Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 58
Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 58: Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 58. Amsawa sukai dukkaninsu cikin kulawa da kauna…
4,495 words
Amsawa sukai dukkaninsu cikin kulawa da kauna suna kallansa da sauyin dayake tattare dashi na wata sabuwar nutsuwa da kwanciyan hankalin dasuke iya hanga a tattare dashi amma ba wanda zai iya tambaya.
Kan Bahar ya dawo da kallansa a natse ya kalli cup din hannunta da abinda yake cikinsa tana sha ahankali batareda ta iya dagowa ta kallesa ba sbd batason ma Ammi taga ko kallansa tana yi.
Maa ce ta kalleta tace
'Yar Ammi bazaki gaida Sultan guda ba gashinan kinyi shiru?
Faduwa gabanta yayi ta dan dago ta kalli Maa din wadda ta kafeta da ido, Kan Ammi ta maida kallanta taga Ammin ko kallanta bataiba dan haka ta juyo da idanuwanta a hankali akansa ta kallesa shi kuwa ya kafeta dasu kaman zai janyota jikinsa.
Bude bakinta tayi cikin nutsuwa da kokarin sakewa tana hana kowace fargabanta fita ta gaidasa.
Sai a lokacin ya dauke idanuwansa daga kanta sbd yanda komai nata ke shigarsa a daki daki, Zai iya kasa riqe kansa ya kama hannunta sbd jin sautin muryanta da yanda ta gaidasa din tana kallansa da mayun idanuwanta dake warware duk wani lissafinsa.
Amsawa yayi kafin a sake cewa komai ta miqe a natse da cup dinta a hannunta tabi ta gefensa ta fice daga dakin tana bar masa wani qamshinta daya shiga hancinsa dakyau.
Wani numfashi ya hadiye yana kamewa dakyau batareda yabita da kallo ba harta fice tukuna ya dawo da nutsuwansa cikakkiya akan iyayen nasa suka fara magana.
Maa ce ta kallesa tana gyara zamanta da dukkanin nutsuwa tace
'LEUL kaje ka samu ganin mahaifinka kuwa? Duka munsan kasan baya nan tsawon wannan lokacin yana can tareda mu a uk dan haka tinda ya dawo ya kamata duk matsayin da kake dashi kaman yanda kazo ka gaida mahaifiyarka kayi mata barka da dawowa shima kaje ka samesa kayi masa gaisuwa da barka da dawowan sbd duk koma menene kowa yakeji matsayinsa na uba,sarki,Mahaifi kuma mijin mahaifiya ya wuce komai'
Shiru Ammi tayi sbd yanda zuciyarta ke harbawa da yanda komai zai bayyana NUAB ya fahimta,
Shi kuwa shiru yayi yana sauraran Maa din, Tinda ya dawo sun hadu so daya dayaje ya samesa da kansa suka gaisa amma bayan nan basu sake haduwa ba sbd bayajin akwai abinda zasu iya zaunawa su fuskanci juna su tattauna a tsakaninsu.
Numfashi ya sauke me sanyi da nutsuwa kafin ya dago ya zubawa Ammi idanuwansa sbd duka wannan maganganun yasan abinda takeso aka isar mata a gurinsa, Itace take son ya samu Sultan su daidaita sbd zuciyarta na son hakan, Zuciyarta bazata iya fifita son datake masa akan na sultan ba shiyasa take masa hakan har itace ayau take kasa masa magana sedai ta saka ai masa magana duka akan sultan.
Dawo da kallansa yayi akan Maa ya bude baki baki a natse yace
'Insha Allah Maa'
Yana fadar hakan sallama yayi musu ya miqe ya fice batareda ya cewa Ammin komaiba sbd koyaushe akan sultan sosa zuciyarsa takeyi tareda danne matsayinsa na 'danta dayake yaqi da jin zafin sultan akanta amma sai tana mantawa da hakan tana zabar sultan kuma tana boye masa tana daukansa da masa kallan wanda yake tsakiyarta da farin cikinta na son rayuwa da mutumin da 'yanci wannan ya kasa bata yana matsayin sultan wanda yake kam mulki sama da shekara talatin.
