Kenza eBookz

Halysaah by khaleesat hydar - Chapter 20

Complete book: Halysaah by khaleesat hydarChapter 20 of 34RomanceBy Khaleesat Hydar

Halysaah by khaleesat hydar - Chapter 20

Halysaah by khaleesat hydar Chapter 20: Halysaah by khaleesat hydar Chapter 20. *My special thanks to those that have already patronized since the…

3,402 words

*My special thanks to those that have already patronized since the beginning of this book, Thank you so much and i appreciate you*🥺 [5/18, 3:12 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Khaleesat ta kusa minti sha biyar a bandakin cikin tashin hankali da confusion, banda kuka babu abinda take yi, she can't even think straight tsabar yanda ta shiga tashin hankali, to ko dai kawai ta fita ta gudu ta bar gidan ne, ko kuma taje ta basa hakuri ya rufa mata asiri, ta ma san bazai taɓa sauraronta ba, da kyar ta mike daga durkushen da take hawaye sosai na zuba idonta har sannan jikinta rawa yake, gani take kamar the world have come to an end for her, hannunta na rawa ta wanke fuskarta tayi karfin halin bude kofar bandakin a hankali tana leka Bedroom dinta, zaune ta gansa edge din gado yana danna wayarsa, suna hada ido ta bude kofar ta fito, ya dinga kallonta daga sama har kasa, hakan yasa ta sunkuyar da kanta zuciyarta na bugawa, Mikewa tsaye yayi yana mata wani kallo yace "So you just wasted my time all this while ba wankan kike ba dama?" tears was just rolling down her cheek tana girgiza masa kai muryarta na rawa tace "Don girman Allah kayi hakuri, kar kace zaka...." Dakatar da ita yayi ta hanyar daga mata hannu, tuni ta ja bakinta tayi shiru tana kallonsa a tsorace ganin yanda lkci daya yanayinsa ya canza, tana ganin ya nufota ta juya zata koma bandakin da gudu yayi saurin fixgota, ta rushe da kuka sosai tana cewa "Don girman Allah kar ka min haka ka rufa min asiri Ya Abdul" Yana mata wani kallo yace "You think i will just waste my time and money coming here at the end in kyaleki da childishness dinki in koma Nigeria? You must be joking, In kika ga na kyaleki yau sai in faduwa nayi na mutu" Zuwa sannan Khaleesat bata ma san kalmomin dake fitowa bakinta ba ta dinga basa hakuri a rikice, ta dai san ko da wasa bazata ce zata yi kokuwa da shi ba, ta ina ma zata fara, da hannu daya in ya riketa ko kwakkwaran motsi bazata iya ba balle ta kwace kanta, Knocking kofar da ta jiyo a kunnenta ne yasa ta zaro ido bakinta na rawa tace "Wallahi Housemate dita ce ta dawo kuma bata da makulli nata ya ɓata..." Yace "And so what? Ita zata hanani abinda nayi niyya ne?" Hawaye na sauka idonta tace "Don Allah ka bar ni in bude mata kilan mantuwa tayi, she is not spending the night here" Saketa yayi fuskarsa babu yabo babu fallasa yace "Remain here, i will open the door for her" Gyada masa kai kawai take zuciyarta na bugawa da karfi, ya dau rigarsa ya saka sannan ya nufi kofa ya fita, a hankali Khaleesat ta sulale kasa tana jin kamar numfashinta zai dauke tsabar tashin hankali, gashi sai knocking kofar parlon ake babu kakkautawa, da sauri ta mike jikinta na rawa ta bi bayansa tana shesshekar kuka at the same time tana tunanin to wa ke kwankwasa kofar Allah Ubangiji ya sa Housemate dinta ne, nan corridor ta makale don tuni har Abdul ya isa kofar parlon zai bude, ya murda makullin ya bude kofar, Khaleesat couldn't believe who she saw standing at the doorstep, ai bata san sanda ta karaso parlon da sauri ba hawaye na sauka idonta, Abdul dake kallonsa daga sama har kasa Calmy yace "How may we help you? Who are you looking for?" Maimakon wanda ke