Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 44
Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 44: Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 44. Abu daya ne ya sani a tsawon lokacin nan da…
4,500 words
Abu daya ne ya sani a tsawon lokacin nan da NUAB yake masarautar ya kasa ne ya tsare dan hanasa tafiya kowace qasa a tinaninsa ya rabasa da mahaifiyarsa kenan ya dauketa,
Ya aiko masa sakon a rubuce da stamp dinsa na ya dakatar dashi daga fita kowace qasa har sai bayan tsawon shekara biyu sbd ya samu hutawan sauka daga mulkin shekaru sana da talatin tareda zuba masa sabbin bayi da securities a bangarensa duka a matsayin basa hutu da kulawan daya kamata,
Ko a wancan lokacin da sakon ya samesa kai tsaye yasan bawai hutun NUAB yake nufiba ya basa a matsayin tausawa da nuna kulawa kaman yanda masarautar da duniya ta dauka yayi hakan ne dan hanasa isa ga mahaifiyarsa dayake jin ya dauke kenan har abada daga rayuwar sultan din,
Yayi hakan ne dan hanasa fita koina kuma shima shiyasa tsawon wannan lokacin bai taba tafiya koina ba yana cikin boyem da kusan fiyeda rabin bataliyarsa da ayanzu suka tare a boyem dan bude sabuwar ghaz da boyem a qasa daya,
Ko ayau ma sultan din tinaninsa daya ne akan wannan particular dokar ta NUAB akan imebētis dan haka baji komai sbd batareda sanin NUAB dinba ya basa wata babbar damar da itace burinsa daya jima dashi akan Ayanah ghaz dan haka kai tsaye a cikin daren shima ya fidda takardar da kadir ya isar a fada wadda washe gari zaa gabatar da ita a fadar wadda itama sabon sultan yana cikin abinda ya soke matiqar ba zaman taro me mahimmanci akeda shi a qasa ba da ake buqatan zama da duka masu matsayin fada to ya sake zaman banza na fadar an sauya tsari zuwa manyan offices sabbi masu tsari da aka gina a cikin masarautar kusan hawa hudu tamkar wata babbar sabuwar palace kowane shugaban fada yanada office dinsa me zaman kansa da securities dinsa da mataimakansa tareda p.a,
Shi kansa Mai boyem din office sabo da babu kamarsa a boyem aka gina masa a floor din karshe da babu kowane office bayan nasa hade da lafiyayyan palo da bedroom me girman gaske dayake hade da bathroom harma da yar closet din hutawansa a ciki idan yaso harma da gurin cin abinci duka a guri daya sai office din Aleey dayake farkon shigowa floor din daga ka fito lifter wanda shima nasa yake babba da toilet lafiyayye kadai a cikinsa dan haka tsaro da security din da floor din yakeda shi yafi na koina,
Bayan sabuwar ginin offices din ba palace officials wata sabuwar ginin bangaren sultan LEUL NUAB me boyem akai acan Asalin bangarensa da aka sauyawa maana ana hade kusan bangare uku aka maidasa daya tareda yi mata tsarin da babu kamarta kaf a masarautar hakama tsarin ginin yanda akasan yana rayuwa da buqata,
Chambers din Sultan NUAB itace bangaren datafi kowane bangare kyau da tsari tareda daula a cikin boyem,
Komai na bangaren nasa akan tsarin mulkin bature yake, Hakama bangaren mahaifiyarsa anyi masa gyara na musamman tareda sauya musu komai hakama sauran gurare da dama an sauya musu tsari wanda ya saka masarautar zamowa tamkar sabuwar masarauta ga sabbin tsare tsare da security cameras nako ina da aka sauya.
