Kenza eBookz

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 47

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 47

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 47: Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 47. Aleey daya san tsantsar bacin rai da baqin…

4,482 words

Aleey daya san tsantsar bacin rai da baqin ciki me tsanani baya saka NUAB magana indai akan manyansa ne sbd komai zai iya faruwa yana ganin NUAB yanayin NUAB din ya sauke kansa qasa sbd aya fushi da bacin ran LEUL yau ya bayyana dan haka yana juyawa baice komaiba shima ya bisa din suka bar gidan a motocinsu tareda securities dinsa.

Yana ficewa Asim ne ya fara sauke ajiyan zuciya mara sauti yana kallan leylah datai mutuwar tsaye gurin kallan NUAB din zuciyarta na bugawa da karfi sbd ya dade bata gansa ba a fili yayi sauyawan data qarasa kasheta gabaki daya akansa,.

Yayi wani irin fresh da duk hasken fatarsa saida taga kaman ya qara haske ya zama cikakken kamilallan namijin dayake juya qasa guda a hannnunsa tamkar manyanci ma ya shigesa hatta fushinsa daya bayyana a tattare dashi da tsananin bacin rai qara masa wani kyau da tsari yayi dan hakanne ma harya fice bata iya dauke idanuwanta akansa ba bare motsawa.

Takaici sake cike Asim yayi yanda ita gabaki daya duk shock da halinda suka shiga bata shigaba matacciyar soyayya ce a idonta dan haka hade fuska yayi tareda dauke kallansa akanta yana juyawa gurin maa sakinah zai kalli Bahar dinsa shima sai yaga wayam bahar din ta silale ta gudu daki sbd halinda ta shiga itama wanda hadda tsoro da shakka a cikinsa hakama ba qaramar bugawa kirjinta keyiba tana jin yawun bakinta suna kafewa har lokacin qamshinsa take ji a hancinta yana shigarta duk da bata iya yadda ta kallesa ba sbd bayyanarsa a rayuwarsu yau yazo a bazatan da takasa ma tinanin komai kawai dai dukansu gidan duniyar ta tsaya musu cak.

Baqin ciki ne ya sake tirnike zuciyar Asim ganin ba bahar din dan haka a fusace yana dan boye zafin kalamansa ya kalli leylah yace

'To mu tafi ko'

Juyowa tayi ta kallesa cikeda zafi itama sedai ganin su maa da hankalinsu baya kansu ya sakata itama dan tausasa nata kalamin tace

'Kaje anan zan kwana'

Kallan baki isa ba yayi mata sbd bazai yadda ba ta fisa morewa ba wato ita ta kwana anan taita ganin Abincin zuciyarta shi kuwa yana can abanza kenan ita ya rako ma dan haka sake daure fuska yayi yace ta wuce kawai su tafi sa dawo goben ai.

Zatai gaddama cikin bayyanarda rashin mutuncinta Maa sakinah ta bude baki a sanyaye tace tayi hakuri tabi mijinta din sa dawo daga baya.

Bude baki tayi zatai magana Maa din ta katseta tana tabbatar mata data tafi din dan haka ba yanda ta iya bayan shirya ta tattaro suka fice.

Komawa dukansu sukai suka zauna a hankali a natse tareda kallan juna a sanyaye dukansu suna jin rashin dadin batawa NUAB din rai sbd yanayinsa ya tabbatar musu da yakai maqurar bacin rai da fushin da bazai iya magana shiyasa ya juya kawai ya tafiyarsa.

Tenya ce ta bude baki tana cewa

'Gashi ba samun Ayanah akeyiba idan ba itace ta kira da kanta ba bare a fada mata isowan NUAB din sbd dai a yanzu ni bansan me zan fada masa gobe ba idan ya sake tambayar'

Numfashi maa sakinah ta sauke a natse kafin ta bude baki tace

'Allah yasa dai ficewan da yayi komawansa kenan Moscow bazai dawo ba sbd shine mafi alkhairi a lamarin yanxu dan gaskia nima bazan iya qara masa bacin ran fada masa ba.'

Miqewa tenya tayi tana zuwa daki ta dauki wayarta ta sake gwada kiran ayanah din ita kuma sakinah miqewa tayi ta nufi dakin Bahar sbd dubota taji abinda ya sakata kaiwa har 9 yau bata dawo gida ba gashi an hadu da tsautsayin da basusan wace makomar zasu fuskanta ba duk da kila fushin samun Asim a gidan da rashin samun ayanah zai boye nata lefin da baima ankare ba tukuna.

