Kenza eBookz

Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 15

Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 15

Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 15: Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 15. Aysha ta dade a dunkule a tsakiyar falon, cikin wannan yanayin ba tare…

3,245 words

Aysha ta dade a dunkule a tsakiyar falon, cikin wannan yanayin ba tare da iya ko ɗaga kai ba balle ta sake kallon inda take, jiran tsammani kawai take yi, ta Allah ta kasance, don tana da tabbacin tata ta kare ta san dai wadannan ba masu garkuwa da mutane ba, yan mafiya ne, ko masu safaran sassan jikin ɗan adam, kuma a irin wannan gida da ake yi wa laƙabi da ihunka banza, ta tabbatar babu wanda zai ji ta balle ya kawo mata dauki sai Allah, gashi harshenta ya yi nauyi kamar an daure mata Allahn ma ta kasa kira, ko numfashi bata iya saukewa da kyau balle ta bude baki, hawaye kuwa zuba suke kamar lalatacce famfo. Kamar daga sama sautinkiran sallar azahar ya ratsa kunnuwanta, wani irin numfashi mai karfi ta ja ta fesar sai kuma ta shiga ajiyar zuciya ta dinga saukewa a jejjere tana jin wata irin nutsuwa na ratsata, tsoron na ɗan raguwa, zuciyarta na karfafa, hakan ya bata damar kama sunan Allah tana ambata. Sannu a hankali komai ya fara lafawa, kamar wacce ake yi wa umarni ta fara ɗago kanta a hankali, abinda ya bata mamaki haske ya cika ɗakin duk fitilu a kunkkune ba kamar ɗazu da babu haske sai wanda ke ratsowa ta window ba, wannan yasa tsoron da ta kasance ciki a ɗazu a yayinda take bin falon da kallo ya ragu kaso hamsin cikin ɗari. Tsananin tsaruwar falon yaso shagaltar da ita har ta so manta halin tsaka mai wuyar da take ciki, domin za ta iya yin rantsuwa tunda take a duniya bata taɓa shiga kayataccen falon da ya yi kyaun wannan ba. Kamar wawiya ta shiga bin ko ina da kallo tun tana ɗari ɗari har ta saki jiki tana kallon aljannar duniya, ko ina fes fes babu alamar kura ko ɗaya, da alamar ana rayuwa a cikin falon sa'i da lokaci. “Ina ne nan? Wane ne ya sanya a ɗauko ta, me ta yi masa me yake nema a gareta?.” waɗan nan sune tambayoyin da suka dinga yawo a kwakwalwarta, sai dai kafin ta samu zarafin hade su a bigire ɗaya ta canki amsarta, idanuwanta suka sauka akan abinda ya sanya ta miƙewa tsaye tana zaro ido cikin tashin hankali, wani katon frame ne manne daga bangon gabas na falon, ji ta yi kawai tana tafiya zuwa gareshi ba tare da ta iya sarrafa ƙafafunta ba, a gabashi ta tsaya, tana bin fuskar wanda ke jikin hoton da kallo, “Ba...ban...gi...da.” Ta furta a rarrabe yayinda ta kai hannu tana shafa hoton, duk da ba asalin hoto bane zane ne, babu abinda ya raba mutumin dake jikin hoto da Babangidanta a zahiri, sanye yake cikin rigar saƙi ta Fulani, kanshi sanye da malfa ya dogara sandarsa da ya rike da hannunsa mai lafiya a ƙasa cikin ciyayi, yayinda ɗaya hannun nasa na dama ake dauke da daurin karaya irinta gargajiya, na saƙale masa shi a wuya kamar dai yadda ake daurin hannu, fuskarsa dauke da sassanyar murmushi. Kanta ne ya shiga juyawa jiri na neman watsar da ita, “Innalillahi wa Inna ilahi raji'un, na shiga uku me ke shirin faruwa.” ta furta tana mai fashewa da kuka, hoton da ke gaba kaɗan da wannan ta kalla, nan ne ta ga abinda ya tsayar mata da numfashi na hucin gadi, shima zane ne, na mutum biyu mace da namiji zaune cikin ciyayi gabansu shanaye ne na kiwo alamar shi su ke yi, duk da sun juya baya, za ta iya shaida su, ita ce, tabbas ita ce tare da shi, a wani lokaci mai tsayi, kamar zararriya ta shiga bin duk frame din dake manne a falon tana kallo, yayinda kuka ya ƙi barin idanunta, memories din komai na dawo mata a kai, zuciyarta ta yi nauyi ta kasa gane abinda take ji game da ganin waɗan nan hotunan, wani abu ne matacce ke kokarin rayuwa a zuciyarta, ta sani har abadan da'iman ba za ta ɓata daina son Babangida ba, amma kuma ba za ta iya yafe masa ma domin ya cutar da ita. “Me take yi a nan, me yasa suka dauko ta, kenan shi yasa a dauko, kenan yasan inda take ya san tana nemansa tsayin shekara takwas ya san ta bar gida ta rabu da iyayenta duk saboda shi, me yasa ya boye bai bayyana mata kansa ba.” abinda ta dinga fada kenan a zuciyarta, bayan ta koma ta zube a tsakiyar falon, “Saboda mugun ne, ɗan mafiya ne mai safaran sassan jikin yan Adam ne.” Wani ɓari na zuciyarta ya bata amsa, da sauri ta girgiza tare da faɗin “A'a ba mugu ba ne.“ sai kuma mike a guje ta nufi kofar fita daga falon tana bubbugawa da karfi tana faɗin, “Ku buɗe ni, ku sanar da ni a inda nake, kaina yana juyawa.” numfashinta ne ya tsaya cak, ta yi baya kaɗan sai kuma ta sulale a bakin kofar ta kwanta idanuta suka rufe ruf...

