Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 17
Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 17: Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 17. Ina shaida muku ko shafin farko ba mu bude na littafin hadin kaddara…
3,203 words
Ina shaida muku ko shafin farko ba mu bude na littafin hadin kaddara ba, ku hanyarta biya kada ku bari nishaɗin nan ta wuce ku, ga wadanda suka san rubutu sun sani, ba za ku yi kaico ba, labari na gaba tafiya ce miƙakkiya wacce za ta gamsar da ku in Sha Allah. [5/20, 1:07 PM] Oum khadeejarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀
By
AyshaNalado
Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍
BOOK 1
Page 24
Takaici da tashin hankali, ba su bari ta iya gama kallon hadadaden bidiyon da aka haɗa hotuna da short clips ɗinta wanda aka ɗauketa a gidan Mother a sirrance ba tare da saninta ba , cikin salo na romantic video editing mai bayyana zazzafar soyayyar Suraj a gareta, tare da voice over na kalamai masu zafi da taba zuciya. Dakatar da shi ta yi tare da kife wayar a cinyarta, ta rintse ido tana fesar da hucin baƙin ciki, zuciyarta banda tafasa babu abinda ta ke yi. Ita Suraj zai yi wa haka? shin da wane lokaci ya samu dama har haka a kanta ya yi mata hotuna harda short clips, yanzu me mutane za su ce, me ya ke so a ɗauketa, tabbas ya ci mata mutunci iyakar cin mutunci. Wayar ta ɗauka ta fara bibiyar sakonnin mutane ɗaya bayan ɗaya, yawanci tambaya ne, dama tana soyayya da Surajudeen Al-Hikima? Ashe Suraj saurayinta ne, wasu kuma fatan alkhari yayinda wasu ke yabon Suraj da taya ta murna da samun irin wannan soyayya, duk ciki babu wanda ta iya amsawa domin idan ta ce za ta yi hakan to lallai za su ji mara daɗi, don haka ma da ta gama ganin sakon take goge chart ɗin. Tana gamawa da nan ta koma kan groups a nan ta tarar da abinda ya lulluka bacin ranta, muhawara aka tafka sosai a group na yan department ɗinsu akan lamarin, wasu na faɗin dama suna soyayya yayinda tsirarun da suka san tsakaninsu ke ƙaryata haka suna bayyana gaskiyar yadda lamarin yake, a General group kuwa. “ Oh my god see luv. Gaskiya sun dace. Wace ce wannan Salmahn ne wai?. Wow the lovers of the year. Gaskiya yarinyar nan ta dace wannan irin soyayya haka. Ta hadu gaskiya, Masha Allah, this is pure love. Awwn this is so beautiful. Love like this is rare. Ire-iren comment ɗin da aka dinga yi kenan, amma masu tambayar wace ce ita sun fi yawa, hakan ya janyo dalilin da aka dinga tagging dinta a group din ana yi wa waɗan da ba su santa ba kwatance da bayaninta, a groups na kawayenta kuwa, zagi da tsokana suka tasa ta da shi a gaba wai dama tana son shi munafuka, jibi yadda take dariya tana nishaɗi tare da shi, waya mutu waya dawo. A last group din da ta shiga a nan ne takaicinta ya ruɓanya, wata yarinya ce yar Meduguri Fannah Bakura, fitattciyar Socialite ce a makarantar, da yan term ɗinta, sune suka ta so ta gaba da zagi da isgili kala kala, yanayin amon kalamansu ya nuna kamar da wata a ƙasa, “In banda kwaɗayi rashin kamun kai da son abin duniya mai zai kai mace gidan su saurayi.” “Iskanci mana, ai da gani ba yau ta saba binsa ba.” “Ai kuwa dai ta yi asara ta bada mata, sam babu class.” “Ku bar jaka yar akuya mana.” Zagi da cin mutuncin salo salo, tsabar bakin ciki bata san sanda hawaye suka fara bin fuskarta ba, ba ta iya ci gaba da duba sakwwanin ba ta kashe wayar gaba ɗaya ta kwanta, babu abinda ke amsa kuwwa a kunneta sai JAKA YAR AKUYA, tunda Ammie ta kawo ta duniya ba'a taɓa yi mata zagin cin mutumci irin wannan ba, amma ba komai laifin Suraj ne, don ko kadan bata ji haushin Fannah ba, wani irin haushi da sabon kiyayyarsa take ji a ranta fiye da na baya, tabbas ba zai ci banza ba yadda ya yi nasarar fassalawa duniya abinda ke lulluɓe a ransa, itama haka za ta fallasa irin kiyayya da ta ke yi masa a gaban dukkan mutanen da suka gani har ya burge su, a gaban dukkan mutanen da suka zageta a kansa, tabbas wannan kukan bakin cikin da ya sanya ta, sai ya yi makamancinsa ko ma fiye da nata ta ci alwashi. Abinda Salmah bata sani ba, ba iya cikin school bidiyon ke trending ba, har a can kafar Tictok, in da a nan ne ya fara daura bidiyon, bidiyon ya samu karɓuwa fiye da tunanin shi karan kansa Suraj ɗin. Muryarsa a voice-over ɗin ta ƙarawa bidiyon wani armashi na musamman, kalaman da ya yi amfani da su suna ratsawa cikin zuciya kamar ana faɗa kai tsaye ga mai kallo. Wannan ne ya sa mutane suka kasa daina sharing likes da comment akan shi, wasu ma suna amfani da muryar a matsayin sound a posts ɗinsu.
