Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 37
Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 37: Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 37. Shigowansa ya saka gabaki daya bayin bangaren…
4,493 words
Shigowansa ya saka gabaki daya bayin bangaren ficewa kofar bangaren suka tsaya gefe daya a jere har sai lokacinda ya fice.
Tenya da sakinah ma cikin tsananin girmamawa tareda farin cikin kasancewansa ayau tareda ayanah suka fito gabaki daya Maa sakinah ma bangaren NUAB ta nufa cikin daren batareda tsoro ba dan dubo halinda Bahar take ciki.
****kai tsaye yaba baro can bangaren da ita bangarensa ya nufa wanda har lokacin tana jikinsa ta kasa dena kukan matsanancin tsoron data samu kanta a cikinsa.
Bude masa kofar shigewa palon farkonsa akai da sauri cikin nutsuwa yana qarasowa ya shige take aka rufe kofar kuma bame shiga sai gobe nadin sarautar da duniya zata sheda tinda safe.
NUAB na shigewa waya aleey ya buga fada yace KEELA babban wanda shine yake bin aleey a matsayi yace a saki manyan fada sbd nadin sarautar gobe da safe.
Ba bata lokaci kuwa aka sakesu take kowannensu ya fice jiki yayi tsami da sauri suna matsuwan gobe tayi susan waye sabon sultan din na boyem. #MAMUH #BEST LOVE #SULTANS #AYANAHS
HAYATEEM novel 700 0022419171 AccessBank maryam sani gummi 09033181070HAYATEEM Mamuhgee
93 Yana shigewa kai tsaye bai iya ajiyeta bedroom din data sama zama ba sbd bazai taba samun nutsuwa ba gabaki daya jin yake duniya kaf bai yadda da kowa da komai akanta ba dan haka hanyar nasa bedroom din ya nufa da ita har lokacin kukanta me fita a hankali na ji da shedar da balain da bata taba ji da ganiba a rayuwarta bai dena fitowa ba yana ratsa kunnuwansa.
Bude kofar bedroom dinsa da babu wanda wanda ya taba shiga bayan mutum biyu rak masu aikin gyaransa a cikin yaransa ya shige tareda rufewa yana nufar tsakiyar dakin inda lafiyayyan king-size royal bed dinsa yake komai na dakin qamshinsa yakeyi dan kuwa hatta niiman da zaa shaqa a dakin kowace iri qamshinsa ne yake tashi a cikinta hakama sanyin aircon dayake ratsa koina qamshin nasa ne shima kusan yake ratsa koina din dashi sbd komai nasa ya riga ya kama qamshinsa da babu me irinsa a masarautar masu nayan shi.
Zaunawa yayi a bakin gadonsa da ita a jikinsa yana yin shiru a natse idanuwansa na dan lumshewa kadan sbd sautin dayake ratsa kunnuwansa har lokacin yanawa komai nasa illa musamman tinaninsa dayake jin wata irin wuta na cin kirjinsa na iya daukan kowace irin mataki akan wainda suka iya haukatar da kwanciyan hankalinta zuwa ga duka tashin hankalin data shedar.
Ita kanta kasa motsawa tayi a jikin nasa har lokacin jikinta yar rawa yakeyi tana dan sake qanqamesa kukanta naci gaba.
Shiru ba motsin komai ba sautin ko fitar numfashinsu a dakin saina kukanta tsawon mintina sosai a hakan kafin tayi shiru tana sauke ajiyan zuciya mara karfi sbd jikinta daya gama mutuwa da rashin karfi tayi sanyi sosai,
Shi ma shirun ya sake yi har lokacin baice komaib bai kuma motsaba tana rungume a cikin jikinsa tana qamqame dashi,
Bayan tsawon mintina bayan ta dena kukan ajiyan zuciya ta ringa jerowa a hankali cikin sunyi jikinta na qara sakewa,
Fara sakinsa tayi a hankali tana jin nutsuwanta tana dawowa jikinta,
Dago kanta tayi a hankali daga kirjinsa tana kasa kallan fuskarsa ta dan motsa tareda qasara sakinsa gabaki daya idanuwanta da sukai jajir suka kumbura suna kasa kallansa.
