Kenza eBookz

Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 19

Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 19

Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 19: Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 19. Zuwan Salman ya kara rikita ɗakin, tuni ya mance da buhuhunan masifar…

3,351 words

Zuwan Salman ya kara rikita ɗakin, tuni ya mance da buhuhunan masifar da ya yi dako ya niko gari takanas ya bar lecture don ya zo ya sauke su akan Salmah. Nan da nan ya ɗauki waya ya kira Abie ya mai albishir ya kira Hajiya Saude da Aunty Aina'u, ya shiga kiran dangi makusanta yana sanar da su, har ya gangaro kan lambar Suraj, nan take abinda ya faru da safe ya dawo, yanayinsa ya canza har hakan ya bayyana a fuskarsa ya ɗago ya kalli Salmah, cikin sa'a itama ta kallosa ya watsa mata wani shegen kallo da ita kaɗai ta san ka menene, bata yi ƙasa a gwiwa ba ta balla masa harara tare da jan dogon tsaki mara sauti, ya yi ƙwafa tare da kau da kai, ya kara waya a kunnensa ya fara magana da Uncle Adam, da ya mayar da akalar kiran Suraj kansa.

Ammie ce kaɗai ta kula da abin da ya faru, bata tanka ba, a zuciyarta ta ce “Allah ya yaye muku.” a zahiri kuwa ta ce, “Salmah taso ki zuzzubawa mutane abinci mana, sam baki da wayo, komai zai an koya miki.” Dan turo baki ta yi kasancewar Ammie ta bata baya, sai kuma ta saci kallon Ammar cikin sa'a suka hada ido, da sauri ta sunne kai, a diririce ta shiga kokarin zamowa daga gadon. Murmushi ya saki tare da kawar da kai, ya mayar kan agogon hannunsa, ganin lokacin sallah ya yi, ya ce, “Ammie ai ina ganin a bari mu yi sallah.” Ya yi maganar tare da miƙewa, “Gaskiya kam.” Anas ya faɗa shina yana kallon agogo “Lokaci ya yi ko? To babu laifi, muma bari mu yi namu tukunnah.” Cewar Ammie. Mikewa Anas ya yi ya kama hannun Salman ya ja shi suka fice a tare su uku.

*************

Yanayin shigowar Suraj ya yi matukar tayarwa Mother da hankali, da sauri ta saki jaka da gyalen da ke rike a hannunta tana kokarin yafawa, domin cikin shiri fita take. Ta nufosa da sauri tana faɗin, “Innalillahi wa Inna ilahi raji'un! Surajudeen! What's happening, me ya sameka haka?” Ta sake bin ƙafarsa da ya yi futu futu da ƙura da kallo, ga dukkan alamu tafiyar kasa ya yi mai nisan gaske kafin ya iso gida, ga idanunsa a zurme sun ƙanƙance sun rine, fuskarsa ta yi jajur musamman siɗe ɗin da Salmah ta mare shi, farar rigarsa a cukurkude duk jirwayen datti da hawaye kamar ba ita ya saka tana ɗaukar ido kafin ya bar gidan ɗazu ba. “Ka gaya mini Suraj, na ce meya faru baka da lafiya ne?” ta sake yi masa tambayar tare da miƙa hannu kasancewar ya fita tsawo ta shiga taɓa wuyansa zuwa goshinsa don ta tabbatar da abin da take zargi, jikin da zafi kuwa don da gaske zazzaɓin yake. Murmushi karfin hali ya sakar mata tare da rike hannuta, muryarsa a dusashe ƙasa-ƙasa ya ce, “Babu komai Mother, I'm fine.” sai kuma ya saki hannunta ya raɓa gefenta ya haura sama zuwa dakinsa. Kamar mutum mutumin tabi bayansa da kallo har ya ɓacewa ganinta, sai kuma kamar wacce ta farfaɗo daga suma, ta zabura ta zura da gudu ta bi bayansa, sai dai kafin ta iskesa, har ya banko kofa ya murza key.

