Kenza eBookz

Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 8

Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 8

Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 8: Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 8. "Cikakken sunana A'ishatu Muhammad Lawal, na tashi a gaban iyayena duka…

3,322 words

"Cikakken sunana A'ishatu Muhammad Lawal, na tashi a gaban iyayena duka biyu wato uwa da kuma uba. Na kasance nutsattsiya kamilalliya, mai tarin hankali da baiwa kala kala. Kyakkyawar gaske ce mai ɗumbin ilimi, kuma shiru shiru ce wacce ko ɗan yatsa ki ka saka mata a baki sai dai ta ciro ta goge miki ta kuma baki hakuri, idan ana neman yarinya mai hankali a kauyen mu a wancen karni to da ni ake kwatance, duk wasu iyaye idan zasu yi wa ƴarsu faɗa a wancen ƙarnin ni su ke mata nuni" Shiru ta yi ta ɗaga kai sama tare da rintse idanu tana sauke ajiyar zuciya hawaye na kwaranya daga idanunta, sam bata kaunar abin da zai tuna mata da rayuwarta ta baya, amma ya zama tilas yau salmah ta san wacece ita, jin shirun ya yi yawa ne ya sa Salmah gyara zama tare da juyowa ta fuskance ta da kyau, ganin yanayin da ta shiga ya karya mata zuciya, amma ta dake cikin dakakkiyar murya wanda babu alamar wasa a ciki ta ce "Ke na ke saurare A'ishatu Muhammad Lawal." Minti biyu ta kwashe kafin sauke kanta tare da share hawayenta ta ɗago ta kalli Salmah cikin ido, sannan ta fara bata labarin rayuwarta tiryan tiryan, tun daga lokacin da ta mallaki hankalin da zata iya banbance tsakanin fari da ɓaki? Haɗuwarta da Babangida da rabuwarsu, barin iyayenta har zuwa yau da suke tare a dai dai wannan lokacin.