Qugunta daya zagaye da hannuwansa masu karfi laushin fata da wata irin dumi ya dan sassauta riqon yana saukar da idanuwansa akan fuskarta data sakasa kasa qarasa sakinta sbd yanayinta yana sake bayyanar da zarewan data kusa yi a halin data shiga.
Shiru tayi ajiyan zuciyarta na kukan datasha yana sake fita akai akai tana jin hannuwansa sun kasa saketa wanda ta kasa doguwar motsi itama tana rufe idanuwanta sbd nauyin idanuwan dana hannuwansa dake rungume da qugunta tana jikinsa sosai,
Dago idanuwanta tayi a hankali batareda ta motsaba tana san kallan fuskarsa amma zuciyarta na hana hakan,
Maida kanta tayi qasa tana son sake rabuwa daga jikinsa,
Sake kallanta yayi yana jin dukkanin motsinta a jikinsa, A natse ya saketa tareda tayar da ita zaune daidai a kan kafafunsa yana qin kallanta sbd zuciyarsa dake wani irin zafi da radadin abinda ya kusan faruwa da ita a daren wanda zuciyarsa ta kasa sakewa ta kasa iya cirewa daga idanuwa,zuciya,kwakwalwan da tinaninsa shiyasa babu sauyi ko daya daga yanayinsa na fushi da tsantsar baqin ciki da bacin rai a daren wanda tabbas bazai mancesa ba sbd abubuwa da yawan da suka faru a cikinsa,
Yanda ya zaunar da ita akan kafafun nasa ya sakata dagowa a hankali jiki a mace ta kallesa sbd jin shiru har lokacin bai iya furta kowace kalma ba hakama hannuwansa tabi da kallo taga jijiyiyin jikinsa duk sun fito alaman jininsa tafasa yakeyi,
Tasan yanada yawan fushi da zafi ga duk abinda aka tabasa akansa amma bata taba ganinsa a irin wannan yanayin ba wanda ya sakata jin jikinta ya sake mutuwa ta dago idanuwanta dasukai mummunan nauyi sbd kuka ta kalli fuskarsa wadda tayi jajir tana kasa dauke idanuwanta sbd shima dagowa yayi a wani yanayin daya saka tsikar jikinta gabaki daya miqewa ya bar idanuwan nasa akanta har lokacin babu wanda ya iya cewa komai a tsakaninsu bare motsawa.
Ahankali ya sauko da idanuwansa zuwa ga wuyanta da jini yake kwance a jikinsa zuwa cikin rigarta daga gefen kafadarta, Fuskarta ya dawo da idanuwansa kafin ya sake maida kallansa akan jinin wanda da alama rauni ne taji wanda itama bata san dashi ba.
Idanuwanta ta dauke akansa a sanyaye tana dorasu akan inda yake kalla da dukkanin jajayen idanuwansa dake qaruwa a lokacin,
Ganin jini a jikinta ya sakata jin kanta ya sara da karfi hannuwanta na dan daukan rawa tsananin tsoro da wata irin firgita na shigarta ta daga hannunta dayake rawa sosai a rikice zata dora a gurin ya kama hannunta da nasa yana hanata tabawa tareda zuba mata idanuwansa cikin wani slow dayake tafasa jininsa,
Wasu sabbin hawayene suka ciko idanuwanta wainda ya kalli cikinsu baya iya cewa komai sbd idan yakai karshen qonuwa a bacin rai da fushi baya magana sam sam.
Hannunsa yakai gurin kai tsaye a cikin wata nutsuwa ya kama rigarta ba tsammani taji ya saukar daga kafarta wanda ya sakata saurin kama hannunsa da tafin hannunta tana dagowa ta kallesa hawaye dake cikin idanuwanta suna gangarowa a hankali.
