Kenza eBookz

Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 11

Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 11

Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 11: Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 11. Koda suka shigo ɗaki kwanciya A'isha tayi kanta na ɗan Sara mata saboda…

3,327 words

Koda suka shigo ɗaki kwanciya A'isha tayi kanta na ɗan Sara mata saboda barcin da bata samu sosai jiya ba, kallon ta salmah tayi,ba dai ta tanka ba ta shige toilet.

Koda ta fito still tana nan a yadda ta barta bama ta da niyyar tashi, har ta gama shirin ta cikin riga da skirt na atamfa ta kuma 6ata lokaci tana shafe shafen ta kasancewar gwanar kwallaya, A'isha bata motsa ba, sunan ta ta kira "Aysha ki tashi ki yi wanka mana tym na going fa."

Ba tare da ta ɗago ba tace "bana jin zan iya shiga school yau, amma dan Allah zan baki Assignment ɗina kiyi mini submitting." Salmah tace "saboda me ye baza kije ki kai da kanki ba, bakya tsoron a samu matsala kin san dai Sir Bala bahagon mutum ne."

" Babu wata matsala Class Captain yace mu ba, shi za ki nema ki ba amma dan Allah ki kai da wuri dan Sir Bala yana da matsala yace 8:30 dot yake bukatar Assignment ɗin a office ɗinsa kuma Assignment ne mai mahimmanci sosai, 30% na exam score ɗin mu ne, ki kula don Allah Salmah kar a samu matsala mutumin bauɗaɗɗe ne kuma bashi da imani."

Zama salmah ta yi a bakin bed ba tare da ta kalleta tace "Menene shirin ki akan shi domin baza mu bari lokaci ya ƙure mana ba." Jin Salmah ta taba mata inda ke mata ƙyaikyayi yasa ta miƙe zaune tare da dafa kafaɗar salmah tace , "Ina da kyakkyawan shiri a kan shi wanda na tabbatar zai yi aiki fiye da zato na."

"Da kyau, menene shirin domin na san ta dame zan taimaka miki."

"Ba wani abu mai tsauri ba ne, na yanke shawaran zan fallasa asirin shi a idon duniya zan tozar ta shi a idon masoyansa ta hanyar shiga gidajen redio da talabijin media na faɗi wanene shi."

Da wani irin mugun dariya Salmah ta fashe, wanda ya saka Aysha ƙanƙance idanun tana kallonta .

Hakan baisa ta tsagaita da dariyar ta ba sai da tayi mai isarta tukunna, kallon Aysha ta yi da nufin yin magana, da sauri ta daga mata hannu. A kausashe cike da tsananin fusafa tace, "I know dama karya kike min yaudara ta Kawai kike yi da kika ce kina feeling pain ɗina, nima nayi wauta domin na riga nasan babu macen da zata iya feeling pain ɗina sai wacce ta haɗu da irin ƙaddarata a rayuwarta, kin tasa ni gaba kina dariya wato ga mahaukacciya ko, ba komai laifi na ne dana gaya miki sirrina nagode." Tana gama faɗin haka ta miƙe tana share hawaye ta nufi hanyar toilet.

Har ta kama handle ɗin kofar toilet zata shige salmah tace "baki fahimce ni A'isha ta yaya kike tunanin bazan yi dariya akan shirmen da kike faɗi ba , kin san kuwa me kike shirin yi, abin da kike shirin yi shi a ke kira da wayon rashin wayo hausawa kance idan baka iya kama 6arawo ba,to kuwa 6arawo zai kama ka, mutum kamar Mr AA kangiwa kike tunanin zaki shiga kafafen sadarwa domin aibatawa,ki sake tunani idan hankali ya gushe hankali ke nemo shi, ta yaya kike tunanin mutane zasu yarda da maganar ki, shin ina hujjar ki, menene shaidar ki? Wai tukunnama, kina da tabbacin shine wanda ki ke nema da gaske, kina da tabbacin shine Babangidan ko akasin haka?“

Da baya da baya ta ringa ja har ta iso bakin bed da6ass ta zaune tare da dafe goshin ta kwata kwata ta manta da batun wani hujja ko shaida, idanunta ya rufe burinta Kawai fansa, tabbas da kuwa ta rafka babban kuskure, lallai Salmah alkhairi ce a gareta, ba da don ita ba da ta daka tsalle ɗaya ta faɗa rijiya wanda sai tayi dubu bata fito ba.