Yana fitowa Aleey kallo daya yayi masa yasan zuciyarsa ba dadi dan haka babu doguwar magana suka wuce Fada dake cike ana jiransa ayau akwai taro da zaman fadar.
Koda suka isa fadar tsit koina yayi sbd shigowansa da aka sanar.
Yana shigowa kowa kansa yayi qasa niimar gurin na gauraya a natse da qamshinsa da zuwa yanzu duk wanda yake shiga fada dashi yasan qamshinsa hakama zazzafan kwarjininsa ya gauraye gurin.
Koda ya isa kan karagar mulkin boyem din tini Aleey ya isa ya tsaye a gerenta daman keelah na tsaye daga bayanta cikin jikinsa babu kalar makamin da babu a soke boye.
Yana zaunawa daga waje securities masu karfi suka dakatar da kowace irin kaida kawo a hanyar fadar ba shiga ba fita saiya fito kuma kowa zai samu yancinsa.
Kusan wuni yayi a fadar bai samu kansa ba sai kusan yamma dan haka yana fitowa daga fada kai tsaye aika sakon zuwansa akai gurin sultan yasar wanda yayi mamakin jin zuwan nasa duk da Ayanah ta sanar masa a waya cewan Maa dinsa sakinah tayi masa magana amma kuma shima daman yana buqatar ganin nasa dan haka koma menene zuwan na NUAB din zai kawo yana shirye dashi dan kuwa lokaci yayi dazaisan uwarsa ta auru.
Shi kansa NUAB din ayau yana son fuskantar sultan ne a karo na karshe insha Allah akan mahaifiyarsa wadda a yanzu baida ikonta yana son yayi masa iyaka da ita sbd kaucewa abinda babu a addini hakama a karan karshe zai sanar masa da zai bar boyem da ita bazata taba dawowaba da zama.
Wannan tabbatacciyar magana ce da zai tabbatar masa sbd shine me cikakken ikon mahaifiyarsa ayanzu idanma sultan din ya manta zai tinatar dashi hakan a tsanake sbd yasan ya rasa damarsa har abada.
Saida yayi wanka ya huta bayan sallan magrib ya nufi bangaren mahaifinsa wanda yake zaune a natse shima yana jiransa da sadakin mahaifiyarsa daya ajemasa yana jiran ranar basa.
Koda Sultan me mulkin boyem LEUL NUAB ya iso bangaren sultan me murabus yasar kadir yana tsaye bakin kofa yana jiran isowansa cikin nutsuwa da Girmamawa.
Aleey ne da keelah a tareda shi sbd ziyarar bata buqatan hayaniyar tsaro tinda gurin mahaifinsa ne yazo.
Kadir ne yayi masa rakiya da iso har palon da sultan yake hutawan yana zaune yayi fresh dashi hutu da kwanciyan hankalin da duk yake nema a rayuwa yanzu ya samu duniya tasan ya mallaki Ayanah ghaz halak malak kadai ya rage wanda shi baya buqatan hakan idan 'danta kawai ya sani ma ya ishesa duk da idan har danta ya amince ya karbi aurensu to dole duniya zata sheda ta sani sbd tsaftata alaqar.
Dagowa yayi yana zaune kafarsa daya akan daya yana duba abu a waya fresh fruits a table din gabansa kallan Fuskan NUAB yayi wanda shima huta da kwanciyan hankali da wani azababben iko da izza ke bayyana tattare dashi na zafin mulki ta uba data uwa da kuma na empire din kansa daya kafa.
Aura ce ta cike gurin ta uba data 'da dake nuna zallan iko da izza dan haka ficewa kadir yayi a hankali a natse yabarsu su kadai.
A 1 seater din dake facin sultan yasar NUAB yake zaune ya dago cikin nutsuwa ya kalli mahaifinsa bai ji komaiba na damuwa ko wani yanayin a natse ya bude baki ya gaidasa yana kallan abubuwan da sultan din zaiji daga bakinsa.
