Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 54
Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 54: Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 54. 'Ah ah tambaya fa kadai nayi naji anyi…
4,462 words
'Ah ah tambaya fa kadai nayi naji anyi maganar tafiyan ne kuma na sani ko akan school ne sukai tafiyan kawai dai naji tinda neesah ta tambaya ba tare suka tafi ba kenan kuma nasan Bahar bazata iya tafiya ita kadaiba shiyasa hakama banason tayi tafiya koinada wainda bata saniba kuma batareda kowa na gida a tareda ita ba.'
Shiru suka sake mata ba wanda ya iya cewa komai sema karfin halin cigaba da cin abinci da sukai musamman tenya da batada abin fada.
Maa sakinah ce tace
'Ai insha Allah bama zata sake tafiya koina ba'
Ko data fada hakan tana cigaba da cin abincinta.
Bahar kasa cigaba da cin abincin tayi gabaki daya ta ajiye ta dauki tissue ta goge bakinta tana daukan ruwa tasha tana ajiyewa ta silale tabar gurin.
Tana barin gurin itama Neesah tabi bayanta amma ita taci sosai sbd tana tareda yunwa sbd tafiya.
Tana barin gurin Ammi ta sauke ajiyan zuciya tareda kallan su maa tenya dakyau ta bude baki tace akwai abinda ya kamata na sani ne?? Wani abin ya faru ne naga kaman ba wanda yaji dadin sanin danayi anyi tafiya.'
Ajiyan zuciya dukansu suka sauke a boye amma ba wanda ya iya cewa komai har lokacin dan haka ta sake shiga zargin akwai abinda ya faru din kenan.
Bata sake cewa komaiba har suka gama ta koma dakinta bayan ta gama komai na shirin bacci ta zauna bakin gado dan qarasa maganarta da Zuhrah da sukeyi akan Leylah da batasan yaya zata fuskanci meyake shirin faruwa ba.
Itace ta saka kiran zuhrah din a lokacin itama zuhran ta gama shirin bacci tana dakinta zaune sbd yunar baya qasar yana kuwait gurin uwargidansa. #MAMUH 09033181070
HAYATEEM Mamuhgee
141 Magana sukeyi sosai a natse da neman mafita da shawara a tsakanin Ammin da zuhrah wadda take cikin damuwa tana sake sanar mata da dole akwai matsalar dake tsakanin Leylah din da Asim wadda ta boye ta kasa fada mata amma ita tinda ba yarinya bace tana gani ta sani,
Shuraim ma wanda take neman shawaransa akan komai taso fada masa amma ganin shima tinda ya dawo daga tafiyar da yayi bata gane masa ba a cikin damuwa yake dan haka take tinanin Allah yasa ba matsala suka samuba dukansu da Sultan LEUL sbd sunce yana qasar sun barosa.
Shiru Ammi tayi jin saukan maganar a kunnenta kamar tsawa me karfi zuwa kirjinta amma bata jin taji abinda zuhrah din ta fada dakyau sbd kaman cewa tayi NUAB yazo Oxford shima kokuwa sultan yasar take nufi dan haka tsayar da tinaninta tayi guri daya dan ta fahimta tace
'NUAB kike maganar sun bari anan kokuwa Sultan? Anan Oxford suka gansa?
'Eh NUAB din dai suka bari anan sbd shima yabar nan kusan satinsa biyar baya nan fa ashe can ya tafi acan suka barosa yandai shuraim ya fada mun'
Sake shiru Ammi tayi tanajin wata zufa na tsinke mata tana sake kasa yadda da abinda zuhrah ke fada, Tayaya NUAB zai taho Oxford bata saniba dan kuwa koda bata nan tana dawowa su Sakinah zasu fada mata,
Basu fada mata cewan yazo ba wanda kenan baizo dinba amma kuma shi kansa Shuraim din tinda yace ya gansa kenan ya gansa din To kenan baizo nan gidan ba qasar yazi kadai ko me??