Wannan dare ya yi Salmah tsayi, domin yadda taga rana haka bakin ciki da damuwa suna habata rintsawa, masifa ya dinga cin zuciyarta, ta dinga jin kamar ta dauki waya ta kira Suraj tun a daren ta wankesa, sai dai sama ko ƙasa ta rasa lambarsa a wayarta, karshe ta yi tsaki ta kashe wayar gaba ɗaya ta kwanta tana tunanin irin abin da za ta yi masa gobe wanda ko hanya ya hado su sai ya canza, wanda zai sa ya ji ya tsaneta ko kyauta Abie ya ba shi ita sai ya mayar. ba ita ta samu rintsawa ba sai gabanin asuba, ko da ta yi sallah kai tsaye kitchen ta nufa ta haɗa breakfast mai sauƙi, ta shirya na su Ammie a basket, ta koma ɗaki ta yi wanka ta yi shirin makaranta, dressing ta yi ranar na daukar magana, wata hadaddiyar abaya ce, ruwan ƙasa mai karshen tsada, wanda ko makaho ya laluba zai shida haduwarta, to balle ya samu jiki mai structure irin na Salmah kyau kan kyau kenan, kun san dai mutuniyar wajen gayu karshe ce.
tsabar yadda bala'i ke cinta ko ruwa ta kasa sha, kana ganinta kasan tana tattare da ɓacin rai, Abie ne ya yi mata magana ganin bata cin abincin. cewa ta yi ta riga ta ci nata a kitchen ci, Salman kuwa da ya riga ya san abinda ke faruwa kai tsaye a kai ya daura zargin yanayin da take ciki, sai dai ya ja bakinsa ya tsuke don baya son ya janyo hankalin Abie a kan su.
Karfe takwas saura minti uku suka shiga asibitin, sun tarar da Aysha na barci, jikin dai sai a hankali, yanzu haka ma Dr Lukman suke jira ya zo ya sake duba ta, idan da abinda za a kara mata a kara, ba su wani dade ba, su ka yi wa Ammie sallama suka tafi, Ammie ta dauka fushin jiya Salmah ke yi da ita, shi yasa ba ta damu kanta da yanayin da ta ganta a ciki ba.
A bakin get Abie ya sauke su, ya basu kudin transport na dawowa saboda yana sauri, don sai kiransa a waya ma ake yi. Bayan tafiyar Abie duk yadda Salman ya so ya yi magana da Salmah ƙi ta yi, sam bai ga fuska ba, sai ma baƙin glass ɗinta da ta zaro a karamar jakarta da ta yi wa wani irin ratayawa ta yan gayu ta kwama, sai kawai ya shareta, amma a baɗini jininsa a ƙumba yake ya san halinta ciki da bai shirunta akan abu yana nufin abubuwa da yawa, bai ankara ma da shigewarta ciki ba saboda abokinsa Abdul daya karaso inda suke suka tsaya suna gaisawa.
