Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 12
Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 12: Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 12. "Wani irin ciwon ciki naga lokacin period din ki bai yi ba." Ta fada…
3,272 words
"Wani irin ciwon ciki naga lokacin period din ki bai yi ba." Ta fada tana tsatsareta da ido, memakon ta amsa ta sai mikewa tayi zata bar mata dakin, har ta kama handle Salmah tace "ba'a boyewa abokin kuka mutuwa." Juyowa tayi ta watsa mata jajayen idanunta kafin tace "I will tell but latter." Ta sa kai ta fice.
Ajiyar zuciya Salmah ta saki, a bayyane tace "Allah ga baiwarka Allah ka shiga lamarinta." Message din daya shigo wayar ta ne ya dauke hankalin ta, karantawa tayi kafin ta saki murmushi, reply tayi, sannan ta shige toilet.
A dining ta samu Suraj da Salman suna cin abinci, kujera taja ta zauna tare da sakin murmushi,duk kallonta sukayi Suraj yace "sister Eshart ina wuni." Ta amsa da "lafiya kalau ya school." "School ba dadi, wlh ni da ace mother zata yarda Kawai tasa father ya bani kudi na fara business Ya B ya bani gida da mota a aura min Salmah kawai mu yi zaman mu ba sai munje school ba."
Karaf a kunnen Salmah da ta iso wajen yanzu. Salman ko mai zai yi banda dariya, A'isha ma yanayin da take ciki ne ya hanata darawa amma duk da haka sai da ta murmusa.
Ganin yadda suke dariya ya kara kona ran Salmah, kankance ido tayi cike da bala'i ta ce "wallahi Suraj ka fita ido na na rufe." Juyowa sukayi gaba dayan su suka zuba mata ido sai lokcin suka san da wanzuwar ta a wajen.
Marairaice fuska yayi yace "meye aibuna da yasa bakya so na." A masife tace "kayi min ‘kan‘kanta." Ya ce "wlh ban miki kankanta ba namiji baya kad’an." Wani mugun harara ta watsa mai tare da zan dogon tsaki kamar bakin ta zai tsinke, fuu ta juya ta bar gurin ba tare da zauna dan cin abincin daya kawo ta ba.
Salman dariya ya kwashe dashi yayin da Aisha ke bin shi da kallon tausayi.
Kallon Salman yayi ya tabe baki cikin irin yanayi na shagwababbun yara, can kuma ya dafe goshi, zirrr sai ga hawaye kamar an kunna famfo.
Duk zaro ido suka yi Salman cikin mamaki yace "kuka! Akan Salmah." Bai kula shi ba sai dauke kai da yayi daga kallonsa, alamar yana cikin ciki da shi.
A'isha ta ce "ya isa Suraj ka share hawayen ka, ni na fahimce ka, ka daina saurin yin kuka idan ta gani zata kara raina ka, ka yi ta addu'a idan Salmah matar ka ce , zaka aure ta."
Ya ce "sister Eshart me nayi da Salmah bata so na? Hala ni mummuna ne shiyasa." Cike da tausayawa tace "A'a wlh Suraj kama fita kyawu." Ya ce "ta6a nan dina kiji." Ya fada yana nuna saitin heart din shi, zuciyar shi d’aya harga Allah da gaske yake ta ta6a kirjin shi.
Da sauri ta girgiza kai gabanta na faduwa, tunawa da wani abu makamancin wannan daya taba faruwa da ita acan baya, yayin da Salman ya sake kecewa da dariya.
Daker ta samu ta Kore wancen tunanin a kanta ta shiga rarrashin shi, tare fa mai alkawarin zata taya shi shawo kan Salmah, jin haka yasa ya fara jin dadi yana zuba mata godiya cike da matsanancin farin ciki yace "idan Yayana ya hau governor zan saka ya baki kyautar mota." Rass gabanta ya fadi jin abinda ya ce take kuma wani shawara ya fado mata a zuciya wannan wani dama ne ta samu.
Da sauri tace " wai da gaske kai kanin Mr AA kangiwa ne." Salman ne ya kalleta da sauri can kuma yace "da gaske ma kike tambayar shi' kenan tum dama baki yarda da magana ta ba Ashe."
Suraj kam murmushi yayi tare da cewa "Eh cousins brother na ne."
"Wow Ashe da gaske ne ta fada." Cikin farin ciki, can kuma ta langwave murya "Dan Allah Suraj ina son na ganshi ido da ieo naji ance yana da wuyar gani."