bakin kofar ya basa amsa kawai ya bi gefensa ya shigo parlon yana kallonta yace "Why did you call my line?" Da mamaki Abdul ya juya ya kalli Khaleesat da ta sunkuyar da kanta hawaye na sauka idonta ta lumshe ido, bata san sanda wani relieve ya zo mata ba lokaci daya, ta sake jin muryarsa yace "Me yasa kika kirani?" Ta daga kai ta kalli Abdul ganin irin kallon da yake mata at the same time ya nufo inda take cikin zafin nama, ganin haka ta fara komawa baya cikin rawar murya tana kallon AJ tace "I need you to help me pls" Ko rufe baki bata yi ba taji Abdul ya sauke mata wani wawan mari a kuncinta, AJ could not believe what he just saw cause bude baki yayi at first, ganin ya kara sauke mata wani marin cikin few seconds AJ ya isa gaban Abdul sending him double fist a fuska, he took Abdul unaware don bai gama recover daga fist din ba ya kara masa wasu ukun a jere, kan kace me ya fara punching dinsa kamar an aikosa, Rikicewa Khaleesat tayi da karfi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku plss stop it" Tana matsowa kusa da su zata rike AJ da ya wani hankadata sai da ta fada kan kujera, Dai dai sanda aka bude kofar parlon Jay ya shigo, buda baki yayi ya jefar da wayar hannunsa saman kujera ganin Abdul a hannun AJ kamar ya samu punching bag, AJ gave Abdul no single space to retaliate, dukansa kawai yake kamar suna gidan dambe, Jay ya nufesu da sauri yana kiran AJ, da kyar ya samu nasaran rabasu yana ma AJ tsawa yace "Are you out of your mind Junaid? Are you mad, Meye haka?" Jay bai rufe baki ba Abdul ya koma kansa da fist din da bai samu yi ma AJ ba, ai ko ya kara ja ma kansa wani dukan wajen AJ, Jay that was shock at the attack Abdul just attacked him ya bude baki yana kallonsu, kar AJ yaje ya ma Abdul illa su shiga uku ya sa Jay ya kara rike AJ, Abdul that was beaten blue black ya nufi kitchen kamar mahaukaci vowing to unalive AJ, Khaleesat tsabar shock ko motsin kirki bata yi a inda AJ ya wurgar da ita, Jay na ganin Abdul ya shiga kitchen yasan makami kawai yaje daukowa, ya kalli Khaleesat da sauri yace "Tashi ki tafi daki" Ai kamar jira take ko rufe baki Jay bai yi ba ta mike a guje tayi Corridor ta tsaya tana zare ido, Jay ya fara jan AJ su tafi daki amma AJ yaki yana cewa "Don babansa me yake takama da shi a Nigeria? Who the F is he? Kakkaryasa zanyi in karya banza wallahi, in ya cika shege mu hadu a Nigeria" Jay yaki biye AJ haka dai ya ja sa har corridor zai shigar da shi daki, sai ga Abdul da wuka ya nufo su kamar Ɗan daba, ai ko karasa shigewa dakin basu yi ba Khaleesat ta riga su, tuni Jay ya sa ma dakin Key ya zare makullin ya saka a aljihu don tsaf yasan AJ sai yace zai bude kofar ga makami hannun Abdul, Abdul ya dinga bubbuga kofar saying all sort of abusive words at the same time yana alkawarin sai ya ma AJ illa, AJ ya tafi jikin window ya tsaya yayi crossing kafa yana kallon kofar dakin, Jay dai ya zauna gefen gado looking speechless and confuse, sai kuma ya dafe kirjinsa da ya fara masa ciwo saboda fist din Abdul, ita dai Khaleesat na rakube jikin gado hawaye na sauka idonta tana kuka a hankali, banda bugawa da karfi babu abinda zuciyarta ke yi, taji muryar Abdul na cewa "Ke kuma sai na maki abinda har ki koma ga mahaliccinki baza ki mance ba, i will make sure you become useless and miserable, i promise you this, kasar nan kuma kamar kin bar sa don karatun ki ya zo karshe" Khaleesat ta kara sautin kukanta, Ajay ya daka mata tsawa yace "I will fling you out of this room in baki rufe ma mutane baki a nan ba" Jay ya wani kallesa, ita dai Khaleesat