Kenza eBookz

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 43

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 43

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 43: Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 43. Shigar idanuwanta a cikin nasa da sauyawan da…

4,486 words

Shigar idanuwanta a cikin nasa da sauyawan da sukai ya saka fatarsa sauyawa zuwa ja a take ya Lumshe idanuwansa da suka sake shigar da ita tsoro ta tattaro karfi daqyar ta bude baki zata sake magana ya isar da bakinsa akan nata cikin wata irin kasala me tsananin sanyi da mutuwan jiki ya hade bakinsu yana sauke ajiyan zuciyar da duminta ya sauka a fuskarta ta sakata rintse ido da karfi sanyin harshensa na ratsa nata bakin daya shiga yayo mata wata irin tsotsar data sakata qanqamesa da karfi hannuwanta na fara rawa me karfin datake qarasa dumama jikinsa ya riqo kanta da duka hannuwansa biyun da kyau yana shigar da bakinsa da kyau cikin nata yafara mata wani lafiyayyan sanyayyan kiss din daya sakata rudewa tana rinste idanuwanta da karfi kaman yanda ta qanqamesa da karfi a rikice.

Kissing din dayake mata shi kansa abu ne da bai taba yaune karan farko na rayuwarsa dayake farawa dan haka ya kasa sakinta ya qarasa janyota jikinsa akan gadon gabaki daya yana tsotsan bakinta nutsuwansa da lissafinsa suna fara kuncewa a karan farko.

Kissing dinta yakeyi yana jin kaman bazai taba iya bari ba sbd abubuwan dayake ji suna ratsasa na cikarsa kakkarfan namiji me lafiyar dashi kansa bai saniba.

Juyar da ita yayi a tsakiyar gadon yana rufeta da kirjinsa ya sake kamo fuskarta ya dago yana sake dora bakinsa akan nata tareda hade tafin hannunsa da nata cikin wata irin sanyi yana matsesu.

Fitar numfashinsa sauyawa yayi zuwa wani irin yanayin daya sakata qarasa tsorata ta janye da karfi daga fuskarsa tana bude idanuwanta da sukai laushi ta kallesa daidai nan ya bude idanuwansa da sukai mugun ja tayi saurin dauke nata idanuwan tana saukowa daga gadon jikinta na dan rawar datake kokarin hanasa gani,

Maida idanuwansa yayi ya rufe a hankali batareda yace komaiba ya fara sauke ajiyan zuciya me sanyi da nutsuwa ko daya sake bude idanuwan ta fice daga dakin.

Wayarsa ya miqa hannu a hankali ya dauka ya cire daga dnd ya kira Aleey kai tsaye yace abarta ta tafi kawai ya kashe wayar ya ajiye.

Batai tsammani ba tana isa kofar aka barta kuwa ta fice dan haka kafafunta har wata yar rawa sukeyi kaman yanda zuciyarta ke bugawa har lokacin ta isa bangaren Ammi.

Tana shiga kasa kallan kowa tayi cikin karfin hali ta gaidasu ta wuce dakinta suka kasa binta da kallo suma sbd kowane motsinta qamshin NUAB dinne yake fita a jikinta.

Tana shiga dakinta toilet ta fada sai data sakarwa kanta ruwa ta fara sauke ajiyan zuciya nutsuwanta na dawowa jikinta cikin mutuwan jiki.

Ko data fito lokaci ya tafi sosai dan haka shiryawa kawai tayi tayi breakfast a tsatsaye suka fito lokacin Ammi bata bangaren ta tafi gurin sultan wadda a tsakiyar daren Sakon tafiyar Ayanah din ta riskesa yayi shiru zuciyarsa na shiga wani irin halin fushi da zafi sosai sbd yasan sbd shi ne sultan me mulki ya aika Ayanah ghaz wata qasar wadda yake ganin hakan shine baqin cikin dazai masa.

Tabbas yaji wani irin zafin tafiyar musamman da baa sanar masa ba sai a daren da babu lokacin da zai iya hana tafiyar tata,

Numfashi da ajiyan zuciya me sanyi da nutsuwa yasauke wadda ke hana duk abinda yake ransa fita shiyasa baa taba gane fushinsa bare abinda yake shiri.

