Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 38
Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 38: Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 38. Securities kuwa take suka sake dauke wuta da…
4,484 words
Securities kuwa take suka sake dauke wuta da qamewa cikin kowane position nasu.
Aleey dayake shine a gaban NUAB din da wasu securities da bama sa jin kowane yare bayan na harbewa without any second thoughts,
Wasu irin qananun zafafan full loaded pistols ne a jikin aleey a boye kusan guda hudu da wata wuqar da kai tsaye zata yanka ko jijiya nawa ne a inda aka sokata tayi musu yankan cin ledar bera.
Keelah ma dayake daba bayan NUAB din tareda manyan boyem da suka taho rakiyar sultan din zuwa fada a loade yake da munanan makamai a cikin jikinsa fuska babu sauki ko a kadan a wannan lokacin.
Kai tsaye fada suka isa wadda yan jarida daga nesa inda aka kebe musu suka fara hasko hasken flashers nasu tako ina kowane sahu da motsi yana daukewa saina isowan sultan me boyem da ghaz da Moscow.
Sultan yasar dayake zaune tinda sultan da yan rakiyarsa suka sako kai a cikin fadar ya zuba masa idanuwansa batareda ya daukeba yana jero masa wasu irin karfafan adduoin da zasu basa kariya da ikon mulkinsa cikin aminci da kwanciyan hankali.
Babu bata lokaci aka gabatar da nadin sarautar wadda tako ina ake fitowa da wasu irin trays na danyan zinarin da shine kawai yake daukan idon koina.
Sultan ne ya taso a daidai lokacin da ake farawa ya tsaya a gaban NUAB din gabatar da sauran al'adar da manyan asalin boyem ke yi a lokacin nadin.
A daidai lokacin da ake kammala komai aka dauko hular datake matsayin rawanin mulkin da zaa saka masa,
A daidai lokacin daya daga cikin securities da aka bari acan gadin bahar ya iso fadar da kansa har gurin aleey dake can gefe a tsaye batareda ya zauna ba dan bazai taba iya zaunawa ba a daidai lokacin bai yadda komai ya shammacesa ba musamman da basuga motsin Asim tako inaba da mahaifiyarsa basu san me suke shiryawaba.
A gurin kunnuwansa ya sanar masa da bahar ta farka amma ba lafiya ba tanata amai ta fito tanason barin bangaren amma basu bude kofar ba.
Aleey kallan NUAB yayi wanda ya basa umarni me karfin gaske cewan ko wane lokaci ne yake a ringa sanar dashi abinda ya shafeta kai tsaye without any delay.
Kallan taron manyan duniyar dake gurin yayi da abinda akeyi wanda duniya gabaki daya take shedawa live a gidajen tv da live shows da media da ma wainda ke shadawa a gaban idanuwansu.
Numfashi aleey din ya sauke tareda tinkaro NUAB din wanda aka kawo hular zaa saka masa ya dan rankwafo cikeda girmamawa ya fada masa daidai lokacin shugaban fadar jinin boyem daya zuba shekaru shine yake nadin sarakunan boyem ya tsufa ya daga hular zai saka take NUAB din ya riqe hannunsa da hannunsa dayake cikeda lafiyayyan karfi da lafiyar fata yana dago idanuwansa da suke jajir tinda aka fara nadin ya dakatar dashi daga saka masa nadin hular darak3 ta asalin saqin sunan boyem da akai da ruwan zinari.
Sultan dayake ganin hakan cikin iko da nasa mulkin kai tsaye ya riqe hannun NUAB din batareda an gane meyake shirin faruwaba na barin gurin da NUAB din zaiyi ya kalli aleey da idanuwansa akan ya koma inda yake a qarasa gamawa.
Baya aleey yaja yana komawa sbd shima yasan babban qaramin aikin mai gidansa ne barin gurin da duniya zata sheda abinda yayi.
