Kenza eBookz

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 46

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 46

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 46: Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 46. Ringing wayar NUAB din tayi harta yanke wanda…

4,448 words

Ringing wayar NUAB din tayi harta yanke wanda tana yankewa kiransa na shigowa ta sauke ajiyan zuciya guda biyu a jere kafin ta dauka a natse tayi sallama.

Amsa sallamar yayi a cikin nutsuwa da sautinsa me ratsa kowace kunnuwa jiki ya mace,

Shiru yayi batareda yace komaiba sbd sautin muryanta dayayi sanyi sosai ya sauya zuwa yanayi na damuwa da rashin karfi,

Itama shirun tayi tana kasa cewa komai wanda ya saka tinaninsa sake tsayuwa akan yanayinta kafin ya bude baki ya gaidata yana tambayarta lafiyanta sbd baijita daidai ba hakama yakira maa sakinah bata daukaba maa tenya kuma wayarta a kashe.

Tattaro karfin hali da qwarin gwiwa tayi tana sauya yanayin muryanta zuwa na sakewa da hanasa fahimtar halinda take ciki ta amsa tana tambayarsa tasa lafiyar tareda Aleey.

Magana takeyi tana kokarin kawar da tinaninsa akan yanayinta wanda shikuma a nasa bangaren kowane sautinta yana sake bada ita ne dan kuwa qarara ya tabbatarda akwai damuwa da rashin kuzari a muryanta.

Sallama sukai batareda ta amsa tambayarsa ko daya ba akan su sakinah sbd ma kada suyi baki daban daban idan ya kirasu sbd ko yayane tasan zai iya gane batada lafiya a muryan tata.

Suna sallama kai tsaye maa sakinah ya dake kira wanda ta dauka wannan karan tana zaune a palo Bahar na kwace jikinta tana karatu a laptop.

Gaisawa sukai ya jeho mata tambayar data sakata neman rikicewa ta tattara nutsuwanta tace

'Tana daki tayi bacci tin dazu'

'Ok daman inata kiran wayarta haryanzu a kashe, Ko akwai abinda yake faruwa daya kamata na sani Maa??

Da karfin hali cikakke da fuskewa maa tace

'Aa ba komai wayarta ma da baka samu a kashe take gatanan ma a hannuna sbd ta huta sosai'

Ajiyan zuciya ya sauke sbd daga karshe dai ya tabbatarda akwai abinda yake faruwa din sbd ya gama waya da Ammin ita kuma maa sakinah tace ga wayar a hannunta.

Kashe wayar yayi ya kira ta maa tenya wadda ta yafe wayarta ta kashe kenan har sai Ayanah ta dawo dan bazata taba iya waya da NUAB ba ayanah batanan a samu matsala. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee

119 Aleey dayake tareda NUAB a lokacin kuma yanajin duk abinda ya faru kafin LEUL din yace komai juyawa yayi daga gurin ya fice yana fidda wayarsa ya nemo numbern dazai kira ya saka kiran.

Kiran mintina uku yayi wa Ari drivern bahar yace yana son tabbatarda me yake faruwa a gidan zuwa da safe, Yanason ya samu tabbacin kowa na gidan yana cikin cikakkiyar lafiya da hayyacinsa.

Yana kashe wayar dawowa yayi ya wuce office dinsa dake cikin ghaz villa dan fara hada tafiyarsu da zata iya yiyuwa zai hada komai ya zama ready ta yanda tafiyar idan ta kama yi kawai zaayi idan kuma ba buqata idan sun tashi boyem kawai zasu wuce sbd baya bata lokaci ko delay ga duk abinda zai iya tasowa LEUL dinsa.