Ya Salam! tuni Salmah ta gama ficewa daga hayyacinta, kuka take yi bil haƙƙi da har da majina, ita karan kanta Aysha ɗin kuka ta ke, domin tana bada labarin ne hoton komai yana dawowa sabo fil a ƙwaƙwalwarta, gani take yi kamar a lokacin komai ke faruwa. Tana dasa aya Salmah ta matsa tare da rungumeta a tare suka sake fashewa da wani sabon kukan, babu mai ƙarfin halin rarrashin wani. Sun ɗauki tsawon lokaci a haka kafin Aysha da yake ta fi Salmah jarumta, ta samu ta zare ta daga jikinta ta dago fuskarta suka kalli juna kowanne idanu jajur cikin son danne kukan dake ƙoƙarin sake kufce mata ta ce "Na gaya miki salmah zuciyar ki ba za ta iya ɗaukar hargitsi da ruɗani da tashin hankalin da ke cikin labarina ba." Bata amsa ta ba saima ƙara maida kai da tayi kafaɗarta suka ci gaba da raira kukansu Salmah na kukan tausayin A'ishatu da iyayenta, yayinda A'isha ke kukan kaico nadama da dana sani, tare da ƙara ɗaukar alwashi bakin rai bakin fama akan sai taga bayan Babangida a duniya sai ta tagayyara rayuwar shi kamar yadda ya tagayyara nata. Sai da suka yi kukan su suka ƙoshi babu mai rarrashin wani, sannan suka rarrashi kansu, Salmah ta ɗago daga kafaɗar A'ishatu ta kamo duka hannayenta ta riƙe cikin nata, kallonta tayi ido cikin ido cikin dasasshiyar murya tace "Tabbas kin yi gaskiya da kika ce labarin ki zai tarwatsa zuciyata, zai ɗaga min hankali zai sanya na tsani Kalmar so da soyayya a rayuwata, na tausayawa Baffa da Inna dama Maryoji, amma ba komai, komai mukaddarine, kuma Kaddara ta riga fata wannan itace naku kaddaran, ya Allah ka kare mana su a duk inda suke." Matse kwallah tayi cikin shehsheka taci gaba da cewa "Babangida ya ci amanarki ya rusa miki farin cikin ki dana iyayenki, na tsane shi nima tsana mafi muni, kuma ki sani daga yanzu yakin ba naki ba ne ke kadai ni nan zan taimaka miki har sai ki kai Babangida ƙasa warwas muddin yana raye,sai dai kafin nan ina son ki amsa min tambaya guda ɗaya tal. Shin me yasa kike alakanta Babangida da familyn kangiwa."Rass! Gabanta ya yanke ya faɗi, ya a ka yi Salmah tasan da hakan don koda gigin wasa bata sako wannan maganar cikin labarin data bata ba, murmushi Salmah tayi mai ciwo tace "kina tunanin ta yaya akayi nasan, kina suspecting cewa Babangida ya fito ne daga familyn kangiwa ko, kina zargin zai iya kasancewa ɗan uwan Mr AA imma wan shi ko ƙanin shi koma dai shine karankanshi Babangidan ko? Karki wahalar da kanki wajen son gano a ina nasan hakan , bari na sauwaƙe miki tun daga ranar da muka fara ganin Mr AA a green land na fara fahimtar wani abu, da gangan naki gaya miki full name ɗinsa a ranar, kuma duk binciken da kikayi a daren ranar tamkar a kan idanuna kika yi shi. Shuru na miki don ganin iya gudun ruwan ki,. Yanzu ya zaki ji idan kika samu tabbacin cewa Mr A A kangiwa shine Babangida." Zaro dukkan idanunta tayi waje baki na rawa ta ce "Ba..ba.. shi bane Salmah." Dafa kafaɗarta Salmah tayi ta ce "Nima bani da tabbaci yakini kawai nake dashi, zuwa gobe zamu, bincika kibar min wuka da nama a hannuna idan har shine Babangida zamu fara shirin a kanshi duk da bana tunanin zai kasance shine Babangida sai dai idan wani na jikin shi ne, kuma dole Mr AA ya zama tsaninmu na cimma Babangida domin ba mu da wani hanya sai shi ɗin, duk da abu ne mai matuƙar wuya mu iya kutsawa rayuwarsa cikin sauƙi domin mutum ne mai matakan tsaro ta ko ina.” Da dasasshiyar murya Aysha ta katse ta da cewa “Ta yaya zamu iya tabbatar wa a gobe goben nan." Wani irin murmushi Salmah ta yi ta ce “ Hanya mafi sauki kuma mafi kusanci a gare mu wato Abie, now ki kwanta kiyi barci domin daga gobe bacci zai zama raggage a garemu." Zuru Aysha ta ma Salmah tana kallon ta bata ko ƙefta ido, mamakin Salmah ne ke neman halakata Salmah data ke dauka mara wayau ita take zaro maganganu haka, murmushin ƙarfafa gwuiwa salmah ta mata, wanda itama ƙarfin hali ne Kawai wai barawo da sallama, "Ki kwanta nece." Ta faɗa cikin kwantar da murya, kasa musa mata tayi, daga inda take zaune akan gadon ta miƙe ta kwanta, ita ma Salmah kwanciya tayi tare da ja musu bargo, shuru su ka yi dukkan su kowa da saƙe saƙen da yake yi a zuciya, dakyar barci barawo ya kwashe Salmah, A'ishatu kam babu maganar barci don yau mikin zuciyarta gaba ɗaya ya dawo sabo dal tunanin su Baffa da halin da suke ciki a yanzu shine abinda yafi daga mata hankali, sai gabanin asuba ita ma bacci ya ɗauketa, bata wani Daɗe ba taji Salmah na tashin ta, ba yadda ta iya haka ta miƙe jiki a sanyaye ta shige toilet ta ɗauro alwala, bayan sun idar da sallah tare da duk wani abu da suka saba yi na al'ada, basu kwanta ba aikin gida suka shiga yi kamar yadda suka saba share share da wanke wanke , sai da suka kimtsa komai sannan suka shiga kitchen domin haɗa breakfast, suna shiga Ammi na sakkowa a kitchen ta same su, duk zuɓewa sukayi suna gaishe ta amsawa ta yi tana binsu da kallon tuhuma, so take ta jeho musu tambayar meya samu idanun su, sai kuma ta tuna da batun accident ɗinsu na jiya hakan ne ya dauke mata hankali daga tambayar data yi niyar yi musu, a tare suka haɗa breakfast, suka jera komai a dining umarni Ammi ta basu akan suje suyi wanka suyi shirin makaranta, kafin lokacin yin breakfast yayi, da to suka amsa mata, tare da wucewa ɗakin su don yin shirin kamar yadda ta umarta.