"In dai kika bi ta hannuna ganin sarkin fawa yafi ganin shi wahala." Ta ce "da gaske." Ya gyada mata kai yana murmushi,
"Yau she zaka hadanI da shi?." Ya ce "Yaushe kike son ganin shi."
"Ban shirya ba amma idan na saka date zan gaya maka."
"To shi kenan no problem."
Fira ta ci gaba da jan shi akan Mr AA kangiwa yana bata amsa, har suka kammala cin abinci, sai da ta gama tattara duk abin da take bukatar sani sannan ta mike ta musu sallama tunda taga alamar fita zasuyi, ta wuce ciki.
Tana juya baya Salman ya daga wayar shi dake kife kan dinning table din ya kalla tare da sakin murmushi sannan yayi saving din recording din shirar su da yayi.
****************************
Har suka gama cinye wunin bata ce ma Salmah komai ba ita ma bata tambaye ta ba duk da irin za‘kuwar da tayi da son jin me ya same ta.
Bayan sunyi shirin kwanciya wuraren 10 :30 wayar Salmah ce ta fara ringing, ganin me kiran ne yasa ta kalli Eshart itama kallonta tayi, kafin kuma ta mike ta fice daga dakin da sauri. Murmushi Eshart ta saki zuciyarta na kiyasto mata wani abu cen dabam.
Falo ta nufa ta nemi daya daga cikin kujeran falon ta zauna, ta kwashe mintuna tana waya kafin ta mike ta koma dakin su,mikawa Eshart dake zaune bakin bed wayar tayi tare da cewa "ana magana.”
**********************************
Tsaye yake gaban mirro a cikin hadadden bathroom, babu riga a jikin shi sai dan guntun short wanda iyakar shi Rabin cinyoyin shi, Ƙuri ya kurawa mirron ido kyakkyawan fuskar nan tashi a mugun hade, surar jikin sa yake kallo daga sama har kasa, so yake ya gono makusan sa da kuma dalilin da yasa ta ce ta tsane ni, ya fi mintuna talatin a tsaye a gaban mirror bai ga wani aibi a halittarsa ba, a zuciye ya dunkule hannu tare da kaima mirror naushi ji kake taratsatsatatat! “ Me yasa na damu da lamarinta,? Mai yasa maganganunta su ka yi tasiri a gareni, mai yasa haduwarmu ya kasance a haka” ya dakata yana kallon jinin dake diga dis dis daga hannunsa saboda yankewar da yayi kadan, sai kuma ya saki wata shegiyar murmushi da ta yi bala'in yi masa kyau, kafin a hankali ya furta, “ Bibiyats take yi tabbas, wannan karon kuma wanene daga cikinsu yake son mu yi yaƙin sunƙuru.” ya dage gira yana kallon fuskarsa a dan sauran ballin madubin da ya yage, kafin ya sake cewa, “ Koma wanene, I will find out, it's kuma tabbas zan nuna mata kuskure ta na hada kai da makiyana da ta yi ..............
Aradu Allah akwai gwarama a gaba😂
Oum Khadijah ce😍 09116099486 [5/14, 6:00 AM] Oum khadeejarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀
By
AyshaNalado
Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍
BOOK 1
Page 16
Hannun Salmah da ke miƙa mata wayar ta bi da kallo, gabanta na ɗan faduwa, “Ya Anas da daddaren nan.” Ta furta a ranta kafin ta miƙa hannu jiki a sanyaye ta karɓi wayar ta kara a kunneta. Sallamarsa da nutsattsiyar muryarsa ya ratsa kunnuwanta, ta lumshe idanunta a hankali ta bude akan fuskar Salmah da ta ja ta yi mata tsaye a gaba, tana binta da wani irin kallo wanda ta rasa gane kansa. Itama ido ta zuba mata, tana nazarin yanayinta, sauyin da ta gani a tattare da ita yau a bayyane yake, wannan ba shine yanayin da take shiga ba a duk lokacin da ta haɗa ta da Anas domin su gaisa, farin ciki da annashuwarta basa ɓoyuwa murmushinta baya yankewa, har takan yi mamaki hakan wasu lokutan. Ta san fushin da take yi da ita akan Suraj bai isa ya janyo wannan sauyin ba. Muryar Ya Anas ce ta katse mata tunani, “Ayush!” ta ji ya kira sunanta da wani salo mai daɗi, “Na'am Yaya.” ta amsa a sanyaye tare da dauke idanunta daga kallon Salmah, “Ki na jina?” “Umnh! Ina wuni?” “ Lafiya kalau kyakkyawar ƙanwata.” Murmushi ne ya suɓuce mata ba tare da ta shirya ba, “kai Ya Anas ina kyan yake.” Ta yi maganar da wani salo wanda ya tilastawa Anas lumshe idanu, a hankali muryarsa cike da nishaɗi ya ce “Yana tare da ke My Ayusher.” Zaro ido ta yi kafin da sauri ta juyo ta kalli Salmah da har lokacin take tsaye a kanta, tasan sarai ta ji domin wayar a handsfree yake, suna haɗa idanu Salmah ta juya da sauri ta shige toilet, jingina bayanta ta yi da kofar toilet ɗin bayan ta mayar ta rufe, tare da sakin wahayen da take ta kokarin dannewa tun ɗazu, da tana da dama da ta hana, data dakatar sai dai bata da wannan ikon a halin yanzu, ta daɗe a haka tana tausar zuciyarta, sai da ta tabbatar sun kammala wayar kafin ta watsa ruwa ta fito bayan ta daura alwala.
