Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 9
Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 9: Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 9. Wanka ta yi sharp sharp ta shirya cikin bakin jallabiya plain bashi da…
3,326 words
Wanka ta yi sharp sharp ta shirya cikin bakin jallabiya plain bashi da adon komai sai dan zip ƙaramin dake kwance a gaban rigar hijjab ta zura ta gabatar da sallah tana idarwa ta dauki abincin da ta zuba wa salmah ta hau tsakura, duk da ba wani daɗin shi take ji ba haka ta shiga turawa kamar wacce aka ce ma ci ko ki mutu.
Ko rabi bata yi ba ta jiyo sallaman Salman a bakin ƙofar ɗakinsu kafin ta kai ga amsawa ya sawo kai , ganintw yasa ya ce "Sister lafiya kuka samfo, me ya faru?."
Ta ce "Wlh salmah ce bata ji daɗi ba, Ashe neman da nake mata ɗazu tana clinic lokacin." Kallon salmah yayi dake kwance kan bed ya ta6e baki tare da cewa "Yau abin ya faɗa kan manya to Allah ya sauwaƙe, naga Ammi bata dawo ba har yanzu kuma naga kamar babu abinci a dining, wallahi mun kwaso yunwa don yau komai banci ba a school, dama mun sa ni wurin mother muka nufa." Ya karashe maganar yana yamutsa fuska tare da shafa ciki, Aysha tace "A Kwai abinci ai, na dafa couscous da muka dawo." Dauke kai yayi tare da jan dan ƙaramin tsaki, kallon shi tayi ta ce "Baza ka ci ba ne?" Ya ce "To ya na iya muje ki zuba ma na mu kore yawa, amma wlh ba wani son abin nan nake yi ba, yzuɓi yake min da ƙuraje" Dakatawa tayi da tauna wanda ta zuba a baki ta dago ta kalle shi "menene haka Salman dan Allah, zaka haramta mana abinci."
" To ai gaskiya na faɗa, na lura ku ƴan gidan nan kuna son wannan abin sosai har da Abie."
Hararar shi Aysha ta yi tare da ajiye plate din da ke hannunta ta yi gaba tana fadin, “ Kai dai ka sani, da iyayinka, wallahi Salman matarkw ta bonu” ya rufo mata baya yana dariya. A falo suka tarad da Suraj yayi balance a kan 3 sitter yana shan iska, jin motsi yasa ya ɗago ya kalli hanyar stairs, ƙur ya ƙura mata ido baya ko ƙeftawa, har suka ƙaraso gaban shi bai sani ba, sai da Salman ya ce "kaiii surajo!."
Firgigit ya juyo ya kalle shi, "Irin wannan kallon shi mai ahlari ya kira nazaratuttuzihi.”
Murmushi Suraj yayi yace "Afwan wlh kamar ce ta 6aci." Har suna haɗa baki wurin cewa "kamar me." Ya ce "kamar Sister Eshart da friend ɗita Maamah da na ke yawan baka labarinta makwafciyarmu ɗin nan, kullum naga Sister Eshart wlh ita nake gani, komai nasu ɗaya bambamcin Kawai jiki siririya ce sosai ita, Sister Eshart ta ɗan fita gwa6i kaɗan, amma wlh kamar an tsaga kara zaka rantse twins ne, kai ko kai da Sweetie da kuke twins baza ku nuna musu kama ba." Salman yace "to Mallam zubairu na ji kullum sai ka dame ni da zancen wata ƙawar ka Maamah amma har yau ka kasan haɗa ni da ita." "Ka ji tsoron Allah friend ranan ba ka ganta ba."
"To ni ina na tsaya kallon fuskarta da daddare ne fa ga duhu." Suraj yace "OK to bari zan haɗa ka da ita anjima idan munje gidan na za ka sha mamaki kuwa."
