Kenza eBookz

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 55

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 55

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 55: Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 55. Ga NUAB ba mulkin da duniya take magana a kai…

4,494 words

Ga NUAB ba mulkin da duniya take magana a kai gabaki daya sbd ya kawo sabuwar duniya me burgewa da zamani da ilimi ga masarautar fiyeda wadda sultan yasar ya kawo sbd shima ya ingata masarautar fiyeda sarakunan baya gashi dansa a yanzu yana wanda ya fi nasa juma alfahari da farin ciki yake da hakan,

Su kansu manyan fada dasuke bayanta sun sauya sun zubar da makaman yakinsu sunbi NUAB fiyeda yanda sukai tsammani sbd daya saukesu 'yayansu ya dauka ya dora a matsayinsu dan haka a cikin farin ciki suke hutun sauka kan mulkin suna kallan yayansu a cikin gina sabuwar boyem da shekaru da zamani da qarni masu zuwa zasuyi alfahari da ita.

Jin sautin dawowan uwar me boyem ya saka baccinta yankewa tana bude idanuwanta ahankali tanajin kanta na mummunan sarawar daya saka taji kaman rabin jikinta yana neman dena aiki sbd wata riqewa da jijiyoyin jikinta sukai sbd tafi farin cikin a sakar mata qarar mutuwan sultan da dawowan ayanah rayuwarsu.

Tashi tayi ahankali tana rintse idanuwanta ahankali wani nauyi yana sauka kirjinta daga kanta ahankali ta sauke numfashi me zafi da damuwa me tsananin gaske.

A daidai wannan lokacin itama Maraki data zama tamkar babu ta a cikin masarautar tana zaune a bakin gadonta ta gama sallar asuba ta koma kenan zata kwanta taji sautin wanda ya sakata qasa da kanta tana rufe idanuwanta a hankali taji wani irin nauyi me radadi ya danne kirjinta sbd alkawarin data daukanwa kanta ayau ya tabbata zai cika kenan sbd tayiwa kanta alkawarin daga ranar da Ayanah ghaz ta dawo rayuwar sultan zata barsa har abada bazata iya rayuwa dashi ba kuma sbd zata iya mutuwa da baqin da babu wanda ya sani kaman yanda shi kansa zai iya shiga wuta batareda ya saniba sbd abinda ta tabbatar dashi shine Allah ya kaddari Ayanah ce zuciyar sultan da zai iya bata akanta batareda ya saniba hakama ita daman babu komai a tsakaninta dashi bayan macen biyan buqata sbd bai taba sonta ba a tsawon shekarun nan,bai taba mata kallan macen da zai iya wani girman abu akanta ba, Bata haihuwa ba dan haka ko matsayin imebētis dinsa bata kaiba su da sun haifa jinin boyem a masarautar, Mantawa akeyi da ita ko a tarihi da zaman masarautar, Batada kowane irin amfani, Batada kowane irin matsayi, Ta zamar masa dole kaman yanda a yanzu itama ya dade da zamar mata dole, Dan haka lokaci yayi da zata tafi ko zuciyarta zata samu sauki daga baqin ciki da damuwan datai shekaru tin na kuruciya tana yi, Shi kansa a yanzu mafita da hanyar tsira yake nema yayi rayuwar aminci da kwanciyar hankali dan haka kaman yanda yayi freeing imebētis dinsa duka tana neman yayi freeing nata ta qarasa rayuwar data rage mata da kwanciyan hankali da dan farin cikin data rasa dan bata taba samunsa ba tinda tayi aurensa.

A zuciyarta ta dauka tanada sauran hope bayan tafiyar Ayanah ghaz amma ayau Ayanaah ta dawo babu sauran kowane hope ga haile ma datake da yaya dashi bare ita da batada kowa da komai.

