Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 41
Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 41: Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 41. Leylah jin bada NUAB din zaa tafi ba hakama…
4,439 words
Leylah jin bada NUAB din zaa tafi ba hakama bada bahar ba sai taji kwata kwata batason tafiyar hakama ita tsoro ne me tsananin gaske a ranta na ziyartar garin sbd ganin takeyi kaman zaa iya sacesu a lula wata qasar dasu a siyar kaddararsu ta sauya sbd suka su mum din ai sunada daula da sarauta aka sacesu.
Shuraim daya lura da yanayinta ne ya dan kwantar mata da hankali sbd zuwan nasu yanada mahimmanci tinda shiga takeson samu da damar da zata auri namijin dayake zuciyarta,
Basusan yariga da ya auri bahar ba dan haka sunada tabbacin zai auri leylah din koda ma ya auri bahar dinne ai ya kasance itama zata iya shiga,
Shuraim baida mugun hali ko daya halayensa daban suke dana yar uwar tasa sedai shikuma ya fita tsananin kishi da tsananin so sbd yanda yake kaunarta da mum dinsu komai yana iya yi akansu hakama kowa yana iya batawa akansu shi haka tasa kaunar da halin yake sam akansu baya duba daidai da abinda ba daidaiba amma bayan wanna baida munin dabia da hali ko daya hakama shima yayi kararu sosai me zurfi fiyema da leylah din sbd a yanzu yana akan matsayin cikakken likita ne.
Kafin su tafi irin kaunar da zuhrah kewa Bahar itama yasake gigita zaman lafiyar zuciyar leylah duk da tasan kowane irin so mum dinta zataiwa bahar bazai taba wuce wanda take mata ba ita data haifa amma sam bata jin zuciyarta daidai akan irin kaunar da dukansu suke mata musamman ta Ayanah datafi komai gigita mata zuciya sbd a bayyane yake ayanah zata iya bada rayuwarta akan bahar din.
Suna wucewa shima NUAB ya shiga wani irin busy na harkar sarautar boyem din daya buqaci dukkanin dokoki da sharudda da kaidojin mulkin msarautar boyem din masu zafi a gabatar masa dasu kaf da tarihinsu da inda suka samo asali da kuma hukunce hukuncensu sbd yana son shafesu kaf ya budewa boyem sabon tsarin mulkin da zai tabbatar musu da shine LEUL BOYEM yake mulki hakama har abada wainda zasuyi mulki bayansa zasu samu yancin da sarakunan baya da kamanninsu basu samu ba,
Manyan fada cikin tashin hankali da tsaka me wuyar wannan tsari da bayanan daya buqata wainda zasu zaqulo asalin asalin boyem suka fara shirye shiryen wannan umarnin nasa da allah kadai yasan waye da waye zasu rasa matsayi da sunansu da zuriarsu har abada.
Aleey ma kusan yafi kowa zama busy sbd shine zai tabbatarda hada kowane bayani da tabbatarda gaskiyarsa da komai tareda fidda duk wani hukunci akan hakan da sultan LEUL boyem zai fitar tareda sabbin dokokin mulkin qasar wainda gabaki daya boyem da duniyarta suke jira cikin zullumi da fargaba da jiran tsammani.
Bahar ma da maa sakinah hankalinsu kwantawa yayi basa cikin damuwan komai allah ya sakowa bahar din dangana da samun nutsuwa sbd koba komai ta hadu da jinin Abaa dinta biyu da suka rage a duniya da kuma yake fatar ta hadu dasu tayi rayuwa a cikinsu sbd yasan ko da rayuwarsu zasu bata kariya da duka kaunar datake nema da gata a duniya.
Maa sakinah ma sakewanta tayi tana cigaba da kulawa Bahar tareda tattalinta da gyara abarta sbd yanda itama bahar din ta gashi hankalinta ya kwanta bata ganin NUAB sbd bai sake shigowa tin ranar dan busy din dayayi sosai bai nemeta ba kaman yanda itama ta tattarasa ta ajiye gefe.
