Kenza eBookz

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 57

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 57

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 57: Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 57. Bata gansa a dakin ba ta isa har bakin…

4,500 words

Bata gansa a dakin ba ta isa har bakin gadonsa ta duba baya kai dan haka ta dan saurara sai taji alaman yana bathroom dan haka babbar glass door dake baya dakin me matsayin window ta nufa ta saka kafarta a natse ta fita ta tsaya a bakin lafiyayyan pool dinsa dake bakin kofar me kyau da tsantsar tsafta da tsari wanda kana sako kafarka wajen yake gurin babu ma wanda yake taba shiga gurin idan ba masu gyarasa ba ruwan sai daukan ido sukeyi kaman glass.

Sanyi gurin yakeda shi sosai sbd ruwan pool din dan haka wata sanyi taji tana ratsata duk da kayan jikinta riga da wando ne sunada kauri hakama da babbar abaya har qasa a jikinta data sako dan zata fito kawo leylah waje.

Shiru tayi tana kallan ruwan a tsaye taja jiran fitowansa dan kada ta koma palo jiransa baisan da itama ta dade tayi dare sosai hakama bazata iya tsayawa dakinba ya fito wanke ta gansa a yanayin da zai fito ba dan hakane ta zabi tsayawa a gurin tana bawa cikin dakin baya.

****Leylah kai tsaye bangaren Asim din suka nufa wanda suna isa ba bata lokaci likitan daya kira yaxo dan tin kafin ya tafi kiranta ya kirawo likitan bai aikasa can ba sbd bazai iya sakewa ba acan din dan haka yace yaxo nan ya samesu shi kuma ya daukota idan angama dubata din ta koma.

Koda suka dawo kirjinsa wani irin nauyi yayi masa sbd ganin da yayiwa Bahar wadda se yau ya ganta bayan lokaci me tsayin da yayi dana sanin ganin nata sbd zuciya da batada qashi akan abinda take so.

Yanda jikinsa yayi tsananin sanyi sosai ya saka zazzabin leylah jin ya dauke mata itama jikin nata yayi mugun sanyi haka likita ya dubata dayake mace ce likitar sai ya fice ya basu guri ta gama dubata.

Kallan Leylah tayi bayan ta mata harda pt test da bin pulse nata da kyau ta tabbatarda ciki ne a jikinta ajiyan zuciya tayi cikin tayata murna a natse ta sanar da ita ciki ne a jikinta amma bata san tsawon kwanaki ko satika ko watanninsa ba sai sunyi scanning zasu tabbatar da hakan.

Kafeta da idanuwa leylah tayi tana kallanta cikeda ficewa hayyaci sbd kalman ba qaramin dukanta tayiba.

Saida likitar ta sake maimaita zancen tana dan dafata tukuna ta sauke idanuwanta ahankali tana sauke numfashi me zafi jikinta na matiqar mutuwa da wani irin sanyi sbd jin abinda batasan murna zatai ba ko shiga tashin hankali sbd tashin farko batasan ma tayaya abinda yake cikinta zai samu karbuwa ko isa ga kunnuwan wanda yake ubansa ba amma zuciyarsa bazata taba sonsu ba sbd tana maqale da son wata so mai karfin da batason zamo masa kaman dole a rayuwansa bare abinda yake cikinta.

Numfashi ta sake saukewa tana sake jin shakka da tashin hankali na rufeta sbd a sanin datai Asim kokarin barin boyem yakeyi kwata kwata gabaki daya ya tafi inda zai fara sabuwar rayuwa Baice zaije da ita ba bai tashi daga kan maganar rabuwan da suka yanke zasuyi da juna ba wandaba ta kasa gane me suka tsaya jira haryanxu duk da tafi saka ran sai zai tafi ne zai sauwake mata yanxu kuma ga ciki a jikinta,

Idan ta sanar masa zai tausaya mata ya duba cikin ya zauna da ita sbd haihuwa wanda har abada batajin zata iya zama dashi akan cikin jikinta, Batajin zata iya cigaba da auren indai har akan cikinta zai mata hakan Zata zabi rabuwan matiqar cikin dake tsakaninsu ne zai zama abinda zasuyi zaman auren sbd dashi.