Bude idanuwanta tayi ahakali da sukai jajir tana sake sauke numfashi me sanyi ahankali tukuna ta dauke kafafunta daga qasa tana dorasu akan gadon tareda kwantawa ahakali tana rufe idanuwanta sbd daga karshe dai nacewa a auren sarauta bai bata komaiba bayan karshe me kadaici da quncin da baida ranar tafiya, Auren sarauta ga duk macen da baa so bai taba zama farin ciki ga kowace mace ba dan haka take jin inama zata iya dawo da baya ta zabi auren soyayya da kauna akan auren sarautar da zaa badaka kyauta ko tukuici.

Shi kansa sultan a wannan lokacin dayaji isowan macen da itace rayuwarsa ayanzu ajiyan zuciya ya sauke yana cigaba da adhkar din dayake yi tin asuba yana jin sanyi da nutsuwa suna sake ratsa ruhinsa sbd yawo da kwana kwana ya qare masa lokaci yayi da ba 'danta kadai ba duniya ma gabaki daya zata san da ita matarsa ce cikakkiya a yanzu ba wishmah dinsa ba duk da duka matsayin biyu nata ne har abada.

***Su Ammi kuwa koda suka isa bangarensu bayin bangaren sun gama yiwa komai na bangaren wani irin gyara na musamman duk da ba wani aiki me girma bane sbd komai da aka sauya na bangaren harma da tsarinsa dan haka kowannensu cikin samun nutsuwa da farin cikin kasancewa a gida suka nufi dakunansu kowace bayi bayi biyu na bayanta da akwatinanta.

Kai tsaye daki bahar ta wuce a gajiye duk da tayi bacci sosai cikin jirgi ta rage ciwon kai da damuwa sbd baccin ya taimaka mata sosai,

Tana shiga dakinta su salmah suka isa da suitcase dinta har gaban closet suka bude suka fara jera mata kayan a ciki ba tareda doguwan motsiba,

Wayarta dake hannunta ta ajiye gefen gadon dakin da already an kunna mata ac da qamshi me dadi yana tashi a hankali ta nufi bathroom.

Zare komai na jikinta tayi ta fasa sabuwar toothbrush me tsada dasuke jere a toilet din ta fara brush.

Tana gamawa wanka tayi da ruwan zafi masu zafi sosai ta gama ta fito daure da towel zuwa lokacin su naimah sun fice daga dakin harma da haske sosai an rage mata.

Shiryawa tayi sama sama ta saka riga da wando na bacci marasa nauyi tai shirin sallah tai sallan asubar da basu samu yi ba tana gamawa da adduointa miqewa tayi ta haye gado ta shige ta kwanta sbd bacci takeji sosai da mutuwan jiki.

Bacci ne ya dauketa kaman yanda kusan dukansu da kowa ya gama komai baccin ya kwanta yi hankali a kwance bayan sun daga hankalin mutane da dama a cikin masaurautar da dawowansu.

Ita kanta Ammi data dawo da damuwa da bacin rai jin tayi tana samun nutsuwa da kwanciyan hankalin bacin ranta na raguwa.

Tsit masarauta tayi dan kuwa ko fada tinda sultan na hutu ayau din na rashin fitowa sai kowa ya zama a low ba wata hayaniyar aiki. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee

144 Asim dayake bangarensa shima yaji isowan Ammin shiru yayi kawai yana sauke kansa qasa sbd yanada tabbacin Ammin da Bahar dinta ta taho wadda yake tsananin fatar Allah ya nesantasa da duk inda zai sake ganinta ya saketa a idanuwansa sbd hakanne kadai zai cire masa ita daga zuciyarsa ya rungumi danganar daya riga ya daukarwa ransa.

