Hadin kaddara by aysha nalado - Chapter 22
Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 22: Hadin kaddara by aysha nalado Chapter 22. Dawo da kanta gare sa ta yi, ta girgiza kai cikin kuka ta ce, “Hamma…
1,884 words
Dawo da kanta gare sa ta yi, ta girgiza kai cikin kuka ta ce, “Hamma Inna bata da lafiya, tana gida bata numfashi, Ni da Baffah za mu kai ta asibiti ne.” Sai kuma ta karasa wajen Mother ta kama hannunta, “Mother ki zo mu je ki kai Inna asibiti kada mu rasa ta.”
“Innalillahi wa Inna ilahi raji'un! Tun yaushe mu je maza.” Mother ta yi maganar tare da wucewa gaba, AA ya zabura zai bi ta, ta ce “Bunayya fito da mota mu je, House no 40.” Gaba ta yi Maamah ta rufa mata baya shi kuma ya nufi mota don ya tuƙo kamar yadda Mother ta umarce shi.
Sun tarar da Baffah a tsakar gida yana safa da marwa cikin tashin hankali, yana ganinsu ya nufo su, yana tambayar Maamah an samu keken? Kai kawai ta gyaɗa masa. Mothe ce ma ta yi karfin halin amsa masa da cewa, “E Baffah ga mota na zo da ita.” Ta kai karshen maganar ne tana shigewa cikin falon.
A bedroom suka tarar da Inna, tana nan kwance har lokacin bata motsi. Da sauri Mother ta yi kanta tana salati, “Ya Salam! Tun yaushe ne bata da lafiya haka Maamah, shine ki ka kasa sanar dani.” Maamah ba ta iya cewa komai ba, sai tallafa mata da ta yi suka ɗagota. dakyar da dabara suka iya fitowa da ita daki, kasancewar jikinta a sake yake sai ta yi musu nauyi.
Baffah ne ya shigo falon yana faɗin, “Za ku iya kuwa Hajiya Asmah, ko dai na saka muku hannu?” Kafin ta kai ga bashi amsa AA ya shigo cikin falon afujajan. Da fuskar Baffah idanunsa ya fara tozali, fuskar da da yake tsananin jin kunya sama da fuskar kowa a duniyar nan, haduwar idanunsu ya sanyi ya yi saurin yin ƙasa da kai, tare da jan wani irin numfashi mai karfi ya fesar.
“Y… y... Yaro!” Baffah ya furta da rawar baki yana nunasa.
“Na'am Baffah am!” amsa da faɗin hakan ba tare da ya sake yarda sun haɗa idanu ba.
Jiri ne ya fara kwasar Baffah ba shiri ya lalubi kujera ya zauna da baya.
Duk yadda mamaki da al'ajabin abinda ke faruwa ya cika zuciyar Mother, haka ta dake domin , ceton ran Inna shine abinda yafi komai mahimmanci a gareta. don haka ta katse yanayin da faɗin “Yawwa Bunayyah hurry up, kamata mu je mota.” Sai lokacin idanunsa suka hango masa Innarsa, matar da bayan wacce ta kawosa duniya, da Mother wacce ta ci kashi da fitsarinsa, babu wata macce da ta kaita daraja a idanunsa a duniya.
Bai tsaya kamata ba gaba ɗaya ya daga ta, ya rungume da sassarfa ya fice da ita daga farkon, Mother da Maamah suka bisa. Ba ƙaramin jarumta Baffah ya sanya ba kafin ya iya miƙewa ya rufa musu baya.
***********
Kamar yadda Dr Lukman ya yi alkawari, a yammacin ranar, ya bawa Aysha sallama. A lokacin su biyu ne kaɗai asibiti, Salmah da Salman ba su dawo daga school ba, Ammie da kanta ta harhaɗa musu kayansu, ta kai mota, duk da Aysha ta nuna son ta saka mata hannu, amma ta hanata.
Sun iso gida karfe biyar ta gota. Me gadi ya yi musu sannu da zuwa ya gayar da Aysha da jiki, a daƙile ta amsa masa as usual, shine ya yi jigilar kwasar musu kayan zuwa cikin falo.
Suna shiga falon suka hangi Salmah kwance akan dogon kujera, ta yi kwanciyar ruf da ciki, tun daga kan hijabi takalmanta loafers har zuwa kan jakan da ke goye a bayanta ba wanda ta cire, kuma da alamar ba shigowarta gidan kenan ba, duk da ba barci take yi ba, idanwanta a lumshe, ta yi nisa cikin tunani, har ba ta ji motsin shigowarsu ba.