Cikowa idanuwanta sukai da hawaye masu yawa da zafin gaske ta dago ta kalli likitan ta bude baki cikin sanyi tace duk tsanani kada ta fadawa kowa ciki ne a jikinta. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee

149 Da mamaki me tsananin gaske dr ta dago ta kalli leyalan zatai magana leylan ta tareta tareda sake roqonta tana kallanta da idanuwanta da sukai jajir tana ji a ranta zata bari kafin tafiyarsa idan har ya rabu da ita din zata sanar masa da cikin bayan ya yanke hukuncinsa na karshe akan aurensu kenan sbd batason cikin ya shiga kowace maganar tasu.

Fitowa dr tayi Allah yasa bata hadu da Asim din ba yana dakinsa yana jin kansa yayi nauyi sake tsanar zaman boyem yayi yana jin kaman yabarta a yau din kwata kwata har abada iyakacinsa da iyayensa a waya sedai kuma idan sun kai masa ziyara a duk inda zaije ya gina rayuwarsa.

Aiki yake nema batareda saka matsayinsa ko asalinsa ko matsayin mahaifinsa a gaba ba dan bayason yayi rayuwar dazai akan kowace irin alfarma a yanxu dan haka a duk qasar daya fara samun aikin a cikin qasashen daya saka akai masa komai ta hanyar mutanensa na arziki acan zai tattara ya koma yayi rayuwansa.

Text dr tayi masa akan ta wuce ta gama duba leylan ta bata magani.

Duba sakon yayi ya ajiye wayarsa ya kasa fitowa sbd bazai iya kallan leylah a halinda yake ciki ba dan bazataji dadin ganinsa ba a hakan hakama tamkar cin fuska ne a gareta dan kuwa tasan akan bahar ne ya shiga wani halin dan haka bai fitoba zaunawa yayi saida yai kokarin daidaita kansa ya wanke fuska ya sauka kaya ya fito a natse yana hana kowane irin yanayin dayake ciki bayyana ya nufi dakinta.

Koda ya isa tana zaune itama ta lallaba ta wanko fuskanta ta dawo ta zauna idanuwanta jajir dan zuwa yanzu ta rasa mema take ciki a rayuwa, Shawara da abokin shawaran da zata fiddawa damuwanta da rashin sanin matsayinta take nema ko zata samu sassauci kada damuwa da baqin ciki su kasheta ita kadai baasan meya kasheta ba.

Yana shigowa ita yake kallo cikeda kulawa harma da kauna ya qaraso har gefenta ya zauna a natse yana saka hannunsa a hankali ya dora akan nata da bata motsaba bata kuma dagoba ta kallesa sbd damuwanta zuwa yanzu tafara mata yawan datake neman amayarwa.

******* Ahankali taji hannuwa cikin hijabinta suna ratsawa suna zagayota cikin nutsuwa da slow zuwa cikinta dayake a shafe kafin ya hade bayanta da kirjinsa ya rungumota da kyau yana sauke ajiyan zuciya.

Bata motsaba sedai idanuwanta data rufe ahankali tana jin wani irin sanyin gurin na sake ratsata.

Ta cikin hijabin nata ya sake zagayeta yana qanqameta jikinsa a hankali zuciyarsa na samun nutsuwan daya kasa samu ayau din sbd ayyukan da suka shiga gabansa sosai.

Janyewa taso yi sbd jin yanda jikinsa ke mutuwa a nata amma ya sake qanqameta jikinsa yana shige mata sosai.

Shiru sukai a hakan tsawon mintina kaman hudu kafin ya daga hijabinta yana shigewa sbd sanyin dayake ratsasa dan daga shi sai towel.