Leylah ma dake bangaren mahaifiyarta tinda ta dawo shiru tayi tana sauke ajiyan zuciya da jin farin cikin dawowan Ammin sbd komawa bangarenta zai rage mata damuwan datake ciki sbd irin yanda su maa sakinah da Ammin ke nuna mata kulawa da kauna duk da tanajin wani irin nauyi a kirji na ganin Bahar da zatai amma kuma zata fuskanci hakan ta hadiye kowace irin radadi da nauyin da zataji harta saba ya dallashe ta dena jinsa sbd bazata illata rayuwarta akan abinda bazata taba samuba koda tanada rabon samun a gaba to gwara yaxo mata a bazata amma a yanzu tana buqatan healing duk da batajin zata samu hakan a kusa sbd damuwa data aureta harma ta zamar mata ciwon daya kasa warkewa tinda ta dawo,

Damuwa ce tai mata yawan da batada kowace irin walwal koyaushe tana kwance a daki cikin rashin karfi da zazzabi,

Abinda yake sake shigar da zuhrah damuwa da tinani kala kala akan auren leylah din shine babu ranar da Asim din baya zuwa bangaren ganinta,

Zai shigo ya gaida mum din su gaisa a girmamawa da mutuntawa tukuna ya shiga dakin Leylah din kai tsaye acan yake zuwa su gaisa ya dubata hakama yayi yai akan kiran likita ya dubata taqi yadda sbd batason mum dinta taji tana cikin damuwa me yawa ne tafara tambayarta abinda yake faruwa tinda ta tsaya akan batada lafiya ne yasa ta dawo bangaren.

Da farko mum din ta dauka laulayi takeyi sai kuma taga kaman Asim din a cikin damuwa sosai shima saita dauke tinaninta daga kan laulayin ta shiga damuwan itama ga shuraim yana kwana biyu bai shigoba batasan sakasa wata damuwan akan wadda take ganin kaman yana ciki shima ta ayyukan sarauta shima dan haka sai bata fada masa ba tayi shiru ta nema yar uwarta Ayanah ta fada mata.

Sai yamma lis kusan kowa ya samu fitowa daga dakinsa lokacin kowa yaci ya koshi ya samu hutu iya hutu,

Su Maa ne ke palo zaune cikin hutawa maa tenya tana waya tana fadawa yarta akan ziyarar da zata kawo a boyem itama,

Ayanah ce ta fito cikin shigar doguwan rigar bahrain me kyau da tsada mara ado sosai ta qaraso ta zauna tana ajiye wayarta gefenta su salmah suka fara shigowa suna jere fresh kayan marmari da sukai sanyi a tsare.

Suna gamawa suka bar gurin daidai nan zuhrah ta shigo bayinta biyu na bayanta suka tsaya daga kofar palon farko suna komawa gurin bayin bangaren dan zaunawa acan su jirata.

Itama leylah da bayinta biyu suke biye da ita dakatawar sukai suna bin bayan bayin Mum dinta.

Suna shigowa palon Ayanah ta zubawa yar uwarta idanuwa cikeda kauna me tsanani tana jinta har cikik jininta ta miqe suka rungume juna Zuhrah ta kama hannunta tayi kissing cikeda kauna kafin itama ayanah din tai kissin tsakiyar kanta tana ambatar sunanta.

Cikeda kauna itama Sakinah dasuke jinta a zuciyarsu ta maye gurbin nurat da babu a cikinsu zuhrah ta rungumeta tana kissin tsakiyar kanta sunawa juna barka da haduwa cikin aminci.

Akan leylah Ammi ta maida idanuwanta tana kalla cikesa mamakin ramar datake gani tattare da ita da wani irin haske data qara fayau ta ware mata hannu ahankali tana cewa

'Zo Yene leylah'

Tahowa leylan tayi a natse tana jin hawaye na ciko idanuwanta sbd jin kaunar da Ammi kewa mum dinta da ita.

Rungumeta Ammi tayi a jikinta sosai da kyau cikeda kauna da kulawa tana cewa

'Insha Allah koma menene damuwan zai zama alkhairi kinji Leylah'

Gyada kai leylah tayi a natse suna zaunawa gabaki dayansu a kujera tana gaida su maa sakinah cikin girmamawa suka amsa Sakinah na mata kallan kulawa da damuwan ramar datake gani a tattare da ita Maa tenya kuwa yanayin fatar Leylah din take kalla tana shiga nazarin sauyawanta.