Sosai hankalin Mother ya tashi domin tunda take da Suraj, yau yana neman shekara ashirin da biyar a duniya bata taɓa ganinsa cikin irin wannan yanayin ba, ko bashi da lafiya jikinta yake kanannaɗewa, kamar sabon ɗan yaye, ya yi ta zuba mata shagwaɓa. Tana da tabbacin koka menene yake damunsa, ba ƙarami ba ne. Sai da ta yi tsayuwar kusan mintuna goma tana knocking tana kiran sunansa amma shiru ko motsinsa bata sake ji ba, jiki a sanyaye ta koma ta zauna ta zuba tagumi, ta rasa me ke yi mata daɗi, tuni ta manta da fitar da shirya yi, kimanin mintinan ashirin ta kwashe a haka, kafin ta zabura ta ɗauki wayarta ta shiga kiran layin Salman, domin tana da tabbacin a wajensa kaɗai za ta iya sanin meke faruwa, sai dai cikin rashin sa'a wayar ta ƙi shiga, sai ta mayar da akalar kiran kan Bunayyah.

A daidai wannan lokacin Mr AA, yana zaune a gaban Abba da kuma baban aminin Abba wanda suke tamkar, tif da taya saboda shakuwa da sanin juna, Alhaji Kabiru , abokinsa ne tun na yarinta irin abotarnan da ɗaya baya iya aiwatar da wani abu a rayuwarsa sai da sanin ɗayan, duk wani gwagwarmaya da faɗi tashin rayuwa tare su ka yi, har kawo zuwa yanzu. Tattaunawa su ke yi akan yarinyar da Abba ya sanya ya yi masa bincike a kanta wato Aysha. Be ɓoye musu komai game da abinda ya faru tsananinsu ranar da ya sanya su Ussy suka dauko masa ita ba, duk shiru su ka yi suna nazarin lamarin, zuciyoyinsu cike da al'ajabi. A haka wayar AA ta ɗauki ruri, ganin sunan Mother yasa ya nemi iznin su Abba, kafin ya daga wayar. Yadda ya ji muryarta yasa gabansa ya faɗi, ya shiga tambayarta abinda ke faruwa hankalinsa a ɗan tashe, hakan ya sa su Abba suka zuba masa idanu, “ Surajudeen ne, Bunayyah.” Iya abinda ta faɗa kenan ta dakata saboda muryarta da yake rawa kamar tana shirin fashewa da kuka, miƙawa tsaye ya yi yana faɗin “Gani nan zuwa gidan yanzu.” Ya katse wayar ta mayar aljihu, ya kalli Su Abba cike da ladabi ya ce, “ Afuwan Abba, ina tunanin babu lafiya zan je na ga mai ke faruwa.” Gyaɗa masa kai Abba yayinda Abba Kabir, ya ce, “Ashha! Jeka maza Ahmad Allah ya sauƙaƙa, ka gaida Asma'un”. “To Abba.” ya Amsa tare da ficewa da sauri, hakalinsa a ɗan tashe, sai dai kwata kwata hakan bai nuna a yanayinsa na zahiri ba saboda tsabar iya kamewa.

