Kenza eBookz

Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 14

Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 14

Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 14: Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 14. Sautin taƙun da ta juyo daga stainrcase, yasa kai tsaye nan idanunta ya…

3,269 words

Sautin taƙun da ta juyo daga stainrcase, yasa kai tsaye nan idanunta ya sauka. Wani irin wuntsilawa ƙirjinta ya yi lokacin da idanunta ya sauka a kan mutumin da ke saukowa daga kan stainrs ɗin, da sauri ta yi baya ta saki robar furar tana zare ido, tare da kiran sunan Allah, sandarewa ta yi a wajen ta rasa abin yi, sai kuma ta juya ta kwasa da wani irin gudu kamar zararriya, ta fice daga gidan, tana waige.

Yanayin da yake ciki ya sanya Mother kasa yi masa musu, lokacin da yake bata uzirinsa na kiran gaggawar da aka yi masa, da sassarfa ya fice daga falon Suraj ya biyo bayansa, suna fitowa waje, motar Salman na kutso kai cikin gidan, tun daga nesa ta hangesa, gabanta ya yi mummunar faɗuwar, shigar nan tasa ta ɓadda kama, ta yi imanin tafi kowa ganesa da shi. Suraj ya hango su, amma uzurin yayan nasa ya hanasa karasowa, sai da ya tabbatar ya shiga motarsa ya tayar, sannan ya nufo su cike da farin ciki, sun na tsattsaye bakin motar, dauke kai Salmah ta yi ta sha mur don sai da aka kai ruwa rana tsakaninta da Salman kamin ta amince ta biyo su, Aysha kam gaba ɗaya hankalinta na kan motar AA dake kokarin ficewa daga harabar gidan.

Gaba ɗaya hankalinsu ya yi gaba domin Suraj har ya kama hannun Salman sun yi ciki Salmah ta bi bayansu, taba harare harare, hakan yasa ta juya ta fice da gudu ta bi bayan motar tasa. Burinta bai wuce ta sake nuna masa koɗɗaɗɗiyar fuskarta, kamar yadda ta yi masa alkawari, sai dai cikin rashin sa'a bai juyo ba balle yasan da zamanta, ciza yatsa ta yi, cike da takaici lokacin guda zuciyarta na ƙara tunzurata, tana jin har idan ta bari wannan damar ya wuce mata ta yi babbar asara, “Ba za ka taɓa tsare min ba, wallahi sai ka ga koɗaɗɗiyar fuskar wacce za ta zama ajalinka Babangida.” Cikin ɓacin rai da rufewar ido, ta miƙa hannu ta tari mai adadaita sawun dake wucewa, ta fara yi masa nuni da motar A A da ta fara yi musu nisa tana basa umarnin bin bayansa.

Duk abinda ke faruwa, akan idanun Ussy da Jarumi yaran A'A da suka yi masa tsakiyar sirri dake zaune cikin mota, suna jira ya yi ɗan nisa su rufa masa baya kamar yadda suka saba, Ussy ya ce, “ Wannan yarinyar victim ce, Maigida take bibiya.” “ Da wanne ta zo.” cewar Jarumi, “ Ban sani ba, amma bana tunanin ita ma kamar sauran ƴan matan ne, duba da yanayinta.” Ussy ya amsa masa idanunsa akan Aysha, “ Hakkinmu mu kare lafiyar Megida, domin don haka ake biyanmu.” Jarumi ya yi maganar tare da kama handle ɗin motar zai fita, “Dakata kasan baya son duk wata harka data shafi mace, mu fara tuntubarsa first.” “Ka yi kyan kai.“ daidai lokacin napep din ya fara tafiya bayan ta shiga, take Ussy ya tada motar su ka fara bin bayansu, yayinda Jarumi ya shiga lalubar A'A a waya, cikin sa'a ya ɗaga, ba tare da kwana-kwana ba, ya sanar masa abinda ke faruwa, kai tsaye zuciyarsa ya bashi yarinyar ce, “ Ku zo da ita.” shine kawai umarnin da ya ba su ya kashe wayar. Ci gaba da bin gefensu suka yi har sai da suka daidaici wajen da babu mutanen kafin suka sha gabansu, babu ɓata lokaci Jarumi ya fito ya nufo napep ɗin bayan ya daure rabin fuskarsa da hankicif, ya kwama bakin madubi, duk da gardama da kafiya irinta Aysha ganin bindiga yau muraran yasa ta yi laushi, sai zare ido take yi tana ambaton Allah a zuciya, ƙirjinta kuwa kamar zai fashe tsabar bugu. Lokacin da ya bata umarnin fitowa ta shiga motarsu ne, ta so tirjewa, sai da ya yi mata jan ido, da kan shi ya saka hannu ya ficikota daga keken, ya wurgata bayan motarsu ya rufe, ya shiga gaba, Ussy ya taka da gudu suka bar wajen bayan sun baɗe mai keke da ƙura.

