Kenza eBookz

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 36

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 36

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 36: Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 36. Da sauri baiwarta daya data taho da ita tayi…

4,500 words

Da sauri baiwarta daya data taho da ita tayi kanta tareda tareta tana kokarin ambatar sunanta amma ba damar hakan dan haka riqeta kawai tayi da sauri tana hanata qarasa zubewa jikinta yana rawa sosai sbd tsoro da fargaban halinda suka ga tana shiga dan kuwa da gasken gaske mummunan balain da masifar da kunnuwanta suka ji mata dauke jinta da ganinta yayi tareda dakatar da kwakwalwanta daga aiki dan haka jikinta ke wani irin rawa yana qarawa tana kokarin bude baki tayi magana amma bakin nata juyewa yake kokarin yi sbd wannan shine shock na karshe da rayuwarta ta samu wanda yake tabata tana ji gefenta daya na kokarin kasawa dan haka ta fara kokarin yunqurawa da karfi ko zata mutu ko rabin jikinta ze dena aiki saita tabbatarda ta kawar da bahar kaman yanda ta kudurta idan ta aikata lahira zata san waye ya hau wannan mulkin da shine abinda take ganin tazo duniya nema, Koma waye a wannan daren ya karbi mulki matiqar ba Asim bane wlh bazata taba shaqar numfashi me karfi ba saita fara kawar da sultan daga duniya kafin ta tarwatsa mulki da masaurautar boyem gabaki daya.

Wani irin mummunan jan da baida kyan gani idanuwanta sukai hannuwanta da kafafunta na wata irin rawa da zufan gaske wanda yake tsiyayo mata ba kakkautawa ta ta miqe tsaye tareda miqa hannu aka saka mata wata mummunan karamar wuqar da batada kyan gani ta riqeta da kyau a hannunta datake jin yana kasawa sbd paralysed din gaske take neman kamuwa da shi dan yanda jininta yake hauhawan gaske yana kokarin harbawa cikin kwakwanta da zuciyarta dake bugawa da mummunan karfin gaske.

Jan da idanuwanta sukai har wasu hawayen dake bayyane da tsanani tsananin baqin ciki tsagwaronsa da tashin hankalin daya fiddata hayyacinta ta bude baki kai tsaye muryanta na rawar tsananin baqin ciki me girma dayake sake kumbura zuciyarta tace

'Duk me rai dayake bangaren nan kada abar kowa da rai,inason kowane bango na bangaren nan ya qawatu ya koshi da jini,kada rai ko daya ta fita.'

Tana fadar hakan ta daga kafafunta dake rawa basaji koina jefawa sukeyi tayi gaba tana saka kai a palon wanda baiwar dake bakin kofar daga ciki kai tsaye kafin tayi motsin komai ta ratsa wuqar hannunta me kaifin gaske maqogoronta wanda take wani irin jini ya feso da karfi har yana bata fuskarta gabaki daya amma bata tsaya ba ta zare wuqar da karfi yana wucewa ciki idanuwanta a tsananin rufe hakama zuciyarta a rife kaman yanda kwakwalwanta ta gama rufewa ruf.

Wainda suke bayanta suma ba imani suka hau cika umarnin data basu suna kashe duk baiwar da suka hadu da ita a bangaren babu imani ko tausayi ko daya a fuska da idanuwansu.

Asim dayayi mutuwar tsaye tin lokacinda sautin ya sauka a cikin kunnuwansa yana ratsa zuciya da kwakwalwansa shima haka ya ringa jin ganinsa na kokarin daukewa da jinsa kafafunsa kaman wanda aka saka kafa aka kwashe haka ya zube a gurin mummunan jiri na dibansa daga zuben a qasa kawai komai yake ganin yana juyawa dashi numfashinsa na kokarin daukewa zufa na gangarowa ta kunnuwansa ciki da waje,

Salman dayake cikin mummunan shock din abinda yaji din shima da tashin hankali me tsananin gaske na harbin da daman shine ya fara Girgiza duniyarsu da rikitar da ita zubewa qasa yayi tareda kokarin Asim dayake wani irin layi daga qasan dayake a zube kan gwiwowinsa,