Zuhrah ce ta bude baki zata tambayi Bahar sai ga bahar din ta fito a natse cikin riga da wandon Flairs Purple masu fadi sosai da sukai mata kyau sosai sbd sun qara fidda haskenta sosai da sauyawan datai itama na sauyin rayuwan data samu.

Zuba mata ido Zuhrah tayi tana kallanta da dukkanin kaunar datake wa Abaas da jinin duk wani ghaz da suka rasa tana jin inama itama zata iya dawo da baya da itace zata nemo bahar ta bata dukkanin kauna da soyayyar uwa da uba data rasa.

Hannu daya ta miqawa bahar din tana ambatarta da sunayen da suke ambatar abaas dasu da yana yaro na kaunar da batada sirki.

Qarasowa bahar din takeyi itama Ammi ita ta dago tana kalla tata kaunar da soyayyar ta daban ce kaf duniya akan bahar dan haka ko data iso itama saida ta kalli Ammin cikeda kauna da kewa na fushin datake yi da ita kwana biyun kafin ta kama hannun Mum zuhrah tana zaunawa gefenta a jikinta tana bude baki ta gaidata.

Amsawa zuhrah tayi tana tambayarta karatu da uk. Amsawa tayi tana maida kallanta akan Leylah ta ambaci sunanta a natse tana gaidata.

Amsawa leylah tayi tana mata ya hanya a natsen itama tanajin ma bataji nauyin kirji da zafin datai tsammanin ji dinba dan haka ta dan sake jikinta a cikinsu tana tinanin halinda Asim yake ciki a yanzu data tabbatarda yaji isowan Bahar din a cikin masarautar.

Firar ahalin dake kaunar juna da babu matsaloli suka ringa yi hankali kwance suna ciye ciyensu wanda ya saka Ammin aje damuwarta a gefe tana jin dadin kasancewa a tareda ahalin da suka rage mata a duniya,

Ita kanta leylah jin tayi damuwarta ta rabe gefe tana samun nutsuwa da walwala dan haka basu tashi daga zaman ba saida akai magrib suka tashi sallah,

Dakin Bahar taje tayi sallah cikin karfin hali sbd tanason cusawa kanta salama, Ita kanta Bahar bata damu ba daman ba itace me matsalarba dan haka dan sake mata tayi har sukai dan firar zuwan nasu uk da dawowansu kafin suka fito cin abinci wanda sukaci dukkaninsu da iyayensu.

Sai bayan ishai Zuhrah tabar bangaren ta koma tabar leylah anan wadda tace anan zata kwana.

Dakin Bahar din still tayi zamanta wanka tayi ta fito ta zauna tafara shirin bacci sbd yanzu da wuri take bacci,

Sabbin layan bacci ta dauka a cikin closet din Bahar ta saka masu kauri riga da wando da sukai mata kyau sosai sbd bata saba saka kayan bacci riga da wando ba tafison riga kawai wadda zata sauka kokuma qarama ta bacci.

Tana kokarin miqewa daga gaban mirror kiran Asim ya shigo wayarta sbd yaje can bangaren kaman yanda ya saba bai sameta ba.

Ajiyan zuciya ta sauke tana komawa zaune a hankali ta dauki wayar ga mamakinta cikin nutsuwa yace mata yana bangaren Ammin yazo ganinta.

Bata taba dauka zai iya tahowa bangaren ba kodan mahaifiyarsa da kuma bahar dan haka miqewa tayi a sanyaye sbd tasan dole zuciyarsa na cikin wani irin mawuyacin hali na zuwansa nan din.

Bata iya saka komaiba akan kayan jikinta ba sbd damuwa hakanan ta fice daga dakin hula ce kadai a kanta wadda itama gashinta dayake sake bata rufesa ba. Palo ta fito daidai lokacinda Maa sakinah data gansa a waje tsaye tai masa iso har cikin palon cikin kulawa da kauna sbd a yanzu shi nasu ne.

