Kenza eBookz

Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 20

Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 20

Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 20: Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 20. Muƙut! Aysha ta hadiye abincin dake bakinta ba tare da ta shirya ba.…

3,305 words

Muƙut! Aysha ta hadiye abincin dake bakinta ba tare da ta shirya ba. Shi ko Anas kyakkyawar murmushi ya saki, ya kashewa ƙanin nasa ido tare da daga mai gira.

“Oshey!! Looks like we are having a good time a nan, ko?” Ya faɗa cike da tsantsar farin ciki.

Duk yadda gabatanta ke faduwa dakewa ta yi, cike da borin kunya ta watsa masa harara, “Kai dai wallahi ka cika surutu Allah, Ya Anas ɗin mu ne fa, ko ka manta ne.”

“Ina kuwa zan manta, ai na gane shi.” Ya amsa mata cikin gatse yana dariya, Ammar da Salmah na taya shi, sai dai ita nata dariyar na yake ne da tashin hankali.

Cikin dariya Ammar ya ce “Kash! Kai kuwa Salman ya lamarinka da haka, lamari na Ya da Ƙanwa, ai ya fi gaban wasa.”

“Ai na fahimta Ya Ammar na janye.” Ya kare da dage hannu alamar surrender.

Zamewa Aysha ta yi ta kwanta, tare da rintse ido duk kunya ta cikata, godiyarta daya Ammie bata ɗakin.

Ci gaba suka ka yi da jan zancen shi da Ammar, Shi dai Anas bai tofa ba illah murmushi da yake binsu da shi, shi kaɗai yasan yanayin da zuciyarsa ke ciki.

Shigowar Ammie tare da Dr Lukman ne ya katse musu yanayin. Sun gaisa da Dr cike da girmamawa kasancewarsa abokin aikin Ammie, ya bukaci da su ba shi guri ya duba mara lafiya.

“Ai Ammie bari na tafi gaba daya kawai, yamma ta riga ta yi gashi har karfe biyar ake nema.” Ammar ne ya yi maganar yana kallon agogon hannunsa bayan ya miƙe.

“Toh Ammar, a sauka lafiya, mun gode sosai Allah ya yi albarka, ka gaida Turan.” Sai kuma ta kalli Anas da shima ya riga ya miƙe, don cika umarnin Dr “Ka bishi ya sauke ka, a gida ka huta ɗan fice gajiyar hanya mana.” Dan yamutsa fuska ya yi, kafin ya amsa da “To Ammie.” ya yi maganar idanu da dukkan hankalinsa na kan Aysha, yana kokarin haɗa ido da ita, ta ƙi basa damar hakan. Shi kansa yasan hana bukatar hutun, to amma buƙatar zuciyarsa ta rinjayi ta gangar jikin.

“Yawwa Yaya mu je, na tayaka hutawa.” cewar Salman, Caraf Salmah ta cafke, “ Ka hana shi hutawa dai.” Wani banzan kallo ya wullo mata, ya yi gwafa tare da shigewa zai fice.

“Ya haka Salman? Daga fadar gaskiya.” Ammar da bai san yadda su ke ba ya yi maganar.

“Rabu da ita Ya Ammar, ba ka san abinda yarinyar nan ta aikata ba ne yau, wallahi ba ƙaramin haushinta na ke ji ba, kuma in sha Allah, you will pay for it.”

Tsaki ta ja, ita sai a lokacinma, take tunawa da abinda ya faru tsabar bata saka shi akai ba.

“Tsaki ko? Ki ci gaba dai.”

“Zo nan Salman, me ya faru?” Ammar da hankalinsa ya fara tashi da sa'insar tasu tun da ba wai ya saba gani ba ne, ya faɗa tare da rike hannunsa ya jasa suka fice daga ɗakin.

“Oummu Salamaaah!” Anas ya kira sunan Salmah yana binta da wani irin kallo, wanda ita kaɗai ta san ma'anarsa.

Dariya ta saka, “Wallahi Yaya ban yi masa komai ba kawai bala'i yake ji da ji kai ma kasan halinsa, ka tambayi Aysha ka ji Allah bana faɗa da shi yanzu na daina.” Girgiza kai kawai ya yi ya kalli Ammie, “Sai na dawo zuwa dare in sha Allah.” “Okey Allah ya tsare.” Idanun Ammie da ke kansa ya hanasa sake juyawa ya kalli Aysha, duk da umarnin da zuciyarsa ke ba shi kenan, haka ya dake ya sa kai ya fice.

A bakin mota ya samu Salman da Ammar, suna magana, yanayin Ammar ya canja lokaci gudu, kuma hakan ya faru ne sanadin labarin Suraj da Salman ya ke basa a takaice, zuwa kan abinda ta aikata yau ɗin.