Bayan tafiyar AA Abba Kabir ya zakuɗa ya kalli Abba ya ce, “Anya baka tunanin makirci a lamarin yarinyar nan, sam ban ji na gamsu da bayanan Ahmad ba.” Abba ya sauke ajiyar zuciya mai karfi kafin ya ce, “Ahmad yana da zurfin tunani da kaifin basira fiye da duk yadda muke tunani, na san ba zai tasa mu a gaba ya fada mana son ransa ba, amma ni ma ina tantama game da wannan al'amari, idan babu rami me ya kawo zancen rami? Sai dai ba Ni da ja, domin ina da kyakkyawar yaƙini akan Ahmad.” cikin ɗan hasala Abba Kabir ya tari numfashin Abba, “Bai kamata mu bar maganar nan haka ba Idris, wannan sanyin naka shi ya sanya har yau muka kasa yi wa wannan tufkar hanci, shekaru sama da arba'in ana abu ɗaya, ya ƙi ci ya ƙi cinyewa kamar cin kwan makauniya, idan har su sun gaza ganin bayanmu, to ya zama dole mu muga nasu, wannan karon ba zan goyi bayanka, rayuwar Ahmad tana da mahimmanci, a garemu da al'umma gaba ɗaya a yanzu haka shine kashin bayanmu, ya zama dole mu ba shi kariya da iya iyawarmu.” Murmushi Abba ya yi, ya ɗauki ruwa a cup dake ajiye kan table ɗin dake gabansu, ya kurɓa kaɗan ya mayar ya ajiye, ya fuskanci Abba Kabir da kyau ya ce “Ai ba za su taɓa iya cimmana ba, domin mun riƙe Allah, kuma ya tsaya mana, ba domin haka ba, shekara arba'in ai ba kwana arba'in ba, ko ka tuna abin da ya faru shekaru takwas baya?” Ya karashe zancen da tamabaya idanunsa akan Abba Kabir alamar yana jiran amsa daga garesa. Gyaɗa masa kai ya yi, ba tare da ya iya bude baki ba. Abba ya sake yin murmushi ya ci gaba da cewa, “Wayon mu ne, ko iyawarmu?” Ya girgiza kai sai kuma ya baiwa kansa amsa, “Babu ɗaya Kabir, Allahn kenan ai, ina fatan ka gane.” Gyaɗa kai Abba Kabir ya yi cike da gamsuwa fara'ar fuskarsa ta faɗaɗa, sai dai kafin ya kai ga sake furta wata kalma, Aunty Rukayya ta shigo falon bakinta ɗauke da sallama, kamar kullum cikin kwalliyarta na hamshaƙan mata, gaban Abba Kabir ta ɗan risina ta ce, “Ina kwana kawu.” Ya bita da kallo yana yar murmushi ya amsa, “Lafiya ƙalau Rukayya, fatan ki na lafiya.” “Lafiya kawu, ya su Aunty Binta da sauran yara.” “Kowa na nan ƙalau duk suna gaishe ki.” Shigowarta shane ya daƙile wancen hirar suka maye gurbinta da wata, Aunty Rukayya ɗiya take ga Alhaji Kabir, yar marigayi yayansa ce Malam Tukur, shi ya aurawa Abba ita bayan rasuwar matarsa Hajiya Zainaba mahaifiyar Ahmad, da shekara ɗaya, ita kuma lokacin tana zawarci, bayan mijinta mahaifin tilon yarta, Na'eemarh, ya gudu ya barta daga cewa zai je ganin gida, ashe ya sayar da ɗan gidan da suke ciki sai watso mata kayanta aka yi wajen, a garin haka ne ta ci karo da takardar sakin da ya rubuta ya saƙale mata a inda yake da tabbacin duk ranar da ta zo kwashe kaya za ta ci karo da shi....