Babu abinda Maa sakinah take so a yanzu bayan samar da ilimin boko me kyau da zurfi ga bahar amman batada daman fadar hakan dan haka ta tsaya a iya koya mata dan abubuwan data sani wayewa da sauransu duk da nutsuwa da wata irin kamun kai da izzar dake cikin jininta ta sarautar data gada ya saka baka iya gane batada irin wayewan da zurfin ilimin boko yake bayarwa. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee
105 Acan boyem kuwa tinda su Ayanah suka isa gabaki daya rayuwarta ta dawo mata baya farko,
Tayi kuka, tayi baqin ciki, tayi inama baya ta dawo, tayi baqin cikin ganin wannan ranar data wayi gari ita daya batareda kowa nata ba a cikin jinin ghaz sedai yayansu,
A kabarin da akaiwa iyayensu daga baya a cikin masarautar ghaz din da kabarin abaas dayake jere dana iyayen nasu ta durkusa tayi musu addua me tsayi tana wani irin kukan daya saka sultan janyeta suka bar gurin,
Jamaar anjom tsoffinsu da sukasanta tin a baya wainda allah yayi suna raye dama wainda basu santa ba sunyi farin ciki me tsananin gaske na ganinta,
Sun taru sunyi jimami sun cika masarautar sun mata gaisuwan iyayenta da abaas tareda kokawa juna kaddararsu data raba kowace ahalin datake anjom babu gidan da bai samu mummunan kaddarar shekarun bayan ba na iftilain daya fadowa anjom din.
Har tsakiyar dare sosai suna garin sai da sukai asuba tareda jamaar garin suna kokarin bankwana su tafi Su zuhrah suka iso.
Isowan zuhrah ya saka sultan barin Ayanaah a garin ya koma jirgi dan kuwa suna buqatan lokaci me tsayin gaske a cikin gidan da shine asalinsu shine abu na karshe daya rage musu na ahali da asalinsu.
Ayanah a lokacinda ta hada idanuwanta da zuhrah bayan shekaru masu tsayi na rayuwarta kasa motsi tayi bare cewa komai hakama kukanta daukewa yayi tsaf sai ajiyan zuciya kadai ta iya ringa saukewa tana bin zuhrahn da kallo ita kuwa kuka takeyi me tsananin gaske tana kasa fuskantar ayanah daga qarshe zubewa tayi a kan kafafunta tana kama kafafunta tana kuka me tsanani.
Tsawon lokaci ayanah din bata motsa ba tana jin kukan yana ratsata kafin ta motsa a hankali ta kama zuhrah din ta miqar da ita tsaye ta rungumeta ahankali jikinta a matiqar sanyaye ta bude baki da sautin daya sake saka zuhrah mummunan yanayi tace
'Yene Zuhrah, Daga karshe kin dawo gareni Zuhrah, Allah ya bamu ikon qarasa rayuwarmu a cikin ta juna a tare tareda 'yayanmu'
Rungumeta zuhrah tayi itama da karfin gaske suna qanqame juna da tsananin karfi zuciyarsu na samuwa da cike gurbinda har abada insha Allah ya cike kenan.
Kabarin iyayensu da dan uwansu suka koma kafin suka sake komawa dakin mahaifiyarsu anan suka shige dan anan zasu sake kwana kafin su koma asalin birnin qasar inda sultan yake jiran Ayanah a lafiyayyar daular daya sauka.
A nan anjom suka kwana wanda kafin safe leylah ta kusa zarewa ta rasa hankalinta sbd mummunan halinda takejin tana cikinsa na rayuwa a garin dama inda suke din dan kuwa a maqale da mahaifiyarta take sam ta fice hayyacinta.