Dr Lukman ya ji daɗin ganin yadda jikin Aysha ya yi kyau sosai sabanin yadda ya barta da safe. “Alhmdlh 'yar gidan Ammie jiki ya yi kyau.” Ta yi murmushi kawai. “ To Masha Allah, zuwa gobe zan duba idan da yiwuwar ki je gida, in sha Allah.” Ta gyaɗa kai. Ammie ya yi wa bayanin ci gaban da aka samu, kafin ya yi musu sallama.

Da dare tare suka dawo asibitin su uku, harda Abie, wanda ya fara biyawa ta gida ya yi wanka saboda gajiyar hanyar da ya kwaso, sannan kuma don ya yi tozali da ɗan nasa, da yake matukar kewa, wanda tunda rana da ya samu labarin zuwansa, a bakin Salman bai sake sukuni ba. Tare su ka yi sallar magriba da isha da samarin nasa kafin su wuto asibitin. Ya ji daɗin ganin yadda jikin Aysha ya yi kyau, murnarsa ta kasa ɓoyuwa ya yi ta mata sannu harda yar zolaya, a kunyace ta yi ƙasa da kai, tana yar dariya, haka kurum ta sinci kanta da kasa sakewa da shi kamar kullum, musamman da ta daga kai idanunta suka sauka a cikin na Anas.

Ya kula da sauyin amma bai kawo komai a ransa ba, face yanayi irinta masara lafiya rashin son magana, balle ga Aysha da bata da hayaniya.

Wai wajen goma da rabi suka yi niyyar barin asibitin gaba dayansu harda Salmah.

Ammie ta yi musu rakiya har wajen mota, sai da ta bari sun shige sun zazzauna, sannan ta nemi ganin Abie, daga ɗan nisa da motar suka tsaya in da take da tabbacin yaran ba za su jiyo su ba.

“Ya aka yi ne My Dr?”

Murmushin ta yi, ta ce, “Wani abu ke tsungulin zuciyata na ke son na raba shi da kai.”

“Umhh really! To ina jin ki Allah yasa ba wanda zai hana ni barcin daren yau ba ne.”

Ƴar dariyar da ya kara bayyana yanayin farin cikin da take ciki ta saki, kafin ta shiga bashi labarin abinda take hasashe tsakanin Aysha da Anas.

Kallonta kawai Abie yake yi yana sakin murmushi tare da murza saisayayyen gemunsa mara tsayi, mai dauke da farin gashi da tsilli tsillin baƙi.

“Ba ka ce komai ba fa.”

“Ai bakin ne ya mutu murus Dr. Na dade ina tunanin mijin da zan kai wa Aysha wanda ba zai wulakanta min ita ba, kullum ina cikin fargabar rashin amincewar Anas game da zaɓin da na yi masa, Allah ya sani ina jin tausayin yarinyar nan sosai Dr.”

“Mu yi wa Allah godiya Brr. Allah ya tabbatar mana da dukkan alkharin da ke cikin wannan al'amari.”

Lumshe ido ya yi a hankali ya bude alamar amsawa. Kusan mintuna goma suka kwashe suna ci gaba da tattaunawa game da wani muhimmin abu wanda ya kasance sirri a tsakanin su. Kafin daga bisani su ka yi sallama, ya tafi zuciyarsa fari tas tas.....

Saura 2 Pages mu kammala book 1, bisa ga rokon da ku ka yi akan a kara 5 pages, kafin mu kammala ga duk wacce ta shirya biya, ta saka 800₦ a wannan account ɗin 7041130088 Aisha Alhaji Yahaya, a turo min shaidar biya ta nan 07041130088. [6/6, 9:20 PM] Oum Oummeetarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

By

AyshaNalado

Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍

BOOK 1

Page 29

Washegari, kamar yadda ta kasance jiya, tun bayan sallar asuba Salmah ta shiga gyaran gida, bayan ta gama, kitchen ta koma ta haɗa musu abincin kari mai sauƙi, ta shirya na su Ammie wanda za ta kai asibiti a basket, sai da ta gyara kitchen ɗin tas, kafin ta koma ɗaki ta yi wanka da shirin makaranta a gurguje.

Duk da sai 10 take da lecture, tana so ta bi Abie ya sauketa a asibiti ne, daga can idan lokacin ya yi sai ta wuce, don ba ta son ta jera da Salman, gaba yake yi da ita sosai, da sun haɗa ido sai harara da ƙwafa, ita ma take ta ke mayar masa da martani ta kara da “Aikin banza! Bayan ta ka dogon tsaki. Ta san shakkar Ya Anas ne ya hana shi cewa zai kai hannu jikinta, ba don shi ba yadda gidan babu Ammie wata kila da tuni sun dambace.