Lumshe idanunsa da suke rine ya yi bayan ya gama sauraren jawabin da Giɗaɗo da ya gama yi masa, ba tare da ya furta komai ba. Cikin salon karfafa gwiwa da son kwantar masa da hankali Giɗado ya matsa kusa da yi, ya ce “ Megida ka yi hakuri ka yi imani ka kwantar da hankalinka, In Sha Allahu za su bayyana nan kusa, ko a jawabin da na baka ya kamata ka saka yakini ka fahimci an fara samun haske a cikin wannan lamarin, Allah yana tare da kai, kuma zai wanke ka gaskiya za ta bayyana, addu'a bata faduwa kasa a banza in dai mutum ya yi ta da cikakkiyar yaƙini.” “Hakuri na ya kusa karewa ne Giɗaɗo, a kwai cutarwa a lamarin, ba zan iya jurar ci gaba da ganin hawaye ta ba, kuma ina tsananin jin kunyarta, ba zan iya fuskantar a haka ba.” “ Ka daure komai ya kusa zuwa karshe.” sun dade suna tattaunawa da Giɗaɗo yana kara yi masa bayani akan ci gaban da suka samu, kuma ya gamsu sosai ya yi masa alheri, sannan ya dumbuza masa kudi masu kauri akan a je a ci gaba da roƙon Allah. A tare su ka yi sallar la'asar, kafin suka fito daga Palace, nan kuma ya tarar da mutanensu yan siyasa, manya ne da yake matukar jin nauyin su, domin yawancinsu abokan Abba ne, duk da ba shi da appointment da su haka ya tsaya ya sauraresu ba shi ya samu kansa ba sai wuraren karfe 6 na yamma.

Fitowa ya yi domin tafiya gida, sai lokacin ya duba wayarsa, a nan ya tare da missed Calls da yawa na Mother, dana Jarumi sai na Abba, a kan na Jarumi ya tsayar da idanunsa, zuciyarsa na tunano masa da ajiyar da ya sanya suka yi masa na wancen yarinyar, rintse idanu ya yi da karfi ya buɗe, sai kuma ya karya kan motarsa ya kama hanyar sabon gidansa dake By pass bayan ya kira su Ussy a kan su haɗu a can.

Assalamu alaikum mutanen arziki, sannunku da jumurin bibiyata a cikin wannan labari nawa mai taken haɗin kaddara, a yadda na tsara hadin kaddara book 1 zai kare ne a iya page 20, wanda iya shine free, yayinda book 2 nasa zai zo mana a matsayin paid in Sha Allah, to duba da sha'afa da na yi wajen sanar muku da hakan, zan ƙara five pages a kan wannan, amma kafin nan, duk wanda yake so a yi tafiyar Book 2 da shi, zai iya yin payment tun yanzu domin a saka shi a paid group wanda a shi kaɗai ne zan ci gaba da posting sai kuma Arewapen, kuɗin karatun littafin 1k ne, amma ga wanɗan da suka shirya biya kafin mu kammala book 1, za su iya biyan 800₦ ta wannan account ɗin, 7041130088 Aisha Alhaji Yahaya Opay, sai ka tura min shaidar biya ta pravate, idan na fara book 2, za ku biya normal price 1k Nagode sosai. [5/14, 6:48 AM] Oum khadeejarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