*************

Cikin ƙanƙanin lokaci AA ya isa Kangiwa Estate, har lokacin Mother na zaune a falo, ta zuba tagumi da dukkan hannayenta biyu, ta yi zurfi cikin tunani sai zaman shi kawai ta ji a kusa da ita, ta ɗago ta kallesa, da idanunta da suka kaɗa, hannunta ya kama, ya rike cikin ƙasa ƙasa da murya ya ce, “Me ya samu Surajudeen ɗin?” Sai da ta ja dogon numfashi ta fesar, kafin ta shiga ba shi labarin halin da suke ciki, bai katse ta ba har ta dasa aya. Shi kansa ya cika da mamaki kuma yana da tabbacin koma menene to tabbas ba karamin abu ba ne, zai jefe Suraj a irin wannan yanayin, sai da ya kwantar mata da hankali, kafin ya mike ya haura sama zuwa ɗakin Suraj ɗin, turawa ya yi ya ji shi a kulle, sai ya shiga knocking kaɗan kaɗan, nan ma ba wani motsi, a hankali ya shiga kiran sunansa ya basa umarnin bude ƙofar. Jin muryar AA ya sanya Suraj dake zaune a tsakiyar gadonsa ya tankwashe kafa ya dukar da kai yana ta rubutu cikin wata ƙatuwar memo ya ɗago kai, ya kalli kofar, “ Ya B!” Ya furta akan labbansa, sai kuma ya miƙe jiki a mace ya nufi kofar ya cire lock ɗin, jin haka yasa AA murɗa kofar dakin ya shiga bakinsa dauke da sallama. Kallo ɗaya Suraj da ya koma bakin gado ya zauna bayan ya bude kofar, ya yi masa kamar wani mara gaskiya ya yi ƙasa da kansa. Daga bakin kofa A A ya yi tsaye yana karewa masa kallo, kusan mintuna biyar a haka, kafin ya sauke idanunsa a kan memo da pen ɗin dake a tsakiyar gadon ya ɗan kura musu ido suma, kafin ya taka a hankali ya isa gaban gadon ya miƙa hannu ya dauƙa yana dubawa............

Wacce ta shirya payment yanzu kafin mu gama Book 1 800₦ ne , a saka a wannan account ɗin 7041130088 Aisha Alhaji Yahaya Opay, a turo shedar biya ta 09116099486. [6/5, 8:29 PM] Oum Oummeetarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

By

AyshaNalado

Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍

BOOK 1

Page 28

Ya fi mintuna goma yana kallon rubuce rubucen da ke cikin memo ɗin, tare da baje su a faifan tunaninsa, ya shiga nazartarsu daki daki. Sosai rubutun ya ja hankalinsa, sai dai ya kasa tantance salon magana ce ko waƙa ya rubuta, ya san dai koma mene ne an tsara shi cike da baiwa da kwarewa. Abin da ya iya fahimta kawai, labarin soyayyarsa ce ya bayar a takaice, tun daga ranar da ya fara ganin yarinyar har zuwa kan abinda ya faru tsananinsu a safiyar yau, wanda a fahimtarsa shine musabbabin da ya jefa sa a halin da yake ciki yanzu. lumshe idonu AA ya yi, yana jin kamar zuciyarsa na narkewa, labarin soyayyar Suraj da ya karanta ya tasar masa da wani tsohon mikin da ya gaza warkewa tsayin shekaru a zuciyarsa, cakwakiyar da ke cikin tasa soyayyar da Noorie ya fi karfin a rubuta shi a cikin 'yan wasu ƙayyadaddun kalmomi irin wannan. Wani irin tausayin yaron ya ji ya kama shi, duka duka shekarunsa nawa ma wai tukunna? Ya aiyana a ransa, Girgiza kai ya yi “ hmm... soyayya!” ya furta akan laɓɓansa, tare da taune lips ɗin kaɗan, sai kuma ya rufe littafin, ya nemi waje kusa da Suraj da har lokacin bai sake ɗagowa ya kallesa ba ya zauna, ya daura masa littafin a kan cinyarsa, “Surajuddeen!” ya kira sunansa da wani amo na musamman da ya tilasta masa ɗago kansa kaɗan ya kallesa, “Soyayya ce ko?” Ya sake faɗa da sigar tambaya. Gyaɗa masa kai Suraj ya yi, sai kuma ya faɗa jikinsa da sauri ya kwantar da kansa a kafadarsa ya saki kuka, tallafe bayansa AA ya yi yana dariya, “Kai shashasha mene ne haka, be a man mana.” “Let me Ya B, let me cry on your shoulder, kar ka hana ni please.” Shiru AA ya yi, yana jin kukanshi na taɓa masa zuciya, wannan wacce irin yarinya ce haka, da ta sanya masa baby kuka, shi kuwa ko da lu'u lu'u da murjani aka ƙerata sai sun mallaketa, ko zuciyarta ta karfe ce, sai ta so Surajudeen soyayya mara iyaka, ya dauƙi wannan alkawarin. Be hana shi kukan ba kamar yadda ya roƙa har sai da ya yi mai isarsa ya yi shiru, yana sauke ajiyar zuciya, sannan ya ɗago shi ya zaunar da kyau, “Kalle ni Suraj.” Ya furta a tausahshe. A hankali ya ɗago ya zuba masa manyan idanunsa da suka ƙara rinewa, fuskarsa dauke da danshin hawaye. AA ya girgiza kai a hankali, yana kallonsa da wani irin tausayi da kuma ɗan tsauri a lokaci guda. “Is this how weak you are?” Ya faɗa a ɗan kausashe. Da sauri Suraj ya girgiza kai, alamar A'a, lokaci guda wasu hawayen suka sake ziraro masa, da sauri ya saka hannu ya share. “A haka dama ka ke tunanin ta so ka, kana kuka kamar mace?.” ya sake girgiza kai. Ajiyar zuciya AA ya sauke sai kuma ya tausasa murya kafin ya ci gaba da cewa “Haƙiƙa na ji kunya Surajudeen. Shin ina mazantakarka take? Ya ɗan sahirta yana kallon cikin idanunsa, kafin ya daura “Ka sani kuka ba shine mafita ba, kuka gazawa ce rauni ce a soyayya, kai ba rago ba ne, domin ba ka fito daga tsatson ragwaye ba, ka je ka bincika tarihin soyayyar Mother da mahaifinka as an assignment.” Ya ɗora hannunsa a kafaɗarsa, ya ɗan bubbuga “Idan har kana sonta da gaske. to ka tsaya tsayin daka. Ka jajurce. Ka yi yaƙi tuƙuru, ka mallaki abinda ka ke so da karfi da jarumtarka.” Ya ɗauke hannunsa a kafaɗansa, ya kama haɓarsa ya ɗan ɗago kaɗan. “Kar ka sake bari hawaye su zama makamin ka. Ka mai da zuciyarka ta ƙarfe, ta yadda za ta iya jure duk wani gwagwarmaya, ba tare da ta tarwatse ba, ina so ka min alƙawarin ba za ka sare ba, ba za ka janye ba, babu gudu babu ja da baya har sai ka yi nasara, ina tare da kai zan tallafeka, ba zan taɓa bari ka faɗi ba.”