Yadda ta shigo gidan a gigice tana hali yasa Inna dake zaune tana tsintar shinkafa miƙewa, ta saki tiren ba tare da ta shirya ba. Kai tsaye a kanta Maamah ta faɗa tana wani irin haki tare da nuna bayanta, tana yi mata bebenci. Jijjigata Inna ta shiga yi hankalinta a matukar tashe, “Innalillahi wa Inna ilaihi! Maryam, Maryama, Mero, Maryoji. Mi waɗi a boni! Me ya same ki ? Ko ɗume waɗata? “ Na ganshi. Inna na ganshi.” “ Mi waɗi a boni, to Maryoji heɓi gamo!, Allah ka shiga lamarinmu.” sai kuma ta hau tofeta da addu'a. Sake shigewa jikin Inna Maamah ta yi, ta rike hannunwanta ta ce “ Da gaske na yi gamo, Inna ki yi min addu'a, ki karanta min Ayatul kursiyyu da falaki da nasi.” Jin haka yasa Inna ta ƙara kaimi, tun tana yi a zuciya har ta koma f yi a bayyane. A hankali nutsuwa ya fara saukar mata, ta lumshe ido ta shi shiru tana sauraren kira'ar Inna da harshenta daya karye da yarenta na fulfulde, kusan mintuna goma sha biyar su ka yi a haka, kafin ta sauke wani nannauyar ajiyar zuciya, kamar me ƙurji a baki, ta ce, “Inna!” Dakatawa Inna ta yi ta amsa da “ Na'am Maryama.” Ɗan jim ta yi kafin ta sake cewa, “ Hamma na gani.” “ Wani Hamman?” Da sauri Inna ta tambaya gabanta na ɗan faɗuwa. “Hamma Babangida.” “ Wane ne haka kuma Mero?” ta sake tambaya cikin yanayin ruɗu da tashin hankalin da ya kasa ɓoyuwa a tattare da ita, duk da iya bakin kokarinta da ta yi wajen dannewar. “ Inna Hamma Babangida na Adda Shatou.” Cak Inna ta dakata, wutar numfashinta ya dauƙe na wucin gadi, kafin ta yi namijin kokarin janyo shi da karfin tsiya, ta saki wani irin kakkauran ajiyar zuciya, wanda ya sanya Maamah sauri sakinta, sai kuma ta rikota ganin kamar tana shirin silalewa ta kwanta a wajen, “Ya Salam! Sannu inna.” ta gyaɗa kai dakyar alamar amsawa, kafin ta ce, “ Ki kaini ɗaki Maryam zan kwanta.” [5/14, 6:00 AM] Oum khadeejarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