Qarasa nadin sarautar akaci gaba dayi cikeda tsantsar iko da farin ciki da kafar da sabon tarihi a qasa da masarautar boyem. #MAMUH
HAYATEEM novel 700 0022419171 AccessBank maryam sani gummi 09033181070HAYATEEM Mamuhgee
96 Kammala nadin akai tareda daga tutar datake dauke da sunansa aka ambaci sunansa kowa da duniya ta sheda a matsayin sabon sultan na boyem me daraja dan haka kowa miqewa yayi cikin sautin daya ratsa kowane lungu na masarautar akai masa barka da sheda wannan rana me tarin daraja da kafar da sabon tarihin da zai dora boyem akan hanyar kalar nasa mulkin da ake fatan ya zamo alkhairi me girman gaske.
Daya bayan daya manyan masarautar boyem masu matsayi a yanzu da wainda ma basa dashi da wainda sunyi sun sauka suka ringa zuwa suna sana sakawa matsayinsa albarka da addua cikin girmamawa wanda hakan ne ya dauki lokaci.
Bayan ana gama wannan sallah akai a cikin babban masallacin masarautar wanda ya dauki mutane fiyeda lissafi mutane masu dibbin yawa har waje wadda hatta ita sai da aka ringa dauka live ana nunawa duniya sallar sultan ta farko a cikin dubban jamaar da suka halarci taron nadin.
Ana gamawa abincin zaa ci wanda anan ne zaayi biki na al'adu da abubuwan nishadi da dama till down dan haka ake bawa sultan daman komawa ya sauyo kayansa daga kayan nadin sarautar.
Dukka wannan abin da akeyi zuciyar sultan NUAB tana rabe ne a cikin tinanika guda biyu wainda suke bayyane a idanuwansa da suka sauya matiqar sosai duk da yayi iya kokarinsa gurin dan sakewa yana gaisawa da mutane sosai sbd babu qaramin mutum a gurin.
Lokacin tafiyarss sauyawa da yar hutawar da batafi ta rabin awa ba zuwa awa daya kai tsaye barin gurin yayi tareda personal securities dinsa da securities na masarautar da daga yau suma suna tsaye a gurin basa kariya.
Tin a hanya yana tafe cikin nutsuwa da kamewa tareda zallan ikon mulki dayake yawo a jininsa ya dan kalli aleey a natse batareda doguwar hayaniya ba yace a kira doctor.
Fidda waya aleey yayi kai tsaye yana kiran likitansu da zaiyi gaggawar biyosu sbd yana masarautar shima gurin hidimar bikin.
Suna isowa bangaren nasa wanda tin daga nesa securities ne masu karfin gaske zagaye da gurin take suka sake gyara tsayuwa dan masa barka da isowa batareda baki ya furta ba sbd shima bai iya amsawan dan haka kai tsaye ciki yake kokarin nufa bayan an wangale masa kofar shigewan da sauri.
Sauran securities din gabaki daya kaf duka burki suka ci a bakin kofar suna jeruwa gefe daban bayan ya shige aka rufe kofar ruf gurin ya sake daukan tsit.
Hatta aleey bai shiga ba daga kofar ya dakata yana jiran isowan Dr.
Shi kuwa yana shiga wata ajiyan zuciya mara sauti ya sauke a hankali tareda numfashi me zafi yanajin zuciyarsa na dan samun sassaucin halinda take ciki na karba da hawa mulkin da bai taba tinanin hawa ba arayuwarsa,
Kai tsaye bedroom dinsa ya nufa ya cire dukkanin kayan sarautar da suke jikinsa dayake jin kansa very uncomfortable a cikinsu,
Yana zarewa bathroom ya fada tareda sakarwa kansa ruwan dumi da suka ratsasa yaji yana dawowa NUAB dinsa, Bai wani bata lokaci ba ya fito wankan a natse ya shirya tareda sauya kaya zuwa marasa nauyi ya duba wayarsa dake kawo haske yaga kiran aleey dan sanar dashi dr ya iso tin dazu.