Bai kalleta ba idanuwansa na kan raunin ya saka hannunsa dayake bayanta ya mannota sbd bayan datai kadan ta manno da kirjinsa sosai ya zagaye qugunta da hannunsa daya tareda qarasa saukar da rigarta daga kafadarta wadda ta sakata rintse idanuwanta da karfi bugun zuciyarta na fita da karfin dayake iya gani a saman fatar kirjinta fara tas datake wani daukan ido.
Jinin ya zubawa ido tin daga inda ya fara zuwa inda ya sauka wanda ya tsananta wani nauyin karjinsa sbd ba raunin dataji jinin wani ne ya dauka a jikinta wanda ya sakasa jin hannuwansa na dan rawar data sakata bude idanuwanta ahankali tana fara saukewa a fuskarsa wadda ya dago jajayen idanuwansa ya zuba gabaki daya akanta yana mata wani irin kallan daya ringa saka bugun zuciyarta qaruwa ta maida kallanta akan gurin wanda itama taga tamkar jinin ne kawai ta daga hannunta dayake rawa ta nufi gurin zata taba ya sake riqe hannunta da karfi yana hanata taba jinin dayake jin yana neman yanke numfashinsa sbd nauyin da kirjinsa yayi sbd tabbatarda jinin a cikin mazan biyu ne da suka tarar a dakin.
Miqewa tsaye yayi batareda yace komaiba ya dauketa kai tsaye toilet dinsa da baya taba iya sharing da kowa a rayuwarsa baya iya sharing toilet da bakwancinsa da kowa tin yana yaro bai taba iya hada gurin kwanciya da kowa ba bare hada toilet,
Ciki ya nufa da ita kai tsaye sbd shi kansa bazai iya saka hannunsa a jinin wanda iya ganinsa tafasa nasa jinin yakeyi ba bare barin ta saka hannunta,
Girman da toilet din nasa yake dashi ya saka suna shiga wani sanyin gaske ya ratsa har zuwa cikin naman jikinta ta rufe ido tana jin wani iri.
A tsakiyar shower ya ajiyeta idanuwansa a rufe ya sakar mata ruwan dumin data ji saukansu a bazata ta ja wani irin numfashi me karfin gaske tana qamqame hannunsa a rude ba tareda tasan tayi hakan ba,
Tin daga tsakiyar kanta da abin rufarta ya fadi tin a farkon shigowansu palonsa na farko ruwan ke zuba suna bin fuskarta suna sauka a wuyanta zuwa kirjinta da gangar jikinta.
Tsaye yake a gabanta ruwan na sauka har a kusan rabin jikinsa shima idanuwansa na kafe a wuyanta zuwa kirjinta da ruwan suke wanke jinin yana sauka,
Akan idonsa jinin ya kama wankewa tas batareda ya saketa ba duk da ruwan sun isheta hakama ya hanata saka hannunta ta wanke sbd zai iya zama makashin gaske idan hannunta ya taba jinin wani.
Ruwa sosai suke sauka a jikinta bayan komai ya wanke tas amma ya kasa saketa cikin wani irin yanayin tinawa da kaman baida cikakken hankali a yanzu ya sakata qwacewa tana fitowa daga ruwan tareda qin kallansa ta nufi inda taga towels dinsa a jere ta ja daya ta fice daga toilet din tana rufe jikinta da towel sbd wani irin sanyin ac daya ratsa har qashinta.
Bata tsaya a dakinba kai tsaye dakin data saba zama ta nufa tana isa dakin cire kayan jikinta tayi sbd wani irin kakkarwan sanyi da jikinta keyi me karfin gaske take tanajin zazzabi na shigarta me karfi shima komai daya hade mata a daren guda ga wani irin tsananin ciwon kai.
Daqyar jikinta na wata irin rawa ta iya zare komai ta saka kayansa da kusan sune a dakin take sakawa.
Bata iya tsayawa busar da gashinta me tsayin gaske dayake a jiqe ba hakanan ta dunqule guri daya a jikinta na rawa sosai.
Acan bathroom din kuwa bayan fitowanta bai iya motsawa ba sbd zuciya ta gama cinyesa ayau tin farkon safiyar babu abinda jininsa yakeyi bayan quna da tafasa har zuwa daren da tsakiyar daren ma da ayanzu yake jin idan bai iya controlling na zuciyarsa ba zai iya zama makashin mutune da dama a daren sbd an wuce dukkanin iyakarsa da baa wucewa a rayuwa.
