Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 16
Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 16: Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 16. Likita data dago yin maganar dole suna…
4,478 words
Likita data dago yin maganar dole suna buqatar kiran Sauran likitocin da zasu taimaka mata Jin abinda Hailen ta fada ya sakata yin shiru tana hada zufan tashin hankali sbd akwai Sauran time dan kuwa service dinta baima gama budewa ba dan haka sunada aiki sosai ga naqudar bame sauki bace yakeyi tinda shock ne Kai tsaye ya tado naqudar,
Fetto Kai da kawo ta fara tana fitowa tana komawa cikin tsananin tsoro da tashin hankali me girma ga Masarautar tayi Wani irin tsit babu motsin komai bare kowa alaman duka manyan BOYEM sun taru a fada jiran naqudar Ayanah ghaz wadda itace wadda kaf BOYEM yanzu ake jira dan haka a kakkarfar doka da baa takewa ta Masarautar gabaki dayanta shine duk jinin BOYEM idan zaa Haifa Ana fara naqudar sa babu me sake fitowa bare kaida kawo tsit akeyi har sai ta sauka dan Kai tsaye duk Wanda tsautsayi ya sakasa fitowa ko kaida kawo a hanya cire kansa daga gangar jikinsa ya halasta,
Dan haka ne Ayau dinma babu motsin komai bare hayaniyar komai koina tsit ne tamkar babu dan Adam ko daya a cikin masarautar BOYEM din,
Duka tarin bayin daka bangaren Haile sun gama shirin tarban abinda zata Haifa dan haka a tsaye suke qyam babu kowane motsi dayake tashi suka anan din sai fetto daka Kai da kawo kaman zata rasa hankalinta ta zare, Zufa sosai take hadawa gashi ba ikon magana so take taje ta isarwa sa sultan labarin naqudar Haile amma ba damar fita dan fitarta daidai take da kwananta kabari Ayau din dan saita bar duniya dan haka babu damar fita, Su kansu bayin dake bangaren duka babu Wanda ma yakeda ikon motsi bare fita zuwa isar da sako dan haka ta rasa yaya zatai da rayuwarta fa naqudar sai abu daya ake kwata kwata babyn bai fitoba,
Ita kanta likitan kokarin tsayar mata daya jinin tayi da taimkon da zata iya bata amma dole haihuwa sai lokacin da Allah yace babyn ya fito zai fito dan haka dukansu zufa suke hadawa ba qarami ba suna rasa abin yi har HAILE din tayi Laushi sosai amma taqi yadda kowa ya tsaya hutawa sbd baqin taurin ranta Akan kada Ayanah ta rigata haihuwa,
Tana tsananin buqatar likita amma babu me ikon fita dan kuwa koda Ka isa ka isar da sako tabbas zaka karbi hukuncin barin duniyar Ka dole Shiyasa kowannensu yake hada zufa suna Kai da kawon taimaka mata gurin samun sassaucin abinda take ji,
Zufan fuskarta zuwa wuyanta ake goge mata da tsaftataccen farin towel qarami suna Jera mata Sannu da kokarin ganin ta haihu lafiya, magani kuwa haka ake kawo mata shi tana sha tana dawo da wani sbd tafara Nisan da bata iya Shan komai amma a zuciyarta ta kasa sake adduar datake yi guda daya tak wato ‘Allah ya bata ‘da namiji koma yayane kuma Allah yasa itace zata fara haihuwa’
Wannan adduar take ta maimaitawa tana kasa sakewa dan tabbacin datake dashi na Allah yana karban adduar me naquda dan haka har a tafara ficewa hayyacinta bata roqarwa kanta ko ‘yayanta komai sai wannan adduar gida biyu.
