Kenza eBookz

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 12

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 12

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 12: Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 12. Sakin Kayan hannunta sakinah tayi cikin…

4,487 words

Sakin Kayan hannunta sakinah tayi cikin mummunan tashin hankali da tsananin tsoro da firgici ta isa gurinta da gudu har tana kifewa ta tashi da rawar jiki tsoronta tsananta ta isa gareta ta riqe kafafunta da sauri koina na jikinta na rawa,

Da hannu daya ta dauki stool din duk nauyinsa ta Dora a setin kafafunta ta tsayar da ita kafin a rikice ta taka gadon dake dakin ta taka wardrobe ta zare daurin suka fado qasa tareda Ayanah din tana rungumeta da tsananin karfi tareda fasa kuka Mara sauti sbd tashin hankalin tinanin rasa ayanar da zatayi da bata shigoba a lokacin,

Ayanah da gabaki daya jikinta ya sake idanuwanta a rufe suna gangaro da hawaye masu dumi bata iya motsawa ba sedai kukan sakina kawai dake Ratsa kunnuwanta yana sake kashe zuciyarta da batada Sauran tinanin komai sbd ta yanke rai da rayuwa.

Kuka sosai sakinah takeyi sbd batasan yaya zatai qarashen rayuwarta babu Ayanah ko daya daga cikin jinin GHAZ ba sbd sune rayuwarta itama sune tamkar nata jinin da batada kowa duniya Bayan su hakama har abada matiqar tana tareda Ayanah ita baiwar tace sbd haryanzu bawai ta yanta bane suna tare ne kawai harma suka manta matsayin junansu sbd sun samu kansu a wata ukubar rayuwar data mantar dasu cewan su din baiwa da uwar daki ne amma har abada koda BOYEM ta yantata matiqar Ayanah bata yantata ba ita din baiwarta ce har qarshen rayuwanta Wanda ita kanta indai tana tareda Ayanaah zata rayu da ita har qarshen rayuwanta to batama buqatar yancin zatai mata bauta ta bita har abada.

Kuka sosai sakinah tayi na tsoron halinda Ayanah din ta shiga kafin ta iya sake Ayanah wadda har lokacin yake kaman batada lakar komai a jiki sai idanuwanta dake bude jajir suna fidda hawaye masu dumi dake gangara a hankali.

Gadon sakinah ta gyara har lokacin itama idanuwanta hawayen sukeyi ahankali tana gamawa ta kamata ta kwantar kafin ta maida komai inda yake ta gyara dakin kaman babu abinda ya faru sbd duk motsinta ma bata Bari anji komaiba sbd kada asan abinda Ayanah din tayi kokarin yi hukuncin dazai hau kanta bazai taba zamowa me sauki ba,

Tana gana gyara dakin ta juyo da idanuwanta da suka sauya sosai ta kalli Ayanaah zatai magana aka taba kofar dakin Wanda ya sakata saurin daidaita kanta tana goge fuskanta ta dauki towels din data shigo dasu dan kaiwa inda zata jere su.

Ayanaah ma idanuwanta ta rufe a hankali sbd bata kaunar ganin komai da kowa idan ba yar uwarta jininta ba Zuhrah.

Tenya ce aka budewa dakin ta shigo wainda ke biye da ita suna dauke da wasu magungunan gargaji masu tsafta da kyau aka shigo dasu Ana jerewa a table,

Idanuwa tenya ta zubawa Ayanaah tana kallanta haka kawai taji bata iya Kyale Ayanah akan zamowanta imebēti wadda koda zata sauya kowa bazata taba sauya Ayanah GHAZ ba komai wuya tanason ganinta a imebēti sbd itace kyanta yakeda tsananin nutsuwan da zai iya girgiza Kyan HAILE da qasar take taqama dashi ita kuwa a nata bangaren batada burin daya wuce takai HAILE qasa ta hanyar samun macen da zata kere ta a gurin sultan musamman idan Allah yasa aka samo LEUL ba a gurin HAILE ba sbd Qin HAILE a jikinta yake tin daga lokacinda ta dauke ran qanwarta uwa daya uba daya da ita kadai gareta sbd kawai ta samu cikin sultan a matsayin imebēti a lokacin da tana yayin dauke rayukan duk macen daya kwanta da ita,