Tsakiyar ruwan data fita ya tsaya yana samun ruwan na sauka a jikinsa suna dan sassauta zafin dayake jininsa da gangar jikinsa.
Mintina ya dauka sosai abubuwa da dama suna yawo a cikin kwakwalwan kansa gameda rayuwar daya samu kansa a ciki a lokaci daya, Da kuma rayuwar da zaiyi daga daren yau dan zuwa safiyar gobe shine Sultan din da zai mulki qasar daya tsana da dukkanin zuciyarsa,
Zan zauna a qasar daya tsana Zai rayu akan mulkin da shine ya hana mahaifiyarsa 'yancinta na shekaru, Daga gobe zai rayu a matsayin SULTAN LEUL NUAB ALMAZZ batareda ta taba kauna ko raayin hakan ba dan kuwa hakan shine abun da yakewa dukkanin tsanarsa da bai taba sanin kaddara zata kawo sa akan matsayin ba.
Fitowa yayi daga shi sai towel mai haske sosai a qugunsa gashinsa dayake sake har a kafadarsa tsiyayar ruwa yakeyi shima.
Tsayuwa yayi a gaban mirror wani irin sanyi me tsananin gaske yana ratsa shi amma bai motsaba ko kadan sbd hakan yana rage zafin dayake ji a cikin gangar jikinsa sosai wanda yake kaman zai kama da wuta.
A haka ya bude tas kafin ya busar da gashinsa da dryer yayi shirin kwanciya ya fice daga dakin jikinsa a matiqar sanyaye ya nufi dakin datake sbd ayau Rauninsa a kusan bayyane yake. #MAMUH #HOTLOVE #BESTSTORY #2SULTANs #2AYANAHs
HAYATEEM novel 700 0022419171 AccessBank maryam sani gummi 09033181070HAYATEEM Mamuhgee
94 Wata nutsuwa ce ta saukar masa wadda take tattareda sanyi da kawar da dukkanin fushi da hayaniyar kansa tareda sakarwa jikinsa sanyi da kamewa dan haka a natsen ya isa kofar dakin ya bude a natse tareda saka kai a ciki sbd bai hangota akan gadon ba.
Da wata irin kwantacciyar nutsuwa ya qaraso cikin tsakiyar dakin yana sauke kyawawan idanuwansa akanta tana dunqule a kan sofa idanuwanta a rufe tayi baccin wahala zazzabi me karfi yana cin jikinta.
Tsayuwa yayi a kanta tareda zuba mata idanuwansa da suka dan sauya kadan yana kallan gashinta dayake a jiqe a jiqe har lokacin bai bushe wanda ya tabbatarda zai sakar mata ciwo.
Durkusawa yayi a hankali daidai kanta ya saka hannunsa ya taba gashin wani sanyi ya ratsa tafin hannuwansa ya dauke hannunsa ya miqe ya nufi inda dryers na dakin suke bama daya ba ya dauko ya janyo har inda take yafara busar mata da gashin a yanda take kwance batareda ya bari zafi ko iskar yayi mata yawa ba,
Duk abinda yakeyi bai kalli fuskarta ba harya gama ya maida ya dawo ya yaye rufar dake jikinta a hankali ya wanda ya sakata bude idanuwanta a hankali cikin zafin zazzabi ta kallesa batareda ta ce komaiba se motsawa datai zata tashi zaune sbd bata buqatan komai da kowa a lokacin ita kadai tasan abinda take ji a gangar jiki da zuciyarta,
Yunqurawa tayi a matiqar galabaice zata tashi ya dakatar da ita da ta hanyar dora hannunsa a cikin sanyi kan kafadarta ya hanata yunqurawan.
