Kenza eBookz

Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 16

Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 16

Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 16: Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 16. Wannan karar ita je ta janyo hankalin Salman Salmah, da Ammie da suke…

3,348 words

Wannan karar ita je ta janyo hankalin Salman Salmah, da Ammie da suke tsaye a compound cirko cirko cike da damuwa, fuskokinsu kadai ka kalla za ka shaida halin tashin hankalin da suke ciki. Kasancewar basu baro gidan su Suraj ba sai bayan la'asar, yasa basu tarar da Ammie ba, don duk da kasancewar Asabar da Lahadi babu aiki, takan shiga asibiti idan tana da patient da yamma ta duba su, rashin ganin Aysha bai sa sun kawo komai a rai su ba, sai zaton ta bi Ammie asibiti don su kan yi hakan a wasu lokutan, dawowar Ammie ita kaɗai shine ya ganar da su wautar da suka tafka, nan da nan suka fayyace mata halin da suke ciki, hankalin Ammie ya fi nasu tashi, domin da fada ta rufe su da fari kafin kuma ta zari mayafinta da ta ajiye a kan kujerar da makullin mota ta sake fitowa suna biye da ita, a bakin motar take gaya musu Police station za ta je ta kai report, a dai dai wannan lokacin ne suka ji karar motar su Ussy.

Salman ne ya fara takawa da gudu ya nufi get shi da Babangida megadi da ya riga shi fita wajen, Salmah da Ammie, suka rufa masu baya.

Taku ɗaya biyu ta yi ana ukun ta gaza, saboda jirin da ke kwasarta, tana shirin durkushewa, suna fitowa, Salman da ke gaba shine ya fara isa gareta ya tarota, sai kawai ta narke a jikinsa, ta lumshe ido numfashinta na fita dakyar. bakinta ya bushe raƙauu kamar me azumi, “ Innalillahi wa Inna ilahi raji'un!” Ammie ta furta, ta yo kansu ta rikota, Salmah kam tuni ta fara kuka, motarsu Ussy da ke daf da ficewa daga layin Ammie da Salman suka bi da kallo, sai kuma suka kalli juna zuciyoyunsu na rawa. Jijjigata Salmah ke yi tana faɗin, “Aysha, Aysha me ya faru, me ya same ki?” “Kamata Salman mu shiga ciki.” Ammie ta bashi umarni, “Zan iya.” ta furta a hankali, tare da girgiza kai, “A'a Aysha bari ya taimaka miki.” Ammie da ta riga ta yi wa karfin halinta farin sani ta yi saurin faɗa. Hakan yasa bata sake musawa ba, Salman ya gyara mata riko Salmah ta taimaka masa suka saka a tsakiya suka shiga da ita ciki har falon ƙasa, akan dogon kujera suka zaunar da ita, Salmah da har lokacin hawaye ta ke yi, ta zauna kusa da ita tana taɓa jikinta da ya ɗauki zafi zauu alamar zazzaɓi ne a jikin “Jikin ki zafi Sister baki da lafiya, meya faru dake, ina ki ka je, ki ka barmu cikin tashin hankali da damuwa?” “Ruwa. Zan sha ruwa. Ki bani ruwa Salmah, ina jin ƙishi.” a hankali ta yi maganar da yanayin da ya kara tabbatar musu tana jin jiki sosai. Salman da ke tsaye ne ya yi saurin nufar kitchen ya dauko ruwan baban gora da cup, Ammie ta amsa ta tsiyaya mata ta bata a baki.

Yadda ta karbi ruwan ya kara ɗaga musu hankali, har tana riƙe hannun Ammie da kyau tana kara tura kofin a bakinta , kafin sakan biyar ta shanye, ganin haka yasa Ammie ta kara mata, nan da nan ta kuma shanyewa, karshe sai ta kafa mata goran a baki, sai da ta ga bayanshi, sannan ta shiga sauke ajiyar zuciya da sauri da sauri. Duk ido suna zuba mata kowannensu zuciyarsa na bugawa. Sai da ta ɗan shiga natsuwarta, Ammie da dauriya kawai take yi tun ɗazu ta sake cewa “Mene ne ya faru Aysha? kin barmu cikin zulumi?”