Wannan ne dalilin daya saka tenya batada burin daya wuce samar da macen da zata fi HAILE komai da samun gurbi a zuciya da ahalin sultan,

A tarihi da doka tareda qaida mai girma a Masarautar BOYEM baa taba auren wadda ba jinin BOYEM ba, Babu macen data taba Matar Sarkin Boyem matiqar ba jinin sarautar BOYEM bace,

Duk yanda mace ta shiga ta mamaye zuciyar Sarkin Boyem komai tsananin so da kaunar dayake mata fiye da matansa matsayinta yana tsayawa ne a iya WISHMAH wato lady mistress ita ta wuce matsayin imebēti hakama bata zama matarsa ta aure ba amma kuma matsayinta daya da matansa a duniya a zuciyarsa kuma tama fi matan matsayi,

Dan haka a koyaushe burin da tenya take kwana dashi take tashi tayi rayuwa dashi shine ta tabbatarda ta samar da wishmah a BOYEM din yanzu wadda zata ruguza power din HAILE koba duka kwata kwata ba to ta tabata sosai dan babu macen datai darajar HAILE a qasar BOYEM yanzu sbd itace mata kuma uwargidan sultan YASAR haka kuma macen datafi kowace macen kyau da iko a qasar.

Duk da Ayanah baiwa ce wadda bauta ta sauya mata abubuwa da dama ita ta hango asalin sirrin kyanta Wanda zai fito fiyeda na HAILE idan ta samu gyara da hutun da fata da gangar jikinta suke buqata ga wata irin sanyi da nutsuwa a tattare da ita wanda zai iya sanyaya zuciya mai Zafin gaske irin ta sultan jinin masu BOYEM da kansu dan haka Ayanah tayi mata tako Ina kuma taci burin fiddo da dukkanin kyanta da kwarjininta da bauta ta boye zata fiddota a matsayin sabuwar wishmah ta BOYEM da aka shide qarnika baa samu ba sbd yawancin sarakunan BOYEM basa soyayya dan bata tsarinsu Sarkin uku ne kadai suka taba wishmah Sai a yanzu datake fatan hakan ga sultan YASAR.

Umarni ta bada aka tada Ayanah Zaune wadda take kwance kaman babu inda baya aiki a jikinta,

Sakinah ce ta saka mata pillows biyu a bayanta suka tareta aka fara bata maganin masu dumi da wani qamshin nutsuwan dayake ratsa hancinta zuwa cikinta,

Gabaki dayansa aka sakata shanyewa kafin suka ajiye cup din akan tray din da aka jero cup da bowl din Dayan maganin masu kyau.

Dayan maganin aka Dora mata a baki yafara shiga maqoshinta ta rufe idanuwanta ahankali tana Jin taste din maganin na ratsa bakinta aka buga kofar dakin da nutsuwa Wanda ya saka dukansu kallan kofar Banda Ayanah din dake Jin zuciyarta na Wani irin nauyi ta sake rintse ido.

Da ido tenya ta basu umarnin su bude dakin dan haka daya daga cikin bayinta ta juya ta nufi kofar dakin a natse ta bude Kai tsaye tana kallan wadda ta bude dakin kanta a qasa ta bude baki da taushin murya tace

‘Daya daga cikin sabbin imebētin da zaayi ta illata kanta harma tana gap da rasa ranta amma…….

Wani irin fesowa abinda yake cikin bakin Ayanaah yayi da karfin gaske idanuwanta na budewa jajir sbd abinda taji Wanda zuciyarta ta tabbatar mata da Zuhrah ce,

Wata irin rawa hannuwanta da kafafunta suka fara ta yunqura da karfin gaske tana Miqewa tsaye harshenta karyewa sbd mummunan tashin hankali ko magana ta kasa sai idanuwanta dake rikidewa jajir b Kyan gani………

Sakinah ma da jikinta ya dauki wata irin rawar tashin hankali saurin dafe Ayanah itama tana Jin tabbacin Zuhrah ce dan haka hawaye suka fara ciko idanuwanta sbd Zuhrah tayi hakan ne sbd yar uwarta Ayanaah…

Ayanah fizge wa tayi daga riqon Sakinah tana Miqewa jiri mai karfi na dibarta tabi bayan su tenya da suka fice dakin batareda sunsan halinda Ayanah din ta shiga ba.

