Kenza eBookz

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 40

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 40

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 40: Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 40. Bahar dinma Kayan jikinta ta sauya zuwa…

4,462 words

Bahar dinma Kayan jikinta ta sauya zuwa doguwar riga Abayar sallah ta tada sallar.

Kusan a tare da maa suka sallame sallar sukai addua sosai dasu azkar kafin suka gama Maa ta kalleta tareda sake rarrashinta da nasihu masu kyau akan hakuri da tawakkali na maraicin da Allah ya kaddaro mata kafin ta fara sake bayyanar mata da labarin asalin waye ayanah a gurin Abaas hakama waye Abaass a gurin Ayanaah dan haka kaman ayanzu da ayanah tasan waye ita tana tabbatar mata da kaf duniya babu wanda zaiso ta kaman yanda ayanah zata sota ta kaunaceta kaman ayanar.

Suna dakin basu fito ba har karfe goma na safe sbd Bahar sai a lokacin baccin ya dauketa me karfin gaske.

Maa sakinah ce ta fito karfe goman ta isa har bedroom din ayanah wadda ta tadda a shirye tsaf idanuwanta sunyi mugun kumbara da ja hakama fuskarta tayi jajir,

Hakuri ta fara bata akan boyewan da sukai mata kafin itama ta dora da tata nasihar ta girman daukan tawakkali akan kowace kaddarar ubangiji tareda tayata murnar kasancewan NUAB mijin Bahar wanda Abaas ya sheda hakan kafin barinsa duniya.

Numfashi me dumi da mutuwan jiki ayanah kawai ta iya saukewa tareda lumshe idanuwanta tana gyada kai kawai bata iya cewa komaiba.

Tenya ce ta shigo dakin ta hada luggages masu shegiyar tsada na tafiyar da Ayanah din zatai a safiyar tareda sultan yasar bama tareda Sultan NUAB ya sani ba har lokacin sbd tsawon daren bai rintsa ba jiran kowane irin kira daga bangaren yake.

Karfe goma da rabi Sultan yasar ya aika kiran Aslam batareda sanin kowaba ya sanar da ita su shirya yau suma jirginsu zai daga zuwa india ya gama hada musu komai batareda sanin kowa ba dan yasan komai da suke ciki hakama bayason kowama ya sani dan haka kai tsaye su ya fara tabbatarda barinsu boyem kafin shima karfe sha daya jirginsa ya daga da Ayanah batareda sanin NUAB ba wanda Ayanah din tayita kiran wayarsa bata shiga kuma bata cikin nutsuwan da zata iya aikawa kiransa dan ko magana kwata kwata batason yi idanuwanta da ruhinta babu abinda yake tsananin kewa da so kamar isa qasarta garinta cikin gidansu a gaban kabarin iyayenta da dan uwanta.

Daga ita sai sultan din sai tenya da wasu bayinta biyu sai kuma securities din Sultan din masu karfin gaske.

Suna ficewa daga masarautar motocin da suka dauko yunar da matarsa Zuhrah ghaz suna isowa gate din shigowa masarautar suka shigo cikin nasu securities din tareda babban danta 'dan uwan haihuwan Leylah Shuraim boyem.

Shigowansu masarautar wadda take da dibbin tarihi me girman gaske a rayuwar zuhrah da yan uwanta ya saka jikinta daukan wata irin rawa bugun zuciyarta na qaruwa da nauyin kirji idanuwanta sukai jajir,

'Danta shuraim dake gefenta juyowa yayi a natse ya kalleta cikin sanyi da nutsuwa sbd shine kadai yasan asalin tarihin mahaifiyarsa data fada masa a lokacin daya fahimci tana cikin quncin dayake ganinta a ciki tin tasowansa bai huta ba saida yasan tarihinta kuma yayi alkawarin sadata da yar uwarta wadda dokar mulkin boyem ta rabasu sunaji suna gani.

Hannunsa ya daga ahankali ya dora akan hannunta yana kamawa tareda kallanta dan bata nutsuwar abinda yasan tana ji a zuciyarta.