Jini ne ya fara gangarowa daga hancin asim din me kaurin gaske da yawa wanda ya saka Salman sake shiga wani irin mummunan tashin hankali jikinsa na sake daukan wata irin rawa,

Kokarin sake kamosa yakeyi yana kasa goge masa jinin a daidai lokacin soldiers din masarautar suka iso gurin da makamansu suka bude tasu wutar data saka su aleey sake bude tasu wutar aleey ya bude baki da karfi yana bawa yaransu umarnin kada su saurara matiqar ba Queen din su ce ta dawo hannunsu ba.

Hakan daya fada tamkar ya zubawa wutar dake cikin zuciyoyin nasu soldiers din fetur ne dan kuwa su abinda suka iya kenan hakama matiqar wani abin ya samu tasu princess din da seconds da suka wuce ta koma queen ta shiga hannunsu ba a shirye suke da cigaba da bude wutar da zata qawata masaurautar boyem da fresh jini me dumi.

Irin wutar da ake budewa ta saka salman sake shiga mummunan tashin hankali yaci gaba da kokarin tada asim din ko jansa su bar gurin dan kuwa matiqar yaran LEUL din suka shigo suka samesu bazasu bata second daya ba batareda sun fasa kawunasu da bullet ba a banza dan haka yake gaggawar jan Asim din shima yana wani irin zufan mafi girman tsautsayin daya kawosu.

Jan Asim din yafara yi zufansa da rawar jikinsa na qaruwa gashi sun riga sun shigo baisan ta inda zasu fita ba dan wutar gaske ake budewa wadda qararta ya saka komai na duniyar baka ji bayan wata irin jijjiga.

Maa sakinah dake dakin da ayanah take a sume ana kokarin ganin ta farfado kai da kawo takeyi cikin wani irin zullumi da fargaba tareda rashin nutsuwan zuciya me tsananin gaske datake ji dan har wani rawa hannuwanta ke yi,

Kallan ayanah ta juyo tayi taga likitoci biyu ne a kanta ga tenya itama data dawo da ita sai kaida kawon takeyi sun kasa cewa juna komai sbd babu wanda yake cikin hankalinsa,

A daidai wannan lokacin ne sautin qarar sanarwar sabon sultan ya ratsa kunnuwansu wanda ya saka kowacensu dakatawa tareda tsayawa cak,

Tsawon mintina kowacensu ta kasa motsawa sbd shock da tsananin tsoron da yasa maa sakinah jin idanuwanta sun ciko da wasu irin hawayen da kafin su sauka kuka me tsananin karfi ya kwace mata sbd tabbatarda 'dan Ayanah ne ya hau milkin qasa me girma kamar boyem ayau.

Tenya ma rawa jikinta ya dauka hawaye masu tsananin zafin gaske suna gangaro mata ta zube qasa tayiwa Allah sujjada sbd ayau burinta dayake qume a zuciyarta ya cika NUAB dinsu ya zama mai mulkin boyem, Duk akan takurawar sultan ne sun tabbata amma ayau din ranar da dukkaninsu bazasu taba mantawa bace harma da duniyar boyem gabaki daya bazasu taba manta wannan daren ba.

Maa sakinah kasa iya hakura tayi sbd a yanzu bahar tafi zamowa a cikin mummunan hadari dan haka kai tsaye tambayar tenya tayi inda suke ko gama fada tenya batai ba ta nufi kofa da sauri ta fice kafafunta na wata irin rawa.