A kwance ta tarar da Aysha wayar kife a kusa da ita, idanunta a lumshe ta juya mata baya, motsin fitowarta bai sa ta juyo ba duk da tana da tabbacin ba barci take yi ba.
Wayarta kawai ta dauka itama ta hau gadon ta kwanta bayan ta rage musu haske, WhatsApp ta shiga ta duba saƙo, ta kai mintuna biyar tana jujjuya sakon a zuciyarta kafin ta yi reply ta kashe wayar ta kwanta bayan ta yi addu'a.
Wannan daren ya zama mai tsauri ga Aysha, abubuwa biyu suka taru suka mata rubdugu, abinda ya faru ɗazu tsakaninta da Mr AA ya kasa barin kanta, ga kuma wata sabuwar da Ya Anas ya Kunno mata, fatanta ya fahimce ta, ya yi mata uzuri, sai dai tana matsanancin jin kunyar Ammie, Abie, dama shi kansa Anas ɗin.
Washegari ya kasance asabar babu aiki kuma babu makaranta, hakan yasa bayan sallar asuba da suka sake kwanciya ba su tashi ba sai kusan goma. Kallo ɗaya Salmah ta yi wa Aysha ta tabbatar tana cikin damuwa, ta san dama za a rina, wai an saci zanin mahaukaciya, ba za ta ce mata komai ba har sai ta nemi shawararta, za ta zuba mata idanu ta ga iya gudun ruwanta.
A tare suka yi breakfast kamar ko yaushe, sai dai yau dining ɗin shiru babu mai cewa komai, tun bayan gaisuwar da su ka yi, dama Salmah ce mai surutun kuma yau kanta ya dau caji, Abie ne ya fara kammalawa, sai da ya goge hannu da bakinsa da tissue, sannan ya kalli Ammi ya ce “ Yaushe Anas ya ce zai dawo?” A zabure Aysha ta dago jin an ambaci Ya Anas, sai dai babu wanda ya kula da hakan sai Salmah. “Au kaima bai faɗa makan ba kenan?” cewar Ammi tana yar murmushi, “ Ya ƙi, amma ya bani tabbacin cikin watan nan zai dawo.” yar dariya Ammie ta yi ta ce, “ Shiryayye wai bazata zai yi mana.” Murmushi Abie ya yi, “ To Allah ya kawo shi lafiya.” duk suka amsa da Ammi, yunkurawa Abie ya yi zai miƙe, da sauri Salmah ta ce, “Abienah.” ya juyo ya zuba mata ido alamar yana saurarenta. “ Abie za mu je saloon ni da Aysha, yau babu school.” ɗan shiru ya yi yana nazari kafin ya ce, “ Okay ku shirya, Salman ya kai ku.“ Ya ciro card ya miƙa mata tare da fadin “ Na san shi a ke wa.” dariya suka saka, Salmah ta karba tare da faɗin “ Mun gode sosai Abie, Allah ya saka da alkhari ya kara buɗi, mu biya Shopping?” Murmushi ya yi kafin ya gyaɗa kai. Daɗi sosai ya kama Salman, jin zai samu damar fita da mota yau, a zuciyarsa sai shiwa Salmah albarka ya ke yi, ta dade bata yi abinda ta faranta masa ba irin yau, don dama tun ɗazun yake jujjuya yadda zai samu aron motar Ammie su fita yau suna da wata ƴar taro na yan team ɗinsu.