Ɗagowa ta yi ta zubawa Ammie kumburarrun idanuta da suka koɗe suka rine tsabar kuka, kwarjini Ammie ta yi mata, ta kawar da kai da sauri, bakinta ya fara rawa, fuskarta ya kwaɓe alamar wani sabon kuka na shirin kwace mata, cikin rawar murya ta ce, “ Am...mie, Ba..ban..gi.” sai kuma ta datse zancen ta fashe da wani irin kuka, mai tayar da hankali.

Ya Salam! Idan ka kalli fuskokin, Salman Salmah, da Ammie a lokacin sai ka tausaya musu, “Babangida?” A ruɗe Salman ya faɗa cikin sigar tambaya kamar ya san wa take nufi. Ta gyaɗa masa kai. Cikin tashin hankali Salmah ta ce “ Kin gan shi ne, me ya yi miki?” “ Wane ne kuma Babangida? Ammie ta furta ita ma. Ɗagowa ta yi ta kallesa duk sai suka bata tausayi, maimakon ta basu amsa sai ta sake kife kanta a jikin Salmah ta saki kuka, “Don Allah ki yi magana Aysha.” Ammie ta faɗa muryarta a raunace, “Ku barta!” Su ka ji muryar Abie yana faɗa cikin bada umarni, duk daga kai suka yi inda suka jiyo sautin, shine yake saukowa daga upstairs jikinsa sanye da jallabiya, da alamar ba yanzu yake a cikin gidan ba. “Ku rabu da ita, kada wani cikin ku ya kara takura mata da tambaya, tunda dai ta dawo lafiya shikenan Alhmdlh.” Ya sake fada bayan ya gama sakkowa. Yadda ya yi maganar cikin tsare gida yasa ko Ammie bata iya kawo masa wargi ba balle su Salmah, sai dai ta dinga binsa da wani irin kallon tuhuma wanda shi kaɗai ya fahimci mai take nufi, sai ya dauke kai ya ki bata damar hada ido da shi, kallon Salman ya yi ya ce, “ Mu je.” Ba musu Salman ya bisa a baya suka fice daga falon domin zuwa Masallaci, su sallaci sallar magribar da har an tayar a wasu wuraren. Kallon Salmah ammie ta yi ta ce, “ Ku je ɗaki, ni ma bari na yi sallah.”