Bangaren Asim bai taba hakura ba da Bahar sbd bai taba jin soyayyarta ta rage bare fitaba daga zuciyarsa dan haka tinda ya samu cikakken bayanin barinsu masarautar zuwa uk da zama take boyem da masarautar boyem din harma da mulkin boyem din ya fice daga ransa yaji yana son barin qasar zuwa duk qasar da bahar take da zama,
Haile na ji tana gani Asim ya koma mata mummunan kaddarar da bata taba zata ba akan soyayyar da babu alkhairi a cikinta,
Bata taba tsammanin akwai macen da kaf duniya Asim zai so fiyeda burinsa da dashi ya girma ba,
Asim ya mutu rayuwarsa ta mutu batada Sauran amfanin da suke buqatarsa dashi hakama yana nan yana macewa da zama marar amfanin NUAB yana can yana gudanar da mulkinsa na gina sabuwar duniya ga boyem hankalinsa kwance hankalin uwarsa a kwance a wata qasar hakama hankalin sultan a kwance yana hutawa tamkar babu su a duniyar sbd kwata kwata tinda ta dawo taqi zuwa tirakarsa sbd tsanarsa datake ji me tsananin gaske da batada burin daya wuce barinsa duniya kuma bai taba nemanta ba tinda taqi zuwar masa maraki ce kadai take zuwa tirakarsa wadda itama a yanzu batada burin a wayi gari ace sultan din baya duniya ta huta tasan kowa a cikin su ukun ya rasa an huta dan kuwa a duk zuwan datake shimfidar sultan din bata taba ganin soyayyarta ba a tattare dashi ko so daya wanda take da tabbacin ba kuka haile bace Ayanah ghaz ce a zuciyarsa.
Su aslam zuwa yanzu sun saddaqar da rayuwa ga qarewa a gagare ba aure sbd a yanda Asim ya koma babu sauran amfani ga tsayuwa akan burin da nacewa nemar masa sarautar boyem dan haka suka zubawa sarautar allah ido da jiran damar dawowansa daidai.
A bangaren Leylah kuwa duk yanda zatai ta isar da kanta ga NUAB babu kowace hanya ta toshe sbd a yanzu ko ganinsa sai me babban rabo da matsayi dan kuwa kwata kwata sun dena ganinsa har ita har mum dinta wadda duka baifi so biyu yazo har bangarenta ya gaidata ba sedai yana aiko mata gaisuwa duk jumaa akai akai sbd bata matsayinta na uwa a garesa.
Duk lokacinda zai taho gaida mahaifiyarta saita sake mutuwa me zurfi akansa sbd gabaki daya ya sauya daga LEUL NUAB a yanzu ya koma cikakken SULTAN LEUL NUAB dinsa me tsantsar kwarjinin dayafi na baya.
Haukacewa take neman yi akan rashin samuwarsa dan haka ta cire kunyarta ta sanar da mahaifinta aure kawai takeso ayi mata ta gaji da jiran maganar aurenta data kwanta da NUAB din ita dai a tada maganar ayi mata auren koda shi bayaso ita tana so.
Maganarta tayi tasiri sosai a zuciyar mai girma yunar wanda shima zuwa lokacin yana ganin ya bada duka lokacin daya kamata ya bayar na barin NUAB yagama shiryawa akan mulkinsa duk da yayi farin ciki sosai da hatta Shuraim ya samu matsayi me girma a cikin tafiyar sarautar ta NUAB wadda Aleey kai tsaye ya saka sunansa a ciki dan hanasa tafiyar daya samu cikakken bayanin tafiyar zaiyi zuwa uk a bakin Mum zuhrah lokacinda sukaje gaidata dan haka kai tsaye ya saka alaman tambaya akan tafiyar da bai samu cikakken dalilin yinta ba a binciken dayayi bayan jinta dan hakanne ya gabatar da sunansa da wasu boyayyun hujjojin daya saka NUAB amincewa batareda yasan asalin dalilinba.