Ko ganin gabanta Ayanaah batayi jiri na dibarta na maganin da aka bata Wanda karfinsa yake dan bugarwa sbd na gyaran mace ne,

Wani dishi dishi take gani a idanuwanta da duhu duhu amma a hakan take jefa kafarta duk inda ta samu ta nufi hanyar da Batama San Ina zata samu Zuhrah dinba,

Sakinah d gudu taje biye da ita tanason ambatar sunanta amma ta kasa sbd kada wani ya jisu asan sun fito komai y qarasa lalacewa dan haka biye take da ita tana wasu irin hawayen tausayi da tashin hankali tareda baqin ciki tana kokarin kamata amma Ayanaah dinba taqi Bari fizge wa takeyi sbd ko zata rasa ranta Ayau sai taje ga yar uwarta.

Ragaita Ayanaah din ta ringa yi tana zagayen Neman inda Zuhrah taje amma koina tsit babu Zuhrah ta zube a tsakiyar gurin qasa tareda dafe kirjinta dake mata Wani irin azababben radadi ta fasa wani irin kuka mai karfi da taba zuciyata tareda ambatar sunan Zuhrah da karfi tana sake dafe kirjinta dake Neman bugawa da sauri sakinah ta zube qasa din itama tana rufe mata baki da hannuwanta biyu tana kukan itama mara sauti jikinsu na rawa su dukan,

Kuka sosai Ayanaah keyi mai tsananin karfin sautin gaske amma Sakinta ta riqeta jikinta da karfi ta toshe mata baki sautin kukan baya fita sbd idan batai hakanba koina zai amsa karar kukan nata Wanda takeyi d karfin gaske tana ambatar sunan Zuhrah.

Motsin tahowa suka Ji Wanda ya saka sakina janta da karfi cikin tausayawa ta boye bayan wani dakin da ita har lokacin riqe take da ita bakinta a toshe.

Zuhrah ce aka dauko tamkar gawa a kan wani qaramin gadon marasa lafiya koina jikinta ba Kyan gani jininta ne yake fita sosai Wanda ya sauya kamanninta dana Kayan dake jikinta,

Babu alaman rai a jikinta idanuwanta a rufe hannuwanta a sake Mutum hudu ne maza dauke da ita jini na bin hannuwanta zuwa yatsar hannunta yana diga qasa,

Tenya ce ta bude baki Kai tsaye cikin iko da bada umarni mai Zafin gaske tace

‘A kaita kurkukun bauta da ukubar da bayi acan zatai jinya t warke tayi rayuwa har qarshen rayuwarta bazata taba fitowa ko wuya ta dauki ranta ko kadaici da ukuba wannan shine hukuncinta……

Wani irin Juyawa duniya tayi da Ayanaah wadda ta bude baki da karfin gaske ta fasa Ihun kiran Zuhrah cikin rikitaccen kukan daya saka sakinah sake saka karfinta duka tana danneta tareda rufe bakinta d karfin gaske itama tana hana nata Ihun gunjin kukan fidda sauti.

Fizge fizge Ayanah keyi tana dukan hannuwan sakinah son qwacewa ta tafi ga Zuhrah kome zaayi musu Ayi tare amma Sam sakinah ta saka karfi sosai ta danneta da gaske sbd tana fita dukansu su ukun rasa rayuwarsu zasuyi dan haka dole ta hana Ayanah dan yanzu ita da zata zama imebēti itace hope dinsu harma dana fiddo Zuhrah cikin wannan mummunan hukuncin na qarshen rayuwa.

Gap da su aka kawo Ana wucewa fuskan Zuhrah dake jina jina da jini tana fuskantar saitinsu idanunwata a rufe Wanda ya saka zuciyar Ayanah kasa dauka ta daga hannu tana miqawa zuciyarta na rage bugawa tana sake kokarin fizgewa tana ihu sosai a zare amma Sam babu sauki a riqon da akai mata tana kallo har aka bace da Zuhrah zuwa inda bazata sake ganinta ba har karshen rayuwarsu kila.

