Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 45
Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 45: Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 45. Ita kanta leylah din ana gama daurin auren…
4,480 words
Ita kanta leylah din ana gama daurin auren wanda kunnanta akai komai suna ji koina a cikin masarautar silalewa qasa tayi tana rintse idanuwanta da suke a jan su tana dafe kirjinta dayake wata irin zafi da quna tana jin a ranta matiqar zata samu NUAB wlh Asim saiya bar duniya. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee
116 Su kuwa masarauta da mutanen dake cikinta dama wainda suka zo bikin hidima akeyi sosai hakama tini masu shirin amarya suka taho wanda ga mamakin zuhrah da maa sakinah da babu rarrashin da basuyi mata ba amma sam taqi sassautawa kanta sai gashi kaman a mafarki ta bari ayi shirin nata dan haka ruwan wankan madara da kayan qamshi da lalle aka hada mata masu karfi kafin maa sakinah ta kamata da kanta ta kaita da kanta zata mata komai.
Sosai Maa sakinah ta jiqata a cikin ruwan lallen da madara tsawon lokaci kafin ta fito tabarta ta qarasa tubewa tayi wanka.
Kodata fito dukansu suna dakin nata suna jiranta,Maa sakinah da mummy dinta dan haka cikin kulawa maa ta isa inda take ta zaunar da ita gaban mirror tana goge mata gashinta dayake daukan ido sbd baqinsa da gyaran dayasha gurin jiqon da maa din tai mata a toilet.
Tana gama goge mata gyarasa tayi ta busar mata dashi da hand dryer ta gyarasa tsaf da abubuwan da duka suka kamata kafin tabarta tashafa mai da kanta ta sake binta da wasu mayun tirarika masu qamshin dayake kashe zuciyar duk wanda ya shaqesa tukuna aka bawa masu kwalliya da shirinta daman shigowa su kuma suka fice daga dakin.
Gyarata akai tsaf kafin aka fito da ita cikik shigar asalin yar gatar sarauta datake daukan ido aka fice zuwa taron gagarumin bikin da zaayi a cikin masarautar wanda aka barar da dukiya gurin hadashi.
Haile bata damu da alaqar dake tsakanin Zuhrah da Ayanah ba wadda aka bayyana sbd tasan dai basa kaunar junansu yanda ya kamata shiyasa suka rabu tsawon shekaru masu yawa hakama wata sabuwar damace gareta ta samun makusancin Ayanaah a jikinta dan zatafi jin zafi da cutatuwa idan aka damu damarta ta hanyar qanwarta uwa daya uba daya hakama duk kaunar da zasuwa juna dole sai zuhrah tafi son yar data haifa akan ayanah hakama mijinda leylah ke aure sai yafi mata 'dan yar uwarta NUAB daya qi yarta.
Bikin alfarma aka gudanar a wuni guda wanda ya zaga koina an baza arziki an zubar dashi anyi duk wata gagarumar al'adah a ranar har dare tukuna aka gama aka watse.
Sabon bangare na musamman washe gari aka warewa Li'ul Asim da amaryarsa wanda aka zubawa sabuwar dukiyar jin dadi luxuries ne tako ina suke kuka sai da akai kwana biyu ana gyaran kafin aka kammala tukuna akai shirin kai Amarya leylah wadda tasha nasiha sosai a gurin iyayenta kafin aka kaita gurin Haile da danginta suma sukai mata tasu nasihar suna jin karfinsu da farin cikinsu ya dawo dan kuwa Asim dole yanzu zai fara dawowa a hanyar da suke buqata dan kuwa dole yana sanin wata 'ya mace zai manta da bahar sbd jin kansa a duniyar da bai taba saniba hakama a duniyar da kila itace yake kokarin son sani a gurin Bahar din tinda daman a imebēti zai karbeta.
Koda aka kai leylah bangaren mijinta babu wani tsayawa dogon bayani aka barota suna ficewa ta miqe daga babban lafiyayyan palon ta wuce bedroom din da aka sanar da ita shine nata bayan guda biyu da suke extra dayan nasa ne wanda yake hade da wani lafiyayyan palon sai dayan dayake nesa kadan da nata din wanda yake extra ko dan baqi tukuna guda daya daga can kitchen wanda yake na bayinta.