NUAB din kuwa shiru yayi kawai a zaune tareda rufe idanuwansa masu kyau da kwarjini yana jin abinda yake kirjinsa na budewa sbd tinda yake bai taba jin nutsuwa ko samunta ba a duk lokacin da baya qasa daya da mahaifiyarsa, Tsawon wannan lokacin da yayi batareda ganinta ba a zahiri yafi masa radadi da ciwo akan na baya daya rayu batareda ita ba, Yanzu kariya yake son bata da dukkanin rayuwarsa amma wata kaddarar ta sake rabasu amma a hakan ma yafi dan samun sassauci sbd ya cireta daga rayuwar wanda sbd shine yake bata kariya, Tabar gurin wanda akansa yake jin tsanar zamanta a boyem, Ya rabata da wanda zuciyarsa bata kaunar alaqar dake tsakaninsu ko daya wato alaqar da ba igiyoyin aure ne a tsakaninsu wanda hakan shine baqin cikinsa da quncinsa tin tasowansa ta yanda Sultan ya kasa 'yanta mahaifiyarsa koda bazai aureta ba ya yantata ya barta ta zabi rayuwar datake so, Shi bai taba baqin ciki ko damuwa da zamtowansa 'dan imebēti ba sbd abu daya yake so yake kuma alfahari dashi shine Ayanaah ghaz ce ta haifesa,kota wace hanyar ta haifesa alfaharinsa daya itace mahaifiyar tasa amma sultan bai duba burinta ba,me takeso bayan zamtowanta imebētinsa,wace rayuwar take shaawa,a imebēti zata mutu duk bai duba wannan ba yabarta ta rayu tamkar mara amfani a cikin masarautarsa da babu ubanda yakeda iko da damar zuba rayuwar dayake so akan ikon masaurautar da masu sarautar da mutanen masarautar da mutanen qasar da qasar gabaki.

Bude idanuwansa da suka sauya yayi sbd a duk lokacin wannan radadin ciwon daya rayu dashi ya taso masa jininsa tafasa yakeyi.

*****Sultan yasar daya gama shirinsa na kwanciya a cikin navy blue kayan baccin masu kauri na Alpias da suka fidda haskensa tareda haibarsa sosai sbd duhunsu a jikinsa zaune yake a natse yana shan ruwan black shai me qarfi da qara lafiyar idanuwa data qwaqwalwa yana duba sako a wayarsa hankali kwance kira ne ya shigo wayar tasa wanda ya sakasa dan dago idanuwansa ya kalli inda ayanah take zaune ta gama shirin baccin itama tana sake goge fuskarta da wipes me dan maiqon oil kadan.

Daukan wayar yayi a natse yafara sauraron gaisuwan Maraki wadda itace tayi kiran kafin ya bude baki ya amsa yana tambayarta lafiyar gida da boyem.

Amsawa tayi itama daga can bangaren tana masa barka da sauka lafiya tareda bangajiya,

Duka hadawa yayi ya amsa yana bayyanar da yar kulawansa akanta sbd ita ce kadai macen dake kiransa ako da yaushe yayi tafiya kokuma idan wani abin ya faru,

Cikin yar kokarin nuna kulawa da son jin ina yake ta tambayesa yana wace qasar ne hala.

Kai tsaye ba boyo sbd baya jin akwai mace ko namijin da a duniya zai iya yiwa kame kame ko boyo dan haka ya fada mata yana Uk kuma dubiya yaxo da hutawa.

Shiru tayi batareda ta tambaya wa yaje dubawa ba sbd zuciyarta bazata iya daukan abinda kunnuwanta zasu jiye mata ba sai kawai ta janyo wani zancen tana masa yana amsawa suna magana yar daidai ta mata da miji har tsawon lokaci kafin ya gama ya ajiye wayar gefensa yana ajiye cup din hannunsa daya gama shanyewa yana wayar.

Juyowa yayi jin tsit a dakin yaga Ayanah bata gabab mirror ta koma bakin gado ta gama komai harma tayi kwanciyarta batareda jin zafin komaiba dan batama gane kan wayar dayake yiba sam.