ko kallonsa bata yi ba kukanta kawai take, after a while ko ina yayi tsit a gidan ko tafiya Abdul din yayi oho, da kyar Khaleesat ta mike bayan kusan minti goma zata dau hijab dinta, Jay ya bi ta da kallo, bayan ta saka Hijab din ta juya suka hada ido, sauke idonta da ya kumbura don kuka tayi, sai kuma ta tafi ta dau karamin towel da ta gani gefen gado seeing traces of blood in Jay's lips, bandaki ta tafi ta jika towel din da ruwan dumi sannan ta dawo dakin without looking at him ta duka gabansa ta dafa gadon ta fara goge masa lip dinsa a hankali, AJ ya wani kallesu sai kuma ya tabe baki ya kauda kai yana kallon outside of the window, Jay dake kallonta yace "Thank you Halysaah" Ita dai bata ce komai ba kuma bata yarda ta hada ido da shi ba ta mike ta tafi bandaki da towel din, AJ ya juyo yace "Kai Malam bani makulli in bude kofar nan in fita" Mikewa Jay yayi ya nufi kofar ya fara budewa a hankali, AJ ya bi bayansa incase of necessity, yana bude kofar AJ ya rigasa fita at the same time being very conscious of everywhere in the house, both angle and corner, a haka ya fito parlon Jay ma that was at alert na biye da shi a baya amma fa sai da ya kulle kofar dakin da makulli sbda Khaleesat, and they realized Abdul ya fice daga gidan, AJ ya juya ya kalli Jay yace "Dau wayarka mu tafi gida" Jay yace "You think i can just go and leave her in here?" AJ ya masa wani kallo yace "How sure are you u are safe being in this apartment tonight? Mahaukaci ne fa gayen kuma zai iya dawowa at anytime, it's already dark now" Jay yace "Nasani, but bazan iya barin ta ita kadai gidan nan ba" AJ yace "Are you her family member or something?" Jay yace "Kai da ka taho nan family member dinka ce?" AJ yace "Look Jay, Billah bazan bari ka zauna a gidan nan ba, koma wani taimako zaka mata kayi mata ni babu ruwana amma baza ka zauna a gidan nan ba, i can't risk leaving you here even for 1 second" Jay that was quiet for a while yace "Toh ka tafi, zan biyoka a baya" AJ yace "Kafata kafar ka Malam, kaji nayi rantsuwa bazan bar ka gidan nan ba, dubi kullin da ya dinga maka babu abinda ka tabuka sai sake baki kayi kana kallonsa" A hankali Jay yace "So kake mu hade masa at the end mu zo mu yi abinda za ayi da an sani, ai gwara da na kyalesa kawai kai ba gashi ka basa kashi yanda ya kamata ba, beside in muka ce zamu dokesa tare hakan zai sa mu gigita yarinyar ne" AJ yace "Aa haukatar da ita za mu yi ba gigita ta ba, pls do what ever you want to do ka fito mu tafi gida, ni yunwa ma nake ji" Jay ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace "Wait for me outside then" Yana fadin haka ya juya ya koma dakinsa da Khaleesat take, AJ kuma ya fice daga parlon ya tsaya nan bakin kofa yana jiransa, bayan Jay ya bude dakin da makulli sai da yayi knocking sannan ya shiga ciki, tsaye ya ganta jikin bangon dakin hawaye na sauka idonta tana shessheka, ya tafi can jikin window ya tsaya yana kallonta, ita dai ta sunkuyar da kanta tana kuka a hankali, Calmly yace "Halysaah" Ta kasa daga kai ta kallesa, yace "Tell me how did you get to know this guy? A ina ku ka hadu? For how long ku ke tare da shi, kuma who is he? Iyayenki sun san da alakar ku?" Sai a sannan ta daga kai wasu hawayen na sauka idonta tana kallonsa, ya sauke ajiyar zuciya yana shafa kansa yace "Where are ur reading material? Suna dakin ki ne?" Kai ta gyada masa kawai, yace "Mu je ki dauka" A tare suka tafi dakinta, bayan yaga inda reading materials din nata suke ya karasa ya dauka har da laptop dinta, ya kalleta yace "Ina wayarki fa?" A hankali tace "Ya fada ruwa" Shiru yayi sai kuma yace "To mu je" Ta ɗan yi jim tana kallonsa, yace "Mu je mana" ba musu ta nufi kofa ya bi bayanta bayan sun fita ya kullo kofar, ita dai duk a tsorace take sai zare ido take tana ganin kamar Abdul zai sake dawowa gidan at anytime, ganin a tsorace take Jay ya shiga gaba yace "Follow me" Bin bayansa ta dinga yi hawaye na sauka idonta har suka fita daga parlon, har sannan Ajay na tsaye waje, ya juya ya kallesu, Jay ya nufi motarsa ganin Khaleesat ta tsaya yace "Mu je mana Halysaah" tana tafiya a hankali ta ci gaba da bin sa, back seat ya bude ya ajiye laptop dinta da sauran reading material dinta ya kulle sannan ya bude mata front seat, ta sauke idonta ta shiga motar ya kulle, yana kallon direction din AJ yaga har ya nufi gun motarsa ya shiga, zagawa yayi ya shiga driver seat ya tada motar, tuni AJ yayi zoom off, Jay ya bi bayansa. A hankali Khaleesat ta sauko daga motar tana kallon Jay da shi ma ya sauka ya bude back seat ya dauko laptop dinta da takardu ya kulle motar yace "Mu je" Sauke idonta tayi ta fara bin sa a baya walking slowly har suka shiga parlon gidan, ya nuna mata kujera yana kallonta, ta sunkuyar da kai sannan ta zauna, ya ajiye laptop da takardunta dake hannunsa sannan ya wuce sama, ta bi sa da kallo hawaye na taruwa idonta, sai kuma ta fara kuka a hankali tana jin kanta na sara mata, Jay ya tafi dakin AJ yana bude kofar dakin yaji yana wanka a bandaki, hakan yasa ya tsaya bakin kofar dakin don baya son issue, yana ta tsaye da tunani iri iri a ransa har AJ ya fito bandakin, AJ na ganinsa ya dakata da goge gashin kansa da karamin towel yace "Me kake nema a nan kuma?" Jay yace "Ban sani ba" Sai kuma ya karasa cikin dakin that was extra clean, kan kujera ya zauna without looking at AJ yace "We need to talk AJ" Ajay yace "Shi ne sai ka shigo min daki?" Jay yace "Zauna mu yi magana" Ɗan tsaki AJ ya ja yana ci gaba da goge gashinsa yace "Ina jin ka ba sai na zauna ba" Jay yace "I think my Housemate will stay here for a day or 2, before she sort her self out" AJ yace "As per you are her family member or who? Bata da iyaye ne? Ko nan din hotel ne?" Jay yace "Ban sani ba" AJ yace "No i am just asking a harmless question, like naga dai ba daga sama ta fado ba, kuma ba kai ka kawota America ba balle kace zaka samar mata solution, who are you to her? Yayanta ko Ubanta? Wanda muka mata ma Allah ya bamu lada, come off it Jawwad" Jay yace "Ai ba permission din ka na shigo nema ba Junaid, kawai sanar maka nake yarinyar nan zata yi kwana daya zuwa biyu a gidan nan kafin komai yayi settle" AJ yace "Toh ni na haifeka da zaka shigo ka gaya min zaka kawo yarinya tayi kwana biyu gidan nan? Ai sai dai ka kira su Abba ka gaya masu, beside the house is very big with multiple rooms to accommodate her, so ni ina ruwana, i just pray u don't have to explain ur self one day" Jay ya mike ya fice daga dakin banging the door behind him, AJ ya tabe baki yana feshe jikinsa da turaren jiki. Bangaren masu aikin gidan Jay ya nufa bayan ya sauko downstairs, ya basu umarnin da zai basu sannan ya dawo babban parlon gidan, Khaleesat dai na zaune ta jinginar da kanta jikin kujera tayi nisa tunanin da ta fada, ganin komai take kamar a mafarki, sai in taji tana da ta sanin abinda ya faru amma da ta tuna raping dinta Abdul yayi niyyar yi da Ajay bai zo ba sai taji ta nemi da ta sanin ta rasa, amma fa bata da nutsuwa bata da kwanciyar hankali, she was just restless and sick, bata san kuma me zai faru next ba a rayuwarta, muryar Jay ne ya dawo da ita daga tunanin