Bedroom din ta shige ta rufo kofarta tareda saka key ta fara zare kayan jikinta dake zuba qamshin da duk ya dameta zuciyarta na suya da tafasar baqin ciki ta wurgar dasu ta fada bathroom ta wanke duk qamshin jikinta da adon duka ta fito ta saka kayan bacci tayi kwanciyanta tana jin tafi Asim din matsuwa dasu bar masarautar su tafi inda zatai rayuwarta yayi tasa kafin tasan matakin dauka akansa dan kuwa bazata taba yadda daci gaba da zaman aure dashi ba.
Shi kansa Asim din baida niyar fitowa bare ganinta ko abinda ma zai tina masa da wata macen yake aure a yanzu ba Bahar ba dan haka har safe basuji ko motsin juna ba.
Washe gari bayin da aka aiko daga bangaren Mameensa suka iso dan fara aikinsu dan haka ko da sukai breakfast da sauran ayyukan har suka gama bata fitoba tana daki sai karfe goma sha daya ta fito sanye da riga da wando masu fadi sosai ta nufi dining da wayarta a hannunta tana duba sakon Shuraim dayake ta kiranta bata dauka ba tana bacci.
Zaunawa tayi batareda ko amsa gaisuwan bayin nata ba aka zuba mata abinci taci sama sama ta koshi ta miqe tabar gurin ta koma palon ta zauna har lokacin idanuwanta da fuskarta basu koma daidai ba a kumbure suke jajir sbd ko a daren jiyan tayi kukan baqin cikin ranar daren aurenta na farko ta kasance da wani ba NUAB ba dan kuwa sa NUAB ne da kanta zata kai kanta garesa dan raya masa daren amma a yanzu batajin ko hannu zata iya hadawa da Asim bare shimfida ya jira bahar kaman yanda zata jira NUAB.
Tana nan zaune shima ya fito yana fidda qamshinsa da shigar kayan shan iska shima ya nufo palon yana waya kallo daya yayiwa inda take ya wuce yana ci gaba da wayarsa sbd ganin itama ko kallansa bata dago tayiba batasan yama fita qin aurenba dan shi zai iya keta kowane irin hadari akan Bahar wanda ita ba lallai ta keta akan NUAB ba.
Breakfast dinsa yayi ya gama ya miqe ya baro ya sake shigewansa basu sake ganin juna ba sai dare wanda ko data fito ta iso dining din yana kai dan haka juyawa tayi zata bar gurin ya bude baki yace
'Ba buqatan wannan takura kan ki kwantar da hankalinki sbd ba kinsan waye a gabana da zuciyata, Ita nake da raayin aure haryanzu kuma bazan huta ba saina tabbatarda na mallaketa a rayuwata so just calm down Miss'
Dakatawa tayi daga inda take din tsaye maganar na shigarta da qani sabon takaici da baqin ta rasa me suka gani a bahar din suke nace mata, Koma dai menene tinda abinda take so kusan shi yake so na raba NUAB da bahar zata kwantar da hankalinta ta ingisa yayi mata aikin da zata samu abinda takeso hankali kwance.
Ajiyan zuciya ta sauke tareda juyowa ta dawo ta zauna dining din ta kallesa a karan farko wanda shima ita din ya dago ya kalla suka hada idanuwansu a cikin na juna ta fara dauke nata taba bude baki tace
'Tinda kasan nima ba kai nakeso ba to da sauki zan zauna dakai nima kafin na samu tawa mafitar a cikin taka da zaka samu'
Murmushin takaici ya sake kawai batareda ya ce komaiba yaci gaba da cin abincinsa itama tafara ci hankali kwance.
Wuni sukai suka kwana biyu babu wanda yaxo bangaren nasu aka barsu suka huta sosai dakyau kuma suka fahimci juna akan tsayawa manufa daya ba takurawa dan haka suka sake nutsuwa suka dan kwantar da hankalinsu da kwallafa rai a sabon buri me karfi.
Maa sakinah ana sati daya da gama bikin ta tattara ta komawarta sbd Bahar da koyaushe data dameta ta dawo ta dawo.
Maa sakinah na tafiya Asim da leylah suka fara gajiya da matsuwan kiran Ammi wadda tace zata kirasu su taho idan ta gama hada musu komai amma shiru ba kowane kiran,
Leylah gajiya tayi ta cire kunya ta kira Mummynta tayi mata maganar tafiyarsu honeymoon din amma zuhrah ta shareta sbd bazata iya yiwa ayanah maganar ba kuma koyaushe suna waya.