Tun daga bakin gate ɗin, mutane suka fara kallonta. Wasu suna whispering, wasu ma kai tsaye su ke nunata. Amma Salmah ba ta ko waiga ba ta ci gaba da tafiya, sanin all eyes are on her ya sa ta dinga yin wani irin taku mai cike da natsuwa da ƙasaita, sai dai sam fuskarta babu rahama, a haka ta dinga ratsa groups na student kuma duk yawansu magana daya ake idan ma ba shi ake yi ba to ana ganinta ake farawa. Kai tsaye in da take da tabbacin samun Suraj ta dosa, yana zaune tsakiyar abokansa, suna ta hayaniya irinta abokai, da alamar tattaunawar da suke tana tsananin ba su citta, Sadam ne ya fara hangota, da sauri ya taɓa Suraj dake kusa da shi ya sanar masa, hakan ne ya ankarar da su duka zuwan nata, sai suka yi tsit suka zuba mata ido, ba su kadai ba harda group din su Fannah da wasu ma da ma duk sauran mutanen da ke kusa da wajen, har yan nisa da ke iya hangen abinda ke faruwa sai da suka natsu suka zuba mata ido don ganin abinda zai wakana.
Yanayin fuskarta kawai Suraj ya kalla gabansa ya faɗi, da sauri ya miƙe tsaye yana jiran karsawowarta, ai kuwa tana isowa gabansa bata yi wata wata ba ta daga hannu ta sharara masa lafiyayyen marin da sai da siririn farin glass ɗin da ke manne a fuskarta ya faɗi ƙasa. Tsit wajen ya ɗauki shiru tamkar mutuwa ta gifta, domin ko a mafarki babu wanda ya yi tunanin abinda za ta aikata kenan, har shi kansa Suraj ɗin, da sauri ya dafe kuncinsa yana zato ido, hannu ta mika ta cire glass ɗinta, ta yi poiting ɗinsa da shi, kafin ta fara magana a kausashe cike da aji, “Wannan farin na abinda ka aikata min ne, Suraj ka wulaƙanta ni a idon duniya, ka gama burge mutane da labarin soyayyarka ta karya. To ka sani cewa ni ba abin wasar ka ba ce. Ni ba tsarar ka ba ce, kai ba ajina ba ne. Ba na son ka Suraj, bana kaunar ka, na gaya maka sai babu adadi, amma ka ƙi ka fahimta saboda ƙwaƙwalwarka cike take da dauɗar Kuruciya, to ka sani this should be the first and last time da za ka kuma saka ni a cikin haukarka, ka kalle bi da kyau Salmah ba matar yara ba ce ko ka ga ne.” Yadda take maganar shi yafi kowa komai tafiya da imanin mutanen da ke kallon abinda ke faruwa, tana gama fadin haka ta mayar da glass ɗin ta ta juyo ta yi wucewarta ba tare da ta kalli kowa da ke wajen ba.
Tsit wajen ya sake daukar shiru kamar babu halittu da ke motsi a kusa, har sai da Salmah ta yi nisa, sannan hayaniya ta barke kusan lokaci guda kamar wadanda aka bawa umarni, kowa na faɗin albarkacin bakinsa.
Ko motsi Suraj ya kasa yi, saboda mamaki da tsoro, kalamanta sun daki zuciyarsa da karfin gaske, maimaita kan su kawai suke yi a kwakwalwarsa kamar a lokacin take faɗa masa, bai san cewa ya yi suman wucin gadi ba, sai da ya ji Sadam yana taɓasa yana ambaton sunansa, wani irin ajiyar zuciya ya sauke, mai karfi, sai kuma ya zame hannunsa daga cikin na Sadam, ya soma tafiya a hankali yana hade hanya, da sauri Sadam ya yi zabura zai sake binsa, Abbas ya yi saurin rike da tare da girgiza masa kai.............
Wacce ta shirya payment yanzu kafin mu gama Book 1, 800₦ ne saura page 2 mu kammala, a saka a wannan account ɗin 7041130088 Aisha Alhaji Yahaya Opay, a turo shedar biya ta 09116099486.