Fitowa yayi bayan ya ajiye wayar ya fara nufar dakinta kai tsaye yana shiga a qasa ya ganta zube ta dunqule guri daya tana wani irin rawan sanyi idanuwanta a rufe fuskarta tayi ja.
Qarasawa yayi kai tsaye baice komaiba ko tsayawa komai a natse ya dauketa daga qasan yana nufar bakin gado da ita ya ajiye a hankali.
Qatuwar jacket ya dauko ya saka mata tareda hulan sanyi me kauri akan kayan dake jikinta kafin ya sake daukota ya fito da ita palon yace dr ya shigo.
Dr na shigowa cikin sauri da nutsuwa ya fara dubata sbd dukkanin aikin NUAB bayason gaggawa a natse yake so da buqatar ayi masa komai nasa bare a yanzu da ake maganar lafiya da rayuwa.
Mintina sosai dr din ya dauka yana dubata kafin ya fidda magani kusan guda uku ya bata tareda daura mata qaramin drip sbd aman datai sosai y dan tafi da ruwan jikinta.
Dr na ficewa haka ya kuma daukanta da drip din ya maida daki tareda daga wayarsa ya kira maa sakinah dan kawo mata abinci da bata kulawa.
Kafin zuwa maa sakinah tini lokacin komawansa bikin da zaa sake farawa yayi amma bai fito haka yabar dubban jamaa anata jira har sai da maa sakinah ta iso tukuna ya fito daga dakin ya sake shiryawa cikin wata shigar daban data fiddo wani asalin zazzafan kyansa da kwarjininsa tareda bayyanarda shi din matashin sarki ne da zai zuba zazzafan lokacinsa akan mulki.
Yana ficewa Maa sakinah ta shiga dakin a cikin tsananin kewan bahar din datai wadda ta kwana biyu bata gani ba dan haka sakawa tayi bayin suka jere komai suka fice ta qarasa gurinta ta zauna bakin gadonta tareda bude baki zatai magana Bahar din ta shige jikinta tana rungumeta tareda fara hawaye masu sanyi tana cewa
'Maa dan Allah kada ki tafi koina ki zauna tareda ni kokuma ki tafi dani can'
Shiru maa din tayi tana rungumeta jikinta sosai tace
'Bahar Allah ya baki lafiya tukuna amma ke yanzu matar Sultan ce a masarautar nan baya kamata ace kina fita yawo koina koma komawa wani bangaren'
Shiru bahar din tayi tareda batareda ta fahimci maganar kwata kwata ba ta Girgiza kai tana cewa aa ita dai tanasonta a kusa da duk inda take.
Shiru kawai Maa din tayi batareda tayi sabuwar magana ba ta saketa tana nufar toilet ta hada mata ruwan wanka me zafi da qamshin wasu irin turarikan wanka na SHUWA INCENSE AND MORE 07042293387 wainda suke na asalin masu kama jiki su wuni fatar jikinka tana qamshi me sanyi da ratsa zuciya.
Dawowa tayi ta kamata zuwa toilet din sbd ruwan drip din ya qare,
Wanka Bahar din tayi a sanyaye sbd ta dan samu karfin jiki daga ruwan da aka sakama mata tana gamawa ta sake brush ta fito daure da towel gashinta a daure tsakiyar kanta a sako sako wanda bama itace ta daure ba da kanta duk da batai tinanin shine ya daure mata dinba.
Maa sakinah cikin kulawa da sangartawa ta tsaya bayanta bayan ta zauna kaman yanda ta saba yi mata ta warware mata gashinta ta dan gyara mata sama sama ta sake dan daure mata kaman yanda ta gansa baa matseba ko kadan,
Tayata shiryawa tayi kafin ta dauko mata kayansa kaman yanda ta saba sune kadai sitirar datake sakawa ta saka wando da rigar datai mata mugun yawa hakama wandon ko zaman qugunta baya yi.
