Halysaah by khaleesat hydar - Chapter 21
Halysaah by khaleesat hydar Chapter 21: Halysaah by khaleesat hydar Chapter 21. *Don't even know where to start from, the patronage was massive🥺, thank…
3,575 words
*Don't even know where to start from, the patronage was massive🥺, thank you soo much for encouraging me fans, Allah ya biya maku bukatunku na alkhairi, Allah ya raya zuri'a, i soo much appreciate ur patronage, marasu auren cikin ku Allah ya baku mazaje na gari, masu aure kuma Allah ya ci gaba da baku zaman lafiya a gidajenku, Allah ya karo maku budi ninkin ba ninki, ya raba ku da iyayenku lafiya* 🥺
_Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta i owe you 500_
[5/19, 5:53 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Khaleesat ta sunkuyar da kanta har sannan bata daina goge hawayen da ya ki tsaya mata ba, she look pained and traumatized, Shi dai Jay kallonta kawai yake waiting for her to continue with what she is saying, jin tayi shiru yace "Halysaah" Ta daga idanuwanta ta kallesa, Calmly yace "I am listening" muryarta na rawa tace "Kawai dai shi ne ke sponsoring dina" Ba Jay da ya kafeta da ido ba yana mata kallon mamaki, har AJ sai da ya juya ya kalleta daga inda yake zaune jin abinda tace, Jay was just speechlessly staring at her, can dai ya gyara zama yace "You mean shi yake sponsoring dinki a kasar nan? Are you related in anyway with him?" Ta girgiza masa kai kawai, da mamaki kawai yake kallonta, after few seconds yace "And ur parent allowed him to sponsor you har zuwa nan America?" Ta gyada masa kai without looking at him, mikewa AJ yayi, yayi wucewarsa sama, Jay ya bi sa da kallo don shi ma ya rasa abun cewa don mamaki, Jay ya maida dubansa kan Khaleesat a hankali yace "Ya kai kudin aurenki ne an sa maku rana?" Ta daga idanuwanta ta kallesa cikin sanyin murya tace "Nima ban sani ba, amma kamar ya kai" Jay yayi shiru for almost 3 minutes with different thoughts running his mind, everything just took him unaware, bai taɓa tunanin saurayin nata ne sponsor dinta all this while ba, can ya daga kai ya kalleta yaga ta jinginar da kanta jikin kujera looking so tired and pale, yana son sanin me ya hadata da Abdul, meye ma dalilin haduwarsu, sannan a ina ma suka hadu da shi din, what is this great thing that motivated her parent har suka amince ma stranger da basu hada komai da shi ba ya turo er su har wata kasa karatu, he just don't want to believe it's because of money they did this.... amma ganin yanayinta yasa yayi keeping all the questions to himself for now don baya son ya kara stressing dinta, she is already stressed, mikewa yayi calmly yace "I will be back now" Ita dai ta bi sa da kallo har ya haura sama, wasu hawaye taji na taruwa idonta, kawai so take tayi kuka me sauti ko zata ji saukin abinda take ji a ranta, ta hade kanta da kujera tana shessheka a hankali, Jay na haurawa sama ya tafi dakin da ya sa daya daga worker din gidan ya kara gyarawa, the room was big sai dai bai kai nasa da na AJ ba, kuma babu abinda babu a dakin sai Duvet na saman bed spread, ya bude press din dakin yaga babu a nan ma, juyawa yayi ya fita ya dau hanyar dakin AJ, yana isa ya danna code din bude kofar dakin ya murda yaga bai buduwa, yasan canzawa yayi kenan saboda ya shigo masa dakin daxu, knocking din kofar yayi, after a while AJ ya bude kofar yana kallonsa alamar what happen, Jay ya turasa gefe ya shiga cikin dakin, AJ ya bi sa da kallo yace "Ka dai san bana son haka Jawwad, what are you looking for?" Jay ya kunna wutan dakin that is more brighter yace "Duvet zaka bani, i don't understand dalilin da yasa zaka kwashe kaf duvet din sauran rooms din all to ur self, this is greed" AJ dai kallonsa