Jinsa cikin hijabinta ya sakata sauke numfashi mara karfi tana jinsa yana qanqameta a ciki tareda saka hannuwansa cikin rigarta ta qasa ya zagaye cikinta ya sake rungumeta ta baya sbd dumin dayake cikin fatarta ya ratsi hannuwansa dayake buqatan dumi a cikinsu.

Ita kuwa saukan hannuwansa masu dan sanyi a fatar cikinta ya sakata fidda numfashi me karfi tana sama da numfashin sbd sanyi sosai ne ya ratsata.

Jin irin sanyin dayake ratsasu ya sakasa yaye hijabin gabaki daya yana cirewa tareda kama hannunta suka koma ciki ya rufe glass din tareda sake electric curtains din suka rufe koina ruf ya dauki remote ya kunna dan warming dakin daya dauki sanyin ac shima sanyin yayi musu yawa.

Zaunar da ita yayi yana magana maganar da ita kadaice take jin me yake fada mata a kunne.

Kasa amsa masa tayi na abinda yake fada matan tana jinsa yana shige jikinta gabaki daya bayan ya zaunar da ita yana hada fatarsa da tata datake da sauran dumin hijabin daya rufe jikinta hakama ko yanzu daya yaye mata shi jikinta yanada dumi sosai.

Dumi dakin yafara dauka wanda ya fara ratsasu jikinsa na manne da nata har lokacin kuma har lokacin magana yake mata wadda baisamu amsar ko daya ba daga bakinta ba sbd babu maganar da batafi karfin kwakwalwa da tinaninta ba dan kuwa magana ce akan haduwan da sukai ayau din da yanda ta ringa cin abincin daya kusan sakasa rasa kansa agurin.

Bude idanuwanta tayi ta kallesa tana kasa yadda da shine me furta mata wainnan kalaman.

Motsawa tayi ahankali tareda janyewa kadan daga jikinsa ta miqa masa hannunta tana bude tafin hannunta a gabansa ta bude baki tace

'My phone??

Bakinta da yayi maganan ya kalla kafin ya maida kallansa a tafin hannun nata ya daga hannunsa ya dora akai yana hade tafin hannuwansu ya kamota yana hura mata iska me sanyi a gefen kunnenta yana bude baki yace

'Haka ake tambayan miji abu??

Wani kallo tai masa daya sakasa jin kunnuwansa biyu duka sun motsa ta bude baki tace

'Haka Saurayi yake tambayar Numbern budurwa ta hanyar dauke mata waya??

Wani irin sauka maganarta tayiwa zuciyarsa daya sakasa sake wani irin murmushi me shegen kyau da sauti daya sakasa fizgota jikinsa da sanyi yana hade kirjinsa da nata ya sake sakar mata murmushi me kyau daya sakata kasa dauke idanuwanta akansa ya kalli Bakinta kafin ya maida idanuwanta cikin nata yace

'Kin manta ne amma ke mace na ce,ke tawa ce dana mallaka ba budurwata ba....

Gefen fuskarta zuwa wuyanta ya saka hannunsa yana yiwa wata irin shafa yakai bakinsa kan kunnenta lips dinsa na gogan fatar kunnen yace

'Ko budurwa,ko mace,ko mata,ko yarinya koma menene ke din ta mutum daya ce har mutuwa'

Duk da tana jin wani irin waiwayin yanda yake maganar lips dinsa na gugar fatarta wani numfashi ta hadiye tana bude baki tace

'Wa kenan??

Hannu ya saka ya juyo da fuskanta suka fuskanci juna sosai har hancinsu yana gogan juna idanuwansa a cikin nata ya sake sake wani mayen murmushi yana zagayota da hannuwansa ya bude bakinsa dayake gap da bakinta qamshin dayake cikinsa ya shiga hancinta da kyau ta lumshe idanuwanta ta bude a wani slow akansa ya sake sakar mata numfashin cikin bakin nasa kafin da wata muryan daya tayar da tsigar jikinsu a tare yace

'Wanda yakeda ikonki a hannunsa fiyeda kowa a duniya yanzu, Wanda yakeda iko da damar sakaki tsallake maganar Amminki.....

