Kenza eBookz

Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 18

Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 18

Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 18: Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 18. Salman ne ya dakatar da maganar da faɗin, “Suraj let's go, ita almost…

3,331 words

Salman ne ya dakatar da maganar da faɗin, “Suraj let's go, ita almost time, za mu shiga, hall yanzu, ka yi hakuri idan mun fito za mu tattauna akan abinda ya faru, ba zan kyaleta haka ba, zan nuna mata ɓacin raina zai hadaya da su Ammie kai harma da Ya Anas da Hajiya Saude.” yadda yake maganar bil haƙƙi a kausashe kai tsaye mutum zai fahimci ransa ya yi matukar ɓaci da abinda yar uwar tasa ta yi. Ɗan duka a kafaɗa Suraj ya kai masa ya ce“ Wa ya aike ka? Ko da wasa kada ka kuskura ka ɓata mata rai, domin akan hakan za a ji mu da kai, ni ta yi wa laifi ka barni da ita zan hukuntata da kaina, ka rubuta ka ajiye wata rana sai ta duka ta bani hakuri akan wannan lamarin a gaban mutane kamar yadda ta aikata a gabansu, in dai har na cika namiji kuma jinin Sulaiman Saless Al-Hikima.” Yunkura ya yi ya miƙe, suma duk suka mike, ya ce, “ Ku je ku yi test ɗin ku, bana jin yau zan iya shiga aji, mu hade gobe.” Yana gama fadin haka ya soma tafiya ya doshi get ɗin da ke ta wajajen wanda masu aikin gini suka buɗe suna amfani da shi. “Surajudeen!.” Salman ya kwala masa kira bayan ya ɗan yi musu nisa, ba tare da ya juyo ba ya daga masa yatsu biyu, sai kuma ya ci gaba da tafiyarsa, a haka har ya sha kwana ya ba cewa ganinsu.

Da alama za mu samu upcoming Hamisu breaker.😅

Kar a manta da payment, yau ne muka kammala book one, 7041130088 Aisha Alhaji Yahaya Opay, a tura shiadar biya ta nan 09116099486. [5/24, 2:29 PM] Oum Oummeetarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

By

AyshaNalado

Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍

BOOK 1

Page 26

A bangaren Salmah kuwa, kai tsaye class ta nufa ta nemi seat ta zauna hankalinta a kwance kamar ba ta aikata komai ba, jin zuciyarta take yi kamar an wanke mata da ruwan madara, wani nishaɗi na musamman na ratsa ta, duk wani ƙullin takaici da bakin cikin da ta kwana da shi a daren jiya ya kau a zuciyarta. Bluetooth ta ciro a jaka ta yi connecting ta makala a kunne ta kunna wakar Ado Gwanja tana saurara, tana gyaɗa kai. Ko minti goma ba ta yi da zama ba, Zahra Bukar ta shigo class ɗin afujajan, kai tsaye ta nufo ta da sauri cikin yanayin ruɗu da ɗan tsahin hankali ta ce, “Salmah me yake faruwa, I'm confused, na ji wani labari ne da bai min daɗi ba da gaske ne?” wani shegen kallo ta kwashe ta da shi tun daga sama har ƙasa ta watsar, kafin ta bata amsa a gadarance ce, “Yes, da gaske ne abinda ki ka ji, ko za ki rama masa ne.” “A'a A'a ni mene ne nawa, daga gyara kayanka, kuma sai ya zama sauke mu raba? Ni dai kawai ban ji daɗin abinda ki ka yi ba ne, kuma dole na gaya miki gaskiya a matsayina na ƙawarki wacce mu ke tare yau da kullum. Da gaske Suraj bai kauta miki ba ya wuce gona da iri, amma kema kin yi gaggawar yanke hukunci, ina laifin mai sonka, wallahi duk lalacewarsa ya fi makiyinka, balle me Suraj ya rasa banda zuciya da kulafucinta na tsiya, ni dai ina jiye miki yin asarar soyayya mai tsada irin wannan.” “Allah ko?” Ta faɗa cikin sigar rainin hankali, sai kuma ta yi yar dariyar daya kara bayyana yanayin nishaɗin da take ciki, ta ce “Kinga Zahra please je ki, bana don dogon turanci, idan son Suraj ki ke ki fito kai tsaye ki fada bana son wani kwana kwana, na bar miki soyayya mai tsadar okey?” Murmushin takaici Zahra ta yi, bata sake tanka mata ba ganin yadda idanu da hankulan tsirarun daliban da ke class ɗin ya dawo kansu, sai kawai ta nemi waje gefenta ta zauna ta ciro book ɗinta a jaka ta fara dubawa. Hakan ya bawa mutanen daman ci gaba da whispering akan abinda ke faruwa.