Karfe takwas daidai dukkansu kowa na zaune akan dining cikin shiri,Abie da Ammi cikin shirin tafiya aiki, Salmah, Salman da A'ishatu duk cikin shirin tafiya makaranta, abinci suke ci jefi jefi akan taɓa hira idan ta kama, Salmah ce ta kalli Abie ta ce "yawwa Abie na tuna dama nace zan tambaye ka." Abie yace "uhumm Allah yasa na sani." Ta ce "dama jiya a school ne musu ya haɗa ni da wata ƙawata classmate ɗina a kan Mr AA kangiwa shine ni kuma nace insha Allah yau zan tambaye ka, Abie kasan me take cewa, wai bayan Mr Ahmed Idris Ahmad, wai ana kiran shi da wani suna Babangida, Abie wai haka ne. " shiru Abie yayi kamar ba zai amsa ba alamar yana tunani, can kuma ya ce, “ Kai anya kuwa, bana tunanin Hakan gaskiya. Can kuma kamar wanda aya tuna wani abu ya ajiye cokalin hannushi ya kalli Salmah ya ce, “ Amma wacce yarinya ce wannan, kuma a ina take?” Kallon juna su ka yi da Aisha gaban kowaccen su na faɗuwa, diriricewa Salmah ta yi, sanin wanene Abie tsohon lawyer ne mai zaman kanshi wannan tambayar daya jeho mata tasan ba'a banza ba,dana sani ta shiga yi data sami Abie da wannan zancen ba tare da ta shirya amsar da zata bashi a duk sanda ya jeho mata tambaya makancin wannan ,Allah ne ya taimaketa wata dabara ta faɗo mata, ta yi yar dariya ta ce "Abie classmate ɗina ce fa, yarinyar tace ma wai ita yar uwar shi ce mamanta yar familyn kangiwa ce." Sauke ajiayar zuciya Abie yayi wanda daga ita har Aysha abin ya matuƙar ɗaure musu kai, ya ce "Umhum! yanzu naji ba tu sai dai kam hakan, bani da wani masaniya akan hakan but zan bincika miki,Mr Ahmad yana da suna kala kala domin zan iya ce miki daga iyayenshi har ƙannenshi kowannen su da sunan da yake ƙiran shi dashi na musammam, domin shi ɗin na musamman ne ko a cikin ahlinsa, zai iya yuwuwa wani nashi na ƙiran shi da hakan amma fa bani da tabbaci yaƙini kawai gareni." Wani mugun tari ne ya sarke A'ishatu lokacin da Abie ke musu wannnan bayanin, wani irin ragargazar faɗuwa gabanta ke yi, zuciyarta kamar zata Faso kirji ta faɗo, da sauri Salmah ta tashi ta tallaɓeta tana mata sannu duk su Ammi da Salman harma da Abie sannu suka shiga jero mata a kusan kunnenta Salmah ta raɗa mata "ki shiga taitayinki Aysha a gaban Abie ki ke." Duk abin da suke akan idon Abie bai daiji mai tace ba amma dai ya ɗiga musu alamar tambaya. haka suka ƙarƙare cin abincin Aysha bata cikin nutsuwa, itace farkon miƙewa daga dinning ɗin ta wuce ɗakin su, zuciyarta na tafarfasa. Idonta idon Babangida idan har ya kasance daya daga cikin ahalin Kangiwa, wato ya barota cikin kunci da bakin ciki yazo yana rayuwar shi cikin kwanciyar hankali, tabbas sai ta zame masa annoba sai ta addabi rayuwar shi, sai ta lalata tanaɗin shi , kuma ta zame mishi kadangaren bakin tulu, Salmah ce ta shigo ɗakin a ruɗe ta tsuguna a gaban ta ce " dan girman Allah ki iya sarrafa zuciyar ki a gaban mutane idan har kina so komai ya tafi mana daidai." Cikin dacin zuciya tace "Salmah wani abin ba zai dannu ba."cikin kwantar da murya Salmah tace "na sani Aysha but dole zaki yi." Ajiyar zuciya ta shiga saukewa a jere a jere ba tare da ta ba Salmah amsa ba, Salmah tace "ki tashi muje Salman na jiran mu, but ki daidaita kanki pls, zamuyi magana a school."

A mota shiru Aysha ta yi ta lula duniyar tunani, Salman nata mata magana bata ji shi bama balle ta tanka, ganin haka yasa Salmah ta yi saurin ɗauke mai hankali daga kanta, ta hanyar jan shi da faɗa kamar yadda suka saba kullum wannan ne yasa bai kula da halin da A'ishatu ke ciki ba har suka isa, buɗe ƙofar bangaren ta da salmah tayi ya dawo da ita hayyacinta, kamo hannunta tayi suka shiga tafiyar ba tare da sun jira Salman ba,dama ba department ɗinsu ɗaya ba dukan su kowa da inda ya nufa, suna tafiyar Salmah tace "why Aisha me yasa kike haka ne? Na gaya miki fa dole ki koyi kiyaye wa idan kina son komai ya tafi mana normal." Gyada kai Kawai tayi don bata jin zata iya buɗe baki ta yi magana, Salmah ta ce"mu haɗu a cafeteria after lecture zamu yi magana mai mahimmanci nasan zaki rigani fitowa lecture da mintuna talatin, ki je ki jirani zan same ki acan." Daga haka suka rabu kowacce ta kama hanyar department dinta.