Ina shaida muku ko shafin farko ba mu bude na littafin hadin kaddara ba, ku hanyarta biya kada ku bari nishaɗin nan ta wuce ku, ga wadanda suka san rubutu sun sani, ba za ku yi kaico ba, labari na gaba tafiya ce cikakkiya wacce za ta gamsar da ku in Sha Allah. [5/21, 9:26 PM] Oum khadeejarh: 🌀 HAƊIN ƘADDARA 🌀
By
AyshaNalado
Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki RUKAYYATU (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍
BOOK 1
Page 25
Tafiya Suraj ya dinga yi cikin fitar hayyaci, domin ko ganin gabansa da kyau ba ya yi balle ya kula da inda yake jefa ƙafafunsa, kaɗaici shine kaɗai abinda yake buƙata a wannan lokacin. Sai da ya shige can karshen campus sannan ya dakata. Wajen tsit babu mutane, da wuya ma wani yazo wajajen sai da kwakkwarar dalili, don sabbin gine ginen da ba a fara amfani da su ba ne a wajen, wasu ma ba a kammala gina su ba, ga kuma tarin bishiyoyi da suka haɗu suka sanya wajen ya yi duhu. Karkashin wani katon itace ya zauna a ƙasa cikin sharar busasssun ganyaye ya haɗe kansa da gwiwa. Jin zuciyarsa yake kamar ta takure ta cure waje guda, wani irin kunci wanda tunda Mother ta kawosa duniya bai taɓa tsintar kansa a ciki ba sai yau, kalamanta masu zafi suka dinga dawowa a kansa tamkar yanzu ke take gaya masa musamman inda take faɗin “Ni ba tsarar ka ba ce. Kai ba ajina ba ne. Ba na son ka Suraj, bana kaunar ka, na gaya maka sau babu adadi, amma ka ƙi ka fahimta saboda ƙwaƙwalwarka cike take da dauɗar Kuruciya, to ka sani this should be the first and last time da za ka kuma saka ni a cikin haukarka.” Sam baya jin zafin marin kamar yadda yake jin zafin waɗan nan kalaman, wanda ya ke jin da ta faɗe su gara ta yi ta zabga masa mari har sai ta ji sanyi a ranta, ji yake a ransa ko sama da ƙasa za su hade ba zai taɓa iya daina sonta ba, yana jin labarin masoyan da suka rataye kansu wasu suka sha guba wasu suka bar gida suka faɗa harkar shaye-shaye a kan soyayya, a baya yana ganin wauta ce, amma a yau a irin yanayin da yake ji a zuciyarsa wallahi zai iya aikata komai a kan soyayyar Salmah. Danshin da ya ji a fuskarda yasa ya fahimci kuka yake yi, hawaye ne suke kwaranya daga idanunsa, sai kawai ya ɗaga kai ya kalli sama ya lumshe idanu yana mai basu damar zuba da kyau, ko zai samu irin sassaucin da yake buƙata a zuciyarsa. Yafi mintina goma cikin wannan yanayin, tun yana yi a zuciya, har ya fito fili ya dinga sauke wani irin numfashi, yana shessheka kamar karamin yaron da aka yi wa dukan zalunci. Bai kara gaskata zancen mutane na cewa zubar hawaye rahama ba ce sai yau, domin ji ya yi kaso hamsin cikin dari na kuncin da yake ji a zuciyarsa ya kwaranye. Sai dai duk da haka, zuciyarsa ba ta samu nutsuwa gaba ɗaya ba. Wani ɓangare na cikinta har yanzu tana masa nauyi, tana masa wani irin ciwo da ba zai iya misaltawa ba.