kawai yake cause he is already angry shigo masa da Jay yayi daki, ganin Jay ya nufi inda duvet dinsa suke yace "Jay me zaka yi da duvet bayan kana da naka a daki?" A takaice Jay yace "I am giving my visitor" AJ ya bude baki yana kallonsa yace "What??? I don't understand, Duvet dina zaka dauka ka kai ma visitor dinka? are you even okay? Can you hear ur self pls?" Jay bai tanka sa ba ya dau na saman gadonsa kawai ya nufi kofa, AJ ya tare kofar on a serious note yace "In ka fita da duvet din nan ka canza min suna yau" Jay ya wani turasa daga bakin kofar har sai da ya kusa faduwa sannan ya fice daga dakin, sai bayan da ya fita ya juya ya kalli AJ da ya bude baki yana kallonsa with shock, Jay yace "Emmanuel" daga haka yayi wucewarsa ya bar AJ da bin sa da kallo, Jay na komawa ya ajiye duvet din kan gadon dakin da aka gyara ma Khaleesat sannan ya sauka downstairs, tana nan zaune yanda ya bar ta idonta a lumshe amma ba bacci take ba, yace "Halysaah" Bude ido tayi da sauri bayan ta dawo duniyar tunanin da ta tafi, yace "Tashi mu je sama, u need rest" Ita dai tayi shiru bata ce komai ba, ya dau laptop dinta da takardunta yace "Mu je" Sai bayan da ya fara tafiya sannan ta mike a hankali ta bi bayansa, har wani jiri take ji amma a haka ta daure ta bi sa har zuwa sama, ya bude kofar dakin ya shiga tana biye da shi, bayan ya ajiye laptop din hannunsa ya kunna mata na'uran da zai dumama dakin, ya nuna mata hanyar bandaki ita dai kai kawai ta gyada masa, ya ciro wayarsa a aljihu yayi dialing number sannan ya mika mata yace "In case u need anything sai ki kira number da nayi dialing it's my other line" Nan ma dai kai kawai ta iya gyada masa, yace "Good night Halysaah, pls kiyi bacci sosai, do not bother ur self kin ji?" a hankali tace "Toh" kofa ya nufa ta bi sa da kallo sai da ya bude kofar a hankali tace "Nagode" Ya juya ya sakar mata murmushi yace "I gat ur back" Daga haka ya fita ya kullo mata kofar dakin, Khaleesat ta ajiye wayar tasa da ya bata sannan ta zauna gefen gadon dakin a hankali staring at the window absently. Har karfe dayan dare Khaleesat bata ji ko digon bacci ya zo mata ba, tana dai kwance tayi lamo cikin duvet, her heart is soo heavy, har wani zafi take jin yake mata, ga wani zazzabin da taji ya lullubeta, tun da Jay ya bar ta take kuka, gani take kamar duniyar ya tsaya mata ne cak, ta ma rasa wani kalan tunani zata yi, abubuwan da suka faru daxu suka dinga dawo mata abun sai yake mata kamar mafarki, she wish mafarkin ne ma kawai, yanzu babban tashin hankalinta bata san me zai faru a Nigeria ba, bata san next step din Abdul ba, bata san me zai ma iyayenta ba, duk wannan tunanin ya hadu yayi distabilizing dinta, zazzabin da take ji ya karu sosai, tana son tashi taje tayi alwala tayi sallah ko zata samu sukuni amma ta kasa, duk jikinta ciwo yake mata ga ciwon kai kamar kanta zai fashe, da taji azaban yayi mata yawa kamar zata kira Housemate dinta ta tambayesa maganin ciwon kai amma ta fasa don bata san ko bacci yake ba, haka tayi ta juye juye jikinta yayi zafi sosai, yanda taga rana haka taga daren nan that was soo long to her, bacci ko na barawo bai dauketa ba, jin vibration din da wayarsa yayi yasa tayi karfin halin jawowa tana kallon screen taga alarm ne na karfe biyar, ta kashe alarm din tana son tashi don tayi sallah amma ta kasa, daga karshe dai haka tayi karfin hali ta daure ta tafi bandaki ta dauro alwalan, tana idar da sallan taji zazzabin da yafi na baya ya lullubeta gaba daya, kwanciya tayi saman gado ta rufe har kanta da duvet din. Wajen karfe takwas na safe Jay yayi knocking kofar dakinta, tana ji amma ta kasa amsawa, sau uku yana knocking jin bata amsa ba sai ya kira wayarsa