Ko da Ayanah din taxo masa bankwana har cikin lafiyayyar bedroom dinsa shima yana zaune bai tashi ba hannu ya saka a natse ya kama nata ya zaunar da ita a gafensa tareda matsowa a natse ya shigar da ita da kyau dumin jikinta yayi masa ratsar dayake jinta har cikin jininsa ya bude baki a natse yace

'Ina tayaki murna da samuwan 'yancinki dan haka ina tafe gareki Ayanah ghaz.'

Kallansa ta dago tayi da kyawawan idanuwanta cikin yanayin daya sake daukan hankalinsa akanta tace

'Zaka iya da 'dana??

Murmushi me kyau daya fidda haibarsa ya sake yace

'Karki manta jinina ne yake yawo jikinsa'

Murmushi itama kawai tayi tareda miqewa suka fito a tare har bakin palonsa ya rakota hannunta riqe a cikin nasa.

Karfe tara saura suka bar masarautar batareda sun saka NUAB a idanuwansu ba kuma kowa baice komaiba sbd rasa abin tambaya ko fada musamman ganin yanda bahar din bata ko kallan fuskokinsu.

Sun isa Airport motocinsu sukai parking daidai da motocin da suka kawo 003 Shifa musa tamu a wanda itama uk din zata wuce kai yara Hutu dan haka kusan a tare suka dunguma zuwa aciki securities na biye dasu da kayansu suna fira cikin sakewa.

Jirginsu na tashi yabar qasar boyem Bahar ta sauke wata boyayyar ajiyan zuciya tana lumshe idanuwanta a hankali. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee

111 Koda jirginsu ya sauka bayan tafiya me tsayin gaske Bahar jin takeyi nauyi me nauyi yana qarasa sauka daga kanta musamman da a cikin iyayenta zatai rayuwa tasan bazata taba damuwa ko kadaici ko maraicin iyayenta ba sbd duka iyayen nata uku babu wanda baya tsananin kaunarta,

A yanzu bata da namiji ko daya a cikin iyaye ta zama 'yar mata wanda batada damuwa ko takaici ko daya akan hakan dan kuwa a cikinsu babu wanda bazai iya yi mata abinda kowane uba namiji zai iya yi mata ba dan haka batajin tanada sauran kowace damuwa akan rayuwar da zatai ta har abada a matsayin 'yar mace.

Daga airport suka rabu da Madam Shifa Musa suka shiga motocin da suka taho daukansu itama ta shiga nata kowannensu ya wuce,

Motoci biyu ne manya suka daukesu wainda Aleey ya tanadar musu tin kafin su baro ma daga can da wasu yaransu biyu dake kusa suka rigasu isowa uk din,

Akwai abubuwan da aka fara biyawa dasu garare biyu akai na wani id card din bahar din da register din wasu files na inda zasu kafin suka wuce Oxford inda acan aka tanadar musu lafiyayyan gidan da zasu zauna suyi rayuwan da duk suke so.

Koda suka iso gidansu dare yayi sosai dan haka babu wani bata lokaci aka tafi aka kawo musu light abinci me lafiya aka jere musu a dining dayake dakin cin abinci na gidan.

Suka tafiyarsu kafin da safe su dawo dan su Ammin na buqatar hutu sosai,

3 bedroom ne hadi da master bedroom dayake can dan lungun shigarsa daban 4 kenan sai 2 sitting rooms dayan na master bedroom ne dayan kuma na sauran,

Babu wanda ya dauki master bedroom din sbd ya kebe daban a cikin dakunan dan haka ko Bahar ba batajin zata iya zama cikinsa dan haka Ammi na daukan daya Maa sakinah da Maa tenya duka dauka daya sai aka barwa bahar din daya suka bar wancan din hakanan batareda kowa ya daukesa ba duk da yafi kowane dakin wata irin tsaruwa da girman duk da sauran dakunan suma sunada girma sosai da tsari tareda lafiyayyar luxuries da aka zuba koina na gidan dan kuwa duk kyau da tsarin boyem nan din ma tsarinsa daban yake sbd nan babu ado sosai kaman na sarautar can amma suma duka abinda aka qawata gidan dashi yayi kyau da tsari kuma dukiya kawai yake nunawa koina.

A cikin nata bedroom din bayan ta shiga batabi takan kayanta ba sai zuwa da safe baiwar da suka taho da ita me suna Hafsat zata gyara mata su a wardrobe dan haka bathroom kai tsaye ta nufa bayan ta zare duka kayan jikinta.