A natse sultan ya amsa yana qarawa da masa kirarin sarauta a natse dan bude filin da abinda zai gabatar masa.
NUAB dayake sauraransa numfashi ya sauke yana dagowa ya kallesa cikin isar iko da izza zai fara magana sultan ya miqa hannunsa gefensa ya dauko silallan zinarin dake gefensa ya ajiye a gaban NUAB din da suke dauke da sunan Ayanah ghaz baro baro a jiki. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee
152 Yana ajiye wa bayansa ya mayar a natse ya jinginar a kujeran dayake zaune har lokacin kafarsa daya na akan daya ya zubawa NUAB idanuwansa wanda shima a natse ya dago idanuwansa masu kyau ya kalli sultan din kafin ya maidasu a natse akan abinda ya ajiye masa a gabansa ya zuba musu ido yana kalla.
Shiru sukai dukansu idon kowannensu na kafe akan abinda yake gaban nasu suna kalla,
Sultan jiran tambayar NUAB yakeyi duk da yasan bazai taba tambayarba koda zasu shekara a hakan koda kuwa menene bazai taba bude baki ya tambaya dinba sedai shi daya ajiye koma meye ya fada da kansa idan ba hakan ba zai gaba abinda ya kawosa ya miqe ya ficewansa.
Dan haka ajiyan zuciya mara sauti sultan ya sauke yana maida kallansa kan fuskan NUAB wanda ya dago shima yana kallansa ya bude baki yana kai hannunsa daya a natse ya tura silallan gaban NUAB din yace,
'Ina gabatar maka da sadakin mahaifiyarka Ayanah ghaz me girma Sultan LEUL boyem wanda aka daura auren sha ashirin ga watan daya gabata, A yanzu ba kaine kake da cikakkiyar iko akanta ba nine mijinta,nine mahaifinka,nine Sultan dinka'
Kallansa NUAB ya dago yanayi da dukkanin idanuwansa yana jin maganarsa na sauka kaman baisan meyake fada ba sbd yasan zai iya fadan komai akan ya mallaki Ammin dan haka a natse ya maida idanuwansa akan zinarin gabansa yana kallan sunan Ammin dayake bayyana baro baro akai ya kalla tsawon mintina kafin ya dago da idanuwan ya sake saukewa sultan yana jin zuciyarsa na fara daukan zafin daya manta rabon da zuciyarsa ta dauka,
Bude baki yayi a natse yana kallan sultan din yace
'Ammin tasan da maganar dake gudana nan din maana tasan da aure a kanta??
Sake gyara jinginar zamansa sultan yayi yana sake murmushi me kyau da nutsuwa yana kallan NUAB din yace
'Kaine da baka saniba nake sanar dakai a yanzu sbd ka sani din Sultan dan Amarya'
Numfashi me dumin daya fara zafi NUAB ya sake kalmar na zafafar zuciyarsa ta tafaso sa ya sake kallan sultan da kyau yace
'Aure irin wanda kayi mata a baya na bata matsayin wishmah ka sake bata sbd bansan Ammina zata iya aure batareda sanina ba ko izinin dan kuwa a duniyarta kaf yanxu ni kadai ne waliyin aurenta da bada aurenta'
Ajiyan zuciya me sanyi da nutsuwa sultan ya sauke yana kallan NUAB din yace
'Aure ne mukai wanda kana buqatar nutsuwa ka fahimta hakan, Ba raayinka ni nake nema ba,ba kuma izininka nake nema sbd mune muka haifeka bawai kaine ka haifemu ba, Aure ne kaman kowane aure da akeyi me daraja da baa buqatan dogon bayani, Amminka tana jin shakkar yanda zaka dauki lamarin ne ya saka aka ja lokaci batareda ka saniba ba amma tinda yanzu ka sani ka sani mahaifiyarka tayi tinanin abinda zaka dauka kafin ta amincewa auren dan haka a yanxu daka sani saka albarkanka kawai take buqata ba bacin rai da fushi ba.'