Aysha dake sauraren su tace "Wai wa ku ke magana a kan ta ne." Salman ne ya amsa mata da "Wai wata makociyarsu ce take mugun kama dake, kamar an tsaga kara." Rass gabanta ya yanke ya faɗi haka Kawai ba tare da tasan dalili ba, zaro manyan idanunta tayi tace " da gaske? aiko dai zan so na ganta yaya sunan ta?" Ta ƙarashe maganar idanunta a kan Suraj alamar shi take tambaya, ya ce "Sunan ta Maamah, Bafulatana ce kyakkyawan kamar ke, ni karan kaina zan so ku haɗu, wlh Sister Eshart idan kika ganta zaki dauka kece, sai kin rasa gane wacce ce ke daga cikin ku." Dariya suka kwashe dashi ita da Salman jin shirmen Suraj wani bin yin abu yake kamar ɗan 5 years ,cikin dariya salman yace "waiii! aiko dai wannan kama ta baci, to ke kinji tsabar kama har zaki rasa tantance wacce ce ke daga cikin ku." kallon su yayi ya ɗan bata rai ya ce " Oh dariya ma na baku ko, to shikenan zan yi kokari na haɗa ku wata rana wlh zaku gane ba wasa nake yi ba, ita ta daɗe ma da sanin labarin ki, don kusan kullum nazo nan na koma sai na mata zancen ki, wlh Eshart har muryar ku iri ɗaya ne, badadan nasan cewa ke Buzuwa ba ce kuma ƙanwar Ammi ce ta haife ki ba da sai nace ku ƴan biyu ne" Murmushi tayi tace "Wlh har naji ta shiga raina, dan Allah idan ka koma kace mata Ina gaisheta." Yace "Aikuwa ina koma wa Estate ta gidan su zan fara biyawa na gaya mata."
Salman ya ce "to munji Mallam Surajo, sis a bamu abinci." harara suraj ya maka masahi jin yana 6ata mai suna a cewar shi, kam ce wa tayi "to acici mala'ikun kauna muje dining."
Bayan tayi serving ɗinsu ɗakin ta koma ta duba salmah tana nan yadda take a kwance kamar yadda ta barta, ji tayi tausayin ta ya kamata ƙarasawa tayi ta miƙa hannunta ta taba goshin ta, babu zafi sosai ajiyar zuciya ta sauke a fili tace "Allah ya baki lafiya ƴar uwa."
Sarai salmah na jinta don kuwa ba barci take yi ba.
Kwanciya tayi a gefen ta , ta lula duniyar tunanin abin da ke gabanta, shiru tayi ta tsurawa ƙaramin fankan Saman dake juyawa da mugun gudu idanu, ta fi minti ashirin a haka kafin ta sauke wani irin nannauyan ajiyar zuciya mai haɗe da huci na zallar bacin rai , a fili cikin kaushin murya ta furta "Babangida! Babangida!! Babangida!!! hmmmmm kaci gaba da 6oyewa kada ka kuskura nayi ido biyu da kai, domin daga ranar da ka ganni na ganka kayi ban kwana da farin ciki a duniya indai har na haifu cikin Inna da Baffa." Ta na maganar nan cike da kawarin gwuiwa da tsantar alwashi.
Da sauri salmah dake sauraren ta ta juyar kai gefe hawaye na ziraro mata, cikin azama ta kai hannu ta goge ɗon bata fatan Aysha ta ganshi a fuskarta, motsin juyawar salmah yasa ta juyo da sauri a kalleta, don a zatonta ta farka ne ganin ba farkawa tayi ba gyara kwanciya tayi yasa ta saki ajiyar zuciya, tare da gyara nata kwanciyar ita ma.
Koda suka kammala cin abincin nan suka bar plate ɗin suka kakka6e duwawunsu suka fice , motar Ammi suka shiga da yake key na hannun Salman, shi ke kai su school da ya dawo take kar6an key sai kuma gobe, ganin bata nan bare ta amshe key ɗin yasa suke Allah Allah su bar gidan kafin ta dawo, sai da suka hau kan titi Suraj dake driving ya kalli Salman ya ce, “ Ina jin kamar na yi mantuwa a gidan Ammi fa.” “ Ya Salam! Me ka bari, Allah yasa ba mai muhimmanci ba ne, don ba zan koma ba kar mu yi kicibis da Ammi.” Salman ya fadi cikin ɗan damuwa. Dauke kai Suraj ya yi ya mayar kan hanya kafin ya ce, “ Zuciyata, na baro friend, Salmah Zuciyata ce yau throughout ban ganta ba, i have missed her terribly ji nake kamar na shekara ban ganta ba“ Wani dogon tsaki ne ya kufcewa Salman, takaicin Suraj ya hanasa magana sai kawai ya shiga watsa masa wani kallo, irin na rasa abin fadan nan. Dariya Suraj ya tuntsire dashi, sai kuma ya yi gyaran murya, da deef voice dinsa mai daɗin sauraro ya fara rera waka cikin wani salo irin ta makawakar zamani mai daukar hankali