Wanka tayi da ruwan zafi sosai batareda wani bata lokaci ba a gurin wankan sbd akwai salloli akanta,

Tana fitowa body oil kadan ta shafa tareda tirare me sanyi ta saka kayan bacci ta dora doguwan rigar sallah akai ta kalli inda taga anyiwa kowane dakin gidan alaman gabas sbd gurin da aka kebe dan sallah a tsare yake kowane daki da lallausan dadduma da Al'qur'an a gefe wanda yake cikin tsarin duka gyaran da aka saka akai musu a gidan kafin isowansu dan kada su shiga kowane stress na buqatan sanin komai an tanadar musu dan haka kai tsaye sallah ta tada a natse.

Duka sallolin dake kanta tayi tana idarwa tayi addua ta gama ta miqe tareda fitowa batareda ta cire kayan sallan jikinta bama sbd yunwa take ji daqyar take iya doguwar motsi ma.

Kai tsaye inda aka jera abincin ta nufa daidai nan itama Ammi ta fito tareda su maa sbd kowa yunwar yake ji sosai duk da sun danci abinci a jirgi.

A dining din suka zauna gabaki dayansu suka fara kokarin cin abincin wanda ayshah tazo tayi serving nasu duk da kusan Bahar ma ce tayi rabin aikin.

Abinci suka ci suka koshi tareda shan ruwan dumi sosai bana sanyi ba tukuna kowa ya shige dan hutawa.

Tana shiga daki brush taje tayi ta dawo ta haye gadonta tayi kwanciyanta take bacci ya dauketa me karfi da dadi.

Bacci me karfi kowa yayi daqyar suka iya tashi sallan asuba suna gamawa kowa ya sake komawa daga nan kam ba wanda ya fito sai karfe goma da mintina tukuna Tenya ta fito a shirye cikin wankanta ta zauna palo tana kunna wayarta a natse.

Ayshah ce taxo ta gaidata cikeda girmamawa ta gama komai na aikin gyaran gidan da breakfast sbd babu abinda babu an tanadar musu komai kuma itama ta samu tayi baccin sosai ta huta ba laifi a dakinta dake ta cikin hanyar kitchen dan madaidaici mara girma sosai.

Maa sakinah ce ta fito itama tana wayar da Zuhrah tana sanar da ita sai yanzu suka samu kunna wayoyinsu suka fada wani zancen tana tambayar leylah wadda tin jiyan take jin duniyarta ta dawo sabuwa sbd Bahar ta tafi NUAB kuma yana nan tareda su a boyem.

Shuraim ma nutsuwan hakan yaji ya samu sosai fiyeda yanda ma ya tsammata dan kuwa tafiyar bahar ma ta saukaka musu komai dan haka shima shirin komawa Oxford kawai yaji yana son farawa sbd rayuwa a can.

Aysha ce ta hada dafaffiyar madara da zuma da tea spices masu kyau da qamshi ta jera a tray ta nufi dakin Ammi dasu,

Ko data kai Ammin na zaune a kan lafiyayyan sofar dakinta tana waya a natse cikin kwanciyan hankali,

Da NUAB take waya dan haka Aysha ajiye kayan tayi akan table din dayake gaban Ammin ta saka hannu a natse ta zuba mata ta ajiye a gabanta ta juya ta fice batareda bada kowace irin sound da zata damu wayar ta Ammin ba.

Kitchen ta koma ta sake hadowa ta kawowa su Maa dake palon kafin ta koma ta sake hada ta Bahar daban ta nufi dakinta tana fatar ta tashi.

Bahar din bata tashi ba dan haka ta juya dashi sbd dole idan ta tashi sai ansake dumama sa.

Tana fita bahar ta farka ta miqe itama toilet tafara fadawa tayo wanka ta fito tana fidda qamshin wani tsadadden shower gel dasu bodyscrub da set set na skin routine dake jere a toilet din kaman ansan nan din zata zauna an jere komai da aka tanada dan ita a gurin.

A natse ta shirya cikin doguwan riga mara nauyi har qasa ta fito tana jin gajiyanta ta sake gabaki daya,

Gaida su Maa tayi cikeda girmamawa da kulawa kafin ta nufi dakin Amminta wadda har lokacin take waya.

Tana shigowa Kallanta Ammin tayi fuskarta na cikewa da farin ciki ta miqa mata hannunta daya ta taho ta kama tana zaunawa gefenta kusan cikin jikinta sosai.