Dakyar Aysha ta iya karasawa dakinsu, har sai da Salmah ta tallafa mata, suna shiga ta sulale ta zauna a bakin gado, ita kuma Salmah ta shiga toilet ta dauro alwala ta fito, a kwance ta same ta ta kudundune tana rawar sanyi, da hanzarin ta karasa, ta na faɗin “ Subhanallahi, jikin ne?” ta miƙa hannu ta taɓa wuyanta, da sauri ta dauke saboda zafin da ta ji, “ Ya Salam! Sannu Sister, bari na kira Ammie.” riko mata hannu ta yi a wahalce ta ce, “ Ki lulluɓeni ina jin sanyi.” fankar dakin ta kashe, sannan ta dauki bargonsu na kwanciya ta ninka shi ta lulluɓa mata, kafin ta fice daga ɗakin a gurguje, ta isa dakin Ammie bata idar ba, don haka sai ta dauki dadduma itama ta shimfida ta tayar da tata sallar, kusan tare suka idar da Ammie wanda ta daura da nafila bayan ta sallame farillah. “Ammie jikin Aysha ya yi tsanani.” ta ɗaura da labarta mata yadda ta barota. “ Ya Salam!” Ammie ta furta tare da miƙewa. A tare suka koma ɗakin, tana nan yadda Salmah ta barta a kwance. Ammie ta ƙarasa bakin gadon da sauri, ta zauna gefen Aysha tana kallonta fuskarta dauke da damuwa, cike da ƙwarewa akan aikinta, ta dora a goshinta, sai ta ɗan lumshe ido na wasu sakanni alamar tana tantance yanayin zafin jikin. “Zazzabi ne mai tsanani…” ta faɗa a hankali. Ta juya ta kalli Salmah da ke tsaye cike da tashin hankali, “Ki ɗauko min thermometer daga drawer na ɗakina, sannan ki kawo towel da ruwa mai ɗan sanyi.” Ba ɓata lokaci Salmah ta juya da gudu. Ammie ta dawo da hankalinta kan Aysha, a hankali ta ɗaga kanta ta ɗora akan cinyarta, tana shafa kanta a hankali kamar ƙaramar yarinya. “Aysha… ki kwantar da hankalinki… kina tare da mu…” ta faɗa cikin sassanyar murya mai cike da tausayi. Numfashin Aysha na fita da sauri, jikinta na rawa kaɗan-kaɗan, wani lokaci kuma tana motsa leɓɓanta kamar mai son magana amma kalmomin na makalewa. Salmah ta dawo da kayan da Ammie ta nema, cikin sauri Ammie ta amsa ta saka thermometer a bakin Aysha, sannan ta karɓi towel ɗin ta tsoma shi a ruwan sanyi, ta matse shi sannan ta fara goge goshinta da wuyanta a hankali. “Zazzabin ya tashi sosai…” ta faɗa bayan ta duba thermometer. Ta miƙe kaɗan ta buɗe jakarta da Salmah ta dauko zo da ita daga asi5ta ciro magani, ta ɗauko cup ta zuba ruwa kaɗan. “Salmah ki taimaka ki ɗaga ta kaɗan.” Suka haɗa kai suka ɗaga Aysha, Ammie ta saka mata maganin a baki a hankali tana cewa, “Ki haɗiye Aysha… zai rage zafin jikin…” Da ƙyar ta iya haɗiyewa. Bayan ta mayar da ita ta kwantar, Ammie ta ci gaba da goge jikinta da towel ɗin sanyi, lokaci zuwa lokaci tana duba numfashinta da bugun zuciyarta. “Ba zazzabi kawai ba ne…” ta faɗa a hankali kamar tana magana da kanta, “akwai firgici da tashin hankali a jikinta…” Ta juya ta kalli Salmah, “Kada ki sake tambayarta komai yanzu. Abinda ta fuskanta ya girgiza ta sosai.” Salmah ta gyaɗa kai tana share hawaye. Ammie ta ɗan yi shiru kafin ta sake cewa, “Zan zauna da ita yau. Idan zazzabin bai sauka ba, sai mu kai ta asibiti da safe.” Ta koma ta zauna kusa da ita, tana riƙe da hannunta a hankali, tana jin yadda zafin jikinta ke raguwa a hankali.

Wani irin kakkarfar ajiyar zuciya Aysha ta saki, sai kuma laɓɓanta suka buɗe a hankali ta furta “baa...shi...ba... ne. Na.. ga.. ni.. da.. ido...nahhh....” Ta yi maganar a rarrabe, amma hakan bai hana Ammie da Salmah fahimta ba, da sauri suka kalli juna.

Dai dai lokacin Salman da Abie suka shigo ɗakin, dakyar suka iya jira har aka isar da Isha kafin su ta so, gabaɗayansu hankalinsu na kan Aysha, “Dacta Jikin ne? ” Abie ya furta muryarsa a raunane, “E zazzaɓi ne mai tsanani, sannan akwai firgici sosai a yanayinta, kamar wanda ya ga wani abu mai razana.” Numfashi ya furzar kafin ya sake cewa “Ta faɗi wani abu?” Ammie ta ɗan tsura masa ido kafin ta ce, “Eh… amma ba a fili ba.”