By

AyshaNalado

Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍

BOOK 1

Page 21

A gigice ta farka, dalilin saukar ruwa mai ɗan karen sanyi a jikinta, cikin fitar hayyaci ta miƙe tsaye idanunta a rufe tana ambaton Allah, ba ta yi aune ba santsin tiles ya kwashe ta. Tif! Ta sake zubewa a inda ta tashi. Faduwa mai kyau ta yi kanta ya bugu da ƙasa sosai, take zafi ya ratsa har kwanyarta.“Wayyo Allahna!” ta furta a wahalce tare da fashewa da wani irin marayan kuka, har lokacin bata gama dawowa hayyacinta, sai da ta tsinci deep husky voice ɗinsa a kanta, cike da fushi ya daka mata razananniyar tsawar da ta sanya numfashinta daukewa na hucin gadi. “Tashi munafuka!” Ya sake daka mata wata tsawar da tafi ta farko. A rikice ta kuma mikewa jikinta na rawa, zuciyarta na wani irin bugu na wuce ka'ida. A karo na santsin wajen ya kuma ɗibanta, rintse ido ta yi da karfi irin ta yi giveup, ba zato ta ji an taro ta, gaba ɗaya ta faɗa jikin mutum, samun wannan damar yasa ta ƙanƙame shi da karfi tare da cusa kanta a jirjinsa tana sakin ajiyar zuciya da sauri da sauri kamar wacce ta yi gudun ceto rai.

Wutar kansa ne ya ɗauke ɗif, wani baƙon yanayi ya ziyarce zuciya, ƙwaƙwalwa, dama ilahirin jikinsa baki ɗaya, tsigar jikinsa ya hau cirawa. Kusan sakan talatin suka kwashe a haka, kafin kamar saukar wahayi wani ɓari na zuciyarsa ta jeho masa tambaya kai tsaye “Me ka yi kenan Ahmad?” “Taimako domin Allah.” Ya furta a kan laɓɓansa yana lumshe ido saboda yadda hucin numfashinta da ke dukan kirjinsa yake yi masa tasiri, da gaske buguwar da ta yi da farko ta bashi tausayi, yana da tausayi na ban mamaki balle a kan mace, “Hakan na nufin ka bada kai makiya sun ci galaba a kan ka kenan? Wannan ba komai ba ne illah makirci irinta gogaggun matan bariki. Be wise mana, wannan ba abar tausayi ba ce” Zuciyarsa ce ta sake yi masa wannan hudubar, lokaci guda ya ji komai ya tsaya cak tamkar an yi ruwa an ɗauke, nan take ya dawo hayyacinsa, ba shiri ya ware idanu tare da fisgeta daga jikinsa ya watsar gefe. Faɗuwan ta kuma yi sai dai wannan karon Allah ya agajeta ta faɗa kan capet ɗin da ke malale a tsakiyar falon mai azabar taushi.

Sai lokacin su ka yi ido biyu, sai lokacin tasan da wa take tare, sai lokacin ta fahimci jikin wa ta faɗa. Yanayin fuskarsa kaɗai abin tsoro ne take ta ji fitsari na shirin kwace mata. “Me ya same shi, ya sauya mummunar sauyi,Wannan ba shi ba ne Babangidana bw, wannan ba shine Babangidan Shatou ba, ba zai taɓa zama shi ba har abada.” Ta furta hakan a ranta kuka na sake kwace mata.