Bude motocin sukai suka fito securities suka fidda kayansu zuwa bangaren masaukin mai girma yunar din.

Suna isa bangaren nasu leylah ta iso bangaren cikin tsananin kewan iyayenta da damuwan datake ciki ta rungume mahaifiyarta tana jero ajiyan zuciya.

Sakin Mum din tata tayi ts juya gurin mahaifinta shima ta dan rungumesa tayi masa varka da zuwa kafin ta koma gurin dan uwanta twin dinta shuraim suka rungume juna yana jin tausayin ganin yanayinta dan kuwa yanada labarin qin karban auren ta da Sultan LEUL NUAB yayi.

Hutawa zasuyi na gajiyan da suka debo kafin neman Sultan NUAB zuwa gobe su tayasa murnar Hawansa mulki dan kuwa suna isowa aka sanar dasu tafiyar sultan yasar dan haka dole zasu jira saiya dawo yanda ma zasu huta dakyau sosai musamman a yanzu da yunar yake shawaran dawowa boyem da zama sbd yarsa da zata zama sarauniyar boyem tinda NUAB ya karbi sarautar mulkin boyem din.

Sai karfe biyun rana baya sallan azahar mai girma sultan LEUL NUAB ya tinkaro bangaren mahaifiyarsa wanda yake tsit ba motsi ko hayaniya ko kadan sbd babu kowa,

Maa sakinah bata bangaren ta nufi bangaren babban store na masarautar gabaki daya dan dauko abubuwan abincinsu da sukai qasa tareda bayin da zasu dauko mata da abinda ake turawa dan daukowa,

Bahar ce kadai a bangaren itama bata wani jima da tashi ba sallah ta fara yi tana idarwa ta fada toilet tayo wanka ta wanke kanta kaman yanda ta saba ta fito ruwa na tsiyayowa daga gashinta ahankali fatarta na daukan ido sbd lafiya da haske.

Towel qarami ta dauka ta goge kanta ra rage ruwan kanta sosai ta ajiye ta nufi gaban mirror ta dauki turare ta shafa bayan ta dan shafa mai kadan tana jona hand dryer zata fara busar da gashinta aka taba kofar dakin a natsen daya sakata juyowa ahankali ta kalli kofar da idanuwanta masu haske da saukai wani laushin baccin data jima tayi sunyi wani ciki cikin daukan hankali.

Bude kofar yayi kai tsaye kaman yanda ya saba tareda sako kai fuskarsa fresh komai nasa kaman bai taba shiga rana ba dan kuwa sosai kwanciyan hankali da hutunsa ya bayyana a tattare dashi,

Dakatawa tayi cak daga inda take tsaye tana kallansa zuciyarta na dan sauya bugawa Shima idanuwansa akanta suka sauka dan haka ya fara kallan dakin a kame da izza baiga kowa a dakin ba sai ita din sbd yaje baiga Ammin ba hakama maa tenya dan haka yayo dakin,

Akanta ya dawo da idanuwansa ya tsayar yana kallan fuskarta data dauke idanuwanta akansa tareda kokarin juyawa tabar dakin ta koma bathroom amma takunsa data ji me cikeda zallan izza da iko ya sakata dakatawa tareda juyowa tana qin kallansa taga ita din yake tinkarowa dan haka ta fara ja baya a natse tana qin dagowa ta kallesa duk da tana jin idanuwansa masu kaifi da azabtarwa akanta,

Bata tsayaba sbd shima din bai tsayaba sai dataji ta isa jikin mirror batada gurin sake motsawa shi kuwa a gabanta gap da ita ya tsaya cak har lokacin idanuwansa masu gasa ruwan jikinta suna kanta,

Qamshinsa ne yayi mata yawan dap hancinta da gangar jikinta bazasu daukaba ta dago ahankali zata kalli fuskarsa sai kuma idanuwanta suka kasa qarasawa ta dauke kai tana kokarin juyawa ya qara taku daya zuwa gareta wanda ya sakata yin baya tana dafa hannuwanta da gaban babban mirror din take hannunta ya taba dryer data dauki dan zafi take tayi saurin sake yar qara mara karfi tana dago hannun da sauri wanda ya kama da hannunsa daya a cikin wata irin nutsuwa da wani irin kallan daya sakata kallansa batareda tasan tayi hakan ba.