Da wani irin sauri ta kallesa tana kokarin janye jikinta ya riqeta dakyau yana murmushin dayake fitowa da sauti yana cukuikuiyeta a jikinsa yana saka kansa a wuyanta yana shaqar qamshinta da baida kamansa a hancinsa.

Turesa ta fara yi tana cewa ya saketa.

Qin sakinta yayi yana sake rungumeta a jikinsa jikinsu na haduwa da kyau yana cigaba da murmushi.

Qin dena kokarin kwacewa tayi tana turesa a jikinta, Riqe fuskanta yayi da hannunsa daya yana hadeta da tasa ba tsammani ya hade bakinsu guri daya ya zira harshensa me sanyi da qamshi cikin bakinta yana sake mannota jikinsa da hannunsa daya.

Kissing dinta yafara yi cikin wani irin sanyi da soyayyarsa me zurfin gaske datai masa mugun kamun da baisan ya zai iya control nata bayan kawai ya sota a koina a gaban kowa fiyeda kowa fiyeda komai.

Ita kanta soyayyarce me karfin gaske take cin zuciyarta wadda batasan ya zatai ba bayan ta sosa din ta kaunacesa ta basa kowace irin dama akanta dan haka ahankali ta saka hannuwanta biyu ta zagayosa tana masa sanyayyar rungumar data sakasa yin baya a kujeran dayake zaune yana jinginar da bayansa tareda ita a jikinsa.

Kissing juna suka fara yi cikin wata irin salon dayake jagorantarsu yana bude mata shafin soyayyar dayake mata me karfi da ba sirki..

Tafin hannuwanta ne suka sauka akan fatar bayansa da babu kaya dan har lokacin towel ne kadai a jikinsa,

Tsigar jikinsa tashi tayi da tafin hannunta ta sauka daidai tsakiyar fatar bayansa ya qanqameta da karfi yana sake kutsawa cikin bakinta da harshensa yana zuqota yana tsotsa cikin wani mayen slow yana zira hannuwansa cikin rigarta yana bin fatar cikinta da cibiyarta da wata irin slow shafa kafin yayi dama da hannuwan ya shafi kirjinta wanda yake cikin bra dan haka ahankali ya zare rigar jikinta ya jefar gefensu yana bude idanuwansa da sukai nauyi suka sauya akan farar convertible bra din dake jikinta qal da ita tana daukan idanuwansa da yada curves din suka zaunu da kirjinta suna dake sama yana qasa ahankali sbd yanda numfashinta yake fita..

Bakinsa yakai a kan bra din cikin wata irin tsima da shauqin kallanta a matsayin tasa shi kadai da har abada bazai iya bari ko kallan daya wuce kaida zai iya barin wani ya mata batareda ya zama makashiba.

Mannota ya sake yi da karfi suka sake mannuwa cikin wani salo fuskansu ya gadu suna shaqar numfashin juna daqyau tareda kallan juna yana jin kaman zai hadiyeta gabaki dayanta,

Ita kanta jin takeyi bazata taba iya tinanin zamtowanta a wata rayuwarba wadda ba shine zai zama mai mallakinta ba dan haka ta daga hannuwanta ahankali ta saka wuyansa yana janye gashinsa dayake sake zuwa bayansa tareda saka hannuwanta duka biyun cikin gashin nasa ta taba tsakiyar fatar kansa data sakasa rufe idanuwansa da yanayi me karfi yana feso mata wani numfashi me karfin daya sauka fuskanta yana sake zagaye qaramin qugunta da hannuwansa biyu.

Bude idanuwansa yayi daqyar tareda kai bakinsa akan hook na hannun bra dinta tauna daya yayi masa ya ballesa gabaki daya hannun ya fita,

Dayan ya maida bakinsa shima cikin seconds uku ya ballasa da bakinsa take bra din ta fadi a tsakiyarsu daman hannuwansa na bayanta ya balla hook din bayan.