Kasa cigaba da magana tayi ta cewa zuhrah ta bari da safe zasuyi magana, Tana fadar hakan ta kashe wayar tana rasa wane tinanin zata kama ko wane zata fara kira ta tambaya.
Shuraim ta kira a waya wanda yana ganin kiranta cikeda girmamawa da kulawa ya daga ya gaidata ta amsa a natse kafin ta dan fara da nasihar su rage saka mahaifiyarsu a damuwa koma menene damuwansu su idan wadda zasu iya sanar mata ne su sanar mata su dena sakata damuwan ganinsu a wani yanayi mara dadi. Tana gama nasihar ta jefa masa tambayar ashe yaxo uk din batanan ta dan yi tafiya,
'Eh Ammi nima dayake ba dadewa zanyiba ina gama dan aikin daya kaini na juyo sbd kadama Sultan LEUL ya rigani baro uk din ya dawo sbd akwai ayyukan dake a qasa'
Ajiyan zuciya Ammin ta sauke tana ji dai NUAB din yaxo uk din kenan,
'Ai nama dauka tare sukayo tafiyar sbd tinanin ko tafiyar data shafi aikin masarautar ne'
'No ba tafiyan masarauta bane a rana daya dai muka isa dan nama rigasu isa nan gida gurin su Maa sbd muna can dukanmu dasu leylah ya iso gidan.'
Masha Allah' Ammi tace daqyar tana masa sallama sbd tagama jin cikakkiyar zancen daya saka jikinta mutuwa gabaki daya wayar hannunta ta zame ta ajiye tana jin tashin na rifeta na damuwa da shakka tamkar NUAB dinne ubanta haka taji fargaba ta rufeta.
Zufa tafara gogewa daga fuskanta sbd tasan ya gama samun cikakken sani ga gani ya shedar ya tabbatarda bata nan tana tarera sultan yasar, Kwana nawa yayi yasan batanan? Ya sani amma bai taba nuna mata yasaniba? Yasan tana tareda sultan amma ya iya danne zuciya da fushinta bai nuna ba? Meyake faruwa?
Kasa motsawa tayi duk da tanason motsawa taje ta tambayi su Sakinah taji me zasu fada mata akan wannan babban lamarin da bazasu ce sun manta fada mata bane dan kuwa lamari ne girman gasken daya kamata ace shi suka fara tarbonta dashi amma sukai shiru, Akwai dalilin daya saka suka boye mata wanda ko wane irine me girma ne sbd babu abinda yakeda girman daya wuce fada mata zuwan NUAB da batanan a yanzu.
Sake shiga rudani da shakka tareda damuwa me girman gaske tayi sbd kenan akwai tashin hankali a tsakaninsa da Sultan suna haduwa dan haka taji zuciyarta na sake rasa nutsuwanta gabaki daya ta dauki waya ta nemo numbern sultan ta saka kira dan sanar masa NUAB yasan bata nan tana tareda shi tsawon wannan lokacin.
Shiru yayi shima sbd a bazata zancen ya shiga kunnuwansa dan haka ya shiga tinanin kenan lolacin da NUAB din zaisan ya shiga gabansa shima yayi dan kuwa a yanxu zai sanar dashi igiyoyi aurensa uku reras ne akan mahaifiyarsa dayake ikirarin ya rabasa da ita,zai kalli cikin idanuwansa ya fada masa har koyaushe shine gabansa sbd shine ubansa kuma a yanxu daya mallaki Ayanah ghaz ya gama dashi gamawan da har abada dole ya bisa dan a mutuwa ce kadai zata cireta daga hannunsa.
Kwantar mata da hankali yayi bata tabbacin zai nemi ganin NUAB din da kansa ya fuskance ya sanar masa da komai.