Cikin ƙasa da awa daya labarin abin da ya faru tsananin Suraj da Salmah ya gama bazuwa a cikin school tamkar wutar daji, sosai abin ya tayar da ƙura ya janyo cece-kuce a tsakanin matasa, duk inda za ka hangi mutum biyu zuwa sama to za ka tarar maganar da su ke yi kenan, ba ga na cikin classes ba, ba ga yan school compound ba. Kasantuwar ra'ayi riga, kowa da kalar tasa, sai abin ya zama kamar wani zazzafar muhawara a tsananinsu, kowa da bangaren da yake supporting da kuma wanda yake bawa laifi. Daga bakin faculty of arts Fannah Bakura ce tare da yan term ɗinta a zazzuane kan dakalin wajen, kamar sauran dalibai suma tattaunawa suke yi game da abinda ya farun, “Ni fa wallahi Salmah ta tashi kaina, kuma abinda ta yi daidai ne, ko kaɗan Banga laifinta ba, ina dalilin ɓakin ɓaci haka, wallahi na tsani irin samarin nan masu nacin jaraba.” Cewar Beelat, Taɓe baki, Amna ta yi ta ce “Mene ne abin burgewa a abinda ta aikata, yar iskar yarinya kawai mara mutunci, ai wallahi ba ta kyauta ba, kuma in sha Allah, sai ta kwashi kashinta a hannu.” “ Faɗi ki kara Amna, wallahi yau na ji na ƙara tsanar yarinyar nan a raina, shegiya ba wani kyau gareta ba fa, sai kayan mazaunai kamar tukuban tsire.” Dariya su ka yi baki daya banda Beelat da Fannah dake binsu da ido tun ɗazu ba tare da tsoma baki a zancen na su ba. Cikin Dariya Farida ta ce, “ Kai Sumy ba ki da kyau, da alama harda jealous a lamarin nan, domin in gaskiya za a faɗa, komai na Salmah ai abin burgewa ne wallahi son kowa kin wanda ya rasa masha Allah, Ni ma ban goyi bayan abinda ta yi ba, Suraj ya bani tausayi sosai kamar na yi masa hawaye, ina fatan su daidaita don sun dace ba karya.” Fannah da kalaman Farida na karshe suka soki zuciyarta ba shiri ta daga musu tsawa '“Ya isa!” hakan ya haifar da wani shiru nan take a tsakaninsu, idanuta da suka rine ta lumshe ta bude a hankali kafin ta ce, “Chapter close please, bana son ji.” duk shirun suka yi kamar yadda ta buƙata, daga bisani suka sauya wata hirar babu wacce ya sake tayar da zancensu Salmah, sai dai tabar zuciyoyinsu cikin wasi-wasi da tunanin mene ne musabbin fusatarta, tun jiya bayan fitar bidiyon nan, sun lura da yadda ta dauki zafi ta yi uwa tayi maƙarɓiya, ta zaƙe tana ta fadar munanan maganganun akan Salmah yan koranta na taya ta, ita da bata damuwa da shiga harkar duk wani dalibi ko daliba a school ɗin saboda tsabar girman kan da Allah ya zuba mata kamar rainon iblis.