Faduwan bra dinta ya sakata mannuwa dashi cikin jin nauyi tana qanqamesa batareda tasan kashesa takeyi ba gabaki daya. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee

150 Sunanta ya ambata da wani irin sautin daya fito a rarrabe yana qanqameta da karfin gaske sbd babu abinda bayaji a kirjinsa daga nata kirjin dasuke kaman magnet din dake janyo ruwan jikinsa zuwa tsakiyar bayansan dan haka cirota yayi daga jikinsa yana dagata cak ya gyara mata zama a jikinsa dakyau yana kamo fuskanta ba bata lokaci ya sake hade bakinsu yana mata tsotsa me zafi dake ratsa kwakwalwanta tana qanqamesa sbd tafara rage kuzari daga yanda taga jikinsa yana vibrating tasan ya gama hawa sama dan haka ta fara sanyi tana son ya sassauto amma sam ba dama dan kuwa ya riga yayi loosing control kisses masu zafin gaske yake bata yana bin kowane sashe da na jikinta da hannuwansa yana wata irin shafa da salon daya sakata dole saddakarwa tana sake sakar masa jikinta.

Akan sofan da suke zaunen ya birkice su yana dawo da ita qasa yayi mata rumfa yana saka kansa a tsakiyar kirjinta yana saka hannuwansa ya yaga doguwar wandon baccinta yayi wurgi dashi yana cigaba da cusa kansa a kirjinta yana bata wutar data zafafa jikinta kafin ya fara basu nutsuwan da kaf duniya sai a gurin juna suke samunta.

Anan kan sofa ya basu lafiyayyan love din daya sake ratsa ruhinsu cikin salo me dadin gaske da ratsa jiki da zuciya.

Akan bayansa ya kwantar da ita bayan komai ya lafa yana jin tudun kirjinta akan fatar bayansa yanajin wani irin nutsuwa da kwanciyan hankali tareda nutsuwan ruhi suna sake cikesa hannuwansu a hade sarqe da juna idanuwansu a lumshe.

Saida suka raba kusan dare sosai a hakan bacci yafara daukansu kafin suka tashi shine ya dauketa sukaje toilet suka kimtso suka dawo,

Tight underwear na CalvinK ya saka wanda babu shape da baa gabi na jikinsa ita kuma farar vest dinsa kawai ya saka mata wadda ta dan sauka har cinyarta kadan suka shige gadonsa cikin wasu lafiyayyun beddings suka kwanta tana cikin jikinsa ya sakata take bacci me karfi da dadi ya daukesu.

Bayan sallan asuba taso tafiya ya kasa barinta yana sake shigewa jikinta yana qanqameta cikin sanyi da kauna tareda nutsuwan da baya son tabarsa.

Akan fuskansa ta dora tafin hannunta a hankali tareda taba shafawa kadan tana kallansa idanuwansa na rufe a lumshe kansa na kwance a kirjinta ta bude baki tace

'Ammi da maa zasu san bananan'

Bai bude idanuwansa ba ya sake shigar da hannunsa cikin vest dinsa dake jikinta ya shafi cinyoyinta masu laushi da santsin fata ya girgiza kai ahankali yana cewa

'Akwai abinda zasu iya yi dukansu idan sun sani? Xan hutar dasu na sanar musu a waya yanxu kina nan...

Bude idanuwanta tayi dakyau akansa tana kalla da mamaki sedai kafin ta gama mamakin ya bude idanuwansa ya miqa hannunda ta baya zuwa bedside ya dauko wayarsa yana tashi daga kanta ya zauna daidai a kan gadon yana kokarin saka kira.

Bata yadda zai iya saka kiran ba sai dataji ringing din wayar Ammi data manta ma ta taho da ita yana tashi yashe a tsakiyar dakin ta kalli wayar ta kallesa shima ita ya kalla kafin ya kalli wayar sbd ya manta datazo da ita dan haka wayar ya kashe ya nemo numbern Maa tenya zai saka kira tayi kansa da dan sauri tana miqa hannu zata kama wayar ya rungumeta gabaki dayanta yana qarasa dorata zaune akansa tsakiyar gadon.