Sake tashi hankalinta yayi dan kuwa tasan idan NUAB din yaji tayi tafiya da sultan ya iya danne zuciyarsa da fushinsa idan yaji cewan aure sukai a yanzu batareda ta sanar masa ba ko neman izininsa batasan yaya zaiyi ba shi da sultan dan haka taji gabaki daya boyem din take buqatan zuwa a cikin daren sbd koma yayane ta fuskancesa a lokacin da zaiji zancen ta bawa zuciyarsa salama da sassaucin halinda zai shiga sbd tasan zata qona zuciyarsa fiyeda yanda zai tsammata.
Kasa rintsawa tayi a cikin daren ta ringa shiga wasi wasi da dana sani kala kala musamman tinawa da alkawarin da sukaiwa juna a tsakaninsu na uwa da 'da wanda babu wanda ya sani sai Allansu sbd bata taba sanin zuciyarta na maqale da sultan a cikinta ba,
A matsayinta na uwa ta karya masa alkwarin dazaiyi shattering nasa hakama duka abinda yayi yanayi ne sbd bata ingantacciyar duniya da kwanciyan hankali tareda kariya da rayuwar data rasa a baya.
Sanyi jikinta yayi gabaki daya taji kunyar kanta da baqin ciki tareda dana sani sun gama lalata rayuwarta babu abinda take tsananin buqata a yanxu irin tafiya boyem taga NUAB din dan haka zata tafi tareda tenya tabar Bahar da sakinah.
Ko da gari ya waye da sassafe kafin kowama ya fito su Bahar sun fice makaranta dan haka koda Ayanah ta fito cikin damuwa me tsananin gaske take bata fara komaiba bayan fuskantar su Sakinah kai tsaye ta tambayesu NUAB daya taho kwanansa nawa? Meyasa suka boye mata ya zo??
Shiru sukai cikeda sanyi jiki sbd ba sauran boyo,
Sake maimaita tambayarta tayi cikeda damuwa da bacin rai tace
'Akwai dalilin boyemin zuwan nasa ne? Akwai wani abin ne bayan zuwan nasa da bazaa fada mun ba??
Tenya ce tayi karfin halin cewa
'Satinsa kusan uku amma baa nan yayi su ba, Kuma munyita kokarin sanar dake tin kina can amma baa samunki kuma kafin ki dawo ya wuce shiyasa baa fada miki ba sbd ya riga ya wuce kuma ba wanda ya fada masa ga inda kika je ya sani amma ya zabi shiru muma mukai shirun'
Shiru Ayanah din tayi tana sake shiga rudanin zuciya sbd ta tabbatar Allah ne kadai yasan abinda yakeji a zuciyarsa ya danne, Kuma satika har uku yayi yaga bata nan? Innalillahi' ta fada a zuciyarta tana jin kanta na nauyi.
Bata iya sake cewa komaiba suma sukai shiru ba wanda yace komai haka ta miqe daga dinin ta koma daki batareda ta iya cin abincin kirki ba,
Kasa kiransa tayi kaman yanda ta saba sbd bazata iya magana dashiba,
Kiransa ya shigo wayarta still kasa dagawa tayi tana kallo ta tsinke tana jin dole ma taje boyem.
Sai yamma su bahar suka dawo basu wani gane komaiba a gidan sbd kowa yayi tsit gidan ba kanta dan haka suma abinci sukaci suka fada karatu har dare ba wanda ya fito ko abinci kowama daban daban yaci nasa,
Bahar cikin damuwa take sosai batareda kowa ya saniba gabaki daya tarasa gane kanta karatun ma yinsa takeyi tana jin kaman baya shiga sbd hakanan take jin damuwa da fushi akansa lokaci daya hakama gashi Ammi ta gane tayi tafiya kowane minti da second tsoron kada Ammi ta gane ko ta fahimci dashi tayi tafiyar take amma duka wannan fargaban da tashin hankalin ita kadaice takeyi shi yama manta da ita da abinda zai biyo bayan idan Ammi ta sani dan haka fushi da bacin rai take ciki sosai wanda ya sana hadda wayarta ta hada haushin ta kashe kwata kwata ta ajiye.