Tasowa yayi ya nufi inda take daidai lokacinda take kokarin saka hannu ta rage hasken dakin ya kama hannun data miqa din a hankali tareda zubawa hannunta ido yana kafe lambarta dake bayyane da kallo.

Dumin dayake tafin hannunsa daya gasa a sane da cup din hot shai dayasha wanda ya sauka a fatar hannun nata ya sakata sauke ajiyan zuciya me sanyi sbd taji dumin har cikin qashinta ta kasa dagowa ta kallesa amma jin shiru bai motsaba ba baice komaiba ya sakata dago ido a hankali ta kallesa.

Inda idanuwansa ke kalla a hannunta ya sakata dauke idanuwanta akansa tana kokarin kalla ya tare fuskarta da dayan tafin hannunsa yana hanata kallan abinda zai tinatar da ita rayuwar datai a baya yana dawo da idanuwansa akan fuskar tata suna kallan juna.

Sake motsawa tayi zata kalli hannun ya sake riqe fuskarta wannan karan tareda girgiza mata kai yana zaunawa a gefenta tareda qanqame hannunsa da nata din yana cigaba da kallan cikin idanuwanta data kasa ta dauke nata tana kokarin janye hannunta daga nasa dan kwanta.

Sanin dole hannun nata zata kalla ya sakasa miqa hannu daya ya rage hasken wutar dakin yana jan hannun nata ya zagaye bayansa dashi wanda hakan ya dagota sosai ta hade da kirjinsa sosai numfashinsa ya sauka akan fuskarta daya seta da tasa yana shaqar nata numfashin tareda duk qamshin dayake fita daga jikinta.

Ba tareda barin tinanin bayanta ta dawo mata ba sultan ya tabbatarda ta samu baccin nutsuwan data samu damar sanin wasu abubuwa da dama dake zuciyarsa a boye a danne wainda babu wanda ya taba saninsu akanta da 'danta dan haka da safe da mamaki da tinani kala daban daban ta tashi akan alaqar dake gudana a tsakaninsa da NUAB matiqar dai abinda ta fahimta na zuciyarsa hakan yake akan girman kaunar dayakewa NUAB.

Da safen haka suka wuni suka sake kwana sukai kwana biyu batareda kowace dan adam ya gansu ba sbd ko masu kawo abinci su jere basu taba ganinsu ba kadir ne yake zuwa ya bude musu dakin da card din hannunsa bayan ya kira sultan ya sanar dashi zaa kawo abincin ya basa izinin a kawo din kuma suna jerewa kadir na tsaye zai saka a jere komai da zasu buqata a yanda yake su fice ya kira ya sanar da sun fice.

A cikin kwana biyun Ayanah ta kasa iya sakewa tayi waya da NUAB yanda ya kamata nauyinsa take ji sosai hakama shakkar abinda zai iya biyo bayan auren idan yaji a tsakaninsa da mahaifinsa ya saka take jin shakka da jin kaman tana danasanin barin sultan ya daura auren duk da kaman kai tsaye shima yayi mata

Da bahar take sakewa tayi waya sosai tana jin yanda take narke mata akan ta dawo a wayar tana kewanta,

Su maa sakinah ma jin hankalinta kwance da kuma jin maganar auren ya saka suka shiga farin ciki me tsananin gaske harma da celebratin abinsu batareda kowa yaji ba dan kuwa abu ne da sai daga baya jikinsu yayi sanyi sbd babu wanda zai iya ma kwatanta yanda zasu fuskanci NUAB wanda jin auren shine kusan mummunan labari na karshe dazai ji a rayuwarsa gashi sunata boye boyen kada ya gane ma Ammi bata ganin bare ma subari koda wasa yaji labarin sultan yana qasar.

Bahar da babu ruwanta batama san wai shakkar ya sani ko kada ya sani ba akeyi ita dai farin cikinta daya ma Ammin ta dawo tayi murnan da bata taba yiba jin Ammin tayi auren da shine burin mahaifinta da baya raye dama su din.