Kasancewar Abie fitar sassafe ya yi karfe bakwai da ashirin a cikin asibitin ta yi musu.

Sun tarar da Ammie zaune akan dardumar da ta yi sallah, hannuta rike da carbi tana lazumi. Ganinsu yasa ta yi addu'a ta shafa, kafin ta gaisar da Abie, ya amsa mata cike da kulawa da soyayya, ya kara da tambayar yadda suka kwana da mai jikin, da ya tarar ta koma barci.

“Alhmdllh. Jiki yana ta kara kyau, in sha Allah muna saka ran samun sallama yau, kamar yadda Dr Lukman ya faɗa.”

Ya gyaɗa kai “Allah ya ƙara sauƙi.”

“Amin ya Rabbi.” Ammie da Salmah suka haɗa baki wajen amsawa.

Dan tattaunawa su ka yi da Ammie akan maganar aikin da ya karɓa mai wahala, wanda ya saka shi gaba, kwata kwata baya samun hutu cikin kwanakin.

Ammie ta nuna tausayinta a gareshi, ta kuma yi masa addu'a da fatan nasara.

Sosai ya ji dadin hakan, ya kara samun kwarin gwiwa akan aikin. Bai wuce minti goma ba ya yi musu sallamah ya tafi.

Sai sannan Ammie ta dawo da hankalinta kan Salmah da tun shigowarsu bayan sun gaisa da Ammie, ta haye wajen zamanta na jiya, ta kwanta ta juya musu baya tana danna waya.

“Ina sauran mutanen gidan? Ya kuka kwana?”

Ta shi ta yi ta zauna, “Lafiya muka barosu Ammie, don lokacin da mu ka fito ma ba su tashi ba.”

“Shi Salman ba shi da lecturen ne?”

Ambaton Salman da Ammie ta yi yasa take yanayinta ya sauya, “Oho masa, nima ban sani ba.” Ta furta cikin yanayin ko in kula.

Harara Ammie watsa mata. Sai ta kyalkyale da dariya, “Ammie wallahi da gaske na ke yi ban sani ba.”

“Me ya haɗa ku jiya?” Ammie ta wurga mata tambayar tana ci gaba da hararanta.

Rass! Gabanta ya faɗi, ko cikin gigin barci ai ba ta ce wa Ammie ga abin da ya faru ba. Muƙut! Ta hadiyi miyau, kafin ta saki murmushin yaƙe, “Uhm... Amm... Kawai fa, Ba komai fa Ammie, kin san halinsa kema dai.” Ta yi maganar cikin inda inda irinta ta rashin gaskiya.

“Baki da gaskiya Salmah.” Ammie ta faɗa kai tsaye tana kallon cikin idanunta.

“Kaii. Wallahi fa Ammie.” sai kuma ta yi shiru tana zare ido.

“Na san halin kowannenku, Salman ba ya fadan rashin gaskiya, na shaide shi da wannan, duk yadda aka je aka zo ke ce ki ka yi masa ba daidai ba.”

Cikin yanayin shagwaɓa, ta na matso kwallar munafurci ta ce, “Kaii Ammie dama kullum ni ce mai laifi a wajen ki, amma Allah ne shaida ni ban masa komai ba.”

“Zan bincika ai, idan na ji saɓanin abinda ki ka fada ranki zai yi mummunar ɓaci na gaya miki.”

Jiki a sanyaye ta gyaɗa kai, gabanta na luguden faduwa.

Motsin Aysha ya ja hankalinsu gareta, “A'a Aysha kin tashi? Sannu ya jikin?” Ammie ta yi maganar tana nufarta domin ta taya ta tashin da take kokarin yi.

Duk da za ta iya tashi don jikin da sauƙi sosai amma Ammie ba ta barta ba, ita ta taimaka mata ta raka ta har toilet ta yi alwala ta yi brush, ta zo ta yi sallah.

Kafin ta idar Salmah ta zuba mata abinci ta haɗa mata tea.

Akan farin kujera ta zauna, kasancewar drip ɗin da aka daura mata tun cikin dare ya kare Ammie ta cire mata, Salmah ta miƙa mata abincin da tea ɗin da ta haɗa mata, ta fara ci kaɗan kaɗan, suna hirar school da Salmah jefi jefi Ammie na saka musu baki.