****A daidai wannan lokacin naquda sosai AYANAH GHAZ takeyi me tsanani itama Wanda ya saka itama nata bangaren da bangaren imebētis din kaf yin tsit babu ko abu daya dayake bada sauti sbd Masarautar wannan Karan tafi kowane karo yin tsit dan kuwa mamaki biyu ne yake ci da kashe kowa amma b damar magana a yanzu wato shine Wishmah data tabbata Bayan qarnika da kuma haihuwar da baa San da cikinba kuma a hakan taci gaba da zuwa shimfidar sultan,
Wannan duka wasu abu ne da suka girgiza masarautar da duk Wanda yake cikinta cikeda tsoro da mamakin dayafi Kama da firgici kowa yake, Masu rubuta tarihin qasar BOYEM da Masarautar BOYEM kuwa a daidai wannan lokacin suna can sun fara rubuta wa a cikin kundun tarihi,
A cikin fadar sultan ma a inda ake Zaune tsit abu daya kowa ke jira wannan Karan sunfi kowace lokaci daukan tsit sbd Ana magana a tsakaninsu duk zaman jiran da akeyi amma a wannan Karan sultan YASAR babu abinda ya bude baki ya furta hankali da nutsuwar sa kaf suna ga jiran sakon haihuwan Ayanah ghaz dake saka zuciyarsa cika da Wani irin nauyi da yanayi na tsumayi dabai taba shiga b duk haihuwan da ake masa,
Sosai yakejin kowace daqiqa tana wucewa ne da bugu wan zuciyarsa mai karfin Akan haihuwar yau dayake jinta har jini da bargonsa dan haka take duk Wanda yake fadar ya dauke wuta sukai tsit suma suna shiga tsimayin jira da Jin tsananin son labarin haihuwan wishmah ta farko data sauya tarihi da dama na masarautar qasar BOYEM gabaki dayanta dan haka sai sukejin haihuwan ta jinin BOYEM wannan Karan ta daban ce a gurin sultan da wannan dalilin suka ta zama ta musamman din tinda kuwa wishmah ce zata haihu kowa yasan haihuwan soyayya ce bata saurauta ba.
Tenya data kasa ta tsare ko motsawa batai ba daga gaban Ayanah dan kuwa duk inda hannuwan likitoci suka taba a jikinta idonta na Kai sbd tsananin tsaro da rashin yadda da kowa,
Sakinah ma a wannan lokacin tana riqe da hannun Ayanah gamgam suna hada zufan tare tana Jin duk radadin da Ayanah ke ji a zuciyarta tana Jin tsananin matsuwa da son haihuwan Ayanah lafiya tana saka mata addua mai kyau a bakinta,
A bakin Ayanah din addua ce guda biyu rak take fita wato Allah ya zama gatan yan uwanta dasuke raye ya kawo sauyi a rayuwarsu sai kuma adduar Allah ya tsaya Akan kowane irin lamarin babynta da zata Haifa,Allah ya haskaka rayuwarsa ya basa kariya daga duka Sharrin duniya’
Wannan adduar itace take maimaituwa a Baki da zuciyar Ayanah da sakinah harma da tenya da ita iya babyn takewa adduar Allah ya basa kariya har qarshen rayuwa kowannensu a zuci yake adduar.
Sosai azabar tayi mata yawan data fara galabaita tsananin tausayinta na saka zuciyoyinsu sanyaya dan haka suka dage da addua da karfi da imaninsu suna Neman mata sauki a gurin ubangiji,
Sakinah jiqe take shar kaf da zufa tana tsananta adduarta a fili tana share zufan Ayanah suna sake qanqame hannun juna Ayanah na Jin kaman bazata rayuba rayuwarta zata tsaya ne daga nan sbd abinda take ji tabbas shine kowace uwa takeji yayin jeho yaya a duniya idan har ta mutu anan ta tabbatarda tayi shahada dan haka take Jin inama zata mutu anan din ta huta.
Lokuta masu tsayi suka dauka dukansu suna naquda me tsayi da rashin sauki, Babu wadda bata Kai qarshen jigata ba a cikinsu tareda fita hayyaci,
Duk wainda suke tareda su sun sare sun shiga tsoro da fargaba tsawon wunin da babu komai cikinsa sai jiran azaba,
Karfe shida na yamma a lokacin da baby ya turo kai fitowa jikin HAILE gadan gadan take su fetto suka shirya tsaf ma tarbansa cikin tsananin matsuwa sbd suna sane da har lokacin Ayanah ghaz bata haihu ba dan akwai sautin karar da ake sakewa masarautar ta amsa gaba daya idan an haihu dan haka tinda basu ji komai ba sun San bata haihunba gashi yanzu tasu zata far haihuwa babbar matsalar shine fita a wannan lokacin batareda haihuwan Ayanah ba zuwa isar da sakon haihuwar.
