Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 13
Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 13: Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 13. Da sauri AA ya isa gabansa, ya zuɓe a marairaice ya ce “Abba don....…
3,316 words
Da sauri AA ya isa gabansa, ya zuɓe a marairaice ya ce “Abba don.... Hannu ya ɗaga masa, “Na gama magana bana son jin wani ƙorafi, tashi mu je mu karya.” ya girgiza kai “ Na ƙo shi.” “ To je ka.” Gen ya faɗa cikin tsare gida. Miƙewa ya yi jiki ba kwari ya kama hanyar ficewa, “ Ka tsaya mana ko Tea ne ka sha.” Cewar Aunty Rukayya bayan ta raka shi da kallo. Dakatawa ya yi ba tare da ya juyo ba ya ce, “ No, Nagode Aunty, fura nake buƙata zan je wajen Mother yanzu.” yana gama fadin hakan ya ci gaba da tafiya. “ Ba ka ji ba.” Muryar Gen. Ya sake katse shi, wannan karon juyowa ya yi saboda girmamawa amma bai ce komai ba, “ ka da ka manta da, binciken yarinyar, ina son sanin komai a kwana bakwai ko ƙasa da haka.” “ In Sha Allah.” shine amsar da ya iya bayarwa kafin ya fice daga falon yana jin kansa na sarawa. Kai tsaye tamfatsetsen sashensa gari guda ya nufa, a gurguje ya shirya cikin shigarsa ta ɓadda kama, dauki karamar mota ya bi ta get ɗin baya ya dauƙi hanyar gidan Mother motor su Ussy babban yaronsa mafi kusanci, na biye da shi a baya ba tare da saninsa ba.
Ko da Aunty Rukayya ta yi serving ɗin Gen kasa zama ta yi, saboda damuwa da tashin hankalin da ke nuƙurƙusar ranta, asiri ta basa, ta tashi ta nufi ɗakinta, a nan ma tsaye ta yi tana kai kawo, tare da nake faifan tunanin da hikimarta, “kai ina ba zai taɓa yiwuwa ba, ya zama dole na samu biyan ɓukata, ba zan taɓa zuba ido na rasa farin ciki saboda farin cikin wasu ba, so so ne, amma son kai ya fi. Wayarta ta zabura ta dauka da sauri ta lalubo wani lamba da ta yi saving da Baby ta danna masa kira...... [5/14, 6:00 AM] Oum khadeejarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀
By
AyshaNalado
Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍
BOOK 1
Page 17
Ajiyar zuciya Aunty Rukayya ta sauke lokacin da aka ɗaga kiran, “Na'eemarh.” Ta ambata a sanyeye cikin taushi, “Na'am Mummy, ya aka yi ne?“ wata siririyar murya ta amsa daga ɗaya hannun a yangance. Jim ta yi tana tauna abin da za ta fadan tare da tunanin makomar fadar, nata, saihar sai da ta ji Neema ta saki ƴar karamar tsaki, kafin ta yi ta maza ta ce “ Ki yi hakuri Baby, abinda zan fada miki ba mai daɗi ba ne, an yanka ta tashi.” “ Ban gane ba Mummy, wa aka yanka? Mene ne ya tashi?” zuciyarta cike da shakkarta, ta daure ta sake cewa, “Maganarki da Ahmad tana tangal-tangal, yau General ke sanar min ya yi masa mata...” “Kutumar babbar kaza kazan can!” Neema ta ja wata doguwar ashar cike da rashin tarbiya tana miƙewa zaune daga kwancen da take, ƙanƙance ido ta yi cike da fitsara ta ce “Mummy! Mummy! Mummy! So nawa na kira ki.” Aunty Rukayya da ke amsa duk kiran da take yi mata, a sanyaye ta ce, “So uku Baby.” “Wallahi ba ku isa ba daga ke har mijinki kun yi ƙadan ku wulaƙanta ni, Ina son AA, ina son na auresa kin fi kowa sanin hakan, kuma wallahi tallahi ba zan taba hakura ba, ko sama da ƙasa za su hade sai Ahmad ya aureni, babu ruwana da yadda za ki yi, ni dai kawai ki aura min shi, idan kina buƙatar kwanciyar hankalina.” cikin rarrashi da kwantar da kai Anty Rukayya ta ce “ Na sani Na'eemarh, na san kina son Ahmad, wannan dalilin ne ma yasa na kira ki domin mu hada hannu mu yi wa tufkar hanci tun wuri, kin san ina son ki, kuma ina son duk abin da kike so, wallahi tallahi na fi ki son na ga kin mallaki Ahmad, ba zan yi saken da za ki rasa shi ba, ki kwantar min da hankalinki, in dai ina da rai da lafiya Ahmad zai aure ki, na yi miki alkawari.