Bawa Shuraim matsayin ministern hukunce hukunce ya saka zuciyar iyayensa farin ciki sosai dan kuwa ya shiga cikin royal politics kenan zai fara kutsawa a sarautar qasar,
Su Ammi ma da suke can sunyi farin ciki sosai da hakan sbd ganin NUAB yafara jan dan uwan nasa a jikinsa,
Haile data samu labarin maganar auren da yunar yake kokarin sake tadawa akan yarsa wadda bazata iya barin NUAB ya aureta ta rasa damarta ta karshe ba akan cire bahar daga rayuwa da zuciyar Asim ba shiryawa tayi a cikin daren takaiwa sultan yasar ziyarar da bai taba tsammani ba dan haka babu kowace irin sauyi a yanayinsa ya karba zuwanta tareda bata damar kasancewa dashi.
A bangaren nasa ta kwana wanda da safe kafin ta wuce ta isar masa da buqatarta da rokonta na nemawa Asim auren leylah a gurin mai girma yunar.
Kallanta sultan yayi a karo na farko bayan lokaci kafin ya juya buqatar tata a zuciyarsa ya sauke numfashi a natse kafin ya bude baki yace ya amsa buqatarta a yau zai aika sakon takardar neman auren leylah wa Asim.
Farin ciki taji ya sauka a xuciyarta bayan watannin data share a cikin quncin baqin ciki tayi godiya tareda ficewa dan kuwa a gaggauce zata tabbatarda an daura auren dan matiqar aka karba auren a kwana uku kafin a samu matsala take son a daurasa.
Tana ficewa shi kansa sultan bai tsaya komaiba ya aikawa yunar sakon wanda yana isar masa shima bai ga illar hakan ba tinda ga dukkan alama NUAB baida raayi kuma shi bazai zabi kwadayin mulki ya aurawa leylah Sultan din da baya buqatanta ba dan haka kai tsaye ya maida saukon bada auren nata ga Asim wanda shima sultan sakon na dawo masa ya buqaci auren da gaggawa sbd yasan zaa iya samun matsala gwara ayi sa su daidaita kansu daga baya.
Koda sakon auren ya isa kunnen zuhrah har yunar ya karbi sadakin auren wanda take aka fidda sanarwar daurawa ranar jumaar da saura kwana hudu dan haka batai wani baqin ciki ko damuwa ba sbd tafi kaunar leylah din tayi aure ta cire NUAB a ranta sbd Bahar daya riga ya aura batason duk abinda zai lalata ko kawo matsala ga kaunarsu da yar uwarta ayanah dan haka da hannu bibbiyu ta amsa auren kafin ta kira leylah dan sanar da ita babban lamarin dake shirin faruwa. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee
114 Leylah na shigowa lafiyayyan bedroom din mahaifiyarta ta nufota a natse yanayinta a dan sanyaye sbd bacci ta tashi dan tin kafin baccin nata sakon kiran mum din ya isa gareta amma sbd tayi shirin baccin hutawa na rana shiyasa bata taho ba saida yammar bayan ta tashi taci abinci tayi wanka ta nutsu amma jikinta hakanan yake mace har lokacin da sauran yanayin baccin datai,
Zuba mata ido Zuhrah tana kallanta a lokacinda take tahowar tanajin tausayinta sbd gabaki daya ta sauya harda yar ramewa tayi sbd kwallafa rai akan wanda takeda tabbacin ba lallai ya taba yi mata so na soyayya ba tinda gashinan bahar din ma da already aurensa yake kanta ba sonta yakeyiba yama mance da ita bare ita da baima aura ba, Hakama bayan hakan tayaya zata iya barin son zuciya yakaita iya barin leylah ta auri NUAB bayan yana auren bahar wadda tin kafin asan ma zasu zo duniyar akai alkawarin aurensu a tsakanin iyayensu wato abaas da ayanah, Gwara dai suji da dayan ciwon rai da damuwan Bahar daya tattara ya watsar akan su qara sa wata damuwar dan haka ta sake jin qwarin gwiwan gwara leylah din tayi aurenta da Asim din tinda shima baida matsalar komai a gurinta bataga kowace illar ba a bayyane dashi.