Karfe goma sha daya suka fito daga test. Kai tsaye Salmah gida ta tafi ba tare da ko Salman ta yi wa sallama ba duk da suna da lecture 1 na rana, amma bata da ra'ayin attending. Nemanta Salman ya shiga yi sama ko kasa ya rasata, duk da ya hangi fitarta daga exam Hall ɗin, wajen kawayenta Zahra da Sofiyyah da ya hango ya nufa, kai tsaye ya tambayesu ita, Sofiyyah ce ta amsa masa, “Ba mu ganta ba Salman, muma nan ita muke nema.” “Okay bari na nemeta a waya.” Ya amsa yana kokarin neman layinta, ringing biyu ta ɗaga, “Ki na ina?” ya tamabaya kai tsaye, “Gida.” Ta amsa mishi a sigar da ya yi tambayar, don ta fahimci yana ciki da ita, bai kara cewa komai ya kashe wayar shi, Taɓe baki ta yi, tare da faɗin “Kai ka sani, can ta matse maka.” Ta juya ta ci gaba da girkin da take yi wanda za ta tafi ma su Ammie da shi asibiti.

Ƙarar buɗe get ta ji, tare da shigowar mota cikin gidan, hakan ya ja hankalinta, ta isa bakin window har zata leƙa wayarta data ajiye akan kitchen cabinet ta yi ƙara, sai ta fasa leken ta nufe shi, ganin kiran daga Ammie ne yasa ta ɗaga suna magana. Sallamar da ta ji daga falon yasa ta yi jim tana wasi wasi akan muryar da ta ji, sai kuma ta fito daga kitchen ɗin da sauri wayar kare a kunnenta har lokacin, wanda ta gani a tsaye a tsakar falon yasa ta saki wani irin karar murna, ta kasa da gudu ta nufe shi tana faɗin, “ Oyoyooooo Yayana Oyoyooooo.” Ta tsaya a gabansa ba tare da ta karasa jikinsa tana washe baki fuskarta cike da maɗaukaki farin ciki, a bangaren Anas ma hakan take domin kana kallonsa za ka fahimci tsantsar kewa da begen gida da ke cike a idanu, “Oummu Salama!” Ya kirata da sunan da shi kaɗai ke gaya mata a gidan. “Na'am Yaya, kai ne da gaske?” Ya gyaɗa kai, “Ni ne salama.” Sai kuma duk suka saka dariya irinta tsantsar farin ciki, “Kin girma Oummu Salama, kin zama ammata, ina sauran mutanen gidan? Ina Ayusherta?” ya karashe maganar da wani sauti mai cike da ɗoki wanda ya fallasa asirin abinda ke zuciyarsa game da wacce ya ambatar. “Uhmm wato anan ka maƙale kenan dama.” Ammar wanda shine ya ɗaukosa daga airport ya furta, gabansa na ɗan faduwa saboda zargin abinda idanuwa da kunnuwansa suka hango masa game da amininsa nasa akan yarinyar da yake kwana yana tashi da tunaninta. Sai lokacin Salmah ta kula da wanzuwarsa a falon, “ Laa Ya Ammar, ashe tare kuke ina wuni.” Juyowa ya yi ya kalleta, da sauri ya dauke kai gabansa na faduwa, ya amsa da, “Lafiya kalau Oummu Salama.” ya kirata da sunan da ya ji Anas ya kirata. “Bari na kawo maku ruwa.” ta juya da sauri jiki na rawa ta yi kitchen hakan ya bawa Ammar damar sake kallonta a karo