Yana gama fadan hakan miqewa zaiyi NUAB ya kallesa idanuwansa jajir zuciyarsa na wata irin tafasa da bacin rai me tsananin gaske da fushin dayake taso masa yace
'Kanada raayin hakan meyasa bakaiba tin a shekarun baya datake tsananin buqatan hakan? Meyasa baka yantata ba a lokacinda hakan yakeda amfani? Meyasa sai ayanzu? Sbd ka kaine me juya rayuwanta a yanda kaso a lokacin da kaso sbd ita ba kowa bace face baiwar da aka saka kudi aka siya?
Yankar zuciyar sultan maganganun sukai ya dago idanuwansa shima da sukai ja ya kalli NUAB din cikin jin zafin maganar yace
'Eh sbd nine me juyata a yanda naso da kuma bata matsayin da duk nakeso sbd nine na siyota ba kaiba,nine me ita da cikakken iko da ita a kaf rayuwarta ba kowa ba,a yanzu danaga lokacin auren yayi shima gashinan na aure ta auren da ba wanda yakesa ikon sakawa ko hanawa idan ba ni dinba.'
Gama maganarsa yayi daidai da shigowan ayanah din wadda ta kasa nutsuwa da haduwan tasu saida ta iso dan haka kallan NUAB takeyi da idanuwanta da suka sauya sbd fargaban abinda zai iya biyowa baya,
Juyowa NUAB yayi ya kalleta da idanuwansa dake tsananta ja maganganun sultan sun gama buga xuciya da jininsa dan kuwa ko ayanzu ya fada masa uwarsa ba kowa bace face baiwarsa da zaiyi dik yanda yaga dama da rayuwarta,
Wani irin kallo yakewa Ammin yana jin ta gama rusa duk wani karfin zuciya da kuzarinsa ya bude baki yace
'Ammi kina ji da kunnenki ke din ba kowa bace face baiwar da aka saka kudi aka siya, A hakan kika kuma zabarsa akan duka radadi da baqin cikin dana rayu a cikinsa sbd ke'
Rintse idanuwa Ammin tayi tana isowa gurinsa zata kamasa ya miqe tsaye yana kallan sultan wanda ransa yayi mummunan baci yace
'Ban karbi auren ba sbd nine me bada auren dan haka......
Wata irin tsawar da tinda sultan yake babu wanda ya taba yiwa ita ya sakarwa NUAB din wadda dakin gabaki daya saida ya amsa take Ammi ta shiga tashin hankali tana kallan sultan din kafin ta kalli NUAB wanda jikinsa ke wata irin rawa sosai idanuwansa jajir fuskarsa tayi ja.
Su kadir dasu aleey harma da maa sakinah data taho tareda ayanah a kunnuwansu tsawar me karfin gaske ta sauka wadda ta saka kowannensu qasa da kai jiki na sanyi da wata irin fargaba da damuwa batareda sun motsaba gurin ya sake daukan tsit.
'Zaka dena fadamun duk maganar dataxo bakinka kowane matsayi kake dashi kuwa daga yau sbd duk abinda kakeji kake taqama dashi nine na bakashi sbd nine na haifeka, Nina na baka sunan dakake amsawa yau, Nine na na baka jinin iko da mulki da izzar da duk kake ji a kanka da jininka, Nine na baka kariyar da kake taqamar ka rayu ayau, Nine na hana kaina duk kwanciyan hankali da farin cikin da duka mulki yake bayarwa nai watsi da girma da iko na na fixgeka daga hadarin dayake tattare da rayuwarka na baka dalilin daka zama jarumin dayake tsaye a gabana yanzu, Nine na bawa mahaifiyar taka kariyar data rayu a cikin cikakkiyar kwanciyan hankalin da kake ganinta a gabanka a yau, Nine wanda ya tsaya ya tsayu akanka na baka kariyar da bazaka taba zama abinda ka zama abinda ka zama ba a qasar da ba taka batareda na taba baka dalilin rauni ba, Ni ba ubanka ne kadai ba daya kawoka duniya ni saviour dinka ne, Ni sultan dinka ne,ni ubangidan mahaifiyarka ne sannan ni ayanzu mijin mahaifiyarka daga karshe ni masoyinta ne da 'dan da muka haifa bai isa ya saka sharadi a gabanmu dan haka ka aje matsayinka na sulta a komai nine ubanka da you must learn how to talk and respect me to the core...'