Bangaren haile ta fara nufa da wani irin sauri sedai ko isa bataiba aka dakatar da ita tareda cewa bata ciki,

Hakan dataji shine ya kusan jefo zuciyarta waje dan daman son tabbatarda haile na bangarenta takeyi dan shine zai bata yar nutsuwar bahar dake can tenya dake basu dan tsaro bata nan,

Kai tsaye bangaren sultan datasan NUAB na can bai isa barowaba ta nufa da saurin gaske dan sanar masa akwai yiyuwan bahar na cikin mummunan hadari. #MAMUH #SULTAN LEUL NUAB YASAR ALMAZZ #BEST LOVE #ROMANCE #ROYALTY #BAHAR GHAZ BOYEM #CRAZYLOVE

HAYATEEM novel 700 0022419171 AccessBank maryam sani gummi 09033181070HAYATEEM Mamuhgee

91 Tana isa ba damar shiga sbd tsaro dan haka ta saka aka kira mata kadir shima sbd ansan daga bangaren wishmah mahaifiyar Sultan LEUL take ne dan haka take aka tafi kiransa da sauri.

Tin kafin ya iso NUAB dinne ya fara sako kai yana gaba kadir din na bayansa wanda take securities da bayin dake tsoron bangaren suka zube qasa akan Gwiwowinsu dan bada asalin girmamawa ga sultan LEUL NUAB.

Bai ko kallesu ba akan maa sakina ya sauke idanuwansa da sukai jan da sai da gabanta yayi mummunan faduwa jijiyiyin fuskarsa da wuyansa duka sun fito sbd asalin Bacin rai da tsabagen fushin dayake yawo a kowace jijiyan dake gudanar da yawon jini a jikinsa.

Dan sassauta kallanta maa sakinah tayi sbd ko yana matsayin 'danta shi a yanzu sarki ne na qasa guda, Sarki ne da dubban miliyoyan mutane, Sarki ne da manyan kasashe da dama suke qarqashinsa, Shi sarki ne a yanzu da zai mulki duk wani me rai dayake qasar boyem da zagayenta Shi sarki ne da zai mulki har iyayensa tinda suna qasar,

Bayani tayi masa wanda baice komaiba kai tsaye ya wuce idanuwansa na tsanantuwa da halinda suke ciki yanajin dukkanin abinda yake ji a xuciya da gangar jikinsa yana qaruwa sbd zata tabbata ne a safiyar goben dole akwai wainda zasu tafi a maimakon tasa matar.

Maa sakinah bin bayansa tayi zuciyarta na sake tsananta rawa sbd qarar harbin datake jiyowa wanda har kayan cikinta rawa sukeyi sbd jin abinda bata taba ji ba.

Yana doso gurin aleey ne ya fara ganinsa take suka riqe tasu wutar wadda ta saka sauran suma dakatawa tin daman kowa kariya yake kokarin bawa nasa bangaren.

Gabaki daya gurin dauke wuta yayi bayyanar sultan NUAB da kansa a gurin dan haka take kowa ya bude sun ja da baya tareda sauke kawunansu a qasa.

Baice komaiba bai kuma tsayaba hanyar isa bangaren ya nufa kai tsaye aleey da mutum uku suna bayansa a shirye da bindigoginsu sbd ihun da suke jiyowa daga ciki yana tashi.

Salman jin harbe harben ya tsaya ya sakasa shiga sabon mummunan tashin hankalin daya qarasa rikitasa gabaki daya yana cigaba da jan Asim dan su samu gurin boyewa dan tsira sbd gabaki daya Asim din ya zama kaman gawa baya motsin komai idanuwansa a bude sai jini dayake fita hancinsa har lokacin,

Qara ce take sake tashi sosai a bangaren ta mata cikin tsananin neman ceto wadda tana ratsa kunnuwan Asim ya dago a hankali yana kallan hanyar qarasawa can qurya inda matan suke ya bude baki da sautin daya fito daqyar yace

'Bahar,Bahar,Bahar na cikin hadari.'

Miqewa yafara kokarin yi a rikice jikinsa na rawa tamkar mara hankali yabi hanyar da wani irin gudu kafafunsa na neman kifewa yayi ciki.

Salman da yake neman zarewa sbd masifar dayake hango musu babba kiri kiri bin Asim din yayi da sauri shima kafafunsa na rawa da wani irin tsallen tashin hankalin qamshin mutuwa daya fara jiyowa.