Ko data je bahar ta lallaba ta shiga wanka da sanyin jiki dan haka bata tsaya ba ta fice itama taje ta dauki wayarta ta fara kiran NUAB din dan bada hakurin da zai sassauta lamarin amma tana kiran farko taji wayoyinsa duka a kashe dan haka ta gwada kiran aleey wanda shima a kashe ta jisa abinda baayi kenan jin wayarsa a kashe sbd shine kunnuwa da idanuwan NUAB baya taba yadda ajisa kashe matiqar ba yana sama ba cikin jirgi kenan.

Cikin damuwa me tsanani da rashin sanin abin yi suka zauna sunata zabga kiran Ayanah amma babu alaman zasu samu hakama tenya datake iya magana direct da sultan shima kiransa takeson yi amma tana kasawa dan batada hurumin kiransa tace a bawa ayanah sannan kuma ta fadawa ayanah ta dawo NUAB yazo duka a sultan din sam bazai yiyuba dan haka kadir ta ringa kira shi kuma wayarsa na silent yariga ya kwanta ma a lokacin.

Sake shiga tashin hankali sukeyi dare na kutsawa ba wata makama kuma sun tabbatarda NUAB matiqar ba wucewa yayi ba da bacin ran daya bar gidan to zai dawo sake buqatar ganin Amminsa ayau din su kuwa babban tashin hankalinsu kenan sbd badai zasu iya fuskantarsa su sanar dashi bata nan ba tsawon lokaci kokuma batama uk din wanda suna fadar hakan sai sun fada tareda wa take wanda abu ne da bazai yiyu jinsa a bakinsu ba sbd bazasu iya dauka da kallan fushinsa ba zaiyi muni koma yayane su gwara iyayen nasa su fuskancesa da kansu.

Da wannan tashin hankalin da fargabar tareda zullumi suka ratsa daren suka kwana har safe a zaune suna sakawa da warwarewa ga bangare daya damuwar maa sakinah biyu ce tana tsananin tsoron ace NUAB ya ankara da bahar da lokacinda ta dawo din dan haka taketa adduar masifar ta tsaya a iya guri daya.

Ita kanta Bahar a daren duk da ta dawo da yunwa sbd wani class ne na fashion design da sukai joining ya sakasu kaiwa dare sosai sbd kayan amarya da akai designing a gurin wanda dukansu aiki suka kusan wuni sunayi kasa fitowa cin abinci tayi ta lafe a dakinta har lokacin zuciyarta bata koma yanda take bugawa ba daidai. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee

122 Koda washe gari tayi safiyar ta waye babu wanda ya samu kuzarin fitowa da wuri suna dakunansu a lafe suna jiran kowane irin tsammani,

Bahar ma lafewa tayi taqi fitowa sam sbd batama son tsautsayin dazai saka su hadu harma ya ankare da ita matsalolinta su dawo zata jira a gefe taji idan ya wuce kenan tukuna,

School ma bata shirya ba sai guraren after 10 ta fito a shirye tareda nufar kitchen tayi breakfast sama sama acan ta fito ta nufi dakin su maa din tana budewa suka bita da kallo kowacensu da waya a hannunta sunata fama da abu daya,

Tenya ce ta fara amsa gaisuwanta tana tambayar ko tayi breakfast tace eh tayi karta dade kaman jiya ta fada mata tana taqaita zancen anan sbd batason bahar din ta wani fahimci halinda suke ciki duk da a bayyane hakan yake suna cikin tsananin damuwa me karfi.

Maa sakinah kuwa tasowa tayi tana gyara mata rolling din dayake kanta na blue qaramin veil din doguwan shaped bahrain gown dake jikinta bata kamata ba sam suka yo palo tana jin sam batason yau bahar din ta fita koina koda school dinne kuwa sbd su fara tabbatarda ya wuce gudun dora wata fitinar akan wata dan kuwa a yanda yake yanzu wuta ne ke cinsa dazata iya kona komai.