{Salmah ke ce hasken idona, Ko a duhu ina ganinki a raina, Tun kafin na fahimci kaina, Na tsinci zuciyata a hannunki ba tare da izini ba, Ban san lokacin da na kamu ba, Sai na tsinci raina yana kiranki a kowane lokaci, Ko duniya ta juya mini baya, Zan tsaya a gefenki ba gudu ba ja da baya, Ko an ce min soyayya kuskure ce, Ni kam zan zaɓe ki fiye da sau ɗari a rayuwata, Idan soyayya laifi ne, To ni na yarda a hukunta ni saboda ke, Salmahtah…..}
Duk da yanayin da Salman yake ciki sai da wakar ta dake shi, sosai ta yi dadi da ma'ana, ga kari irinta kwarewa da baiwa tsantsa da aka yi mata, da murya da ta samu mai daɗin amo, amma don dai kawai ya nuna Suraj baya tare shi, sai ya taɓe baki kawai ya kawar da kai, dariya Suraj ya sake yi, ya ce “ Sai da kai surukina abokina, Allah ya nuna min ranar da za ka fita daga cikin yan adawata, ranar da za ka damka min Salmahtah da hannuwanka. Yanzu dai ina muka nufa?" Maganarsa ta karshe yasa Salman kallonsa kadan kafin ya ce "Mu je wajen Mother mu ci abinci, dan wlh ban ƙoshi ba tsatstsakura kawai na yi don ba wani iya cin couscous na yi ba." "Ok sai dai mu faka motar Ammi a gidan su Maamah don kasan mother sarai ƙaniyar mu zata ci idan ta ganmu da motar nan." Salman ya ce "su iyayen Maamah ba za su faɗa mata ba?" "Baza su fada ba, ai sun saba da rigimata."
Tun kafin su ƙarasa bakin get ɗin shiga kangiwa Estate su ka fara cin karo da mutane tsaitsaye, yan kabu kabu, da ƴan napep, wasu a ƙafa wasu ma a mota, da alama an hana su shiga ciki ne don ga get ɗin wajen nan a garƙame Salman ne ya fara lura da da sauri ya juyo ya kalli Suraj yace "friend what is going on here." Sai lokacin Suraj ya kula, wani irin zaro ido yayi cikin zaƙuwa ya ce "big bruh!" Salman yace "kai I don't understand meye big bruh." Dai dai lokacin suka isa bakin get horn suka yi, sai da sojojin dake gadin bakin get ɗin wajen suka leƙa ganin Suraj yasa aka buɗe musu get ba tare da bata lokaci ba, tun da suka shigo cikin wajen zargin Suraj ya ƙara tabbata, cikin maɗaukakin farin ciki ya ce "Salmah Ya Ahmad." Salman cikin rasahin fahimta yace "waye Ya Ahmad?" Suraj da duk ya ruɗe Ya ce "Ya B" Tsaki Salman yaja ya ce "kaiii dallah nutsu kamin bayani ka na ta ƙara saka ni a kwana wanene Ahmad wanene kuma Ya B?" Sai lokacin Suraj ya tuna Salman fa bai san shi da haka ba, da sauri ya ce "oh sorry friend , Mr Ahmad Idris Ahmad kangiwa nak e nufi." Zaro ido Salman yayi ya ce "A ina?".......
PLS AYI COMMENT KO BABU YAWA😅
Oum Ummeetarh ce😍
09116099486 [5/14, 6:00 AM] Oum khadeejarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀
By
AyshaNalado
Page 12
Ta daɗe tana tunane tunane kwance kusa da salmah da duk a tsammaninta barci take yi, bata san sanda barci ɓarowa ya kwashe ta ba, jin saukar nunfashinta yasa Salmah mikewa zaune, ta tankwashe ƙafa tayi a tsakiyar bed din tare da rafka uban tagumi da hannun bibbiyu.
Bata san iya adadin lokacin data kwashe a haka ba, ba komai take yi ba sai tufka da warwara a karshen dai ta tsaida matsaya ɗaya wanda take ganin shine daidai ta tabbata za su yi babbar asara, amma ba komai wani hanin ga Allah baiwa ne, za ta yi komai domin ganin farin cikin A'ishatu a duniya ciki harda sadaukar da nata farin cikin.
Ƙarar shigowar message wayarta ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula da sauri ta buɗe saƙon, kamar ɗazu lamba ce babu suna, tana gama karantawa ta saki kayatatcen murmushi, juyawa ta yi ta kalli Aysha dake barci sai haɗa uban gumi take duk da gudun fankar da suka ƙure, kallo ɗaya ta mata ta san barcin bana dadi bane Kawai fin karfin ta yayi ya kwashe ta ba da son ranta ba, wayarta ta saita a daidai fuskarta ta dauke ta hoto kala biyu, juyawa ta yi kan wayarya ta yi ɗab danne danne na kamar minti uku kafin ta kife wayar ta mike ta shige toilet.