Asim daya kasa hakura kuma bazai iya cigaba da jira ba fara shirya musu tafiyar yayi da kansa kai tsaye,
Koda haile taji tafiyar da suke kokarin yi din bata damu ba bari tayi suje su yawota duniyar su dawo tukuna ta dorasa daga inda ta tsaya dan haka da kanta ta tayasu shirin tafiyar ta hanyar fara yiwa leylah sabbin shirye shiryen gyara da tsimawa da gyaran fata.
Biye mata kawai sukai akan gyaran muradi dai su samu su tafi subar boyem,
A lokacinda Maa sakinah ta koma Uk cikin mamaki ta tadda Ayanah na fama da mura me karfin gaske data kaita har kwanciya asibiti kuma basu fadawa kowaba suka boye shiyasa ma bahar da hankalinta ya tashi sosai ta takurawa Maa din ta dawo sbd ganin ayanah a asibiti ya tada hankalinta sosai ta shiga tsoro sosai.
Ciwon nata ne ya hana sam ta tada maganar zuwansu leylah honeymoon din datai alkawari saita warke,
Zuhrah ma bata saniba sbd tana kokarin waya da ita dan kada ta gane.
Sultan da NUAB kuwa kwata kwata a kwana biyun dena waya tayi dasu wanda take hakan ya sakawa sultan tinanin ba lafiya ba.
Tenya ya kira personally ya tambayeta abinda yake faruwa ta sanar dashi suna asibiti da Ayanah har lokacin sbd kaman sanyi ne ya shigeta sosai amma tafara jin sauki.
Shiru yayi kafin ya kashe wayar kawai ya ajiyeta gefensa tsawon mintina masu dan tsayi kafin ya miqa hannunsa a natse ya dauki wayar ya saka kiran kadir.
Kadir na dauka cikin nutsuwa ya sanar masa ayi masa shirin tafiya uk a kwanakin da bazasu wuce sati daya ba. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee
117 Kadir amsawa yayi da tabbacin cika umarnin dan haka yana kashe wayar ya saka kiran hada tafiyar shima,
A daidai wannan lokacin Shima Sultan LEUL me boyem shirin barin qasar yakeyi zuwa Moscow sbd wani babban business meeting da zaiyi da manyan business tycoons dinsa da suka jima suna son ganinsa ba dama sbd sarautar daya tsaya daidaitawa dan haka a yanxu ya basu damar ganinsa zasu hadu a Moscow suyi meeting din dan bazai hade GHAZ business dinsa ba da sarauta dan haka a karan farko bayan hawansa mulki zai bar qasar boyem yayi tafiya zuwa wata qasar dan haka keela ne wakilinsa da zaa bari da sauran manyan masarautar da zasu kula da komai kafin dawowansa.
Koda labarin tafiyar Sultan LEUL zuwa Moscow ya riski Sultan yasar jin yayi ya samu wata nutsuwa da kwanciyan hankalin tafiyarsa a natse duk daman NUAB kome zai zama a rayuwa bazai iya hanasa duk abinda yayi niya ba kawai dai ya zauna ne a bisa umarnin nasa sbd bayyanarda zaman lafiya a idon duniya a tsakaninsa da 'dansa tare kuma da hanasu samun hayaniya a wannan lokacinda NUAB din yake buqatar tattara hankali da nutsuwansa akan abinda yake gabansa na daidaita mulki tareda kuma bawa ayanah cikakken hutun dataje yi kafin ya isa gareta amma a yanzu dayaji batada lfy babu abinda zai hana isarsa gareta bayan mutuwarsa amma jin tafiyar da NUAB zaiyi saita sake basa nutsuwa dan yasan a yanda ya dade baya Moscow to zai kwana biyu sosai acan kafin dawowansa.
Ko kwana biyar baayiba da maganar ta isa ga sultan yasar tawagar Mai girma Sultan LEUL NUAB ta daga zuwa Russia wanda yana barin qasar boyem masarautar ta sake tsit sbd ba wata mulki kuma sai me qasar ya dawo.
Ita kanta haile suna jin fitar Sultan NUAB daga masarautar ajiyan zuciya suka sauke itada yayanta a tare suna fatar har abada kada ya dawo ya hadu da ajalinsa acan.