dake wajenta nan ma tana kallon kiran amma ta kasa daga hannu ma ta dau wayar, sai da ya katse sannan ya bude kofar dakin da sallama ya shiga, yana kallonta da mamaki ya nufeta yace "Are you Okay Halysaah?" Kai kawai ta girgiza masa, ya duka kusa da ita yace "Baki da lafiya ne? Why didn't you call my line?" Hawaye ya gani idonta, yace "Haba Halysaah, ba nace kar ki sa ma kanki damuwa ba? Did you want to hurt ur self?" Ita dai bata ce komai ba, ya juya ya fita daga dakin, after some minutes ya dawo da Hot chocolate ya ajiye mata yace "Ki daure ki sha pls, let me get you medicine" Yana fadin haka ya juya ya fita daga dakin, ko da ya dawo ya ga bata tashi ba still, duk yanda yayi da ita ta tashi ta sha shayin ya bata magani taki tashi, gaba daya ya ma rasa yanda zai yi da ita, can ya kara dukawa kusa da ita yace "Did you have ur frnd safiyyah's number offhand?" Da kyar ta girgiza masa kai, yace "U have her IG handle? Is she active on IG?" Bata ce masa komai ba don ta ma kasa maganan, he look confuse at this point, can dai yace "To zaki iya daurewa ki tashi mu tafi asibiti?" Ta girgiza masa kai, mikewa yayi kawai ya fita daga dakin, downstairs ya sauka don AJ na dinning yana breakfast ga Legend dinsa zaune ɗan nesa da shi a dinning area din, Jay ya nufesa looking confuse yace "AJ, the girl is seriously sick fa" AJ dake sipping tea dinsa yace "Which girl?" Jay ya masa wani kallo yace "Please be serious AJ, wallahi bata da lafiya sosai" AJ yace "To yanzu daukar ta zaka yi ka kai ta Hospital kenan..." Jay yace "How?? ko tashi fa bata iya yi, plss ko zaka mata allura ta ɗan samu relieve tukun?" A hankali AJ ya ajiye Mug din hannunsa yana kallon Jay baya ko kiftawa, can ya matsar da shayin gabansa yace "Amma dai don Allah me yasa ka raina ni haka ne Jay? Me nayi maka? Kai me hannunka yake da bazaka mata allura ba sai ni?" On a serious note Ajay ke masa tambayoyin nan looking at him and waiting for his answer, Jay yace "Da gaske fa you are Heartless Junaid, ince maka yarinya ko tashi bata iya yi? Why are you like this pls?" AJ yace "But like seriously kai uban me hannunka yake da bazaka mata allura ba sai ni? Baka fi ni zama likita ba? Wato ni ne ɗan iska ko?" Juyawa Jay yayi ya bar wajen ya koma sama, yana bude kofar dakin ya ganta duke kusa da kofar bandaki, ya karasa kusa da ita da sauri ganin yanda ta galabaita yace "Did you throw up?" Kai kawai ta gyada masa tana maida numfashi, gun da ya ajiye hot chocolate din ya tafi ya dauko mata yace "Pls ki sha ko kadan ne sai in baki magani" Ta girgiza masa kai, yace "C'mon Halysaah, kadan fa za ki sha" Yana rike da cup din don kar ya sakar mata ta zubar, a haka ta kurbi shayin kadan, sai da yasa ta kara sha sannan ya ajiye shayin ya dauko magani, tana ganin maganin ta fara girgiza masa kai da sauri don har taji wani aman zai taho mata, bude kofar dakin aka yi Jay ya juya, AJ ya gani tsaye bakin kofar yana kallonsu, Jay bai sake kallon inda yake ba ya maida dubansa kan Khaleesat yace "Pls ki daure ki sha Halysaah, ko baki son ki samu relieve?" Kara girgiza masa kai tayi hawaye ya fara sauka idonta, lallabata Jay ya fara yi akan ta sha maganin, AJ ya wani hade rai yace "Kee baza ki amshi maganin da ake baki ba? Wa zaki ba wahala?" Jay yace "Ba ruwanka pls AJ, get out" Ita dai Khaleesat ko kallonsa bata yi ba tana fama da kanta, Jay bai sake takurata kan ta sha maganin ba ya mike yace "Toh ki daure ki hau kan gado ki kwanta, i am coming now" Ta gyada masa kai, ya juya ya nufi kofa, ko kallon Ajay bai yi ba ya fita daga dakin, AJ ya tabe baki ya juya ya koma downstairs. Haka nan Jay ya hado alluran da za mata don saukar mata da zazzabin, sai da ta ga ya dawo dakin