Cikin idanuwanta yakewa natsatsen kallo yana shigar da dogayen lafiyayyun yartsun hannunsa cikin nata yana kama yatsar daya dan kone din tareda qarasa matseta jikin mirror din sanyin gashinta yana fidda qamshin man datake wanke kan dashi me sanyin kamshi yana shiga hancinta ya juyar da idonsa akan gashin nata yana binsa da kallo sanyin cikinsa na sake saukar masa a fuska,

Motsawa tayi cikin tsananin sanyi tana kokarin zare yatsun hannunta daga nasa sbd yanda qamshinsa yake shigarta sosai ta dago idanuwanta masu sakasa kallanta ta kallesa zatai magana ya matse inda take jin yar zafin ta kallesa da sauri tana bude baki da sauti me tata kamewan tace

'Kada ka manta nan ba bangarenka bane na Ammi ne kuma a dakin Maa.....

Bata qarasa ba ya sake latsa hannun wanda ya sakata yunqurowa da dan karfin daya hade kirjinta da nasa take ya dago idanuwansa ya sauke mata wani kallan daya sakata kokarin yin baya da sauri tana kokarin faduwa ya tarota da cikin sanyi da kamewa tareda dawo da ita jikinsa ta fado kirjinsu ya hade da kyau suna mannuwa da juna ya a jikin madubin. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee

102 Dago kanta tayi idanuwanta na dan matsewa ta qi yadda ta sake kallansa ta motsa ahankali tana sbd yanda take hade dashi sosai gashi a jikin mirror din suke sosai,

Turesa takeson yi amma yanda suke din hannuwanta ma bazasu iya shiga tsakaninsu ba bare ta iya turesa din dan haka ta daure ta sake dagowa batada xabin daya wuce daga idanuwanta ta saukesu akansa wanda hakan yake jira sbd idanuwansa suna kafe da ita hannunsa daya yana xagaye da ita dayan kuma yana sarqe da yatsun hannunta daya har lokacin.

Kallo daya tayiwa cikin idanuwansa ta cire idonta a cikinsu sbd bazata iyaba bakuma dan komai ba sai dan yanda tsigan jikinta ke tashi daga kallan cikinsu amma bawai dan tsoro ko shakkarsa ba,

Bude baki tayi zatai magana cikin karfin hali da kame fuska maganar Maa ta bayyana daga wajen palon,

Kallan kofar shigowa dakin tayi da sauri kirjinta na bugawa da karfi,

Zamewa tayi kokarin yi amma riqon bame zarewa bane hakama karfinsu ba daya ba duk da ko kwatan rabin karfinsa bai saka ba,

Kallansa tayi cikin ido ta bude baki tace

'Kasan me kakeyi kuwa?

Shigarsa kalman tayi da kyau da kaifi sbd itace kadai take wuce iyakarta gurin fada masa maganar da zata iya zama ajalin wani idan ya fada akansa,

Bai saketa ba ya bude baki yace

'Kinsan waye a gabanki?? Bakinki da kalamanki zasu iya sanadin wainda kike tareda su idan baiyi naki ba akan abinda yake furtawa.....

Turesa take kokarin yi tana dauke kallanta daga kansa da sautin hankali a kwance daga kalamansa da kuma fargaban dawowan maa tace

'A yanzu dai inaga kana buqatar barin dakin nan kafin me shi ta shigo ta sameka a cikinsa sbd......

Bata qarasa ba ya saketa ya juya a natse ya kalli kofar dakin kafin ya kama hannunta ya juya ya nufi kofar da ita zai kira Maa sakinah din ta shigo dakin ta samesa a hakan yanda bahar din take.