Asim ma numfashi da ajiyan zuciyar farin ciki ya sauke yana jin kamar an sauke masa wani mummunan nauyi sbd a yanzu kam zaiyi tafiyarsa a saa da farin ciki NUAB da shegunsa basa boyem hakama basa uk suna wata qasar da fitowansa ba yanzu ba dan haka ya sake bada qaimi a gurin ganin tafiyansu ta kammalu, Ita kanta leylah tinda taga NUAB yayi tafiya gabaki daya ta tada hankalinta akan suyi su isa uk dan ganin takeyi kamar zai iya wucewa can ba Moscow din ba gwara su isa su samu bahar kafin ya isa ya ganta ta sauya ya iya sauya tinaninsa akanta.
Yanda ta takurawa Asim din akan tafiyar har fada sukai sosai yayi mata gorin marasa zuciya akan namiji itama tai masa gorin maye akan mace ba dadi dai suka rabu a daren sai kuma gashi da safe sun shirya kaman basuyi yar gorinba a daren sukaci gaba da shirinsu na tafiya.
Tafiyar NUAB da kwana biyu jirgin sultan yasar shima ya daga zuwa uk wanda ya saka Haile kusan mutuwa sbd baqin ciki da mamaki me girma sbd ta gama shirinta tsaf akansa shima na kaudasa 'dansa NUAB da ayanah basa nan daga ita sai yayanta a masarautar sbd yanzu baima sa imebēti ko daya daman tin daga kan ayanah bai qara dauka ba wainda suka rage guda biyu suma ya sallamesu kwanakin da NUAB ya fidda sabon tsari daman an dade da shafe tarihinsu basada amfani ko daya zaman kadaici da jin dadi kawai sukeyi.
Maraki ma koda sakon Sultan na tafiyar ya sameta a wayarta kasa dauke idanuwanta daga kan sakon tayi tayi shiru zuciyarta na qullewa da baqin cikin da shine zai zama ajalinta tin na shekarun quruciya datake kwasa haryanzu bata dena kwasa ba,
Jefar da wayarta tayi gefenta tana rintse idanuwanta da suka sauya tareda jin bazata iya ba ta gaji da rayuwar datakeyi gwara tasan takabarsa takeyi akan mugun baqin cikin datake kwasa dan haka kai tsaye fatar kada Allah yasa ya dawo tafara yi masa ya mutu a hanya kowama yayi takaba ya huta asan babu sultan yasar batada 'yaya baqin cikinta kadan ne na mutuwar tasa.
Sultan na barin boyem wani sabon farin cikin yayiwa Asim da leylah yawa dan shima suna shakkar ya hana tafiyar cikin saa kuwa sai gashi tafiyarsu ta kammala amma jirgin yawo ne suka samu saiya tsaya qasa kusan uku kafin ya isa dan haka tafiyar zata zama ba direct ba amma basu damu ba kawai sedai su mummynta sukaji zatai tafiya tareda mijinta.
Da mamaki zuhrah tayi farin ciki sosai ganin Leylah din na farin ciki kaman ta hakura ta karbi auren dan haka da murnarta itama ta bata turarika masu karfi a zuciyar namiji ta qara da yar nasiharta ta rakata har gurin abbinta tayi masa bakwana ta koma bangaren Mamee itama tai mata bankwana harma ta dan zauna acan zuwa dare Asim din daya shigo suka koma tare haile nata jin dadin cigaban datake gani a tattare da rayuwan danta.
Washe gari tinda safe motoci suka kaisu airport karfe 9 jirginsu ya daga daga boyem suma.
Bayan tafiyarsu da kwana biyu shima shuraim ganin ba wani aiki tinda sultan me qasar baya nan saiya hada tasa tafiyar dan zuwa Gurin Ammi da Bahar da ko numbern wayarta bayada sedai suna gaisawa sosai da wayar Ammin idan ya kira amma kwana biyun shiru ko wayar Ammin baya samu idanma ya samu baa dauka kwata kwata.
Shima babu dogon jira sosai tafiyarsa ta kammala ya daga zuwa uk din.
******* Sultan Yasar ne ya fara sauka a Uk din wanda kai tsaye yanada masaukin kansa da duk yaxo qasar anan yake sauka,
Lafiyayyar royal suite ce da babu me sauke se me babban matsayin da harya mallaki pass na gurin dan hakanne tsaro da duniyar gurin daban take,
Guri ne da tamkar baa duniyar mutane ba sbd ko sautin komai baa yadda ayi ba a gurin sbd duk wanda yake gurin babbane wanda daula ta ratsa baya buqatan hayaniya,
Pass din gurin matiqar ka mallakesa to kayi nisa a daular duniya dan haka koda suka sauka daga royal din aka tafi Airport aka daukosa tareda securities nasa dama wainda aka tanadar masa anan.
