Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 10
Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 10: Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 10. Tafe yake a motar shi kaɗai yana driving sai sharara gudu yake yi a…
3,345 words
Tafe yake a motar shi kaɗai yana driving sai sharara gudu yake yi a hanya, Allah Allah yake ya isa gida domin bakin shi cike yake da labarai kala kala , sai gyada kai yake yi yana sakin murmushi kamar sabon gaula, can kuma kamar an tsikare shi ya ce "kaiii! Mutumin nan duniya ne wlh, Allah ya tara mai baiwa alkur'an ina ma nine Suraj wai da anga fankama da iyayi." Haka yai ta sambatu shi kadai kamar sabon kamu, yana isowa layin su ana tada sallar isha'i a masallacin bakin layin, fakin yayi ya fito don gudun rasa jam'i bayan an idar ya fito, ya 'karasa gida, yana isa bakin get motar Abie na 'karasowa, kusan a tare sukai parking, da sauri ya isa wajen Abie yana mishi sannu da dawowa, ya kar6i jakar shi da ledodin dake hannunshi, tambayar shi Abie yayi daga ina yake, kasancewar yasan ba'a ma Abie karya yasa direct ya gaya mishi daga gidan su Suraj, Abie yace "Waya aike ka." Yace "babu kowa." Ba zato yaji saukar rankwashi a kokon kanshi, "washhh!" Yace tare da dafe wajen "ban hanaka kaiwa dare a waje ba." "Kayi hakuri Abie wlh 'kwa'kwaran uzurine ya tsare ni bansan dare yayi ba sai jin kiran sallah magariba mukayi."
Abie yace "OK to da kyau, itama Ammin ku na hanata ta baka mota indai ba school zaku ba taki ji." Jin Abie ya ambaci Ammi da mota sai da hantar cikin shi ta kad'a, shi sai yanzu ma ya tuno da abin da ke gaban shi, bai ankara ba tuni Abie ya kusa shigewa ciki da gudu ya rufa mai baya.
Falon babu kowa duk suna ciki, Allah Allah yake Abie ya amshi kayan shi ya samu ya je dakin su Salmah ya fesa shafa musu labari.
Har d'aki ya raka Abie gaban shi na fad'uwa kar yayi kicibus da Ammi aiko dai bata ciki, da sauri ya ajiye kayan hannun shi tun kan Abie ya kai ga amsa, don yasan yana kara kwakwkwaran mintuna biyu Ammi zata shigo d'akin, aiko dai cikin rashin sa'a yana fitowa sukayi kicibus, rass gaban shi ya yanke fadi, idanun su na haduwa yayi kasa da kai, bai san karasowarta ba sai ji yayi ta kama kunnenshi d'aya ta murd'a "Auww wayyo Allahnahhhh Ammi!" Tace "kunnnen kashin nan yau sai na tsinke shi." "Dan Allah kiyi hakuri Ammi." Ya fada yana mi'ka mata key,sai da ta amsa da daya hannunta sannan ta sake mishi kunne tare da bashi kyakkyawan rankwashi dafe kai yayi yana sosa wajen, da sauri ya fice, shigewa dakin Abie tana surutu akan kunnen 'kashi irin na Salman.
Direct dakin su ya dosa, da sallamar shi a baki ya shiga dakin, Salmah na kwance tana karatun novel ɗin nata na fama, Aysha na zaune kan rug a tsakar dakin ta barbaza takardu da alama wani abu take nema.
Yana shigowa duk suka tsaya da abin da suke yi suka d'ago suna kallon shi, fuskar shi cike da mad'aukakin fara'a yace "bebs albishirin ku." Har suna had'a baki gurin cewa goro tuni salmah ta mi'ke zaune, tana kallon shi, ya ce "yau nayi hand to hand da Mr Ahmad Idris Ahmad kangiwa." Gaba ki d'ayan su sai da gabansu ya yanke ya fadi, kusan a tare suka furta “ Are you serious......... [5/14, 6:00 AM] Oum khadeejarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀
By
AyshaNalado
Page 13
Kamar saukar aradu haka kalaman salman suka daki zuciyarta,cikin matsanancin bugawar zuciya ta zare manyan idanunta tare da watsa su a kan shi, bai kula da yanayin da ta shiga ba sai ma ƙarasowa cikin ɗakin da yayi ya nemi bakin gado ya kai zaune, cike da zumuɗi ya gyada kai tare da ce wa " Hmmm! yau naga abin mamaki da al'ajabi, gaskiya ba banza ba mutane ke haukacewa da son ganin bawan Allah nan, Innalillahi! wlh ya haɗu ta ko ina ne guy ɗin nan kaiii! miskiline na ƙarshen ƙarshe, ban ta6a ganin mutumin da murmushi ke bala'in yi mishi kyau kamar shi ba, kamshin turarensa kawai ya isa ya shaida maku shi na musamman ne, kyawun shi mai firgitarwa ne, takun shi abin kallo ne wallahi kamar wani basaraken bijimin zaki a dokar daji ,dole ka mata su haukace a kan shi, don ba su kadai ba hatta maza shagala suke da kallon sa."