Zaunawa yayi a natse yana kasa dagowa ta wuce taje ta sanarwa Ammi Asim yace yanason gaidata.

Leylah kuwa qarasowa tayi tana kallansa tareda kasa dauke idanuwanta akansa zuciyarta na wani irin harbawa ahankali da sanyi sbd tausayinsa shima dagowa yayi ya kafeta da idanuwansa masu kyau da sukai sanyi yana kallanta tareda jin confidence da karfin zuciyar iya fuskantar komai.

Fitowan Ammi ta dakatar da ita daga isa garesa sbd tasan ba qaramar quna yake ciki ba akanta ya daure ya danne ya shigo dan haka dauke idanuwanta tayi daga kansa tana saukewa qasa.

Qarasowa Ammi tayi cikin kalama da kulawa tana ambatar sunansa da sakewan data sakasa dago idanuwa ya kalleta yana jin kwarjininta har cikin idonsa dan haka ya dan sauke ido yana gaidata da mata sannu da zuwa cikin girmamawan dataji dadi tai masa sannu da kokari da kuma basa hakurin sunje bata nan.

Sama sama sbd rashin sabo duka danyi magana kafin ta miqe tabar palon.

Tana barin palon leylah zubawa hannuwansa dake rawa ahankali ido tayi yana boyewa kada kowa ya lura take idanuwanta suka sake cikowa da hawaye ta tako ta iso gabansa bata iya cewa komaiba ta kama hannunsa a hankali ta miqar dashi tajasa suka bar palon suna ficewa daga bangaren.

Hanyar bangarensa take kokarin nufa dashi ya dakatawa a hankali kafin ya cire jacket din dake saman kayansa ya saka mata sbd batada rufa a jikinta duk da dare ne.

Yana saka mata ya dauketa cak daga qasa sbd hadda takarmi ta manta bata sakoba ya nufi bangaren nasa da ita yana jin gashin jikinsa na miqewa da irin lafewan datai a jikinsa tareda saka hannuwanta biyu ta zagayesa dasu sbd irin daukan da yayi mata.

Suna barin bangaren karfe tara da rabi ta buga a lokacin Ammi ita kuma ta fito dan tafiya magana da sultan wanda ta dakatar daga zuwan dayaso yi bangarenta wanda tasan tsaf zai iya haduwa da NUAB a bangaren dan shima yanada wuya ya kwana bai taho gaidataba amma ganin har 9 ta wuce baizo ba ya sakata ficewa xuwa bangaren sultan din bada niyar karban kwana ba sam.

Tana ficewa tara da talatin da hudu manyan securities dinsa biyu da duk inda ya saka kafa a cikin masarautar suna bakin gurin suka iso kofar bangaren nata suka tsaya 9:40 a natse sukuma tukuna sai gasa ya sako kai a cikin wata lafiyayya sanyayyar nutsu da izzar ikon mulki da kamewa tareda kwarjininsa me karfin gaske yana sanye da fararen Armanis da sukai masa kyau tareda fidda kyau da samartakansa.

Aleey ne a gefensa suka iso suka shigo wanda take bayin ciki suka fice daga bangaren a natse suka bar gurin gavaki daya har saiya bar hanyar gurin ma kwata kwata.

Su Maa sun shige dukansu dan haka kai tsaye palon Ammin ya nufa bai ganta ba ya fidda wayarsa ya saka kiran Maa sakinah wadda ta fito a natse suka gaisa ta sanar dashi Ammin bata nan taje gurin sultan.

Bazata iya saka kanta a tsaka me wuya ba shiyasa ta fada gaskiyar kai tsaye sbd lokaci yayi da kowa zai fuskanci abinda yake zahirin gaskia.

Shiru yayi idanuwansa na dan fara sauyawa kirjinsa na fara nauyi zuciyarsa na fara wani irin daci da jin wata irin damuwa na lullubesa sbd da gaske Amminsa takeyi Sultan zata zaba akansa.