Kamar yadda Salmah ta faɗa goma da rabi daidai A'ishatu suka fito daga lecture, direct kuma cafeteria ta nufa ta samu wuri daga cen baya ta zauna tana jiran Salmah, after 30 minutes Salmah ma suka fito, bata ɓata lokaci ba ta nufi hanyar cafeteria ita ma don ta samu Eshart su tattauna kamar yadda tai mata alkawari, tafiya take Cikin sauri hankalinta kacokam nakan hanyar inda ta nufa wata bakar jibgegiyar jeep mai bakaken glass ne ya parker a gabanta saura kaɗan ma ta bugeta, kafin ta gama dawowa hayyacinta daga tsoratar da tayi taga an bude ƙofar wani mutum murɗaɗɗe ya fito daga motar daf da ita yazo kamar zai bata hakuri Kawai taga ya manna tsinin wani abu a gefen cikinta wanda bata da haifi a kan bindiga ce, cikin ƙasa da kakausar murya shi ya ce "shi ga muje." Zabura ta yi za ta kwace ya ce “kul! Kada ki kuskura ki yi wani yunkuri, idan ki na so ki fita lafiya ........ [5/14, 6:00 AM] Oum khadeejarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

By

AyshaNalado

Page 11

Take jikinta ya dauki rawa zuciyarta ta shiga bugawa da karfi, ba tare da wani zaɓi ba ta shige motar, shi ma mutumin ya shiga ya mayar da murfin motar ya rufe, da mugun gudu driver ya ja suka bar cikin school ɗin.

A karo na uku ta ja guntun tsaki tare sake duba agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunta, kimanin awa daya kenan ta kwashe tana jiran Salmah amma shiru, tun goma da rabi take nan gashi har sha ɗaya ya gota, mayar da kai ta yi ta jingina da kujeran da take zaune tare da dafe goshin ta da ke matsanancin sara mata. A haka ta sake kwashe wasu mintuna ashirin ɗin, amma shiru kake ji tamkar malam ya ci shirwa, miƙewa tayi ta ɗauki jakarta ta rataya jiki a sanyaye ta fito daga wajen, kai tsaye department ɗin su salmah ta nufa don ganin ko lafiya, tun kafin ta ƙarasa ta haɗu da Zahra ɗaya daga cikin ƙawayen Salmah, kasancewar sun santa sosai yasa ta tsaya suna gaisawa bayan sun gaisa take tambayar ta Salmah, Zahra ta ce "wlh nima ita nake nema kinga handout ɗinta nan da ta ce na riƙe mata tana zuwa shiru kusan awa ɗaya gashi har ana shirin shiga second lecture." "OK nagode bari na dubata wajen Salman ko can ta je." Ta juya ta tafi tana saƙe saƙe a ranta, shin ina Salmah ta shiga ne?

Ta tamu Salman da Suraj da wasu friends ɗins, fitowarsu kenan daga lecture an zazzauna ana hutawa, Salman na hangota ya miƙe ya nufota da sauri, dakatawa ta yi ganin ya taho har ya isko ta, Suraj ne daya biyo shi ya fara gaisheta, amsawa ta yi, tare da ce wa "Salmah na zo nema ko tazo nan." "Bata zo nan ba gaskiya don yanzu Suraj ke damuna ma wai mu je wajen ku, ina ce ma kuna tare ai." Cewar Salman, "A'a bamu tare wlh." Ta faɗa cikin damuwa tare da ɗan fara waige waige, a zuciyarta tana cewa Salmah ina kika shige ne?

Ganin yanayin data shiga yasa har suna haɗa baki wurin tambayarta ko lafiya me ke faruwa, girgiza kai tayi ta ce "ba komai abu zan ƙarba a wajenta, tunda bata nan, sai anjimanku." Daga faɗin haka ta juya da sauri ta wuce.