Ya sauke numfashi a hankali, ya buɗe idanunsa kadan yana kallon hasken ranar da ratsowa daga sararin samaniya ta ratsin ganyanyakin, da suka yiwa wajen rumfar. “Me yasa…?” Ya furta a hankali, kamar yana tambayar wani a kusa da shi. “Me yasa ita…?” ya sake faɗa a hankali tare da runtse idanunsa da ƙarfi, hotonta na sake bayyana a idanun da ƙwaƙwalwarsa kamar wanda yake kallon allon majigi, yadda ta tsaya a gabansa tana jifansa da mummunar kallo na tsantar raini da wukakanci, yadda bude baki tana gaya masa maganganu don ranta, musamman kalmar nan da ta fi komai masa zafi “Ba na son ka Suraj. Na tsane ka…” Tuna wannan yasa ya ji numfashinsa ya soma sarƙewa, ya ɗan girgiza kai kamar yana son kore tunanin… amma ya kasa. A hankali ya kai hannu kan kirjinsa, yana jin yadda zuciyarsa ke bugu da ƙarfi… kamar tana son ficewa daga ƙirjinsa. “Ba zan iya ba…” ya furta da ƙyar. “Ba zan iya daina sonta ba…” Muryarsa ta yi rauni, ta karye sosai kamar ba, buɗaɗɗiyar zazzaƙar muryar nan tasa ta musamman ba. Wani irin shiru ya sake lullube wajen, sai motsin iska mai ɗan sanyi da ke kaɗa ganyayen Wannan yanayin yasa ya ji kamar zuciyarsa na karanta masa wani saƙo, wani abu sabo da bai san shi ba, kalmomi ne a tsare daki daki. A farko bai kula ba, sai dai ko wannen sakon da yake ɓatawa ji yake yi kamar ana raɗa masa su a kunne. Ya lumshe ido a karo na biyu, ya ja dogon numfashi ya fesar, kafin a hankali, cikin rauni, ba tare da ya shirya ba, ba tare da ya sani ba, ya fara maimaita abinda take zano masa cike da ladabi da bin umarni. A hankali ya fara rera waka da buɗaɗɗiyar zazzaƙar muryarsa mai wani irin amo na musamman.
Me yasa zuciyata ke kiran sunanki, Ko da kina nesa kina ƙin ganina? Na rasa kaina a cikin soyayyarki, Ko ba ki sani ba… ke ce raina…
Na ce zan daina… amma na kasa, Na ce zan manta… amma na kasa, Duk inda na dosa, ke nake gani, Ke ce hasken da ya hana ni duhu ya cinye ni…
Ko kina cewa ba kya sona, Zuciyata ta ƙi yarda… Ko kina cewa na bar ki, Raina ya makale a gare ki… Idan son ki laifi ne, To ni zan rayu da wannan laifin… Saboda ke kaɗai ce… Da zuciyata ta zaɓa…
Na ji kalamanki kamar wuta, Sun kona raina sun bar ni babu kowa, Amma duk da zafin da na ji a yau, Ba zan iya kin son ki ba… ko da zan so…
Idan kuka ne zai wanke raina, To bari hawayena ya zuba har ya ƙare… Amma soyayyarki… Ba za ta taɓa gushewa ba a cikina…
Ko kina cewa ba kya sona, Ni zan ci gaba da ƙaunarki… Ko kina korata daga ranki, Ni zan zauna da ke a raina… Saboda ke kaɗai ce… Da zuciyata ta sani…
Rintse idanu ya yi sosai yana tsara baitocin soyayya cike da hikima da baiwa kai tsaye daga zuciyarsa ba tare da ya tsara, ya rubuta ko ya yi nazarinsu ba. Tun yana yi a hankali har bai san san da ya zage ya ware dukkanin karar muryarsa ba.
Tsananin daɗin sautin da tsarin kalaman suka haɗu suka daskarwar da, Salman da Sadam da suka biyo bayansa suna neman shi, da kyar suka hango bayansa da ya juya musu, suka kwaso a guje domin karasawa inda yake, sai dai tun daga nesa sautin ya yi musu maraba, kallon kallo suka shiga yi a tsakanin juna zuciyoyinsu na tainkewa da tsananin tausayinsa, yayinda a daya bangaren, mamakinsa ya cika musu ciki. Sai dai shi bai ma san da wanzuwarsu ba. Salman ne ya fara takawa a hankali ya isa bayansa ya duka tare da dafa kafadarsa, a raunace ya ce “Surajudeen!” Cak ya dakata, kafin ya ware idanunsa da suka rine a hankali har lokacin da danshin hawaye don bai goge ba, sai kuma ya karya kai ya juyo kaɗan ya kalli Salman da gefen ido ba tare da ya amsa ba. Sadam ne zagaya ta gabansa ya duka, ya ce, “ Wow!!! Ma sha Allahu laƙuwata illah billah, Suraj dama kana waka ? Are you a artist? Ko da wasa ba ku taba sani ba, Gaskiya kai dan baiwa ne, You are so amazing wallahi, ga murya, gaskiya an tashi kaina.” zuba masa ido Suraj ya yi cike da nazarin kalamansa, at the same time, abinda ya faru yanzu na dawo masa a kai, shi dai yasan ba ya yin waka, kuma bai taba sha'awar yi ba, balle har ya rubuta ya yi nazarinta.