na biyu, “ Ya Subhanallah! Dama haka yarinyar nan take?” Ya faɗa a ransa, ashe ranar kallon tsoro ya yi mata saboda tana cikin hijabi da kuma hasken Aysha da ya dusashe nata a idanunsa a wancen ranar. “Bismillah ga ruwa.” Muryarta ya dawo da shi hayyacinsa, murmushi ya yi ya karba tare da faɗin, “Thank You, Pretty.” Kunya ta ji, amma ta dake ta yi murmushi kawai, miƙawa Anas ta yi, shima ya karba ya kafa kai ya sha sosai, kafin ya sauke kofin, ya yi wani kakkarfar ajiyar zuciya, tare da faɗin, “Bature ya yi gaskiya da ya ce, no place like home, wallahi ko ruwan gida ɗanɗanonsa daban yake, Allah ya yi miki albarka Oummu Salama.” Daga ita har Ammar dariya suka saka, Tafiya ya fara yi yana faɗin “Bari kuga na ga Ammiena.” “ Laa Yaya bata nan fa, babu kowa ma a gidan sai ni.” Dakatawa ya yi ya juyo ya kalleta, “Tana asibiti ne?” “Eh, tare da Aysha, ba ta ɗan jin daɗi an bata gado.” A ruɗe ya ce“ Ya Salam! Me ke damunta, tun yaushe? wane asibitin, na su Ammie?” “Eh' ɗan zazzaɓi ne kawai kuma da sauƙi.” “Allah ya bata lafiya. Lemme take a bath please, sai ka sauke ni.” Ya yi maganar yana kallon Ammar, “Okey take your time.” Jiki a sanyaye ya juya ya nufi ɗakinsa dake makwabtaka da na Salman, zuciyarsa babu daɗi ko kaɗan, damuwa jin ciwon Ayush ya yi 50 50 da karkashi da farin cikinsa na dawowa ƙasar haihuwarsa. Sai da ya tura kofar dakin ya ji gam, sannan ya tuna da batun key. Sake dawowa falon ya yi, ya tarar da Ammar shi kaɗai yana danna waya, Salmah ta koma kitchen kan aikinta.“Oum Salama.” Ya kwala mata kira kira, “Na'am Yaya.” Ta fito tana amsawa, “Makullin ɗakina yana ina?” “ Yana wajen Ammie, kuma last da aka gyara ɗakin Aysha ce ta yi, ban san inda suka ajiye ba, amma bari na duba maka side drower na san ba zai wuce nan ba.” Tana maganar ne tana haurawa sama zuwa ɗakin Ammie. Bayan minti biyu ta dawo dauke da key ɗin, tana faɗin, “ Yaya amma dai ɗakin nan naka ya yi kura, baka sanar da zuwanka ba, da an gyara maka shi.” Dan yamutsa fuska ya yi, don Anas ko misƙala zarratin baya son datti ko kazanta. “Anya zan iya wankan nan kuwa, na san toilet ɗin ma ya yi kura.” Dariya Salmah ta yi don ta san halinsa, ta ce“ Ka yi amfani da toilet ɗin Salman mana.” “ Raba ni Sallama wannan ƙazamin.” Ta sake kyalkyale dariya saboda tuno wani lokaci daya shuɗe a baya, kafin tafiyar Ya Anas makaranta. “Yaya ai yanzu ya daina, ya girma.” “Oh really.,” Ya faɗa yana taya ta yar dariyar.” “ Yeah!” “To shikenan, ai zan gani.” ya juya ya koma domin ya yi amfani da toilet ɗin Salman kamar yadda ta ba shi shawara, ita kuma ta koma ta ci gaba da kwashe girkin da take yi.