Zaunawa leylah tayi tana kallan Mum din ta sauke ajiyan zuciya tareda bude baki tace
'Mummy Lafiya kika kafeni da kallo haka kaman na tausayi?'
Numfashi Zuhrah ta sauke a karo na biyu tana sake tausayawa Leylah din dan haka take zuciyarta taji gwara ma kada ta fada mata a yanzu sai ankwana biyu zuwa gap da auren ta yanda kafin tafara damuwa da shiga tashin hankali anriga an daura auren dan haka dan sakewa tayi tana murmushi me kyau tace
'Ba komai tukuna amma maganar aurenki ce ta taso wadda insha Allah zuwa friday muke saka ran komai ze iya kammala dan haka saiki fara shiri hakama kada ki fita koina daga bangaren nan dan kaucewa matsala tinda kinsan dai amarya kike'
Wani irin yanayi taji yana ratsa zuciyarta wanda yake na tsantsan farin ciki da kuma ta bangare daya mutuwar jiki sbd bata taba tsammanin jin hakan ba dan kuwa ko a yanzu idan akai magana kila zaa iya saka date na daura auren nesa amma dai koma yayane taji tana tsananin kaunar zuwan ranar jumaar sbd jin matsayar da ake akai.
Da farin ciki ta rungume Mum din tana godia sosai tareda miqewa da sauri tabar dakin dan zuwa dakinta ta fara lalaban wayarta dan kiran qawayenta ta sanar dasu cikin izza da alfahari,
Ajiyan zuciya Zuhrah ta sake bayan fitar leylan tareda bude baki batareda jin tana karaya ba akan auren tace
'Allah ya sakawa auren albarka ya saka ya zamar miki mafi alkhairi akan na NUAB din tareda farin ciki da dawwamamman kwanciyan hankali dan yafi muna gabaki daya kwamciyan hankali da kawar da damuwan da zata iya shigowa zumunci.'
Leylah na isa dakinta tinda ta fara wayoyi bata sake fitowa ba har washe gari wanda yake sauran kwana uku kenan,
Daga mai girma yunar har sultan gayyatar daurin auren a tsare suka fitar akayi shi bayan sultan ya isar da sakon auren ga sultan LEUL NUAB shima baiji komaiba ya aminta tareda bada approve na auren duka a cikin qanqanin lokacinda kowa yake mamaki banda wainda zaa daurawa auren da basada cikakken sani sbd haile datasan Asim bazai taba yadda da aurenba tare duk wani motsinsa na yanda sakon auren zai isa garesa tayi ta hanasa fitowa bangarensa cikin kwanakin tamai alkawarin basa mamakin da zai sauya rayuwarsa zuwa ta farin ciki a kwanakin idan har ya zauna bai fita koina ba bai kuma kunna wayoyinsa ba ya fake da cewan baida lafiya kawai takeso.
Idanuwansa da zuciyarsa a rufe suke da son samun yancinsa na barin boyem da mahaifiyarsa ta saka masa takunkumi dan haka jin zata iya barinsa yabar qasar daga ranar jumaa din ya sakasa amince kawai tareda kashe wayoyinsa sbd daman baya fita koina yanzu hakama koyaushe cikin damuwa da rashin amfani yake shiyasa rayuwar tasa take a mace mutus yanzu.
Su Aslam kuwa da tashin hankalinsu baifi kada Asim ya taba barin boyem ba sbd dukansu sunsan gurin wa zai tafi kuma zuwansa ga bahar zuwa ne ga mutuwarsa duk da a ransu da zuciyoyinsu tare ma da masarautar boyem din sun gama tabbatarda ba aure a tsakanin Sultan NUAB din da bahar dan kuwa basu ga alamarsa ba tayaya sultan yana nan yana mulki matarsa na wata qasar daban tana rayuwar da ba ranar dawowa.
