta ba.

Tunda idanun shi suka sauka akan fuskarta ya kafe ta da su, bai san me yasa ya kasa dauke idanu daga fuskarta ba. Tuna abin da ke gabanta yasa ta zabura da sauri ta ware idanunta, fuskar data gani ne ya saka ta sauri zaro sauran dukkannin girman idanunta, "baa ba ba ba Babagida.” Ta furta cikin rawar laɓɓa zuciyarta na tsintsinkewa.." .............

Please ku dinge react ta haka ne zan gane yadda kuka karɓi labarin na samu gwarin gwiwar ci gaba da typing, tunda comment ya gagara.😏 [5/14, 6:00 AM] Oum khadeejarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

By

AyshaNalado

Page 9

"Baa... Ba.... bangida." Haka ta dinga maimaita sunan a rarrabe idanunta ƙem cikin nashi. Sake ta yayi ta tsaya kan kafafunta kallon cikin idanunta yayi kafin a hankali da t muryarshi mara hayaniya ya ce "Ki dinga kallon gabanki idan kina tafiya Miss." Jin sautin muryar shi yasa ta ƙara gwalalo idanu waje, a ruɗe ta sake ce wa"Baban gi daa." Girgiza kai yayi ya ce "Not Babangida, I'm Ahmad Kangiwa." Kafin ta sake cewa wani abu ta ga ya ɗuka da sauri ya dauki face cap da box ɗin shi dake ƙasa kafin tayi wani yunkuri ya bace ɓat a wurin kamar walkiya, daidai time ɗin kuma salmah ta iso ta da sauri ta rirriƙeta hankali tashe take ce wa "Sister me ya same ki, meke faruwa waye ya biyo ki garin yaya kika fito daga ciki mota?" Duk wannan tambayoyin da Salmah ke jero mata babu guda ɗaya da ya shiga kunnenta, hanyar da ya bi Kawai ta ƙurawa idanu babu abin da ke amsa kuwa a kunnenta sai muryar shi da ya ke cewa "Not babangida, I'm Ahmad Kangiwa." Can kuma kamar zautacciya ta shiga cewa "shine, wlh shine Salmah Babangida ne." Kafin Salmah ta kai ga tambayarta wani Babangidan wanene ma Babangida, taga ta zabura tabi hanyar da yabi da mugun gudu, bata saurari kiran da Salmah ke mata ba ganin haka yasa ta rufa mata baya ita ma a guje tana ce wa "Ya Ammar pls help me, na shiga ukuna." Jin haka yasa Ammar security da sauran maza je biyu da suka biyo ta ɗazu suka sake rufa mata baya a guje.

Tana fitowa daga cikin wajen, motar shi na barin compound ɗin wajen da mahaukacin gudu, zubewa ta yi akan gwiwowinta ta fashe da wani irin matsanancin kuka, tuni hankalin mutane ya dawo kanta wasu duk sun bar abinda suke yi sun zubo mata idanu, wasu ma har sun fara kwashewa a samu na yaɗawa a duniya, dai dai nan, su salmah suka ƙaraso inda take, da sauri Salmah da ke kuka ita ma hawaye bibbiyu ta tsuguna tare da rungume ta a jikinta, cikin kuka take ce wa "Na haɗa ki da wanda rai da numfashin ki yake hannunsa ki tashi Aysha, duka idanun mutane yana kanki." A hankali take maganar amma kuma Cikin matsanancin kuka, rintse idanu Aysha ta yi ta tsayar da nata kuka tana sauraren na Salmah wanda take jin shi har cikin bangon zuciyarta, gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, a ranta taji babu daɗi yadda ta saka Salmah kuka bata ji ba bata gani ba, to ya zata yi itama abin ne yazo mata a bazata, daure wa tayi ta saka dukkan karfinta ta danne zuciyarta, ta zare Salmah daga jikinta ta miƙe tsaye tare da miƙar da ita, share mata hawaye tayi da hannunta, suka kalli juna, murmushin yake ta sakar mata don son kwantar mata da hankali, cikin muryarta irin na wanda yaci kuka ya gaji, ta ce "ki daina yi min asarar hawayenki masu daraja kinji salamatuna mai..." Kafin ta kwai ga karashewa Salmah ta katseta da cewa " ta yaya kike tunanin hawaye zasu daina kwaranya a idanuna idan har zaki ringa shiga ciki irin wannan halin,wannan ba shine karon farko da kika taba yin irin hakan ba,na tambayeki sau babu adadi wanene shi kin ki ki gaya min ya kike so nayi da rayuwata ne A'isha."ta karashe maganar tare da fashewa da matsanancin kuka hawaye na kwaranya a idanunta, kama hannayenta Aysha ta yi, ba tare da ta tanka mata ba ta ja ta suka nufi gurin da Ammar ya faka motar shi, mutane sai kallon ikon Allah suke, security ne suka shiga yima Ammar faɗa wai me yasa yake yawo da mai larurar hauka, yanzu da ta jima wani a gurin fa, shidai hakuri ya ringa basu don shima harga Allah ya tsorata, kuma ya yarda da maganar security ɗin da suka ce ita ɗin mai lalurar hauka ce, to idan ba hauka ba ta yaya mutum zai kama gudu shi kaɗai.