Kofar dakin Bahar ce ta bude a natse wanda ya saka Maa sakinah juyawa ta kalli kofar daidai nan Bahar din ta sako kai a palon sanye da kayan bacci riga da wando marasa tsayi ko kadan amma ta sako hijabi dogo har qasa yana ja sbd tinanin mijin leylah din yana nan kuma tana buqatan dauko abu a dakin maa sakinah.

Batasan dashi ba saida tayi taku biyu ta tsaya cak sbd qamshin daya ratsa hancinta ahankali ya shiga kanta har zuwa kirjinta ya bawa zuciyarta ahankali cikin wani sanyi daya saka jikinta sanyi ta dago ahankali.

Numfashi me zafi na abinda yake cin zuciyarsa ya sauke yana hadiye fushinsa tareda dago fararen idanuwansa dake kashe kowace mace akansa ya sauke akanta,

Barin gurin maa sakinah tayi tana komawa dakinta tareda masa saida safe,

Kallo daya yayi mata dukkanin abinda yake jin yana cinsa yaji yafara sauka ahankali yana narkar da zuciya da sakar da duk wata zafin dake jini da zuciyarsa.

Kasa dauke idanuwansa yayi daga kanta yana jin duniyarsa ta tsaya cak,

Lumshe idanuwansa yayi tareda sake wani numfashin da taji saukansa har cikin ranta itama ta sauke idanuwanta ahankali tanajin idanuwanta na cikowa da hawayen da batasan na mene ba. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee

145 Saukan tafin hannunsa me sanyi taji a gefen fuskarta batareda tasan ya iso gabanta ba daya sanyata dago idanuwanta ta sauke masa yaji yana sake rasa kansa dan kuwa ayau ya gama tattarda itace farin ganinsa da babu abinda yake sauke fushinsa a lokaci daya idan ba itaba.

'Finally Yar Ammi' ya furta da wani irin sautin daya saka tsigar jikinta tashi ta sauke idanuwanta qasa daga kallansa tana jin maganar datake son fada masa idan sunzo akan Ammi da zata tambayesa suna bacewa daga bakinta amma batajin zata iya barin ta kasa fadarsu sbd zata iya somewa a gaban Ammi idan ya bude bakinsa yace magana zaiyi.

Motsi bakinta ya fara wanda yakeson furta magana amma ta kasa sbd komai na jikinta daya mace.

Kallanta yakeyi batareda motsawaba kallan da bai taba yiwa kowace irin halitta shi ba ya gangara da idanuwan a bakinta dayake motsi yagane magana takeson furtawa dan haka dauke hannunsa daga fuskanta yana sake bude baki yace

'Inason koma menene bakin yakeson furtawa a karan farko'

Kama hannunta yayi zuwa dakinta wanda tayi saurin cin burki tana kallansa da sauri ta girgiza masa kai.

Oh ok' yace yana juyawa da ita suka nufi kofa suka fice.

Suna fita taga suna kokarin nufar bangarensa dan haka da sauri ta sake cin burki tana kokarin zare hannunta.

Wani kallan yasake mata kafin ya dakata a hankali yana binta da wani irin kallo sbd ya karanci tsoronta a bayyane wanda ya saka jikinsa sake mutuwa akanta.

A sanyaye ta bude baki tace

'Magana ne kadai nakeson muyi banason Ammi tasan bana nan'

Kafeta yayi da idanuwansa yana mata kallan da zuciyarta ke tabbatar mata da mutuwa yakeyi akanta hakama itama tata zuciyar kasa riqe kanta takeyi akansa da duka kallan dayake mata wanda yake kawar da duka tsoro da shakka tareda fushin datakeyi akansa tanajin ganinsa kadai na bude nutsuwan data rasa ta dauke idanuwanta daga kallan dayake mata a hankali.