Cikin azababbiyar azaba da Nishin dayake hade da ihu mai karfi Haile ta saki tana qanqame hannuwan yarta da karfin gaske ta sunbulo babyn dayake cikinta ya fado a hannun likitar dake gabanta idanuwan fetto kaman zasu fado qasa sbd jiran ganin abinda aka Haifa,
A daidai wannan lokacin itama Ayanah ta sauke wani kakkarfan nishin daya fito da nata babyn duniya itama Wanda ya fado a hannun tenya Wanda jikinta ya dauki mummunan kakkarwar abinda aka Haifa tama kasa yadda da abinda ta gani. #MAMUH #THE LION ARRVL
HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070
Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali*_HAYATEEM_* Mamuhgee
38 *_ZUZEAM VENTURES_* 08144015291 Bononza bononza Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me kamawa insha allah -Da 5k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani, -Da 10k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba, wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online Dan haka duk wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri kafin ta kare Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah Idan kinada 3k ma zaa baki ciccibi kawai sai gari da tsumi masu kyau da ingancin suma, Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma suka shiga na 10k kinada package din 5k Idan kin kawo mutun goma suka shiga na 5k kinada package din 3k. Zuzeam ventures 08144015291
******* Doctors din guda biyu na masarautar tin tsawon shekaru masu dan dama da basa karban kowace haihuwa sai ta asalin Matar sarki qananun su ne suke karban haihuwan imebētis amma Ayau sune sultan da kansa ya bada sakon umarnin kiransu amsar haihuwan wishmansa Shiyasa Haile bata samu damar samunsu a masu karban haihuwant wannan Karan koda kuwa Ana iya samun damar dan aike ya fita a lokacin naqudar to ba samunsu zatai ba sbd suna Akan wishmar BOYEM,
Ajiyan zuciya suka ringa saukewa suna kallan babyn Wanda kukansa mai karfin gaske ya cike dakin da bangaren gabaki dayansa harma daga wajen GHAZ chambers Ana jiyo kukan nasa.
Ita kanta tenya ajiyar zuciyar ta ringa jerowa ba kakkautawa kafin ta bude Baki da karfi tana cewa
‘MashaAllahhh,Barakallahu laka fi’l-mawhubi lak,wa shakarta’l wahib,wa balagha ashuddah,wa riziqta birrah. ALHAMDULLILLAH YA ALLAH’ ta qarasa fada da karfi tana karban lallausan showel fari tas hannuwanta na rawa ta dunqulesa tana dawo da kallanta Akan Ayanah cikin rawar murya tace
‘Allah ya qara miki Nisan kwana da lafiya tareda albarka me dorewa UWAR BOYEM GABAKI DAYANTA TA YANZU, UWA GA ZAKIN BOYEM, UWAR MAZAJEN BOYEM, UWAR ME BOYEM NA GABA.
Sakinah rawa jikinta ya dauka da karfin gaske tana juyowa da karfi ta tsira wa babyn hannun tenya din ido bata ko kyaftawa.
Ayanah ma duk da bata hayyacinta bata dawo daidaiba bude jajayen idanunwata tayi zufanta na qaruwa ta zubawa hannun tenya ido tana kasa gasgata da gaske namijin da qasar BOYEM da qasoshi da dama suke jira shi ta haifa,
Hawaye ne suke kokarin ciko idanuwanta na fargaba tsoro da tsananin tausayi da son danta da rikicin qasar gabaki dayanta yake jiransa.
A daidai wannan lokacin bangaren HAILE shima wani Tiriri ya dauka na samuwar cikar Buri dan kuwa itama namijin ne ta haifa Wanda ya sakata kokarin tashi da kanta dan isar da sakon haihuwar ‘da namijin ga sultan tin kafin Ayanaah ta haihu sbd farin cikin samun cikar burin shekaru ya mantar dashi Ayanah da kowa menene zata haifa.
Hanata Miqewa likita ke kokarin yi tareda yarta harma da fetto sbd jinin da babu sosai a jikinta kuzari tareda azabtuwar datai sosai tayi pale sosai suka dage cikin tsananin kulawa da kauna dan komai ze iya faruwa da ita idan ta tashi tsaye amma Sam taqi yadda da hakan rungume take qam da babyn tana kokarin Miqewa zuciyarta a rufe bata Jin ko zata rasa ranta zata iya jiran Ayanah ta haihu batareda sultan yafara sanin ta haifa Zakin qasar BOYEM ba,
Miqewa tayi suka miqe dukansu tareda riqeta zuciyoyinsu da hankalinsu duka a tashe da mugun tsoro da tashin hankalin hukuncin laifin da suke kokarin aikatawa na Binta su fita,
Wani jinin ne ya kuma gangarowa daga qafafunta Wanda ya saka hankalinsu sake tashi dake sauri bayi biyu sukai saurin durqusawa suna goge mata jiki da towel me dumi da suka matse daga ruwan Zafin da aka goge mata jiki gabaki daya.