Kallo juna Ammie da Aysha su ka yi, zuciyoyinsu cike da ɗan fargaba, ganin Salmah a haka alamace ta akwai wata matsala, don banza bata kai Zomo Kasuwa.
“Salmah.”
Ammie ta kira sunanta.
Bata motsa ba balle su saka ran za ta amsa.
Sake kira ta yi wannan karon da ɗan karfi,
“Salmah!”
Sai ta zabura ta miƙe zaune tana rarraba Idanuwanta da suka dusashe suka koɗe alamar ta ci kuka ta gode Allah.
“Ba ki da lafiya ne?” Ammie ta tambaya Idanunta kafe a fuskarta tana nazartar yanayinta.
Gyaɗa kai ta yi kafin a hankali ta ce, “E mara na ke ciwo.”
Kusan a tare Ammie da Aysha suka sauke ajiyar zuciya.
“Ayya! Sorry Sister.” Aysha ta yi maganar tare da karasawa ta zauna kusa da ita.
“Sannu Allah ya sawwaka. Me yasa baki sha magani ba, kafin ki fita? Ko babu ne?” Cewar Ammie a yayin da take kokarin zama.
“Ni fa Ammie, Allah mantawa na yi.” Ta yi maganar a narke kamar za ta fashe da kuka.
Gyaɗa kai Ammie ta yi “Da kyau, ai kin ga aikin nanatuwa yanzu, Allah ya sawwaka. Ayshatu ta shi ki shiga ciki yi wanka da ruwan zafi, za ki kara jin ƙarfi.”
“To Ammie.”
A tare suka miƙe da Ammie, “Ni ma bari na yi wankar, kwana biyu nan man samu wankan kirki ba, na kasa sakin jiki da toilet ɗin asibiti wallahi, wankar da na yi jinya, haka tsigar jikina ya dinga tashi.”
Murmushi Aysha ta yi tuna wacece Ammie a fagen tsabta, “Ammie ai babu laifi, asibitin suna kokari sosai wajen tsabta.”
“Uhm! Ba laifi.” Yadda ta bata amsar tana yatsina fuska yasa ta gane bai kai ciki ba, dariya ta saka. Murmushi Ammie ta yi, kafin ta yi gaba tana faɗin, “Ki dai yi sauri ki yi wankar, tun da sauran rana, kin san dai babu kyau wanka da goshin mangariba.”
Ruwan mai zafi ta haɗa ta yi wanka mai kyau, ta warware gashinta da tun parking ɗin da aka yi mata a salon ɗin da suka je ranar da abin nan ya faru ne, ta wanke shi tas da sabulan wanke gashinsu dake bayin, a cewar ta warin asibiti kan yake yi, ta jima sosai a toilet ɗin kafin ta fito daure da tawul babba da wani karami da ta naɗo gashinta a ciki.
A bakin gado ta tarar da Salmah zaune ta zuba tagumi, hakan yasa ta ƙasara wajenta da sauri, “Sannu Salmah jikin ne dai?” Ta yi maganar cike da damuwa tare da mika hannu ta taɓa goshinta.
“Jikin naki babu zafi, marar ma in sha Allah zai daina, kin ci abinci?”
Hannu Salmah ta sa ta cire hannunta dake goshinta, ta kalleta a hankali ta ce.
“Ni fa lafiya ta ƙalau Aysha, kawai raina ne a ɓace.”
“Subhanallah! What is happening?”
“Mene ne ma bai faru ba.”
Zama Aysha ta yi a gefenta ta bata dukkan hankalinta.
“Salman ne? Ko su Azizah?.”
“Suraj ne.”
“Suraj kuma? Me ya yi miki?”
Ajiyar zuciya ta sauke, cike da tsantsar takaici da baƙin cikin da zuciyarta ke kunshe da shi, ta fara baiwa Aysha labarin abin da ya faru wanda bata sani ba tun daga rabuwarsu a gidan Mother har zuwa kan abinda ya faru yau.
Zuba mata ido Aysha ta yi kawai tana kallon bakinta, yayin da abu biyu suka taru suka danne zuciyarta, na ɗaya dai takaicin Salmah ne, na biyu kuwa matsanancin tausayin Suraj, sanin da ta yi duk abinda za ta faɗa a lokacin ba zai haifar musu da ɗa mai ido ba, sai kawai ta girgiza kai ta ce, “Allah ya kyauta.“ Tare da kokarin miƙewa. A yanayin fuska da furucinta Salmah ta fahimci ranta a nace yake, riko hannunta ta yi, haka yasa ta dakata ta juyo ta zuba mata ido fuskarta babu walwala.
