Kenza eBookz

Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 21

Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 21

Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 21: Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 21. Jiya bayan ta bar school an samu wani clips na dai dai wajen da ta mari…

3,337 words

Jiya bayan ta bar school an samu wani clips na dai dai wajen da ta mari Suraj da irin zafafan maganganun da ta yaɓa masa, yana ta yawo a group group na school ɗin, wadanda ba su ga zahiri abinda ya faru ba, da wandan da ma ba su san an yi duk suka gani. Wannan shine asalin abinda ya kara hura wutar zancen. Bugu da ƙari kuma a cikin daren aka samu wani matashi shima ɗan school ɗin ne, kuma tictoker ne sosai, ya kafe bidiyon Salmah wanda Suraj ya fitar, da kuma na abin da ya biyo baya, wato marin da ta yi masa a bainar nasi, ya yi sharhi akai, ya faɗi maganganu son ransa akan Salmah, ya kuma ce idan har Suraj bai zo ya rama marin da Salmah ta yi masa a gaban kowa ba, su kungiyar matasan Royal Crest University (RCU) Kaduna suna Allah wadai da shi. Nan da nan gayen nan ya yamutsa hazo, kasancewar dama already mutane sun riga sun san abinda ya faru. Kafin kace kwabo take comments section dinsa ya zama filin cece-kuce. Salmah Mu'az term Vs Suraj Al-Hikima term. Nan da nan duniyar yanar gizo ta san da zaman Suraj da Salmah.

A daidai wannan lokaci, Suraj ne zaune cikin motar AA bangaren me zaman banza. Idanunsa dake ɓoye cikin baƙin glass akan faskekiyar wayar Ya B dake hannunsa, ba komai yake kallo ba sai yadda duniya ke juyin waina da labarin soyayyarsa, wani comment wanda ya samu over 2000 reply a karkashinsa ya tsurawa ido yana kallo babu ko keftawa. Kallonsa AA dake driving ya yi, ɗan murmushi ya yi ya girgiza kai, “Suraj!” Ya kira sunansa a tausahe, a hankali ya juyo ya kallesa “Me ka ke kallo haka? Ko zantukan mutane sun fara rinjayar zuciyarka ne? Ko kana jin tsoron su yi maka dariya su raina ka su kira ka da lusari, bayan sun yi Allah wadai da kasancewar ka jinsin su?” Murmushi ya yi mai ciwo, “Ya B, ban fara son Salmah domin su sani ba, kuma maganar su ba ta isa ta canza ni ba.”

“Very Good!” AA ya furta tare da gyaɗa kai, a daidai lokacin da yake daidaita parking a kofar shiga RCU.

“Je ka ƙanina. Ka fuskanci kowa da dukkan kwarin gwiwa da jarumtarka, kada ka bari su kai ka ƙasa, ka tuna cewa har abada ina tare da kai.”

Gyaɗa kai ya yi, yana jin tamkar zuciyarsa na rikiɗewa daga zallar tsoka mai bugawa, zuwa namijin dutse. Da sauri ya bude kofar motar ya fito, tsayawa ya yi, yana karewa kansa kallo ta tinted glass ɗin motar Ya B.

Suraj kyakkyawan matashi ne dogo mai cikakkiyar siffar mazantaka, jikinsa a gine, kirjinsa a buɗe, diri na isassun mazan da za a yiwa kallo ɗaya a kira maza. Fuskarsa mai ɗan tsayi mai dauke da wasu shanyayyun idanu masu bala'in kyau da daukar hankali, hancinsa mai tsayi da kauri, labbansa sirara masu ɗan fadi da suka baiwa bakin wani irin shape mai kayatarwa, suman kansa mai taushi da sheki baƙiƙirin, da ya yi mata wani irin aski irinta matasan zamani yan kwalisa masu ji da gayu, gemu da sajensa irinta matasa sababbin jini masu shekaru irin tasa. Duk da shigarsa ta yau da kullum, amma yau ta musamman ce. Sanye yake da, fitted black jeans da plain white T-shirt ya ɗora slim black jacket mai sauƙin nauyi. A ƙafarsa sneaker ne fari fes irinta gayu, hannunsa daure da wata tsaddiyar a agogo mai shegen kyau, Baƙin glass ɗin da ya toshe idanunsa da shi, ya ƙara masa wani irin kwarjini da mysterious presence.