“Yau kuma gulmar ce ta motsa?“ Ammie ta faɗa tana hararar Salmah, dariya duk saka saka saboda gane abinda take nufi, “ To Ammie ai ke ce baki sakar mana kuɗi kamar Abie.” Cewar Salmah tana dariya, “ Ya yi kyau ai, ni kujerar zama ce, ina nan za ku lallaɓo ku same ni.” “ Ayya ki yi hakuri farar uwa tauraruwar Abienah in Sha Allah ba za ta kai mu ga haka ba.” “ Ahaf! Ai kuma sai ki yi.” Ammie ta ƙarashe maganar tare da miƙewa ta ji bayan Abie da ya kama hanyar ɗakinsa yana dariyar surutu da iya kalmashe zance irin Salmah.
Daga haka cin abincin ya tashi, duk su ka yi ciki domin ƙimtsawa. Karfe goma sha daya da kwata, suka kammala shiryawa, kamar kullum, Salmah fuskar nan ɗau da makeup, yayinda Aysha ko hoda bata shafa ba, suka fito a tare cikin ankon atamfa, Salmah na mata mitar rashin son kwalliya. Zuba musu ido Salman dake tsaye a falo shima cikin shiri yana wulwula makullin motar Ammie da ke hannunsa ya yi, yana kallonsu tare da nazarin kowacce, ko daga yafa mayafinsu za ka hangi bambamcinsu a zahiri, Salmah yar gayu ce ta karshe mai son ado da kyale kyale, kana ganinta ka ga big girl, yayinda Aysha take mai tsananin natsuwa da kamewa, a suffa kuwa, Salmah dirarriyar macece full option, kana ganinta kaga matar manya kamar yadda take faɗa kullum, iya hips da mazaunanta ka kalla zaka shaida hakan, ba ƙiba gareta ba sai dai akwai ƙaya, shiyasa kullum Salman ke ganin tsaurin idon abokinsa, da tunanin inda zai kai wannan zuƙeƙiyar halittar. Yayinda Aysha ta ƙasance, mai jikin Fulani, siririya fara mai yalwar gashi, sai dai tana da sharp mai matukar ƙayatarwa da daukar hankali, cikin nan nata a shafe kamar bata cin abinci hakan ya baiwa ƙugunta damar nuna bajewarsa a bayyane daga sama kuma abubuwan basu da wani girma ɗas da su daidai jikinta. A fuska kuwa kowacce da kalar sanyayyar kyawunta mai tafiyar da imanin mai kallo.
A gurguje su ka yi wa Ammie sallama suka tafi, Salmah a baya Aysha a kusa da Salman, tuƙi yake yana amsa kiran abokansa yana shaida musu ya yi nasarar samun motar, ciki harda Suraj, shiru Aysha ta yi a gaba tana tunani, yayinda Salmah ke baya tana charting.
********************
Kasancewar daren jiya bai samu isasshen barci ba, domin kwana ya yi da damuwa da tunanin yarinyar da ko sunanta bai sani ba. Hakan yasa ya tashi yau asabar very weak. kamar yadda ya zamar masa a jiki, in dai ya kwana a gida ɗaya da mahaifinsa to da safe zai shiga su gaisa, yau ma hakan ta kasance, misalin karfe tara na safe, ya tarar da General Idris Kangiwa a falonsa yana zaune shi kaɗai yana karatun jarida daily trust, kallo ɗaya General ya yi masa ya fahimci a kwai damuwa tattare da ɗan nasa, jaridar da ke hannunsa ya ajiye tare da zare gilashin kara karfin gani da yake da sawa idan zai yi karatu saboda jikin girma, ya fuskancesa da kyau. “ Ina kwana Abba.“ Ya furta cike da tsantsar ladabi bayan ya rusuna ya sunƙuyar da kai ƙasa alamar girmamawa irinta al'adar gaisuwar malam bahaushe. Yana ci gaba da ƙare masa kallo ya amsa da “Lafiya ƙalau Babana, yau an kwana a nan kenan.” “ E Abba na shigo around 11, ka kwanta lokacin, ya ƙarfin jiki.“ “ Alhmdlh, da sauƙi.“ “ Masha Allah, Allah ya ƙara maka lafiya.” “Ameen, Allah ya yi maka Albarka ya jiƙan Zainaba.“ lumshe idanu ya yi a hankali ya bude a fuskar Gen. Alamar amsawa,daga haka ya koma ya zauna a ƙasa yana fuskantar Mahaifinsa, a ƙa'ida idan suka yi irin wannan zaman, su kan yi hira su yi raha su tattauna abubuwa ma su mahimmanci, su ji damuwar juna, har zuwa lokacin da za su yi karin kumallo, daga nan kuma sai su yi sallama, wata ƙila kuma ba za su sake haduwa ba sai bayan wasu kwanaki domin shi AA ba zaunin waje guda ba ne. Sai dai koda bai kwana a ƙasar ba, ƙa'ida ce kullum safiyar duniya sai sun gaisa da mahaifinsa ta waya.