A zaune yake kafafunsa a miqe a bude dan haka zaune da ita yayi akan cinyoyinsa yana zagayo kansa da kafafunta ya matseta sosai dakyau jikinsa yana kallanta ita shi take kalla tace

'Da gaske zaka iya kira? Kamun Alkawarin bazaka fadawa Ammi bafa... qarasa zancen tayi tana masa wani kallo da bayyanarda dan fushi.

Sake matsota jikinsa yayi suka hade dakyau yana kallanta yace

'Zasu sakaki takura da kunyar abinda bazan iya barin ki takura ba shiyasa zan sanar musu su sani shikenan sai bakin kowa ya mutu'

Kallan bakinsa da yayi maganar tayi kafin ta maida idanuwanta a cikin nasa idanuwan ta kalla tanama rasa abin fada masa sbd mamakinsa dayake kasa sakinta koyaushe.

Sake mannota yayi gashinta na biyowa ta gefen wuyanta ya saka hannu daya ahankali yana janyewa yakai bakinsa a fatar kafadarta ya dora lips nasa ya sakar mata wani lafiyayyan kiss daya sakata dagowa ta kallesa.

Bakinta yakai nasa yayi kissing lips dinta a natse Nan ma kallansa tayi shima ita ya kalla yana kai bakinsa tsakiyar gefen wuyanta ya dora lips dinsa anan ma yayi kissing.

Dagowa yayi yakai bakinsa a kunnenta ya dora kafin ya sauke mata kiss tsotsan kunnen yayi cikin wata irin salon data sakata rufe ido tana kamasa ta qanqame tsigar jikinta na tashi kafin ya sakar mata kiss me sanyi.

Bude baki ta sake yi jikinta a mace zata ce masa wucewa takeson yi da gaske amma ya hana maganarta qarasa fita ta hanyar rufe bakinta da nasa cikin sanyi da nutsuwa yana kissing nata da zafi me slow din daya sakasu su dukan shagala.

Da hannunsa daya ya dago vest din jikinta sama kadan ya zare bakinsa yana saka kansa cikin rigar zuwa sama ya fito da kansa ta wuyan inda nata wuyan yake ya sake hade bakinsu yana qanqame qugunta da bayanta.

Duk yanda taso qwacewa ta gudu ta koma bai barta ba da wasu lafiyayyun romances nasa da yanda yake cukuikuiyeta a jikinsa yana kasa barinta.

Basu ankara ba har sai da 10 na safe ta kusa tukuna suka rabu da gadon ta dauki wayan Ammi tafara kiran leylah wadda itama ta kasa komawa kwanan zaune tayi cikesa damuwa sbd ko a daren kwana sukai itada Asim a tare suna aikata wata zazzafar romance amma ta kasa fada masa kaman yanda ta fahimci shima ya kasa tayar mata maganar rabuwansu har lokacin.

Tana ganin kiran Ammi da farko fargaba taji amma tinawa da tace bangaren Mum zasu sai ta fuske ta dauki wayar.

Jin Bahar ya sakata ajiyan zuciya kaman yanda bahar din itama ta sauke ajiyan zuciya tana zaune akan kafafunsa yana bata fruits masu sanyi dake cikin madara me tsananin kauri a kwance sbd kusan hakanne yake shan fruits nasa yawanci.

Bahar bata iya tsayawa cewa komaiba fara tambayarta tayi tana bangaren Ammi ko bangaren mijinta??

Amsawa leylah tayi tana tabbatarda Bahar din bata komaba kenan itama.

Sake sabuwan ajiyan zuciya Bahar tayi cikin jin dadi tana cewa idan ta fito ta kirata su koma tare pls.

'Ok ganinan nima na gama zan fito nan da mintin biyar'

Ajiye wayar Bahar tayi tana kallansa shima ita yake kalla hankali kwance sbd baitaba jin komaiba ko damuwan komaiba akan wani tinanin su Ammi sbd yasan daga lokacinda duk ya gama abinda yake gabansa babu wanda zai hanasa daukanta ta dawo hannunsa kwata kwata dan kuwa bayajin a yanzu zai iya kowace rayuwar da babuta a ciki.