Kallonsa kawai Suraj ke yi, yayinda zuciyarsa ke wani irin buɗawa, duk wata kalmar da yake faɗa tana shiga kasan zuciyarsa kai tsaye tana tasiri, tare da samun Kyakkyawar matsuguni. Take duk wani tsoro da raunin da suka soma tasiri a kansa suka juye zuwa jarumta, hawayen da ke gudana a idanunsa suka ƙafe. Murmushi AA ya saki, saboda fahimtar da ya yi wutar da ya kunna ta soma ruruwa. “Ka nuna mata kai ba ƙaramin yaro ba ne, daga ranar irinta ta yau, ina son ka yi min alƙawarin ba za ka sake zubar da hawaye akan ta ba, ba za ka sake kuka kamar mace ba, kada ka sake nunawa kowa rauninka akanta.” Lumshe idanu Suraj ya yi a hankali ya buɗe akan fuskar yayan nasa, kafin ya gyaɗa masa kai, ya kara da faɗin, “I promise Ya B, Amma ina neman alfarma, ka bani dama duk lokacin da na ji ina buƙatar yin kuka zan zo in da kake zan yi a gabanka.” murmushinsa ne ya faɗaɗa ba tare da ya shirya ba, ya shafa kumatunsa, ya ce “ Na baka wannan damar ƙanina, ina maraba da kai a kowanne lokaci, ina yi maka fatan nasara.” Ta shi ya yi ya rungumesa, “Thank you, Ya B, I really love you.” “ I love you too, kanina Romeo baban soyayya, Oh ya Rab! Wai har baby Surajudeen ya girma har ma ya balaga, ya fara neman aure.” Da sauri ya sake shi ya yi baya, sai kuma ya kwashe da dariya tare da rufe fuska da tafukansa irin ya ji kunya. Shima ɗan murmushi ya yi.