Babu wanda ya maida hankalinsa akanta a cikin su biyun sbd abinda yake kansu shine ya damesu,
Fuskokinsu da idanuwansu kadai zaka kalla kasan suna cikin mugun hali sbd sun kumbura sunyi jajir ba kyan gani hakama ko muryoyinsu basa fita.
Daqyar leylah taga gari ya waye karfe tara tayi anzo daukansu da securities din sultan da wasu mahaukatan motocin da suke iya shiga kowane daji da bindigogi.
Ta riga su Ayanaah fitowa ta fada mota da sauri tana sauke ajiyan zuciya ta kalli Shuraim dayake gaba dan shima bai kwana anan ba komawa yayi yau aka dawo dashi,
Cikin wani irin yanayin dayake fitowa daga qasan zuciyarta ta kalle shuraim bayan sun zauna a cikin lafiyayyan jirgin ruwan dazai bar dajin garin gabaki daya dasu ta sauke ajiyan zuciya tana kallan shuraim tace
'A hakan kake tinanin zan iya hada miji da illiterate macen data taso anan? Tayaya ma zata iya rayuwa a tsakanin ni na SULTAN din da mukeda tarin ilimin da batada shi? Bama zan iya zama da jahila ba sbd ilimin nawa 'yayan dazan haifa.....
Shuraim ne yayi saurin dora hannunsa akan nata cikin wani irin salon da Ammi data tsare leylah din da ido bazata gane ba ya dan dakatar da ita yana fuskewa.
Ayanah shiru tayi tana kallan Leylah cikin sanyi da nutsuwa hakama wani nauyi yana danne kirjinta da batajin komai a cikinsa yanzu bayan zallan kauna da soyayyar bahar wadda itace zata kasance uwa kuma ubanta.
Zuhrah ma da zancen ya ratsa zuciyarta da kaifi tareda rakaici da baqin cikin jin hakan daga bakin 'yarta akan 'yar dan uwanta kallan ayanah tayi a sanyaye sedai ganin ayanah ta dauke idanuwanta ahankali akan leylah din batateda tace komaiba ya saka itama tayi shiru kowama yayi tsit har suka isa ba wanda yace kala.
Suna isa kai tsaye masaukin sultan aka nufa da ayanah su zuhrah kuwa a ranar suka bi jirgin dare suka koma.
Ayanah tinda ta dawo sultan ya fuskanci damuwa sabuwa dake tattare da ita dan haka a daren bai samu nutsuwa ba saida yaji damuwarta wadda kai tsaye ta sanar masa tanason bahar tabar boyem ta tafi wata qasar karatun datake son ta sauya rayuwarta ya bata yancin zabar raayin auren NUAB ko sabaninsa.
Sultan daya fahimci daci da radadin dayake zuciyarta akan bazata taba iya barin bahar ta samu tangardar rayuwa ba NUAB yace ta fara sanarwa,
Girgiza kai tayi cikin nutsuwa tareda bude baki tace
'Nice zan dauki nauyin karatunta da kaina banason NUAB yayi mata komai akan duk abinda ya shafi neman iliminta'
Sultan hakan shine yayi daidai da nasa raayin akan Bahar wadda Ayanaah zata tsayawa tai mata gatan komai kaman yanda Kowa iyayensa ke tsaya masa su basa ilimin daya kamata dan haka kai tsaye ya kira kadir ya bada umarnin komai na bahar da karatunta ya kammalu a cikin qanqanin lokaci.
******Ayanah batai raayin baro kasarta ba a kwanaki kadan dan haka kusan sati uku suka share a qasar batareda kowa ya taba samunsu a waya ba sbd hatta tenya su Zuhrah tabi ta koma.
A bangaren kadir ma cikin wata irin rashin bata lokaci da tsayuwa cak akan umarnin sultan din ya nemarwa Bahar kusan komai da ake buqata na karatu a qasar UK sbd sunada manyan connections.