Wata irin jijjiga takeyi tana Ihun Wanda har jikinta ya fara sakewa ahankali ta some a jikin sakinah din gaba daya numfashinta na tsayawa. #MAMUH

HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070

Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali*_HAYATEEM_* Mamuhgee

29 *_ZUZEAM VENTURES_* 08144015291 Bononza bononza Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me kamawa insha allah -Da 5k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani, -Da 10k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba, wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online Dan haka duk wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri kafin ta kare Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah Idan kinada 3k ma zaa baki ciccibi kawai sai gari da tsumi masu kyau da ingancin suma, Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma suka shiga na 10k kinada package din 5k Idan kin kawo mutun goma suka shiga na 5k kinada package din 3k. Zuzeam ventures 08144015291

******* Cikin tsananin sabon tashin hankali da tsananin tausayin Ayanah dake kashe duka jiki da zuciyarta ta fara girgiza Ayanah din da dan karfi tana ambatar sunanta da sauti qasa qasa amma ba alaman Ayanah din zata motsa ko alamar akwai Sauran rai a jikinta dan haka da sauri ta saka qarfinta ta daukota a bayanta tana waiwayen hanya dan gudun a Gansu ta ringa bin bango a tsorace da firgici ta koma har dakinsu ta fada gado da ita tana sauke wani wahalallen numfashin gajiya da tsoro da firgici,

jikinta na rawa ta miqe tazo kofa ta rufe da sauri hadda saka keyi kafin ta dawo inda Ayanaah din tana sake girgiza ta tana ambatar sunanta da sauti mai bayyanar da tsoronta na rasa Ayanah din ga kuma tausayin Zuhrah dake sake sako mata kukan daya kasa ma fitowa zuwa lokacin sedai jan ido da rawar jiki,

Ruwa ta dauko hannuwanta na rawa ta zubawa Ayanaah din wadda bata motsa ba saida ta zuba mata ruwa sosai tukuna ta motsa kadan idanuwanta da sukai mummunan ja suna budewa ahankali ta saukewa sakinah su batareda ta kyafta ba ko motsawa tamkar gawar da baa shafe wa idanuwa ba,

Hawaye ne masu tsananin zafi suka gangarowa sakinah ta sunkuyar da kanta qasa tana dauke kallanta daga kan fuskan Ayanah da ko kyaftawa idanuwanta basu yi ba tana mata kallan da batasan na menene ba amma dai koma na menene tasan akwai kallan yanke kauna a cikinsa dan haka jikinta yayi sanyi hawayenta na tsananta gudu ta bude baki koina na jikinta na qara sanyi tace

‘Allah ne ya kaddaro muku hakan da gani har ke har Zuhrah babu Wanda zai iya sauya hakan, Allah ya fini sanin dalilinsa na yin haka hakama yafi ki sani yafi Zuhrah sani harma da duka masarautar BOYEM din, Ga dukan alama kaddararki ce ta sako mu halinda muke ciki sbd Allah ya riga kila ya kaddara tarayyarki da sultan YASAR Wanda matiqar akwai rabo a tsakaninku to shine yayi sanadin komai daya faru dan zuwanmu nan, Komai daya faru ya samu yan uwa da iyayenki ki yadda da rabo mai karfin dayake tsakaninku ke kila ya haddaso hakan dan haka ko a yanzu rabon ke dince ya saka yar uwarki sadaukar da rayuwarta sbd bazata iya qazantar dake shirin shiga tsakaninku ba ta hada shimfida daya da Mutum daya ku haifa masa yaya ku hada yayanku uba daya Kina raye tana raye,

Kinyi kokarin daukan taki rayuwan Amma Allah ya Hana hakan sbd kece wadda kila ya kaddarowa hakan,

A yanzu Zuhrah ta Riga takai karshen tata kaddarar kila dan kuwa har abada mutuwarta ce kadai zata fiddo da ita inda aka kaita waton gawarta ce kadai zata fito idan zaa rufeta kenan,

Tsananin so da kaunar da kike mata da saka rayuwarki a halakar da zaku rasa Ranku gabaki daya bazai taba sauya kaddar datake boye a cikin wannan lamarin ba,

Lokaci yayi da zaki rungumi kaddarar da gaske AYANAH GHAZ, Zamtowanki imebēti ki haifi jinin BOYEM ko mace ko namiji shine zai baki hope na koba yanzu ba zaki fitar da yar uwarki daga wannan ukubar data Riga ta shiga sai mutuwa, Zamtowanki cikakkiyar imebētin sultan YASAR BOYEM shine gatan da zakiyi wa yar uwarki da komai dade wa bazata cire rai daga samun ceto daga gareki ba dan kuwa tayi abinda tayi dinne dan ke ki samu zama imebētin ke kadai bada ita ba dan tasan zaki taimaka mata daga lokacinda kika samu daman tashi daga baiwa hakama matiqar kika zama imebētin kika tashi daga baiwa ko ba yanzu ba Kinada Sauran saka ran samun yancin Neman dan uwanki Abaas da shima matiqar yana raye yasan indai Kina raye wata ran Zaki iya nemansa,

Ke kadai kika raye a GHAZ wadda yan uwanki suka Dogara dake dan Allah Nima Ayau Ina rokonki ki jure ki daure ki rayu ko dan yan uwanki Dani kaina…….