Haile samun abinda takeso da zatai ya saka karfinta dawowa dan tabbatarda auren Asim da leylah zai fara dawo da abubuwanta a hanya dan kuwa dole asim din zai fito daga mutuwan dayake yiwa kansa da rayuwarsa daganan komai zai sauya musu,
Shirye shiryen gaske sukeyi sosai na bikin wanda babu wata doguwan shagalin da zaayi daman su bikinsu a rana daya ake yinsa ayi duk gagarumin shagalin da zaayi a lokaci daya a gama shikenan,
Dukiyar Uwar Ango da ake kaiwa amayar komai da komai masu bayyanarda tsantsar gata da daular arziki haile ta hada tareda iyayenta da suka qaraso qasar duk da sun manyanta sosai amma hakanan sun taho auren asim din haka aka hada aka aika bangaren me girma yunar zuwa ga Mahaifiyar Amarya kuma sun karba tareda tukuici me girman gaske daga iyayen leylah din tin daga nan al'adun biki suka barke tako ina aka dauki harama ba sauki wanda dole ya saka Leylah shiga wata muguwan fargaba da shakka ta samu mahaifiyarta tin kafin tayi maganar data kawo ta akan kunnuwanta taji maganar aurenta da sunan da batajin kunnuwanta sunji daidai daga bakin mahaifinta take kafafunta suka kasa daukanta ta zube qasa batareda shiri ba ta rarrafawa idanuwanta na sauyawa ta isa gaban mahaifinta dake zaune a tareda mahaifiyarta a palon tareda shuraim wanda yayi mugun busy din da yau kusan sati guda basu gansa ba sedai a waya yana can bangarensa ayyuka sun mugun yi masa yawa yana jin shima hankalinsa na rabuwa biyu a tsakanin matsayin daya samu na sarautar da tattarawa ya koma uk yayi aikinsa acan da rayuwarsa.
Leylah rawa jikinta yakeyi sosai tana wani irin bari tareda kokarin danne abinda yake kokarin tasowa ya danne numfashinta daga cikin kirjinta ta kalli Abbinta tace
'Abbi hidimar me akeyi ne? Kuma ta auren waye abbi?
Juyawa mai girma yunar din yayi ya kalli Zuhrah sbd mamakin bata sanar da ita ba bayan tintini ya fada mata ta sanar da ita tin farkon ma maganar auren.
Kallansa Zuhrah itama tayi cikin dan rasa abin cewa yanayinta na nuna sanyi da tausawa.
Maida kallansa yayi akan leylah din wadda har lokacin hannuwanta rawa sukeyi tana kallan Abbin bugawan zuciyarta na mugun tsananta amsar zancen take jira a matse.
Take Abbin ya karance halin da take ciki wanda ya tabbatarda taji maganar kenan tabbatarwa take son yi kuma da cikakkiyar alaman bata shirya karban hakan ba dan haka numfashi ya fitar shima a natse sbd bayajin wannan karan shima ya shirya sake barin maganar aurenta ta gantale a karo na biyu dan haka kai tsaye ya bude baki yana dan kama fuskarsa zuwa tabbatar mata sa abinda zai fada yace
'Aurenki Sultan ya nemawa 'dansa Asim kuma ba bayar dan haka gobe ne kadai bazaa daura auren naku ba insha Allah'
Dif kunnuwan Leylah suka dauke tareda bugun zuciyarta ta kasa motsawa ta qame idanuwanta na sauyawa zuwa mummunan ja na shock din dayafi kowane zama balain rayuwarta ta fara wata irin rawar jiki tana son bude baki tayi magana amma ta kasa dan haka sai kawai ta zube a gurin.
Kallanta Abbin yayi cikeda mamaki sbd yasan dai wannan karan aurenta ba fashi dan haka ya kalli mum din tata data tashi da sauri tayi kanta tareda shuraim wanda ya sauketa gavaki daya yana barin palon da ita zuwa dakinta.