Sai da sukai wata guda cif a qasar suka diro boyem wanda yayi daidai da lokacin tafiyar bahar da NUAB baisan da itaba hakama daidai dawowan haile da yayanta hakama tsawon wannan lokacin BAHAR da NUAB din basu taba haduwa ba.
A ranar da suka dawo a ranar saura kwanaki kadan a tafiyar bahar din wadda zata tafi tareda maa sakinah a gidan da aka tanadar musu acan domin rayuwa a cikinsa.
A daren Ammi tana isowa ta kira NUAB ta sanar dashi wanda yayi shiru ya rasa abin cewa zuciyarsa na wani irin daukan zafin dayake ciki tsawon wata gudan nan da sukai basa nan sbd sultan daya gama shan gabansa akan mahaifiyarsa.
Baicewa Ammin komaiba akan tafiyar haka ya miqe ya tafi zuciyarsa kaman zatai bindiga sbd yasan koma menene da ina wannan tsarin ya fito ya fito ne daga mahaifinsa dan haka shima zai san ya tabasa,
Yana dawowa bangarensa kai tsaye aleey ya kalla da jajayen idanuwansa ya basa umarnin a nemawa Ammi komai na tafiyar bahar da ita zaa koma UK din tabar boyem har sai bahar ta kammala su dawo tare.
Kallansa aleey yayi da dan sauri cikin fargaba da mamaki amma baida ikon fadar komai haka dan haka cewa yayi angama kawai ya juya fice yana daga wayarsa dan samar ma da bayanin komai akan tafiyar ta bahar da inda zata zauna da inda zatai karatun wanda ba iya Ammi kadai ba hatta su zai samar da komai na tafiyarsu ya ajiye sbd daga yanzu qasar zata zama gurin zuwansu kowane lokaci. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee
106 Bahar har zuciyarta tafiyarta karatun yayi mata daidai tareda bata dukkanin nutsuwan datake jin tana buqata na rayuwa a wajen Boyem sbd a cikin wani irin tsananin tsaro suke rayuwar babu yancin shan iskar rayuwar da duk kake buqata,
Damuwarta daya ce rabuwan da zatai da Ayanah wadda a yanzu kauna ce me karfin gaske a tsakaninsu sbd ita kallan Abaa dinta takeyi mata kaman yanda itama ayanah din kallan Abaas dinta takeyi mata hakama a yanzu da suka san juna suke tare da juna suke kuma kaunar juna a bayyane a zahirance babu shamaki ko daya,
Kauna ce ta asalin bayyane dake cikin jininta ayanah kewa bahar din wadda kusan a hankali duk wanda yake tareda dasu a masarautar suke sani,
Itama bahar a yanzu tana kokarin sakewa da Ayanah din kaman yanda ta sabu da maa sakinah dinta dan bawa ayanah din dukkanin sanyin zuciyar datake buqata daga gareta,
A bangaren daya tenya da Maa sakinah gabaki daya soyayyarsu suma da kaunarsu akan bahar din take duk da suna nunawa Leylah tata kaunar sosai itama amma sbd kaunar da sukewa Bahar ta bangare uku ce zuwama hudu sai tata din tafi bayyana,
Ta farko asalin kaunar mahaifinta ce, Ta biyu ta zamtowanta mata a gurin 'dansu da suke tsananin so wato sultan LEUL, Ta uku kasancewanta Rabin zuciyar ayanah da bata hada da komai, Saina karshe shine zamtowanta marainiyar da batada uwa batada uba saisu,
Ita kanta Zuhrah kauna me karfi mara sirki takeyiwa bahar din wanda taso saka hannu sosai akan bawa bahar din ilimi da inganta rayuwarta amma Ayanah ta dakatar da kowa daga hakan bata son kwandalan kowa a gurin bawa Bahar din ilimi sbd har abada tako wane bangaren bata son ayiwa Bahar gorin komai na rayuwa matiqar dukiya zata nema ta samar mata dashi koma menene.