Kankanar dataji wata irin madara hartana digar da madara me kaurin gaske ya dauka da yatsun hannunsa yakai bakinta yana cigaba da kokarin bata sbd kada ta fita bataci komaiba yakai bakinta yana duba wayarsa shima.

Bude baki tayi ta amsa tareda tsotsan hannunsa dayake daddabe da madaran daya debo wanda ya sakasa dakatawa daga abinda yake dubawa a wayan ya kalleta yana kallan yanda bakinta ke taunawa bayan yaji tsotsan dataiwa yatsar hannunsa har cikin kirjinsa da qashin bayansa.

Batasan abinda yake kalla ba wayarta daya bata take kalla tana bin sakonnin Neesah dake jere da kallo tana karantawa tana murmushin dayake sake kashesa.

Sake diba yayi da hannunsa yakai bakinta ta bude baki ta amsa batareda tana kallansa ba dan idonta na kan wayar,

Yana zare hannunsa data sake tsotsa a wannan karan kasa riqe abinda yaji yayi sai saukan harshensa taji a bakinta yana lashe lips dinta tareda zirasa ciki yana laso zaqin dayake bakinta wanda ita kuma ta kasa motsi tana tsayawa cak daga abinda takeyi tanajin yana tsotsan bakinta a natse har saida ya lashe komai tas tukuna ya zare bakinsa yana kallanta ita shi take kalla da mamaki da wani irin murmushi fuskanta.

Hannu yakai ciki ya sake debowa ya saka a bakinsa yana jinginar da bayansa a kujeran da suke zaune a kai palonsa ya kalli tsakiyar idanuwanta yana jiranta kafin tayi kowane irin motsi wayar Ammi dake tsakiyarsu tayi ringing din daya hana abinda yake shirin faruwa ya farun.

Leylah ce ta kira tana baro bangaren Asim,

Daukan wayar Bahar tayi idanuwanta na kansa kaman yanda nasa suke akanta bai daukesu ba sunyi ciki sosai da buguwa da wata irin kwantacciyar soyayyarta.

Tana dauka yaji abinda tace ya lumshe idanuwansa bai budeba yanaji ta tashi daga jikinsa tana daukan wayarta data Ammin a hannunta zata bar gurin ya kama hannunta daya ya dawo da ita kai tsaye yayi kissing gefen fuskanta kafin ya saketa yana kallo ta fice daga dakin tana murmushi me kyau.

Tana fitowa take securities suka miqe suna bude mata kofar ficewa bangaren kansu a qasa cikeda girmamawan da suka saba.

Tana ficewa daga hanyar gabaki daya tana kama hanyar bangaren Ammi leylah ta bullo suka nufi bangaren Ammin kowannensu a dan tsarge.

Ita Leylah kunyarta da jin nauyinta akan mum dinta da Ammi harma da Maa sakinah sunyi sunyi da ita akan ta koma taqi yadda ta koma kuma ta kasa fadan komai akan abinda yake faruwa dan haka suka kyaleta sbd jiran Dad dinta ya dawo dan a tinaninsu auren ya riga ya qare ne batason fada jiran takeyi a dad nata ya dawo a zauna.

Dan hakanne take jin kunyar bayan taqi yadda takoma ta kuma qi cewa komai a ganta tana zuwa gurinsa batasan me zatace ba kuma hakama bazata iya kwasa ta komaba batareda tasan matsayinta ba.

Koda suka shigo bangaren gaban Bahar yafi faduwa da shiga fargaba amma ganin ba kowa a palo ya sakasu wucewa daki batateda bata kowane lokacin ba.

Suna shiga kai tsaye wanka Bahar ta wuce toilet tayi ta gasa jikinta da kyau kafin tafito ta sake cin abinci kadan ta kwanta bacci koma awa daya ne kafin 11 tayi.