sannan ta daure ta koma saman gadon tana ganin jiri ta kwanta, ya tsaya gefen gadon yana rike da alluran yana kallonta, ta marairaice ta girgiza masa kai kawai alamar bata so, ya kwantar da murya yace "To ya kike son in maki Halysaah? Kin ki shan magani" wayarsa dake aljihunsa ya ciro jin yana ringing ganin Salem ke kiransa ya ajiye alluran hannunsa yace "I am coming Halysaah" Fita yayi daga dakin, ya sauka downstairs ya tarar da Salem zaune parlor, bayan sun gaisa Salem yace "Slide dina nake son zaka duba min Jay" Shi dai AJ na zaune yana kallon kwallo ga Legend a gefensa, Jay yace "Ohk, but tunda ka zo pls zaka yi injecting Housemate dita she is sick" Salem yace "Ayya, shi sa ta kira jiya, Allah ya bata lafiya, tana can gidan nata ne?" Jay yace "No, she is upstairs, mu je in nuna maka dakin da take" A tare suka wuce sama, AJ dai kallonsa kawai yake a TV kamar bai san suna parlon ba, Jay bai shiga dakin ba bayan ya nuna ma Salem ya dawo downstairs ya zauna, Khaleesat bata yi ma Salem wani musu ba don ba ma ta da wannan strength din duk da yanda bata son allura haka nan ta bari ya mata, tsabar zazzabin dake jikinta ko zafin shigar alluran bata wani ji ba, Salem yayi mata Allah ya sauwake sannan ya fita daga dakin ya koma downstairs, Jay yace "Thank you, bari in duba maka" Sai bayan kusan minti talatin Jay ya tafi dakin Khaleesat ya sameta tayi bacci, ya sauke ajiyar zuciya ya karasa kusa da gadon ya kai hannu kusa da goshinta sai dai bai taɓa ta ba, nan yaji temperature dinta ya fara sauka, juyawa yayi ya dau sauran shayin da ta bari ya fita daga dakin..... Wajen karfe sha daya da rabi Khaleesat na kwance hannunta rike da wayar Housemate dinta, tun 20 min ago ta tashi daga baccin da ya dauketa daxu, she felt a bit relieved now da alluran da Salem yayi mata, sai dai har sannan kanta bai daina mata ciwo ba kamar ta cire ta huta, tayi kokarin ta tashi ma ta tafi bandaki amma ta kasa, she is so weak kamar warce ta dade tana ciwo, hakan yasa kawai ta jawo wayar Jay, da har zata shiga gallery dinsa to while away time amma sai taga it's not proper ta shiga hotunansa, hakan yasa ta shiga wani game da ta gani kawai tana yi daga kwancen da take, bude kofar dakin aka yi ta daga idonta, Jay ne ya shigo dakin AJ dake bayansa yaki karasowa ciki ya tsaya daga bakin kofar, Jay ya nufota yace "Ashe kin tashi, how are you feeling now Halysaah?" Ta gyada masa kai a hankali tace "Good morning" Yace "Morning Housemate, are you feeling much better now?" Kai kawai ta gyada masa, yace "Ohk bari a kawo maki breakfast, idan kinyi sai ki daure ki sha magani kin ji" Ita dai bata ce masa komai ba ya juya ya nufi kofa ya fita ya mika ma AJ wayarsa sannan ya sauka downstairs zai kawo mata breakfast, shi dai AJ daga sama har kasa yake kallonta, ta ɗan saci kallonsa to see if he is still standing by the door ko ya tafi, hada ido suka yi ta dauke idonta tana ci gaba da game dinta da take, after a while ta kara satan kallon bakin kofar taga ya bar wajen, sai ga Jay ya shigo ya ajiye mata tray din breakfast ta dinga kallon plate din baked beans irin na turawa a gefe da soyayyen kwai a gefe, with veggies, sai sausages, ga cup din hot chocolate with few slices of bread a gefe su ma, ita dai tasan ba iya cin wannan abincin zata yi ba, yana kallonta yace "Can you give me ur frnd Safiyyah's Home address?" Ta sauke idonta ta gaya masa address din, yace "Ohk, na ma san area din, i have a frnd there" Ita dai tayi shiru, ya dauko mata maganin da taki sha daxu ya ajiye kusa da ita yace "Pls ki daure kiyi breakfast din, sai ki sha drug din kafin in dawo" A hankali tace "Toh nagode" ya mata murmushi ya juya ya fita daga dakin ta bi sa da