Daukanta ya sake yi batareda hayaniya ba ya nufi gadon dakin ya kwantar da ita ya rufe mata jikinta dayake dan rawa ya zauna bakin gadon tareda rintse idanuwansa sbd a yanzu wata irin damuwa ce me tsananin nauyi ta danne kirjinsa a rayuwar daya samu kansa na matsayin daya hau kan kansa duka a cikin dare daya, Nauyin daya rataya a kansa jin yake tin ayanzu ya danne kirjinsa yana raba gangar jikinsa da wani sashensa dashi aka haifesa.
Mahaifinsa ya yanka rayuwarsa ya datsata a gabansa ya lalata masa buri da dukkanin abinda yayi shekaru yana ginawa a zuciya da rayuwarsa, Mahaifinsa ya wargaza tsarinsa da akidarsa ta rayuwa Mahaifinsa ya tilasta karban rayuwar da babu ita a kundin rayuwar daya tsarawa kansa da mahaifiyarsa.
Numfashi ya sauke me zafi daya fito a natse tareda bude idanuwansa da suka sake sauyawa zuwa ja ya waiwayo ya kalleta ta sake komawa baccin wahala itama.
Zubawa fuskarta datake bayyanar da halin ciwon datake ciki ya dauke idanuwan yana miqewa ya koma kan sofan datake dakin tana facing gadon ya zaune a natse tareda jinginar da bayansa ya dora kafarsa kan daya a natse tareda folding hannuwansa yana sake kwantar da kansa jikin kujeran yana rufe idanuwansa sbd kansa dayake sarawa.
******** Sultan me murabus kuwa a daidai wannan lokacin da shima ya isa har asalin bedroom din ayanah ghaz wadda qamshinsa ne ya fara ratso mata cikin dakin duk da tana cikin mummunan halin tinanin bayyanar halittar data kasance jinin abaas a gabanta batared bayyanarsa ba da shine mahadin karshe na rayuwarta shigowan qamshin namji na uku a rayuwarta wanda sune suke da rayuwa da ruhinta ya sakata rufe jajayen idanuwanta da suke cikin matsanancin halin da zuciyarta take ciki sbd Abaas shine namijin da yafi kowane namiji a rayuwarta kafin 'dan ta NUAB da mahaifinsa Sultan yasar.
Rufe idanuwanta yayi daidai da sako kansa dakin a cikin wata irin nutsuwan da bai taba samu ba a tsawon shekarun mulkinsa ba,
Idanuwansa masu kyau da haske saukesu yayi akan ayanah ghaz wadda nata idanuwan suke rufe tana jin zuciyarta na kokarin bugawa ya tako a natse har gabanta daidai nan ta miqa hannu zata dafe kirjinta dayake wani irin radadi.....riqe hannun nata yayi da nasa a cikin wata irin nutsuwa da samun cikar burin dayafi kowane burinsa a duniya yana kafawa hannun nata daya riqe da nasa idanuwansa batareda ya kyafta ba tasa zuciyar na wani irin ciwon daya debi shekaru yana hadiyewa shi kadai.
Hannunta daya ta dago zata dafe kirjin dashi sbd jin takeyi zuciyarta na kasa daukan abinda take ji ya sake riqe hannun da dayan hannunsa tareda dago idanuwansa ya kalli fuskarta cikin cikakkiyar asalin nutsuwansa daya jima da rasawa akanta yaba kafesu tareda tsayar dasu akan fuskar da yayi shekaru bai yiwa kallan daya bawa zuciyarsa sanyi da hasken data rasa,
Bude nata idanuwan tayi a cikin wani irin mutuwar jiki hawayen abinda take ji na radadin zuci da gangar suna gangarowa daga idanuwanta ta sauke su akan fuskarsa da tinda take bata taba masa kallan ido cikin ido ba sai ayau din ta zuba masa su hawayenta na tsananta gangarowa ta kasa riqe abinda take ji zuciyarta na neman bugawa sbd bazata iya rayuwaba idan aka fada mata wani labarin daban akan abaas ta bude bakinta ahankali muryanta na cikeda wani irin raunin datake shirye da barin duniyar da babu abaas tace
'Abaass gha.....