Da sauri taso kwacewa amma ya riqeta da kyau yana nufar kofar batareda kunya ko daya ba dan baima santa ba,

Ganin da gaske yakeyi kiran maa din zeyi ta samesu a hakan tinda tasan zai iya a yanda tasan hankalinsa dan haka da sauri suna kaiwa kofar tasha gabansa tareda dafe kofar da bayanta tana hanasa budewa idanuwanta duka biyu akansa tana kallansa da wani irin yanayin jin zafi,

Daga kafafunta ya fara kallanta zuwa samanta yana qarewa lafiyayyan farar fatarta kallo kafin ya tsayar da idanuwansa akan sarkar kafarta asalin farar azurfar data gada ta mahaifiyarta me tsananin sanyin kyau da rashin ado sosai data zauna da kyau a farar kafarta wadda itace abin farko daya fara gani akanta a ranar farko ta haduwansu a duniya a kuma ranar data zama ta farkon ta zama ta aurensa daya doru akanta,

Hannunsa daya ya miqa zai matsar da ita ya bude kofar ta miqa hannunta ta riqe nasa din batareda tinanin komaiba,

Hannunta daya kama nasa ya saukarwa idanuwansa ya kalla dakyau cikin nutsuwa da yanayin da bata iya gane komai akansa kafin ya dago ya zubawa fuskarta idanuwansa da suka jikinta da babu kaya jin wani irin sanyi na feso mata kaman ana watso mata ruwan sanyi.

Sakinsa tayi a hankali tana dauke idanuwanta akansa sbd ganin irin kallan dayake binta dashi ta sake tare kofar tana jinginar da bayanta jikinta tana dannewa idonta na qin kallansa zuciyarta har lokacin bugawa takeyi sbd idan ya kira maa dakin a cikin wannan yanayin datake kuma tareda dashi a dakin bazata iya kallan Maa din ba dan haka gwara tinda tasan sake komawa maa din zatai dauko wasu kayan idan sun sake juyawa sun koma saiya fice ta shirya batareda maa tasan ya shigo dakin ya sameta a hakan ba harma ya shigo an rufe kofa.

Yanda ta tare kofar ya tana dauke kanta daga kallansa ya sakasa rankwafowa sosai yana dafe jikin kofar da ita gabaki daya,

Ba tsammani taji saukan dumin numfashinsa a fatar saman kirjinta da wuyanta har gefen kunnenta wanda ya sakata juyowa da dan sauri sedai fuskarsa na gap da tata ashe take fuskar tasu ta hade hancinsu na haduwa tayiwa qamshinsa da numfashinsa wani shaqa me karfi batareda saninta ba take ta rufe ido tana fidda wani numfashi daya saka kirjinta yin sama tana qanqame hannun kofar ta bayanta da hannunta daya daya tsananin fara rawa.

Nata Numfashin data fitar shima ya shigesa sosai har cikin kansa da kwakwalwansa yaji saida idanuwansa suka nuna hakan dan haka ya dauke idanuwansa daga kanta yana buqatan ficewa sbd abinda yake yawo a cikin kansa da kirjinsa harma da zuciyarsa.

Hannunsa daya ya saka a bayanta ya kama hannun kofar ta sake dora hannunta akai itama tana dagowa ta kallesa idanuwanta suna tausasa da yanayin damuwan halinda zata shiga idan yayi mata hakan sbd maa din na nan har lokacin dan suna jin maganarta kaman waya takeyi.

Kafesa da idanuwanta tayi wanda yanajinsu akansa amma yaqi kallanta dan hakan nada hadari a lokacin dan haka kokarin janyeta yayi dan ficewa yakeson yi kai tsaye a dakin kwata kwata,

Wasu hawaye ne suka ciko idanuwanta ta dan sake dafewa tana kasa dauke idanuwanta akansa ta bude baki cikin wata irin sanyayyar murya me tsananin taushi da magiyar da batada zabi bayan yi tace

'Dan Allah kada ka......