By

AyshaNalado

Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍

BOOK 1

Page 19

Lokaci ɗaya Inna ta fita daga hayyacinta, ta shiga sauke numfashi dakyar, tana sakin ajiyar zuciya mai karfi lokaci bayan lokaci, kana kallon fuskarta zaka fahimci halin da zuciyarsa ke ciki na tsananin damuwa. Sosai hankalin Maamah ya tashi, sai lokacin ta dawo hayyacinta ta gane katoɓarar da ta yi, ta yi dana sanin sanar da ita wannan maganar yafi cikin carɓi, ko bata tambaya ba tasan ciwonta ne ke son tashi na hawan jini, wanda ta yi imanin idan da abinda ke saurin tado mata shi, to zancen Adda Shatou ne, kuma bata da tantama akan ta dalilinta ta samu larurar. Har yau da ake neman shekara tara da faruwar abinda ya faru, ta kasa sabo da rashin Shatou, wannan na ɗaya daga cikin dalilin da ya sanya daga Baffa har ita babu mai ambaton sunanta ko wani abu daya shafe ta a gabanta, saboda irin wannan yanayin da take shiga. Ko da ta taimaka mata ta kaita ɗaki bata kwantar da ita ba, sai da ta ɓalla magungunanta ta bata ta sha. Kwanciya Inna ta yi ta lumshe ido, zuciyarta cike da bege da kewar ɗiyar tata mai tsanani, tana jin idan har ta mutu ba ta yi ido biyu da Shatou ta nemi yafiyarta ba, to tabbas Ubangiji zai tuhumeta kuma zai hukuntata a kan hakkinta, har yau laifin kanta kaɗai take gani akan abin da ya faru, kullum tuhumar kanta take yi a kan me yasa bata saurare ta ba , a lokacin da take kuks tana rungumar ƙafafunta? Me yasa bata jata a jiki ta ji damuwar ta ba? Me yasa ta kasa yi mata uzuri, ta kasa sarrafa fushinta akan yar tata a lokacin da kowa ya gaza fahimtarta, a matsayin ta na uwa, itama sai ta saje da sauran mutane, itama sai idanunta su ka rufe har ta mance da irin tarbiya da nutsuwar Aysha, ta kasa tantance abinda zata iya aikata da kuma aikin kaddara wanda ya riga fata. A hankali ta shiga motsa bakinta ba tare da ta buɗe idanu ba, “Ya Allah ka tsare min ita a duk inda take, eɗe e nder kene, eɗe waɗa mo e laawol moƴƴol, ka kare min mutuncinta, wonaa sabu mo mi waɗi, ya Rabbi.” Jin irin addu'ar da take yi ya sanya Maamah saurin ficewa ɗaga ɗakin zuciyarta na rawa, kai tsaye ɗakinta ta nufa ta faɗa kan godo ta saki wani irin kuka mai cin rai, kukan da suka kwashe shekaru suna rairawa ita da iyayenta, a fili da zuciya, tabbas Ubangiji sai ya yi musu sakayya, hakika an cutar da su...

A bangaren su Salmah kuwa, har suka ƙarasa cikin tamfatsetsen falon Mother, ba su kula da rashin Aysha a tare da su ba. Mother dake zaune a ɗaya daga cikin kujerun falon , ta dago da fara'a tana kallonsu, kai tsaye Salman gabanta ya nufa, ya risina yana gaisheta cikin yanayin da ke nuni da tsantsar sabon da su ka yi da juna. Suraj dake tsaye ya juyo ya saci kalon mutuniyar tasa da ta coge daga bakin kujera, ba ƙaramin kyau ta yi masa ba, har ya kasa dauke ido daga kanta, zuciyarsa na wani buɗawa saboda nishaɗin ganinta a kusa da shi da yake yi, Allah ya sani yana kaunar Salmah so mara iyaka, wanda yake jin a shirye yake da aikata komai domin mallakarta, kuma idan za a saka masa bindiga ba zai ce ga abinda ke daukar hankalinsa gareta ba, kawai so ne sadidan minal lahi, wanda ya fara shi tun daga gani na farko da ya yi mata, tun yana daukar abin wasa har