da take ta gyara zama tana kallonsa a sanyaye, ya zauna kujeran dake kallon wanda take zaune yace "Bana son ki sa ma kanki damuwa Halysaah, ki kwantar da hankalinki pls kin ga kina da jarabawa a gabanki" Khaleesat ta sunkuyar da kanta hawaye ya fara sauka idonta, Yace "Kin yi sallah?" Ta gyada masa kai, yace "Ohk za a kawo maki abinci sai ki ci kafin mu yi magana" Ta girgiza masa kai tace "Bana jin yunwa" Yace "No, sai kin ci abinci ko ba yawa" Dai dai nan kukun gidan wanda bature ne ya taho da abinci zai kai dinning Area, Jay ya masa umarnin ya kawo parlon sanin abincin AJ na kan dinning din, dawowa kukun yayi Jay ya nuna masa inda zai ajiye abincin, nan ya jerasu a kasan lallausan Centre carpet, ya koma ya dauko sauran, bayan ya ajiye komai ya tafi Jay ya mike yana kallonta yace "Ki sauko ki ci abinci, let me pray" Ta gyada masa kai kawai, ya wuce sama sannan ta sauko kasa a hankali tana duba abincin da aka kawo mata taga duk abincin jajaye ne gashi abincinsu da yawa ita ba iya ci tayi ba duk shekarun da tayi a kasar su. Almost 30 mins after Khaleesat dake ta zaune tana tunane tunane ko abincin ta kasa ci ta daga kai taga Ajay ne ya shigo parlon, sunkuyar da kanta tayi, bai kalli inda take ba yayi wucewarsa dinning Area ya fara cin abincinsa, after a while Khaleesat ta daga kai a hankali jin footstep, taga Housemate dinta ne ke saukowa downstairs, ya karaso har inda take ya zauna kan kujera yace "Kin ci abincin?" Ta gyada masa kai, cook din gidan ya kira ya dauke sauran abincin ya tafi da su, Jay yace "To ki koma kan kujera" Ita dai Khaleesat kanta na kasa bata ce komai ba, har sai da Jay ya sake mata magana sannan ta mike ta koma kan kujeran ta zauna, AJ ya dawo cikin parlon ya tafi reading nook dake parlon, Jay ya bi sa da wani kallo har ya gama kakkabe kakkabensa ya zauna, ko uban me zai yi a can don yasan dai baya ma zuwa nan balle yayi karatun a nan, muryar Jay ya dawo da hankalin Khaleesat jikinta, taji yace "So Halysaah i want to even know what happen first of all at ur apartment today, don ni ban san me ya faru ba, Salem called me yace kin kirani ban daga ba and you sound disturb, and he gave you AJ's number, i rang you back quickly sai kiran bai shiga ba, shine nayi deciding in je can gidan kawai, menene ya faru?" Khaleesat ta sunkuyar da kai don bata ma san me zata ce masa ba, ta yaya ma zata fara cewa raping dinta Abdul ya so yi, muryar AJ suka ji a parlon yace "Allah ma yasa ba rashin kunyan da ta saba yi ma mutane taje tayi masa ba, kawai ta sa na doki bawan Allah a banza" Khaleesat dai bata dago kanta ba, shi dai Jay yayi murmushin da bai yi niyya ba yana kallon direction din da AJ yake, A hankali Jay yace "You are not saying anything Khaleesat" Hawaye ne ya cika idonta, ganin haka Jay yace "Or you don't want to talk about it?" Ta girgiza masa kai hawaye na sauka idonta da kyar tace "Ba haka bane, he tried molesting me" AJ that heard what she said duk da ba kallon direction dinta yake ba yace "He tried molesting you, amma da hannunki ai kika bude masa kofar ba ta window ya shigo ba" Jay ya wani kallesa yace "Stop this please AJ, why are you so wicked and heartless" AJ yayi wata dariyar bosawa, Jay ya dinga hararansa, ita dai Khaleesat hawaye ne kawai ke zuba idonta, tsabar ciwon da kanta ke mata har wani dishi dishi take gani, Cikin kwantar da murya Jay dake kallonta yace "Tell me who he is, and where did you know him from" Ta gyada masa kai tana share hawayen da yaki tsaya mata a hankali tace "Shekara hudu kenan na san shi....."

Readers Also Read