Tun da Salman ya fara zubo bayanai, bakinsa ta tsurawa idanu tana kallo, babu abin da zuciyarta ke yi sai luguden daka, so take ta buɗe baki ta tambaye shi a ina ya ganshi amma ta kasa.
Salmah da take jin zancen Salman kamar wani almara ko tasuniyar gizo ne ta ce "You are not serious, mu zaka rainawa hankali, a ina ka ganshi da har ka mishi irin wannan sanin a gani na farko, ka kuwa san wa ka ke cewa ka gani, Mr AA kangiwa fa, haba haba dai in mafaɗin magana wawa ne ai mu majiyan ta ba wawaye bane kai dai barshi Kawai a kaji ana bada labari ka kwaso ka gaya mana, Mr AA kangiwa ya wuce duk yadda kake tunani."
Harara ya ɓalla mata tare da jan guntun tsaki "Tsiyata dake shegen kankanba aure bashi, ke da ko fuskar shi baki taba gani da kyau ba kike wani maganar banza, abin da baki sani ba sai ki ringa wani zaƙewa a kai, to bari na miki mai kankat, Mr AA kangiwa yayan Suraj ne, da mahaifin shi Gen. Idris kangiwa da Mother uwarsu ɗaya ubansu ɗaya." Ba Salmah da Aysha ba hatta Ammi dake rike da handle din kofar sai da abin ya dakar mata zuciya, kusan suman zaune Aysha ta yi wanda dama tunda Salman ya fara bayani ta nemi inda kanta yake ta rasa, a ranta sai maimaita sunan Suraj ta ke yi.
Ci gaba Salman yayi da cewa "ko ni kaina na shiga shock din da yafi wanda ku ka shiga, da farko na dauka karya ce sai da idanu na suka gane min shi ra'ayil aini a cikin gidan suna zaune a kujera daya shida mother, tana bashi damammiyar fura a baki, ba ku ga yadda Suraj ya ɗane jikin shi ba da sunan yana mai oyoyo ba, wlh kai na kwancewa yayi, mother da kanta ta gabatar dani a gurin shi da ya dago ya zuba min idanun shi kadan ya rage na saki futsari kwarjini gareshi kamar zaki, kallon 20 seconds ya min sai kuma na ga ya saki wani irin kayataccen murmushi na gefen baki wanda ya kusa tafiya da imani na, ya miƙo min hannu, alamar na zo, kamar mara laka haka karasa na bashi hannu, baku jo taushin tafukan hannunshi ba kamar auduga ban san sanda na lumshe ido ba, uwa uba kuma ga dadɗan kamshin shi daya cika falon, kusan suman tsaye na yi ba zato na tsinci maganarsa a kunne da husky voice ɗin shi ya ce “Salman Right? ai ba shiri na ware idanuna Suraj kuwa sai dariya yake min baku ga yadda ya ringa mai shagwaba ba wallahi lamarin ya tashi kaina."
A mamakance salmah tace "Dakata, Salman, wai wani Suraj din ma tukunna?”
"Suraj dai da kika sani." "kai I swear ban yarda ba." "Wlh tallahi da gaske ne in kin musa bari ma kiga hoton su a tare." Ya fada yana lalubar wayar sa a aljihu.
Hotunansa daya turo a wayar Suraj din ya shiga nuna mata, wani shi kadai wani shida Suraj da wasu da ba ta sani ba wani shida Mother ga dai hotunan barkatai sun fi ashirin, shi da familin shi makusanta, Wawan ajiyar zuciya ta sauke, a ranta ta ce “Tabbas shine.“ A zahiri kuwa cewa ta yi "To ya akai duk shakuwar ka da Suraj baka taba sani ba." Yace "bar dan rainin hankali wai shi bai gaya min bane saboda kar nace ba zan yi abota da shi ba." Wani hoto ta tsurawa ido da yafi daukar hankalinta, shi ne da wata mata da wani dottijon mutumi mai tsananin kama dashi sai kuma wata yarinya wacce take kama da matar sosai kamar an tsaga kara, kallon sani take ma fuskar yarinyar amma ta rasa a in da ta ta6a ganinta, kafin ta kai ga tambayar salman, Ammi ta shigo ɗakin bakin ta dauke da sallama, fisge wayar shi yayi a hannun Salmah yana gyara zama, bai ji daɗin shigowar Ammi ba don bai kai ga gaya musu abin da yake zumuɗin gaya musu ba.