Washe gari Neesah ta tattara ta koma hostel tabar gidan tabarsu a cikin yanayin da suke ciki,
Ammi tafiyarta boyem tafara shiryawa a lokacin ne Bahar taji maganar tafiyan a bakin Maa tenya da laifinsu na boye zuwan NUAB dan haka hankalinta yayi mummunan tashi ta shiga rawar jiki da rudanin jin Ammin tasan da zuwan NUAB,
Dakinta taje da gudu ta rufe ta zauna a qasa ta ringa kuka kaman ranta zai fita tanajin rayuwarta tagama tsayawa tinda Ammi taji abinda ya faru,
Wuni tayi tana kuka mai tsima zuciya daman kukan ne yake cikeda kirjinta tsawon wannan lokacin dan haka a wuni guda kammaninta suka sauya tayi jajir idanuwanta sukai luhu luhu ko ruwa ta kasa fitowa tasha.
Har dare bata fito ba bata bari kowa yaga yanayin datake ciki ba,
Harta kwanta aka bude kofar dakin aka shigo a natse.
Ammi ce ta iso har bakin gadonta ta zauna tareda dan qara hasken dakin kadan tana kallanta.
Cikin damuwa ta kalli fuskanta data kumbura sosai kammaninta sun sauya tace
'Subhanallh Bahar??
Kafin ta sake wata maganar Bahar din ta fashe da sabon kuka tana tashi zaune ta sauko qasa ta zube gaban Ammin tana kama kafafunta tace
'Wallahi Ammi shine yamun dole bada son rainaba, Ammi ko su Maa zasuyi shedan dole yamun, Hakama ko tafiyar Birmingham daga zuwa ganin likita ya tafi dani bada son raina ba dan Allah Ammi kiyi hkr kada kiyi fushi akan hakan ki tafi Boyem ki barni Ammi bazan sake ba dan Allah kiyi haku.....
Somewa kusan Ammin tayi daga zaune idanuwanta na tsayuwa cak akan Bahar din cikeda mamaki me girma na jin sabon zance kuma bayan wanda takeji a kwanakin kullum, Me bahar din ke nufi?
Miqewa tayi hannuwanta na dan rawa ta kasa cewa komai sbd ita lura da yanayin sanyin Bahar din daya saura rayuwanta a kwanakin ya sakata jin tausayinta takejin ko zata tafi da ita ta yawato ta dawo ko zata koma daidai duk da batasan meyake damunta ba ya sakata zuwa dakin amma tana jin sabon zancen tashin hankali.
Kafe bahar din da ido tayi tana rasa abin cewa har lokacin tana qare mata kallo zuciyarta na bugawa da abinda ke shirin faruw tace
'NUAB dinne ya miki dole? NUAB dinne ya tafi dake Birmingham daman? Me kukaje yi acan? Meye hadinki da tafiyarsa? Duka su sakinah suna me harya kwasheki kuka tafi? Tafiyan wuni guda ce ko kwana?
Rikicewa bahar tayi da tambayoyin tayi shiru tana tsiyayo hawaye wanda ya saka Ammin jin tafara fusata dan haka juyawa tayi tabar dakin ta nufi dakinsu sakinah kai tsaye.
Tana zuwa tambayar data jefa musu shine meya faru tsakanin NUAB da Bahar?
Da mamaki suka kalleta kafin sukai shiru take tinaninta yake inda bata son yaje wani baqin ciki da bacin rai take ya rufeta ta rasa abin fada ta juya tabar dakin tana zuwa wayarta ta dauka ta kira tace ticket din tafiyarsu takeso na tafiya dukansu a goben.
Tana kashe wayarta numbern NUAB data kasa dauka kwana biyun ta kira ido rufe.
A natse ya dauka cikin kwanciyan hankali sbd tinda ya dawo boyem baya cikin nutsuwansa sbd ayyuka da 'yarta data tsayar da rayuwarsa guri daya cak.