Salman ya matsa kusa da Aysha yana kallonta da tausayawa ya ce “Me ta ce Ammie?” Salmah ta kalli Ammie kamar tana neman izini, sannan a hankali ta ce, “Ba shi ba ne. Na gani da idona…”

Duk shiru suka yi kowa na nazari kafin Abie ya kashe hakan da faɗin, “Allah ya ba ta lafiya ya kawo mata haske a cikin rayuwarta, hakika ta ga jarabawar rayuwa kala kala, ina fatan gobenta ya yi kyau fiye da zaton mai zato.”

Idanu Salmah ta lumshe ta bude a hankali, tana mai jinjina kalaman Abie domin bayan shi ita ce mutum ta biyu da tasan hakikanin wacece Aysha. Yayinda Ammie da Salman suka amsa da Amin............

Shin wai wacece Aysha, me ya faru da rayuwarta, da gaske AA shine Babangida ko kuwa dai ya abin yake? [5/17, 8:39 PM] Oum khadeejarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

By

AyshaNalado

Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍

BOOK 1

Page 23

Wannan dare sam bai ya wa iyalan Abie daɗi ba, gaba ɗayansu babu wanda ya iya cin abincin kirki saboda damuwa da halin Aysha take ciki, ga fargaba da tunanin, ina ta je? Me ya faru da ita? Su wane ne suka sauke ta a mota? sai dai babu wanda ya kuma ɗago maganar kamar yadda Abie ya yi musu umarni. Har cikin dare Ammie bata huta ba kwana ta yi karya tsakanin ɗakinta da ɗakinsu Salmah, tana duba jikinta da ruwan da ta daura mata daga baya. Washegari ta tashi jikin da ɗan sauƙi,sai dai sam babu walwala a tare da ita, don haka ta yi wanka da taimakon Salmah, daga zaune ta ranka sallolin dake kanta, da kyar ta idar, a wajen ta kuma zamewa ta kwanta, saboda kanta da ke ciwo, “Sannu Sister. Ya jikin?” Salmah dake zaune akan darduma ta faɗa tana kallon ta, bayan ta idar da azkar ɗinta. Lumshe ido ta yi ta bude a hankali sai kuma ta ɗan jinjina kai alamar amsawa. Kafin Salmah ta sake cewa komai wayarta dake maƙale a jikin caji ya ɗauki ƙara. kasancewar ya fi kusa da Aysha, yasa ta yi karfi miƙa hannu ta zare mata shi daga cajin, “Waye?” Salmah ta tambaya fuskarta dauke da mamakin wane ne ke kiranta a daidai wannan lokacin, tambayar da ta yi ya bawa Aysha damar kallon screen ɗin wayar, dan sunan ido ta yi gabanta na faduwa kafin ta ce “YA A.” Zaro idanu Salmah ta yi irin na kaɗuwa, sai kuma ta yi murmushi kafin ta miƙa hannu da sauri ta karɓi wayar, tare da miƙewa tsaye, cikin ɗan inda inda ta ce, “Laa Yayana ne.” Sai kuma ta juya da sauri za ta fice daga ɗakin ba tare da ta ɗaga wayar ba, saura ƙiriss su gobza karo da Ammie da ta sawo kai a bakin kofa, hannunta dauke da kofin shayi mai zafafa da kuma ledar magunguna mai dauke da tambarin asibitin da take aiki. Baya ta yi da sauri ta kauce mata tana faɗin, “Ya Salam! Sannu Ammie. Sai kuma ta raɓa ta gefenta ta fice a gaggauce kamar za ta tashi sama. Bin bayanta da kallo Ammie ta yi har ta ɓace, sai ta girgiza kai ta ce “ Allah ya shirya.” Kafin ta juyo da kallonta kan Aysha da ta yi kasaƙe cike da mamakin yanayin Salmah, ko me suke boyewa ita da Ya Anas ɗin oho, “ Surprise ɗin dawowarsa mana, da yake shirin yi mu ku.” zuciyarta ta ba ta wannan amsar, sai kuma ta yi yar murmushi kawai.