Sake shiga tashin hankali su fetto da likitar sukai harma da ‘yarta sbd hatta ita Haile din hukunci zai iya hawa kanta dan babban tsatsauran dalilin daya saka wannan tsaurin yake a masarautar lokacin haihuwan kwace mace shine hana cutatar da kowace jaririn da zaa haifa ko uwarsa kokuma sace jarirai musayarsu dan haka baa yanzu wannan dokar take ba tin asalin asalin kafa masarautar yake.
Jiri ne sosai da rashin isashen jini ke Neman zubar da ita amma a haka suka riqeta dan suma bazasu taba son imebetin ta haihu batareda sultan yasan an samu magajin BOYEM ba,
Taku daya biyu sukai suna daga qafafunsu su hudun a tare zasu fito dakin wata kakkarfar sautin qarar da baa taba kada wa ba tin tsawon shekarun da sultan YASAR ya hau mulki bace ta ratsa kunnuwansu cikin sanyi da rikitaccen yanayin daya saka dukkaninsu Sakinta cikin mugun firgita da ficewa hayyacin dan kuwa sautine dayake fadawa BOYEM da duniya gabaki daya MAGAJI kuma ZAKIN BOYEM ya sauka a duniya tsohuwar imebeti sabuwar wishmah AYANAH GHAZ ta haifosa.
Shigar sautin kunnuwan Sultan YASAR da gabaki daya manyan masarautar boyem a lokaci daya suka zube qasa suna yiwa Allah sujjada batareda ma sun sani ba,
Haile kuwa Numfashi daya ta fitar bugun zuciyarta ya tsaya cak sakamakon sautin sakon daya ratsa kunnuwanta ya Harba cikin kwakwalwanta ta zube a gurin jaririn hannunta yana subucewa daga hannunta zuwa qasa,
Cikin wata gaggawa da tashin hankalin dayake Ninkuwa Akan mugun shock din dasuke ciki fetto ta tare babyn koina na jikinta na rawa da kakkarwa,
‘Yarta Aslam ce tayi saurin tarota jikinta itama jikin nata yana rawa sosai da firgici tareda tsananin tsoro sukai qasa har ita har mahaifiyar tata sbd batada karfin da zata iya riqeta tinda jikinta a sake yake kaman babu rai a jikinta,
Dr Kadee ce tayi saurin bin Aslam din qasa tana tayata riqe Hailen itama jikinta rawa yakeyi da firgicin yanda duk wahala da azabar da suka sha ta tashi a iska labarin haihuwan Ayanaah ghaz ya fara shiga kunnuwan sultan YASAR da qasar BOYEM harma da duniya gabaki daya.
Fetto babyn ta rungume jikinta tareda budesa sa sauri taba duba idan yana raye babu abinda ya samesa daga faduwar taga lafiyarsa kalau sedai tinda aka haifesa baya wani kuka saida ya fadin ya fasa kuka sosai Wanda ya sakasu sauke ajiyan zuciya suna tattalar HAILE din dan maidata shimfida a bata taimakon gaggawa.
***A daidai wannan lokacin kuma sautin qarar ya ratsa kunnuwan Zuhrah dake Zaune daqyar sbd azaba da rashin lafiyar da kowace gabar jikinta keyi a cikin wani irin kurkuku mara Kyan gani,
Tinda aka sanar da Masarautar kaf cewa imebeti AYANAH GHAZ na naquda ta tashi Zaunen idanuwanta dake ciwo basa gani sosai ta bude su tareda daga Kai sama ta qurawa sama ido tafara jerowa Ayanah da abinda zata haifa addua jikinta na rawa tana fadawa Allah adduarta Akan yar uwarta Bata Dena addua da fadawa Allah ya tsayu Akan rayuwar babyn ayanah dinta ba har saida sautin ya ratsa kunnuwanta Wanda ya sakata rufe idanuwanta ahankali tana silalewa qasa kwance tareda fashewa da Wani irin kuka mai ratsa zuciya tana gode wa Allah da bai karbi ran ayanarta gurin haihuwa hakama wata irin tsananin kewarta da kaunar son ganinta a lokacin ta saka sabbin hawaye gangaro mat a tana Jin tsananin so da ganin abinda Ayanah ta haifa musu ta rungumesa a jikinta taji duminsa tareda sakawa rayuwarsa albarka da fada masa sun yafe masa ita da ‘yan uwanta da basa raye sbd kaddarar haihuwansa a jinin BOYEM ce ta lalata tasu rayuwar da babu gyara a cikinta har abada.