Zuhrah ma da kanta ayanah ta kirata ta sanar mata wanda zancen ya saka zuhrah zubewa qasa tayiwa Allah sujjada tana gode masa tareda fashewa da kuka tana jin inama sauran yan uwansu da iyayensu suna raye su shedar da wannan auren na ayanah da suke jira da fata tin suna qanana Allah bai cika sa ba sai yanzu da manyanci ya kamata.

Ita kanta Ayanah sai a lokacin da zuhrah ta fara kuka nata kukan ya taho tana kasa riqesa sukai abinsu sosai kafin sukai sallama.

Bayan gama waya da Ayanah sakinah ta kira itama suka taru sukai kukan farin cikin da sakinah ma sai lokacin takeyinsa suna jin dadin da rayuwar Ayanah din ta kammalu cif cif yanzu.

A can boyem Zuhrah sam bata fadawa kowa auren ba har 'yayanta kuwa musamman leylah wadda suka wuce a ranar tareda Asim wanda tasan dole zaiji idan har ta fadawa leylah tinda duk inda suke a yanzu din suna tare kuma yana ji tamkar mahaifiyarsa taji ne dan haka tai shiru bata fadawa kowa ba tayita farin cikinta ita daya tareda hada gagarumar walimar data sanar cewa ta cikar burinta ne na auren yarta data wuce.

Bahar da itama hakanan take jin rayuwar tayi mata dadi farin ciki kawai takeyi tako ina dan kuwa duk yanda take tsammanin tana tsananin kauna da kishin Amminta abin ya wuce nan sai yanzu da Amminta ta zama matar aure halastacciya jin takeyi ta matsu Ammin ta dawo ta rungumeta taji ta cika zuciyarta da nutsuwa dan kuwa duk farin cikin da mahaifinta zaiji idan yana raye akai auren to shine take ji masa batareda ma tasan hakan ba. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee

120 Aleey daya gama samun dukkanin bayanin dayake jira akan binciken dayasa akai masa dan tabbatarda lafiyar kowa dake uk din Ari ya dawo masa da bayanin kowa gidan lafiya kalau da alama ma suna cikin farin ciki a kwanakin sbd kullum sai Ms Bahar ta fita dasu yawon shaqatawa basa dawowa gidan ma wani lokacin sai dare duk da ba wani son yawon sukeyi ba sabanin bahar da kullum sai dare wani lokacin take dawowa gida amma akwai lokutan ma datake kwana hostel gurin qawarta.

Shiru Aleey yayi xaune a cikin office dinsa dake cikin villa dinsu yana juya zancen bayan ya gama saurara yaji babu inda sunan Ammi ya fito dan haka ya tambaya Ari din a daban cewan ina Ammi?

Amsa ari ya basa wanda ta sakasa cewa ok ya kashe wayar ya ajiye yana tsayar da tinaninsa da nazarinsa cak akan farin ciki da sabuwar walwalan me suke yiwa celebration din daya saka suke biyewa Bahar datake yarinya yawon shaqatawa kullum bayan sam dukansu ko fita idan ba dole ba basayi,

Dauke tinaninsa yayi daga kan hakan ya dawo dashi akan duka wannan ina Ammi take sukeyinsa? Meyasa Ari yace tsawon kwanaki kenan bai saka Ammi a idanuwansa ba bayan an sallamota kenan daga asibitin data kwana basu ma sani ba sai yanzu Ari yake fada,

Idan Ammi batada lafiya bazasu taba farin ciki ba harda samun walwalan ringa fita dan haka dole Ammi na cikin koshin lafiya, To idan tana cikin koshin lafiya bazai taba yiyuwa ayi kwanakin da sukai sati ace baa gangaba cikin gidan,

A taqaice idan tinaninsa da lissafinsa yana tafiya daidai yanada tabbacin Ammin bata gidan....