Tafin hannunsa me sanyin dayake keto a cikin daren ya saka yana rufe bakinta a cikin wata irin sanyi da tsantsar kaunar datake bayyanuwa a idanuwansa babu burki yana tsayar da kallansa dakyau akan fuskarta baya buqatan jin dacin dayake tattare da zuciyarta wanda yana jiyosa a tasa zuciyar sbd yasan wani tsantsar baqin ciki da mafi dacin rayuwarta ne zata ratsa a duk abinda zaa sanar da ita gameda 'dan uwan nata wanda ya gama sanin komai akanta amma koma wane halin zata shiga na rashin dan uwan da shine rayuwarta ya shirya tayata shigarsa da tsayuwa akanta batareda ta rasa kanta ba har sai ta samu nutsuwa da saukin komai daga abinda zata dandana rashin da jajjiga rayuwa da duniyarta,
Babu abinda yakeson ji daga gareta ya yafe wannan damar da matsayin ga 'danta sbd shine wanda zai iya bata sassaucin datake buqata a lokacin da zataji komai daga bakinsa,
Tin daga lokacin da ta shigo rayuwarsa mulki da matsayin da dukkanin mulkin yake bayarwa ya fita a kansa, Rayuwa yakeso wadda ita kadai ce zata kasance dashi a cikinta, Rayuwa yake so wadda shine kadai zai kasance mata a cikinta ya bata dukkanin farin ciki da walwalan da qasarsa ta bata dan kuwa kaddarar haifa masa 'da ce ta rabota da komai nata da farin cikin da har abada kila ta rasa,
Wasu hawayen nata ne masu zafi suka gangaro a sanyaye suka sauka akan fatar hannunsa datake rufe da bakinta ya gangara da idanuwansa akan hawayen dake kan fatar tasa suna gangarawa zasu sauka kafin ya dawo da kallansa akan fuskarta da itama shi din ta dago ta sake tsayar da idanuwanta kafin wani irin kuka me tsananin tsima zuciya ya taho mata ta fasa a hankali tana rintse idanuwanta da karfi babu abinda ruhi da zuciyarta da idanuwanta da gangar jikinta suke tsananin nema da muradi a lokacin bayan bayyanar abaas a gabanta.
Qamqame hannuwanta Sultan yasar yayi yana sauraran kukanta da sautinsa suna ratsa sa idanuwansa na sauyawa kafin ya saketa a hankali tareda zaunawa a gefenta a wata irin nutsuwa ya bude hannuwansa ya zagayota a natse ya shigar da ita jikinsa ya rungume da sanyayyar nutsuwan data isa gareta ta rintse idanuwanta tana sake fasa wani kukan dayake jinsa har tsakiyar kirjinsa data toshe.
Kuka takeyi sosai wanda yake na tsantsar tsananin tsoron dayake shigarta wanda bata shirya ji ba koma menene ya kawo bahar gareta batareda abaas ba dan haka zuciyarta ke wata irin karyewan da bazata taba gyaruwaba.
Dukkanin kukanta da radadin dayake tafe dashi ratsasa yakeyi yana karbansa hannu bibbiyu da radadin da quncin da komai duk karba yakeyi a zuciyarsa idanuwansa jajir yana sake rungumeta da karfi a jikinsa.
A haka ya qarar da kutsawa a cikin kowane quncinta daya shirya rayuwa a cikinsa har qarshensa tareda ita. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee
95 Acan bangaren ma SULTAN NUAB a zaunen ya kwana batareda rintsawa ko ta second dayaba idanuwansa a kafe guri daya zuciyarsa a nauyaye da abinda baisan ya shigesa ba har akai asuba tukuna ya iya miqewa dan sallah.
Kai tsaye masallacin masarautar dayake duk wani sultan acan yake sallah tareda manya ayau shima da yaransa can suka nufa dan gabatar da sallarsu acan sabanin tasu da suke hada jam'i suyi a nasu masallacin da suka tadarwa kansu a bangarensa.
Ba dukkaninsu suka tafi ba wasu anan bangaren sukai sallarsu shi kuwa da aleey da keelah tareda wasu daga securities dinsa masallacin suka nufa a karan farko sbd a yanzu shine me masarautar gabaki dayanta.