“ shiru kamar ba za ta sake magana ba, sai kuma ta fesar da numfashi kafin ta ce “ Yanzu me ki ke so na yi?“ “ Ki dawo 9ja, ki matso kusa da Ahmad ki nemi kusanci da shi, ki bayyana masa soyayyaki, ta haka ne kawai zan iya cika miki burinki.“ “ Ai ko ba ki ce ba dama dole zan dawo, don wallahi tallahi duk wacce ta auri Ahmad ta auran ma kanta masifa, don haka maganin kar a yi kar ma a soma, ki saka idon ganina ko da yaushe cikin sati mai kamawa.” Murmushi Aunty Rukayya ta yi nan da nan farin ciki ya bayyana a fuskarta, tana jin kamar ta janyo tilon yar Tata ta cikin waya ta rungume tsabar so da ƙauna, “ Mummy ina buƙatar kudi, account ɗina ya yi ƙasa. ” Muryar Neema ya dawo da ita hayyacinta, gabanta ya faɗi domin cikin satin nan ta tura mata kuɗi masu kaurin gaske, amma saboda gudun ɓacin ranta, sai ta hadiyi miyau ta yi yar dariyar yaƙe cikin yanayin wasa ta ce, “Kai Baby, kina nufin har kudin ran nan sun ƙare?" “ E sun ƙare, ina buƙatar wasu, ko babu?” Yadda ta yi maganar cike da raini, amma sam Aunty Rukayya bata ga hakan ba, da sauri ta ce, “ No a kwai kuɗi baby, ba Ni minti biyu.“ tana gama wayar ta datse kiran a take a tsaye a inda take ta yi mata transfer na 2M, sannan ta sake kiranta, “ Oh thank you My lovely Mummy, Nagode Sosai i luv you so much. Muahhh! Ta sakar mata kiss a kunne daga haka ƙit ta kashe wayarta, ba tare da ta bata damar sake yin magana ba. Murmushi Aunty Rukayya ta yi tana bin wayar da kallo zuciyarta wasai domin kalaman Baby na karshe sun wanke duk wani damuwar da ta cusa mata na tatsar ta da take yi kamar shanuwar tatsa......
****************************
Tun a hanya AA ya kira Mother ya sanar mata da zuwansa. Daga muryarsa da yadda yake magana ɗaɗdaya Mother ta fahimci yana da damuwa, sai dai bata ce komai ba tunda gashi nan zuwa gidan nata koma mene ne za ta ji. Mikewa ta yi ta sauka ƙasa zuwa kitchen domin ta samar masa abinci, tunda bata san da zuwa nasa ba girkinta kadan ta yi ita da Suraj kuma ba wani na musamman ba ne, ta san ba zai so shi ba, sauƙinta ma tana da sauran fura, ta san shi zai fara nema kafin wani abin. Kai tsaye frizan da take ajiye masa damammiyar furan ta nufa, ta bude da nufin ta dauka ta gyara masa kafin ya iso, sai dai wajen wayam, ko bowl ɗin babu a balle ta saka ran samun ko ƙadan ne a ciki. Goshi ta dade cike da takaici tana mai jerowa Suraj addu'ar shiriya a zuciya, ta san dai shine ya dauka domin su biyu ne a gidan, baya da haka sai da ya tambaye ta, ta ce masa kar ya sha na Bunayya ne amma da yake shi mai kunnen ƙashi ne, ya shammaceta ya ɗauke, tun da ya mayar da ita kakarsa. Ɗakinsa ta nufa a fusace tana mita, domin ta kirasa ya zo ya je wajen Inna idan Allah ya taimaka a samu rogowar ajiya a wajenta, sai ta dama masa wani tunda tana da sauran kindirmo mai kyau a fridge, yana kwance ya yi ɗaɗɗaya akan makekiyar gadonsa yana sharar bacci, daga shi sai yar boxes. ga bowl ɗin furan nan kife a tsakiyar ɗakin. Ɗakin ta shiga bi da kallo tana girgiza kai, ko ina a hargitse, kamar ba jiya ta ɓata lokaci mai yawa wajen gyara masa ɗakin ba, kayan cikin wardrobe kusan rabi a ƙasa, ga takardu ya barbaza wasu a kan gado wasu a ƙasa kar dardumar da ya yi sallah, banda ledojin dangin su chocolate da ya sha ya zuzzuba su duk inda ya samu kofar toilet a bude, ga kofuna da plate da ya ci abinci girgiza kai ta yi cike da taikaci, “Oh ni Asma'u wai ɗakin saurayi ɗan jami'a kenan kamar na ɗan goye saboda sakarci, zan ga ranar da za ka girma suraj.” ta kai karshen zancen tare da kai masa duka a baya, firgigit ya mike tare da banƙarewa yana sosa bayan idanunsa na sake lumshewa saboda barci. “Surajuddeen!