Sallah tayi tana idarwa maa ta zuba mata madara me zafi sosai da zuka tafara sha a hankali harta dan sha sosai kafin ta ajiye maa din da kanta ta ringa bata abinci tana lallabata sbd ta saba zuwa lokacin ta gama sangarta bahar din duk da ma bahar din bata gama sake damuwarta da rayuwar data tasoba gaba daya.
Tana gama cin abincin maganin ma itace ta bata da kanta tasha daqyar sbd batason magani sam bare irin wannan din,
Suna gamawa rokon maa tafara yi akan su tafi su koma bangaren can batason zaman nan din.
Yanda ta dage ne ya saka maa fidda wayarta ta saka kiran aleey ta sanar dashi duk da ana cikin hidima sosai haka aleey ya isa ya sanar da sultan NUAB din,
Dan shiru yayi kafin ya dago manyan fararen idanuwansa batareda ya jiyo ba yace abarsu su tafi din.
Aleey barin gurin yayi ya isa bangaren da kansa yayi musu jagora har bangaren Ammi wadda bata bangaren suna gurin hidimar sbd tinda angama nadi bikin yanzu da akeyi kaman lunch ne kowa ya halarta maza da matan duka jinin boyem da masu matsayi tareda masu muqamai na qasashe harma da abokan business dinsa mata masu karfi a duniyar business suma.
Tenya ma da sauran bayin da securities din da aka tanadarwa Ayanah din duka suna can dan hakanne ma bata nema bahar ba tabarta ta huta kaman yanda suka duba kafin fitowansu bangarensa dazun sukaga tana bacci sosai.
Suna shigowa daki ta nufa tana shiga ta sauke ajiyan zuciya sbd samun dawowan cikakkiyar nutsuwanta.
Kayan jikinta tafara zarewa a natse cikin rashin karfin jiki kafin ta sauya da wasu ta isa ta haye gadon dakin ta kwanta tana sake samun nutsuwan gangar jiki data ruhi.
Maa sakinah ma farin cikinta da kwanciyan hankalinta taji itama ya dawo ganin bahar din a gabanta ta dawo mata a cikakkiyarta dan haka fara kokarin bata labarin nadin da akai yau din gaske tayi wanda ya saka Bahar shiru jikinta na wani irin sanyi da mutuwa,
NUAB a matsayin SULTAN na qasar boyem gabaki daya? Yana a matsayin SULTAN a dazu ya taho gareta ba NUAB zallah data saniba.
Numfashi mara sauti ko kadan ta sauke daga zuciyarta tana lumshe idanuwanta ta rufe a hankali batareda ta furta kalma ko daya ba amma dukkanin abinda maa take fada akan zamowan NUAB din sultan dazai mulkin dubban miliyoyin mutane tana jin saukan kalaman cikin kunnuwanta,
Acan kuwa cikin babban makeken Palace hall din masarautar boyem din wanda yake a tsare da wani irin tsarin dayake bayyanarda tarin arziki ba qarami ba masarautar boyem take dashi tareda wayewa da ilimi dan kuwa komai na gurin class da dukiya me yawa yake nuna,
Tamkar fadar masarautar gurin yake komai golden da black ne dan haka gurin yake daukan ido kaman ka shiga fadar da aka qera da zinari,
A tsare cikin burgewa da daukan ido komai yake na tables kala kala na cin abinci wanda babu kalar tsadaddiyar abincin da babu wanda qwararri professionals akan girki suka dafa da tsarawa. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee
97 Hidimar aka fara wanda kowa yake a tsare a waye ba hayaniya duka jamaar Echoes suma sun halla a tables daya farin cikinsu ya kasa tsayuwa Musamman 002 Asia,003 Zulee da Zee Amiru,Ummu Asim,Maman Anees da Amina Maikatifa Abinci kawai suke ci idanuwansu sun kasa tsayuwa guri daya sai ganin jamaar su sukeyi suna qarasowa,
Naimah ce a cikin manyan bayin da aka zaba dan shigo da abinci a tsare cikin yaran tsadaddun caterers da aka dauko daga wata qasa tana isowa table din yan Echoes din kanta a qasa cikin uniform dinta sa suke fes sunfi wata designer din tsari da kyau harma da kudi ta fara jere musu ruwan madara me dumin da ake kawowa dan dumama ciki da bawa fatar jiki lafiya.