A lokaci daya ya iso masallacin tareda mahaifinsa wanda ya kallesa da idanuwansa da basu gama dawowa daidai ba shi kuwa bai dagoba sbd baya buqatan kallan kowa a yanzu bare wata hayaniyar da zata qarawa kansa nauyin dayake ji,
Ganin securities dinsa suna kokarin cike rabin masallacin yasa kusan kowa iya kansa yana bin sahun sallah a natse dan tada sallan da zaayi batareda tsayawa kallan kwaf ba zuciyarsu na shiga rudanin ganinsa a masallacin tareda tsananin tsoro da fargaba da zullumin abinda suke ganin kaman yana shirin tabbata cewan shine Sultan din boyem a a yanzu.
A guri daya ya tsaya sahu kafada da kafada da mahaifinsa wanda shima yake cikin yanayi na rashin son hayaniya,
Sallah akai aka kammala kowa yayi tsit da adduar da kowa yake sanarwa ubangiji har gari ya fara haske wanda kowa ya fara silalewa daya bayan daya suna barin masallacin dan tafiya fara shiri sbd da safiya ake nadin sarautar qasar wadda a cikin tsakiyar daren dukkanin labarin nadin sarautar goben ya fita yana isa ga duniya da duk inda ya kamata ya isa sbd akan dole manyan fada basu rintsa ba suka kwana aikin nadin mulkin sbd dolensu ne.
Koda ya koma bangarensa babu wanda ya sake zuwa fara shirye shirye kawai akeyi tako ina wanda ya saka koina ya dauki wata irin harama da hayaniya amma banda bangarensa wanda yake tsit babu kowace hayaniya duk da su aleey wani irin zazzafan shirin sukeyi tareda tsananta wani irin tsananin tsaro da securities tako ina,
A bangaren ayanah tinda sultan ya fice su tenya suka sanar da ita NUAB ne sultan na yanzu wanda zaayi nadinsa ayau.
Wani irin sabon nauyi taji ya danne kirjinta amma tin da kansa ne ya karba ba dole aka dorasa ba tasan an cika mata alkawarinta,
Tausar zuciyarta tayi daga dukkanin abinda takeji zata jira ayi nadin sarautar ayau din a gama kafin ya fuskance ta shi da Sakinah su sanar da ita menene yake faruwa wanda bata saniba dan haka ta saka dukkanin karfin hali da taurin zuciyar da batada ta danne abinda takeji dan barin Hayateem dinta ya fuskanci wannan ranar da zata zata fara gina tarihi me girma a rayuwarsa.
Manyan baqi daga qasashen kusa dana gari da duk wani jinin boyem dake duniya fara halarta sukai a qasa da masaurautar boyem wanda yake tsananta tsaron qasar ayau gabaki dayanta da masarautar sbd tsaron har yayi yawan da hankali ma bazai daukaba,
Kayan nadin sarautar da sultan ya jima da tanadar masa aka aiko daga bangarensa wanda sakon ya iso da bayi kusan sama da ashirin tareda kadir suna daukan idanuwa tamkar zinari sai asalin zoben zinarin dayake dauke da adon black diamonds a cikinsa na sarautar wanda wata narkakkiyar dukiya me tarin yawan gaske sultan ya batar gurin qerosa daga qasar Kuwait me dauke da sunan SULTAN NUAB 40 wanda kowane sultan me mulki saiya mallaki nasa.
Isowan sakon bangaren Amminsa ya saka ammin tasa bada tukuicin dukiya me tsananin gaske hakama su tenya da maa sakinah saida kowannesu ya bada tukuicin zinari me yawan gaske kafin daga baya suka dauki kayan Ayanah na gabansu suna bayanta dauke dasu da bayi sama da goma suka nufi bangarensa dan mahaifiyarsa ce zatai shirinsa a bisa al'adah.
Koda suka isa ya fito wanka yana sanye da fararen kaya tas riga body hug da farin dogon wando fuskarsa tayi wani irin haske asalin kwarjininsa yana fita a natse yana kwantar da tsigar dukkanin wani me kallansa.