Suna shigewa NUAB shima yana sako kai aleey na kallan jini daya fara gani a gurin cikin tsananin mamaki yana fidda dayar bindigar dake jikinsa ya hada biyu a hannunsa.

Haile ma da idanuwansu suka gama rufewa kai tsaye dakuna suka fara bi suna banka kokafin da karfin gaske suna kashe duk ran da suka hadu da ita wanda ya rikita bangaren gabaki daya da wani irin ihun tarin bayin dake bangaren masu dan yawa suna gudun neman tsiran da babu hanyar fita ganin kisar da ake musu ta rashin hankali da imani.

Leylah da Bahar da gabaki daya bayin ma dake bangaren daman a cikin matsanancin tsoro da tashin hankali suke na irin harbe harben dayake daga wajen bangaren tin farko shiyasa su sam basu ma samu hankalin jin sautin karar daya tashi ba,

Bahar da bata taba jin karar bindiga ba a rayuwarta wani irin matsanancin tsoron da bata taba shigaba ta samu kanta tana shigewa bayan gadon dakinta ta boye tareda rufe kunnuwanta da duka hannuwanta biyo koina jikinta yana wata irin muguwar rawa zuciyarta ta gama tsinkewa da bugawa idanuwanta sunyi jajir harma bata iya gani dakyau dasu zufa ne me tsananin gaske take fitarwa tareda ficewa hayyacinta.

Leylah ma cikin tashin hankali jikinta na rawar da bata taba shigaba tayi karfin halin fitowa jikinta na tsima,

Jinin datake gani kusan koina ne da ihun dayake tashi me tayar da tsikar jiki na bayi da masu kulawa dasu dake gurin ya sakata ja baya da karfi cikeda matsanancin tsoro da tashin hankalin da bata taba sanin akwai ba ta juya da gudu jin ihun yana sake gauraye koina.

Baya ta koka inda ta fito da gudu kafafunta na neman kifewa a rikice ta wuce dakinta bata sani ba tana isa dakin dayake na karshe gabaki daya ta fada,

Tana fadawa ciki taga babu kowa hankalinta ya ninka tashi gashi bazata iya sake fita ba sbd yanda komai na jikinta ne tsananta rawa tsoronta na tsananta sosai shima.

Kuka ta fasa me rikitarwa tana nufar bayan gadon dakin itama zata boye tana fadawa da karfi idanuwanta suka sauka akan Bahar wadda idanuwanta ke rintse da karfi hannuwanta na toshe da kunnuwanta komai na jikinta na wata irin rawar dake nuna bata hayyacinta cikin mummunan firgici take.

Tsallaketa leylah tayi komai na jikinta itama yana rawa sosai ta wuce qurya ta durqusa itama tareda qanqame jikinta kukanta na qaruwa sosai ta saka hannu tana rufe bakinta da sauri jin yanda aka banko kofar dakin da wani irin karfin gaske.

Wasu samudawan marasa imani biyu ne a gaba gurin shigowan bayan sun bankewa haile kofar dakin kafin ta shigo komai na jikinta itama rawa yakeyi gabaki daya ta zare takejinta gawa kawai zata maida bahar ta samu nutsuwa dan haka a haukace ta nufi toilet ta banka kofar da karfi tana fadawa ciki ta duba babu kowa.

Fara birkita dakin da nema sukai cikin rashin hankali daidai lokacin Asim ya fado dakin a haukace bayaji baya gani ko gabansa Cikin mummunan tashin hankali ya bude baki zai ambaci sunan mameen tasa salman yayi saurin rufe masa baki sbd baa taba zuwa aikata laifi irin wannan ayi magana sbd abinda zai iya biyowa baya.

Ture hannun salman yayi kokarin yi cikin tsananin tashin hankalin abinda idanuwansa suka gano masa a hanyar koina na bangaren wanda duk aikin mahaifiyarsa ne.