Rufe idanunwata tayi hawayen data manta rabon datai yi su sbd kuka ma kansa ya gujeta sai Ayau din datake Jin kewa da tsananin son Ayanah da ‘danta suna ratsata.
****A kuma wannan lokacin ne sultan YASAR ya dago daga sujjadarsa ya daga hannu sama yayiwa Allah godia yana jerowa dan nasa addua me tsananin karfi,
Danyen zinari aka fara fitowa dashi a tray mai shegen kyau aka fara kyautarsa a matsayin tukuici hakama duka manyan dake cikin farin ciki mai tsanani da annashuwa suka fara gabatar da tukuici ga AYANAH GHAZ da kyautar data ringa girgiza mutane da tabbatarda Ayau burin qasar BOYEM ya cika na shekaru,
Ko da tenya ta fito daga babban kofar fitowa bangaren Wishmah gabaki daya wasu irin securities ne da bayin da zasu rakata har zuwa fada Sbd Mai BOYEM dayake hannunta.
Gabaki daya Wani irin Juyawa tenya taji kanta na yi sbd tarin bayi da securities da suka cika hanyar dan kawai rakiyar Magajin BOYEM ga mahaifinsa.
Kafafunta sanyi sukeyi mata a duk lokacinda tayi Taku daya na tafiya zuwa fadar mai girma sultan YASAR dauke da jaririn dayafi kowane ‘da daraja a qasar BOYEM yana dunqule cikin farin lallausan bargon daya babu hannun Wanda ya shiga duniya Bayan nata saiya shiga hannun mahaifinsa kafin ma ya shiga hannun mahaifiyar data haifesa,
Kai tsaye hanyar fada suka isa babyn na rungume a jikin Tenya data ke Jin sabuwar duniya ce yake kafuwa a BOYEM daga lokacin da ‘dan nan ya gado duniya.
Isowarsu bakin kofar fadar da Wani irin tsit akai tareda wangale mata kofa Sauran securities da bayin suka tsaya daga kofa ta sako kafarta ta dama ta shigo tana Takawa cikin nutsuwa tana nufar karagar mulkin BOYEM da sultan yake Kai idanuwansa masu tsananin kyau da kwarjini suna kan hannuwanta biyu dake rungume da hasken dayake tsaya zuciya da idaniyarsa,
Dukkanin Wanda yake cikin makekiyar fadar da Taku ne me yawa kafin Ka isa karagar daga bakin kofa kowa idanuwansa Akan hannun tenya yake suna fidda silallan zinari a gabansu suna ajiye wa qasa inda duk tenya ta taka ta wuce matsayin tukuici gareta ita kanta Wanda hakan ke saka kafafun tenya rawa da farin cikin datake Jin kaman zata some tin daga lokacin da magaji ya shiga hannunta.
Ko data isa gaban sultan YASAR a hankali ta zube Akan gwowowinta tareda daga masa magajin BOYEM tana miqa masa kanta a qasa tana zuba masa Wani irin Kirarin daya saka fadar dama masarautar yin tsit sautin muryanta me karfi ce kawai taje tashi tana amsa Amon kirarin datake wa sultan YASAR da magajinsa.
Wasu manyan sarkokin zinari ne aka fito dasu Ana tsayawa gefenta dasu Sultan da hannuwansa ke rawa miqawa yayi ya dauki babyn dake kan hannunta yana ambatar sunan Allah da sautin daya saka kowa maimaita sunan Allah din,
Ita kuwa tenya sultan na dauke babyn daga hannunta aka fara dora mata sarkokin zinarin tukuicinta tayi qasa da Kai tana zubda hawayen farin cikin samun cikar Buri.