“Me ki ke nufi da Allah ya kyauta?”
A ɗan hasale ta ce “Komai ma Salmah, duk abinda ranki ya baki shi nake nufi. Ba dai kin yi abinda ki ke ganin ya dace ba ai shikenan.”
Sake ta ta yi ba tare da bata amsa ba, a zuciyarta kuwa cewa take, “E ai dole ku dinga ganin laifina, tunda ba ke ya yi wa iskancin da ya yi min, shegen yaro mara kunya kawai.” Ta yi ƙwafa da karfi kafin ta zame ta kwanta tana huci.
Girgiza kai Aysha ta yi, a ranta ta ce“Allah dai ya ganar dake kafin lokaci ya kure miki.”
Sai bayan sallar isha, Salman da Ya Anas suka shigo gidan a tare daga masallaci suke, shigowarsu kamar da minti ashirin Abie ma ya shigo a gajiye, duk suka yi masa sannu da zuwa ya haura sama Ammie ta rufa masa baya bayan ta bawa Salmah umarnin ta kula da girkin da ta ke yi. Ba su sakko ba sai da ya yi wanka ya kimtsa, lokacin har abincin ya yi Salmah na jerawa a dining. Kai tsaye dining ɗin suke nufa, don yin dinner.
As usual wajen ya ɗauki shiru baka jin karar komai sai ba cokala dake gwaruwa da plates, sai kuma na Tv dake tashi daga falo ƙasa ƙasa.
Wayar Salmah da ke ajiye kan table ɗin kusa da plate ɗinta ne ya yi ɗauki ruri, hakan ya ja hankalinsu baki daya kan wayar. Ya A sunan da ya bayyana kenan a kan screen ɗin. Cike da mamaki Aysha ta ɗago da sauri ta kalli Ya Anas don ganin kiran daga shi ne. Sai dai ga mamakinta, babu alamar shine ya yi kiran don ga wayarsa nan shima ajiye a gabansa. Hakan yasa ta dawo da kallonta ga Salmah, da ta yi tsuru tsuru kamar kazar da aka tsamo a ruwan zafi. Idanun Abie Ammie Ya Anas, duk akan ta, da alamar wayar suke jira ta ɗaga, wani busasshen yawu ta haɗiye, sai kuma ta mike zuruf ta ɗauki wayar, za ta bar wajen, “Salmah!” Abie ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta da karfi, a diririce ta juyo. Babu alamar wasa a fuskarsa ya ce, “Accept the call!........
Ta tabbata dai AA shine Babangida😳
Alhmdlh Alhmdlh Alhmdlh!
A nan na kawo karshen Labarin Haɗin kaddara kashi na ɗaya.
Ku sani yanzu aka tsoma ƙafa, nasan zuciyoyinku na cike da tarin tambayoyi.
•Shin mene ne dalilin AA na ɓoyewa Aysha gaskiyar cewa shine Babangida?
•Ya Aysha za ta ji idan ta gane wasan kura AA ya yi da zuciyarta?
•Za ta ɗauki fansar ko ya za a karƙe?
• Yaya haduwarta da iyayenta zai kasance?
• Mene makomar soyayyarta da Ya Anas?
•Ta yaya aka yi iyayen Aysha suka kasance a Estate duk tsayin wannan shekarun. Baro rugar suka yi ko yaya?
•Ya aka yi Aysha ta faɗa hannun su Ammie bayan ta baro rigarsu, da nufin neman Babangida don ta dauki fansarta?
•Na san za ku so ku ji karshen Soyayyar Romeo da Salman, ga kuma Ya Ammar a gefe guda.
• Wane ne ke bibiyar rayuwar AA, Da gaske yan jam'iyyar hamayya ne?
•Shin wai mene ne ma asalin HADIN KADDARAR MA.????
Duk waɗan nan amsoshin dama wasu da dama suna cikin HAƊIN ƘADDARA litattafi na biyu 2.
#Soyayyah #Yaudara #Fansa #Nishaɗi #Fadakarwa #Gen z vibes #AyshNalado
Ga wacce ta shirya yin payment don a ci gaba da tafiyar nan da ita. Kudin labarin 1k ne za ta saka a wannan account ɗin, 7041130088 Aisha Alhaji Yahaya Opay, sannan ta turo min shaidar biya ta 07041130088. Ga ma'abota amfani da manhajar Arewapen kuma ku garzaya can za ku samu in sha Allah. Only Chart pls ban da kira musamman da daddare Nagode.