Babu abinda ya fara sauka a wayar tasu bayan tambayarta data saka wayoyin nasu shiru.
'NUAB meya hadaka da Bahar daka zo??
Shiru yayi na mintina maganar na amsa kuwwa mara karfi a cikin kunnuwansa ya sauke numfashi mara sauti yana bude kyawawan idanuwansa masu kwarjini ya ajiye file din dayake hannunsa yana dubawa ya bude baki da muryansa me sanyi yace
'Ammi zaki iya jin amsar tambayanki???
Kashe wayar tayi da sauri tana jifa da wayar sbd zai iya bata amsar da zata kasheta kafin safe dan haka gwara ta jira garin ya waye su isa boyem din ya fuskanci fushinta sbd ga dukkan alama yafara lalata karatun yarinyar nan san taga alama amma bata dauka aikinsa bane. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee
142 Dukkaninsu ba wanda yayi baccin arziki musamman da a daren ta sanar dasu tafiyan gabaki dayansu zasuyi yanzu zuwa boyem din.
Bahar sake shiga fargaba da tsoro da damuwa tayi sbd fargaban abinda zaa tafi yi, Idan ta hadasu da NUAB ta tambayesa zai iya fada mata amsar duk abinda zata tambayesa wanda kila bazata taba iya sake kallan fuskar Ammi ba har abada dan haka taji tana fatar masa magana kafin Ammi ta hadasu guri daya ta tambayesa.
Sanyi jikinta yayi tanajin bata taba tafiyan dataji hankalinta yana tsananin tashi ba faduwan gaba na kamata ba idan ta tina irin wannan.
Kasa komai tayi dan haka maa sakinah ce ta hada mata kayanta a suitcase guda daya tinda acan tanada kaya sosai kuma sunyi waya kafin su isa su Naimah da salmah zasu fidda komai akai a wanke a sake gogewa da tirarawa na sitirarsu.
Washe gari ansiya duka tickets dinsu na tafiyar dan haka da dare jirginsu zai tashi amma kusan tinda safen suka gama shirin komai.
Breakfast ma sama sama sukai a dining din duk da Tenya da sakinah hidimar gabansu kawai sukeyi tinda dai ba yanda zasu iya yi, Ammin ce taketa bacin rai da zafinsa sbd taji ciwo da tsananin zafin abinda NUAB din yayi matiqar gaske duk da ta kasa zaunawa ta tambaya taji cikakken bayanin komai a bakinsu sakinah sbd zuciyarta bazata iya daukan jin ba hakama shima datake son yiwa maganar dakyau sbd alkawarin da yayi mata akan zai jira har dai bahar ta gama ko nisa da kama karatun sosai tukuna zaaji raayinta akan shi da aurensa matiqar bata so sunyi alkawarin ba dole zaa sauwake auren a barta ta jira lokacinda duk ta tashi sbd tayi alkwarin bazata bari alkwarinsu itada Abaas ba ya tauye Bahar tinda ko babu komai sun cika nasu alkawarin tinda dai anyi auren.
Yanzu ta tadda wannan labarin da aka boye mata me daga hankali gashi karatun yana neman rikicewa tin baa kusa kammalawa ba, Qarin tashin hankalinta na biyu da shikenan sedai ta tsinci ciki a jikin Bahar. Dalilinsa na karya mata alkawarin daya daukan mata tana matsayin uwar data haifesa takeson ji dan kuwa ya saka mata radadi me zafi da hakan da yayi na watsi na alkawarin.
Bahar ma bata iya fitowa cin abinci ba seda Ammin ta saka aka kirata akan umarni ne ta bada.
A silale take tahowa jikinta a sanyaye kaman mara lafiya tana sauke kanta qasa.