Ana daukosa suka dawo kadir ne kadai yakeda daman daya shiga palon farko na hutawan dakin amma sam bayada ikon shiga na biyun bare isa ga bedroom dinsa dan haka yana ajiye komai da zai ajiyewa sultan din yasaka aka kawo masa abinci kala kala dayasan yana buqata aka jere suka fice masu jerawan shima ficewa yayi tareda rufe dakin gabaki daya ya hau lift ya sauka zuwa nasa dakin dayake bangare daban dana asalin manyan.
Wanka da sallah tareda samarwa kai isashen hutu sultan yayi har dare bai nemi kowa ba bai kunna wayarsa ba saida safe ya kunna yana zaune a natse ta kira tenya wadda tai sharing location na inda suke sbd an sallamosu a daren jiyan sun dawo gida.
Da mamaki tenya ta sanar da sakinah sultan yana qasar cikin yar fargaban kada NUAB yasan da hakan gashi daman sunata faman yi masa boyan rashin lafiyar da Ammin tasa tayi.
Sakinah ma jin tayi ta dan shiga fargaba amma tin da dai sultan din yanada ikon zuwa gurin Ayanah ba yanda zasuyi bayan kawai su hana NUAB sani.
Yamma lis motocin sultan yasar suka iso bakin entrance na street din gidansu da akwai yar security sosai a street din dan haka a natse motar dayake ciki ta isa har kofar gidan ta tsaya a kofa ta security system nasu suka bude masa gate daga ciki take qaramar gate din mara tsaya ko kadan ta bude kadir ya sako kai ciki yayi parking.
Su tenya da suka san da zuwan nasa harma itace ta bude masa gate din ta ciki fitowa sukai cikeda girmawa me yawa suka tarbesa suna kasa kallansa sosai sbd kwarjinsa da wata irin kyan fuskarsa.
Bahar da batasan da shi ba tana bedroom dinta tana video call da Neesah akan skancare routine class da suka shiga kwana biyu bata samu zuwa ba sbd jikin Amminta school kadai take iya zuwa ta dawo ta dena zuwa koina sabanin yawon da koyaushe suke kan yi na shopping,saloons,spas da classes barkatai da kowanne shiga sukeyi.
Yana shigowa Maa sakinah ce taje har dakinta ta sakata tazo cikeda girmamawa da faduwan gaba da tsoro ta gaidasa kanta a qasa tana kasa kallansa sbd jin tayi itama kwarjininsa yayi mata yawan da bazata iya qwaqaran motsiba irin na 'dansa.
Kallanta yayi da idanuwansa na dattijantakar hutu da nutsuwa ya amsa yana tambayarta karatunta ta amsa har lokacin bata iya dagowa ba.
Ammi ce wadda tenya ta isarwa da sakon zuwansa ta fito a sanyaye cikeda mamaki da jin jikinta yana mutuwa da tsananta sanyi da ganinsa musamman yanda ya kafeta da ido take kowa ya matse aka bara palon gabaki daya kofar kitchen suka nufa suna barin cikin gidan zuwa baya inda swimming pool na gidan yake suka zauna a kujerun hutawa,
Tenya komawa tayi takai kayan marmari da duk abinda tasan sultan zai iya ci ko sha ta jere a rable ta baro ta dawo cikinsu Maa sakinah din ta zauna suna fira hankali a rabe da tinanin NUAB duk ranar da allah yasa tsautsayi yasan sultan ya ziyarce su.
Bahar wayarta ta isa bakin pool ta zauna taci gaba dayi tana saka kafafunta cikin ruwa daman short wando ne a jikinta da sleeveless shirt sai babbar rigar data doro a kai ta fito dan haka cire rigar tayi suna zuwa bayan ta ajiye tana qarasa abinda takeyi hankali kwance fatarta na wani daukan idanuwan Maa sakinah dake kallanta sbd hutu da lafiya da tsadaddiyar rayuwar datake yi tamkar yar datafi kowace 'ya gata a duniya duk da a gurin su sukam hakan ne babu yar datakai musu tasu dan haka ne ma tayi sauyawan da babu wanda zai kalleta bata shiga ransa ta kwanta ba.