Wani irin kuka mai tsananin ratsa zuciya ne sakinar ta sake tana sake sunkuyar da Kai tace

‘Matiqar kika jure kikai sadaukarwa tabbas ranar da zaki fiddo yar uwarki zata zo harma Kuyi rayuwa a tare idan bazaki iyaba ki daure ki iya kiyi sadaukarwar da yar uwarki tayi ki jure kiyi yaqi da komai ki ceto yar uwarki….’

Rufe idanuwa ahankali Ayanah tayi wasu hawaye masu dumin gaske suna gangarowa daga cikinsu batareda ta motsa ba har lokacin,

Shiru sakinah itama tayi hawayen na gangarowa daga cikin idonta babu Wanda ya sake motsawa a cikinsu hawayen Ayanah takeyi sosai hatta gashin jikinta sun kwanta gabaki daya tamkar sun mace,

Babu Sauran rayuwar data rage mata a yanzu da batada kowa a rayuwarta bayan sakinah,

Dukkanin kuzari,farin ciki,ruhi da bugun zuciya da hasken idanuwanta an rabata dasu babu ko daya a tattare da ita dan haka babu Sauran abinda ya raye komai na rayuwa bayan gangar jikinta da yanzu itama zata zama ba nata ba saina biyan buqatan wani Wanda zai watsar da ita ya manta ita da duk abinda ya rabata dashi ta zama fanko sauransa har qarshen rayuwarta,

Batada Sauran zabin daya wuce wannan din matiqar ranar da zata fiddo yar uwarta zatazo tabbas zata zama fankon ragi da Sauran wani din har karshen rayuwarta sbd daman babu abinda ya rage a rayuwan Bayan gangar jikin.

Hawayen ne suka cigaba da gangarowa gefen idanuwanta dake rufe batareda ta motsa ba har lokacin sedai sakinah ce ta saka farin qaramin handkerchief mai tsafta tana share mata hawayen ahankali suna saika Akan kyallen batareda ta sake cewa Ayanah din komaiba sbd ba abinda ya rage ma fada.

Shiru dakin yayi ko numfashinsu Baka Ji har tsawon Daren haka suka shafe sa cikin toshewan zuciya babu motsi,

Sallan asuba ce ta saka Ayanah din motsawa bata iya tsayuwa daidai ta miqe sakinah na riqe da ita har toilet.

Dukkaninsu sallah sukai suka ringa kuka mai tsima zuciya suna fadawa Allah damuwa da quncinsu har gari ya fara haske lokacin sakinah ta fice zuwa dakinsu tayo wanka ta sauyo uniform ta taho tafara aikinta ita kuwa Ayanaah na Zaune zuru ta kwantar da kanta a gwiwan kafafunta seti da window ta zubawa waje ido bata ko kyaftawa.

*********Ayau din aka taho aka kawo masu fara mata gyara ma Musamman Wanda zai qarasa dawo sa asalin kalar fatarta fara sol da gyaran fata da qamshi na musamman Wanda tinda masu gyaran suka iso bata iya cewa komai ba ko kuzarin komai duk yanda akai da ita tana Zaune babu gardama ko hayaniya ta zama tamkar Mutum mutumi dan haka suma suka zags sosai sukai aikinsu hankali kwance a natse,

Har kusan dare Ana abu daya da jikinta kafin suka tafi sai kuma gobe,

Washe gari ma haka suka taho sukai aikinsu suka tafi,

Tsimata akeyi cikinta da fatarta da asalin zallan madarar raqumi da lalle da zuma tareda wasu Hadi masu tsananin qamshin da hatta gashinta dayake Shan gyara qamshi yake fiddawa me sanyaya zuciya da kwantar da hankalin mai shaqa tareda basa nutsuwa da mutuwar jiki,

Sati guda akai Ana mata gyaran daya sauya kalarta da kamanninta asalin Ayanah dinta ta dawo sedai duk tsawon lokacin nan babu Wanda ya taba Jin koda muryanta sbd gabaki daya ko magana ta dena ido ne kadai se Numfashi ya rage mata sai kuma yanda akai da gangar jikinta ta sauya gabaki daya ko sakinah bata samun maganarta se dai ido kawai.