Maganar salmah ne ya katse mata tunani. "banji daɗi ba A'isha da kina ce bana feeling pain ɗin ki, idan da wanda ke jin ciwon abin da ya same ki a yanzu baya na yake, ki sani ko babu aminta tsakanin mu ciwon ya mace na ya macece."

Da sauri Aysha ta kai hannu ta rufe mata baki, cikin rawar murya ta shiga cewa "Kiyi hakuri ƴar uwa ta ki yafe min ban kyauta miki ba, kaidin zuciya ce wacce bata da kashi." Hannu salmah ta kai ta cire hannun Aysha dake bakin ta ta kalle ta ta ce "Babu komai ƴar uwa na fahimce ki."

Ɗagowa tayi ta kalleta ta itama murmushi suka sakarwa juna wanda bai kai zuci ba, Aisha ta ce "yanzu meye abinyi." Shiru salmah tayi tana nazari kafin tace "Abinyi shine, mu fara da samun tabbacin a kan Babangida ta hanyar bibiyar Mr AA, ina da tabbacin idan ma ba shi bane Babangida to tabbas ma kusancinsa ne, daga na sai mu ne mi shaida da hujja kafin mu kutsa kai gadan-gadan cikin aikin, na yi miki alkawarin in dai ina numfashi sai an bi miki hakkinki Aysha."

"Ta yaya zamu samu shaida da hujja nidai a yanzu kinsan bani da wani shaida sai Allah, sai iyayena waɗan da bansan a duniyar da suke ba a halin yanzu, bani da wani hujja kwakwara da zan kama."

Murmushi salmah tayi tace "kar ki damu ƴar uwa zamu samu shaida cikin sauki ta hanyar bibiyar sahunsa, duk da bamu da isasshen lokaci don yanzu saura wata biyu cif za6e amma ki bar komai a hannuna."

Kafin A'ishatu ta bata amsa suka jiyo muryar Ammi tana kwala musu kira, da alama tana nufowa ɗakin nasu ne da sauri salmah ta miƙe tare da daukar Assignment ɗin A'ishatu da zata mata submitting ta saka a jaka ta fice.

Ammi da kanta ta sauke Salman da Salmah a school, sannan ta wuce Asibitin da take aiki.

Kwanciya ta gyara lokacin da ta ji get man ya maida koƙa ya kulle, rintse idanunta tayi ta shiga tunanin yadda zasu samo shaida da hujja, ta dade a haka bata hango wata mafita ba, zumbur ta miƙe lokacin da ta tuno wani abu, durowa ta yi akan bed ta dauki wayarta da sauri ta fice daga ɗakin, bata zarce ko ina ba sai ɗakin Ammi in da take adana takardu masu mahimmanci, filla filla ta shiga dubawa cikin sauri sauri, bata ga abin da take nema ba, tattara takardun tayi ta mayar, a fili ta ce " ya ilahi! ina takardun nan suke ne?" Dakin Abie zuciyar ta bata amsa, kamar wacce aka tsikara ta fito daga ɗakin Ammi ta nufi na Abie har ta kama handle ɗin ƙofar zata buɗe,kira ya shigo wayar ta,lamba ce babu suna kamar ta share sai kuma ta ɗaga, daga ɗaya bangaren ta ji muryar namiji yana cewa "A'ishatu m Lawal kizo school yanzu yanzu, sister ki ta zo ta yi submitting Assignment dinki, na harhada na dauka na kai masa Office yace na mayar ya fasa kar6a a haka, zai biyo class ya kar6a a hannun kowa, means kowa zai yi submitting nashi by his self, kizo da wuri don 20 minutes ya bani akan na mayarwa kowa script din shi." Daga haka aka katse call din ba tare da an bata damar cewa komai ba.

Sai lokacin ta gane mai magana class captain ɗinsu ne Al-mustapha.

Dafe kai tayi tare da furta "innalillahi wainnailaihi rajiun." a bayyane,tsaki taja ta ce "amma wannan mutumin anyi jarababbe." Tunani ta shiga yi ta yadda 20 zai kaita school, gata a gida ko wanka bata yi ba.

Dakin su ta koma a gaggauce ta canza kaya , ta dauki kudin transport ta fito tana sauri kamar zata tashi sama, tafiya take tana duba agogon dake ɗaure a tsinstiyar hannunta, tasan ko a jirgin sama zata baza ta isa kafin lokacin ba amma duk da haka za ta yi iya yinta.