Addua da huduba sultan ya daga babyn yayi masa tareda rungumesa jikinsa tsawon mintina uku kafin ya dago idanuwansa da kwarjinsu ya sake cike niimar gurin ya bude Baki da sautin daya saka tsigar jikin duk Wanda yake gurin tashi ya ambacesa da sunan daya saka masa Wanda duniya zata kirasa dashi, ‘LEUL NU’AB ALMAZZ YASAR BOYEM’
#MAMUH
HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070
Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali*_HAYATEEM_* Mamuhgee
39 *_ZUZEAM VENTURES_* 08144015291 Bononza bononza Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me kamawa insha allah -Da 5k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani, -Da 10k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba, wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online Dan haka duk wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri kafin ta kare Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah Idan kinada 3k ma zaa baki ciccibi kawai sai gari da tsumi masu kyau da ingancin suma, Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma suka shiga na 10k kinada package din 5k Idan kin kawo mutun goma suka shiga na 5k kinada package din 3k. Zuzeam ventures 08144015291
******* A take gabaki daya fadar kowa ya miqe tsaye suna sakawa LEUL NUAB albarka cikeda wata irin girmamawa da shauqi Su kuwa bayi gabaki daya cikin fadar dana kofa da waje zubewa sukai qasa kawunansu a qasa suna masa adduar securities ma qame wa sukai suna sare maza da addua.
Tenya da gashin jikinta ke tashi yana qarawa bude Baki tayi ta ringa jero sabbin kirari da addua kafin sultan ya maida mata Almazz din hannunta ta amsa Bayan ta miqa tukuicinta ga bayinta kafin ta miqe tsaye A lokacin ne aka fara fitowa da wasu sabbi trays masu dauke da sarkokin da suka sakata rungume LEUL da kyau sbd rawan da hannunta yakeyi,
Tukuicine ga Wishmah AYANAH GHAZ na hasken idanuwan da ruhin data basa Wanda zuciyarsa bazata taba mantawaba da wannan feeling din da itace tafara basa shi dan kuwa koda zai samu wani haihuwan namijin a gaba to tabbas wannan feeling din na farko na daban ne daya bude zuciyarsa ga abubuwa da dama ya kuma kulle wasu kofofin dake zuciyar tasa da dama.
Bayin tenya dana wishmah dinne suka fara shigowa a hankali suna jeruwa suna daukan tukuicin Ayanah Wanda ya ringa fitowa daya bayan daya daga masu boyem dake cike a fadar harma da wainda ke isowa a lokacin da securities dinsu dan samun raya farin cikin lamarin batareda bata lokaci ba,
Tukuicin MARAKI ne itama ya iso a lafiyayyan tray din silver mai kyau an rufesa da wani golden kyalle mai kyau da daukan ido itama set din sarkar kafa ce data Kai sai sarkar hannuwa biyu duk na gwal masu kyau marasa nauyi,
Karba akai Bayan ansanar daga inda kyautar ta fito take bayi suka zube suna miqa godia ga jakadiyarta data kawo sakon tareda bayi biyu.
Tarin kyautar isowan LEUL duniya harya fi na mahaifiyarsa da aka bata tukuicin haihuwar sa dan kuwa shi haka ake zuba silallan zinari a cikin kyautar da ake masa kaman baa san zafi da ciwon su ba tamkar abin banza,
Shiru babu dan sakon Haile na miqa taya Murnarta ga sultan bisa ga wannan gagarumin cikar burin da babu kamarsa da Allah ya cika masa,
Tenya data matsu a koma da LEUL gurin mahaifiyarsa ta sakasa a jikinta itama taji duminsa zuciya da ruhinta su samu sassauci shima ya samu shiga jikin mahaifiyar data haifesa duminta ya ratsashi Miqewa tayi tana sake godia suka juya zasu fice tareda tarin kyautitikan da zasu sauya rayuwarsu da duk ahalin da zaa haifo a zuriar su,
Taku biyu tayi aka qwalla sanarwar shigowan me isar da sako daga bangaren Haile dan haka take tenya ta daya cak sbd dole ne tsayawan kowa idan zaa isar da sakon masu boyem,
Fetto ce ta sako Kai a cikin fadar kafarta ta dama itama ta fara sako wa a cikin fadar koina nata rawa yakeyi amma ta kanne zuciyarta babu abinda take tsananin marari Bayan isa gaban sultan ta isar da labarin haihuwan magajin sa daga Haile datake matarsa ba imebeti ba dan kuwa a tsatsaurar dokar boyem matiqar akwai ‘da namiji daga Mata to ‘dan imebeti bazai taba zama magaji ba dan haka da confidence mai girma ta tinkaro tsakiyar fadar dauke da farin showel itama a hannunta babyn dake ciki na kwance A ciki yana bacci hankali kwance.