Sai da ya gyara zaman glass dinsa, kafin ya juya ya tunkari get ɗin RCU cike da wani irin confidence. [6/10, 12:39 PM] Oum Oummeetarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

By

AyshaNalado

Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍

BOOK 1

Page 31

Da wani irin taku ta ɗaukar magana mai cike da nutsuwa da kasaita ya dinga ratsa gungun daliɓan da ke walwala a harabar school ɗin. Duk inda ya gifta sai an bishi da kallo kamar wani sabon halitta.

Da yawa sun yi zaton kunya ba za ta barshi ya iya shigowa school yau ba, yayin da wasu ke tunanin ya zo ya ɗauki fansa ne, kamar yadda suke tsammani. Sai dai sanyayyar murmushi da annashuwar da ke tashi akan fuskarsa ya raba musu hankali, yanayinsa bai yi kama da wanda yake cikin baƙin ciki ko damuwa ba, saima sabanin hakan da ke bayyane ƙarara a tattare dashe.

Sam bai bar fuskar da za a kawo masa wargi ba. Da yawan kananan gasping din dake tashi kai tsaye suke shiga kunnesa, amma bai daga kai ya kalli kowa ba balle su saka ran zai tanka.

Kai tsaye hanyar department ɗin su Salmah ya tunkara.

Tun daga nesa ya hango ta zaune a tsakiyar kawayenta, kanta a duƙe, hankalinta kacokam akan wayar Sofiyyah wacce ita ce zaune kusa da ita, da alamar wani abu mai muhimmanci take nuna mata. Wani kalar murmushi ne ya kwace masa ba tare da ya shirya ba. Allah ne kaɗai zai iya shaida yadda ya ke jin soyayyar yarinyar nan a zuciyarsa. Duk tarin hayaniya da ke tashi kunnesa ya toshe. Duk tarin mutanen da ke wajen ita kaɗai yake gani ta dabam, ƙwalli da walwali take a idanunsa tamkar Zahra a cikin taurari.

Hannunta Zahra dake zaune a daya gefen ta damƙa, tare da faɗin, “Salmah! Ga Suraj!.”

Rasss! Gabanta ya yi wani irin faduwa, da sauri ta ɗago kai, cikin sa a idanuwanta kai tsaye ya sauka akan fuskarsa. Duk da idanuwansa a toshe suke da glass bai hana ta jin kaifinsu ba, da sauri ta dauke kai ta tamke fuska ganin yana tunkarosu.

“Mun shiga uku, nan fa yake zuwa.” Azizah ta yi maganar a matukar tsorace, tana rarraba idanu kamar mara gaskiya a gaban kuliya.

Kafin wani daga cikin su ya kai ga bata amsa kanshin hadadden turarensa ya kawo wa kofofin hancinsu ziyara.

Suraj bai dakata sai da ya isa gaban Salmah ya ja ya tsaya tare da miƙa hannu ya zare glass, take kyakkyawar fuskarsa mai cike da kwarjini ta fito fess.

Kallo ɗaya ta yi masa ta wani irin dauke kai kamar taga shara. Murmushi mai sauti ya saki, ire iren waɗan nan abubuwan da take yi wallahi ba ƙaramin cizon zuciyarsa suke yi ba, maimakon haushi burgesa take ƙara yi, “My Salmah!” Ya kira sunan da yake kiranta da shi a hankali da wani irin narkakken salo. Bata daga kai ta kallesa ba balle ta amsa, sai ma mayar da kai da ta yi akan wayar Sofiyyah dake hannunta tana danne danne. “Kin tashi lafiya?” still ba ta tanka ba, “please ki kalle ni mana Salmahtah, you are hurting me inside.”