Danne zuciya da feelings dinsa yayi a cikin yanayi na karfin hali sbd Su aleey da securities din dake tareda su a bayansu nesa kadan biye dasu ya dan sauke numfashi me sanyi da nutsuwa kafin ya bude baki yace

'Na fahimta you just wanna talk right? Ammi bazata taba sanin bakya nan ba sbd tana gurin Sultan'

Hannunta ya dan sake kamewa a cikin nasa din daman bai saketa ba ya jata a natse suka fara takawa zuwa bangaren nasa tana jin tsoro da nutsuwa a lokaci daya amma koma menene ta zabi magana dashi akan yayi mata alkawarin bazai taba maganar da Ammi zata iya tambayarsa ba ita shine kadai abinda take so.

Tsit hanyar take babu kowa ba motsin kowa sbd matiqar ya gifta wannan hanyar ta zuwa bangaren iyaye mata zuwa gurin Ammin babu me sake bi hanyar zaa tare farkonta da karshenta har sai ya gama ya fito koda kuwa awanni nawa zaiyi dan haka har suka taka a hankali a cikin wata nutsuwa suka bar bangaren babu kowa da komai,

Hanyar bangarensa suka nufa wadda take dauke da wani irin hasken dayafi koina a hanyar dan haka suna sako kai a hanyar aka fara kashe wutar hanyar daya bayan daya ana hana kowane haske haske kaskesu sbd aleey daya tura sakon a kashe wutar hanyar da gaggawa.

Duhu mara cutatarwa hanyar ta dauka har saida suka isa bakin main kofar shiga wadda haskenta baiyi yawan na hanyar ba dan haka miqewa masu tsaron kofar sukai suna wangale kofar kansu a qasa duka dan haka basu ma iya ganin Bahar dake tareda shi ba tayi shiru itama har lokacin hannunta yana cikin nasa suka shige.

Har kofar palo Aleey yake biye dasu suna shigewa shine ya rufe kofar tareda sauke ajiyan zuciya me sanyi kafin ya juyo ya sauko stairs ya dawo ya kalli tarin securities din baiyi doguwan magana ba yace sultan yana tareda GHAZ princess dan haka ba shiga ba fitan kowa a duniyar nan ko waye kuwa har sai tabar bangaren ko zuwa yaushe ne.

Cikin tsayuwa akan umarninsa suka gyada kai suna komawa kan aikinsu shi kuwa dakinsa ya nufa yana kashe wayarsa gabaki daya dan kada ma aikin da zai sakasa katse hutawan iyayen gidansa ya taso.

Suna shiga palon qamshinsa da sanyin aircon suka sauka akan fuskanta suna shiga hancinta da ratsa zuciyarta ta sauke kanta qasa tana kasa kallan yanayin tsarin da ayanzu yake sbd komai na duniyar bangaren ya sauya bama inda ta sani bane kwata kwata.

Kai tsaye palonsa na kurya wanda daga shi sai bedroom dinsa ya nufa da ita suna shiga taji wani yar a jikinta sbd anan ne qamshinsa yafi karfi da shiga hancinta ta zare hannunta ahankali tana zaunawa akan sofa cikin nutsuwa kafin ta dago ta kallesa yana zaunawa gefenta a natse idanuwansa a kafe kanta sbd ya kasa riqe abubuwan dayake ji a xuciyarsa na bayyarnata gabansa ayau a lokacinda bai taba tsammata ba dan xuwansu daga saka yaji sa kawai.

Zaunawansa gefenta gap da ita kafafunsu na gogan na juna ya sakata sauke kanta taji hannuwansa biyu sun kama hannunta daya ya shigar dashi cikin tafin hannunsa ya hade tafin hannuwansu ya sauke ajiyan zuciya a karo na babu adadi ya tsurawa hannuwanta ido yana kalla jikinsa na sanyi ya kasa fadan komai sbd ayau itace zata fada yana saurara.

Jin shiru ya sakata dago idanuwanta ta kalli fuskarsa ya dago ya zuba mata idanuwansa da suka sakata kokarin kasa magana ta sauke ajiyan zuciyar daya sakasa bude baki a natse yace

'Yar Ammi kina dafani da wannan shirun dahuwan da bazan moru ba so pls say something'

Ratsa maganar tayi ta lumshe ido tana kokarin zare hannunta daga nasa ya sake riqewa da kyau yana hana hannuwansu rabuwa idonsa akanta.