“ Ta kira sunansa da karfi, da sauri ya ɗago shanyayyun idanunsa cike da barci ya zuba mata, sai lokacin ya kula da wanzuwarta a ɗakin, “ Mother!” ya faɗa yana wartsakewa da kyau, hararar ta ɓalla masa, kafin ta ce, “Wato da na hana ka daukar furan Bunayya jiya, sai da ka dauƙa din in yi abinda zan yi ko?” Da sauri ya girgiza kai, “ To ba zan yi komai ba, Allah ya shirye ka. Sai ka tashi ka shiga gidansu Maamah, ka tambaya min Inna idan da ragowar ajiyar fura a wajenta ta bani, ga Bunayya nan a hanyan zuwa yanzu.” kalamanta na karshe suka shi sauyin miƙewa ya fito daga gadon ya faɗa toilet, ya yi brush ya wanke fuska ya fito, a gurguje ya dauki jallabiya ya zura ya yi waje. Mother dake tsaye tana kallonsa ta girgiza kai, kawai ta fito to rufo masa kofar ta koma kitchen ta ji gaba da aikin gabanta kafin ya dawo.
Gida huɗu ne tsakanin gidansu da gidansu Maamah a cikin Estate, don haka bai yi wata doguwar tafiya ba ya isa, akwai tazara mai yawa tsakanin gidansu Maamah da gidansu Suraj, ta wajen kyau da ababen more rayuwa, duk da tsari da zubin ganinsu ɗaya, sai dai gidan su Maamah ba gidan sama bane saɓanin na su Suraj wanda yana daya daga cikin manyan gidajen dake cikin Estate ɗin.
Tun daga bakin kofa ya fara rangaɗa sallama yana kiran Inna, Maamah dake kwance a doguwar kujerar falo ta mike zaune tana hararar kofa da jiran ya ƙasaro, Inna kuma dake kitchen ta fito da sauri tana amsa sallamarsa.
Dattijuwar Bafulatana kyakkyawa da ita, ta tarɓesa cikin tsananin fara'a. Shima da fara’a ya ƙarasa kusa da ita ya ɗan risuna ya ce “Jam na Inna?” Murmushi fal fuskarta “Jam tan, Surajuddeen,” ta amsa da gangariyar fullancinta na kwararrur ba irin tasa ta masu ci da karfi ba,. Ya sosa kai ya ɗaga kai alamar yana tunani , sannan ya ƙara cewa, “On jaaraama?” Wannan karon dariya sosai Inna ta yi kafin ta ce“Jam tan, alhamdulillah. A jaaraama, on?” Shima dariyar ya yi cike da jin daɗin bai ɓace a gaisuwar ba yau kamar yadda suke yi kullum sai ta ci gyaransa, ya sake c wa “Jam tan, Alhmdlh Inna.” Inna ta girgiza kai cike da nishaɗi ta ce “Ehee, lallai Surajudeen ya zama fulfulde . Ka yi kokari sosai, yaron kirki.” “Laamiiɗo haala, a arii ɗum!” Maamah ta faɗa tana hararansa, juyowa ya yi ya kalleta ba tare da ya game me tace ba, ya ce, “E ɗin.” Dariya su ka yi a tare ita da Inna don suna da tabbacin ya dai amsa ne kawai ba tare da yasan me ta faɗa ba. Sun ɗan taba wasa da Maamah kamar yadda suka saba matsayinta na kawarsa kafin ya isar da saƙon Mother. “ Ayya, ai kuwa babu furan nan Surajo, yanzu dai na ke yi, ka gansi can a turmi,ka bashi hakuri ka she ya jira ƙadan, yanzu zan gama sai Maamah ta kawo mata, bai yi magana da wuri ba, da tunda safe zan yi mata ai.” sai da Suraj ya gama shan dariyar Hausar Inna kafin ya fice daga gidan don ya kai saƙo.
Yana daf da shiga gudansu motar Ya B na sawo kai, dakatawa ya yi har ya kasaro, a tare suka karewa ciki bayan mai gadi ya budewa AA get, duk da halin da zuciyarsa ke ciki sai da ya sakarwa Suraj murmushin ya mika masa hannu suka gaisa, kafin su shiga cikin gidan hannayensu sarƙe dana juna.