Sultan bai wani jima ba kadir ya kira tenya a waya suna bayan ya fada mata sun tafi harda Wishmah zata ga likita na kwana biyu kafin ta dawo.
Shock tenya ta shiga gabanta na faduwa ta rasa abin fada dan batama dashi kawai to tace sbd bata isa cewa komaiba akan kowane hukuncin sultan yasar me boyem da sultan din boyem.
Sakinah data ji abinda tenya ta fada dagowa tayi zata kalleta kiran NUAB ya shigo wayarta dake hannunta wani irin mamaki sabo ta shiga sbd yanda kiran ya shigo Ammi na ficewa da Wanda aka dawo da ita nan sbd shi gashi basuda ikon fada. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee
118 Tenya ma data ajiye tata wayar tana rasa abin cewa kallan wayar sakinah din tayi tana NUAB ne take kafin ta sakinar ta yanke ta kashe tata wayar gabaki daya sbd yana gama kiranta bata daga ba tata zai kira ita kuwa tasan baifi Ammin tasa yake nema ba sbd kwana biyun bai samu jinta ba a jiya kuma koda aka sallamosu sunyita kira basu samesa ba harma yau da safe sunyita kira harda ita Ammin amma basu samesa ba duka.
Duk yanda maa sakinah taso ta daure ta daga wayar kasawa tayi sbd tsoron kadama yace kai tsaye a basa Ammin dan haka ta ajiye wayar a hankali gabanta tana kallo harta yanke,
Ajiyan zuciya suka sauke a tare bayan wayar ta tsinke dan haka suka miqe suka tattaro suka koma ciki banda bahar da batada ma niyar komawa ciki lokacin tayi nisa sosai a wayar datake ta zubawa har lokacin.
Sultan yasar bayan motarsu tabar gidan da anguwan gabaki daya hanya suka dauka ya juyo a natse ya kalleta da idanuwansa da itama ta dan dago tana kallansa ta sauke nata idanuwan sbd bazata iya jure kallansa ba musamman yanda yake ya kasa daukesu akanta cikeda wata irin kewa da shauqi.
Hannunsa ya daga yakai zai kama nata a cikin nasa din ya dakata sbd tinawa da ayanzu babu halasci ya tabata sbd an yantata ta tashi daga kowane matsayin datake dashi na zama halak dinsa a baya,
Ajiyan zuciya ya sake a hankali a natse kafin ya dan lumshe ido ya sake sauke su akanta yana tabbatarda kowane bangare na jiki da zuciya tareda jininta sunji kallan tareda isar da sakon da kallan yake tattare dashi,
Cikin sautin muryan daya saka tsigar jikinta tashi ta dago ta kallesa da nata idanuwan dake kashe masa kamewansa ba tsammani taji kalmar da har abada bata taba saka ran jinta ba sbd ta gama cire aure a rayuwarta har abada tin daga ranar data zama cikakkiyar imebēti.
Kada dauke idanuwanta akansa tayi hakama kasa cewa komai tayi saida ya sake maimaita mata kalman da shikuma itace burinsa akanta da bai taba cire rai ba tindaga ranar data zama cikakkiyar imebētinsa da data kama zuciya ruhi da rayuwarsa.
Wasu hawayen da bata san dasu bane suka ciko idanuwanta suka gangaro ta bude baki da wani irin sauti tace
'Dana bazai bazai baka aure na ba'
Numfashi me sanyi ya sauke sbd jin 'dan nata ne matsalar bawai ita din ba dan haka shima yace
'Danki nine Ubansa nine nakeda iko dashi bawai shine yakeda iko damu ba, Zan aure ki zan kuma miqa sadakin aurenki ga hannun danki daga baya da kaina ba aike ba ba sako ba amma ayau zan tabbatarda cikar burina na dora igiyoyin aurena akanki ayanah ghaz.'
Dauke idanuwanta daga kan nasa tayi sbd bata iya daukan kallansa ta dake bude baki ta ambaci sunan NUAB wanda sultan ya miqa hannu zai sake kama hannunta ya sake dakatawa yana girgiza mata kai tareda jifarta da kalaman da suka sanyata sauke ajiyan zuciya tana jin yanayi na sanyin jiki yana ratsata.