kallo. Jay ya tarar da AJ zaune a waje gurin shan iska dake compound din yanna danna wayarsa, hakan yasa ya nufesa ya zauna kujeran dake facing dinsa yace "AJ, i think i am confuse at this point, what do u suggest about this young girl's issue?" AJ ya daga ido ya kalli Jay yace "My suggestion is that... ka barta ta tafi duk inda ma zata ka cire hannunka da bakinka cikin wannan case din babu abinda ya shafe ka, a cikin kunnenka kaji tace shi gayen ne ke sponsoring dinta, babu kuma ta yanda zai yi sponsoring dinta without the consent of her parent, kaga they are comfortable with that, so who are you to intrude Jawwad? Baka san komai akan ta ko kan saurayin ba don me zaka zakalkale haka? Tare fa ka gansu, da can baya zuwa America din ya sameta ne a gidan? sai yanzu tasan yana molesting dinta? Girl's can be very cunning fiye da tunaninka, don't start what u can't finish Jawwad" Jay dake ta kallonsa yace "So now what are you insinuating?" AJ yace "Since you are daft kar Allah ya sa ka gane abinda nake insinuating" Jay dai kallonsa kawai yake, after a while a hankali yace "But duba da abinda ya faru tsakaninka da guy din kasan zai iya hurting dinta idan nace ta koma gidan nan AJ, she is no longer safe in that apartment, ka dai ga ba ma cikakken hankali ke gare gayen ba, ka duba fa wuka yaje ya dauko a kitchen" AJ ya gyara zama yace "Sai kayi mata hanyar komawa gun iyayenta as the good Samaritan that you are from Samaria, kaga in ta koma sai ta gaya ma iyayen nata abinda ke faruwa da abinda selfishness dinsu ya ja mata a kasar mutane, sai su yi sorting kansu a can kawai" Jay yace "Kar kace haka, we know nothing about why they allowed him to sponsor their daughter, we shouldn't judge them har sai mun san dalilinsu AJ" AJ yace "Dalilin banza, babu responsible parent din da za su damka ma kato irin wannan mutumin er su ya kai ta wata kasa da sunan karatu, it doesn't even make sense, sai kace ba musulmai ba, ko da cousin brother dinta ne ma abun bai yi tsari ba balle babu ko wani relationship na jini tsakaninsu, who does that" Jay ya sauke ajiyar zuciya yace "Duk da haka dai ni bazan yi judging dinsu ba tare da nasan komai ba, let give them benefit of doubt" AJ yace "Sai kayi ta basu ai, ni kam bazan bayar ba" Jay yace "But komawarta Nigeria yanzu bazai yiwu ba AJ, ba shine solution ba, Monday za su fara exams, John Hopkins university take ita ma fa" AJ yayi dariya har da kyakyatawa yace "Tabb, lallai gayen ya kashe kudi ba na wasa ba" Jay dai kallonsa kawai yake, AJ yace "Toh za a fara exams me kake nufi kenan? Naji ka ce apartment din nata is not safe for her anymore..." Jay yace "She will remain here har su gama exam kafin ta koma Nigeria wajen iyayenta" AJ ya wani kallesa da sauri yace "What do you mean? Kana nufin mu zauna gida daya da balagaggiyar yarinya da ba muharramar mu ba kamar wasu jahilai marasu tsoron Allah? Kai da wa za ku yi wannan nonsense din??" Jay yace "Duk yan iskan turawan da kake kawowa gidan nan ka basu daki su zauna dama muharramanka ne ban sani ba?" AJ yace "Turawa kace ai, kuma babu komai tsakanina da su kai ma ka sani, i am only helping most of them tunda ba a garin nan suke ba" Jay ya mike yace "Ita ma haka za mu yi helping dinta tunda ba a garin take ba, take it or leave it" yana kai wa nan yayi wucewarsa inda yayi parking motarsa, Ajay ya bi sa da wani kallo, can yace "Sai dai ku je can ku biya wani apartment din ku zauna tare, babu wanda zai takurani a gidan nan wallahi, dama ai kun saba zama gida daya tare, it's not a new thing, dole ne sae ta zauna gidan nan cikinmu mu ba maguzawa ba" Shi dai Jay ya shiga motarsa ya fita daga compound din ya kama hanyar gidansu Safiyyah....