Bata qarasa ba ya riqota gabaki dayanta da hannuwansa biyu ya ciro daga jikin kofar ya maida jikin bango ya jinginar da ita yana dafeta da kirjinsa cikin wata irin yanayin daya sakata rintse ido zuciyarta na harbawa da karfi ta qanqame hannuwansa batareda ta sani ba sbd tinanin jefar da ita zaiyi.

Numfashinsa ne me tsananin dumi yake sauka a fatar fuskarta da wuyanta sbd fuskarsa dake hade da tata fatarsu na gogan juna da jin dumin fatan tana rata dayan fatar.

Kirjinsa dayake hade da nata ya saka numfashinta sauyawa yana fita daqyar dan haka itama kai tsaye nata Numfashin saukar masa yayi a gefen kunnensa wanda take ya saka fuskarsa gabaki daya fara yin jan daya sakasa sakinta kai tsaye batareda ya juyoba ya bude dakin ya fice.

Yana fita kai tsaye barin bangaren yayi sbd babu wanda zai gani a yanayin da fuskarsa din take.

Yana fitowa Maa sakinah data san yana bangaren sbd taga aleey shiyasa ma taqi shiga ta qirqiri wani aikin tinda sai angama juye wancan din kafin su sake komawa.

Ganinsa babu rahama a fuskarsa hakama baida Alama ko fuskar magana da kowa ko tsayawa ya sakata bata ma fito daga kitchen din datake hangosa ba ta kyalesa.

Aleey ma na ganinsa kai tsaye ya sauke kai suna bin bayansa ba kalma ko daya data fita.

Aleey daya samu labarin Sultan me murabus Yasar yabar qasar tareda Ammi a ranar hakama ya fitar da Haile da yayanta duka daga boyem sun daga zuwa wata qasar da bai gama tabbatarwa ba tukuna, yana son sanarwa Sultan LEUL din amma ganin yanayinsa ya sakasa shiru tukuna sbd labarin zai tada fushinsa me tsananin gaske dan kuwa a yanzu dayake sultan me mulkin boyem shine yakeda cikakken ikon mahaifiyarsa fiyeda sultan yasar sbd babu igiyoyin aure a tsakaninsu dan haka baida cikakken ikonta duk da tana matsayin wishmah dinsa a yanzu shi danta dayake sultan ma zai iya sauketa matsayin ya kuma yiwa sultan yasar iyaka da ita wannan haka yake dan a yanzu duk abinda sultan yake nema a gareta saida izini da umarnin 'dan SULTAN LEUL NUAB wanda zamowansa sultan duka ya basa wannan ikon akan uwarsa da batada iko da yancin kanta a masarautar har yanzu, Duka hakan ya sake tabbatuwa ne sbd ta kasance mahaifiyar Sarki me mulki a yanzu dan haka bazaayi ikonta a matsayin imebēti ko wishmah ba darajarta ta uwar boyem ce gabaki daya, A yanzu itace uwa mafi daraja a kaf boyem sbd itace uwar me mulkin.

Bayan isowansu bangaren NUAB da aleey dake bayansa ne kadai suka shige palon sa na farko,

Tsayawa aleey yayi daga bayansa bayan ya zauna ya dan sassauta tareda tausasa sautinsa yace

'Sultan me murabus baya qasar baifi awanni hudu da dagawaba shi da Ammi wanda a lissafin dana dora tafiyar ina kyautata zaton Anjom zai tafi da ita wanda kuma hakan na nufin yasan komai akanta da 'yan uwanta a cikin video din Abaas......

Wani daci da radadin zuciya me zafin gaske ne ya ratso tin daga kansa zuwa zuciyarsa ya dago idanuwansa da har lokacin basu dawo daidai ba bacin rai na qarasa sauyasu yace

'Tayaya yasan da video din Abaas??