A fusace ta dago ta watsa masa idanu tare da kiran sunansa a ɗan tsawace, “Suraj!” “Na'am Salmatah!” Ya amsa kai tsaye yana murmushi. Girgiza kai ta yi cike da takaici, ji take kamar ta ƙunduma masa ashar tsabar baƙin ciki.

Ɗan ƙara matsowa kusa kaɗan ya yi. Ya ɗan duƙa yana kallon fuskarta da kyau, lokacin guda kuma yana murza kumatunsa da hannun hagu, bangaren da ta mare shi yana murmushi mai ciwo.

“Salmahta har yau wurin nan zafi yake min.” Ya yi maganar a raunace. Ba Zahra, Sofiyyah da Azizah da ke kusa da su ba harta sauaran mutanen dake wajen sai da jikinsu ya yi sanyi.

“Amma ba zafin mari ba ne.” Ya yi maganar yana murmushi lokaci guda wani maiko na taruwa a cikin idanunsa tamkar hawaye.

“Zafin tambaya ne. Tambayar da nake yi wa zuciyata a kowane dare na duniya. Me ya sa ta zaɓe ki? Ya ɗan lumshe shanyayyun idanunsa ya bude ya ci gaba da fadin “Yau na zo da amsa.”

Ya kai hannunsa dake kumatunsa ya sumbata,

“Amsar ita ce. ko da za ki sake mari na sau dubu, zan dawo gareki sau dubu da ɗaya. Ina sonki Salmah, ina tsananin kaunarki, kuma in sha Allah sai na mallake ki.”

“Suraj! Ya isheka haka!” Ta daka masa tsawa tare da miƙewa tsaye a fusace.

“Bai isa ba Salmahta, ba zan taɓa daina furta cewa ina sonki, ko da za ki sake marina, I love you! I love you!! I love you so much Salmahta”

Hannu ta ɗaga a fusace za ta zaba masa mari, farar ta ji an rike hannu, da sauri ta juyo suka yi ido hudu da Fannah Baƙura, wani shegen kallo ta watsa mata kafin ta fincike hannunta da karfi, Gaba daya zuciyarta ya gaba yin baki har wani tiririn ɓaci rai ke fita daga kunnawa da hancinta. Zahra ce ta rikota da nufin ta mayar da ita ta zaunar ta fisge hannunta tana watsawa Suraj wani mugun kallo, tana wani irin a huci kamar kububuwa ta fasa kai.

Take wajen kaure da hayani, majority dariya suke yi wa Suraj, suna nuna sa irin ga wawa Shashasha ɗin nan, har da masu tsaurin idon ja masa riga, suna fadin Romeo! Romeo!! Romeo!!! Har lokacin murmushi bai ɓace daga kyakkyawar fuskarsa a hankalin ya fara ja da baya, sai kuma ya ware hannu idanunsa akan Salmah, ba tare da ya shirya ba ya tsinci harshensa da karyewa, da daddaɗar muryarsa mai sanyi da amo.

_“Duba a kanki ana kallona majnuni!!!”_

Ya ɗan lumshe idanunsa ya sake budewa akan fuskarta, ita kaɗai yake gani a wajen ita kaɗai zuciyarsa ke nuna masa. A hankali ya ci gaba…