Dagowa Zee tayi ta kalleta tace
'Allah sarki Sannu da kokari naimah ina salmah ne??
Sauke kai ta sake dan yi qasa girgiza kai alaman Salmah dai kila marigaya zata bi.
Dariya me karfi suka kece da ita gabaki dayansu suna tausawa salmah din wadda da alama Salman dinta na Asim zata bi.
Hidimar biki aka ci gaba da ita a tsare babu tsiya babu talauci babu qaranta koina da komai arziki ne kawai ake saki ana wasa dashi cikin harkar arziki ta masu abun duniya.
Ammi ma a tare take cikin manyan matan duniya da duniya tasan dasu suna bata girmamawa sosai cikin wayewa da ilimi sbd kasancewanta mahaifiyar sultan NUAB me manyan mutane a qasashe daban daban,
Hakama jamaar sultan yasar suna nuna girmamawansu sosai da tarin kulawa ga Ayanaah din wadda ayau duniya ita kadai ma take kalla a matsayin tararuwa ga 'danta sultan LEUL NUAB hakama tauraruwa ga sultan me murabus Yasar almazz sbd babu wanda yaga haile ko Asim, sai 'yayanta mata da akan dole suka shiryo suka fito hidimar sbd gudun asan halinda su hailen suke ciki hakama babu wanda ya tambayi inda suke,
Maraki ma tana gurin ta iso cikin ado me tsarin gasek da koina na jikinta ke daukan idanuwa da adon gwalawalai sedai babu farin ciki ko rahama ko daya a cikin tsakiyar zuciyarta sbd abinda idanuwanta suke gane mata a yanzu shine asalin son da acan baya ma basu gani komai ba a idon sultan akan ayanah,
Baya wani kallanta amma kallo daya yayiwa Ayanah daga inda yake zuwa inda take wanda yayi akan idanuwan marakin jin tayi duniyarta ta tsaya cak,
Abu ne ta gani wanda a yanzu da baya mulki babu wanda zai iya kutse a cikin rayuwar da duk ya zabawa kansa dan haka taji gashin jikinta ma suna miqewa tsananin kishin da babu abinda zai mata bayan kaita ga ciwon zuciyar da zata mace a banza yana rufeta tana jin inama bata samu kanta a rayuwa cikin wainda babu wanda ya taba sanin mahimmancinta har kusan shi wanda ya ajiyeta din,
A yanzu da baya mulki zuciyarsa batada shamaki,rayuwarsa batada shamakin bayyanarda dukkanin abinda yake ransa ko burinsa ga kowace mace ta jinin sarautar boyem da wadda ba jininn sarautar boyem ba yanada ikon auren kowa babu shamaki a wane matsayin take ita?