'Bahar ko zaki hakura da school dinnan yau da gobe ne mu jira NUAB ya tafi'

Kallan maa din tayi tana dan marairaice fuska sbd tana buqatar tafiya school tabar gidan dan bazata iya barin ya taho tana gidan ba wanda a yanzu hakan haryanzu palonsu qamshinsa yakeyi dan haka gwara ta tafi idanma yazo batanan bata gansa ba bai ganta ba idan ya wuce din kuma shikenan.

Numfashi maa ta sauke ganin yanda bahar din ta narke dan haka sai kawai tace

'To ana tashi yau kada kije kowane class na komai da kuke zuwa ki tabbata kin dawo gida kai tsaye.'

Batareda taso hakan ba tace ok tareda nufar kofa ta fice.

Tana fitowa yau bata tadda Ari ba wanda bai taba fashin zuwaaba tinda sassafe kuwa sai dare yake tafiya.

Time ta kalla batason kiransa sbd kada ta janyowa kanta attention din yaransa dashi kansa dan kuwa tasan dole Ari hanasa zuwa akai ko kuma akwai wani dalilin dan haka ficewa tayi kawai ta hau mota ta tafiyarta.

Tana tafiya su Maa sakinah suka fito daqyar suka iya breakfast suka shishirya dan zaman jiran tsammani kaman yanda suka fada,

Karfe goma sha daya daidai su Leylah suka iso gidan tareda Asim wanda gabaki daya ya qarasa zama wani irin kamar sakarai dan kuwa sai baza idon neman bahar yakeyi ya samu ya kalleta son ransa yayi magana da ita kafin wani abin ya kuwa zuwa ya giftawa jin dadinsa,

Ita kanta leylah a zaune take suna fira sama sama dasu maa amma hankalinta a rabe yake kaman yanda nasu yake a raben kowa hankalin rabi anan rabi a wani gurin.

Suna wannan zaman ne wayar leylah tayi ringin ga mamakinta number ce kaman bazata dauka ba sai kuma ta dauka Shuraim taji take ta ciro wayar daga kunnenta ta kalla taga numbern qasar ce da sauri ta maida kunne tana tambayarsa yana ina ne?baya boyem?

Fada mata yayi yana uk ya kasa samun numbern Ammi hakama yanata kiran wayar Maa sakinah baa dauka yanason zuwa gidan ne ta turo masa numbern maa tenya.

Wani yawu ta hadiye da karfi tana jin rashin dadin zuwansa sbd zuwansa zai iya hanata sakewa musamman tinda tasan shima meyake so wanda harga Allah tafison Asim ya samu bahar a maimakon shi dan uwanta sbd Asim ya samu bahar shine zata samu yancinta na abinda takeso hakama tafison Bahar tayi takaba idan Asim ya tafi a maimakon ta auren dan uwanta da zata samu rayuwar soyayya me kyau.

Badan taso ba ta masa sharing location nasu baiyi awa uku ba kuwa sai gashi a gidan ya iso cikin kwanciyan hankali shima kuma tin acan yake mamakin abinda su leylan sukeyi a gidan bayan honeymoon zasu tafi.

Su Maa da ayanzu gabaki daya basa murnar zuwan kowane baqon hakanan suka daure suka danne suka tarbesa da nuna farin ciki sosai dan haka gidan ya dauki haramar murna da yar hayaniyar farin cikin baqi da suma baqin kowa ke cikin farin cikin kasancewa a gidan.

Shuraim kai tsaye shi kam ya tambayi bahar aka sanar dashi tana school dan haka ya ringa kiyaye time dan jiran dawowanta.

Shiru shiru su maa suna jiran jin ta inda NUAB zai bullo ko a zahiri ko a kiran waya amma shiru dan haka suka dan sassautawa kansu suna kokarin sake sakewa a cikin baqin nasu da duka dai na gida ne.

Karfe uku Bahar ta dawo gidan zuciyarta na dan shiga yanayi na fatan basada kowa a gidan,

Tana sako kai a palon yar hayaniyar datake jiyowa ya sakata jin kirjinta yayi nauyi amma sanin ba NUAB bane ya sakata qarasowa tana kallan palon sbd idan shine tin a gate zata ga motoci da securities nasa hakama sam bazaa samu kowace hayaniyaba a duk inda yake a guri.

Ganin Shuraim da idanuwanta suka fara sauka akansa ya sakata sauke ajiyan zuciya me dan karfi tana maida kallanta akan maa sakinah data gode Allah bahar din ta dawo kafin zuwansa duk da sun cire rai sun tabbatarda ya wuce.