Kaman wanda akaiwa aike ta samu kanta da bude baki tana gaidasa gaisuwan data sakasa mutuwan zaune cikesa mamakin daya sakasa sakin hannuwanta ahankali sbd abu ne dabai taba tsammanin ji a bakinta ba ita kuwa sbd samun biyan buqatan da zata fada masa ne ya sakata gaisuwan duk da batasan ya akai tai gaisuwan ba dan haka ganin mamakinsa ya sakata kokarin juyar da fuskarta gefe wadda bai bar hakan ba ya taro fuskan da tafin hannuwansa biyu yana dawo da ita seti da tasa yana kafe ta da ido farin cikin da baisan dashi ba a rayuwansa yana mamaye kirjinsa ahankali.

Bakinsa yakai gefen fuskarta yayi kissing ahankali kafin ya bude baki yace

'Thank you da wannan gaisuwan yar Ammi, Thank you da wannan dawowan 'yar Ammi, Thank you for shigowa rayuwana 'yar Ammi, Thank you ga dandanon yanayin rayuwan da kika kawo a rayuwana yar Ammi, Yar Ammi thank you for being You...

Tashi tsigar jikinta sukai ahankali ta kasa motsawa sbd kowace kalmansa tana fitowa ne daga bakinsa direct duminta yana sauka akan fuskanta tareda wani irin qamshin mint dayake fitowa daga bakinsa yana shiga hancinta kai tsaye yana ratsa kanta da kwakwalwanta.

Goshinta yakai lips dinsa yayi kissing cikin sanyi yana saka tafukan hannuwansa cikin wuyanya yana kamowa ahankali ya matso da ita sosai gap da fuskansa numfashinsu ya hadu ta rufe ido ahankali tanaji ya bude baki ya tambayeta yaya take tsawon wannan lokacin,

Qin amsawa tayi ta sbd jin zafin zancen daya dawo mata kadan a kirji ta bude baki ahankali tace

'Ammi tasan da tafiya Birmingham, Tana fushi dani, Bazan iya ganin fushinta ba, Pls kada ka gaya mata komai akan tafiyan dan Allah......

Bakinta dayake maganar ya zubawa idanuwa cikeda wani irin shauki da mamaki sbd bai taba tunanin abinda take son fada ba kenan,

Bude ido tayi akansa tana kalla da jiran amsarsa amma shi bakin datai maganar har lokacin yake kalla yana juya maganar a kunnuwa da zuciyarsa,

Menene yake shirin faruwa akan kawai ya mallaki matar datake tasa Ammin ke shiga damuwa da fushi haka?? Ita kanta Bahar tana tinanin laifi ne kenan ko me da har zata rokesa yayi shiru?? Kaf duniya bayajin idan akwai wanda yakeda zimma da iya karfin zuciyar tambayarsa to babu amsar da bazai iya badawa ba daidai da tambayar da akai...

Ahankali bahar din ta dora tafin hannunta akan hannunsa dake riqe da wuyanta ya tallafo fuskanta ta bude baki da sauti me sanyi tace

'Plss' Cikin tsakiyar idanuwanta ya kalla da kyau ya bude baki da salon daya sakata lumshe ido batareda tasan tayi hakan ba wanda shikuma hakan ya sake taba zuciyarsa tabawa me karfi yace

'I'm sorry Yar Ammi'

Yana fadan hakan ya dora bakinsa akan nata sbd ba qaramar kewa da da wata zazzafar soyayyarta ce ke neman illata tinani da kamewansa ba.

Iska da qamshin dayake tashi a bakinsa ya fara sakar mata ta shaqa da kyau kafin ya hade bakinsu da kyau a natse yana mannewa tareda fara mata wani lafiyayyan tsotsa yana lumshe ido a cikin slow da sanyi. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee

Readers Also Read