_“Babbannn burina ki kasanceee dab dani.”_

_“In zaaa ki ƙirga masoya ni ki sanyooo dani.”_

_“Dubass a kanki ana kallona majnuni.”_

_“Ni kuma na ce ina dai kai na ki bannn faɗi ba.”_

_“Sakooo ya bayyana ne tun daga zuciya.”_

_“Sannannn kaunarki tana kaman zuciya.”_

_“Kin kaaama min kurwata tun jiya._

_” Har yaaa kai matsayin bana samun lafiya.”_

_“Kin shiga raina kin zauna don kin samu guri.”_

_“Kin yi kirana, na amsa kuma na zo da wuri.”_

_“Ke ce farkooo, kuma ke ce karshe.”._

_“Bishiyar nannn tai girma wacce ki kai min ni dashe.”_

_“Ba na ji , ba na gani, ba na son mai kushe.”._

_“Burinaaaah in rayu dake har numfashi karshe.”_

_“Kin rikita dukkan tunanina.”_

_“Taimaka ki bani gurin kwana.”_

_“Son ki ya hana mini barcina.”_

_“Ina ganin ko har a mafarkina.”_

_“Son ki ya naiiii min daɗi, ban so mu rabu.”_

_“Ki jaddada jarumtata ki kadan kambu._

_“Ba ni da komai sai ke.”_

_“Na tafe yawa wani falke._

_“Ina duhu ki kunna haske.”_

_“Za na ji dakeee.”_

Yana raira waƙar ne yana motsi, yana takawa yana bayyana dukkan emotions ɗin da ke cikin zuciyarsa a aikace. Tamkar wani super star ne a kan stage, yake performing.

Da fari wajen ya kaure da dariya, da ihu.

“Kaiii this guy don turn full Romeo o!”

“Wallahi ina tunanin Guy ɗin nan ya gama zarewa.”

“I love you Salmahta!” Wani ya faɗa cikin kwaikwayon salon Suraj ɗin.

Nan take wajen ya sake fashewa da dariya.

Sai dai me? A hankali yanayin ya fara sauyawa.

Kaifi da tasirin muryarsa ta fara ratsa zuciyoyi.

Yadda yake rera waƙar a tsanake kai tsaye daga zuciyarsa, yadda yake saka feelings ɗinsa a ciki, cike da baiwa da kwarewa, kamar wanda ya shiryawa lamarin, babu wanda zai ce ba kwararren artists bane a gabansu.

“Wait guys, hold on. Kuna jin abinda na ke ji kuwa?” Cewar wani saurayi cikin masu yi wa Suraj isgili.

“Ma sha Allah! his voice is actually nice though!!!.” Wata ta faɗa cike da shauƙin abin na yake saurara.

“Billahillazi an tashi kaina.”

“Subhanallah… this guy get talent fa…”

“No be joke… he’s actually good,” Wani ya amsa mata kai tsaye.

Ire iren waɗan nan zantukan sune suka maye gurbin dariyar isgili da hayaniyar da ke tashi a wajen.

Idanu da zuciyoyi suka fara komawa kansa da wani sabon kallon mamaki.

A hankali tafi ya fara tashi. Daga mutum ɗaya , zuwa biyu, wai kuma wajen ya kaure gaba ɗaya, hatta Zahra da Sofiyyah sai da suka tafa, tafi irin na girmamawa da burgewa

Suraj ya ci gaba da waƙarsa ba tare da ya tsaya ba, yana ƙara nutsewa cikin emotion ɗin da yake ji. Bai dakata ba sai da ya kai inda zuciyarsa ta umarce shi da tsayawa. Ya kafe a gabanta yana kallon cikin idanuwanta.

Ya Salam lokacin guda wajen ya fashe!

Ihu! Sowa! Shewa!

“Suraj!!!

Romeo! Romeo!! Romeo!!!

Nan da nan samari suka fara matsowa kusa da shi da farin ciki, musamman abokansa cikin harda Salman da Sadam da labarin abinda ke faruwa ya je musu. wasu na dariya da excitement, wasu na rike baki cikin mamaki.

“OMG you’re so good!”

“I’m obsessed already.”

Wasu suka kama hannun shi wasu kuma suka hau rungume shi cikin farin ciki.

Kowa na faɗin albarkacin bakinsa

“Bro respect!”

“Gaskiya kai ɗan daiwa ne!”

“You deserve her Bro.”

“In sha Allahu sai ka yi.”

Cike da Soyayya da kulawa tsantsa.

Amma duk a cikin wannan tarin mutane da ke kewaye da shi, bai manta da muradin zuciyar tasa ba, idanunsa na kafe a kanta, ita kaɗai yake ji da gani.