Ruwa ta sake watsa wa tare da yin alwala ta fito daure da tawel, sharp sharp ta shirya cikin dogon rigar materiya mara nauyi saboda yanayin da suke ciki na shigowar zafi gadan gadan, sallar la'asar ta gabatar, wanda tuni masallatai sun idar, har ta idar Aysha bata motsa ba, sai da ta gama addu'o'inta, ta shafa, sannan ta matsa kusa da ita a hankali ta shiga tashin ta ta hanyar kiran sunan ta ƙasa ƙasa tana ɗan bubbuga kafar ta.
Bata kasance mai nauyin barci ba hakan yasa kira biyu tayi firgigit ta bude idanu a firgice tana karanto *A'uzu bi kallimatil lahi, tammat min sharri ma kalaƙa* ganin Salmah a gabanta tana sakar mata kayataccen murmushi mai dauke da manufofi kala kala, ya matukar bata mamaki, a hankali tace "Salmah kin tashi ne ya jikin naki?"
"Da sauƙi sosai alhmdllh na ji dama, na farka tun ɗazu har na gabatar da sallar la'asar."
"Alhmdllh Allah ya ƙara sauki."Aysha ta faɗa ntana ƙoƙarin sakkowa daga kan bed ɗin, har ta miƙe tsaye ta fusakanci haryar toilet ta ji Salmah ta ri'ko hannunta jutowa tayi ta kalleta, murmushi Salmah ta sakar mata tare da cewa "Meke faruwa naga kamar baki cikin kwanciyar hankali."
"Mafarki nayi Salmah me firgitarwa, da ace abin da na gani a mafarkina na yau zai zama gaskiya da babu makawa sai na saka wuka na farke cikina, domin babu amfani rayuwa a gareni."
"A'uzubillah minash shaidanir rajim." Salmah ta fad'a cikin zaro ido. Hannun tasa ta ɓamɓare hannunta daga riƙon da Salmah ta mata jiki a sanyaye ta shige toilet.
Hankalin Salmah ba ƙaramin tashi ya yi ba da jin kalaman A'ishatu, ta sha jin tana furta kalamai makamantan wannan a lokuta mabanbanta, amma basu taɓa tashin hankalinta kamar yadda wannan ya tashi hankalinta ba, a da bata san wacece A'ishatu ba kuma bata san wanene Babangida ba shiyasa bata damuwa da kalamanta masu shige da zaurence, amma a yanzu da ta riga tasan komai baza ta juri jin makanatan su na fitowa daga bakinta ba, duk da bata tambaye ta ba tasan ba zai wuce mafarkin Babangida ta yi ba.
Wuri ta ne ma ta zauna a toilet ɗin, ta yi shiru ta zurawa waje guda ido, mafarkin da ta yi yanzu na sake dawo mata filla filla a kwkwalwa, rintse ido tayi lokacin da take hango shi rungume da ƙugunta, idanuwansu cikin na juna, a hankali ya dinga matso da kyakkyawar fuskarsa gare ta har ya yi nasarar hade bakunansu waje guda ya fara sakar mata wani irin al'amari mai kama ƙwaƙwalwa, abin da yafi bata takaici da ba'kin ciki yadda take mayar masa da martani cike da shauƙin soyayya.
Fashewa tayi da kuka mai cin rai, cikin murya kasa kasa yadda tasan Salmah baza ta jiyo ta ba, ta ce "Ya Rabbi na roƙe ka kada ka sake muna min makamancin wannan mummunar al'amarin, wanda ganin ranar mutuwata ta fi shi sauki a gareni."
Tafi minti 30 a zaune a cikin toilet ɗin, kafin ta miƙe da kyar ta watsa ruwan sanyi tare da dauro alwala ta fito.
Koda ta fito Salmah bata ɗakin hakan ya mata daidsi don dama tana shakkar tsareta da tambayoyi da salmah za ta yi, shiryawa ta yi ita ma cikin riga da wando marasa nauri sakakku ne sun mata kyau sosai, hoda da kwalli ta shafa duk a kokarinta na kar Salmah ta gane ta yi kuka, wanda tuni bata san aikin gama ya riga ya gama ba domin harta addu'ar da ta yi duk a kunnen Salmah.