Addu'a ta ringa yi Allah yasa ta samu koda mashin ne ta hau don tsakanin gidana su da babban titi akwai dan tazara ga shi layin ƴan gayu ba'a cika samun abin hawa ba.

Haka ta ringa zuba sauri Kamar zata tashi sama, daga bayanta taji mota yana mata horn da sauri ta juya tare da kaucewa duk da tasan ba akan hanya take ba, maimakon ya wuce sai,matsowa yayi kusa da ita yayi parking tare da sauke glass matashi ne, kyakkyawa, duka bazai wuce tsaran su salman ba, murmushi ya sakar mata tare da cewa "sister school kika yi ne." Ido ta zuba mashi tana son gano inda ta san shi, bai jira jin amsar ta ba yace "OK dama ina ce school zaki in ce ki shigo mu tafi don nima can na nufa." Ta ce "kaima ɗalibin p.u.t, ne." Ya ce "yes." Jin haka yasa ta bude motar ta shiga da zuciya ɗaya.

Tunda suka fara tafiya saurayin nan bai ƙara ce mata kala ba sai zuba tukin shi yake cike da kwarewa. Har gaban department ɗinsu ya kaita, ta sauka tana ta zuba mashi godiya.

Koda ta ƙarasa a waje ta samu da yawan yan class ɗin su, wurin class captain data hango ta nufa, shima yana ganin ta, ya tare ta, da cewa "A'isha kin makara yanzu ya gama fita, ya kuma ce bazai sake amsar na wani ba ko dan uban wanene?" Zaro ido tayi tace "shi kenan zan fadi a subject ɗin, dama ranar da a ka yi text bana nan, yau kuma gashi an yi submitting assignment ɗin da nake da yaƙinin zai taimaka min na yi passing." wata daga cikin su ne tace "ki bi shi office ki roke shi ƙila ya karba."

Ta fi mintuna ashirin a bakin office ɗin kafin a bata izinin shigowa, daga gefe ta tsaya ta ce "gud morning Sir," sai da ya gama shan kamshin shi ya ɗago ya mata kallon sama da ƙasa sannan yace "morning! meke tafe dake." Cikin in'ina ta buɗe baki zata fara bada hakuri, wayar shi ta fara ringing dakatar da ita yayi ta hanyar daga mata hannu, ya yi picking call ɗin tare da karawa a kunne, bata san mai aka gaya mai ta ɗaya bangaren ba zumbur ta ga ya miƙe, yana cin gaba da waya can kuma taga ya nufi hanyar fita, da hannu ya mata alamar ta jirashi yana zuwa ya fice da sauri.

Tayi tsayuwa a cikin office ɗin sir Bala ya kusa na 30 minute bai dawo ba, ita ba abin ta wuce ba, ji tayi ciwon da kanta keyi ya fara karuwa ga wani jiri jiri da ya fara diban ta, idanu ta lumshe tare da jingina da wall ɗin office ɗin.

Ƙaran buɗe kofar ne yasa da sauri ta bude lumsassun idanunta da suka fara rinewa zuwa launin jaa.

Wani irin zabura ta yi lokacin da idanunta ya sauka akan fuskar shi, duk da cikin shigar shi ta 6adda kama yake hakan bai hanata gane shi ba zuciyata ce ta hau dakan uku uku, yayinda ta nemi miyau a bakinta ta rasa............

Diyar Nalado ce😍 09116099486 [5/14, 6:00 AM] Oum khadeejarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

By

AyshaNalado

Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍

BOOK 1

Page 15

Kansa a ƙasa yana gyara ɗaura agogon dake hannunsa, ya shigo office ɗin laɓɓansa ɗauke da yar karamar sallama. Har ya iso tsakiyar office ɗin bai lura da mutum a ciki ba, sai da ya ja kujera zai zauna sannan idanuwansa suka sauka a kan fuskarta.

Dakatawa ya yi da zaman da ya yi niyya, ya zuba mata idanu na y‘an wasu sakanni, kafin yasa hannu ya zare glass din da ke manne a fuskarsa.

Wani irin kallo ƙurillah yake bin ta da shi alamar yana son tuno inda yasan fuskarta, can kuma ya murza yatsunsa biyu suka bada wani sauti tass! tare da pointing ɗinta ya ce "At dausayi ko, me gudu bata kallon gabanta right?" Ya faɗa cikin siyar tambaya?