Shigowar Ammi ne ya dawo da Aysha daga suman wucin gadin da tayi don ko batun hotuna da Salmah ke kallo bata san suna yi ba gaba daya tunanin ta ya tafi wani waje can dabam.
Kallon su daya bayan daya Ammi tayi har ta bude baki da niyyar yin magana akan abin da taji yanzu sai kuma ta fasa, bai kamata tayi magana a gaban su Salmah ba, zata bari sai sun ke6e da Salman din, canza akalar zancen ta tayi da ba su umarnin fitowa su yi dinner, Daga haka ta juya abinta zuciyarta cike da al'ajabin wannan lamari, bata karyata shi kuma bata yarda sosai ba, amma ta yanke shawaran zata tambayi Abie tasan idan ma hakan ne shi bazai rasa sani ba.
A dining suka tarad da Ammi da Abie , kujera suka ja suka zazzauna Ammi da kanta tayi serving din kowa, cike da nishaɗi Salman ke cin tuwan shi sai murmushi yake yi, albishir yake so yama Ammi da Abie akan gagarumar kyautar da Mr AA kangiwa ya basu shida Suraj amma tsoro ya hana shi, bai san yaya zasu karbi lamarin ba.
Salmah kam al'ajabi ne ya hanata sakin jiki ta ci abinci da kyau, kanta ya ƙulle tamau, yayin da Aysha rashin kwanciyar hankali da faduwar gaba ya hanata cin abinci, tsab Abie ke kallonsu yana lura da takun kowa, akan Salman ya tsaida idanunshi, yana kare mai kallo can yace "Salman lafiya dai wannan irin fara'a kamar wanda aka ba kyautar mota." Rass gaban shi ya yanke ya fadi, a tsorace ya dago ya kalli Abie can kuma ko me ya tuna sai ya saki murmushi yana ɗan sosa kewa, murmushi Abie yayi yace "to naga fara'ar ce taki karewa, nasan dai kyuatar mota kawai za'a maka ka ringa irin wannan farin cikin haka."
Rasa abin cewa yasa ya kyalkyale da dariya, duk dagowa sukayi suna kallon shi, Abie ya ce "tofahh!" Yana rike haɓa.
"Abie yau ji nake kamar an min albishir da Aljannah, Abie kasan wani abu wai Ashe Suraj kanin Mr AA kangiwa ne." Zaro ido Abie yayi cike da mamaki yace "wane Suraj din."
"Suraj abokina, yau da na je gidan su na ganshi har..." Sai kuma yayi shiru, Abie yace "ikon Allah, amma kuma ni ban san yana da ƙane namiji ba."
"Ba Maman su daya ba, Maman Suraj ita ce kanwar Gen Idris kangiwa." Abie yece "ikon Allah Ashe surajo dan gida ne, rashin sani yafi dare duhu."
A haka suka ci gaba da cin abincin Salman na ta basu labarin, makudan kudaɗen da ya bayar a rabawa mutanen dake tsatsaiye suna jiran fitowar shi abin sai da ya basu mamaki baki daya kudi ne bana wasa ba, murmushi Abie yayi ganin yadda duk suka rude ya ce "to ai hakan ba komai bane a gurin shi, don ya dauki irin wadannan makudan kudin ya ba mutum daya kyautar su karamin abu ne a gare shi daga shi har mahaifin shi haka suke shi yasa ko cikin yan siyasaa suka fita dabam." Ammi tace "hmmmm lallai kuwa Allah ya basu."
Kallon salmah , Salman yayi yace "yawwa sister ina tambayar da kika ma Abie shekaran jiya."
Duk i zuba mai ido duk su ka yi, ya ci gaba da cewa, “ Da gaske fa kamar yarinyar nan ta fiki gaskiya, domin da kunne na na ji Suraj ya kira sa da Yaya B, kuma ya amsa, ni sai yanzu ma abin ke dawo min, ina da tabbacin Yaya Babangida ya ke nufi.” Ya karshe maganar cike da confidence.