Kafeta da ido Ammin tayi tana qarewa tafiyanta kallo data sauya kwata kwata ba kaman da tana budurwanta ba a baya, Dauke idanuwanta tayi daga kallanta tana jin wani iri duk da tasan su tenya zasu gyara mata ita su bata kulawa fiyeda yanda ya kamata amma dai jin takeyi tayi babban baqin cikin da bata nan ta kula da ita da kanta sannan shi kansa yaga bacin ranta yanda ya kamata dan kuwa duk namijin dazai sauya tafiyar mace bayan maidata cikakkiyar macensa to ba qaramar karfi da wuya tasha ba a hannunsa da nacewa.
Bahar din na isowa zaunawa tayi gefen Ammin tareda bude baki a sanyaye ta gaidata kafin ta gaida maa tenya sbd maa sakinah ita tana dakinta ma tin dazu.
Ammin ce da kanta ta zuba mata abinci da wani kakkarfan hadin madara me zafi datace daga yanzu kullum shi zaa ringa bawa bahar din kullum,
Daman tenya shi take bata tinda abin ya faru tafiyar da sukai ne ta dena sha sai kuma da Ammin ta dawo shima suka dena bata sbd kada ta gani tasan Bahar ta san Namiji kenan sbd hadi ne da kadai ake bawa wadda ta zama macen cikakkiya a cikin masarautar boyem.
Madaran kadai tasha sama sama sai abinci kadan tace ta koshi zata miqe Ammi tace ta sake ci ta koshi.
Sake cin abincin tayi ta tura ta gama ta miqe saita kasa komawa daki taxo gurin Maa sakinah ta lafe gefenta sbd har lokacin ba fuska sosai a gurin Ammi gashi taqi mata fada jira takeyi su isa ta hadasu su biyun kila wanda hakan ke daga hankalin Bahar sosai taji tana shiga damuwa.
Haka suka wuni har dare sukai sallolinsu magrib da ishai suka fiddo komai aka saka a mota suka bar gidan.
Suna ficewa kai tsaye ba doguwan bata lokaci da tafiyan slow suka isa airport daga nan ma ba bata lokacin suka bar qasar zuwa qasar Boyem.
Baccin da basu samu yiba a daren kusan dukansu suka samu a jirgin dan haka hankali kwance sukai baccinsu sbd suna first class,.
Ammi ce batai wani bacci ba sbd abubuwan dake kanta kala kala dana NUAB dana sultan dana Bahar ma ga damuwan da Zuhrah take ciki itama dan haka kanta ya dan dauki zafi da damuwa.
Bayan asuba har gari ya fara wayewa suka sauka dan haka already motocin sultan yasar guda biyu data securities daya suna airport suna jiransu,
Shiga motocin sukai aka bar Airport dasu zuwa masarauta kowannensu na sauke ajiyan zuciya me sanyi da nutsuwan sauka lafiya.
Ita kanta Bahar datake cikin sanyin jiki ajiyan zuciya ta sauke a daidai lokacin da aka wangale musu makeken gate din masarautar na farko wanda yaji sauyi da wasu zafafan securities hakama babu inda bai sauyaba a masarautar tin daga gate din komai ya sauya ya zama na asalin zamani dake ihun ilimi da wayewa dan kuwa wata nutsuwa ma ba shakka ko tsoro irin na baya ba masarautar take ba a yanzu dan a baya kana shigowa zakaji kanajin tsoro da shakka sbd koina karfin ikon mulki kawai yake bayyanawa sabanin yanxu da shaawa da burgewa da wani irin ikon mulki me burgewa zakaji kana gani da ji.
Parking motocin akai suka fito bayin bangaren nasu suna jere a tsaye suna jiran isowansu dan haka cikeda girmamwa suka fara musu barka da zuwa suna karban hadbags din kowacensu kansu a qasa kafin suka tafi suka fara jan suitcases dinsu a natse zuwa ciki.