Binsu Zuhrah tayi da sauri tana ji itama a ranta ba maganar fasa auren nan sedai leylah din tayi hakuri,
Shuraim ne ya taimaka mata kasancewansa likita kuma dan uwanta dan haka bata wani jima ba ta farfado cikin mummunan tashin hankalin da bata shigaba rayuwarta ta fara kallansu daya bayan daya su biyun sai kawai ta fashe da wani irin kuka me karfin gaske tana kama hannuwansu ta qanqame da hannuwanta dake rawa sosai cikin mummunan baqin ciki da rikicewa tace
'Dan Allah da girmansa Mum kada kumun haka, Mum wlh banma riqe kamanninsa ba,bana sonshi ban taba son kowaba mum bayan NUAB, Wlh mum zan iya mutuwa idan na auri wanda ba NUAB ba,ni wlh mum shi wannan din bana kaunarsa,bana sonsa bana son jin ma maganar auren dan Allah ku ceci rayuwana ku hana wannan auren,,,,
Qanqame hannun shuraim tayi da karfi shima tana dawo da kallanta akansa da jajayen idanuwanta da sukai jajir tace
'Shuraim mutuwa zanyi idan akai auren na wlh tallahi banaso ban kauna ka taimaki rayuwata dan Allah a hana wannan auren'
Dukkaninsu ba wanda ya iya ce mata komai sbd anriga angama komai baqin bikin auren tini suka fara cika masarautar hakama sultan NUAB ya riga ya fidda sanarwar auren harma anyi komai na daurin auren an gama babu ta yanda zasu iya hanasa sedai tayi hakuri kawai gashi shi kansa Shuraim din a yanzu yafi mata shaawan auran wanda ba NUAB ba sbd a yanxu dayake tareda shi ya qara sanin asalin waye shi sam babu alaman akwai tsarin mace a rayuwarsa koda akwai to tabbas kila bazatai darajar da mace ke yi ba a gurinsa sbd babu wani me daraja a gurinsa da yaransa bayan shi kadai kansa hakama duk macen da zata shiga rayuwarsa batareda yana sonta ba tabbas zata sha wahala me tsananin da rayuwarta zata iya mutuwa a banza sbd tsaurin raayinsa da zafinsa da kaf duniya ta sheda yanada shi dan haka ba amfanin taje gurinsa tinda bai taba sonsa ba bahar ma dayake aure insha Allah zai tabbatarda ta fito ta rabu dashi ya mallaketa dan shi ne kadai zai bata rayuwar datake buqata ta kauna da tattali. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee
115 Ganin babu wanda ya nuna alaman tausayawa da yadda ga buqatartaba ya sakata saukowa daga gadon datake idanuwanta a rufe ta koma gurin mahaifinta tin kafin ta iso gabansa ta zube qasa jikinta na tsananta rawa tafara rokonsa cikin mummunan tashin hankalin daya sakasa cewa mum dinta ta jata su tafi kawai bayason jin komai.
Tana jin hakan kanta ya qarasa zarewa gabaki daya ta fara wani irin kuka tana jin son barin duniya kawai,
Janta Zuhrah tayi akan dole suka koma daki wanda har lokacin wani irin kuka takeyi tana jijjiga sbd batajin zata iya zaman aure da kowane namiji har abada idan ba NUAB ba, Idan NUAB dinne yace bazai auretaba tafison abarta ta tsufa harta mutu tana jiransa har yayi raayin auren nata amma bazata taba iya auren dan uwansa ba wanda tana aurensa batada sauran hope ma sbd aurenta da NUAB ya gama haramta kenan matiqar Asim din yana raye...
Rungumeta zuhrah tayi da sauri a jikinta tana qanqameta sbd ganin yanda jikinta ke wani irin bari yana fizga sbd tsananin tashin hankali da baqin cikin dake neman buga zuciyarta a banza.