Wani shegen kallo yake watsa mata da idanunsa dake cike da tsantsar kiyayyarta a bayyane, yayinda ya shiga takawa yana nufarta. Baya ta dinga ja daga zaune da take, a haka suka dinga tafiya har ta dangana da jikin royal cshion ɗin dake falon. “Ba... Ban gi...da.. Ka da ka cutar da ni.” Ransa ne ya kara ɓaci jin sunan da take kiransa da shi kenan ba za ta daina raina masa hankali ba, ta rantse dai sai ta yi wasan kwaikwayo da shi, to kuwa zai nuna mata karen bana shike maganin zomon bana, zai gwada mata idan ita yar yau ce shima haka. Wani shegen murmushi ya saki, kafin ya miƙa hannu ya ɗago habarta ya miƙar da ita tsaye ba tare da ya sake ta ba yace “ Da kyau hadaddiyar yar kafce, aikin ki yana tafiya da kyau successfully gaskiya kin burge ni. Yanzu dai duk ba wannan ba. Su wane ne? Nawa suka biya ki?” “Ba...ban...gida..” Ta sake faɗa a hankali tana kallon fuskarsa da ke daure tamau, yayinda hawaye ke tsere a tata fuskar. Tamkar ta watsa masa wuta haka ya ji da ta sake ambatar sunan Babangida, rintse ido ya yi da karfi ya buɗe tare da fesar da hucin takaici, ji yake kamar ya shaƙe ta har sai ta daina numfashi, a duniya rainin hankali na daya daga abinda ke saurin ɓata masa rai, wato dai yarinyar nan ba za ta yi giveup ba kenan. Jijjigata ya yi sai kuma ya hankaɗata da karfi ta faɗa kan cushion, ya dafe goshinsa yana tunanin abinda zai mata don ya huce takaici. Juyawa ya yi ya ɗan duka kanta cikin tsatsar ɓacin rai ya ce, “ Wannan shine karo na Uku da zan sake maimaita miki cewa, Ni ba Babangida ba ne, AHMAD KANGIWA nake ko kin gane.” lokaci guda ta ji Zuciyarsa ta dake duk wani tsoro da shakkarsa da take ji ya kau, cikin karaji ta ce “Karya ka ke yi kai ne, wallahi kai ne Babangida, kuma ba zan daina kiranka da Babangida ba domin da shi na sanka, mugu kawai azzalumi, kana tunanin raba Ni da budurcina da jefe rayuwata da ta iyayena a cikin garari da ka yi, za ka ci bulus ne, never wallahi ko mutuwa na yi fatawalta sai ta hana rayuwarka kwanciyar hankali.” Kauuu! Ya ɗauke ta da mari yana huci ya nunata yace, “ Wane ne ya ɗauki budurcin naki, Ni za ki yi wa ƙazafin zina, Oho sai yanzu na fahimci inda ki ka dosa, in dai haka ne to ashe ke karamar yar wasa ce” Ya ja baya yana kallonta daga sama har kasa , sai kuma ya yi murmushi ya ce, “ Ciki na yi miki ko, ɗan wata nawa ne?” ya faɗa cike da isgili, Dafe kuncinta ta yi tana jin tamkar zuciyarta na rarrabewa “Anya kuwa shi ɗin ne?” ta yi imani Babbangida ba zai taɓa marin Shatou ba. Sai dai tuna hotunan da ta gani dazu gewaye da bangon ɗakin ya rushe wannan hasashen nata da ta fara. Kamar zararriya ta mike da gudu ta nufi wajen hoton da ta gani na shi dazu tana faɗin “ Idan ba kai bane Babangida to wanene wannan?” turus ta taka burki, lokacin da idanuta ya sauka akan hoton, sabanin abin da ta gani dazu, yanzu hoton mutumin da ke gabanta ne, bana Babangida ba, hoton kusa da shi ta kalla inda wanda suke su biyu, nan ma hoton shi ne shi da familynsa. Wani hoton ta kalla nan ma haka. Bin hotunan falon ta dinga yi amma kamar almara babu ko ɗaya daga cikin hotunan da ta gani dazu ko ire irinsu a falon. Kafafunta ne ya ɗauki rawa yayi da wani irin tsoro ya kamata, sai kawai ta zube a wajen ya yanka ihu mai karar gaske tana dage da kanta da ke juya mata.

Kallonta AA ya tsaya yana yi cike da shakku, anya wannan kanta ɗaya, “ Kai ina! Ya faɗa tare da girgiza kai, da ya ɗauka yar wasa ce, amma yanzu ya gama yin ammana da cewar mahaukaciya ce. Lokaci ɗaya zuciyarsa ta yi laushi, har ya ji kamar ya fara jin tausayinta, lamarinta yana da matukar daure kai, a zahiri gaskiya ba ta yi kama da mai larurar Hausa ba amma maganganunta da aikinta sun nuna hakan, to me ke faruwa gareta, wanene Babangida mai ya aikata mata haka. Wadannan tambayoyi ne da bashi da amsar su a yanzu don haka sai ya nemi guri ya zauna, tare da zaro wayarsa ya dannawa Ussy kira. Mintuna biyu tsakani ya shigo falon, har lokacin Aysha na duke a inda take dafa da kanta tana kuka.