Da wani irin zafin gaske ya qarasa maganar wadda take fita da karfin gaske cikin bacin ran da babu wanda ya taba gani wanda ya saka Ayanaah kallan NUAB wanda shima rawa jikinsa yake sosai har lokacin jan idanuwansa kaman zasu kama da wuta sbd ayau ya tabbatarda idan aka haifeka angama shan gabanka duk kuwa abinda kake ji dashi ko kake dashi dan kuwa abinda yake ji yafi wuta ci a jininsa amma baida yanda zaiyi bayan tsayawa yana sauraran gorin da ubansa ke masa shida uwarsa bama tareda ita tasan hakan ba.
Dago idanuwansa yayi ya kalli sultan din wanda ko kallansu ya dena sbd tafasar da zuciyarsa ke yi shima ya gaji da zafi da fushin NUAB dayake tolerating tin yana yaro wanda yana masa uzuri ne sbd yasan zafin son dayake wa Amminsa dashine ya saka ya tashi da jin zafin rashin ganinsu a tare amma sam ya kasa gane cewa son dayake masa ne yake sakasa jin tsananin zafinsa daya kasa zabarsu da Amminsa akan kowa bayan shi kuwa yafisa jin zafin ciresu da yayi daga jikinsa sbd basu kariyar da ayanzu suke tsaye tareda juna.
Magana NUAB din zaiyi shima cikin kololuwan quntata da maganganun Amminsa ta katsesa da tsawa me karfin gaske itama tana riqosa cikin damuwa da rasa abin yi tace
'NUAB mahaifinka ne kome kake ji zaka hadiyesa ayanzu batareda ka bayyanaba sbd tinda ya haifeka ya gama maka komai, Kome laifinsa a gurina ni na yafe masa sbd nasan dalilinsa daga baya na hakan hakama ko babu dalili tinda zamansa nakeyi dole zan fuskanci damuwa da baqin ciki na zamantakewa wanda gashi a yanzu ya wuce, Ka aje komai ka bar komai ka bari zuciyarka datake tsananin sonsa ta karbesa, Ka aje fushinka ka fuskanci matsayinsa daya wuce komai da kowa... Ayau ina fada maka ka dauka umarni ne ko shawara ko baki koma menene ayau ina fada maka ka ajiye duk abinda kakeji bazaka sake disrespecting nasa ba zaka girmamasa zaka bari zuciyarka ta karbesa matiqar kanason naci gaba da rayuwa a matsayin mahaifiyarka........
Da wani irin slow me mugun zafi da wani duhu da wuta dayake ganin suna ci a idanuwansa da kirjinsa ya juyo yana kallanta fuskarsa na qarasa komawa jajir ba kyan gani yana kasa motsawa bakinsa na mutuwa daga furta kowace irin kalma.
Shi kansa sultan din dago jajayen idanuwansa yayi ya kalli Ayanah din wadda idanuwanta sukai jajir wasu hawaye masu tsananin radadin kalman data fada suna gangarowa daga idanuwanta sbd tasan ayau NUAB zai shiga mafi qunci da radadin zuciyar dabai taba shiga ba jin hakan daga bakinta.