Kukan datakeyi ya wuce na hankali dan haka jikin zuhrah yafara sanyi tana jin fargaba na shigarta dan kuwa da gaske kila mutuwar zatai sbd take ta sauya idanuwanta sunyi jajir ba kyan gani,
Rungumeta zuhrah ta sake yi tana kokarin rarrashinta sedai ko jinta leylah batayi.
****Asim shima a ranar Yayarsa Neesa ta iso boyem sbd auren tareda yayanta duka dan haka dole ya fito sbd babban 'danta daya samesa har bangarensa ya gaidasa sukai fira sosai wanda a bakinsa yake jin maganar auren wadda bai fahimtaba sam duk da yayi mamakin zuwan nasa katsam amma sam bayajin a daidai yaji maganar dan haka ya dan sake kallan Farhan din yace
'Kace hidimar aure kukazo??
Gyada kai yayi yana ajiye wayarsa gefensa ya sake kallan uncle din nasa yace
'Eh,naso ma zuwa tin shekaran jiya kafin su Maamah su iso flight ne na baro germany ban samuba zuwa gida dole sai daga baya na samu shiyasa dole na jirasu muka taho tare'
Asim still bai gane ba dan se bai sake magana ba sbd baya ma son farhan ya gane halinda yake kokarin shiga dan haka yabar maganar har saida farhan din ya wuce tukuna ya shirya ya baro bangarensa kai tsaye bangaren sultan ya fara zuwa ya gaidasa cikeda girmamawa wanda sultan ya kallesa da mamakin yanda ya koma tamkar wani sakarai sbd kome mahaifiyarsa ta dora akai hawa yakeyi batareda tinanin komaiba duk da hakan ba illa bane amma kasancewansa namiji ya kamata yasan wani tinanin da aikin na mata ne kadai koda kuwa uwa ce.
Babu wata sauran kwana kwana ko boye boyen dayasan haile nayiwa Asim din ya sanar dashi halinda ake ciki akan daurin aurensa da zaayi banda goben kuma ya tabbatar masa da baya buqatar kowace irin hayaniya ko wani sabon zance ya tashi ya tafi kawai yaje yayi shiri.
Yanda sultan yayi maganar a daure da kaifin umarni ya saka Asim kasa cewa komai yai mutuwar zaune yanajin duniyarsa na juyawa,
Ta jima zaune bai iya motsawa ba kaman gunki kafin ya motsa daqyar ya miqe ya fice zuciyarsa na wata irin tafasa da radadin dayake jin kaman gangar jikinsa zata kama da wuta sbd mameensa ta rifesa tayi masa abinda ya mugun ruguza zuciyarsa akan ayyukanta daga yau hakama ta kashe masa sauran hope na rayuwar dayake dashi dan kuwa har abada bazai taba so ko rayuwar aure da kowace macen da ba Bahar ba,
Bahar yake so kuma akanta yake shirye da mutuwa dan kuwa tinda ba aminta NUAB yayi ya amsa aurenta ba ya tabbatarda zata fito idanma bata fito dinba kenan dan haka bai taba cire rai daga mallakarta ba, Me zaiyi da wata 'yar yunar wadda NUAB ya gama cewa baya so shine zaa liqa masa to shima baya so sam baya kauna,
Tsananin bacin rai da baqin cikine me girma suka cike zuciyarsa da idanuwansa dayaje jin inama ya bude ido ya gansa a inda shi kadai zaiyi rayuwa batareda kowaba sbd baqin cikin da sukai masa,
Fasa zuwa bangaren mahaifiyar tasa yayi sbd babu amfanin zuwansa ga abinda yasan ba fasawa zaayi ba hakama a yanzu da sultan yayi magana ko mameen tasa bata isa ta saka a fasa wannan auren ba wanda baida suna a zuciyarsa,
Bangarensa ya wuce kai tsaye tareda manyan bayinsa biyu dake biye dashi,
Yana zuwa rife kansa yayi bai sake fitowa ba hakama bai sake barin kowa ya shigoba dan umarni ya bada haka ya kebe kansa wani mummunan baqin ciki na neman kashe sa,
Haile hidimarsu kadai sukeyi sbd zuwa lokacin tasan ya sani amma tinda bai taho ba itama tafison hakan dan ko yayane koma wane halin zai shiga ya shiga ita dai ta samu a daura auren ko zata samu nutsuwan zuciya.