A mota ya same su dukan su a gidan baya fuskokin kowacce su babu alamar fara'a salmah ta haɗa kai da kujera sai shehshekar kuka takeyi yayinda A'ishatu ta daga kanta tana kallon saman motar bayanta jingine da kujera, hawaye sai gudu suke a fuskarta a gefe guda kuma sheshshekar kukan Salmah na taɓa mata zuciya. Jiki a sanyaye ya buɗe gaban ya shiga yaja motar suka bar wajen, har suka isa kofar gida babu wanda yace uffan, a cikin motar, a bakin get ya ajiye su, shiga cikin da yayi niyya ma tuni ya fasa don jikin shi ya mutu muruss, yana yin parking suka buɗe kofar suka fito Salmah ce tayi karfin halin zuwa wajen windo ta daidai saitin da yake ta ce "mungode yaya Ammar." ƙaƙalo murmushi yayi ya sakar mata tare da cewa "ba komai Salmah ki gaida Ammi bazan samu shigowa ciki ba yanzu, naji anata kiraye kirayen sallah amma zan dawo ko gobe ko jibi na gaisheta." Gyada kai tayi ba tare da ta iya cewa komai ba Koda ta ɗago A'ishatu har ta buɗe get ta shige, bin bayanta tayi jiki a sanyaye, har suka isa entrance din part din Ammi babu wacce ta ce wa yar uwarta uffan, Salmah ce ta miƙa hannun zata dannan doorbell da sauri Aisha ta riƙo mata hannun kallon juna sukayi cikin ido kowacce idanu jajur anci kuka an ƙoshi, girgiza mata kai A'isha tayi, kafin kuma taja hannunta da sauri sauri suka nufi wajen bakin famfo dake daga gefe, wanda anyi shi ne don bama flowers ruwa, gane abin da take nufi yasa Salmah kwace hannunta, ta juya mata baya da sauri ta ce "Akan me kike so mu boye wannan maganar ga Ammi, ki sani anyi na farko kuma na karshe in dai ni baza ki iya gaya min wanene wannan mutumin nan ba, ai ita nasan idan ta tuhumeki zaki gaya mata." Da sauri ta riƙo hannunta ta baya cikin yanayin tashin hankali tace "A'a Salmah A'a A'a don Allah da manzonsa karki min haka." "Zan iya rufe wannan maganar akan maslaha ɗaya, idan kin amince yau zaki gaya min wanene *Babangida*." Shiri tayi tana sauke ajiyar zuciya, bata ce uffan ba kuma ɓata saki hannunta ba, ganin haka yasa ta fisge hannunta zata yi wucewarta da sauri ta sake riƙo hannun, cikin sanyin murya tace "Salmah bazan sanar dake wanenen Babangida domin sanin wanene shi bashi da amfani a gareki, babu abin da zai haifar miki sai bakin ciki da bacin rai da ƙuncin zuciya." Ajiyar zuciya Salmah ta sauke tare da juyowa ta rungume ta, suka ci gaba da kuka, cikin kukan Salmah ke cewa "saboda meye baza ki gaya min ba, shin bakyaso ki raba damuwarki da nine, a she har yanzu baki dauke ni ƴar uwa ba? ba wai na damu da son sani wani boyayyen sirrinki saboda komai bane sai don saboda soyayyar da nake miki, ina sonki soyayya irin ta jini , ina jinki a rai na har fiye da yadda nake jin Salman ɗan uwan tagwaitakana, idan har ina miki irin wannan soyayyar ta yaya bazan so ganin farin cikin ki ba, ta yaya damuwarki bazai dameni ba, ina son na ganki watarana kina dariya mai amsa sunan dariya bawai wannan kalar dariyar da kike mana kullum ba wanda ni ce kadai na fahimci na yaƙe ne wanda yafi kuka ciwo, na fahimci rashin walwala da farin cikin ki nada nasaba da Babangida tun ranar da kika faɗo hannun iyayena, ko kin san sau da yawa nasha laɓewa na saurare ki kina kuka a toilet kina ambatan wasu maganganu da wani yare wanda bana iya ji, abinda Kawai nake iya ji a cikin zancenki shine Babangida, haka ma ciki barcin ki, kusan kullum a cikin barcin ki sai kin ambaci sunan Babangida ba tare da kema ki a sani ba, abin da ya faru rannan a green land har yau yana rai na bawai na manta bane shirya ta yadda zan tunkareki da zancen nake shine yauma kika sake maimaita abin da yafi wanda ya faru ranar kuma duk a silar Babangida, to na gaji ina son sanin wanenen Babangida." Tana gama faɗin haka ta ɗuka ta tari ruwa ta wanke fuskarta ba tare da ta jira Aisha ba ta wuce abinta.