Tsayawa bugun zuciyarsa yayi cak daya gama wannan tinanin sbd idan Ammi bata gida duk duniya ina zata tafi a qasar??babu.

Idan kuma qasar ta fito yanada tabbacin bata boyem sedai idan Anjom wanda shima yasan har abada Ammi bazata iya tafiyar barin qasa ko wani gurin da zatai ko kwana daya ne batareda ta sanar da 'danta ba dan haka Ammi bata bar qasar ba tana cikinta kuma ko a ina take tinda bata fada wa NUAB ya saniba to ba gurin dayakeson taje bane,

Fara hada wayoyi da rashin daukan wayarta daya yakaita a kwanakin da yanda su Maa sakinah suke baki daban daban da ita wanda dalilin hakanne ma NUAB ya sakasa bincika ko lafiya suke sbd suna boye wani abu tabbas Qarasa hada duka komai yayi take kansa ya sara sbd kaf duniya abu daya ne ayanzu NUAB yayiwa tsanar gaske shine haduwan Amminsa da Sultan yasar kuma dukansu Maa da Ammin sun san da hakan.....

Sarawa kansa ya sake ya dauki wayarsa yana miqewa tsaye ya saka kiran keelah dake boyem yana fatar kada yaji abinda zai tambaya sbd matsala ce babba xata iya biyowa musamman ayanzu da NUAB din kaman zafinsa ya qaru duk da hutawan gaske sukeyi a Moscow sun gama abinda ya kawosu amma ba yanzu zasu komaba.

Wayar keelah na kowane ringin ne da sarawar kan Aleey wanda yake jin tinanika da dama na yawo cikin kansa wanda bama yajin a yanzu zai iya isar da sakon ga NUAB.

Keelah na daukan wayar kafin ya fara cewa komai aleey ya jeho masa tambayar

'Sultan me murabus yana cikin masarautar boyem da qasar boyem ma gabaki dayanta???

Keelah koda yake 'dan kadir kuma tamkar idon sultan akan kowane motsin 'dansa hakan bai taba hanasa zamowa loyal dan gani kashenin NUAB ba dan kuwa shine uban gidansa daya wuce kowane matsayi a gunsa dan haka babu kowace irin sakayawa ko daya yace

'Baya masarautar bayama qasar gabaki daya amma babu tabbacin inda ya tafi nima sai ayau din da safe nake samun labarin tafiyar sbd bai bari kowa yasan da tafiyar ba tinda ya rufe rayuwarsa ta fita daga idon kowa da sanin kowa.'

Shiru Aleey yayi tareda rintse idanuwansa kafin ya bude yana kashe wayar, Sultan yasar yana uk,ya tabbatarda shine a qasar wanda ya saka Ammi bacewa daga ganin Ari da sauran masu aikin gidan.

Komawa yayi ya zauna a kujera yana ajiye wayarsa gabansa tareda dafe kansa dayayi nauyi sbd baisan ta ina zai fuskanci hakan ba dan bayajin zai taba barin NUAB ya sani kawai zai rufe zancen batareda barin ya sani ba kawai fatarsa Sultan ya koma kafin komawansu wanda zai tabbatarda hakan dan kuwa bazai bari Sukoma Boyem ba a yanzu har sai ranar da sultan ya koma ta yanda suna komawa NUAB bazaisan sultan har yayi tafiya ya dawoba.

Da daddare dole zai isa gurin NUAB isar masa da duka bayanin abinda a samu a binciken dan haka koda ya isa gabansa bayan sunyi dinner a table tare ya dauko masa wasu bayanan ayyukan yafara yi masa kafin cikin nutsuwa ya sanar dashi cewan babu abinda yake faruwa acan uk kowa lafiya kalau yake kawai Ammi ce tayi yar jinyar kwana biyu shiyasa sukaita masa baki daban daban kila dan basason ya sani ya damu amma ayanzu ta warke sarai tana ma gida an sallamota.