******************
Kasancewar shagon salon din babba, kuma babu layi don sun je da wuri yasa nan da nan aka kammala yi musu abinda ya kaisu, Salman ya zauna a mota ya jira su har suka fito, suka shiga ya kamo hanya domin ya kaisu wajen shopping kamar yadda suka so, Suraj ya kira, don ya sanar da shi su hadu a can, Suraj ya sanar da shi ba zai samu fitowa ba saboda Ya B ya zo gidansu yanzu, zaro ido Salman ya yi ya ce, “ Ka rantse.” “ Wallahi ko na kira ka bidiyo call ne don ka tabbatar, “ No bar shi, ga mu nan zuwa gidan yanzu muma.“ yana katse wayar ya karya kan mota zuwa gidan Mother ba tare da ya nemi shawarar abokan tafiyar nasa ba a kokarinsa na yi musu surprise.......
Yau za ku ga ba yawa, hakan ya faru ne saboda kuma comment da reaction ɗin ku na juya ba yawa, ehe daidai ruwa daidai gari😜 [5/14, 6:00 AM] Oum khadeejarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀
By
AyshaNalado
Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍
BOOK 1
Page 18
Sosai Mother ta yi busy a kitchen, hakan yasa ba ta ji shigowar su Suraj ba. Zama AA ya yi a ɗaya daga cikin kujerun falon ya lumshe idanu tare da dafe kansa da ke sara masa, ganin haka yasa Suraj jiki ba kwari ya yi kitchen domin kiranta, duk wani karsashi da murnar ganin Yayan nasa na juyewa zuwa damuwa, saboda damuwar da ya gani a tattare da shi. Motsin shigowarsa kitchen ɗin ya janyo hankalinta, ganinsa hannu sake, nan take fuskarta ya canza “Oh Allah! Ba a dace ba ko?” ya gyaɗa kai “ Ai duk laifinka ne Surajudeen, yanzu ya kake so na yi da Bunayya?” Ta karshe maganar tana jifansa da harara, ƙasa ƙasa ya ce “Yau ni dai na shiga uku, na taɓa ajiyar ɗan gwal.” “ Me ka ce?” Ta tambaya tana matsowa da cokalin miya ta roba a hannunta, da sauri ya yi baya yana ƴar dariya, “Inna ta ce fa za ta aiko miki, yanzu take yi, ta ma kusa gamawa.” Ajiyar zuciya ta sauke, tana nuna shi da cokalin ta ce, “Allah yaso ka.” ta yi ƙwafa ta juya ta ci gaba da aikinta. “Ya B ɗin ma ya iso fa.” Juyowa ta yi “Yana ina?” “Falo, ina ganin kamar baya jin daɗi, very upset da shi.” gabanta ya ɗan faɗi, dama ta zargin haka, gas ta rage, ta ajiye cokalin suka fito falon tare da Suraj. Har ta zauna gefensa ba shi da labari, “Bunayya.” Ta kira sunansa a hankali cikin taushi, amma shiru, hakan yasa ta ɗan kara ɗaga sauti. A hankali ya ɗago ya zuba mata idanunsa da suka sauya launi. “Na'am Mother.” “Mene ne?” Ya girgiza kai ƙadan kafin ya ce, “Babu.” “Akwai.” ta bashi amsa kai tsaye tana kallosa cikin ido, Dauke kai ya yi daga kallon titsiyen da take yi masa, ya ce. “Ina jin yunwa Mother, a bani fura.” Sai da ta juyo ta wullawa Suraj dake zaune yana kallonsu kamar ya samu TV kallon ka gani ko, kafin ta sauke ajiyar zuciya, ta ce “Babu fura a ƙasa Bunayya, na aika yanzu ake yi, ka yi hakuri, ban san za ka zo da wuri ba, amma bari na hada maka tea ka sha kafin na ƙarasa maka girki.” Sai da ya lumshe ido ya bude kafin ya girgiza kai ya ce, “ No furan kawai nake buƙata zan jira.” da kai ta amsa masa. Sai kawai ya miƙe ya yi sama zuwa ɗakinsa ba tare da ya sake cewa komai ba. Kallon juna Suraj da Mother su ka yi, “Mother me yake damunsa?” “Ban sani ba Suraj, gabana na faɗuwa, ina jin tsoron wani abu.” Da sauri ya ce “Mene ne?” “Sanin naka ba shi da amfani.” Sai kuma ta mike ta wuce kitchen don ci gaba don girkinta. Zamewa Suraj ya yi ya kwanta a 3 sita, yana jin zuciyarsa babu daɗi, gafe daya kuma yana jiran karsawowar su Salman dake hanya, ya so yau ya gabatar da Salmah a wajen Ya B da Mother, ya so kwarai ranar da Salmah za ta fara taka ƙafa cikin gidansu ya yi mata tarba ta musamman, sai dai yanayin Ya B ya rusa masa tsari, Ya B ba kawai Yaya bane a garesa, rabin jikinsa ne, damuwarsa tasa ce haka farin cikinsa nasa ne, yana jinsa a ransa fiye da duk wani hasashe, shi ya raine shi da hannuwansa, a tsakanin kafaɗa da kirjinsa ya bude ido har ya fahimci wanene shi, akan Ya B ya fara sanin soyayya da daɗinta.