Zaro idanu Salmah ta yi gabanta na wani irin faduwa, ta ce "ka rantse da Allah."
"Bangane na rantse da Allah ba." Yana aika mata harara, sai lokacin ta gane ɓaram ɓaramar da ta ku sa yi, cikin pretending ta kalli Aysha ta ce " Lol! Kin ji ko Sister shikenan Sahla Balarabe ta yi winning ɗina dama bet muka kulla." Ta karshe maganar tana yar dariya.
Kallonta Abie yayi ya saki guntun murmushi tare da dauke kai.
A'ishatu kam tunda ta ji abin da Salman ya fada, ta daina fahimtar komai, tuni kanta ya fara juyawa ta rasa a sama take ko kasa, har suka kammala cin abincin bata san me suke cewa ba.
Abie ne ya fara barin dining din, Ammi tabi bayan shi. Ajiyar zuciya salmah ta sauke kamar kazar da aka ɗagawa wuka a maƙogaro, Dama Allah Allah ta dinga yi su tashi don tun dazu ta lura da yadda gaba daya Aysha ta fice daga hayyacinta, tsoro ta ringa ji kar tai wani abin da zai jawo musu zargi, ganin sun shige yasa ya tashi da sauri ta kimtsa dining din, ba tare da ta kula salman dake ta yi mata surutu ba ta kama hannun Aysha ta mikar da ita, ba musu ta bi ta, kamar wata sakarai, dakin su ta nufa da ita suna shiga ta maida kofar ta rufe tare da murza key.
Kallon juna suka yi, cikin rawar murya ta ce "Salmah kin ji ko a she shine Babangida,dama ni zuciyata ta bani, cewa shine, Salmah ki dubi yadda yake rayuwa cikin kwanciyar hankali cike da ɗumbin nasarori bayan ya tarwatsa nawa farin cikin." Tana gama faɗin haka na ta fashe da wani irin kuma mai ban tausayi, da saurin Salmah tafaɗa jikinta ta rungume ta tana bubbuga mata baya alamar rarrashi.
Kuka ta yi sosai, ba tare da ta kula da rarrshin da Salmah ke mata ba, ji take a lokacin zuciyar a lokacin kamar zata faso kirji ta fito, babu abin da take yi sai iza mata wutar ɗaukar fansa, a hankali ta tsagaita da kukan da take, shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya, ta dau tsawon lokaci a haka kafin ta dago ta watsa Salman runanun idanunta, ta daure fuska tamau babu alamar fara'a ko dariya a kausashe ta ce " ki zama shaida yar uwata Salmah, wannan hawayen dana zubar, shine na karshe da zan zubar akan Babangida, ada na dauki alwashin a duk sanda na hadu da shi, baza mu rabu ba saina dauki ranshi da hannuna, but a yanzu na canja shawara, bazan kashe shi ba saina bari ya ɗanɗani bakin cikin duniya, sai na fallasawa duniya cewa shi ɗin mugun ne mara imani mara tausayi mai tarwatsa farin cikin wasu domin gina nasa butulu ne shi wanda yake saka alkhairi da sharri, a karshe kuma sai ya girbi abinda ya shuka da hannunwansa."
Da sauri salmah da tunda Aysha ta fara magana jikinta ke rawa zufa na karyo mata, ta kai hannu ta dafe bakin ta,cikin tsananin tashin hankali tace "baki da hankali wai A'ishatu, wannan wace irin magana ce haka, wani irin zuciya ne a kirjin ki haba sai kace ba musulma ba, Shin kina da cikakken tabbacin B din Babangida yake nufi kamar yadda Salman ya faɗa, ki bari mu bi komai a sannu fa Aysha kar mu yi gaggawa."
Buge hannunta Aysha ta yi kafin a fusace ta ce "Shin dama kin nemi dana baki labarina domin ki karya min gwuiwa ne Salmah?"
Da sauri Salmah ta girgiza kai, ta sake cewa "Shin bake ki ka ce zaki taya ni na dauki fansa akan Babangida?" Sake girgiza kai Salmah ta yi, Alamar E , "To me ya canza mini ra'ayi?" Ta fada cikin tsattsare ta za rinannun idanunta. Shiru Salmah ta yi ta kasa amsa yayinda Zuciyata ke wani irin bugu na wuce misali, girgiza kai Aysha ta yi bayan ta dauke kai daga kallon Salmah, ta ci gaba da cewa, “ A tunani na sai kin fini daukar zafi idan gaskiya ta yi halinta, Amma abin mamaki sai gashi kina neman tankwarar da ni.“
"Ba canza ra'ayi na yi ba A'ishatu ina nan akan bakata zan taya ki zan taimaka miki har sai kin dauki fansa akan shi, amma dan Allah da manzonsa ki daina cewa zaki kashe shi da hannunki, bana son ji yana tada min hankali,insha Allah baza ki taba zama silar rasa rayuwar wani ba."