A hankali ta sulale ta ɓace ɓat a wajen, ba tare da kowa ya kula da hakan ba sai shi kaɗai da suka wani motsinta ke kan idanunsa. Ya rakata da kallo gabansa na faduwa domin sam bai ga alamar sassauci a fuskarta ba.

***************

A Bangaren su Inna kuwa, tun ranar da Maamah ta ambaci Hamma Babangida a gabanta, bata sake lafiya, ko da Baffa ya dawo daga kasuwa ya tarar da halin da take ciki, ya yi jimami sosai ya shiga damuwa. Amma gudun tashin nasa hankalinsa shima sai Maamah ta yi shiru da bakinta bata sanar masa da musabbabin tashin ciwon innar ba duk da ya tambaya.

Kwanaki biyu suka kwashe a haka suna fama, amma babu wani sauƙi ko canji sai wanda ba za a rasa ba, duk wani maganin da take sha Baffa ya siyo ya kawo mata, kuma har ya haɗa mata da na gida irin nasu na fulanin daji, tunda ba a san ta inda za a dace ba. Duk da sun yi batun zuwa asibiti amma ta dage akan bazata je ba, ita su barta kawai idan lokacinta ne ya gabata gara ta mutu a dakin aurenta, tunda kaddara ta raba ta da ƙasar haihuwarta, bata da rabon kwanciya a makwanci ɗaya da mahaifanta.

Wannan magana ta Inna ta ɗaga wa Maamah da Baffa hankali, har Baffah ya kasa fita wajen aikinta a ranar don shima jikin nasa kamar da zazzaɓi ya wuni.

A rana ta uku suka tashi jikin da sauƙi, kasancer daren ranar Baffah ya ɓata yana yi mata nasiha akan imani da tawakkali, duk da har lokacin bai san da maganar ganin Hamma Babangida ba, amma zuciyarsa ta bashi, domin yasan tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi. Hakan yasa Baffah ya shirya ya tafi wajen aikinsa, ya barta da Maamah wacce tun ranar dama bata sake fita ko nan da can ba.

A cikin daren rana ta hutu, cikin barci ta yi mafarkin Shatou, a cikin halin matsanancin jinya tana kuka yana miƙo mata hannu, tana rokon ta yafe mata. Wannan shine abinda ya kara dawo da ciwon Inna sabo ɗal har ma yaso ya fi na kwanakin baya, Sunan Allah da sunan Shatou sune kaɗai abinda take iya faɗa suma ba da kyau ba don sai ka nustu za ka fahimta, abinci da maganin duk babu wanda ta karɓa.

“Innalillahi wa Inna ilahi raji'un! Baffah! Baffa!! Inna walaa numfashi. Mun shiga uku, Inna ta mutu.” Muryar Maamah ya daki kumnuwan Baffah dake zaune a tsakar gida yana karatun Alkur'ani bayan ya idar da sallar walha.

Gabansa ya yi mummunar faɗuwa, “Innalillahi wa Inna ilahi raji'un.” Ya shiga maimaitawa ya mike da Kur'anin warshu irin mai falle fallen nan a hannunsa ɗaya ɗiba yana karantawa, da sassafa ya isa ɗakin.

Yanayin da ya tarad da Innar a ciki, ya yi matuƙar kayar masa da gaba, hankalinsa ya yi mummunar tashin, tana kwance kamar matacciya, Maamah na rungume da ita a jikinta tana kuka kamar ranta zai fita. Duk da ksancewarsa dakakken namiji jarumi, dakyar ya iya daga ƙafafunsa da su ka yi masa sanyi kalau, ya isa gaban gadon “Kauce Maryama.” ya furta muryarsa na rawa. Da sauri ta bashi guri. Tsintsiyar hannunta ya kama ya ya riƙe na yan sakkani. Kafin ya saki ajiyar zuciya mai karfi. “Tana da rai Maryama, ni nasan Hauwa ba za ta taɓa barina haka kurum ba, in sha Allah.” Jin haka yasa Maamah ta zabura ta miƙe, “Baffah mu kaita asibiti don Allah, bari na samo abin hawa.” Tana faɗin maganar nan tana ficewa ba tare da ta jira jin ta bakinsa ba. [6/11, 11:49 AM] Oum Oummeetarh: 🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