Hakan ya saka ta sake ta fidda dukiya me yawan gaske dan sauya rayuwar 'yarta zuwa duk inda 'ya mace me gata zata kai,
Bedroom daya aka warewa Bahar din acikin bangaren itama aka gyara matashi da komai sabo me tsadar gaske da duk wani jin dadi da tsarin da zai tabbatar maka daka shigo dakin mace yar gata me aji,
Closet din gaske aka kira masu shiryawa suka shirya mata da wasu irin designers na kasashe daban daban fiyeda a tsaya kirgawa,
Undies da kayan bacci ma haka aka taho dasu masu kyau da tsada ba adadi aka jere kafin suma designer shoes and hand bags harma suitcases na tafiya da tirarika da wasu duk abubuwan da akasan mace na buqata an kawo an jere su a dakin an kammala mata komai tamkar ba wadda zatai tafiya ba tabarsu kuma taje can a siya wasu kayan,
Ba iya kayan designers aka tsaya ba hatta sitirun sarauta dana Al'ardarsu an kawo su masu tsada an jere mata su tareda Tirarikan da Maa tenya ta hado mata da kanta wainda suna kama jikinka to shikenan ka gama zama mai ratsa zuciyar duk wanda zai shaqa qamshin wanda komai na irinsa akwaisa zaka samu a gurin (SHUWA INCENSE AND MORE 07042293387)
Maa Sakinah ganin rayuwar Bahar ta sauya sawu zuwa kyakkyawar rayuwar da kowane dan gata me uwa da uba zai samu ya saka zuciyarta da hankalinta kwanciyan da a yanzu babu abinda take so da buqata arayuwa bayan gamawa lafiya.
Ayanah ma kasancewan Bahar din a rayuwartata ya saka dangana me karfi da tawakkali da cire dukkanin wani qunci a ranta suke shigeta tasan bazata taba manta rayuwar data fito da kaddara me girma da muni ba amma kuma samun Bahar ya lullube mata kaso me girma a cikin baqin ciki da quncinta ga kuma ganin Zuhrah a tareda ita da 'yayan Zuhrah dan haka ta rungume sabuwan rayuwan data zo mata da hannu biyu dan hana 'yayansu shiga damuwa da quncin da zasu ringa fuskanta da gani a tattare dasu.
Zuhrah da itama ta samu hadin kai sosai daga mai girma yunar akan kasancewa da yar uwarta ba shamaki sakewa tayi suna bayyanar da kaunarsu da aka raba ta shekarun da sun riga sun rasa dan ba lallai su maimaita irinsu ba..
Duk wannan shirin da akeyi da kokarin inganta rayuwar Bahar LEUL baya ciki sbd sosai zuciyarsa ta tabu da hakan dan babu inda ko shawara Amminsa tayi dashi dan haka yaqi cewa komai ya kuma dena shiga komai din dan kuwa ita kanta Bahar bayajin zai sake bi ta kan rayuwarta kwata kwata zebarwa Amminta ita koma me sukeso suyi,
Ya rage shigowa sosai bangaren na Amminsa sbd ayyukan gabansa da sukai masa yawa da kuma tattara komai nasu da yayi ya ajiye musamman koyaushe bangaren kusan a cike yake da Zuhrah da 'yayanta dake wuni bangaren basa taba tafiya sai dare duk da leylah har lokacin a bangaren take bata koma bangaren iyayenta ba,
Sultan ma dayake bangarensa hutun gaske yake samu babu kowane irin damuwa da tinanin mulki dayake kansa dan haka shirye shiryen barin qasar yakeyi zuwa dogon hutun da kansa sai sake bayan shekaru masu yawa akan mulki,
Leylah duk inda hankalinta yake baya cikin jin dadi ko kadan kowane dare da baqin ciki take wuni hakama kowane wuni da baqin cikin take wuni sbd yanda aka jingine maganar aurenta tsaf a gefe da sultan me mulkin boyem an maida hankali akan yanda zaa inganta rayuwar wadda take ganin aikin banza ne kawai sbd har abada bazata samu ilimin da zai saka LEUL me boyem sonta ba harma ya iya zaman aure da ita sbd alamu suna nunawa mulkin yanzu da zai wakana a boyem na sauyin zamani da ilimin boko ne da baa buqatar duk wani mara ilimin a cikinsa.