Wani irin sanyi dukkanin jikinsa yafara a hankali sbd ayau ya samu kalman datai breaking zuciyarsa kacakaca a take batareda qara kowane second ba. #MAMUH 09033181070
HAYATEEM Mamuhgee
153 Hawayen fuskarta dake gudun sosai ya saka sultan takowa gabanta har lokacin zuciyarsa daci take masa sosai sbd ganin yanayi halinda suke ciki a tsakaninsu da babu wata kauna ko soyayyar data wuce tsakaninsu dan kuwa sune haske idaniya da ruhinsa da ayau yake tsaye sbd soyayyarsu daya riqe ya hana kansa sakewa ga kowane irin challenge har suka kawo inda suke yanxu amma gashi suna tsaye cikin jin zafin juna maimakon kaunar dayake fatar su rayu a cikinta.
Rintse idanuwansa da har wani radadi sukeyi NUAB yayi jijiyoyin hannuwansa dana kansa duk sun fito.
Bai iya cewa komaiba ya juya a hankali yabar palon idanunsa na fidda wata zafi,
Binsa Ammi tayi da kallo hawayenta na sake gangarowa tana daga kafa kaman zata bisa ta rungumosa Sultan ya saka hannuwansa biyu ya riqota yana rungumeta a natse sbd a yanzu NUAB din na buqatan space sbd ayau yaji abubuwan da zuciyarsa zata jima tana tafasa bata saukoba kafin ya fahimci gaskiyar da suke kokarin fada masa ya dawo daidai dan kuwa shi kansa yasan kaman yanda yake tsananin kaunar dansa haka NUAB yake kaunarsa kawai zafi ne na rabuwa dasu daya kasa cirewa aransa tin yarintar.
Kuka Ammin keyi a hankali a jikin sultan din tana jin kaman kalamanta sunyiwa NUAB din tsauri.
Zaunar da ita sultan yayi ransa ba dadi shima ya rungumeta yana kasa cewa komai dan haka sukai shiru dukansu.
Shi kuwa yana sako kai kofar Aleey ne ya fara ganinsa fuskansa kawai ya fara kalla bai iya qarasa kallan idanuwansa ba yayi gefe yana buda masa hanya idanuwansa na sauya take sbd ganin halinda ubangidansa yake ciki wanda kusan hayaniya sosai suka jiyo daga ciki a tsakaninsa da iyayensa wanda ba dan adam dayake da daman shiga dan haka duke a tsuru suna jiran iyayen gidansu dukansu.
Wata irin aura ce ta zafinsa kawai ta bugi dukkaninsu dake kofar take kowa yayi qasa da kansa fadawa ma dake hanyar ficewa bangaren zubewa qasa sukai da sauri kansu a qasa sbd tamkar guguwan wuta haka suka ga tahowan tasa cikin wata zafi da zafaffen izzar mulki.
Aleey da keelah ne suka bi bayansa babu wanda idanuwansa basu sauya ba a cikinsu musamman aleey shi keelah kuwa a lokacin ya samu damar wani me laifin akansa abinda suke ji din zai sauka.
Kai tsaye bangarensa suka nufa wanda suna tinkarowa tin daga nesa kowa ya miqe suna shiga wata irin nutsuwa sbd a tafe suna iya hango yanayin ba daidaiba.
Koda ya iso an wangale masa kofa hatta kofar shigewa palo an an bude masa dan haka yana isowa shigewa kawai yayi aleey ya rufe kofar yana juyowa ya bada umarnin ba shiga ga kowa kaman yanda aka saba duk da daman babu me zuwa bangaren bayan masu aikin da suna gamawa suke barin bangaren.