“Sannu Aysha, kin tashi?” Muryar Ammie ya katse mata tunani, “E Ammie.” “ Ya jikin?” ta sake faɗa tana taɓa goshinta, bayan ta ajiye kayan hannunta “Alhmdlh da a sauƙi Ammie.” “Har yanzu jikin ki da zafi, anya ba za mu tafi asibiti ba kuwa.” Girgiza kai ta yi kafin ta ce, “A'A Ammie ciwon kan ne yafi damuna yanzu, amma jikin da sauki.” “ Ba zan biye miki ba, Aysha don nasan halin nukufurcinki zuwa yamma idan banga irin saukin da nake son gani ba, dole zan yi addimting ɗin ki a asibiti.” Ɗan kwaɓe fuska ta yi cikin salon shagwaɓa. Ammie ta harareta, sai kuma ta dauki kofin shayin da ta shigo da shi ta mika mata tana faɗin, “ Oya ungo ki sha, mu yi allura ki sha magunguna maza.” Ƙarba ta yi ta fara kurɓa a hankali tana ya mutsa fuska saboda rashin jin daɗin shayin da take yi, bakinta babu test.

A haka Salman da Abie su ka yi sallama, dawowarsu kenan daga Masallaci kai tsaye suka zarto ɗakin domin duba jikinta. Cike da tausayawa Abie ya tambayi yadda ta kwana haka ma Salman. Ammie ce ta yi musu bayanin yanayin jikin duk su ka bada goyon bayan zuwa asibitin anjima idan idan jikin ya ƙi.

A haka wunin wannan ranar ya shige, sosai Aysha ke samun kula a wajen waɗan nan halin ta ko'ina, yadda suka nuna tsananin damuwarsu yasa ta yi ta kokarin karfafa kanta, amma abu ya ci tura, zafin jikin da sauki matuƙa amma fa ciwon kai tamkar karuwa ya ke yi, har ya kai matsayin da, ko ido bata iya budewa da kyau balle ta yi kwakwaran motsi, , ga tunanin abinda ya faru da ita a gidan AA ya gaza barinta, idan ta tuna har wani zabura take yi saboda tsoron da ke kamata.

Ganin babu sauƙi, kamar yadda Ammie ta faɗa rana na yin sanyi, ta shiryata ta dauketa a mota suka tafi asibitin da take aiki, bayan ta kira abokin aikinta Dr Lukman, kwararren likita sosai yana da baiwa ta musamman akan aikinsa, shiyasa Ammie ta kirasa, don ta yarda da shi duk abinda ya shafi iyalinta wanda ya sha kanta taimakonsa take nema.

Kai tsaye emergency aka nufa da Aysha, sosai ya dubata, ya bata gado, bayan ya yi mata test, ya gano jininta ne ya haura, hakan ya yi sanadiyar haifar mata da ciwon kai, sai kuma buguwar da ya gane ta yi a kan wanda shima ya ƙara hassasa ciwon, sai zafin jiki da rashin kuzari wanda stress da tension ɗin da take ciki suka haifar mata.

Godiya Ammie ta yi wa Dr Lukman bayan ya gama yi mata jawabi, jiki a sanyaye ta fito daga office ɗinsa, zuciyarta babu daɗi, kalmar hawan jini nata nanatuwa a zuciyarta, ta san Aysha na da hawan jini a baya, amma tun daga lokacin da su ka rungumeta suka kwantar mata da hankali tare da nusar da ita rayuwarta tana da muhimmanci, sai suka nemi larurar suka rasa, to menene musabbin motsawarsa a yanzu? Ƙarar wayarta ne ya katse mata hanzari, ganin Salmah ce ke kiran yasa ta ɗaga ta kara a kunne, “Ammie ya ake ciki, ya tsare ta ne.” ta tambaya cike da damuwa, “ E Salmah.” Ta amsa mata a sanyaye, “ Ya Rabbi! To gamu nan biyo ku yanzu.” “Ok ku taho da duk abinda ya dace.” Bayan sun gama wayar, Abie ta kira shima ta sanar masa da halin da suke ciki, don baya gidan bai san ma sun zo ba, ya san dai za su je. Shima ya jajanta, kuma ya ce idan ya gama zai biyo.