Da tsananin farin ciki da sanyin zuciya shuraim yake kallanta yana mata barka da dawowa itama kokarin sake fuskarta tayi sosai tana masa barka da zuwa kafin ta juya ta kalli Asim wanda kusan yayi mutuwar zaune a gurin kallanta tai masa barka da zuwa shima tukuna ta kalli leylah ta masa sannu da zuwan wanda duka basu samu sunyiba jiyan.

Gaggaisawan da sukai idanuwansu duka akanta ya sakata kasa zama a cikinsu ta wucewanta daki dan cire gajiyan data dawo da ita.

Leylah data kafe bahar da idanuwanta harta shige wata nauyi taji ya danne kirjinta sbd babu wani abu daya rage a bahar din data sani baya dayake tareda ita a yanzu sbd gabaki daya ta sauya sauyawa kuma ba qarama ba dan kuwa hatta skin tone nata ya tashi daga fara zuwa kaman butter dan kuwa har wani daukan ido takeyi ga wata irin calmness da class tareda basarwa kaman ita kadai ce 'yar sarauta a gurin,

Suturar jikinta da duk abinda yake jikinta babu wanda ba original designer ba,

Sake jin tayi kishin bahar din me tsananin gaske yana rufeta ta juyo ta kalli maza biyun da suka gama mutuwa akan bahar din wadda batama jin bahar din ta basu hankalinta dama zata san me suke ciki,

Tsoki taja mara sauti sosai cikin takaici da baqin ciki tana kallan Asim da farin ciki yake bayyane sosai a fuskarsa duk da ya dena kallan hanyar da bahar din tabi amma kana kallansa zakasan yana cikin farin ciki da walwala.

Akan Shuraim ta maida kallanta shima wani tsokin baqin cikin ta sauke tana jin kwata kwata ma ta gaji da gidan fitarsa take son yi.

Tinda bahar ta shige bata fitoba ba wanda ya sake ganinta tana bedroom dinta tayi wanka ta saka skinny jeans da farar loose top tayi kwanciyanta a daki tana wayoyinta da duba abubuwa a laptop abinci ma sedai tayi waya me aiki ta kawo bata har dakinta taci tana harkan gabanta hankali kwance.

Har yamma ba labari NUAB dan haka yanzu kam sun sakewarsu gabaki daya duk da a cikin zuciyoyinsu suna jin tsananin rashin jin dadi kuma har lokacin har wayarsa harya ayanah bame zuwa.

Da daddare suna kokarin fara dinner a table yauma sukaji shigowan mota wadda kai tsaye ta saka kowa shan jinin jikinsa sbd dai ba bahar bace tinda tana gida motarta ma tana pake.

Maa sakinah ce ta baro dining din hakama tenya suka dawo palo tareda baro su Leylah can wainda suka fara cin abinci daga Shuraim har Asim hankali kwance da farin cikinsu.

Bude kofar akai kai tsaye aleey ya sake bayyana kaman jiran sedai babu NUAB din a tareda shi ga mamakinsu luggages din da suka tabbatarda na NUAB ne sbd tsarinsu da sanin tsadar da suke screaming aleey ya fara shigowa dasu bayan ya tsaya a gabansu cikin girmamawa me karfi ya gaidasu yana sake tambayar Ammi ta dawo??

Ganin ba tare ake da NUAB dinba ya saka tenya bude baki tace

'Aleey na tabbatarda zuwa yanzu kai kasan bata nan kuma mun kasa samunta a waya kwata kwata dan Allah kada ka bari NUAB ya dawo nan wlh yana dawowa zai iya sanin abinda kansa bazai dauka ba.'

Kasa kallanta aleey yayi sbd girmamawa kafin yace

'Maa banda abinda zan iyayi sbd tin acan nayi kokarin hana zuwan tinda yaxo da kansa koma menene zai sani sbd ya kamata ya sani din'

Maa sakinah kuwa mutuwa jikinta yayi da sanyi ta tabbatarda akwai matsala babba dan kuwa dawowan NUAB gidan batareda cewa komaiba kasawa zaiyi ya tsare ya ganewa kansa lokacinda Ammin zata dauka ta dawo daga koma ina ta tafi kuma ta tabbatarda hakan da yayi yana nufin bazai sake tambayar kowa komaiba kawai da kansa zai tabbatar kuma hakan alamar ya gama kai qarshen bacin rai da fushi me zafi akansu.