Nauyi kirjinta yayi mata tana dago idanuwanta ta zubawa ayanah dake zaune a cikin manyan mutane suna kokarin samun kusanci da sanin juna da ita tana kallanta batareda kyaftawa ba tinanika da dama suna dawo mata a zuciya na rayuwar da ayanah ta samu a matsayin imebēti da ita bata taba samu ba,
Su aslam ma dake gurin zuciyoyinsu zafin dayake ciki zai iya babbaka gurin da wuta sbd wani irin abinda basu taba ji bane yake yawo a jininsu musamman aslam datake tabbatarda maganar mahaifiyarsu ayau cewan Ayanah ghaz itace silar dukkanin wani baqin ciki da kuncin rayuwarsu da har abada idan bata bar duniyaba bazasu taba samun farin ciki ba,
Leylah ma bata iya fitowa taron ba tana dakinta ta rufe kanta cikin tsananin baqin cin rayuwar datakejin kaman ta kunnawa bangaren gabaki daya wuta sbd wutar dake cin zuciyarta ta tsana me tsananin gaske datakewa bahar,
Tinda safiyar ta waye bata fitoba hakama Kusan kowa ya manta da ita sbd lamarin da suka tashi a cikinsa ayanah kuwa dukkanin zuciyarta koda ake kowace hidimar tana akan Bahar da batasan tayaya zata fara kallanta a cikin idanuwanta datajin kaunarta a kowane lungun na jijiyar dake gudanar da jini a gangar jikinta,
Jin takeyi zuciya da ruhinta na tsananin matsuwa da son saka Bahar din a cikin idanuwanta da gangar jikinta amma tana daurewa sbd tsoron abinda zata iya ji.
Maa sakinah ma sam bata sake tinawa da leylah dinba sbd dawowan Bahar da kuma rashin ganin fitowan Leylah din dan haka hidimarta kawai takeyi hankali kwance da farin cikinta wani akan wani tinda 'dansu NUAB shine mai iko da mulkin qasar a yanzu da kuma bahar dinta datake a cikin koshin lafiyar da a yanzu tana cikin tsaro da ikon Allah.
Wuni akai cur ana bikin wanda sai dare aka watse zuwa lokacin babu wanda bai gaji ba matiqar gaske dan haka har dare sosai baqi basu gama watsewa ba sai tsakiyar dare kowa ya gama watsewa masarautar ta dauki tsit wanda sai ankwana biyu kafin cikakken motsinta ya dawo sbd hutun da zaayi na hidimar da kowa gajiya ta ratsesa.
Sultan NUAB ma yana isa bangarensa a cikin daren take aleey shima da keelah suka nufi dakunansu suna barin sauran securities din da zasu ringa sauyin juna wasu na hutawa,
Cikin ruwan zafi sosai masu fidda wani hayaqin qamshin dayake hade da qamshin shower gel dinsa na Aesop na wanka ya shiga a cikin bathtub din ya kwanta tareda rufe idanuwansa zafin na ratsa kafafu da fatar jikinsa yana warware masa duk wata gajiyan dake tattare dashi wanda bai taba samun kansa a cikinta ba tinda ya kafu ya gina ghaz empire dinsa.
Ya dan dauki lokaci a ciki kafin ya fito yayi brush ya fito daure da towel gashin kansa na tsiyayar ruwan da dole ya goge ta busar da gashin nasa dayake cin kayan gyaran da kudinsu kadai zai iya tada wani business din,
Dogon wandon bacci kadai ya saka jikinsa na fidda wani lafiyayyan qamshin tsadaddiyar designer body mist dinsa na Sol de janeiro cheirosa ya sake gashinsa batareda ya kamasa ba ya kwanta kai tsaye tareda lumshewa fararen idanuwansa yana sauke numfashi me sanyi da nutsuwa dan samun cikakkiyar hutawan da babu me ganinsa a gobe kwata kwata.
Acan ma koda Ayanah ta koma itama kai tsaye bedroom dinta ta nufa batareda tasan bahar ta dawo bangarenba ta kalli agogo tana tinanin a wane halin Bahar take ciki a yanzu gashi ba zata iya zuwa ba yanzu dare yayi sosai hakama NUAB yana can tasan zai bata kulawan daya kamata dan haka itama wanka tayi ta rage gajiyarta kafin tayi shirin bacci ta kwanta tareda lumshe idanuwanta ta rufe batareda tabbacin baccin zai taho mata ba dan kuwa zuciyarta na tsaye ne cak guri daya wato akan tsananin matsuwan haduwa da Bahar.