Bahar bata taba damuwa da kiyayyar datake gani a idanuwan leylah ba sbd tana daukan hakan ne a matsayin rashin sabo da sakewan da basa dashi kwata kwata a tsakaninsu dan sam ko guri daya basa zama sbd ita kanta hakanan bata jin shaawan zama idan leylah din ta fito a guri sbd irin kallan datake mata da magana a cikin rashin mutuntawa ko nuna darajar dan adam gareta ita kuwa sam bata iya zama da duk wanda yake hakan dan batajin tanada rashin darajar da har zaa ringa mata kallan qanqantacciya dan haka saima tafi leylah din rashin son zama a duk inda take sam bata buqatan zamowa inuwa daya da ita.
Shuraim kuwa tinda ya dora idanuwansa akan bahar a ranar farko yaji zuciyarsa ta nutsu da ita nutsuwan dayake jin zai iya rayuwa a duk inda take dan haka sai bayada gurin zama fira a boyem din idan baa bangaren Ammi ba a tareda iyayen nasa da Bahar wadda take wata irin sauyawa tamkar ba ita dinba dan kuwa sosai ayanzu tenya take mata gyara itace ke kulawa da komai na bahar din musamman kasancewanta mace akwai abubuwan buqatarta da amfani da dole sai masu kyau da tsari da banbance ta da sauran matan daba jinin sarauta ba data tanadar mata suna jere birjik toilet dinta da gaban mirror dinta a tsare.
Sosai shuraim yake shigewa Bahar wadda sam bata saba muamala da mutane sosai ba dan haka bata wani sake masa duk da a cikin salo da nutsuwa da kauna tareda saka alaqar zumunci me karfin da suke dashi ya ringa janta a jikinsa duk da yasan akwai auren NUAB a kanta amma a yanda a yanzu Ammi ta tabbatarda aurenta da NUAB idan tanada raayi ne zaaci gaba idan batada shi sam babu zaa raba sbd bata damar rayuwa da zaban duk wanda takeso dan haka kafin ta fara karatu koma karatun yayi nisa ayi wannan zaman tambayar yana buqatar shaquwa da kauna a tsakaninsu dan kuwa a shirye yake da aurenta daga lokacin da auren NUAB ya sauka akanta daman kuma yanada tabbacin ba iddarsa akanta dan kuwa zai kafe ya tsare ya tabbatarda iddar NUAB bazata taba hawa kanta ba,
Leylah ma data samu wannan bayanin batai wani farin ciki ba duk da tafara karantar halinda shuraim yake ciki amma batajin zata iya barin shuraim ya mallaki bahar din dan kuwa shima zai cutu idan ya aureta ya wuce wannan ajin dan haka bazata bari yana rabin jikinta ba ya kwashi sauran wani duk da tana shakkar idan ma NUAB din ya amsa auren bare cikesa da kusantar Bahar da batada dogon banbanci da bayin masarautar a gurinta.