Yana gama bayanin bai jira abinda NUAB din zai fada akan hakan ba ya fada wani bayanin sbd bayason zancen su Ammin yayi tsayi,

Kokarin nuna masa bayanan dake kan laptop din gabansa yayi yana kutsawa sosai a bayanin da nunawa.....

'Zancen Ari bai gamsar dani ba,da kaina zan tabbatarda idan Ammin ta warke shikenan kaman yanda ya fada maka...'

Itace kalmar data katse Aleey dayake kokarin nisa a bayaninsa dan rufe na Ammin dan haka ba zata kaman daga sama yaji maganar NUAB din wadda ta sakasa dakatawa yaba sauke numfashi me dumi ya aje abinda yakeyi ya dago ya kalli NUAB din wanda shi yake kallo da mayun idanuwansa sbd aleey ya basa kansa daga lokacinda yafara masa bayanin su Ammin yana dauke idanuwansa daga kansa sbd bai taba masa boyo ba ko karya a kowane zancen komai zafin lamari fada masa yakeyi su fuskancesa amma ayau karan farko ya gabatar masa da zancen daya tabbatarda ba shi bane dan haka baya buqatan gyaran zancen zaije da kansa ya fuskanci koma menene.

Aleey da daman a cikin ciwon kai me tsanani yayi bayanin sbd rashin sabon haka a tsakaninsu numfashi me zafi ya sauke a natse kafin ya kalli NUAB din yace

'zan tabbatarda tafiyar a lokaci qanqani'

Ficewa Aleey yayi yana fidda wayarsa dan fara shirin hada tafiyan dan baida zabi a yanzu kam bayan na jiran abinda zasu tadda da wanda zai biyo baya.

****Su Asim sun saka a uk din dan haka kai tsaye Leylah kasa barinsa tayi saida suka fara zuwa gidan su Ammin wadda basu samuba a waya dan haka dole maa sakinah ta kira ita ta basu location suka iso har gidan sedai saida suka fara tsayawa lodge mai kyau da tsada sosai dayake kusa suka fara tsayawa harma sukai wanka ko abinci basu tsaya ci ba suka tafi.

Ko da suka isa bahar bata nan dan haka a cikin rashin sabo da jin alaqar wata iri Asim ya gaisa dasu maa din ya tafi yabar leylah a gidan kafin ya dawo da yamma wanda yasan zuwa lokacin Bahar ta dawo, Rashin ganin Ammi da baiyiba baima tsaya tambaya ba sbd bayajin zai iya hakan a yanzu sedai zuwa kwana biyu idan ya shiga jikinsu akan bahar.

Duk wanda yake gidan yayi mamakin zuwan nasu ba sanarwa gashi ko zuhrah bata sanar masu ba sbd batai tinanin nan sukayo ba kai tsaye itama ta dauka honeymoon dinsu zasu tafi suyi.

Duk da baa san da zuwansu ba farin ciki sosai sukai da zuwansu musamman maa sakinah data ringa tarairayan Leylah din tana fatar Allah yasa cikine da ita yanda taga kaman ta sake yar ramewa.

Bugawa Ayanah sukai suka sanar da ita zuwan leylah din itama tayi murna sosai sedai basa ma nan suna Liverpool sunje zata ga wani likitan herbs akan tin sanyin da likita yace ta dan qauracewa shine Sultan ya baqaci taga wannan likitan batama so tafiyar ba amma dole ta tafi.

Har 8 Bahar bata dawoba hakama tsawon wunin Asim akai akai yake kiran leylah jin ko Bahar din tadawo tana sanar masa bata dawoba harma takaicinsa ya fara kamata baida zance bayan na bahar wadda kunnuwanta suka gaji daji harma take jin a yanxu tana buqatan zaunawa ta qarewa bahar kallo taga menene take dashi da ita batada dan haka ta dena daukan wayarsa haka yayita kira tana qin dauka baqin ciki da takaicinta ya rufesa sbd idan itace take maida kiran sunan NUAB wanda yake jin ai bai rasa koma me NUAB yake dashi ko jin haushi ba ko hanawa tsoki yayi ya jefar da wayarsa ya kwanta dan hutawa da kyau dan kamar marasa hankali haka suka kwasa zuwa gidan daga isowansu batareda sun tsayawa hutawaba dan haka gwarama ya huta yayi kyan gani anjima idan zai isa gidan.