Kamar daga sama suna daga kafa ko taku hudu basuyiba wata lafiyayyan sautin qarar dawowan Uwar sultan me mulki a yanzu me boyem ta fara karade masaurautar tana ratsa koina.
Sultan NUAB dinne da kansa dayake zaune a daya daga cikin lafiyayyun sofas dake office dinsa a hawa na karshe dake building na offices nasu yaji saukar sautin yana ratsa kunnuwansa ya tabbatarda Ammin tasa ce ta iso sbd ya samu labarin barowansu daga daga drivern Bahar dan haka lumshe idanuwansa yayi ahankali yanajin wata niimar sanyi na ratsa gangar jiki da zuciyarsa sbd daga karshe dai matarsa ta iso garesa a maimakon tafiyan da zaiyi zuwa gareta a satin wanda ya shirya tsaf dan fuskantar Amminsa shima.
Sake sauke numfashi yayi me sanyi da nutsuwa yana dago kyawawan idanuwansa da harsun sauya sbd sabuwan nutsuwa da niimar data shigesu ya kalli Aleey da keelah dake gabansa sukai qasa da kai a natse sbd bazasu iya daukan idanuwansa a cikin nasu ba musamman da wani sabon yanayin yake bayyana a cikinsu.
Files din hannunsa ya ajiye a gabansu a natse yana maida bayansa ya jinginar a kujeran dayake ya bude baki yace
'Na duba duka abarsu a yanda tin farko aka tsaro, And bazasu samu ganina ba sam a yanzu ko a kusa ba sai munga yanda business dasu din zai kasance, Keelah kaine zaka hadu dasu a Moscow din ka gudanar da komai daidai yanda kasan muna komai na sealing deal din.'
'Yes LEUL' keelah ya fada yana daukan files din a hannunsa yana karanta wasu a ipad din hannunsa sbd daman sun saba dik businesses dinsu sune masu zuwa shi keelah ko Aleey sai manyan ne kokuma wainda suke na mahaukatan daloli yake zuwa da kansa hakama idan har tattaunawansu akan businesses nasu ne na GHAZs basa ambatarsa da sultan da LEUL kaman yanda suka saba suke kiransa wato Zaki sai idan harkar sarauta ce suke tsayawa kansu a qasa su ambacesa da Sultan LEUL boyem.
Su kansu tinda sukaji sautin isowan Uwar me boyem din suka shiga sabuwar nutsuwansu musamman aleey daya san lokacin haduwan NUAB din da sultan yasar yayi sbd Ammin dake tsakani ta iso.
Gama tattaunawa sukai kusan a office din suka kwana suna aiki sosai dan haka yanzune suke kokarin tafiya kowa ya kwanta ya huta dan yau sultan NUAB din bazai fito office ba kwata kwata sai gobe.
Fitowa sukai tareda hawa lift suka sauko securities da fadawan sultan din na masarauta suka miqe tsaye dukansu sbd suma anan suka kwana din suna gadi.
Gaba yayi a natse cikin kamewa da wata irin kwarjini da kyansa na sanyin safiyar dake hana kowa sauke idanuwansa akansa sbd tamkar wani sabon tauraro me haske haka yake haskawa yana daukan ido sbd lafiya da hasken fatarsa da kyau da jan hankali da cika ido.
Kai tsaye bangarensa su nufa sabo wanda girmansa yafi kowane bangare girma sbd girman ginin da akai da tsarinsa tareda zagayesa da qaramar katangar datai kyau da tsari ta kuma ji security.
Suna isowa aka bude masa kofa wangale duka securities na bangaren suna miqewa tsaye cikin girmamawa ya shige batareda ya bude baki ya amsa gaisuwansu ba da hannu kadai ya iya amsawa sbd yana buqatan hutawan gaske da samun nutsuwa a cikin kwakwalwansa.
Yana shigewa main kofar palonsa na farko tareda keelah da aleey iyakacinsu palon ba farko suma suka dakata tareda kai abubuwansa da suka shigo dasu a hannu inda ya kamata su ajiye suka juyo suka fice.