Bahar yake son bude baki ya tambayeta idan batai mata komaiba amma salman ya saka dukkanin karfinsa ya hanasa magana wanda yafara kokarin kokawan kwacewa amma haile tayi alaman kada ya kuskura ya bari Asim din yayi magana dan jikinsu duka ya basu akwai mutum a dakin.

Samudawan datazo dasu din ta kalla ta bude baki da sautin da bame ji idan ba su ba tace a tabbatarda mutuwar ko waye a dakin dan tinda bata ga bahar koinaba ta tabbatarda nan ne dakinta kuma tana ciki.

Bayan gadon Daya daga cikin yaran nata yake kokarin nufa shi kuma salman cikin karfi ya fara jan Asim shi da daya daga cikin yaran suna toshe masa baki da karfinsu suna kokarin ficewa da shi.

NUAB ne ya shigo palon Aleey na saurin shigewa gabansa dan basa kariya tareda nufar dakunan suna fara dubawa,

Ganin irin mummunan al'amarin daya faru a bangaren ba kyan gani koina jini ya saka Jinin NUAB kaiwa matakin karshe na tafasa da konuwa dan haka da kansa ya ringa bankar dakunan da kafarsa yana duba dakunan idanuwansa na tsananta ja hakama jijiyoyinsa.

Aleey kuwa yaransu dake waje ya kira kai tsaye suna dauka yace

'Duk motsin daya fito daga nan ko shadow na dabba ne kona mutum koma waye idanuwanku basu ga kowa ba bayan shadows na marasa gaskia just open fire, I repeat open fire ga duk motsin dazai fito ta kowane bangaren dayake zagaye da nan din.'

'Zan tabbatarda na fasa qashin duk wanda zai fito daga bangaren na bullet dina,wannan alkwari na ne sire'

Kashe wayar Aleey yayi yana qarasa cire imanin dayake idanuwa da zuciyarsa dan fuskantar wanda yayi wannan mummunan aikin da gabaki daya ya gigita NUAB sbd yanda jikinsa ke tsananta wata irin rawar da ko gani bayayi sosai a karan farko tsoro yana bayyana qarara a idanuwansa wanda babu wanda ya taba gani duk duniyarsa.

Su salman na dosowa suka hango NUAB din da mahaukatansa su Aleey da a shirye suke da komai cikin tsananin tashin hankali suka saki Asim suna dawowa da gudun gaske jikinsu na rawar tashin hankalin da basu taba tsammata ba.

Shi kansa Asim din da aka saki Zabura yayi yana juyowa da gudun gaske batareda ya bari kafafunsa sun saki sauti ba dan kuwa harbi guda Aleey zai sako ya fasa kansa ta bayan qeyarsa dan haka da wata irin tata me saurin gaske ya koma shima ya fada dakin rawan jikinsa na tsananta hakama habon hancinsa dayake gangaro jini ya tsananta sbd tashin hankalin da shima bai taba tsammata ba daya diro masa na ganin NUAB,

Cikin wata irin sauti mara fita suka kalli haile da sauri suna cewa NUAB ne da mahaukatansa sun shigo da manyan makamai.

Kallan yanda jikinsu gabaki daya ya dauki rawa tayi zuciyarta na wata irin harbawa ba daidai ba hannuwanta na rawa ta kalli kofar tana jin wani abu na tsaya mata cak a kirji dan kuwa idan har NUAB ne yake nan kenan ba shine ya karbi mulkin boyem ba wani ne daban, Waye ne to? Kokuwa kuskuren da baa taba yi bane akai yau na buga qarar? Kokuwa harbe harben da akeyi ne aka bugawa qarar sabon sultan sbd a dakatar?

Kama hannunta Asim yayi komai na jikinsa yana rawa wanda shima ganin NUAB anan ya tabbatar masa da ba shine ya hau milki ba hakama sunada tabbacin yana ganinsu anan wallahi bazai qara minti daya ba batareda ya rabasu da duniya ba.