Masu aiki biyi Maa sakinah din ta kira ta je ta dauko card din bude palon da basu taba shiga ba wanda master bedroom na gidan yake ciki sedai a bude duk bayan kwana biyu a gyara a sake rufewa, Bawa masu aikin tayi tace suje su gyara komai da kyau da tsaftar datafi duk wadda suka sani a duniya.

Karba sukai suka tafi daman sun saba gyaran dakin dan haka wata irin gyara sukai masa a cikin kiyayewa sbd komai na bangaren kana gani kasan yafi koina a gidan.

Ba bata lokaci suka gama aleey ya isa dakin da kansa ya jere kayan NUAB din a tsarin dayasan zai san inda komai ya buqata yake dan duk inda suka tafi ko duk inda zasu sauya guri aleey bai taba sauya yanayin tsarin yanda yake aje komai na NUAB dinba dan haka duk inda yaje yana shiga dakin da duk zai zauna yasan inda zai samu komai sbd tsarinsa da aleey bai taba sauyawan ba.

Bayan gama komai seta sanyin aircon daidai da yanda LEUL din yakeso yayi ya sauya qamshin dakin zuwa blooming wolf wanda take dakin yayi daidai yanda NUAB zai nutsu dashi tukuna ya fice dan hatta toiletries nasa da duka abin amfaninsa an jeresu tsaf. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee

123 Aleey na fitowa daga bangaren koda ya iso main palon su Maa din na zaune shiru babu me abin cewa hakama su Asim suna zaune suna qara har fira kafin wucewansansu batareda sun san meyake faruwa ba bama susan Aleey yazo yana cikin gidan ba saida suka gansa kwatsam a palon suka dago suna kallansa cikeda mamaki shima kallan Shuraim din yayi da mamakinsa daya kasa barin ya fito fuskarsa ba kyau duk da bazaka fada a bace da rai yake kai tsaye ba dan shi Asim ko kallansa baiyiba dan yana kokarin danne zuciyarsa ne daga musu abinda zaifi wulaqanci ya dan haka time din agogon hannunsa na blackmambaC36 ya kalla ya bude baki yace

'Sultan zai kasance anan nanda mintina kadan if you guys c......

Bai qarasa ba leylah ta bude baki zatai magana Asim ya katseta yana cewa ta tashi su tafi tukuna gobe sa dawo.

Girgiza kai leylah tayi tana kokarin mayarwa Asim din magana Aleey da baida time ya juya yabar gurin yana ficewa gabaki daya.

Securities ne yazo dasu masu karfi ya fito yafara musu bayani suna zagaye harabar gidan shirinsu na bawa gidan tsaro sbd mai qasa daya dawo gidan.

Aleey ma daya gama tabbatarda komai yayi daidai da ina NUAB din zai iya rayuwa dakin dayake daga wajen harabar ya isa daman shima an gyara masa ana gamo gyaran na NUAB ajiye ipad dasu laptop da sauran abubuwan da baya nesa ko kadan dasu yayi ya fito yaja mota ya fice gidan tareda tabbatarwa da securities kafin ya dawo da NUAB duk wanda yake cikin gidan ya fita bayan su maa da masu aiki ko waye a tabbatarda an fidda shi idan bai fita ba a mintinan da suka wuce talatin.

Aleey na ficewa gardama da fada ya barke tsakanin leylah da Asim sbd batajin zata bisa ayau din dan ganin aleey ya tabbatar mata da NUAB yana nan har yanxu kenan dan haka ba inda zata.

Asim kuwa dagewansa akan tafiya da ita sbd ya ringa fakewa da ita yazo kawowa kullum ya shigo yagaisa da bahar sabanin idan ya barta dole zai daga kafa kwana biyu kafin yazo gidan dan haka yace saita tashi.

Maa sakinah da aleey yana ficewa tabar gurin ta isa kitchen tana bawa masu aiki umarnin su sake gyara koina kuma yanzu da Sultan me boyem zai kasance a gidan sai sun kiyaye sosai sun sani,

Shai ta fara kokarin hada masa ita kuma wanda yakeda karfi a lafiyar kwakwalwa da lafiyan jiki batareda tana da wani karfin jikiba sosai sbd dawowansa gidan kadai hukunci ne me karfi ga dukkansu sbd zai tabbatarda kasawarsu a abubuwa da dama dazasu ji kunyarsa akan kasawan.