Zuwa nasu dakunan dake waje amma a cikin bangaren kowannensu lafiyayyan babban room and palo ne da toilet da sukaji luxuries suma suka tsaru suka hadu.
Kai tsaye hanyar bedroom dinsa dake kuryan wani palon na biyu ya nufa yana isa ya shige ya nufi closet dinsa ya zare kayan jikinsa tas a natse ya dauki towel a cikin jerin towels din dake jere kaman shago ya daura a qugunsa ya fada bathroom dinsa me girman gaske da tsari. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee
143 Wanka yayi wanda ya dauki lokaci me dan tsayi a ciki yanayi sbd su brush da sauran abubuwan daya saba yi duk safiya kafin wanka tukuna ya fito yana fidda qamshin showerset dinsa dake tashi a fatar jikinsa.
Gashinsa dayake tsiyayan ruwa kadan kadan ya saka towel qarami yana gogewa yana nufar inda zai busar dashi da hand dryer dinsa.
Bai wani jima yana bata lokaci ba ya gama komai ya saka wata black bvlgari tight underwear data kama jikinsa ta zauna a qugunsa ya saka doguwar wando me santsi da fadi ta bacci ya isa lafiyayyan gadonsa ya haye ya shige bargo ya kwanta cikin jerin tarin pillows din gadon masu tsananin laushi ya lumshe idanuwansa yana rufewa take ba bata lokaci bacci ya daukesa hankali kwance.
Bangaren kaman yanda aka saba matiqar yana ciki yana hutawa kowane motsi ya dauke kenan dan haka kowama hutun ya kwanta yanayi sbd hana motsi.
***Haile ma dake kwance tana bacci cikin dan kwanciyan hankalin daya rage mata mara yawa sbd abubuwa sun taru sun tsaya gabanta ba sauki ko kadan sbd gasu Aslam a gabanta zuwa yanzu sun rikice sun fice hayyacinsu sun aje komai aure suke tsananin so ko wane iri ne dan haka ko lokacin komai basuda a yanzu idan bana neman hanyar samun miji ba sbd daga karshe dai sun gaji da zama akan kowace kalar tirban data dorasu tin kuruciyarsu har yanzu da manyancin yazo musu batareda samun komaiba, Sun taso a wahalar neman mulkin da babu abinda zasuyi dashi suna mata, Sun lalata future dinsu tin a baya da yaqin neman mulki ga wanda shi kansa yanzu ya tattara mulkin ya aje baya so sbd rayuwarsa data rasa madafar dafawa a yanzu,
Ta bangaren daya Asim tinda ya dawo daga tafiyar da yayi da matarsa ya kebe kansa baya son hayaniya ko doguwan muamala da kowa yana bangarensa gaisuwa kawai yake zuwa suyi ya koma bangarensa ba kamar baya ba hakama ya sauya sosai ko a gurin muamalantar mahaifinsa ya zama sabon mutum na daban ya samu karfi da taurin zuciyar daya rasa a baya ya zama cikakken namiji me dauriya da karfin zuciyar da bazai iya abubuwa da dama ba na mata ko hawa tirban da Mamensa zata sakasa kowace iri ce kuwa.
Wannan sauyin da haile take gani a tattare da yayanta da suka ajeta suna rayuwan da suka zabawa kansu ba wadda ta zabar musu ba suka koma wasu mutanen daban ya sakata rasa tudun dafawa sbd sune kadai abinda take dasu ta dogara dasu da aikatawa ko samar da kowace irin rayuwar datake so sbd sune tamkar makamanta datake son yaqar kowane yaqin datake so dasu batareda tinanin illar da hakan take musu ba ko zatai musu ba,
Damuwa take cikinta sosai ga Sultan daya tafiyarsa yabar qasar ya tafi ga mistress dinsa yabarsu ya zabeta wanda duniya take shadar da hakan a sannu a sannu,