Sai 6:30 ya isa gidan cikin shigar ash fendi wears yana fidda qamshi me tsada da sanyi yana isowa har palo aka sake masa iso ya zauna yana sake gaidasu maa suna dan kokarin sakewa dashi sbd Leylah dayake aure ayanzu ya zama nasu dole.

Fira sukeyi sama sama kowa na iya kokarinsa gurin yar sakewa da dan uwansa sabanin Leylah da hankalinta yake kan bahar da har lokacin bata dawoba.

Shi kansa Asim hankalinsa na kan dawowan Bahar din wanda duk leylah na lure dashi takaicinsa duk yabi ya sake ciketa sai tsoki mara sauti take saki yana sane da ankare da ita amma yaki ko kallanta jira yake su koma yaji dalilin rainin wayon abinda take masa.

Abinci aka gama shiryawa a dining suka dunguma dukansu suka zauna suna kokarin farawa Bahar ta dawo gidan ta hanyar jin shigowan mota ya saka sukasan itace dan haka kasa fara cin abincin sukai duka su biyu suja juyawa ga kofar.

Cikin nutsuwa aka buga kofar wadda ta saka Maa sakinah da Maa tenya suma dakatawa suka juya ga kallan kofar sbd sanin ba Bahar bace sbd ita bata buga kofar sedai kawai ta bude ta shigo,

Faduwa gaban Maa tenya da sakinah sukai a lokaci daya sbd sanin ba kuma ayanah bace sbd ko yanzu basu jima da gama waya da itaba tana Liverpool haryanzu to waye kuma dan suna cikin matsanancin yanayin da basa buqatan zuwan kowa idan ayanah bata dawoba.

Asim kuwa zuciyarsa tafi ta kowa bugawa sosai sbd idanuwansa har wani sauyawa sukai tamkar hawaye zasu ciko a cikinsu sbd tsananin shauqin son ganin bahar wadda ganinta kawai zai saka zuciyarsa sanyaya.

Leylah ma da faduwan gaba take tsananin son ganin bahar din dan haka dukansu kafe kofar sukai da ido babu ko kyatawa.

Sake buga kofar akai kafin kai tsaye aka budeta gabaki daya wanda iska ta kado musu qamshin daya saka dukansu miqewa daya bayan daya idanuwansu na kasa daukewa daga kofar,

Aleey dayake gaba shine ya fara sako kai yana qarasa budewa mai boyem din kofa yana sako kai a natse cikin wata sanyin iko da izza tareda kamewan datake qafar da yawun bakin dukansu.

A daidai wannan lokacin karfe 9:30 ta buga kuma a daidai lokacin motar bahar ta shigo gidan tana kallan motoci biyu dake harabar gidan zuciyarta ta fada mata Amminta ta dawo bata fada mata ba dan haka da sauri ta fito motar tana sanye da purple Milan palazzo mai tsananin fadi da vneck chiffon shirt da ake ganin vest din kayan daga ciki sai scarf na versage da hanbag dinta ta lv tayo cikin gidan da sauri ta fado palon tana qwala kiran Ammi kowa na tsaye cirko cirko zuciya na bugawa ba dadi. #MAMUH 09033181070

HAYATEEM Mamuhgee

121 Kowa kasa motsawa yayi daga inda yake bayan sun mimmiqe tsaye dukansu,

Kusan dukansu tsoro ne mai tsananin ya cika gangar jikinsu da zuciyoyinsu sbd shine mutum na karshe a duniya da zasuyi tsammannin gani a wannan ranar kuma a daidai wannan lokacin,

Shi kanshi Asim tsoro ne yaji ya shigesa mai tsanani na bayyanar NUAB din gidan sbd kai tsaye sunsan meya kawosa koda kuwa su Maa sakinah su basu taba kawo hakan ba sbd ganin wa yake aure.