ya fahimci da gaske fa sonta yake so irin na aure so irin na rayuwa a tare har abadan da'iman. Duk da ɓacin ran da take ciki hakan bai hanata gaisar da Mother a mutunce cike da tsantsar ladabi ba, sai dai fuskarta a tamke babu alamar Rahama “Lafiya ƙalau Salmah, karaso ciki mana mu gaisa da kyau.” Mother ta faɗa tana miƙa mata hannu karasawa ta yi zata zube a gabanta, ta janyo ta ta zaunar kusa da ita, tana ci gaba da faɗin, “Tabarkallah masha Allah, yau dai naga ƴata Salmah, to ya kike ya Ammienku.” “Tana Lafiya.” “Ma sha Allah, haka a ke so. Am Suraj kawo wa baƙuwa ruwa, don dai shi Salman ɗan gida ne.” Mother ta faɗa tare da sauke idanunta a kansa, tsananin shagaltar da ya yi a bagen Salmah yasa bai san ta yi maganar ba, sosai mamaki ya cika Mother ganin irin kallon da yake binta da shi, abinda ta karanta a cikin kwayar idanuwansa, ya sanya bata san sanda ta kira sunansa da karfi ba “Surajudeen!” Firgigit ya juyo, suna haɗa idanu ya yi ƙasa da kai, sai kuma ya dake ya ɗago ya kalleta tuna a gaban Salmah suke kar ya yi abinda za a yarfa shi, Salmah ta sake raina shi “ Na'am Mother.“ ya amsa da wata kamillayar murya mai cike da nutsuwa, wacce Mother bata san shi da shi ba, yana wani kame fuska. Zancen da za ta yi ne ta nema ta rasa saboda mamaki “Ikon Allah sai kallo.” Mother ta faɗa a ranta tana riƙe haɓa, sai kuma ta mike ta yi kitchen ɗin da kanta. Tana tashi Suraj ya zauna kusa da Salmah, da tunda ta shiga ko gefen da yake bata kalla ba, tana nan a kan bakanta na alkawarin da ta yi na daina sake mai fuska don taga rainin nasa na neman wuce gona. “Welcome Salmahtah.” Ya furta ƙasa ƙasa, yi ta yi kamar ba ta ji ba, hankalinta na kan wayarta sai da ta kwashe kusan sakan talatin kafin ta dago ta yi masa wata shegiyar kallo na tsantsar raini kafin ta ce, “ Thank you.” ba tare da kallesa ba. Murmushi ya saki mai taushi, don hakan da ta yi ba ƙaramin tafiya da shi ta yi ba. Dogon tsaki Salman da ke binsu da kallo ya ja cike da takaici kafin ya ce, “Ku wai ina Aysha?” sai lokacin gaba ɗaya hankalinsu ya kai ga rashinta, Salmah ta yi tsammanin ta ɗan tsaya wani abu kamar amsa call haka shi yasa bata biyo su ba, kasancewar kuma tana fushi da ita akan dan hatsaniyar da suka yi a hanya, yada bata koma ta jira ba ta yi shigowarta. Sai dai yanzu da Salman ya yi magana hankalinta ya rabu, domin koma mai ta tsaya yi zuwa yanzu ya ci ace ta shigo ai. “Bata shigo ba, ban san me ya tsayar da ita har yanzu ba, ko zaka duba.” “Wace ce?” Mother da ta dawo dauke da tiren ruwa da drinks, ta tambaya. “ Aysha yar uwarmu ce tare muke, kuma mun ga har yanzu bata shigo ba.” “ Ah ahh, maza dubo ta Suraj ko lafiya.” kafin ma ta gama maganar Salman ya mike don haka suka fice tare da Suraj ɗin. Fitarsu kamar da minti shida, su ka dawo, da damuwa a fuskokinsu, Salmah ce kadai a falon don Mother data ajiye tiren ta koma kitchen, “Ba mu ganta ba fa.” Salman ya fada yana kallon Salmah, “ Kamar ya? ” “ Kamar yadda ki ka ji, kuma har megadi mun tambaya.” Murmushi ta yi Irin na an raina ma mutum wayon nan, ganin hakan yasa Salman ya kara cin serious ya ce, “ Ke wallahi da gaske fa na ke yi.” wannan karon Dukansu suna ɗunguma duka sake komawa wajen don sake dubata.