Amminsa ce kadai ta iya isa palonsa na kurya sai Maa sakinah da tenya wainda suka tsaya daga nesa Ammin tasa ta tako tana isowa garesa yana tsaye ya kasa motsawa ya zuba mata idanuwansa yana kallanta dukkanin jikinsa na mutuwa da wani irin dumi da zafi.
Itama wasu hawaye ne suka cika idanuwanta tana qarasowa rungumesa tayi ahankali tareda sauke ajiyan zuciya tana bude baki tace
'Daga yau ina rokon allah ya baka dukkanin kariya har ranar da ranka zai bar jikinka, Ina rokon ka samu dukkanin kariya da rayuwa me albarka da jin dadin da kwanciyan hankalin da baida kishiya har ranar da zaka sauka wannan mulkin lafiya.'
Hannuwansa biyu ya saka ya qanqameta jikinsa sosai yana rufe idanuwansa yana rokon allah ya karbi adduar mahaifiyarsa akansa.
Mintina suka bata a hakan kafin suka saki juna ta kama hannunsa ta zaunar dashi sai lokacin su maa suka iso suka fara bata komai na sarautar a hankali tana saka masa tana shiryasa.
Hannuwanta biyu ta saka ta dauki zoben dayake daga mahaifinsa ta saka masa kafin ta zaro nata kyautar ta chain din asalin azurfa da aka saka sunansa a jiki da manyan baqaqe da larabci wanda tin a shekaru tayi masa shi ta saka masa a hannun da agogon dubban daruruwan dollars suka siyesa ta kama hannun takai bakinta tayi kissing ahankali tareda jero masa wata irin adduar data sakasa sake rungumeta yana kissin tsakiyar kanta.
Maa sakinah ce ta dafa kansa a hankali itama ta karanto masa adduoi masu kyau da tsafta kafin maa tenya itama tayi masa a daidai lokacin komai ya kammala masarauta ta hallata ta cika maqil da wasu irin manyan mutane tako ina ga medias daban daban da bazasu taba kirguwa ba hakama mutanen NUAB din da turawan kasashe daban daban kusan duk sun bayyana wainda zasu iya zuwa a short lokacin da aka sanar.
Duk wani babban fada na yanzu dama wainda sukai retire da murabus suna bakin kofar bamgarensa a jere a tsaye tareda wasu irin securities dan jiran fitowansa dan rakiya garesa zuwa fada wanda haka tsarin yake.
Aleey ayau din tsaron daya zuba a masarautar boyem ya wuce dukkanin hankali sbd tako ina yaronsu ne a cikin shirin da basu taba zamaba na rayuwarsu,
Idanuwan aleey da duk wani ghaz member a bude suke sharp suke hatta yaransu da duka suka qasashe da sukai isowan gaggawa a shirye suke tsaf da bawa kowace daqiqa ta ranar kariya a ransu.
Karfe goma sha biyi daidai ne lokacin fitowansa dan haka dago manyan idanuwansa da ayau tsantsar mulkin dake jininsa yake bayyana yayi ya kalli agogo sha biyu da hamsin da tara,
Juyawa yayi ya kalli hanyar kofar dakin da babu wanda ya shiga har lokacin sbd har lokacin bata farka ba sbd kwanan datai da wani mummunan zazzabi me karfin daya hanata baccin lafiya sai bayan asuba.
Juyo da kansa yayi ya daga kafafunsa yana takawa a natse da kamewa tareda tsantsar ikon dayake yawo a jininsa ya nufi kofa wadda yana isowa aleey ya wangale ta take dukkanin mai rai dake gurin suka gyara tsayuwa suna sauke kansu kaf a lokaci daya cikeda wata irin girmamawa da wata qarar da aka saki data tabbatarwa duk wanda yake ciki da wajen masarautar jiran nadin SULTAN LEUL NUAB ALMAZZ ya fito.
Take masarautar ta dauki wani irin tsit duk da dubban daruruwan mutanen dake cikinta da zagayenta shiru koina yayi.