Naimar gurin gabaki daya daukewa tayi tai wani irin tsit dumi da tiririn gaske yana tirnike yanayin kuma har lokacin ba wanda ya motsa ba wanda ya bude baki,

Idanuwansa da suka gama kallansu daya bayan ya tabbatarda ko waye da waye a gabansa ya dan rufe su ahankali sbd sauyawan da suka fara suna wata irin yajin da zai iya saka kafafuwansu kasa daukansu daidai wannan lokacin ne itama bahar din ta fado palon tana kwala kiran Ammin wanda har cikin kirjinsa sautin muryan ya keta yana yankarsa akan radadin dayake jin kansa na dauka da zafi,

A rikice cikin wata irin shock ta tsaya cak bayan ta iso tsakiyar palon ganin Aleey da shine yake facing kofa take komai nata ya fara dena aiki daidai yana slow ta kasa juyawa bangaren datakejin qamshinsa na bugowa ta tsayar da idanuwanta akan su maa dake cirko cirko.

Kan Asim ta saukar da idanuwanta shima tana kalla cikin tsananin mamakin ganinsa suna hada ido yayi saurin dauke nasa idanuwan duk kuwa yanda yake cikin tsananin son ganinta kaman zai rasa rayuwarsa amma yana ganin yanda idanuwan Aleey suke kafe akansa haka ya hakura ya danne maitarsa yana dauke ido sbd yana tsananin buqatar rayuwa da ganinsa maana da idanuwansa a yanzu,

Bahar daqyar ta iya daga kafafunta ta isa bayan Maa sakinah a hankali ta dan rabe wanda takunta ya sakasa bude idanuwansa da sukai jajir akanta ya qare mata kallo ita da sitirar sake jikinta kafin ya juya kansa ya kalli agogon dayake dakin da wani kallan dayake na tsantsar isa da bacin rai ya duba time karfe tara harma da rabi na dare sai a lokacin take dawowa gida,

Shine ya yanke shirun wanda ya wakana sbd iyayen nasa babu wanda ta iya samun abin fada sbd basu gama fitowa shock ba ya bude bakinsa da muryan datake bayyanarda tsantsar bacin ransa dayake iya kokarinsa gurin dannewa a lokacin a natse da kamewa yace

'Na same ku lafiya?

Maa sakinah ce tayi karfin halin amsawa tana kokarin takowa ta qaraso tsakiyar palon daga dining din zata jefa wata maganar ya sake furta

'Ammi fa??

Cak ta dakata tana fasa qarasowa gurin nasa ta kallesa tana kokarin nemo maganar da zata fada a bakinta.

Kafeta da ido yayi yana jiran amsarta wadda babu dan haka ya juyar da kallansa akan maa tenya yana jiran ko zata basa amsa itama shiru tayi tana kasa ma kallansa sbd nauyinda take ji duk da shine 'da gaskia ayau suna jin nauyi da kunya harma da shakkarsa sbd anyi masa laifi mai girma.

Jin shiru ya sake ratsa gurin ya dauke idanuwansa daga kan tenya din ya saukesu akan Bahar wadda har lokacin taqi dagowa ta kalli inda yake sbd yanda kirjinta yayi nauyi.

Bai sake iya dora idanuwansa masu daraja akan shigar datake jikinta ba sbd loosing control na tsantsar bacin rai dayaji yanayi wanda ya sakasa juyawa kai tsaye ya fice idanuwansa da jijiyiyin kansa da suka fito sunyi jajir fushi da bacin ransa me karfi daya jima baiyiba yana tasowa ya gauraye jininsa gabaki daya da idanuwansa.

Readers Also Read