Karfe ɗaya da kwata motar Ammar ta yi parking a harabar, Nagarta special hospital, Salmah ce ta fara buɗe bayan motar ta fito riƙe da babban kwandon data shirya warmers ɗin abincin da ta riko, sai kuma katon ledar fruts da Ammar ya tsaya ya siya a hanya, da sauri Ammar ya isa gabanta ya ƙarba ledar, ya kara miƙa hannu zai karɓi kwandon ta janye, tare da faɗin, “Ka barshi Ya Ammar zan riƙe.” “No pretty ki kawo Please ba girman ki ba ne.” “Na shiga uku!” Ta faɗa a ranta, ba shiri ta sakar masa, ya juya da kayan suka fara tafiya shi da Anas da yake jiransa, ta kai minti ɗaya da rabi a tsaye inda ya barta cikin wani irin baƙon yanayi a gare ta, don har sai da ta daina hango bayansu kafin ta rufa musu baya da sassarfa sanin ba su san ɗakin ba.

Suna tsaye kuwa suna jiranta, kasa kallon Ammar ta yi saboda yadda take jin idanunsa dabam dana Ya Anas a jikinta, a haka ta zo ta shige gaba suka bi bayanta, duk da hijab ta saka, sai ta ji ta kasa sakewa sosai saboda Ammar.

Ammie na zaune a farar kujerar roba, tana faman lallaɓa Aysha dake zaune jincire da pillow, akan ta daure ta sha tea ɗin da ta haɗa mata, su ka ji an turo kofar ɗakin tare da sallama, a tare suka kalli bakin ƙofar. Duk da daga Ammie har Aysha sun san da batun dawowar Anas, a cikin satin, sai da ganinsa ya daki zuƙatansu har hakan ya kasa ɓoyuwa a fuskokinsu, musamman Ammie da soyayyar Anas yake na musamman a zuciyarta, sai dai kasancewarsa ɗan fari, ba a iya gane hakan a bayyane sai dai a aikace, yanzu ma bayan kyakkyawar murmushin da ya kwace mata, bata ce komai ba, sai dai duk da haka idanunta sun fallasa asirin zuciyarta shekara shidda ai ba kwana shidda ba. Cike da ɗokin ganinta ya isa gabanta ya tsuguna, tare da kama hannayenta, “Ammienah!” ya furta yana kallon kyakkyawar fuskarta, lokacin guda kuma yana sake haɗe hannunwansa da nata, yana Bata amsa ba sai murmushi kawai take yi, “Ammie i really missed you.” Sai kuma ya juya ya sauke idanunsa akan da tunda ta daura idanu akansa gabanta ya hau wani irin bugu, “My Ayush!” Ya faɗa kai tsaye ba tare da nauyin Ammie ba, da alamar a shirye yake tafe don fallasawasa duniya soyayyar da ya raina na tsayin shekaru takwas a zuciyarsa.........

Wacce ta shirya payment yanzu kafin mu gama Book 1 800₦ ne , a saka a wannan account ɗin 7041130088 Aisha Alhaji Yahaya Opay, a turo shedar biya ta 09116099486. [5/30, 5:54 PM] Oum khadeejarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