A cikin sati biyu tenya ta gama samun duka abinda takeson samu a gurin Ayanah na zama imebēti kafin zuwa wishmah dan kuwa hatta yatsun kafafun Ayanah dama hannunta abin kallo da daukan hankali ne sbd ta fito asalin balarabar ANJOM GHAZ dinta,

Haskenta da kyanta wani daukan ido yake yana fizgar hankali, Qamshinta kuwa daya gama Kama kowane saqo na jikinta da gashinta tana tinkaroka zakaji qamshin asalin Larabawan BOYEM yana tashi a jikinta musamman idan tai motsi haka zakaji sa yana ratsa zuciya da gangar jikinka dan haka kwata kwata aka hana kowa ganinta bare Jin qamshinta bayan sakinah da ita kadai ce baiwar da tenya ta yadda ta Barwa hidimart sbd labarin Kyan Ayanah GHAZ na isa gurin HAILE zata iya yanke mata hukuncin Kisa Kai tsaye tin kafin sultan ya mallaketa a shimfidarsa dan haka tenya ta saka ido sosai da tsaro akan AYANAH GHAZ kaman yanda take kiranta kafin ta hau shimfidar sarki sunanta ya tashi daga hakan.

Tsaro sosai Ayanah GHAZ take samu daga tenya wadda daga qarshe dauketa tayi daga bangaren gabaki daya ta dawo da ita gurinta sbd barazanar datake ji a jikinta na kusanto Ayanah din sbd kyanta da yayi Wani irin yawan da itama idan ta kalleta Jin takeyi gabanta ma faduwa.

Dawowan Ayanah gurin tenya ya sakata sake shiga ran tenya sbd shirunta daya zamo tamkar nutsuwar datafi ta kowa data sani a rayuwarta hakama hakanan takejin a ranta Ayanah zata iya sauya musu kaddara dan yanda take Jin nacin son kasancewanta imebēti kota halin yaya dan haka ta matsu safiyar Washe garin ranar ta wanye dan sultan YASAR na kan jirgin sauka BOYEM Wanda a Daren goben ne zata isar da Ayanah shimfidarsa da insha Allah take masa fatar samun rabon haihuwa da ita. #MAMUH

HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070

Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali*_HAYATEEM_* Mamuhgee

30 *_ZUZEAM VENTURES_* 08144015291 Bononza bononza Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me kamawa insha allah -Da 5k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani, -Da 10k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba, wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online Dan haka duk wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri kafin ta kare Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah Idan kinada 3k ma zaa baki ciccibi kawai sai gari da tsumi masu kyau da ingancin suma, Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma suka shiga na 10k kinada package din 5k Idan kin kawo mutun goma suka shiga na 5k kinada package din 3k. Zuzeam ventures 08144015291

******* A Daren Ayanah bata rintsa kona minti daya ba kwance kawai take amma babu ta inda bacci ya tinkaro idanuwanta sbd koda Yazo na iya ido ne babu kowane sauki da sassaucin dayake bawa ruhi da zuciyarta sbd a daidai wannan gabar ta rasa nutsuwa da farin ciki tareda walwala ko sakewa har abada sai kuma ranar data iya saka daya daga cikin jininta biyu da suke raye a idonta dan haka zata rayu ne kawai gangar jikinta na aiki amma Banda zuciya wadda itama bugawa kawai take amma duk abinda zata samu a duniyar nan yanzu bazai taba bata farin ciki Kona seconds ba sbd ta gama rufe babin rayuwarta babu farin cikin dazai shigo bayan qarasa rayuwa da qunci daddabe a ranta kuma a hakan zata bar duniya.