Muryansa taji ahankali ta ratsa kunnuwansa a daidai lokacin dayake sanar da Ammin baida ranar da zasu gansa sbd bazai bar boyem ba saiya seta abubuwan daya fara setawa da dama dan haka su kula da kansu kuma akwai mota da driver da aka tanadar musu yana nan zuwa ayau din shima.

Cikin kulawa da kauna me tsafta da ba sirki Ammin tace

'Ka kula sosai da kanka, Ka rage fushinka illa ce ga lafiyarka da imaninka, Ka sassautawa kanka akan mahaifinka, Ka ringa cin abinci akan lokaci da samun hutu sosai Allah ya baka kariya daga kowane sharri Hayateem'

Ajiyan zuciya nai hade da numfashi ya sake cikin nutsuwa wanda har cikin kunnuwanta taji saurin saukan numfashin nasa da yayiwa Ammin ya bude baki a taqaice yace

'Love you Ya Ammi'

Murmushi Ammin tayi tana ajiye wayar sbd ya kashe tana kallan Bahar wadda tayi shiru a jikinta tana hana zuciyarta tina abinda ya faru a tsakaninsu sbd zata iya kasa hada ido da Ammin wanda zai iya saka a gano wani abin ma.

Cikin kokarin basarwa ta gaida Ammin tana daukan cup din dayake gabanta tana bata cikeda kulawa.

Amsawa tayi tana karban cup din bata sha ba takai bakin bahar din tana cewa ta fara karyawa tukuna.

A tare suka shanye duka madaran a different cup da aka ajiye kafin Zuhrah ta kira Ammin suka dan jima suna waya tukuna aka bawa bahar itama sukai magana sosai kafin suka fito.

Breakfast sukai suna gamawa driver yaxo ya dauki bahar din suka fita tana dan jin tsoro da shakkar fita daga ita sai wanda bata saniba a qasar da bata taba saniba bare xuwa hakama batada doguwar ilimi da wayewan muama sosai da mutane dan haka a sanyaye sukai fitar.

Makarantar da zatai karatun ya kaita kai tsaye gurin wanda akace a kaita,

Suna zuwa sauran formalities aka qarasa cikewa da kammalawa akai komai da komai harma ta shiga class din karshe da dagashi an tashi.

A gajiye ta fito suka bar makarantar zuwa gida sbd ko ruwa bata iya sha ba sbd rashin sukunu da fargaban datake ciki,

Suna dawowa bata wani iya tsayawa palo ba gurin su maa dakinta ta wuce ta fara ajiye su laptop da ipad da sauran tarkacen karatun da zata duqufa dayi kafin ta fada bathroom tayo alwala tazo tayi sallah ta fita taci abinci ta zauna tana fadawa su Ammi duk abinda ya faru a makarantar tana jin kaman bazata iya karatun ba,

Karfin gwiwa Ammi da maa sakinah suka bata sosai sbd tenya tana kitchen tareda Aysha dan ita sam bata wani son zaman hutawan nan sosai hakama idan ba ita tabawa Ayanah abinci ba ganin takeyi sam batada nutsuwa.

Sosai suka bata kwarin gwiwa tareda tabbatar mata da zata iya idan ta dage sbd tana buqatan karatun da ilimin a yanxu datake da sauran kuruciyanta.

Da wannan ta sakawa ranta zata daure ta dage tayi karatun insha Allah. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee

112 Washe gari da wuri ta shirya sbd karfe 8 zata ringa shiga aji dan haka bata tsaya bacci ba bare jiran Maa sakinah taxo tada ita ta fito a shirye maa sakinah na kitchen da kanta ta hada mata breakfast mara nauyi ta kawo mata tareda zaunawa gefenta tana taimaka mata gurin ci akan lokaci.

Tana cikin breakfast din Ammi ta fito ta iso gurinta tana miqa mata jakarta me kyau data hado mata yan abubuwan buqata da wayar data bude mata sabuwa dal ta saka mata numbers nasu duka a ciki tana mata addua.

Ammi da maa sakinah kaman zasu bita makarantar haka suka rakata har kofa ta fice da sauri tana musu sai anjima.

Mota ta fada suka wuce makarantar tana saka ipad dinta a jakarta.

Koda suka isa da farko taso ta sake karaya amma wadda aka hadata da ita Neesah yar qasar ghana ce a makarantar dan ta taimaka mata sosai sai ta sake mata sosai tareda nuna mata itama zata iya dan haka saita sake sakewa dan daukan kowane darasin dazai taho mata ta karatun.