******A daren da washe gari Bahar zasu tafi a daren NUAB ya isa bangaren Ammin da kansa dan isar mata da sakon tafiyar da zaayi din hadda ita,
Tinda fadawansa suka fara isowa kofar bangaren tareda securities suka jeru a natse suna bawa bangaren kariya take bayin bangaren suka fito gabaki dayansu suna rabewa gefe sosai inda bama zai gansu ba dan sai bayi ma masu mahimmanci suke iya ganin Sultan me mulki a masaurautar duk da bayin bangaren Ammin kaf suna yawan ganinsa su kam sbd girman darajar Amminsa da kusan tafi ta kowace macen cikin boyem a yanzu kafin sultan din yayi auren da duniya zatasan matarsa a matsayin matar Sultan LEUL NUAB duniya da yan media su shedar da hakan. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee
107 Tin kafin shigowansa palon Maa tenya ta isar da sakon isowansa wanda itama kafin isar da nata sakon qamshinsa ne yafara ratso palon ya shigesu musamman Bahar da leylah wainda suke kusan saiti da kofar dan haka Leylah ce ta fara dago kanta ta juya a hankali ta zubawa kofar idanuwanta cikeda wani irin shauqi da tsananin natuwa da mutuwa a sonsa tana jiran shigowansa ta kallesa dan jin maitarta tana fadawa da samun sassauci,
Bahar kuwa qin nuna tama ji qamshinsa tayi bare nuna ta fahimci waye ne akace ya iso bangaren bare juyawa ta kalli kofar cigaba da duba laptop din datake gabanta tayi wadda Shuraim yake nuna mata da koya mata abuwa da kuma yanda zatai amfani da ita dakyau.
Shi kansa Shuraim ita ya zubawa idanuwansa batareda ko kyaftawa ba cikeda wani irin sanyi da kauna tareda soyayya me tsafta ba hayaniya da kamewa tareda aji yana jira da kokarin karantar yanayinta akan shigowa da zuwan NUAB din wadda dukansu sun manta yaushe suka samu ganinsa last.
Amminsa dake gurin zaune tsakiyar masoyanta Bahar na gefenta itada shuraim ita muma leylah tana gefen zuhra wadda take dayan bangaren ayanah din.
Maa sakinah tana dakin Bahar tana qarasa hada mata duk abinda zata buqata marasa yawa sbd acan ma zaa siya mata komai dan haka ba buqatar ta kwashi kaya da yawa su tafi dasu.
Sako kansa ya saka niimar gurin qarasa sauyawa a natse da qamshinsa daya kashe jikin leylah gabaki daya hakama iyayensa kamshinsa yana ratsatsu duk da ita zuhrah sai a yanzu ne take saninsa da abubuwan da suka shafesa.
Idanuwansa akan Amminsa kadai suka sauka ya qaraso har inda suke din wanda ya saka shuraim daya mace a gurin yiwa Bahar wata natsatsiyar kallo miqewa cikeda basa girmamawa hakama leylah miqewan tayi suka gaidasa cikeda girmamawa,
Amsawa yayi a taqaice batareda yayiwa kowannensu cikakken kallo ba sbd kallo baya cikin dabiarsa,
Gaida Zuhrah yayi ta amsa cikeda kauna da kulawa me yawa tana sake fuskarta dukda itama tana girmamasa sosai sbd matsayinsa na me mulkin qasa gaba daya.
Amminsa ya tsayar da idanuwansa akanta cikeda kaunar da babu sirki ya gaidata ta amsa tana miqewa zuwa palon da suka saba zaunawa suyi magana suyi fira,
Suna barin palon Bahar dake zaune duka abinda takeyi ta kasa cigaba sbd jin tayi ta dena ganewa miqewa tayi a natse ta silale tabar palon tana nufar bedroom dinta ta shige tareda rufo kofar tana kokarin basarwa da ci gaba da harkar gabanta.
Maa sakinah dake dakin ta kammala komai tana kokarin hada mata undies a wata yar qaramar suitcase dake cikin set na akwatin da zata tafi dasu din ajiyewa tayi tana kallanta tace
'Har kun gama karatun ne??
Gyada kai kawai tayi tana zaunawa bakin kujeran da Maa take hada kayan tace
'Maa ki ajiye hakan ki bari zan qarasa hadawa'
'Kinsan dame dame zaki hada ne to??