A daidai wannan lokacin ne, motar su Ussy ta faka a tsakiyar farfajiyar katafariyar gidan AA dake by pass. Jarumi ne ya fito kamar ɗazu ya bude bayan motar, ya watsa mata idanunsa masu ban tsoro kafin da dakakkiyar muryarsa ta garada ya ce, “Fito.” idanunta da suka rine suka juye lokaci guda daya dai babu ɗigon hawaye a cikinsu ta watsa mai, a daidai wannan lokacin tabbas da za a tsaka jikinta za a iya ganinsa a bushe babu jini saboda matsanancin Firgici da tashin hankalin da take ciki, zuciyarta kuwa kamar zata faso kirji, amma saboda karfin hali fuskarta a bushe, ko ƙadan yanayinta bai nuna hakan a zahiri ba...

Ku yi hakuri babu yawa, yau na fita, da kamar ma ba zan yi ba, na ce dai bari na daure ko yaya ce, mu tara gobe da yardar Allah. [5/14, 6:00 AM] Oum khadeejarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

By

AyshaNalado

Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍

BOOK 1

Page 20

“Ki fito.” Ya sake furtawa a karo na biyu, fuskarsa babu alamar rangwame, razannanun idanuwansa kafe cikin nata da suka juye saboda tashin hankali, yayinda a zuciyarsa yake jinjinawa karfin halin yarinyar. Dakyar ta bude bakinta da ya bushe ƙamas, muryarta na ɗan rawa ta ce “Su waye ku? Me ku ke so a gare ni? Me na yi... “Fito na ce.” ya katse ta da cewa cikin tsawa mai firgitarwa tare da dukan saman motar a fusace. Sai da ta saki ɗan guntun fitsari tsabar razani, sai dai kafiya irin tata, maimakon ta fito sai ta sake shigewa can karshen motar ta maƙure tana faɗin, “Ba zan fito ba, ai ban maku komai ba, ni ku mayar da ni gida.” Duk yadda yake daure wa ya riƙe fushinsa kasa jurewa ya yi wannan karon, a fusace ya zagaya ta bangaren da ta koma, ya bude tare da fincikota waje, ya hade hannyaneta waje guda ya yi mata riƙon maza, ya shiga janta da karfi tana turjewa, tare da faɗin “Ka kyale ni.” bai saurareta ba, sai da ya danganata da ƙofar rantsattsen grand two-storey mansion ɗin da ke farkon gidan wanda ya fi kowanne gini da ke cikin harabar gidan girma da haɗuwa. Ba tare da ya saki hannunta ba, ya mika hannunsa ɗaya ya dannan wasu madannai dake jikin kofar wajen, take ta bude bayan ta yi scan na fuska da yatsarsa. Hankaɗata ciki ya yi har sai da ta kusa kifawa, bai ɓata lokaci ba ya mayar da kofar ya rufe ta waje. A kunneta motarsu ta bar cikin gidan a guje, take wani irin shiru ya ratsa ƙwaƙwalwarta, tabbacin babu wani mahalukin dake motsi a cikin gidan sai ita rak. Ƙafafunta ne suka ɗauki rawa, tsoro da tashin hankalin da take dannewa da karfin tsiya suka bayyana a kan fuskarta, motsi ta ji daga bayanta hakan yasa ta juya a tsorace da bala'in sauri, babu kowa sai iska dake ƙada fararen labulayen da ke kewaye da falon, rarraba idanunta ta shiga yi a wargajejen falon da ba shi da wadataccen haske. tsananin girmansa yasa ta ga kamar yana juya mata take ta zube ƙasa tare da fashe da wani irin kuka, ji ta yi sautin muryarta ya karaɗe falon tamkar wacce ta yi magana a amsa kuwwa, hakan ya karasa rikitata ta yi saurin dunkulewa waje guda ta cusa kanta cikin ƙafafunta jikinta na rawa kamar kazar da tasha dukan ruwan sama.

Kamar wasa karamar magana ta zama babba, tun su Salman na saka ran ganin Aysha a kusa har lamarin ya fara ba su tsoro, domin babu inda ba su duba a ciki da wajen gidan ba, Suraj da megadi tuni suka bazama cikin Estate da makota. yayinda Salmah da Salman su ka shiga rige-rigen kiran layinta, yana ringing amma har ya katse ba a ɗagawa, Mother kan ta hankalinta ya tashi sosai, ta kasa zaune ta kasa tsaye, musamman idan ta tuna yanda ƙasa ta lalace da sace-sacen mutane ga kidnaping da ake yi yanzu na isa da mallaka har makwancin mutum ake binsa a sace, to balle wannan da akan hanya take, amma da tana kyautata zaton in sha Allah ba wata gagarumar matsala bace domin Estate ɗin su a kwai tsaro duk wanda wanda ya shiga ya fita ana da record ɗinsa infact ba ma kowanne irin abin hawa ake bari ya shiga wajen ba sai yantattu, idan kuma moto ko keken haya ne sai mai register.

“To ko dai gida ta tafi?” Salman ya faɗa yana kallon Salmah da a karo na ba adadi ta kara wayarta dake ringing a kunne tana tsammanin jiran a ɗaga. Da sauri ta kallesa, sai kuma ta girgiza kai, ta ce “ Bana tunanin haka, Aysha ba za ta tafi gida sai dai idan da wata matsalar.” “To ko za mu kira Ammie mu tambaya.” “A'a kar ku kira ku ɗaga musu hankali, mu dai kara duba ta tukuna, Khairan in Sha Allah.” Cewar Mother, Salmah ta bude baki za ta yi magana, Suraj da megadi suka shigo tare da megadin makotansu, wanda shine ya yi musu gamsasshen bayani game da ganin da ya yi mata ta tari keke napep ta hau, nan suka dinga jero masa tambayoyi game da yanayinta har ma da shigar jikinta, yana amsa musu daidai, hakan ya kara basu tabbacin tabbas ita ɗin ce. Ajiyar zuciyar samun natsuwa Salmah ta sauke ta daura da faɗin “ To amma me ke faruwa me yasa Aysha za ta yi haka?” Salman ne ya amsa mata “Ki kwantar da hankalinki, kin fi kowa sanin wace ce ita, duk ma abinda ya sanya ta hakan to dalilinta mai karfi ne.” Gyaɗa kai ta yi ta ce, “Kuma haka ne.” Da wannan tunanin suka samu karfin gwiwar komawa cikin gidan suka ci gaba da sabgoginsu bisa umarnin Mother da ta sake kwantar masu da hankali da kalamanta masu taushi...

Readers Also Read