Tenya dake zaune cikinsu ma itama barin gurin tayi bama tareda ta ankare da wai fada ne sukeyi ba sbd maganarsu bata wani tashi sosai Tana barin gurin suka fara daga muryansu wa juna suna kokarin bankada sirrinsu a gaban Shuraim wanda yake mamakinsu da fada akan abu qanqani dan haka ya bude baki yana kokarin dakatar da leylah ita datake mace yana rokon Asim din akan ya barta ko kwana daya ne iya yau tayi shikenan.

Asim da baiso hakan ba amma sbd kada a gane maitarsa a fili sai ya amince yana daure mata fuska sosai ita kuma farin cikin hakan ya sakata kallansa tana kokarin taimaka masa tace

'Bara na kira Bahar kuyi sallama da ita'

Dagowa Asim yayi ya kalleta da idanuwansa da suka dan sauya ta saki murmushi tana daga masa gira alaman ko bai gode bane?.

Dan sakin fuskarsa yayi yana daga mata tasa girar shima wanda hakan ya saka shuraim dake tsakaninsu jin wani iri sbd kaman ba yanxu suka gama fada ba harsun shirya da dagawa juna gira cikin sexy way bama tareda kila sunsaniba da manta yana guri.

Barin palon Leylah tayi ta nufi dakin da akace mata shine na Bahar shima kofarsa tana dan daga lungu kadan tana isa kai tsaye ta bude kofar dakin wanda qamshin Bahar din me wata irin ratsa kai da zuciya na hadin Oud na gyara tenya daya gama kama jikinta sbd kusan duk bayan kwana biyu tenya ke gyaranta shiyasa hatta fatar jikinta koyaushe qamshi takeyi bare sitirarta da kuma dakinta ko undies nata hatta jerin handbags nata kamshinta sukeyi sbd sun riga sun kama.

Sanyin aircon ne da qamshin suka daki fuskar Leylah tareda shiga hancinta kai tsaye ta dago a yanayi na tsananin mamaki da mutuwan da jikinta yayi na kamshin kadai data shaqa ta kalli cikin dakin wanda komai yake a tsare da tsarin wayewa da turawa da kuma gata da luxuries da koina ke nunawa.

Akan Bahar din dake tsaye gaban mirror ta daure gashinta da band sako sako sbd tayi shirin bacci already kayan bacci ne a jikinta na riga da wando masu santsi maroon mai kyau dataiwa fatarta kyau sbd duhun kalar.

Ita kanta Bahar juyowa tayi a hankali da wata irin nutsuwa tana kallan kofar da aka bude kai tsaye, Ganin leylah ya sakata mamaki sosai amma bata nuna ba ta baro jikin mirror din tana tahowa a cikin takun nutsuwanta data zama tamkar jan ajinta.

Kasa dauke idanuwa daga kanta leylah tayi tanajin hankalinta kaman yana tashi da halittar datake gani gaban nata tana tinkarota.

Bahar bata qarasa har gabanta ba ta tsaya tana dauke kallanta daga kan leylah ta bude baki a natse tace

'Zaku tafi ne??

Sai a lokacin leylah ta iya hadiye wani 'dacin daya mamaye bakinta tana dan dauke kallanta daga kanta tace

'Yes zasu tafi ni ina nan sai bayan kwana biyu zan tafi so gasu can zasu tafi'

Dan shiru bahar tayi na jin leylah na nan har kwana biyu bayan sam basa jituwan da zasu iya kwana biyun a guri daya amma bata nuna komaiba ta basar tace

'Ok' a taqaice tana juyawa zuwa ina wayarta da sauran su ipad dinta suke ita kuma leylah juyawa tayi kafin zuciyarta ta buga da baqin ciki ta sanar musu ta fada mata tana zuwa.

Bahar kuwa tinda ba cewa leylah tayi ana nemanta ba batai yunkurin tafiya ba sbd ta dauka kawai ta fada mata ne zasu wuce,

Wayarta ta dauka tana kallan time taga 8 ta wuce kuma take taji gidan yana fita ranta sbd batason hayaniya ko damuwan da suke shiga a baya na zama guri daya da leylah dan haka taji inama baa samu matsalar bayyanar NUAB ba a jiya data tattara ta tafiyarta hostel har sai ankwana biyu leylah ta tafi,

Wayarta ta dauka ta saka kiran Neesah ta rarrasheta tazo ta tayata rokarsu Maa akan su tafi hostel gobe sunada wani class tinda sassafe karfe 7.