Dan sake sauke numfashi aleey yayi yace

'Shine ya wuni tareda ita jiyan a lokacinda take cikin halin sanin rasuwar har dare yana bangaren'

Kafe Aleey din yayi da idanuwansa yana kallo take aleey yayi qasa da nasa idanuwan sbd yasan yayi kuskuren rashin fada masa tin jiyan wanda shi kuwa yayi hakan ne sbd NUAB din bazai taba iya ganin kuka da dacin zuciyar mahaifiyarsa ba shi kuwa Sultan zai iya tsayawa ya hadiye kowane irin baqin cikinta da kukanta dan dole itama a wannan lokacin tana buqatan daya daga cikinsu biyun ko 'danta ko sultan din su kasance da ita.

Dauke idanuwansa yayi daga Aleey din yana miqewa tsaye yabar palon zuciyarsa na tafasa da abinda sultan din ya aikata dan yasan yana sane da babu me ikon mahaifiyarsa yanzu sai shi sbd haryanzu ita mallakar boyem ce tsawon shekarun bata taba samun yantawa ba daga kowa dayake da ikon yantata a yanzu kuwa Allah ya basa damar a hannunsa. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee

103 Bahar ma yana ficewa daga dakin wani irin damuwa da takaici ne lokaci daya suka danne kirjinta sbd Maa sakinah zata gansa kenan,

Juyawa tayi daga bakin kofar ta isa gurin closet din dakin da wani irin sauri jikinta har rawa yakeyi sosai ta saka doguwar riga baa natse ba ta koma gaban mirror da sauri ta kashe dryer din ko busar da gashinta bataiba ta daure gashin a hakan ta saka mayafi me girma ta rufe kanta tazo ta zauna da sauri tana zaunawa Maa sakinah na shigowa dakin dan haka ta kasa dagowa gabaki daya.

Maa sakinah ma bata iya kallanta sosai ba ta qaraso tana janyo mata wani zancen batareda tayi mata maganar ganin NUAB din ba sbd jin qamshinsa a dakin ya tabbatar mata da daga dakin nata ya fita.

Ganin firar ba yi zatai ba sai kawai maa din ta sake miqewa ta fice tafiya aikin dayake gabanta,

Tana ficewa Bahar ta dago a sanyaye tareda sakin ajiyan zuciya me dumi tana jin takaicin rayuwar datake samun kanta a ciki da takaicin bayyanarsa a inda take dan kuwa nesancinsu shine alkhairi a gareta ita kam sbd bata buqatan bayyanarsa a koina na rayuwar datake yi a yanzu.

Kasa tashi ma tayi kwata kwata daga inda taken bare qarasa shirinta datai cikin tsantsar gaggawa,

Acan nasa bangaren kuwa yana shiga ciki wayarsa ya fidda a natse yana zaunawa kan sofa ya saka kiran Amminsa,

Qin shiga kiran yayi sbd wayarta dake kashe kwata kwata,

Magana yake tsananin son yayi da ita dan jin yaya tafiyar take hade da sultan wanda yakeda tabbaci tabbas sultan dinne yayi ikon tafiyar da Ammin batareda saninsa ba kuma batareda ya bari Ammin ta sanar dashi ba,

Sake kiran Ammin yakeyi idanuwansa a rufe da bacin ran tafiyar da sultan din yayi da ita amma har lokacin bata shiga,

Bayajin zai iya kiran sultan dan baima da tabbacin ko akwai numbernsa a cikin wayar dan haka ya jefar da wayar a gefensa yana 'dan rufe idanuwansa sbd sassauta bacin ransa ya kwantar da bayansa jikin sofa.

Maa sakinah aikinta ta ringa yi hankali kwance bama tareda tasan Zuhrah na cikin masarautar ba ta iso har dare suna daki ta gama shirin kwanciya tana zaune tana waya da tenya akan sun isa amma basu kai ga isa can cikin garin Anjom din ba sai washe gari zasu bar masaukinsu su isa tukuna.

Bahar ma tayi shirin kwanciyanta tana gefen maa din a zaune tana sauraron wayar datake yi tana jin inama itace taje anjom din koma inama ace da itane aka tafi,

Maa sakinah na ajiye wayar ta kalleta tace

'Maa zasu dawo yaushe ne? Zamu tafi muma wata ran amma ko?