Girgiza kai tayi tana jin wani irin abu na sukarta a zuciya, ta fi minti biyu a tsaye tana bin hanyar da Salmah tabi da idanu kafin ta duƙa itama ta tari ruwa ta wanke nata fuskar, ta bi bayan ta , a falo ta samu Ammi da Salmah, tana shiga duk suka zuba mata idanu hakan yasa gabanta ya yanke ya shiga faduwa, duk da bata tunanin Salmah ta gaya wa Ammi wani abu gama da abin da ya faru. Cikin sanyin muryata wanda yadan dashe saboda kuka ta ce "Ammi mun dawo." bata amsata ba sai cewa da tayi, "zo nan kema." Zuwa tayi gabanta, ta tsuguna, cikin ido Ammi ta kalleta kafin tace "shin ina kuka tsaya bayan hajiya turai tace min tun tuni kuna hanya kuma mai ya samu idanunku kukan me kuka yi." Rasss gaban A'ishatu ya faɗi koda wasa baza taso Ammi tasan abin da ya faru ba, kuma ita baza ta iya ma Ammi karya ba, ta yaya zata yi karya bayan ga Salmah a wajen ɗagowa tayi ta kalli Salmah cikin sa'a itama Salmah ta kalleta haɗa idanu sukayi, da idanu tayi mata alamar roko akan karta gayawa Ammi komai, dauke kai Salmah tayi tace "Ammi na riga na gaya miki accident muka samu me napep dinmu ya buge wata yarinya, duk taji ciwo gwanin tausayin shine ma abin da ya saka mu kuka, Ammi naga kamar baki yarda dani ba to A'ishatu ke da ta fi yarda da ke ki mata bayani." Da sauri A'ishatu tace "eh haka ne Ammi yarinya karama abin tausayi Ammi sai da muka jira ya kaita asibiti mafi kusa a ka yi mata magani sannan ya karaso damu gida." Cikin tausayawa Ammi tace "Allah sarki yanzu ina yarinyar?" Salmah tace "tana gurin iyayenta ciwon da sauki ƙujewa ne, a hannun da gefen fuska." Ammi tace "Allah ya bata lafiya Allah ya kiyaye na gaba." Har suna hada baki wurin amsawa da amin , ta ce "ku tashi kuje kuyi sallah gashi nan har an kusa idarwa a masallatai." Ita ce ta fara mikewa ta nufi ɗakinta, sai da ta kulewa ganin su Salmah ta mike ba tare da ta kalli inda A'ishatu take ba ta bar wajen, sauke ajiyar zuciya tayi, kafin itama jiki a sanyaye ta mike tabi bayan Salmah.