Daga Daren yau shima tana kwana a shimfidar ‘da namiji zata tashi daga AYANAH GHAZ dinta zuwa macen da batada Sauran amfani a duniya Bayan biyawa namiji buqata, Zata tashi daga Ayanar Ammanta da Abaa dinta harma da Abaas dinta Wanda ya gwammaci mutuwansa akan ganin an keta haddinta Shiyasa ubangiji ya rabasu sbd kada yaga wannan mummunan ranar da Ayanaah bazata taba aure ba har abada,auren dayake fata tayi ya hada zuria da ita,auren dayake da mafi girman Buri akansa sbd shine yayi alkawarin bada aurenta ya karbi zinariya da azurfar sadakin aurenta a hannunsa koda yana qaninta wannan Alkawari ne daya dauka kuma mahaifinsu ma ya yaddar da cika masa wannan burin na shine zai bada auren Ayanah dinsa,

Duka wannan Buri kashe a iya mafarki da Buri zai tsaya,

Aurenta a matsayin ‘ya babba ga shugaban ANJOM kuma mace mafi kyau a GHAZ shine abinda garin ANJOM gabaki daya da ahalinta suke jira sbd sake daukaka darajarsa a garin gabaki daya, Ashe kaddararta ma babu aure a cikinta kwata kwata Ayau gata zaa kaita a matsayin abar biyan buqata da sauke shaawa batareda daraja ko daya ba,

Ayau itace ranar yancin jiki da sunanta na qarshe sbd daga yau din bazata sake sunanta Ayanaah ba dayake da daraja sosai ga iyayenta da yan uwanta daga yau sedai a kirata da imebēti Ayanah har karshen rayuwarta, Daga yau ta haramta ga kowane irin namiji har karshen rayuwarta dan haka aure sedai taji sunansa kokuma taga Ana yinsa……

Lumshe idanuwanta tayi ahankali radadin dayake cikinsu ya ratsa har zuciyarta yana sauka maqoshinta ta hadiyesa zuwa cikinta da babu komai a cikinsa sai tarin quncin da dashi zata mutu.

Har asuba bata rintsa ba bata kuma iya dogon Motsi sbd Sam hanayaniya ya dade da fita rayuwarta bare doguwar magana dan haka sai hakan yake sake qara mata kaman aji da nutsuwa,

Nafila tayi kafin lokacin sallar asubar yayi tayi sallah ta sake miqa dukkanin lamarinta ga ubangiji har gari ya waye sosai tana Zaune kanta akan kafafunta shiru idanuwanta Lumshe tamkar fresh fulawa sabon tsiro.

Karfe tara na safe aka shigo dakin nata aka sake hada mata wasu ruwa masu fitinanniyar qamshi da wani abu a cikinsu aka sakata cikinsu Zafin su na ratsata zuwa cikin jikinta take gashin jikinta suka miqe tanajin hatta kanta saida ya sara yayi mata nauyin daya sakata bude idanunwata data Lumshe ta rufe Bayan shigarta ruwan,

Ruwan ta kalla cikin sanyi kafin ta sauke Numfashi me dumi tana Ji suna sake shigarta sosai suna saka jikinta daukan dumi sosai,

Tsawon awa kusan biyu tayi a cikin ruwan kafin aka fiddo da ita aka fara shafe jikinta da Wani irin hadin danyar madarar datake hade da manshanu danye da baa rabasu ba,

Ahankali ake shafe jikinta Ana murzawa tamkar Ana gudun fatarta ta yage,

Ana gama shafe wa wani turaren hayaqi aka fara mata yana saka abinda aka Shafa mata kama fatarta da shiga tsigan jikinta dan kuwa hatta dogon gashinta saida aka shafe sa tas dashi,

Tenya ce da kanta ta shigo Ana biye da ita dauke da farar kakkaurar madarar shanu me Zafin gaske ta dauka da hannunta ta miqawa Ayanaah din wadda hannu kawai ta miqa batareda ta dago ba ta karba takai bakinta ba musu ba cewa komai ta fara sha a natse jikinta sanyaye.

Sai data shanye kafin aka kawo ruwa masu zafi da kyau da qamshi aka fara zubawa a jikinta Ana wankewa tana Zaune cikin pool din da babu ruwa daga ita sai abinda iya nonuwanta kadai ya rufe sai wandon da shima baida banbanci da pant Wanda shima kusan har ciki an shafa komai,

Wanketa tas akai kafin aka bata damar wanka da ruwan sabulu masu tsananin tsada da qamshi,

Readers Also Read