By

AyshaNalado

Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍

BOOK 1

Page 27

*BARKA DA SALLAH*

Rass! Gabanta ya yanke ya faɗi, Da sauri ta kalli Ammie, sai dai ga mamakinta babu wani sauyi ko razani a tare da ita ba, sai ma juyowa da ta yi tana kallonta har lokacin da sanyayyar murmushi a fuskarta, ta sake juyawa ga Salmah da tun shigowarsu ta nemi waje ta zauna akan extra bed din dake dakin, da kuma Ya Ammar dake tsaye daga bakin kofa jingine da bango, kafin ta hadiyi wani busashen miyau, ta kallesa ta saki wani gajeren murmushi wanda iyakarsa laɓɓanta, ta amsa masa da faɗin “Na'am Yayana, Oyoyo.” Murmushi ya yi yana sake narke idanunsa a kanta ya ce “Gawa ta ƙi rami. Ya jikin?” “Da sauƙi Alhamdulillah.” Ta amsa a sanyaye da muryarta ta marasa lafiya, “Ma sha Allah, Allah ya kara miki sauki Ayush, duk da nasan don kar ki tarbe ni ne, kika langwabe ki ka kwanta ciwo har gadon asibiti.” Murmushi kawai ta yi ba tare da ta amsa masa ba, ta riga ta saba da yanayinsa na barkwanci, haka yake very simple, har ma yafi Salman sakin fuska da sauƙin kai, duk yanayinsu ɗaya da Abie. “ Ina wuni Ammie?” Ammar ya tsuguna daga inda yake tsaye ya gaisheta, “Laa Ammar ashe tare ku ke, wallahi ban kula ba.” yana murmushi ya ce “Tare muke Ammie ya mai jikin?” “To gata nan da sauƙi dai zance Ammar.” “Allah ya kara sauki. Sannu Sister, ya jikin naki?” Ya mayar da gasiuwar kan Aysha, “Da sauki Ya Ammar ina wuni?” “Ina gajiya mai babban suna, Sannu Allah ya kara miki lafiya.” Da Amin duk suka amsa. Sai sannan Anas ya mike daga gaban Ammie ya koma kusa da Salmah ya zauna, Ammar kuma ya ja farin kujerar roba irin wanda Ammie ke kai ya zauna shima, nan take hira ta barke , a tsananin Ammar da Anas, irinta abokan da suka dade ba su ga juna ba, hirar tafi karkata ne akan labarin kasar da ya baro Singapore, yadda ya dinga gudanar da rayuwarsa a can, kalubalen da ya ɗan fuskanta da farko kafin ya saba da kasar, hakan ya sa daƙin ya yi tsit, suna saurarensa, sai Ammar da ke yi masa tambayoyi da sharhi, Ammie na saka musu baki jefi jefi. Salmah kam kasa sakewa ta yi saboda idanun Ammar da ke yawo a kanta, ta takura sosai ga wani irin kunyarsa da take ji, ita kanta har mamakin kanta take yi, kamar ba ita ba, wayarta ce ta ɗauki vibaration, alamar shigowar kira, da sauri ta katse kiran, ta ɗago a ɗan diririce kamar mara gaskiya ta kalli mutanen ɗakin. Duk babu wanda ya kula da yanayinta, illah Ammar da rabin hankalinsa ke gareta, ganin haka yasa ta lallaɓa ta haye can karshen gadon ta shiga latsa wayar, kimanin mintuna goma, ta gado kaɗan cikin dabara ta shiga yiwa Aysha da ta koma ta kwanta lamo ta lumshe ido kamar mai barci tana sauraren muryar Ya Anas da ke sanya zuciyarta girgiza bidiyo ba tare da sanin kowa ba. Mintuna ashirin suka kuma shuɗewa a haka kafin a turo kafar ɗakin, Salman ya shigo bakinsa dauke da sallama can ƙasar maƙoshi, fuskar nan tasa turbune, babu alamar Rahama, duk ido suka zuba masa yayinda Ammie da ita kadai ce ta ji sallamarsa ta amsa masa, bai kula da baƙin da ke cikin dakin ba har sai da ya mayar da kofar ya rufe ya yi taku biyu, kafin idanunsa suka hasko masa ya Anas zaune a bakin gado yana sakar masa sanyayyar murmushin nan nasa mai kwantar musu da hankali. Turus ya yi irin na ganin bazata, sai kuma ya juya ya kalli Ammie, ya miƙa hannu ya murza ido ya sake juyawa gefen da yaga Anas still ya sake ganinsa, sai kawai ya nufesa da sauri suka rungume juna suna dariya, Ammie da Ammar na tayasu, Aysha da har lokacin idanunta ke lumshe, ta kasa budewa saboda gani take kamar za su gane halin da zuciyarts ke ciki ta kwayoyi idanunta, ita ma murmushi take yi, don tana hasaso mai ke faruwa a zuciyarta, Salmah kam ɗauke kai ta yi, tare da taɓe baki, duk da zuciyarta cike take da shauƙi da farin ciki.

Readers Also Read