Haka suka karkare cinye dan sauran yinin ba tare da Kalmar A ta kuma shiga tsakanin su ba, fushi sosai Salmah take yi da ita wanda ko haɗa ido taki bata damar suyi, maganar duniya Aysha ta mata amma ta danne zuciyarta taki tankawa, damuwa goma da ishirin suka taru suka mata caa, kan kace koba zazzabi na neman rufeta, Salmah tsab ta fahimci ce ta, tausayinta ya riga ya gama karshe zuciyarta amma dole ta danne na ɗan wani lokacin idan tayi da fushin taga babu riba zata sauko ta koma da rarrashi wata kila ta dace, har Ammi da Salman sai da suka so fahimtar yau kamar da matsala a tsakaninsu ko wani abu na damun su, Salman ne ya kasa hakuri ya jeho musu tambayar "wai yau meke damun ku ne, ƴan mata, naga kunyi wani irin kamar Baku cikin walwala." Ammi ce ta bashi labari haɗarin da suka samu yau, shima ya tausayawa kwarai yayi jimami, koda suka zo kwanciya baya Salmah ta juya mata tare da daukar wani bargo dabam bata shiga wanda suke amfani dashi tare ba, abin yayi wa Aysha ciwo, gefe daya ga tunanin Ahmad kangiwa daya ke ta azalzalan zuciyarta nan kuma ga Salmah na kokarin haifar mata da ciwon kai, duk shuru sukayi a kwance babu wacce ta iya rintsawa a cikin su abu ne da bai taɓa faruwa ba tun tasowar su, samun sabani a tsakanin su, daren yau yazo musu a baibai, kasa daurewa Aysha tayi duk kuwa dauriya da jarumtarta, a hankali shehshekar kukanta ya fara karaɗe ɗakin nasu, Salmah na jinta amma ta share ta bata tanka ba, don ta fahimci ta fara laushi, tana da tabbacin idan ta daure zataci galaba akan ta, tayi kuka yafi na 30 minute kafin kuma a hankali ta kira sunan Salmah, shareta ta yi wannan karon ma, cikin dasasshiyar murya tace "nasan kina jina Salmah kiyi hakuri ki fahimce ni." Yaye zanin rufa Salmah tayi ta miƙe daga kwancen da take ta zauna bakin gado tare da sauke kafafun ta kasa, cikin yanayin nuna fushi da bacin rai tace "hakurin me kike bani A'ishatu, babu komai ai rayuwa ce, yau kin nuna min cewa ke ba yar uwata ta jini bane ashe ni kadai nake haukana ke baki dauke ni a yadda na dauke ki ba, zanyi kokari na cireki a zuciyata zanyi kokarin na sauke ki daga matsayin da na daura ki a cikin zuciyata." A hankali ta tashi daga kwance ita ma, ta bayan ta ta tsaya ta miƙa hannunta ta daura akan kafadar ta, cikin dasassiyar murya tace "ban ki gaya miki tarihin rayuwata saboda wata manufa ba sai dan kuje miki shiga damuwa, da tarwatsa miki zuciya da cusa miki tsanar Kalmar so, da duk wani abin da ya shafi soyayya a rayuwarki, labarina zai saka miki tsanar duk wani ɗa namiji a rayuwar duniyar nan." Shuru tayi ta ɗan nisa kafin ta ci gaba da cewa "cikakken sunana A'ishatu Muhammad Lawal........" [5/14, 6:00 AM] Oum khadeejarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

By

AyshaNalado

Page 10

Readers Also Read