Yana shiga kai tsaye palonsa ya wuce na qurya shima yana isa kokarin daidaita kansa yayi da zuciyarsa ya nufi inda zaiyi sallah ya tada sallar ishai da aka aka fara yabi jam'i daga nan batareda ya iya tafiya masallacinba dan gabaki daya fuskansa ba kyan gani,
Ana idar da sallar jin yayi numfashinsa na sarkewa yana kasa fita daidai hakama wani irin zufan gaske yake fitarwa idanuwansa har wani rufewa sukeyi yarintarsa da duk abinda ya taso a cikinsa yana dawo masa da tinanin da radadin da kaunar dayake wa mahaifinsa me karfi da kishinsa dayake tada duka wani fushinsa,
Miqewa yayi bedroom dinsa ya nufa bai tsaya komaiba tin daga kofar bedroom din yafara bude botiran gaban rigarsa ya zare ya jefar yana zare komai daya baya daya kai tsaye ya nufi glass door din dake dakin ya budeta gabaki har qarshe yana saka kafarsa batareda komai a jikinsa ba bayan tight CalvinK short underwear dake jikinsa fara qal ya isa bakin lafiyayyan pool din dake gurin ruwan ciki na daukan ido yasaka kafa yana shigewa ciki ahankali harya gama shigewa gabaki daya ya rintse ido sanyin ruwan na ratsasa tsananin zafin jikinsa da jininsa ka neman fara karbuwa su daidaita.
****Ammi da Sultan kusan babu wanda ya iya cewa komai a yanayin da suke ciki har ya fice sallan ishai bai iya cewa komaiba bayan ce mata da yayi kada ta damu NUAB din zai sauko daidai babu yanda zaiyi bayan ya gama bacin rai da fushi kuma dole ya bisu hakama daga yau aurensu dasu sun samu cikakkiyar yanci da duniya zata san da sun zama maaurata kuma masu tsananin son juna duk wanda zai mutu ma ya dade bai kwanta ya mutu ba.
Yana ficewa itama barin bangaren tayi ta fito Maa sakinah data kasa tsayawa sbd tension din yayi yawa na abinda yake faruwa a ciki ya sakata komawa tabar bayi biyu suna jiran fitowan tata palo ta zauna tinda ta dawo tayi shiru cikin tsananin damuwan NUAB da itama takeson ya hakura ya aje komai yabi mahaifinsa wanda a yanxu duniya tafara sanin sirrinsa dake boye a ransa cewan babu wanda yakeso fiyeda ransa a cikin yayansa da duniyarsa kaman NUAB din.
Maa tenya ma datasan suna can din hankalinta bai kwanta ba saida sakinah ta dawo kallo daya tayi mata ta fahimci komai ya dauki zafi dan haka itama zaunawa tayi palon tana dan kallan tv sama sama.
Ammi na shigowa yanayinta kadai suka kalla jikinsu yayi sanyi sbd idanuwanta da sukai jajir zuciyarta cikeda daci.
Kallansu tayi tana sauke numfashi me zafi ta qaraso ta zauna tana dafe kanta a hankali tareda sake sauke numfashi ta dago tace
'NUAB ya kasa fahimtar abinda nakeson ya gane,ya kasa fahimtar abinda mahaifinsa yake son ya gane Bansan tayaya zan fahimtar dashi batareda ya dauka ina zabar bangare bane, A tsakaninsa da sultan ba maganar na zaba bane maganar ya fahimta ya yadda a yanzu aure mukeyi ba zaman baiwa da ubangidanta ba, Ayau ya saka na fada masa abinda bansan ya akai bakina ya furta ba.'
Shiru sukai suna sauraranta damuwan sakinah na bayyana ta bude baki tace
'Kada ku ga laifinsa duka sbd duk abinda yakeji yake ciki an dasa masa shine tin yana yaronsa dan hakane ab8j ya tsaya a ransa hakama auren da kukai kun boye masa musamman ke dayake ganin komai yana yinsa ne sbd farin cikinki da baki kariya, A qalla kafin auren ya kamata ku zauna dashi kuyi sharawa tinda shine waliyin dakike dashi amma tinda duka baayi hakan ba yanzu daukan zafi duka ba shine mafita ba hakuri zaayi a basa lokaci ya fuskanci komai da kansa.'
Shiru sukai dukansu tenya ta amsa zancen da itama fara jero tarihin irin yanda yayi rayuwa tin tashinsa a cikin ganin shi din da uwarsa ba kowa bane face abin takawa a wulaqanta a banza a masarautar karkashin mulkin mahaifinsa wanda shine ya fito ya nunawa duniya din su ba kow bane face mistress dinsa daya gama amfanuwa da ita da 'danta da kuma yanda aka rabasa da uwa da qasarsa aka kaisa qasar da baida kowa baida komai aka jefar dashi tinda qananun shekarun har girmansa ba wanda ya taba nemansa tayaya ake tunanin zuciyarsa zata sake wannan zafin duka a lokaci daya?dole sai ahankali insha Allah zai sake komai.