Shiru shirunsa da ya yi yawa yau, ya kara gaskata zargin Gen. Akansa domin duk da kasancewarsa mara surutu da hayaniya a gaban mahaifinsa ba haka yake ba, shine mutum na biyu bayan Mother da yake sakewa da shi su yi hira sosai har ya ji wani sirrinsa, shine mutumin da yake ganin rauninsa, shine mutumin da yake zama ya yi kuka a gabansa domin ya samu salamar zuciya idan wani damuwar ya ciyosa, yana da tarin abokai amma mahaifinsa shine amininsa.
Cikin hikima Gen. Ya fara jansa da hirar da yek da tabbacin zai rage masa damuwarsa, kafin ya jeho masa tambaya game da halin da yake ciki. Shiru ya ya yi kusan minti ɗaya, kafin ya sauke numfashi a sanyeye ya ce, “ Abba bibiyata su ke yi, Abba mai yasa ba za su barni ba, me na tsare musu.” shiru ya yi yana kallon Gen. Da ya lumshe ido tunda ya fara magana, ya ci gaba da cewa, “Abba, wannan karon sun zo da sabon salo, mace su ka sanya, da ita suke so su yaudare ni su kaini ƙasa.” Jin hakan ya sanya Gen. Bude idanunsa da suka rine nan take ya zuba masa alamar karin bayani, gane hakan yasa ya ci gaba da basa labarin haduwarsa da Aysha har karo biyu da yadda haduwar ta kay, kiransa da suna Babangida da nuna sanyayyarta a garesa har zuwa irin munanan kalaman da ta farfaɗa masa.
Murmushin manya Gen ya yi, a ransa ya ce“ Lallai sun yi danganci, wannan abinda da suka yi tamkar sun yi wa kansu talala ne, lokaci ya yi da zan gano su wanene mutanen da ke bibiyata a duhu, ana daf da yin walƙiya.” a zahiri kuwa cewa ya yi, “ Ina bukatar sanin komai a kanta yar gidan wanene menene kamashonta a tafiyar, ka sanya ido sosai mata shu'umai ne, sannan ka zurfafafa bincike.” sun ci gaba da tattaunawar sirri na abubuwa masu mahimmanci da suka shafe su, kafin daga bisani su gangaro harkar siyasarsu, yadda zabe ke gabatowa da shirye shiryen da su ke yi mata. A haka Aunty Rukayya matar Gen. Ta shigo falon da sallama cikin ado na kece raini, sosai fara'ar fuskarta ta fadada lokacin da ta hango AA a falon, “ A'a ɗan gidan Mother yau an kwana mana nan kenan.” Da murmushi ya kalleta tare da faɗin, “ Eh Aunty ina kwana.” “ Lafiya kalau ya gajiya, ya kwana biyu, jiyan nan na ke cewa Gen idan ka yi aure dai nan za ka ajiye mana ɗiya, wata kila albarkacinta mu dinga ganinka.” Da sauri ya kalleta jin za ta jiƙo masa aiki, domin idan da yar tsamar da ke tsaninsa da Abba to maganar aure ne, kuma yasan da gangan ta yi hakan, domin ita da Mother suna mayaƙan Abba, sai dai abinda babu wanda ya sani, ita da tata manufar a kansa. Da ido ya yi mata alamar ta yi hakuri ta yi shiru, ta ko dauke kai alamar ta ƙi, ganin haka yasa ya yi zaraf ya mike, yana neman hanyar arcewa. “Oh don na yi maganar Aure shine ka miƙe, to Allah ya shiryeka, na yi shiru.” kallonta Gen. Ya yi ya ce“ Barshi ya fi ruwa gudu Rukayya, ni dai ki zama shaida zan fada a gabanki na yi masa mata.” a tare gabansu ya faɗi shida Aunty Rukkey, kasancewarta wayyayiyar mace, sai ta yi kokarin aro jarumta ta yafa, ta saka shewa tta yi guda tare da faɗin, “ Ma sha Allah, yaushe aka yi hakan.” “ Yau.“ ya bata Amsa yana sakin murmushin da shi kaɗai ya san manufarsa.