Karfe tara da minti biyu, Salman, Ya Anas, da Ya Ammar, wanda shine ya dauko su zuwa asibitin suka shigo ɗaki. Idanun Ammar akan Salmah su ka fara sauka, sam jiya bai iya rintsawar kirki ba saboda tunaninta da ya adabi zuciyarsa, ita kuwa kamar ta san kallo ta yake ko da wasa ta ƙi ɗagowa, domin tana jin muryarsa gabanta ya hau faduwa for no reason.

Sai bayan sun gaisa da Ammie da Aysha, sannan ta dago cike da aji ta gaishe su a tare gaba ɗaya. Cike da ɗokin ganinta ya amsa mata, daga haka suka zauna su ka shiga tattaunawa da Ammie, batu ne mai muhimmanci hakan yasa ta basu dukkan hankalinta.

Ganin haka yasa Salman ya koma kusa da Aysha ya zauna suka hau tasu hirar, yayinda Salmah ta duƙufa kan waya.

kimanin mintuna talatin suka kwashe kafin Ammar ya miƙe yana kallon Agogon da ke daure a tsintsiyar hannunsa.

“Anas, we should go now, it’s getting late.”

“Ok let's go.” Ya amsa shima yana miƙewa.

Addu'a da fatan dawowa lafiya Ammie ta shiga yi musu, hakan ya janyo hankalin su Salman kan su, ganin sun mike za su fita yasa ya diro da sauri.

“Ya Ammar, please let me come with you, you can drop me at school.”

“Okey, ba matsala mu je, kan hanyarmu ne dama.”

Kallon Salmah Ammie ta yi, “Ke ma ba na ji kin ce kina da lecture 10 ba?”

Kamar za ta fashe da kuma ta gyaɗa alamar e.

“To tashi ki bi su?” Ba tare da sake tankawa ta mike ta dauki jakarta na baya karama irinta yan gayu matasan 'yan jami'a, ta goya akan dogon hijab ɗinta irin wanda ake ya yi, wanda ake yiwa laƙabi da me capacity wani mai yanayi da riga, sannan ta rufa musu baya, tana tafiya a hankali kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki.

Kafin ta isa har sun shiga mota sun tayar ita suke jira, baya ta buɗe ta shiga, ta zauna kusa da Salman da ko kallonta bai yi ba, Ammar ya ja motar ya rufe suka ɗauki hanya.

Tafiya mintunar da ba su wuce ashirin ba ya kawo su school ɗin, har cikin makarantar Ammar ya shiga da su, ko da ya sauke su, kuɗi ya debo masu yawa ya fito ya bawa Salman, sannan ya miƙawa Salmah nada har ta fara tafiya itama, dai da ta kalli kuɗin kafin ta daga kai a hankali ta kallesa ba tare da ta karɓa ba. Idanunsu ya hadu cikin na juna, gyaɗa mata kai ya yi, sai ta samu kanta da girgiza masa kai, alamar A'a, ya sake gyaɗa mata kai, ta sake girgiza, ya sake a karo na uku itama ta sake girgizawa, sai kawai suka saka dariya a tare.

“Come on, take it my Friend! Na yi kama da abokin wasan ki ko? Idan Anas ne ya baki ai ba za ki karɓa ba.”

Hannu ta miƙa ta karɓa, tare da faɗin.

“Thank You.”

“You’re welcome… but don’t do that next time. I don’t like being refused.”

Murmushi kawai ta yi, ba tare da ce komai ba ta juya ta fara tafiya, bayanta ya bi da kallo na sakwanni goma, yana shafa sumar kanshi, kafin ya saki murmushi ya juya ya shiga motarsa ya tayar suka fice daga harabar school ɗin a guje........ [6/8, 9:26 PM] Oum Oummeetarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

By

AyshaNalado

Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍

BOOK 1

Page 30

Damƙe kuɗin a hannuta ta yi da karfi, gabanta na faduwa. A hankali ta dinga takawa, ƙafafuwanta na hardewa kamar na me koyan tafiya, saboda tasirin idanuwansa da take ji suna yawo a bayanta. Sai da ta yi taku goma sha kafin ta ji sautin rives da tashin motarsa. Dakatawa ta yi, ta lumshe ido tare da sakin wani wawan ajiyar zuciya, ta kai hannu ta dafe ƙirjinta da ke bugawa, “Ya Salam! Me ke shirin faruwa? Ya Ammar why?” A hankali ta yi maganar da raunatacciyar murya.