Jan haile Asim yayi da karfin gaske suna juyawa suka fice da tsananin gudun gaske suna hana kafafunsu fidda sauti suka fada wata kofar da zata kaisu kitchen wanda ba zaa rasa kofar baya ba a cikinsa su salman na bayansa sun baro mutim biyu wanda haile ta tabbatar musu da ko zasu mutu su kashe mata bahar wadda suka tabbatarda akwai mutum bayan gadon. #MAMUH #LOVE #SULTAN NUAB BOYEM #BAHAR GHAZ BOYEM #SULTAN YASAR BOYEM #AYANAH GHAZ BOYEM #BEAUTIFULLOVE #ROYALTY VS LOVE

HAYATEEM novel 700 0022419171 AccessBank maryam sani gummi 09033181070HAYATEEM Mamuhgee

92 Kai tsaye bayan gadon yaran biyu na haile da aka bari suka qarasa isa idanuwansu a rife dasu kammala aikin su bi bayan su Salman,

Leylah da idanuwanta suke bude tana kuka sosai da bakinta toshe ihu me karfin gaske ta sake tana ganinsu tareda fara wata irin jijjiga tana me karfi tana ja da baya tana qasa nisa a cikin bayan gadon,

Bahar da bata hayyacinta kwata kwata bata motsa ba rawa kawai jikinta yakeyi sosai har lokacin idanuwanta a rinte gam hakama kunnuwanta,

Leylah dake ihun da zai iya basu babbar matsalar da zasu iya rasa ransu suka fizgo da karfi waje tareda daga wata kakkaifar wuqa zasu ratsa cikinta da ita aka bugo kofar dakin da karfin gaske da saida gefenta ya balle,

NUAB ne ya bugo kofar amma bullet din aleey ne guda biyu suka riga NUAB din shiga dakin suka sauka kai tsaye akan wanda yake riqe da leylah daya a tsakiyar goshinsa daya a tsakiyar wuyansa wanda jininsa ya fesu har a gefen fuskar Leylah wadda tayi mutuwar tsaye kunnuwanta na dauke ji sukai dip bata jin komai sbd qarar bindigar daya ratsata da kuma mummunan shock na jinin daya sauka har a jikinta.

Dayan cikin tsananin sauri yakai hannunsa bayan gadon zai sokawa bahar wuqar hannunsa da dukkanin karfinsa sbd koda zai mutu ya cika aikin da yayi alkawarin cikawa,

Ko numfashin daya shaqa na yunkurinsa bai fitarba NUAB ya fizgi wata arniyar wuqar dake soke jikin yaronsa dake gefensa ya jefa masa da karfin gaske wadda lokaci daya ta sauka da bullet din aleey a jikinsa ta sauka tsakiyar jijiyar hannunsa data saka jijiyan ya kewa a take tana feso jini aleey kuwa gefen wuyansa ya harba wanda ya goga wuyan sosai kafin ya harbe gefen kafarsa ta dama itama wadda ta sakasa zubewa qasa take cikin mummunan hali sbd suna buqatarsa a raye.

Qarar harbin ya saka su Asim dake zuba wani irin sauri suna tatata sbd gudun bada sauti tsayawa cak kayan cikinsu na wata irin rawa suka waiwaya bayansu suna kalli kofar da sauri cikin sake shiga tsaka mai wuya kafin suka qarawa tatarsu sauri suna zare takarman duka kafafunsu sbd a yanzu babu abinda suke tsananin tsoro irin fitar sautin takunsu dazaisa asan da su fata kawai su isa kofar baya su fice.

Bahar da leylah a lokaci daya jinsu ya qarasa dauke wa dip sbd dukkaninsu harbin bindiga abu ne da basu taba jinsa live ba har gwara Leylah tana ji a tv da sauran guraran kallo amma bahar ko a tv bata taba jinsa ba dan haka jikinta ya fara kokarin saki komai nata na sakewa tana kasa daukan tashin hankalin daya rabata da hayyacinta.

Leylah ce tayi karfin halin bude bakinta bata cikin cikakken hayyacinta ta furta

'NUABBB' tareda kokarin isa garesa tana neman somewa.