Hawaye sosai Ammi take gangarowa da jin irin yanda tenya ke jero quncin da suka rayu a cikinsa a cikin masarautar wanda NUAB ya taso a cikinsa ya kangarar masa da zuciya,
Komai dawo mata yayi ta rintse idanuwanta tana jin zafin abinda tayiwa NUAB din sosai kirjinta na nauyi.
Maa sakinah ma nauyin kirjinta yayi ta kasa cewa komai idanuwanta jajir kaman yanda na tenya din sukai sbd sune kadai sukasan radadi da zafin quncin da suka rayu a wancan lokacin a cikin masarautar data zamar musu tamkar maqabarta sbd qunci da baqin ciki tareda kadaici da damuwa.
Bahar datake tsaye duk abinda suke fada da faruwa a kunnenta nauyi kirjinta yayi idanuwanta suka ciko da hawaye tana kasa motsawa musamman ganin hawayen Ammin da kuma yanda ake fadar rayuwar da sukai wadda itace ta busar ta kangarar da zuciyar NUAB wanda ya taso ba soyayya da kulawan kowa ya rayu shi kadai sai soyayyar uwarsa da bata hayyacinta bata san ta kaunacesa ba a lokacin.
Kasa tsayuwa tayi jikinta na tsananin mutuwa da wani irin sanyi zata bar gurin Ammi tafara fadar abinda ta gaya masa ayau din wanda take jin nadamar fada masa hakan duk da tayi hakan ne sbd sakasa ajiye komai ya shirya d mahaifinsa.
Shiru suka sake ba wanda ya iya cewa komai sbd bama me daman tinkarar NUAB din yanzu dole saiya nemesu da kansa zasu iya samun damar magana dashi su dan taushesa.
Bahar data sake yin sanyi dakinta ta koma ta zauna a kan sofa tana kasa motsawa zuciyarta cikeda tinani.
Leylah dake kwance shiru itama tana fama da kanta zuba mata ido ganin yanayinta kafin ta rufe idanuwanta bacci ya dauketa.
Ita kuwa kasa motsawa tayi daga inda take din zaune har tsawon lokaci abubuwa da yawa na yawo cikin kanta cikeda damuwa da mutuwan jiki sbd bayan damuwan da Ammi ke ciki akansa harda fushi da bacin rai me girma tana ciki kan NUAB din wanda shima a daidai wannan lokacin tasan yana cikin matsanancin halin da baya buqatan kowa amma kuma tasan dole wani yana buqatan kasancewa dashi.
Sallar ishai da akai tin dazu ta tashi jiki a mace tayi tana idarwa tai shirin bacci har lokacin jikinta a matiqar sanyaye tana jin rashin nutsuwa.
Zaunawa tayi bakin gadonta tareda dago idanuwanta ta kalli agogon gefen gadonta taga karfe goma har tayi.
Numfashi ta sauke a sanyaye a natse kafin ta miqe tana rasa nutsuwanta kwata kwata ta dauki hijabi har qasa ta saka tana daukan wayarta ta fice daga dakin.
Ko data fito palo babu kowa koina yayi tsit alaman kowa ya shige sbd yanayin da ake ciki na damuwa.
Kofar ficewa take nufa daidai zata saka hannu ta bude kofar aka kirata a natse Tsayawa tayi cak cikin faduwan gaba me karfi daya sake sanyaya jikinta.
Juyowa tayi daidai Maa sakinah na isowa gabanta dauke da tray me kyau dayake dauke da white and gold tea set masu daukan ido sabbi dal na amfanin LEUL din ta miqa mata sbd daman dakinta zata kai takai masa sai gata ta gani tasan kuma can din zata.