Murmushi Maa tayi me sanyi tana ajiye wayarta a gefe zatai magana aka kwankwasa kofar dakin ta juya tana kallan kofar sbd badada wanda zai iya zuwa gurinsu a yanzu din.

NUAB ne inaga' Maa ta fada tana miqewa tsaye ta nufi kofar sbd harsun dan rufe da key daga ciki,

Tana nufar kofar Bahar ta miqe tana kokarin barin gurin zata nufi bathroom ta shige har sai yabar dakin tukuna,

Sakinah data lura da kaman NUAB din bahar zata gudarwa murmushi tayi tana qarasa isa kofar ta bude kai tsaye murmushinta na qaruwa sedai kuma wanda ta gani bakin kofar dakin ne ya saka komai nata da yawun bakinta tareda bugun zuciyarta tsayawa cak idanuwanta na tsayuwa qyam da wani irin hawayen dake cikosu hannuwanta da kafafunta na nauyi da sanyin da suke kokarin kasa daukanta ta bude baki da qyar ta iya lalabo kalman 'ZUHRAH' ta fada cikeda tsananin mamaki da shock.

Bahar ma da sunan ya sauka kunnuwanta tsayawa tayi cak daga inda take zuciyarta na wani irin muguwan bugawa tareda sarawan kai,

Kasa juyowa tayi saida Maa sakinah ta sake maimaita kalman sunan zuhrah din wadda itama take a kafe bakin kofar ta kasa motsawa idanuwanta jajir da wasu irin hawayen da rabon data fiddosu tin ranar da aka rabata da ayanah da sakinah din,

Sakinah take kalla wadda itama ita din take kalla tana sake jin gabaki daya jikinta yana mutuwa duk da sunsan zuhrah na raye amma sun cire rai daga sake haduwa da ita,

Akan Bahar data jiyo a sanyaye da mutuwan jiki zuhrah take maida idanuwanta da hawayen ciki suka gangaro daga saukan idanuwanta akan 'yar Abaas dinta jininta rabin jikinta..

Takawa tayi ahankali jikinta na tsananta mutuwa me tsanani ta isa gaban Bahar din leylah na biyeda ita cikeda mamakin dayake sakata jin kishin Bahar na tsanantar mata,

Tana isa tsayawa tayi tana kallan Bahar din da dukkanin idanuwa da nutsuwa da imaninta kafin takai hannunta dake rawa ta kamo hannun bahar din ta dago ta zubawa numbarn Abaas dake hannunta ido wani irin kuka me tsananin zafi da tsimin gaske ya taho mata ta rungume Bahar din da karfi cikin jikinta tana qanqameta tsamtsam a jikinta tana cewa

'Wannan jinin Abaas dinmu ce' Ke jinin ghaz ce, Kece ayanar da Abaas yakeda burin haifowa ayanah ghaz, Ke jininmu ce, Ina Abaas? Ina Abaas???

Tambayarta ta karshe ce ta saka Bahar sauke numfshi me zafi a jikin zuhrah din tana rintse idanuwanta da sukai jajir kuka ma ya kasa fitowa a cikinsu,

Sakinah datake a tsaye jiki a mace qarasowa tayi gabansu tana kasa dauke kallanta daga zuhrah wadda ta saki bahar ta juyo gurin sakinar ta rungumeta da karfi cikin tsananin kewan shekaru da kauna me karfin gaske sbd sakinah ta jima da zama jininsu.

Leylah kasa motsawa tayi ganin abinda yake faruwa tsakanin mutane biyu da bataso da mahaifiyarta dan kuwa sam bata kaunar maa sakinah sbd yanda take bayyana kaunar bahar fiyeda kowa a bayyane.

Bahar komawa gefe tayi ta rabe tana kasa cewa komai kanta a qasa,

Bahar din ce ta fara silalewa ta fice daga dakin kafin leylah ma fito cikeda zullumi sbd alamu suna nuna mata alaqa ce me karfin gaske a tsakanin mum dinta dasu ayanah ghaz wadda sunansu yaxo daya.