Saukar sautin sunansa da aka ambata a cikin kunnuwan bahar da jinsu yayi qasa ya sakata bude idanuwanta da sukai mummunan jajir basa hayyacinsu tana miqewa daga bayan gadon batareda tasan ta miqe din ba,

Kokarin juyawa yakeyi a zafafe zuwa nemanta ta miqe daga bayan gadon idanuwanta na sauka akansa wasu irin zafafan hawayen da batasan dasu ha suka rufe idanuwanta gabaki daya

Wani irin abu yaji ya caki kirjinsa ya juyo tareda nufota cikin wani irin yanayin da ko gabansa baya gani ganin itace kenan akaso kashewa da bai iso dakin da wuri ba,

Yana nufota ta fasa wani irin kukan daya tada tsigar jikinsa gabaki daya itama ta fito gurin da gudun gaske tayi kansa take ta fada jikinsa yayi mata wata irin rungumar da bai taba yiba a rayuwarsa dan kuwa zagayeta yayi da hannuwansa biyu yana mata kyakkyawar runguma idanuwansa na tsananta jan baqin ciki me tsanani da bacin rai da wutar fushi dake cin jininsa.

Su aleey komawa sukai daga kofa suna juya baya tareda tsare kofar dakin bayan sun janyo wanda suke buqatar sun dauresa tsaf babu sauki a fuskokinsu.

Kuka take fitarwa sosai me sautin dayake sake tada tsigar jikinsa yana tsaye da ita a jikinsa har lokacin yanajin yanda take sake qanqamesa jikinta na tsananta rawa sosai tana qara ficewa hayyacinta,

Kasa cigaba da sauraran kukanta yayi ya dauketa gabaki dayanta yana juyawa ya nufi kofa da ita ransa na tsanantuwa da wata irin qunar da zai iya komai a lokacin ya fice daga dakin.

Babu imani aleey ya saka a jawo wanda suka kaman a qasa suka bi bayansa bayan ya juyo ya nunawa leylah hanya akan ta tafi su fice gabaki daya.

Duk da leylah na cikin matsanancin tsoro da tashin hankali jin tayi komai da duniyar sun tsaya mata cak akan abinda idanuwanta suka gane mata daga NUAB wanda baima tantance waye a dakin ba bayan bayyanuwan bahar a gabansa.

Jin tayi kirjinta yayi mummunan nauyin da gangar jikinta kaman bazata iya daukaba wasu sabbin hawayen tsantsar baqin ciki da radadi na gangaro mata take tanajin abinda tagani a idanuwan su haile suna ji a lokacinda suke dakin dan kuwa kaf dinsu babu wanda bata gani ba.

Daga kafarta tayi daqyar tana takawa jikinta na tsananta rawar baqin ciki da dana sanin kasancewa a dakin tareda baqin cikin nasarar dasu haile basu samuba akan rayuwar bahar din.

Kofa suka nufa aleey ya fara isa kofar kafin NUAB ya iso ya daga hasken daya tabbatar musu da su dinne suna fitowa kai tsaye babu inda NUAB yake tsayawa barin gurin yayi aleey na bayansa da wainda suka shiga dasu.

Suna barin gurin kawai suka fara jin qarar wata wuta da aka bude daga kofar baya babu ji ba gani kawai suna jin motsin alaman takun mutane basu tsa6a komaiba suka budewa gurin wutar da hatta bangon gurin zuba yakeyi ba kakkautawa.

Wani irin harbi ne ya ratsa hannun Asim na dama ya fasa qashinsa take ya zube a gurin yana jan ciki cikin wata mummunar azabar da be taba ji ba ya ratsa da jan ciki cikin qura da duhun ya samu ya tsira yabar gurin dan bazai yadda ya mutu a banza ba hannun mahaukatan Moscow batareda ta tsira ba ya nema bahar wadda yasan a yanzu tana hannun NUAB.