“Wace ce, surukar tawa?”

“Sunanta Salmah Mu'az, yar uwar tagwaitakar abokina Salman.”

“Wonderful! kana nufin Salman dai da na sani.”

“E shi, Yayarsa ce, ita ce Hassana shi Hussaininta.”

“Kai kai kai ka ce yayarku ce,da gaske fa ka yi mata yaro Surajo magana ta domin Allah.” Ya yi maganar cike da zolaya. Dariya Suraj ya yi, a zuciyarsa ya ce, “Sai kun aura min ita za ku samu tabbacin wannan amsar ba yanzu ba.” A fili kuwa cewa ya yi, “Ba komai na ji, na amince, zan bata girmanta zan yi mata biyayya, in bita sau da kafa, ko kara ta ajiye ba zan tsallake in Sha Allah.” Sosai zancensa ya bawa AA dariya, ai kuwa suka hau darawa a tare kamar ba babu mai wata damuwa a cikinsu.

Dai dai wannan time ɗin Mother ta turo kofar dakin ta shigo. Tana can zaune a falo in da AA ya barota cikin alhini da tsumayen sakkowansa ta ji abinda ke faruwa, sai dai shiru kamar malam ya ci shirwa ba shi ba dalilinsa tun tana irga mintuns tana kallon agogo har ta sare, ganin wankin hula na neman kai ta dare yasa ta mike ta biyo bayansa, sai dai me? Tun da ta sharo kwanar dakin take jin dariyarsu na tashi, hakan yasa ta kara da gudu har tana tuntuɓe.

Ja ta yi ta tsaya a bakin kofa tana binsu da kallo baki sake. Hakan ya karawa dariyar tasu power sai ta hau tafa hannu tana sallallami, “Allah Ubangiji ya shirya min ku.” ta furta kafin ta girgiza kai ta fice, tana hamdala a zuciyarsa, lokaci guda kuma duk wani nauyin da zuciyarta ya yi a dazu ya shiga yayewa kaɗan kaɗan....

******

A can asibiti kuwa, wunin ranar ya zamto na musamman a gare su, saboda kasancewar Ya Anas a tare da su. Yanayi ne da suka jima suna kewa. A kallo ɗaya idan ka yi wa fuskokinsu za ka shaida haka, ba ga Ammie ba, ga ba 'ya'yan nata ba, hatta Aysha da ke halin jinya, jin yau ɗin take na dabam, duk da tarin fargabar da ganin nasa ya haifar mata.

Hakan ya yi tasiri matuƙa wajen rage mata nauyin damuwar da ya haifar mata da jinya.

Da takura da lallashi cikin salonsa na barkwanci ta samu ta ci abincin da Salmah ta kawo, wanda rabonta da shi har ta manta.

Cikin Hukuncin Ubangiji kafin yamma sai gata a zaune tana hira harda dariya.

Sosai Ammie ta ji daɗin hakan, musamman da ta gama fahimtar sauyin na tattare da wanzuwar Anas ne, wanda tun daga irin kallon da taga yana yi wa Ayshar, ta tsinci kanta cikin wani irin farin ciki da annashuwa irin wanda ta dade ba ta yi ba, amma sai ta dake ta yi kamar bata gane abinda ke faruwa ba, saɓanin Salman da baya iya gani ya kyale sai da ya tofa. Sai da ya bari Ammie ta ɗan fita, ya kallesu a lokacin Anas na zaune a gafenta rike da plate ɗin abincin da yasa Salmah ta zuba mata, yana rarrashinta akan ta daure ta kara koda cokali biyu ne.

“Ya Anas…” Ya kira sunansa yana sakin murmushin tsokana.

“Salmanu...” Ya amsa ba tare da ya juyo ya kallesa ba.

“Hope ba wata special treatment ake yi a nan ba? Because this level of care, it feels like something more.” Ya ƙarasa yana ɗan dariya.

Readers Also Read