Koina tsit yayi kowa yayi bacci cikeda gajiya da samun nutsuwa da farin ciki tareda har kwanciyan hankali,
Shi kansa aleey ayau baccin kwanciyan hankali da farin ciki yake dan kuwa daga yanxu baida shakkar komai akan Bahar da Ammi a duk inda suke cikin boyem da masarautar boyem din babu wanda zai iya tabasu sbd kuwa kai tsaye mutum yasan mutuwarsa ce yake tabawa.
****a cikin tsakiyar daren daidai wannan lokacin a bangaren Aslam da dukkaninsu suke har lokacin sbd bullet din da aka cire musu su biyun duka batareda sanin kowaba hakama su hailen da Asim din suna cikin wani matsanancin halin da suke buqatar ganin manyan likita koma fita zuwa wata qasar matiqar anason hannun Asim da kafar hailen taci gaba da moruwa.
Suna dawowa daga gurin taron daqyar Aslam ta iso bangaren sbd baqin cikin dayake neman makantar da ita da mummunar ranar da ayau suka sheda da idanuwansu na wani ya karbi mulkin boyem ba Asim ba a kuma lokacinda Asim din da mahaifiyarsu suke kwance cikin mugun hali.
Suna shigowa meryam da babu ta inda ta hango musu nasara sbd a bayyane komai yake Tin farko NUAB ne mahaifiyarsa a zuciyar sultan ya boyesu ya juyar da kowace kiyayyar da zata illata su zuwa kansa,
A yanzu duniya gabaki daya tana iya ganin soyayyarsa me zafi a bayyane cikin idanuwansa dayakewa Ayanah ghaz da 'danta,
A yanzu kam indai sune a qasan zuciya da ruhinsa duniya zata sheda hakan sbd baida kowane shamaki akansu, Baida kowace iyaka akan ayanah ghaz, Baida kowane sharadi na sarautar dayake riqesa daga mallakarta da samunta tareda rayuwar da duk yakeso da ita wanda ita ta hango hakan a tattare dashi wanda Aslam bata nutsu ta gani ba sbd wani kallo ne yakewa ayanah da dukkanin nutsuwa da ruhinsa wanda bata taba ganin yayiwa mahaifiyarsu ba bare ma ta taba ganin kowane irin namiji yayiwa mace wannan kallan,
Kallo ne da kai tsaye yake bayyanar da wata tsimammiyar soyayyar da ba ayau take ajiye a gurin da babu wanda ya taba shigarsa ba, Soyayya ce datake hade da kaunar da babu sirki tareda sallamawa gabaki daya ga wanda akewa ita,
Gashin jikinta ringa tashi yayi tana jin kowace buri da rayuwarta na narkewa suna zubewa qasa a banza sun riga sun rasa komai a wannan fadan sbd ayau ayanah ghaz ta samu dukkanin abinda suke tsananin buri da yaqin nema da rai da lafiyarsu.
Silalewa tayi a qasa bakin gadon da Mamen su take idanuwanta a bude kafe guri daya sunyi jajir ba kyan gani dukkanin qunci da baqin cikin datake ji tana gani a abinda yake faruwa yana shiga kunnuwanta zuwa zuciyarta amma bata iya motsawa ba sbd kusan bata iya dogon motsin komai da jikinta,
A yanxu take tabbatarda rayuwar data rayu a cikinta ta aure da soyayyar mijinta ta mafarkin da baitaba zamowa gaskiya bace,
Ayau ta zuciyarta tana dandana wani zallan baqin ciki da qunci tareda heart break na zambatarta da Mijin datake aure yayi wanda bata taba dandanawa ba. #MAMUH 09033181070
HAYATEEM Mamuhgee
98 Rufe idanuwa haile tayi ahankali wasu hawaye masu tsananin zafi suka gangaro daga cikinsu suna bin gefen fuskarta dake kallan sama batateda koina na jikinta ya motsa ba sbd dukkanin nadin da akai tana kwance tana jin komai yana ratsa kunnuwanta sbd koina sautin ratsawa yakeyi a masarautar da wajenta sbd koina kake kaji yanda nadin yake gudana,
Meryam ma data zube gefen mahaifiyar tasu wani irin kuka ne mai tsananin tsimar da zuciya dayake fitowa daga qasan zuciyarta tattare da wani irin dukkanin sarewa daga kowace irin samun nasarar rayuwa,
Kuka sosai takeyi mai wani irin sautin dayake shiga kunnuwan haile tana kasa bude nata idanuwan itama hawayen na gangaro mata jikinta na wata irin rawa mai tsananin radadin baqin ciki.