Yau shine karo na uku da ta sanya shi a idanunta kuma karo na farko da ta yi wa fuskarsa kallon sosai, yayinda ya zama karo na biyu da ta saurari muryarta, wanda ya haifar mata da matsanancin faduwan gaba, zuciyarta ta shiga rawa, ta nemi miyau a bakinta ta rasa balle ta zamu zarafin bude baki ta bashi amsar tambayar da ya yi mata, kuma ta kasa dauke idanunta a fuskarta, wani dan siririn tabon yanka dake gefen fuskarsa take bi da kallo.

“Babangida ne. Wallahi shine, mutumin da ya ɗaiɗaita kyakkyawar rayuwarki da ta ahalinki tare dasa miku dawwamammen bakin ciki mara yankewa, shine a gaban ki, mutumin da kika shafe, shekaru takwas masu kyau kina bulayin nema, domin ki danƙwafar da shi a gabanki ya kwashi kashinsa a hannu.” Zuciyarta ce ke raya mata hakan, yayinda take ƙara nutsa idanuwanta cikin nasa, wanda hakan ya kara bata tabbacin akan abinda zuciyarta ta raya mata, lokaci guda wani irin ɗaci ya dabaibaye zuciyarta, take kallon da take masa ya juye zuwa wani irin mugun kallo mai cike da tsantsar kiyayya da tsana, zuciyarta na wani irin tafarfasa sai wani irin zazzafan huci take fesar wa kamar wata kububuwa.

Ganin irin mugun kallon da take jifan shi da shi ya sa ya hade rai, ya lura yarinyar kwata kwata bata da kunya, shi kuma a yaruwar shi baya shiri da fitsararre take ya ji tsanar ta ya d’arsu a ransa, ranar da suka fara haduwa a Dausayi ya rasa dalilin da yasa fuskarta ya kasa bace mai a idanun shi, bini bini ta fad’o mishi a rai abin da bai ta6a faruwa dashi ba a tarihin rayuwar shi, tunanin wata mace bayan *NUR* dakyar ya samu yakice ta a ranshi ya watsar, har ya manta da kamannin ta sai kuma kwatsam ga shi yau ya sake had’uwa da ita a inda bai taba tsammani ba, sai dai kuma yadda ya ke zaton ta Ashe ba haka take ba.

Takowa ya yi yazo gabanta ya mata rumfa kamar za su had’e don spaces din da ya bari a tsakanin su baifi taku daya ba, kusancinsu ya haifar mata da miji mummunar tashin hankali, amma ta dake a zahiri yayinda daga ciki Zuciyarta ke rawa. Sai da ya gama karewa fuskarta kallo, kafin ya mika hannu ya kama ha6ar ta, da sauri ta saka hannu ta buge hannunshi, tana watsa mai mugun harara kamar kwayoyin idanunta zasu fad’o ‘kasa.

Wani irin kayataccen murmushi ya saki na gefen baki wanda da gani kasan na zallar takaici ne, a take kuma ya daure fuska, kamar ba shi ne yayi wannan murmushin ba, a zuciyar shi yace "lallai yarinyar nan tana bukatar na nuna mata other side d’ina."

Sake kamo ha6ar nata yayi wannan karan da mugun karfi ya d’ago fuskarta , kici kicin kwatar kanta ta shiga yi, amma duk yadda taso ta kwace ko ta buge hannunshi ta kasa, ganin baza ta iya ba yasa ta dakata tare da watsa idanunta da suke rine zuwa launin ja cikin nashi.

Kallo cikin idanun juna suka shiga yi kowa a harzuke , a kausashe ya ce "ke wacece da zaki ringa jifana da irin wannan mugun kallo, ni tsaran wasan ki ne ko kinga na miki kama da dan iska ne." Yana maganar yana kara matse mata ha6a da 'karfi.

Cikin tsananin azaba tace " mugu bakin azzalumi, dama nasan duk tsawon zamani baza ka tana canzawa ba, Babangida na tsane ka " ta karashe maganar kicin kaurara kalman *na tsane ka*

A tsawace yace "Ahmad kangiwa I said,karki sake kirana da Babangida, tukunna ma Wacece ke me kike nema a wajena waya turo ki?" Ya karashe maganar Tare da kara shakar wuyar ta, zafin da taji yasa ta saki yar 'kara, sake danko kanta yayi yace "lallai kinyi gaskiya ni mugune azzalumi, don kin tsane ni sai me? Ya fada da karfi ,sai kuma yayi low da voice din shi, ya ci gaba da cewa "Dubban mutane so na suke, kuma daga yau bana son na kara ganin wannan kodadden farin fuskar taki a in da nake idan kuma kika yi kuskure kika bari muka sake yin ido biyu dake sai na saba miki kaman...." Kafin ya kai karshen zancen shi ya ji sauka kakkuran miyau mai hade da majina a bakin shi, be san sanda ya sake ta fa kafin ya gama dawowa hayyacin sa ta kai wajen kofar fita office din da mugun gudu, tsayawa tayi tana kallon shi yana ta faman kakari.