By

AyshaNalado

Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍

BOOK 1

Page 32

Kai tsaye gidan su Suraj ta yi nufin tunkara, amma tunawa da ta yi war haka , Mother ta na wajen aiki, Suraj kuma bata da tabbacin samun shi, yasa taga gara kawai ta yi ta kanta. Bata tsaya jiran abin hawan da sukan shigo Estate ɗin lokaci lokaci ba, kai tsaye gate ta nufa da sassarfa, ta na yi tana haɗawa da guda gudu. Takalma dake ƙafafunta gamin bauta, ɗaya nata daya na Baffah, dogon rigar jikinta a tattare ta rike da hannunta, kana yi mata kallo ɗaya za ka shaida akwai matsala. Tana zuwa daidai gidansu Suraj me gadi na buɗe get, kai tsaye idanunta ya sauka akan motar Mother dake kokarin fitowa daga cikin gidan. Ba tare da tunanin komai ba ta faɗa gidan tana jero hamdala a zuciyarta.

AA dake ƙoƙarin tayar da mota, ya hango mace tana nufosa a firgice kamar wacce ake bi a baya, hakan yasa ya dakata.

Tana zuwa ta kama murfin motar ta buɗe, cikin kuka ta fara faɗin “Mother Inna! Inna am, bata numfas......” Sauran zancen ya maƙale sakamakon idanuwanta da suka sauka a cikin na AA, da sauri ta saki murfin motar ta ja baya tana zare ido irin na tsantar kaɗuwa da ganin abinda baka zata ba.

A bangaren AA kuka lokacin da idanuwansa suka sauka akan fuskar Maamah, cak zuciyarsa ta tsaya da bugu numfashinsa ya dauƙe na wasu daƙiƙai, da kyar da tsiya-tsiya ya fisgo iska ya shaƙa tare da fesarwa, hakan ya dawo da shi hayyacinsa, da wani irin speed ya ɓalle murfin motar ya fito, ya zagaya ta gefen da take tsaye daf da ita ya tsaya yana yi wa fuskantarta wani irin kallo, kamar me son tantance gaskiyar wani abu.

Fashewa ta yi da kuka tare da faɗin, “Hamma am!” Kafadarta ya kama ya girgiza da karfi kamar zai kayar da ita, sai kuma ya janyota gabansa da kyau ya tsayar da ita, ya duka daidai fuskarta, yana kallon cikin idanuwanta, muryrasa na rawa ya ce, “Ɓeɓɓe am! Maryama ke ce?” Ya yi maganar cikin sigar tambaya da son tabbatar, bata iya bashi amsa ba sai kuka da ta sake fashewa da shi da karfi.

Bai san lokacin da ya fisgota gaba ɗaya ya saka a kirjinsa ya rungume da karfi ba. Kuka take yi sosai yayin da shi kuma idanunsa suka kaɗa, jijiyoyin kansa suka tashi.

Wani irin wawan burki Mother da ta kwaso da sauri domin ta zo ta cimma AA da zai tuƙata zuwa gidan Abba ta taka, saura ƙiris wayarta dake riƙe a hannu, ta suɓuce ta faɗi. Cikin matsanancin tashin hankali bakinta na rawa ta ce “Sub, subhanallah! Bunayyah Maamah mene ne haka?” Jin muryarta ya sanya AA ya sassauta riƙon da ya yi wa Maamah amma bai sake ta gaba ɗaya ba. Sai ita ce ta zame jikinta ta ja baya tana kallon Mother bakinta na rawa alamar tana da abin faɗa amma ta kasa saboda kuka da ya ci karfinta.

“Maryama, ina Innata? Ina Baffah, me ki ke yi a nan wajen, dama kin san gidan nan ne?” AA ya yi maganar da wani murya mai raunin gaske wanda basu san shi da shi ba.

Readers Also Read