Bayan fitowansu class din farko da kusan bata gane komaiba library suka nufa ta zaunar da ita can ta fara fahimtar da ita komai da abubuwa,

Bata dawo gida ba sai yamma sosai sbd lesson din da aka wuce da ita wani gurin daban wanda shima kullum daga school can zaa ringa kaita tana koyan turanci da ilimin muamala da mutane da duk inda zaka shiga.

Acan baa hadata da kowa ba dan haka shiru kawai tayi tana saurare tareda recording komai sbd neman cikakken qarin bayani idan ta isa gida.

A gida babu sauran lokacin kowane irin hutu a gurinta sbd a gidanma tanada online class da shima aka tanadar mata komai na turanci da larabci wanda zaisa tafi ganewa.

Har dare bata fito ba dan haka Ammi da kanta ta saka aka hada abincinta takai mata har dakin tana zaunawa kusa da ita suna duba karatun tare tana ganar da ita abinda ta sani itama kafin suka qarasa kammalawa ta sakata taci abinci ta koshi cikin kulawa ta goge mata bakinta da tissue.

Anan gurin daga fira bacci ya dauketa jikin Ammin cikin gajiya da dan ciwon kan rashin sabon abinda dole ya zama rayuwarta kuma.

Sai data dan yi me nisa ta rage ciwon kanta tukuna ammin ta tada ita tayi shirin bacci tayi sallar ishai da akai tini tukuna ta kwanta take baccin ya sake dauketa.

Washe gari ma haka ta tafi tinda safe bata dawo ba sai 6 na yamma a gajiyenda saida maa sakinah ta kamota jikinta ta rungume ta rakata har daki ta tayata zare kayan jikinta ta fada toilet tayo wanka da alwala tayi sallah Amminta ce ta bata abinci kaman zata tayata ci harta koshi tukuna ta fada online class dinta wanda tayi har kusan 8 tukuna tai sallah ta sake kwantawa.

****Haka karatun nata yafara tafiya a cikin wata irin gwagwarmayan rashin hutu ko kadan wanda ya sakata tafara ramewa duk da tana samun lafiyar fata sosai sbd yanayin garin da luxurious abubuwan datake amfani dasu da kuma gyaran da fatarta ke samu a cikin sanyi da nutsuwa daga Maa tenya dinta da ita anan ne tafi kwarewa.

Dukkanin wani abinda zata buqata na rayuwa da amfani ansiya mata harma an wuce kaidarsa sbd komai nata tamkar baa san zafin dukiya ba ake siya mata shi a cikin gata da daular da suke ciki,

Ammi ta samu sauyin rayuwar da bata samu tayi ba a baya yanzu itace takeyi wato ta zamowa cikakkiyar uwa me dawainiya ga abinda ta haifa,

Ko data haifi NUAB ba itace take kowace irin dawainiyarsa ba sbd yanayin da Allah ya sakata bayan haihuwan dan haka bata samu daman wahalta masa da jiki da lafiyarta ba sai ayanzu ne take sanin menene dawainiyar 'yaya dan kuwa kusan komai na Bahar din itace takeyi duk ba itace take girki da sauran abubuwan ba amma kowace safiya itace take fitowa taje dakin ta tadata bacci ta tayata shiryawa kaman qaramar baby ta sakata tayi breakfast ta rakata har waje saita tabbatarda ta wuce tukuna take samun daman hutawa harma ta bari ayi tata dawainiyar da kulawa da ita itama har sai Bahar din ta dawo kuma ta tayata fuskantar online classes nata da sauran karatun da shine yake ramar mata da yarinya,

Maa sakinah ma kusan duk dawainiyarta akan bahar dince sbd ta saba hakama akwai abinda itace kadai take iya yiwa Bahar din kaman wanke mata kai haryanzu itace take shiga toilet tareda ita ta wanke mata sbd sam Bahar din batajin kunyarta a matsayin uwar gaske ta dauketa sabanin duk kauna me karfin datakewa Amminta bata iya shiga toilet da ita duk da wasu lokutan tanayi musamman idan maa bata wanke mata kai ba Ammin ke mata amma kuma duk ranar da Allah yasa ta tina NUAB jin takeyi bata iya shiga toilet da Ammin ta ringa zame zame kenan har sai kuma an kwana biyu ta manta.