Itama leylah kwantawan tayi sbd already tayi wanka acan tana kwantawa baccin da bata samu tayiba shine ya dauketa. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee

151 Ammi da daddare bata nemesu ba sbd itama ba anan din ta kwana ba saida safe ta nemesu shima ba dakinsu taje ba jinsu shiru ya saka ta aika naimah dubowa saigashi naiman tace basa nan,

Maa sakinah data san babu wanda ta kwana a bangaren duka su biyun sbd taje da daddare dubosu ba kowa kuma har wani dare tana dakin tana gadinsu amma ba wadda ta dawo dan haka shiru tayi batace komaiba har naiman ta dawo ta sanar da Ammin basa nan.

Shiru Ammin tayi amma batai tinanin komaiba tinda suna tare tasan NUAB bazai samu ganin Bahar din bama tinda suna bangaren Zuhrah.

Wayar zuhrah taso kira taji ko suna can din sai bataga wayarta ba sai kawai ta share ta kama wata hidimar.

Babu wanda ya sake fitowa dan haka basu hadu ba sai after 11.

Bahar ce ta fito da wayar Ammin a shirye cikin kayan shan iska marasa nauyi sosai riga da wando ta nufi dakin Ammin ta shige.

Wayarta ta kawo mata ta gaidata tana shigewa gefenta ta zauna tana amsa tambayan datake mata akan wayarta data ga sakon gaisuwan da zarah yar tenya datake aiko mata kullum.

Anan leylah ta sameta ta gaida Ammin itama tana ficewa dan wayarta da Mum dinta ke kira dan amsawa.

Bata fito dakin ba Maa ta shigo dakin dauke da tray din dayake dauke da madarar data dafa mata me karfin gaske ta ajiye kan table tana zaunawa akan kujera itama tana shiga firar da sukeyi cikeda kulawa sunayi akan wani hukuncin da Abaa dinta ya taba yankewa batareda ya iya mulki sosai ba a anjom suna dariya maganar na shigar Ayanah datake jinta har zuciyarta da farin ciki da dariyan jin yanda Abaas yayi mulkin anjom batareda taimakon kowannensu ba shi kadai.

Sakinah ma dariya takeyi suna maimaita lokacinda yake tamkar mace bayason ace shine zaiyi mulkin Anjom yafison Ayanah tayi ya bita.

Bawa bahar din mug cup din dayake fidda hayaqin madarar Maa tayi ta karba suna cigaba da firar su cikin nishadi da kewan Abaas wanda a yanzu koyaushe adduarsu bata yankewa akansa da sauran iyayensu da Nurat.

Fara sha tayi a hankali tana dan bata fuska kadan sbd karfin madarar dan haka bakinta ya mutu ta rage magana tana sha a hankali tana saurarensu tana murmushi da yar dariya jin irin kuruciyar da mahaifinta yayi wanda firan take mata dadi sosai sbd batada labarin da ako yaushe yake mata dadi da bata gajiya da sauraro irin firar mahaifinta.

Nishadi sukeyi sosai suna firar tana sauraronsu tana murmushi tana shan abinda yake hannunta a natse tana lafe gefen Ammi.

Qamshinsa ne ya fara ratso su dan haka maa dake dariya sosai ta dago ta kalli kofar daidai nan ya sako kai da sallamarsa me nutsuwa da kamewa tareda wani irin iko.

Ammin itama kofar ta kalla har lokacin fuskanta dauke da dariyarta me kyau datake tino mata farin cikinta na baya data rasa a tareda rayuwa da iyaye da yan uwanta.

Ganin nishadin dasuke ciki ne ya sakasa qarasowa fuskansa daukeda wata natsatsiyar annushuwa da kwanciyan hankalin da shima yake tattare dashi wanda kasancewan 'yar Ammi a boyem din yake basa.

Zaunawa yayi a gefen Ammin a natse cikin kwanciyan hankali ya kalleta ya gaidata cikin kulawa da kauna kafin ya maida kallansa kan Maa itama ya gaidata.

Readers Also Read