Murmushi tayi me kyau tana dasuke kafafunta daga qasa zuwa kan kujera ta lankwasasu tana gyara zamanta dakyau tace
'Eh mana ba iya wainndan ne kadai suka rage ba?
Murmushi Maa tayi tana dan zaunawa itama gefen Bahar din tana biyewa zancenta datake son yi batareda saniba kawai so take tayi ta fira sbd mantar da kanta komawa palon koma fita dakin gabaki daya dan daman koba komai idan ba tareda Ammi ba bata jin dadin sakewa da zama a cikinsu Shuraim da leylah duk da Mum zuhrah ma bata sake da ita ba da kauna me karfi kaman Ammin sbd tana ganin su leylah yayanta ne bazata iya zaqewa ta nuna musu fin kauna akan mahaifiyarsu ba musamman leylah da akan komai kishi da tsanarta takeyi dan hakanne take dan riqewa da taqaita kaunarta akan Mahaifiyarsu.
Acan palon Ammi kuwa lokacinda LEUL ya zauna facin Ammin yayi cikeda kaunar dayake jin tamkar tayi masa nisa a tsakaninsu yanxu sbd a yanzu tana tareda 'yar uwarta da yayan yar uwarta da uwa uba 'yar abaas data ke jinginar da nasa matsayin akan Bahar din kwata kwata tareda manta shi waye a gurin Bahar din batareda tambayar raayinsa ko jiran umarninsa akan komaiba sedai ta sanar dashi kawai ga abinda ta yanke wanda ya tabbata ya sani dorata Sultan yakeyi akan wasu tinanin da abubuwan dan haka shima sam hankalinsa yafi kwanciya ya nesanta Amminsa tasa da Sultan tin kafin ya gurbata masa tinaninta itama zata tafin bazata rasa ilimin koya ba acan ta samu nutsuwan da bata samu ba a shekarun baya, Taje ta shaqi iska da numfashin 'yanci da tsara kowace rayuwar zata zaba acan.
Ajiyan zuciya me sauti Ammin ta sauke tareda motsawa ta dawo kusa dashi ta zauna gap dashi tareda miqa hannunta duka biyu ta kama fararen hannuwansa masu karfi da lafiyar fata a cikin nata ta sake sauke ajiyan zuciya tana kallan fuskarsa daya dago idanuwansa da ita kanta wani kwarjini me karfin gaske suke mata kawai dai bata sauke masa nata idanuwan ne sbd tana mahaifiyarsa kuma har yanzu babynta dake bacci a jikinta yana yaro take kallansa dan haka zuba masa ido tayi zata bude baki tayi magana ya kalleta da kyau ya dakatar da ita ta hanyar fada mata kai tsaye da itane zaayi tafiyar goben dan zuwa itama ta huta ta samu sauyin muhalli.
Kafesa da idanuwanta tayi tareda tsayawa cak har lokacin hannuwanta suna cikin nasa riqe,
Mamaki ne ya bayyana a fuskarta kai tsaye sbd ba tsammani taji zancen da bata ma gama ganewa ba duk da daman a cikin ranta tana jin inama zata bi su Bahar din can qasar sbd zatafi samun nutsuwa da farin ciki idan tana tareda bahar din duk inda take amma kuma yanayin dayake fuskar NUAB din yana nuni da kaman hukunci ne ya yanke akanta.
Numfashi me sanyi ta fitar tareda bude baki baki tace
'Hayateem,Umarni ne wannan ko hukunci kokuma raayina kakeson bi??
Sauyawa idanuwansa sukai ahankali yana kafeta dasu cikeda matsananciyar kauna me karfin gaske dayake jin inama duka babu wannan a cikin dadi ne zai dauketa su tafi duk inda zasu tafi dan tayi yawo a cikin yancinta,
Zare hannuwansa yayi daga nata a natse kafin ya zagayota da hannunsa daya zuwa jikinsa ya rungumeta ta gefensa yana dan lumshe ido ya bude baki yace