Tana saka kiran Neesah din itama tana kokarin komawa hostel kenan daga fashion house nasu da bahar din bata samu zuwa ba yau dan haka tana fada mata tace me motar ya juya da ita zuwa gidan akan koda baa barsu tafiyarba ita Neesah zata tsaya ta taya bahar din kwana biyun.

Su Asim jira suketa faman yi na fitowan bahar amma babuta shuraim sai sake son jiran ta fito yakeyi duk da yana kallan time sosai sabanin Asim da duka hankalinsa ya tashi yaji tafiya yakeson yi tin kafin NUAB din da akace ya iso gidan ya sake samunsu shi yanzu bayason matsala a rayuwarsa da kaddara me muni dan haka gwara ya lallaba ya samu bahar din da salama.

Mintina ashirin da biyar ne suka cika take akai Knocking kofar data saka Asim miqewa bai jira komaiba ya nufi kofa yana kasa yiwa su maa saida safe ma,

Shuraim ma miqewa yayi yana bin bayan Asim din yana jin da kaman ya sake aikawa kiran Bahar din ita kuma leylah dazai aika ma tana kitchen da rawar jiki ta saka hannu aikin hadawa NUAB din duk abinda ake kokarin hada masa sbd itace take son takai masa idan yaxo sbd su gaisa.

Bude musu kofa security guard din yayi batareda ma ya iya ce musu komaiba ya basu hanyar datake seti da gate na ficewa gidan alaman su saka kai kawai.

Asim dayake gaba saukowa stairs na kofar yafara yi wanda yayi daidai da bude gate din dakai hasken mota ya haskesu tas suna fitowa da saukowa zuciyarsu na dan shiga shakka.

Qarasa shigowa da motocin guda biyu masu daukan ido duk da dare ne amma akwai haske daya saka ake iya ganin ba kudin banza ya siyesu ba akai harabar gurin ana parking nasu a natse.

Asim bai tsaya ba ya fice gate din gabaki daya, Shuraim ne yaso tsayawa ya gaida Sultan din Aleey daya fara fitowa ya sanar dashi yaje yanzu ba lokacinda ya kamata bane ya bari sai wani lokacin.

Shuraim na jin hakan ya saka kai shima sbd a yanayin aleey kadai ya gane akwai bacin rai,

Suna ficewa aleey ya sanar da security a rufe gidan a kuma rufe shigowan kowa a gidan saida bincike da izini.

Budewa NUAB din kofa yayi wanda kallo daya idanuwansa sukaiwa Su Asim din dake fitowa a lokacinda motarsu ta sako kai gidan ya dauke idanuwansa daga kansu sbd zuwa yanzu ya gama fahimtar mutanen dake cikin gidan makashi sukeson ya zama.

Fitowa yayi a kame yana nufar ciki kai tsaye idanuwansa a take sukai mugun sauyawa amma baice komaiba bai kuma nuna komaiba wanda duk wanda yake karkashinsa yasan ya harzuqane take da fushi da bacin rai duka wanda wannan gidan dai da ba iyayensa ne a ciki ba dukansu mata da ko waye yake maida gidan tamkar gidan gala da tin jiyan bazaiga safiyar yau ba sbd zai zama makashinda dai suke son ya zama. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee

124 Ko daya shigo palon tsit yake sai masu aiki dake sake gyarasa daman fitar su Asim din suke jira kuma kaman sunsan sultan din yana hanya suna ficewa qamshin palon suka fara sauyawa daga qamshin su Asim din suma me tsada daya kama palon.

Kuma dayake ba wata gyara da palon yake buqata sbd dukansu ba yara bane maza ne masu nasu ajin da wayewa da ilimi kawai dai dan abinda baa rasaba sukeyi.

Suna jin bude kofar aleey kadai suka iya gani sukai saurin zubewa qasa batareda ma sun bari idanuwansu sun kalli wanda kallansa tafi karfin idanuwansu suna sauke kansu qasa da tsananin girmamawa suna yin tsit sbd basuma da damar bude muryoyinsu a gaban sultan matiqar ba an buqaci hakan daga garesu bane.

Readers Also Read