Kimanin awa daya bayan nan, su Salmah su ka iso, lokacin anata kiraye kirayen magriba. Suna nan tare har wajajen karfe tara na dare, lokacin Abie ya zo shima, sai wajen karfe goma har ma ta gota, sannan ya hada kan Salmah da Salman kasancewar gobe za su fara test, su ka tafi duk da Salmah ba ta so ba, don rigima ta saka akan su barta ta kwana Ammie ta wuce amma Abie ya ki amincewa ya ce ta je ta yi karatun jarabawa, a haka suna tafi yayinda Ammie ta zauna za ta kwana.

Suna zuwa gida ta shige ɗakinsu, ta mayar da kofarta ta rufe ba tare da kula Abie da Salman dake ta kokarin tsokananta ba, zama ta yi a bakin gado ta yi waya na kusan mintuna shidda, kafin ta mike ta fara rage kayan jiki ta, sai da ta kammala duk wani abu na al'ada irin wanda su kan gudanar kafin kwanciya barci kamar wanka alwala da sauransu, sannan kwaso handout ɗinta ta fara dubawa, saboda gobe, sai da ta ga ji, ta ture littafan gefe, ta janyo wayarta, missed calls din Zahra Bukar, da na wasu daga cikin friends ɗin su har uku ta gani a wayarta, da sai lokacin ta kula a silent yake, “Lafiya kuwa? ” Ta furta tana miƙewa zaune maimakon kwanciyar da ta yi, Zahra ta fara kira, user busy, don haka ta canza akalar kiran kan Sofiyyah, ringing ɗaya ta daga kamar jira take yi dama, “Salmah Mu'az ina kika shige yau ne, tun jiya bakya online kina da labarin abinda ke faruwa kuwa?” cike da wani irin annashuwa ta yi maganar, gaban Salmah ya faɗi ta ce, “No tun jiya da safe ban kunna data ba, saboda bana cikin natsuwa me ya faru?” Dariya Sofiyyah ta kece da shi, hakan yasa Aziza Bello dake kusa da ita ta karɓe wayar, ta ce “Salmah hau online faka faka ki ga me ke faruwa.” daga haka ta kashe wayar, tsaki Salmah ta ja, ta san halin iskancin ƙawayen nata idan ya motsa, yanzu haka ma ba wani abin kirki bane ko kuma wata gulmar ce may be, kamar ta share sai kuma zuciyarta ta gaza hakuri, sub na data ta yi, sannan ta hau WhatsApp, sannu a hankali messages suka fara shigowa, ganin tagging ɗinta da aka yi ta ko ina a duk wani groups da take ciki wanda ya shafi makaranta, kama daga kan general group, group na yan year ɗinsu, na yan department ɗinsu, na friends da sauransu, ga kuma sakonni ta private hada bakin lambobi mara suna, sai ta ji hankalinta ya tashi, zuciyarta ta tsananta bugawa, sai ta shiga maimaita Innalillahi wa Inna ilahi raji'un, sakon Zahra ta rufe ido ta fara shiga, bidiyone sai kuma voice kusan guda biyar, bidiyon ta fara shiga hannunta na rawa. Abinda ta gani a bidiyon ne ya sanya wayar kusan subucewa, “Kutumelesi! Surajjjj!” Ta furta da wani irin sauti tana ƙanƙance idanunta cike da bala'i........

Wacce ta shirya payment yanzu kafin mu gama Book 1, 800₦ ne saura page 2 mu kammala, a saka a wannan account ɗin 7041130088 Aisha Alhaji Yahaya Opay, a turo shedar biya ta 09116099486.

Readers Also Read