***bangaren leylah gabaki daya ta fice hayyacinta ta wuni ta kwana kuka har karfinta ya qare tas ko tashi zaune bata iya yi sbd jiri da ganin da batama iyayi sbd kumburan ido da fuskarta,
Zuhrah tayi iya yinta akan rarrashinta amma sam babu cigaba ko sassauci dan haka ta barwa Allah ta ringa yi mata addua gashi ta kasa fadawa Ayanah sbd kada ma Ayanah tayi tinanin tirsasa NUAB dan auren kwata kwata hakura dashi sune best ga dukkansu,
Tadai sanar mata zaa daura auren a kurarren lokacinda bazasu samu tahowa ba dan haka ayanah tace ana daura auren su taho uk din honeymoon a matsayin nata tukuicin.
Leylah na jin hakan sake shiga mummunan hali tayi, Asim kuwa sakon na isar masa take zuciyarsa tayi naam da hakan cikin wata irin sanyi daya manta yaya take a zuciya dan kuwa damar dayake jira ta tsawon lokaci ta samu zai bar boyem kuma kai tsaye uk zashi,uk dinma kai tsaye gurin wadda Bahar dinsa take hannunta..
Wannan sakon shine ya sauya halinda Asim din yake ciki take ya dan warware yana fara shirin daya kamata yayi na auren wato gyaran jiki dana fuska irin na maza da dai sauransu.
Duk yanda akaso yiwa Leylah gyaran daya kamata baa samu cikakkiyar damar ba sbd mugun yanayin datake ciki wanda gabaki daya ma a qanqanin lokaci ta rikice ta yamutse tamkar ba itaba ta koma kaman me zaman takabar miji da 'yaya.
Duk da hakan zuhrah bata kyaletaba dole tayi mata aka dan fara yimata gyaran da zai samu sbd ko anyi baya wani bayyana dan halinda take ciki na baqin ciki da qunci.
A haka dai ba dadi bangaren Amaryar suka samu akai duk abubuwan daya kamata har zuwa daren daurin auren wanda har safiyar garin ta waye leylah bata rintsa ba taba zaune tana kukan da baida magani,
Ba kyan gani ko kadan ta tashi a safiyar daurin auren hakama ta rufe dakinta babu wanda ya ganta duk yanda akai akai tafito abin ya gagara sai kawai zuhrah tace a kyaleta,
Kafin daurin auren da safe Maa sakinah ta iso ita kadai sbd dole dayansu na buqatar kasancewa a gurin bikin yar zuhrah duk tsanani kuwa ko ita ko Ayanaah sbd sune iyayen amarya kuma iya su kadaine dangin Zuhrah dan haka zuwansu dole ne.
Ayanah bata taho ba sbd akwai abinda NUAB yayi mata ashe batareda saninsu ba na bazata iya barin qasar ba sai shekaru biyu dan haka dole ta hakura zata shirya tarban su Leylah din da mijinta acan.
**Ana gama sallar jumaa a babban masallacin qasar boyem dake cikin masarautar boyem aka daura auren na LI'ULI ASIM ALMAZZ BOYEM da LEYLAH YUNAR BOYEM wanda dubban manyan qasa da sarakunan qasashe suka sheda tareda yan jaridu akan sadakin silallan zinari masu yawa sa Sultan LEUL NUAB ya biya masa wanda ko sultan yasar bai tsammanin hakan daga garesa ba amma yaji dadin hakan sosai.
Ana gama daurin auren Asim ya koma bangarensa ya rufe yana jin kaman zai kone sbd baqin ciki da tiririn dayake,