Yana barin gurin haile itama bullet ya ratsa gefen cinyarta jini na zuba sosai haka ta rarrafa ta tsira ta gudu daga gurin tana jan qafar datake ji tamkar baa jikinta ba hakama idanuwanta tini suka dena gani ko tafiyar rabin barin gurin bataiba ta yanke jiki a gurin ranta na kokarin barin jikinta a some.

Cikin tashin hankalin da su aslam basu taba samun kansu a ciki ba daman suka nufo bangaren tinda suka ga mahaifiyarsu bata nan hakama Asim, Harbe harben da suma basu taba ji ba ya sakasu lafewa cikin matsanancin tashin hankali a gurin har NUAB ya fice suna kallo sai ga Asim hannu na tsiyayar jini me yawa ya fito ta hanyar bayansu yana layin jirin dake dibarsa da sauri sukai kansa suna cire mayafinsu suka tare masa jinin da tsananin sauri hankali tashe.

Kokarin barin gurin sukeyi haile ta bullo kafin ta yanke jiki a gurin ba rai,

Ihu meryam ta sake me karfi kafin tayi saurin toshe bakinta tana qarasawa kan hailen itama ta zare sauran rufar dake jikinta ta toshe mata inda jinin ke fita.

Ba shiri suka jasu hankali tashe cikin duhun suka bar gurin dasu suna hana jini ko daya diga a qasa sbd kada a bi sahunsa.

Kai tsaye bangaren Aslam dayake kusa suka nufa dasu suna shigewa ta bada umarnin kada kowa ya shigo bangaren nata batareda izininta ba.

Waya meryam ta dauka cikin rawar jiki ta kira likitansu a boye tareda sanar dashi abinda ya faru dan haka ba shiri ya hado duk abinda zai bugata ya nufo bangaren aslam din cikin duhun daren.

******Duk abinda akeyi Sultan yana jin qarar komai a kunnuwansa amma sbd a yanzu baida hurumi ko daya na shiga ko daukan mataki a matsayin shugaba kokuma me mulkin boyem sedai a matsayin uba ko me bada shawara idan ta kama dan haka shiru yayi a zaune batateda motsawaba a zuciyarsa yana fatar a cikin yayan nasa duka da matansa babu wanda yabi sharrin zuciyarsa yayi abinda zai zama matsala ga rayuwan dukkaninsu.

Har daren yayi tsit aka dena harbin dare ya qara tsalawa koina ya sake dauke motsi batareda anyi sautin mutuwar jinin boyem ba ya sakasa sauke wani boyayyan numfashi me sanyi da nutsuwa kafin ya miqa hannunsa a natse ya dauki wayarsa ya saka kiran wayar tenye.

Babu bata lokaci tenya ta dauki wayar cikeda girmamawa ga tsohon sultan duk da dare ne sosai su kam bazasu iya bacci ba a wannan daren sbd tsimayin dake zuciyoyinsu na shedar da wannan daren na alkhairi a garesu.

Magana daya zuwa biyu yayi da ita ya kashe wayar ya sake sauke ajiyan zuciya a karo na babu adadi bayan saukarsa a matsayin sultan cikin daren tukuna ya miqe a natse cikin kamewa da samun cikakken yancin da ayau zai fara samun rayuwar da zuciyarsa ke tsananin muradi tin daga ranar daya fara dora idanuwansa akan AYANAH GHAZ.

Kai tsaye fitowa yayi batareda yan rakiyar kowaba cikin samuwan cikakkiyar nutsuwan yanci daga mulkin dayake tauye da abubuwan rayuwarsa da dama wanda a yanzu yasan NUAB zai kawo sauyi daga mulkin dayake na takura da rashin yancin kai zuwa mulkin da zai baka nutsuwa da yanci tareda hana kowace irin al'ada me tsananin datake sanadin rayuka da dama.

Kai tsaye bangaren wishma dinsa ya nufa wadda ta farka a daidai lokacin itama jikinta a tsananin sanyaye tana kokarin dawo da tinanin dukkanin abinda ya faru zuciyarta na wani irin nauyi.

Readers Also Read