“Salmah Mu'az!” Muryar Zahra ya katse mata tunani, da sauri ta ware idanunta, akan Zahra dake nufota da sassarfa. Hannunta ta damƙa, cike zaƙuwa da ɗokin ganinta ta ce, “Mutuniyar tun ɗazu nake ta zuba idon ganinki, na kira wayarki ya fi a kirga ta ƙi shiga.” Ido kawai ta zuba mata tana kallo,saboda yanayin da take ciki. Zahra ba ta kula da sanyin da ke tattare da ita ta ci gaba da cewa, “Jiya kun yamutsa hazo a cikin Campus fe ke da mutuminki, kun bar baya da ƙura, hmmm ko kin san bidiyon marin nan ya fita?” Tamkar dukan wuta, batun ya daki zuciyarta, amma a zahiri ko gezau, yamutsa fuska ta yi ta taɓe baki “And so what?” Kallon ba ki da hankali, Zahra ta watsa mata, sai kuma ta girgiza, “Ina ga baki fahimci abinda nake nufi ba ko?” “Look Zahrah. Go straight to the point, ki gaya min abinda ke faruwa.” “Ai ni kin wuce tunani Salmah Ɗan tsaki ta saki, “Ki na da matsala wallahi.” Ta bata amsa tare da fara tafiya cike da kwarin gwiwa, yayinda daga cikin ƙirjinta, zuciyarta ke dakan uku uku. Zahra bata kara ce mata komai ba sai biyota da ta yi suka jero zuwa cikin school ɗin.

Tun daga yanayin yanda idanun suka yo kanta yuuuuh! ana binta da kallo kamar za a cinyarta ɗanya, ta fahimci da wata a ƙasa. Duk da school ɗin bai kai jiya cika ba, ya fi jiya daukar zafi. Duk in da ta gifta kuskus, da hayaniya ke tashi ƙasa ƙasa, wasu tana jin abinda ake faɗa wasu kuma bata iya tantancewa me suke nufi, take ta samo shinshino abinda Zahra ke son nusar da ita. Siririn tsaki ta ja, ta san dai ba zai wuce akan abinda ya faru jiya ba, mutane sam ba su raina abin gulma. Sake ɗaure fuska ta yi tamau, ta ci gaba da tafiyarta a tsanake, sam babu wani alamar ruɗani a yanayinta na zahiri.

Kai tsaye corridor ɗin da zai sada su da department ɗinsu suka nufa.

“Ah, my celeb friend… seems like you’re the talk of the whole campus today, ko kin lura?” Cewar Zahra ta faɗa tana ɗan murmushin tsokana.

Salmah ta ɗan kalleta da gefen ido ta ɗan ja numfashi kadan sannan ta kawar da kai ta ce. “Hakan ba sabon abu bane ai.” Girgiza kai kawai Zahra ta yi tana ci gaba murmushi, a haka suna suka isa bakin department ɗinsu.

Kamar inda suka baro, nan din ma dai bata sauya zani ba, zance ɗaya ake yi kamar cin kwan makauniya.

Bullowarsu ya ja hankalin dukkan jama'ar wajen, dake tsattsaye kamar abinda da suke jira kenan dama.

“Ita ce yarinyar?”

“Yaran nan fa suna cikin alheri, wato shi trending na Allah ne, kalli yadda dan karamin abun nan ya jawo musu suna a duniya, kaga yadda suke zagayawa a media kuwa?”

“Ni na rasa wanda ya yi bidiyon marin nan ya fitar.”

“Shege kamar yasan abin da zai faru kenan, tun daga shigowar wajen ya fara dauƙa.”

“Wow Salmah ta zo, yanzu wasan zai fara.”

“Ni haduwarsu ta yau kawai nake son gani.”

“Kai dai bari, akwai show fa, don ina da tabbacin sai ya rama marin nan.”

“Dama shi ɗan iska ne da zai bari ta sha shi sillah.”

“Ni kuma bana tunanin zai iya rama.”

“Allah yasa dai ya zo ɗin, kasan jiya kunya bai bari ya sake dawowa cikin school ba.”

“Gaskiya dakyar ya iya zuwa.”

Ire iren hirarrakin da ke tashi kenan a tsakanin matansa, kuma da yawa daga cikin zantukan sun sauka a kunnen Salmah, amma ta dake kamar ba ta ji komai ba, sai ma murmushin da ta ara ta yafa, ta shiga ɗan jan Zahra da hira.

Ba su shiga lecture hall ɗin ba, kamar yadda suka tarar da sauran daliban da yawa a waje, suma wajen zamansu na yau da kullum suka nufa, wani ɗan bench na karfe dake kafe daga gefen corridor.

Suna zama sai ga Sofiyyah da Azizah, nan take hira ta barke suka shiga mayar da zancen a tsakaninsu kamar dai sauran dalibai, a nan ne Salmah ke samun labarin sahihanin abinda ke faruwa.

Readers Also Read