Karatunta yafara nisa dukda nauyi da karfin da yayi mata ta tsaya dakyau tana fahimta hakama tafara ganewa sosai ga lesson din datake zuwa shima suna kokari sosai gurin ganin tafara gane turanci tana dan kokarin yi da sakewa da mutane tareda fara iya hulda dasu dayasa tafara sani da wayewa akan abubuwa ciki kuwa harda iya zuwa siyan abu da kanta gurare daban daban ita kadai sai drivernta wanda duk inda zata yana tsaye yana jiranta harta gama ya juyo da ita.

Neesah ma sosai take sake sakewa tana bada himmar karatun Bahar din sbd sun fara samun shaquwa sosai da kuma sabon karatun da Bahar din ta dage sosai akansa dan yanxu ta dena jin wahala da fargaba ta karbesa hannu bibbiyu.

Neesah a hostel take zaune sbd batada kowa a garin sam iyayenta suna Sheffield city dan haka ahankali ahankali sabonsu da tsananin son karatun Bahar din ya sakata janyota gidansu tana zuwa tayi kwanaki haka tareda su kafin ta koma hostel sai kuma wani lokacin ta sake zuwa tai musu kwanaki harta saba sosai dasu Ammi da maa da suke kaunarta sbd kaunar datakewa bahar da tsayawa akan karatun bahar din wanda ya fara shigarta sosai dan kuwa bahar din ta cire duk wani kadaici da kama jiki ta fara wayewa da qasar da rayuwar qasar sbd maganar wata kusan shida sukeyi a qasar kuma sosai rayuwar ta sauya musu gabaki dayansu sun fara sajewa da yanayi qasar tinda daman sun saba da dan yawonsu na qasashe hakama a cikin daula da tasu duniyar me zaman kanta suke rayuwa dan haka babu wani sabon abu sosai a qasar da basu saba da shi ba suka waye dashi ba.

*******A tsawon wannan wata shidan babu kowace ranar da NUAB baya waya da mahaifiyarsa dasu maa ba amma bai taba tambayar Bahar ko nuna ma ya tina da akwaita cikin rayuwarsa ba,

Ita kanta Bahar din ta tattara komai nasa ta manta dashi gabaki daya harma tinawa datake dashi 'dan Amminta ne ta ajiye ta manta yanzu Ammin tata ce ita kadai ta fuskanci rayuwar gabanta datake mata dadi yanda ya kamata sbd yanzu har yawo sukeyi sosai da Neesah wadda ta zana very close da ita,

A zuciyar Ammi babo. ranar da zatai waya da NUAB din batai tsammanin ya tambayi 'yarta ba ko da badan auren dayake tsakaninsu ba kodan kasancewanta yar datake ji da ita fiyeda tata rayuwar amma bai taba tambaya ba barema nuna yasan da akwai wata rayuwar bayan su uku iyayensa dake Oxford din,

Abin yana sosa ranta kuma batason tayi masa magana sbd kada ya dauka son cusa masa ita takeyi amma hakan sosai yake mata ciwo dan haka ta tattara itama ta ajiye maganarsa da bahar auren nasu na ficewa daga ranta tana tsayar da shawara daya akan rabasu matiqar tanason ta zauna dasu kowa da matsayinsa na me mahimmanci a rayuwarta batareda ta cutatar dasu ba ga bahar ta samu rayuwar da ba takurawarsa.

*****A boyem ma gurin sultan LEUL me boyem kaman yanda Ammi ta tattara maganar auren ta ajiye akan rabuwa hakan ne a gurinsa sbd yanajin rayuwarsa a yanda take tafi masa ba damuwa da rigimar da bahar din take tattare da ita a rayuwarsa dan haka ya hakura ya taba kaiwa Ammin tasa ziyara sbd baya buqatan duk abinda zai sake saka rayuwarsa a matakin zarewa ko zama makashin dayake neman zama,

Hankalinsa yana kan mulkinsa sosai daya sauya kusan duka manyan fadar masarautar ya zuba sabbi masu zafi da ilimi me karfi da tsayuwa akan raayin gaske a cikin manyan 'yayan fadar da wasunsu ma duk sun zama dattijan zamani masu ilimi suna qasashe daban daban suna rayuwa ya gayyatosu suka dawo qasarsu ya basu matsayin daya tattaro dasu ya dawo dasu qasarsu a qanqanin lokaci dan bawa iyayensu daman hutawa daga sarautar da zaman fadar daya fara tsatsar da zuciyoyinsu.