Aslam data kasa kukan ta kasa iya cewa komai zaunawa tayi a kujera tareda rafka wani irin tagumi tana rintse idanuwanta da sukai jajir suna mata radadi me tsananin gaske,
Shiru sukai dukkaninsu babu motsin komai a dakin bayan na kukan meryam dake tashi ahankali wanda sautinsa ke isa har dayan dakin Aslam din wanda Asim yake kwance yana jin kowane irin sauti a cikin kunnuwa da zuciyarsa suna yaga dukkanin abinda zuciyarsa take riqe dashi tin yarinta,
Rintse idanuwansa yayi wasu zafafan hawayen shima suna gangaro masa masu tsananin ciwo da radadin rayuwarsa data tsaya cak guri daya a yanzu,
Salman ya mutu ya barsa ayanzu baida amintaccen yaronsa da shine yake tsaya masa a komai kuma sbd hidimar nadin sarautar su aleey sun tattara komai sun rufe zancen kaman ba babu wanda ya mutu sbd kawai kada ma hayaniya ta tashi haka akai janaizar wainda suka rasu din tareda su salman din aka rufe tinda safe kafinma nadin sarautar batareda kowa yasan da hakan.
Hawaye ne suka gangaro masa sosai babu kakkautawa yana damqe hannuwansa duk da azabar dayake ji,
Abu dayane yakejin yana riqesa ga rayuwa a duniyar shine BAHAR wadda yasan tana raye bazai taba iya dakatawa ba saiya sameta a rayuwarsa ta zama mallakinsa sbd tin farko ai tasa din ce,
Bahar itace soyayyarta da bayaji baya gani zata saka yayi yaqi da karfin hali ya nema lafiyarsa ya warke ras ya kwatota zuwa rayuwarsa da bazata taba moruwa ba batareda bahar a cikinta ba.
Aslam ma data ga bazata iya cigaba da kallansu a wannan halinba suna buqatar neman lafiyarsu da gaggawa dan da ita ne zasu iya tsayawa su fuskanci komai su tsayu akan komai da suka wahaltawa dan haka a cikin daren ta sake bugawa dan tabbatarda shirin tafiyarsu ya kammala zuwa india ganin likitoci kwararri da dr ya nemar musu dan a cikin gaggawa takeson subar boyem batareda angama duka shagalin bikin sarautar ba dazai hana a gane halinda suke ciki.
****Washe gari da safe babu wanda ya tashi da wuri a cikin masu iko da masaurautar a yanzu sbd hutun gaske suke buqata musamman da a ranar babu baqin da zasu shigo masarautar sbd sai sultan ya huta da kyau sai jibi baqi zasu iya fara shigowa bankwanan tafiya da taron karshe.
Bahar sai kusan karfe goma da mintina ta farka cikin samun lafiya da karfin jiki tareda jin ta samu dawowan kuzarinta da nutsuwanta.
Maa sakinah bata dakin dan haka kai tsaye toilet ta nufi tareda brush da wankan da bata samu karfin yi ba dakyau jiyan.
Da ruwan dumi sosai tayi wankan ta fito daure da towel tana nufar gaban mirro Maa ta shigo dauke da tray qarami dayake dauke da ruwan tea na herbs masu kyau da zuma ta nufota tana kallanta a sake tace
'Lokacin shan magani yayi'
Juyowa bahar din tayi ta kalleta tana dan sanyaya fuska sbd bata son maganin,