Tenya kafe idanuwanta tayi a hannun fetto din zuciyarta na dan bugawa da tinani masu tsauri da girma Kala kala sbd idan idanunwata suna gani daidai baby ne a hannun fetto din Wanda da alama shima baa jima da haihuwansa ba,
Gabaki daya wainda ke fadar tsaida idanuwansu Akan hannun fetto sukai cikeda mamaki da shiga tinanin ko yan biyu Ayanah ta haifa Sai yanzu Dayan ya fito to amma ganin jakadiyar HAILE kuma sako daga bangaren Haile akace ya saka kowa aje tinanin yan biyu aka haifa.
Fetto na isowa tsakiyar fadar me girman gaske zubewa qasa tayi ahankali kanta na qasa ta daga babyn cikeda kulawa da girmamawa me girma tafara zubo masa kirari kafin daga karshe ta sanar dashi queen HAILE ta sauka awa daya da mintina arbain da tara da suka wuce Wanda sakamakon cikin datake Reno ne ya sakata karban hutun zuwa tiraka kuma tayi hakan ne sbd kebe kanta ta samu jinya da Renan ciki mai nutsuwa kuma a cikin yardar Allah ta haifo asalin magajin boyem.
Da tsananin mamakin daya dakatar da komai kowa ke kallan hannun fetto din shock na kama kowa,
Tenya ma wani irin dum taji kunnuwanta sunyi ta rungume LEUL da karfi kirjinta tana kasa dauke idanuwanta Akan hannuwan fetto zuciyarta na nauyi da tsananin mamaki da tashin hankalin maganar fetto din kafin ta maida idanunwata Akan sultan YASAR da shima shiru Yayi idanunwansa Akan fetto tsawon seconds kafin ya maida idanuwansa Akan babyn hannun nata ya kallesa yana mamaki mai tsananin daya dan bayyana.
Tsit koina da kowa yayi Ana rasa abin fada sbd magana dai a Kai tsaye take babu wani kwana kwana kowa ya fahimci komai da fetto ta fada babu abinda kowa zaice bai ji daidai ba kokuma Neman karin bayani akai Kai tsaye itama HAILE magaji ta haifarwa Masarauta.
Sultan da yayi shiru yana kallan babyn kawai suke jiran bayani daga garesa Wanda shima kai tsaye yaji komai daidai ba buqatan kowace tambaya Akan qarin bayanin komai,
Mintina aka share kafin sultan ya sauke Numfashi me sanyi tareda dauke ajiyan zuciya mata sauti zuciyarsa na ratsuwa da wani sabon farin cikin samun wani hasken idanuyar da baima San dashi ba dan haka hannuwansa ya miqa a natse cikeda kulawa da soyayya mai karfi ta uba ga ‘dansa ya amshesa tareda rungumesa a jikinsa na mintina shima yana masa addua kafin yayi nasa huduba ya daga sa sama ya ambacesa da,
‘LI’ULI ASIM YASAR ALMAZZ BOYEM’ (prince Asim yasar almazz boyem)
Take kowa ya maimaita sunan suna saka masa albarka tareda addua duk da baaji shauqin na ratsa jini da kwakwalwaba kaman farkon amma shima sunyi Murna sosai da kasancewansa sabon prince din boyem hakama yau rana ce mafi girma da tarihi tinda aka haifar musu jaruman babys biyu a daya rana.
Kyauta da tukuici aka fara fiddawa Ana bawa fetto itama sedai kasancewan baa San da haihuwan ba bata samu kyauta irin wadda tenya ta samu ba sultan kuwa kyautarsa da tukuicin sa daidai iri daya yayi da wadda yayiwa NU’AB,
Cikin karfin Hali da dake wani zuciya fetto ta karbi ASIM tareda dagasa tayi masa kikarin daya saka kowa yin tsit dan kuwa Kai tsaye da asalin magajin sarki ta kirasa bayan sultan ya riga ya Ambaci NUAB da magajin BOYEM.