Zaunawa sukai hannuwan zuhrah na qanqame dana sakinah tana kukan rabonta dasu a rayuwarta da itama har wannan lokacin bata samu cikakken yancin da zata taho da yar uwarta ba sbd doka da yancin da Ayanah bata dashi tsawon shekarun,

Basu taba neman juna ba sbd zazzafar dokar data rabasu suke akanta,

Sakinah ce take kukan farin cikin daya gama kashe mata jiki ta fara bawa zuhrah labarin halinda ake ciki na rasuwan Abaas da tafiyar ayanah zuwa gida jikinta a mace da damuwa,

Kuka sosai zuhrah takeyi jikinta na rawa sosai ta qanqame hannuwan sakinah tana jijjiga da tashin hankali da baqin ciki tareda damuwa da tausayin kansu me tsanani sbd a yanzu su biyu kadai suka rage a jikin ghaz sai Bahar.

Tsawon lokaci suka dauka sosai har tsakar dare basu fitoba sai daga baya shima zuhrah kai tsayace tace anan zata kwana tareda bahar.

Leylah datake neman sake rikicewa a rudani zaunar da ita Zuhrah tayi ta fayyace mata komai wanda ya sakata shiga tashin hankali da farin ciki harma da baqin ciki duka a lokaci daya,

Farin cikinta jin yanda matsayinta yake a gurin Ayanah ghaz da NUAB wanda dole take da a kaunaceta kauna me karfi harma fiyeda bahar sbd ita ana ganin idon mahaifiyarta,

Baqin cikinta kuwa shine kasancewan bahar ce jinin abaas ba ita ba sbd kusanci da kaunar dake tsakaninsa da ayanah kenan yafi yawa akan wanda yake tsakanin mahaifiyarta da Ayanaah ghaz wanda shima bazata yadda ba bazata iya hakura ba kome zai faru ita tana son NUAB kuma tana son kasancewa matarsa sbd itace ta dace dashi ita datai karatu me zurfi ta waye ta taso cikin daula da arziki kamarsa,

Tashin hankalin data shiga da tsoro me tsananin gaske kuwa na jin tarihin da ko amafarki bata fatan ya sameta dan kuwa batajin har abada ma zata iya rayuwa a inda baa cikin daula irin boyem ba. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee

104 A bangaren wishmah din zuhrah ta kwana tareda bahar itama batareda ta rintse ba tin daga farkon daren har qarshensa sbd rasuwan Abaas tayi mata irin jijjigar dataiwa Ayanah dan haka itama gari na wayewa ta koma ta sanar da Mai girma yunar tana son zuwa asalin qasarta wadda a yanzu ta samu wanda ya san inda qasar take tinda a baya itama nata 'dan yayi kokarinsa bai samar da inda take ba,

Baiyi mata musu ba ya bata damar tafiya tareda cikakkiyar iko itada shuraim da Leylah,

Maa sakinah ce ta kira NUAB ta sanar masa zuwan Zuhrah a garesu wanda shima yayi shock da jin hakan duk da alkawarine da yayi na hadasu itada Amminsa amma tinda tazo shi kuma zai isar da ita Anjom su hadu a asalin qasarsu cikin gidansu inda iyayensu da dan uwansu suke a kwance nurat ce kadai babu a cikinsu yanxu wadda sukewa fatar rahama.

Ko da ya iso bangaren Bahar na jin qamshinsa ta silale tin bai shigowaba ta koma dakin maa sakinah tai kwanciyanta bata fitoba ba har saida ya gama abinda yakeyi ya fita cikeda samun nutsuwan mahaifiyarsa zata kasance da yar uwarta a yanzu.

Aleey ne ya fara musu shirin tafiya anjom din su uku Mum zuhrah,shuraim da leylah sai securities biyar da zaa hadasu dasu,

Readers Also Read