“Ku fita da ita mahaukaciya ce?” Ya faɗa ba tare da ya kalli Ussy. Kallonta ussy ya yi cike da mamaki yana maimaita kalmar hauka a zuciyarsa, kasa daurawa ya yi ya ce “Megida anya ba pretending take yi ba, don gudun tonuwar asirinta.” “ Bana tunanin haka, lamarinta akwai sarkakiya a ciki, ina ganin wani ne ya cutar da ita, har hakan ya yi affecting din ta sosai, ku kaita gida kawai.”

Jiki ba kwari ussy ya matsa kusa da ita, yace “Ki taso mu kai ki gida.” kamar abinda take jira kenan ta mike zaraf. Gaba ya yi ta bisa a baya tana harde hanya, AA ya zubawa bayanta ido cike da nazari, yana cin zuciyarsa na narkewa wani abu mai nauyi ya yi matsa tsaye ba tare da ya san ko mene ne ba.

Wacce ta shirya payment yanzu kafin mu gama Book 1, 800₦ ne a saka a wannan account ɗin 7041130088 Aisha Alhaji Yahaya Opay, a turo shedar biya ta 09116099486. [5/15, 4:58 PM] Oum Oummeetarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

By

AyshaNalado

Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍

BOOK 1

Page 22

Hannun da ya mareta da shi ya bi da kallo na 'yan sakanni bayan sun kurewa ganinsa, cikin mutuwar jiki ya nemi guri ya zauna dan ƙafafuwan sa sun kasa daukarsa “Mene ne haka Ahmad? Me ka aikata haka? Ina tunaninka ya tafi? Wannan babban zunubi ne... Wannan babban zunubi ne.“ Abin da yake ta maimaitawa kenan a can cikin zuciyarsa, yana jin kamar ya fashe da kuka ko zai samu sassauci, amma shi kansa yasan ba abu ne mai sauƙi ba, abinda zai saka shi hawaye a yanzu dai, to lallai ya gawurta. Zabura ya yi kamar wanda ya tuna wani abu mai muhimmanci, ya jawo waya cikin sauri ya shiga lallatsawa, gajeriyar saƙo ya tura ma wata lamba da ya yi saving da Fav kafin ya ajiye wayar akan cinyarsa ya kureta da kallo kamar mai neman jiran tsammani wani abu daga cikinta. Ya dade a haka kafin lokacin guda ya saki wata kyakkyawar murmushi bayan ta tuno abinda ya aikata.

Kai tsaye Ussy wajen da motarsa ke fake a compound ɗin gidan kusa da ta AA ya nufa, tana biye da shi a baya kamar jela ,duk da rana ta fadi duhun magriba ya fara shigowa, tsakar gidan tamkar safiya saboda wadatar haske. Kofar baya ya bude mata, babu musu ta shige, ta zauna ta dafe kanta da take jin ya yi mata bala'in nauyi kamar zai rikito. Sai da ya mayar da murfin motar ya rufe kafin ya zagaya ya shiga ya zauna a mazaunin direba, yayinda Jarumi dake cikin motar yana jiransa ke zaune a gefen hagunsa, da hannu Ussy ya yi masa wata inkiya, gyaɗa kai ya yi alamar ya gane, sai kuma ya ɗan juya ya saci kallon Aysha, da shesshekar kukanta ke ratsa kunnensa, dai dai lokacin da Ussy ya fisgi motar tsiyace suka fice daga harabar gidan.

Sosai Ussy ke sharara gudu a hanya cike da kwarewa a iya sarrafa sitiyari, cikin kankanin lokaci suka iso kafar gidan ba tare da wani daga cikinsu ya tambayeta ko da sunan unguwar ba ne. Jin sun yi parking baisa ta dago ba, sai da ta ji kakkaurar Muryar Jarumi yana bata umarnin sauka. A wahalce ta ɗago don ganin inda suka kawota, ganinta a kofar gidansu ya bata matukar mamaki, sai dai yana yin da take cikin bai bari mamakin nata ya yi tasiri ba, dakyar ta iya miƙa hannu ta buɗe motar, haka kafin ta ja jiki ta fita sai ta kusa kwashe minti ɗaya saboda yadda jikin nata yake babu kwari. Tana sauka suka yi wani irin ribas na garari, daidai saitinta suka tsaya Ussy ya cillo mata yar jakarta kamara data fadi a motar tun lokacin da suka dauko ta, kafin suka figi motar a tsiyace suka bar layin.

Readers Also Read