Sultan Yasar dayake cikin masarauta yana hutun da kusan kaman baya duniyar gabaki daya bare masarautar dan kuwa ko ganinsa babu me sai wanda yaso gani Yana sane da sabuwar boyem da NUAB yake tsarawa wadda ake ta magana a kafafen yada labarai musamman sabbin dokokin daya fitar da suka girgiza duniyar gabaki daya wanda ya fidda su jere ciki kuwa harda bayyanarda cikakkiyar Alaqar mahaifiyarsa da Matar mai girma yunar ya kuma soke kowane irin dokar da zata hana jini daya yan uwa daya aiki a cikin masarautar boyem matiqar yana mulki dama duk wanda zaiyi mulki bayansa ya dakatar ya kuma goge wannan dokar a shafin tarihin boyem gabaki daya har abada,

Dokarsa ta biyu data girgiza boyem itace soke Imebētin data wuce daya ga kowane jinin boyem ko a ina yake dan haka ga duk wanda haryanzu yakeda Imebēti zabi biyu yake dashi kodai ya sallamesu kokuma ya daura aure dasu a cikin qanqanin lokaci.

Doka ta uku shine soke kawo bayi maza ko mata na siya sedai a daukesu a matsayin ma'ikata da masarauta zata ringa biyansu hakama kowane bawan dazai kai shekaru sama da talatin da shida zuwa arbain indai mace ce zaa yanta su sutafi a zuba sabbin masu karfi da sauran kuruciya idan kuma maza ne shekaru arbain zuwa da biyar kema zaa yantaka sbd kaje ka qarasa sauran lokacinka a cikin yanci. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee

113 Dokarsa ta uku itace fidda sanarwar cin kasuwan bayin qarshe na masarautar boyem da zaa ci garin da kasuwan bayin qasar take na bakin border na ruwa wanda kai tsaye a bangarensu shirin tarbon kusrawa ne a qasar sbd bazasu taba wuce wannan cin kasuwan ba na karshe a boyem hakam an saka cin kasuwar nesa sosai sbd bada isashe kuma wadataccen damar isar labarin koina na duniyar da har zai isa inda ake son ya isa harma da lokacin da zasu samu kafin hada bayi da isowa dasu qasar wadda take shirye tsaf tana jiransu dan kuwa hatta matakan tsaron kowace border ta qasar an sauyasu zuwa masu tsananin da suka ninka suka qaru suka wuce na asali dan kuwa yanzu mulki ake na tsananta kowane matakin tsaro dan bawa qasar da mutanenta kariya tako ina......

****A lokacin da aka gama kaddamar da wainnan dokokin masu karfin gaske da wainda ma bamu zayyanoba a cikin babban fadar masarautar a cikin wata irin karfin ikon data saka koina daukan tsit masu jarida da yan media na dauka da gidajen television Sultan ma dayake zaune palonsa yana ji suna sauka kunnuwansa suna ratsashi shiru yayi sbd abubuwa ne da shi baiyiba sbd takunkumin dayake daure dashi na ya riga ya kaddamar da duk abubuwan daya tarar akan mulkin batareda ya sauya ba kuma tinda ya kaddamar dasu a yanda suke tin can baya baida ikon sauyasu har abada shiyasa koda ya samu sauyin shigowan Ayanah da soyayyarta me karfi rayuwarsa bai taba samun sukuni da kwanciyan hankali ba saida ya tabbatard ya sauka ya dora wanda zai sauya masa su ko bai fada masa ba sbd raayinsu da zuciyarsu dake bugawa a matsayi daya akan kuma buri daya na inganta tareda kawon sauyin duka akan rayuwar mace daya dasuke tarayya akan kaunarta da zasu iya komai akanta wato AYANAH GHAZ.

A cikin dokokin da sabon sultan din ya fidda gabaki daya akan daya ne zuciyar sultan yasar ta tsaya a yanxu waton sallamar imebētis ko auransu kafin wani lokacin,

Wani sanyayyan numfashi sultan ya sauke yana dago fararen idanuwansa yana sake kallan makekiyar flats screen tv din dake palonsa yana kallan yanda ake jero sabbin dokokin mulkin sultan NUAB LEUL boyem wainda ake yinsu a live shima kuma dayake masarautar yana jinsu a kannuwansa a lokacin suke shigarsa a lokaci daya dana tv din,

Readers Also Read