Duk inda tasan zata samu Salmah ta je, ba ta nan itace har hostel don tasan ta da yawan ƙawaye wata ƙila wata cikin su ta ja ta, wasa wasa ana neman kwashe awa biyu babu Salmah gashi har ƴan class ɗinsu sun kuma shiga lecture, ita ma ga nata lokacin shiga second lecture ɗin saura 20 minutes jiki a sanyaye ta juya ta kama hanyar department ɗinta zuciyarta babu daɗi sai saƙe saƙe ta ke yi kala kala ga tunanin Ahmad daya addabi zuciyarta motsi kaɗan ya faɗo mata a rai ga kuma tashin hankalin rashin ganin Salmah da yake neman dagula mata lissafi.

Daga bayanta ta ji an ce "A'ishatu Muhammad Lawal." Jin muryar Salmah yasa ta saurin juyowa, zaro ido ta yi ganin yadda idanunta suka yi jajur alamar ta yi kuka ta gaji, da sauri Aysha ta ƙarasa gareta a ruɗe take ce wa "ina kika shiga daga ina kike me ya same ki kike kuka?" Girgiza kai ta yi ta ce "babu komai Aysha." Ta kama hannunta ta fara janta ba tare da ta bata gamsasshen amsa akan tambayar da ta mata ba, a dan harzuƙe tace "ina tambayar ki baki bani amsa ba, nace me ya same ki daga ina kike na zageya faɗin school ɗin nan ban ganki ba yanzu kuma ga ki na ganki ki na kuka."

Bata saurareta ba sai da ta kaita bakin wani matakala suka zauna, kallon fuskarta ta yi, sai kuma ta yi saurin kawar da kai, tare da sauke ajiyar zuciya zuciyarta na mata wasi wasi akan abinda take shirin aikatawa, sai kuma ta tuna girman alkawari, a sanyaye ta ce "Na gaya miki babu abin da ke damuna kin san dai bazan boye miki komai ba ko, kaina ke dan mini ciwo shine naje clinic aka haɗa mini magunguna, to ciki harda allura kin san ni kuma bana son allura ko? To shine ya saka ni kuka." Sauke ajiyar zuciya Eshart tayi ta san Salmah ba ta mata ƙarya kuma ba ta boye mata komai na ta, bugu da ƙari tafi kowa sanin ƴar tsaman dake tsakanin salmah da allura, bata ƙaunar allura ko misƙala zarrati, don haka ba tare da wani dogon nazari ba ta yi amanna da batun ta, take ta shiga jero mata sannu, lumshe ido Kawai Salmah tayi tana sauraren ta ba tare da ta amsa sannun da take jero mata ba, jikinta gaba ɗaya yayi sanyi tausayin Aysha ta ke ji a zuciyarta kamar kamar me, gaba ɗaya yanzu lissafinta a dagule yake, tana bukatar ke6ewa domin ta yi nazari da tunani, karar da wayarta ya yi alamar shigowar message yasa ta ware idanunta, bude saƙon ta yi, ta duba lambar ce babu suna, tana gama karanta ta yi delete ɗin shi, juyowa ta yi ta kalli Aysha da duk ta shiga damuwar jin cewa bata da lafiya, ta ce "Da sauki sosai na ji dama, ki tashi ki je class ba 1: 30 zaku shiga ba."

"baza ni ba Salmah ko na shiga babu abinda zan fahimta a ciki kawai mu wuce gida."

Shiru Salmah ta yi tana nazari ita karan kanta yanzu babu abin da take bukata kamar ta ganta a gida, da gaske kanta ciwo yake yi kamar ya rabe biyu, ganin halin da Aysha ta shiga yasa ta amince mata.

Text ta turawa Salman ta sanar masa wucewarsu, ba tare da bata lokaci ba suka fice daga school ɗin.

Koda suka dawo gida babu kowa, Ammi bata dawo daga asibiti ba, dkai tsaye ɗaki Salmah ta wuce ta watsa ruwa ta yi Sallah ko abinci bata nema ba, ta haye bed ta kwanta tare da lumshe idanunta kamar tana bacci duk da kuwa ba ta jin zata iya yin wani bacci a halin da take ciki.

Aysha kam kitchen ta nufa kai tsaye don Samar wa salmah abin da za ta ci, sharp sharp ta daura farin couscous ganin akwai miyan sauce na hanta a fridge dauka ta yi ta kunna gas ta daura shi ta dumama tana gamawa ta zuba mata a plate ta dauka tare da ruwan sanyi, koda ta shiga ɗaki sai ta tarar da ita a kwance tana bacci, a raunane ta ce "Ayya ta samu bacci ga shi ba ta ci komai ba." Ajiye abincin ta yi ta rufe tare da shigewa toilet.

Duk abin da take yi Salmah na jinta shiru kawai ta yi bata tanka ta ba, don a halin da take ciki bata tunanin zata iya buɗe baki tayi dogon magana.

Readers Also Read