Murmushi ta saki na zallar bakin ciki, ta ce "kodaddiyar fuskata yanzu ka fara ganinta bazan kyale ka ba har sai naga bayan ka sai na rusa dukkan farin cikin ka, mugu kawai *na tsane ka*" ta sake maimaitawa a kausashe, saboda fahimtar da ta yi kalmar na dukansa sosai.

A zuciye ya dago idanunsa da suka rine saboda ɓacin rai tare da kawo mata wawura. tuni ta fice a office din da mugun gudun.

Bango ya kaiwa naushi, tunda yake a rayuwar shi ba a taɓa ci masa mutunci kamar yadda wannan yarinyar dako sunan ta bai sani ba ta ci masa yau, babu abin da yafi kona mishi rai kamar kalaman *na tsane ka* da take jifan shi, tun da aka haifeshi soyayya Kawai ya sani kowa sanshi yake , dan me yasa ita zata ringa cewa ta tsane , tabbas zai tsumayi haduwar su ta gaba kamar yadda tace kuma sai ya tabbatar ya koya mata ladabin zaman duniya.

*************************

Sai da ta kusa ɓulla wajen da mutane suke sannan ta dakata da gudun, ta gyara zaman hijab dinta, kafin ta ci gaba da tafiya a hankali, sai lokacin hawaye masu dumi suka samu damar sauko mata, jefe kafa Kawai take duk inda ta samu don kwata kwata bata ganin gabanta, tsawar da ya daka mata lokacin da ta ce *Babangida na tsane ka* ke amsa kuwwa a kunne da kwakwalwarta, "Ahmad kangiwa I said, karki sake kira na da Babangida, tukunna ma wacece ke me kike nema a waje na waya turo?" Shin da gaske bai gane ta ne? To ko kuma da gaske ba shine Babangidan da take nema ba, ko shine ko ma bashi bane zata bibiyi sawun shi idan ta tabbara shine wasa yake mata da hankali zata yi wasa da nashi hankalin ta inda bai ta6a zata ba.

Bata san ta fita daga babba get din school din har ta hau titi ba sai da taji wani gigitaccen horn, a firgice ta dago kai tare da kwallah wata uwar salati,tare da rintse idanu.

A firgice ya taka birki ya fito daga motar, hakuri ya shiga bata kamar bakin shi zai tsinke duk da yasan ba laifin shi bane, ganin yadda take kuka ne hankalin shi ya tashi duk a tunanin kukan abin da ya faru take yi, ganin yadda duk ya rude yana bata hakuri duk da laifin ta ne, yasa ta dagowa ta zuba mai idanu, turuss ya yi kafin kuma yace yace "Maamah?" Bata saurare shi ba sai ma tare mai napep da ta yi ta fada tare da gaya mai inda zai kaita.

A matukar mamakan ce mutumin ya bi napep din da kallo har ta bace wa ganin shi, kamar wanda akan tsikara kuma ya zaro wayar shi tare da lalubo wata lamba da yayi saving da my Queen ya danna mata kira, d'aga wa tayi muryar ta cike da barci tace "Yayana ina wuni." Bai amsa ba sai ce wa da yayi "kina ina ne Sister.' Tace "ina gida bacci ma nake wayar ka ne ya tashe ni." Jiki a sanyaye yace "OK to koma kiyi baccin ki anjima zan shigo Estate mu gaisa." Bayan ya maida wayar shi aljihu tasbihi ya shiga jerowa ubangiji, lallai Allah mai hallita buwayi gagari misali.

****************************

Sai gurin Karfe uku su Salmah suka dayo su uku harda Suraj, kan sallaya Salmah ta same ta, sai dai kallo daya ta mata gabanta ya yanke ya fadi, da sauri ta isa gareta tana cewa "sister Eshart lafiya meya same ki, kukan me kika yi." Murmushin karfin hali ta kakaro tare da cewa "babu komai cikina ne ke ciwo."

Readers Also Read