Kamar yadda Inna ta yi alkawari, bayan fitar Suraj cikin ƙanƙanin lokaci ta kammala haɗa, lafiayyar furarta dakan hannu da ta ji kayan ƙamshi, ta cura da yawa ta zuba a tsabtabbiyar roba mai murfi, sannan ta kwalawa Maamah dake tsakar gida tana wankin fararen uniform ɗinta na school of midwife kira. “Hee inna.“ ta amsa “ki zo ki kaiwa Umman Surajo furan nan.” “ Hee Inna, mi ɗo.” ta faɗa tana cire hannu a ruwan wankin, ta dauraye tare da miƙewa, baƙin hijabinta dake kan igiyar shanya ta ja ta saka, ta shiga ɗaki ta karɓi robar furar ta tafi.
Yana shiga ɗakin, kai tsaye fridge ya nufa, ya buɗe ya dauki ruwa mai sanyi, ya lalubi bakin gado ya zauna, ya ɓalle murfin goron ya kafa kai ya shanye, wurgi ya yi da goron, kafin ya koma da baya ya kwanta daga zaune da yake kafafunsa a ƙasa yana kallon saman ɗakin, kirjinsa ya yi zafi, zuciyarsa kamar zata kama da wuta, zai iya jurar komai, banda abu ɗaya, zai iya yin biyayya a komai banda abu ɗaya, bai taɓa yin jayayya da umarnin Abba ba, tun da ya mallakin hankalin kansa, kuma baya so ya fara a yanzu, zazzafar huci ya furzar sannan cikin raunatacciyar murya ya furta. “Abba… why? Abba me yasa kake son shiga gonar NURIE? Abba ka yi haƙuri, ban taɓa gaya maka ba, my heart belongs to someone else, the girl that’s so, so, so special… beautiful, rare, and impossible to forget.” lumshe idanu ya yi, lokaci guda kuma wata irin haɗaɗɗiyar murmushi wanda kana gani kasan kai tsaye daga zuciyarsa take, ta suɓuce masa. “Na tsane ka!” kamar saukar aradu muryar yarinyar ya ratsa kunnuwansa, babu shiri wa ware idanu lokaci guda murmushin fuskarta ta ɓace ɓat, "koɗaɗɗiyar fuskata yanzu ka fara ganinta, ba zan kyale ka ba har sai na ga bayan ka, na yi maka alkawarin sai na rusa dukkan farin cikin ka, mugu kawai, na tsane ka, na tsane ka, na tsare ka!…" Haka kalmar ya dinga amsa kuwwa a kunnuwansa, take jikinsa ya dauƙi rawa, ya toshe kunnuwansa tare da rintse ido da ƙarfi, amma ina babu abinda ya ragu, domin sautin daga zuciyarsa take fitowa kai tsaye tana zarcewa ƙwaƙwalwarsa. Ya fi mintuna biyar a haka kafin, ringing ɗin wayarsa ta dawo da shi hayyacinsa, ɗaga wa ya yi kai tsaye ba tare da ya duba ko wanene ba, daga ɗaya bangaren, ya ji muryar da ya sanya shi ware idanu, “Alhmdlh Maigida akwai kyakkyawar albishir, ina bukatar haduwa da kai da gaggawa idan babu damuwa.” zaune ya karkare miƙewa, muryarsa na ɗan rawa ya ce, “Giɗaɗo, an same su ne?.” “A'a amma da yiwuwar samun nasu nan da ko wanne lokaci.” Sai da ya sauke wani irin ajiyar zuciya, kafin ya ce, “ Mu haɗu yanzu a palace.” yana katse wayar ya miƙe tare da wurgata a aljihu, kai tsaye ya fice daga ɗakin da sassarfa. Daidai wannan lokacin Maamah ta sake rangaɗa sallama a bakin falon Mother, jin ba a amsata ba a karo na biyu ya sa ta shigo kan ta tsaye da tunanin ko basa ƙasan ne, tunda gidan ba baƙonta ba ne.