Kai tsaye gidan wani tsohon Amininsa wanda yake babban Masanin Addini Asalin balaraben Morocco dayake qasar tin lokacin samartaka gashi har an manyanta ya tara iyali sosai shima yama yi retire shima a yanxu harkar addini kawai yakeyi.
Tin kafin su isa sakon sultan ya isarwa Saeed din dan haka suna isa tarba ta musamman akai musu a babban gidan sbd matsayin da sultan yake dashi da yanda kuma sukai shekaru basu hadu ba sai yanzu.
Ita kanta Ayanah tarba me kyau ta samu daga matarsa babbar mace kamarta me kyau da kyan jiki,
Sosai suka dan jima a gidan har lokacin sallah yayi sukai sallah suna gamawa a masallacin cikin gidan Saeed din aka daura auren Yasar Almazz boyem da Ayanah ghaz akan sadakin zallan danyan zinarin da aka ajiye a gabanta bayan daurin auren ta zubawa zinarin sadakinta idanuwanta da sukai jajir tana hana hawayenta gangarowa sbd ayau wani irin abu take ji a kirjinta yana sauka yana barin duka kirjinta sbd daga qarshe dai rayuwarta ita baiwa Ayanah ghaz ta gama tabbatuwar ta fita ta tashi daga baiwa ta zama cikakkiyar mata wadda aure ya hau kanta kaman kowace mace,
Ayau aure irin wanda iyayenta da abaas dinta suke fatar tayi su gani ya hau kanta bayan ta cire rahamar hakan daga kanta gabaki daya,
Auren Mahaifin 'danta ubansa ne yau kanta wanda zata mutu a cikin inuwan aure kenan itama kaman yanda tayi fara a baya.
Ajiyan zuciya da numfashi ta sauke a lokaci daya tana hana hawayenta sauka har lolacin sbd a inda suke dan haka sauke kanta kawai qasa tayi zuciyarta na miqa jinjina ga ubangijin dayake sauya kaddara da rayuwar kowane dan adam.
Shi kansa sultan a zuciyarsa Allah yayiwa godiyan samun cikar burinsa na karshe wanda a yanzu baida sauran buri ko daya bayan na fatar cikawa da imani lafiya.
Sai bayan sallar laasar da sukai sallarsu anan tareda Saeed da tukuna akace Ammin ta fito suka wuce.
Kai tsaye masaukinsa suka nufa wanda tinda suka biyo hanyar kafin su isa Kadir ya kira aka tanadar musu qwararrren likitan da zai duba Ayanah din.
Suna isa ko kofar dakin Kadir bai isa ba daga qasa bakin lifter ya tsaya suka wuce sama ya tafi dan jiran isowan likita ya isar dashi dakin.
Baa wani jima sosai ba likitan ya iso kadir ya iso dashi har bakin Dakin wanda yake tamkar flat sbd palo biyu ne a jere da saika wucesu zaka isa asalin bedroom din hutawa.
A palon farko Likitan ya tsaya tareda zama a natse kadir na tsaye daga bayansa ta fito tareda sultan din suka zauna tareda gaisawa da Likitan kafin ya fara mata yan tambayoyin dubata yana kokarin fahimtar abubuwan da akai mata a asibiti ya tabbatarda komai da akai shine daidai ya qara mata wasu maganin kawai tareda cewa ta dan rage barin sanyi na shigarta ta kansace koyaushe warm.
Bayan tafiyan doctor da kadir ciki suka koma sai dare aka kawo musu abinci aka jere a dining wanda saima da sukai ishai sukaci abinci.
Duk yanda takeson kunna wayarta ta kira gida da kuma NUAB shakka da nauyin NUAB na laifin datai masa din hanata yakeyi gashi ta kasa samun nutsuwa kuma idan ba jinsa tayi ba,
Ganin duk yanda ta damu ya saka sultan kama hannunta ya nufi quryan bedroom dinsu da ita har bakin gado ya zaunar a natse kafin ya dauki wayarta dake ajiye a kashe data fitar ta ajiye tanata shakkar kira ya bude tafin hannunta ya saka mata wayar ya mata kallan kulawa da bada qwarin gwiwa tareda kunna mata wayar ya saka mata kiran HAYATEEM din kai tsaye tareda bar mata gurin sbd ta sake da dan nata tayi magana.
Bathroom ya fada tareda sakarwa kansa ruwan dumi dan wankan shirin bacci.