Tana cikin sallah, Salmah ta turo kofar ta shigo ganin bata idar ba yasa ta zauna a bakin bed ta jira ta, tana sallamewa ta kalleta, already dama ita idanunta na kanta, ido cikin ido suka kalli juna kowacce zuciyarta da abin da take saƙa mata, Salmah ce tace "Allah ya karɓa.“ da amin ta amsa mata, ta sake cewa "Ammi ta dawo tana kiraki." Cikin ɗan mamaki tace "Ammi ta dawo fa kika ce?" Gyada mata kai Kawai ta yi, "Amma dai ba da moto ta dawo ba ko?" Salmah tace "kamar yaya?"
"Naga ko karan bude get ban ji ba ne balle dirar motar ta." Ta6e baki Salmah tayi tareda watsa mata wani kallo tace "Ta yaya zaki ji diran motarta bayan kin shige toilet kin rufe kina kuka." Shiru tayi ta rasa me za ta ce, sai kawai ta tasttsarreta da idanu, ganin haka yasa Salmah mikewa ta yi ficewarta.
Sai da ta yi yan addu'o'inta ta shafa, ta kwashe daddumar sannan ta dauki siririn gyalen kayan jikinta ta yafa, ta bi bayan salmah, basa falo hakan yasa ta nufi bed room din Ammi kai tsaye, sallama ta yi a tare duka amsa mata, tana shiga gaban Ammi ta zarce ta risina tare da cewa "barka da dawowa Ammi." Murmushi Ammi ta saki tare da amsa mata da "barka kadai A'ishatu." Ita ma murmushi tayi tare da cewa "ya aiki ya zafi."
"Lafiya kalau Aisha ya makaranta. " tace "Alhmdllh."
"Salmah ta gaya min kun dawo ba tare da an tashi, shiyasa nace ta kiramin ke, a kul! kar ku sake yin haka, idan d'aya baiji dad'i ba d'aya ya tsaya yayi karatun shi kunji ko." Har suna hada baki wurin cewa "to Ammi."
Ammi tace "Salman bai dawo ba ko." Ta fad'a tana kallon A'ishatu don already ta riga ta tambayi Salmah tace mata bata sani ba ita tana barci, Aisha tace "ya dawo sun zo tare da Suraj har na basu abinci,to na shiga daki barci ya kwashe ni ban san sanda suka fice ba." Kwafa Ammi tayi ta ce "zai dawo ya same ni daga shi har surajon ba motata ta zama ta tsarar wasan su ba, A'ishatu kuje a daura sanwa tuwon shinkafa za'a yi miyar ogun, kuje ku fara zan zo na same ku Salmah ki yanka Ogun ki nika kayan miya,ke kuma Aisha ki daura tukunyan tuwo ki wanke shinkafa ki zuba ki dibi naman rago ki tafasa, kafin nazo."
Bayan sun fice toilet Ammi ta shige ruwa ta watsa ta fito ta kimtsa cikin dogon rigar atamfa duk da bata shafa ko mai ba saboda zafi sai da ta balbale jikinta da tsadaddun turarakan ta Ammi akwai son kamshi kasancewarta haifafaiyar Maiduguri kanuri ce gaba da baya, hula ta saka mai kyau wanda ya shiga da atamfar jikin ta fito tana baza kamshi ta nufi kitchen.
Ta tarad duk sun maida hankali akan aiyukan data saka su, duba wa tayi taga sunyi komai yadda ta umarta, kujera ta ja ta zauna a kitchen tana basu umarni suna yi sai dai fa cikin taka tsantsan dan Ammi ko kadan ba son kazanta, kuskure kad'an wanda su suna ganin shi ba komai bane zata fara musu fad'a, tana cewa bata son kazanta haushi kuwa duk ya cika Salmah don anfi samun matsala da ita a haka har suka kammala lafiyayen tuwan farin shinkafa miyar Ogun da agushi da yaji naman rago da stock fish ga ganda, ba tare da ta saka musu hannu ba, sai da suka jera komai a dinning sannan ta umarce su da suje su su watsa ruwa suyi sallah, cikin dan kasa² da murya Salmah tace "Ammin nan wlh tsabtan ta ya wuce misali minti daya biyu tace ayi wanka sai kace wasu kifaye wlh ni ba wankan da zanyi." Ammi da bata jita sosai ba tace "me kika ce?" A'ishatu ne da taji komai rass ta bud'e baki zata yi magana, da sauri Salmah ta kai hannu ta rufe mata baki tare da cewa "cewa nayi Amminmu mutuniyar kirkice sosai ga tausayi." Da ji ma tasan karya take yi hararanta ta yi tace "kuje Allah ya shirye ki, ban iyawa da jidalinki Salmah." Dariya suka saka kafin su fice daga kitchen ɗin.
******************