Murmushi takaici da bakin ciki ta sake tare da dafa kafadar har ta bude baki za ta yi magana sai kuma tayi shiru, da sauri ta juya ta fada kan bed tare da kife kanta tana sakin wani irin nurfarfshi.
Juyawa salmah tayi da sauri ta bar dakin hankalinta a tashe kitchen ta nufa ta bude kofar kitchen ɗin wanda idan mutum ya biyo zai fitar dashi backyard din gida. bata kula da rashin takalmin dake kafar ta ta ringa zuba sauri, sai da ta tabbatar tayi nisa da asalin part din su, sannan ta ciro wayar ta, Yaya Anas shine lambar data laluba hannunta na rawa, babu bata lokaci ta danna mishi kira, ringing biyu ya ɗaga.......
Kuna fahimta ko dai har yanzu kan ku ƙara murfi yake😅 [5/14, 6:00 AM] Oum khadeejarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀
By
AyshaNalado
Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍
BOOK 1
Page 14
Kusan 20 minute Salmah ta kwashe tana waya, kakkarfar ajiyar zuciya ta sauke, tana jin zuciyarta sam babu daɗi, jiki a sanyaye ta juya ta kama tafiya a hankali kamar mai tausayin ƙasa, ta koma ciki ta hanyar data fito. Tana isowa tsakiyar main falo, ba zato ta tsinkayi muryar Abie “Daga ina ki ke?" A tsorace ta juyo ta kalle shi , bata taɓa zato ko tsammanin da mutum a falon fa, cikin inda inda tace "Ab, Abie na amsa call ne." Cike da mamaki yace "Call! Call ɗin wa?" Ya jeho mata tambaya, da sauri tace "call ɗin yaya Anas." Tsare ta da idanu yayi yana kallonta duk alamar rashin gaskiya ya bayyana ƙarara a fuskar ta. Miƙa mata hannu ya yi tare da cewa "Mu ga wayar." miƙa misa ta yi zuciyar ta na bugawa, danne danne ya yi na ƴan sakanni sannan ya miƙa mata, hannu biyu tasa ta kar6a ya ce "you can go."
Da sauri tabar falon har tana haɗawa da gudu gudu, da kallo Abie ya bi ta har ta ƙule ma ganinsa, kafin ya girgiza kai yayi cike da nazari, a fili yace tabbas yaran nan akwai abin da suke ɓoyewa kamar yadda aka sanar masa, kuma ya zama dole ya na ƙara sanya idonu a kansu.
Jingina ta yi da ƙofar ɗakin na su bayan ta shiga ta maida ƙofar ta rufe, ajiyar zuciya ta shiga saukewa, a gefe guda kuma abinda suka tattauna da yayan nata na sake dawo mata filla filla a kwakwalwarta, sai da ta ɗan samu nutsuwa sannan idanunta ya sauka akan Aishatu, a yadda ta bar ta haka ta same ta a kwance sai dai yanzu ta yi lamo kamar tana bacci, sa6anin ɗazu da take ta sauke nunfashi, duk da haka a kallo ɗaya ta gane baccin ƙarya ne.
Bata ce mata komai ba sai ma toilet data shige ta watsa ruwa ta fito shiryawa tayi cikin kayan baccin ta, ta kashe musu light tta haye kan bed ta kwanta a gefen ta.
Gaba ɗaya ranar basu samu bacci kirki ba, duk shiru suka yi kowacce na tukwa da warwara, kowacce da abinda take saƙawa da kwancewa, ba tare da ɗaya tasan ɗaya na farke ba, Salmah ce ta fara yin barci bayan ta gama tsaida matsaya ɗaya, yayin da A'isha sai da ta raba dare sannan bacci 6arawo ya kwashe ta.
Koda suka tashi ba su yi wannan maganar ba, normally suka gudanar da ayyukan su na yau da kullum, bayan sun yi breakfast, ɗaki suka dawo domin yin shirin makaranta, Aysha bata da lecture sai dai akwai assignment mai mahinmanci da za ta yi submitting Karfe takwas da rabi yayinda salmah ke da lecture ƙarfe tara.