Kenza eBookz

Heedayah complete Novel - Chapter 16

Heedayah complete Novel - Chapter 16

Heedayah complete Novel Chapter 16: Heedayah complete Novel Chapter 16. Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very…

2,950 words

Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 馃槏 9/12/21, 8:04 PM - ,: Shuraim ya dauke kai ya juya ya koma gaban mirror ya dau makullin motarsa, Kaka ta mike tace "Baxa ka kira min shi bane Shureen?" Ba tare da ya juyo ba yace "Ehh baxa a kira ba, waye kuma wani Junaid...." A fusace Kaka tace "Aa wllh kar ka xagar min shi don in ka xagesa ni ka zaga, kar ma ka fara wllh, ance maka bai fiye min kai ba sau dubu, Ina ruwana da kai dama idan ba kaddaran na haifi uban ka ba, wllh Junaidu ya gama min komai, kana xagin sa xaka xago ma kanka fitina, don ni ka xaga...." Ta koma ta xauna ta fashe da wani sabon kukan, bude kofa Shuraim yyi ya fice daga dakin ya kulle, kaka ta tsaida kukan da take a hankali tace "Ehh lallai d'an Amadu ya ci ganye..." Mikewa tayi ta bi bayansa fa fita. Mumy ce tsaye ta wajen flowers dake bayan gida, sbda shuke shuken flowers din wajen sai ya fi kama da garden, waya ne kare kunnenta cike da damuwa tace "Wllh kuwa Baffa, ni dai nayi ta bata hakuri ina kwantar mata da hankali, to kaga bbu ddi idan ban kira ka na sanar maka ba tunda cewa tayi kai ma ba son xamanta kake a gidan ba, kuma idan anyi duniya don manzon Allah ita da gidan har abada tunda xaman dole ku ke da ita, har mayar da ita na yi niyyar yi tace ta koma a wani matsayin?? Tunda har ynxu bbu wanda ya biyo ta ko ya kirata ya bata hakuri yace ta tashi su koma, to shine nake ga gwara ka taho da kanka ka kara bata hakuri sannan ku tafi don wllh ta dau xafi sosai, ni ban ma ta6a ganin bacin ranta irin na yau ba, kuka kuwa ta sha shi har ta gode Allah, xan kira barrister in sanar masa ta hanani wai ita xaman garin ma duk ya fita a kanta, gidan nawa ma ba xama xata yi ba, wai xa a iya wayan gari a ga bbu ita ta bar garin, to shine naga gwara in kira ka..." Baffa dake ta sauraranta ya sauke ajiyar xuciya yace "Shkkn Maryam nagode, sai na shigo anjima" Mumy tace "Babu komai, amma don Allah kar kace ni na kira ka, idan ma kace mata ni na kira ka kara baci ranta xai yi tace wato ma sai da na kiraka ka xo, da ban kira ba baxa ka xo ba, kuma idan xaka xo sai ka d'an taho mata da abinda kasan ta fi so" Baffa yace "In sha Allah, sai na xo" daga haka suka yi sallama, Mumy ta katse wayar tana wani murmushi, lkci daya ta sauke ajiyar xuciya, cikin compound din ta koma dai dai shigowar Junaid, har xata hade rai ganinsa ko me ta tuna kuma sai ta sake fuska sosai, ya gaisheta da ladabi ta amsa tace "Sannu da xuwa junaid, kwana biyu baka shigo ba" yace "Ehh naje Zaria ne" Mumy tace "Kuna da 'yan uwa can kenan" yace "Aa, naje wani uxuri ne a can" tace "Ayyo... To sannu da xuwa" yyi mata godiya sannan ya nufi entrance din shiga gidan, ta bi sa da wani kallo har ya shiga parlor... Sajida ce ke ta share share a parlor, ta mike tana gaishesa ya amsa yace "Wani dakin Kaka take?" Sajida ta nuna masa hanyar dakin, can ya nufa, yyi sallama bakin kofar, Kaka ta amsa da karfin ta, ya bude kofar ya shiga, kaka na xaune ta daura kafa daya kan daya, Khadijah na jera mata tarkacenta na tsofaffi a gaban madubi, kofar bathroom a bude Karime na ciki tana ta faman wankewa, Junaid ya xauna nan kasan carpet yace "Sannu kaka, Ina yini" tana washe baki tace "Lfya lau Junaidu, sai ynxu??" Yace "Ehh kaka, ashe kin dawo nan..." Ta gyara xama tayi narai narai da ido tace "Baxan dawo ba Junaidu, kwai suka soya min duk karni gashi fari fatt sai uban albasa to hakan ba alamar an gaji da kai bne, to shine naga tun kafin sun barbadamin shinkafar bera gwara in gudu, ynxu hka ba wanda ya san ina nan, kilan suna can hankali tashe sun kai rahotu gidan 'yan sanda" Junaid da kansa ke kasa yana murmushi yace "Da dai kinyi hakuri Kaka...." Shiru tayi tana kallonsa can tace "Aa kar ka xama gantalalle kai ma mana, ae in kowa ya gaya min wnn mugun magana kai bai kamata ka gayan ba, inyi hakuri su cuceni su kasheni a banxa, sae kace Umaru kadai na haifa, ga dai Amadu, Aa ba ruwana, ni duk wanda yace in koma can gidan ma haushi na kawai yake ji ya tsaneni" Junaid ya ajiye ledan hannunsa yace "Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi" Kaka tace "Toh ka ga ynxu kayi magana, Kuma in sha Allahu alkhairin ne dama" murmushi kawai yake yi, kaka tayi kasa da murya tace "kana ji Junaidu, dama uwarka haka take ban sani ba?" Junaid ya daga kai yana kallonta, kaf ta kwashe labarin abinda Mami tayi mata ta sanar masa tana matsar kwalla, tace "A gantale fa ta barta gun mai aiki dake naso uwa an tuttula mata jarkan man gyada, ynxu hka fa ga Mai aikin can na sa ta wanke bandaki na, kuma ban amince ta shiga bandaki na ba sai da tayi wanka wllh, to mata daga dawowa kuma sai ki dauke min yarinya haka kawai, yini fa muka yi tare da yarinyar bbu wanda ya ji kanmu, muna ta hira fa in gaya maka" Junaid yace "Gaskiya bai kamata....." Kaka tace "Allah ya maka albarka, daga shigowa gida sai ta fara fito da mugun halinta da wuri wuri hka tun ba aje ko ina ba, ni sai nayi tunanin ma ko tasan uwar yarinyar ne wnn isa haka da ta nuna min...." Junaid ya d'an yi murmushi yace "Xan je in dauko maki ita ynxu kaka" kaka tace "Amma fa kar kace nace maka komai, ba ruwana kar ta kullaceni, kawai dai kayi mata nasiha ta canxa halinta, wannan ba halin xaman gidan miji bane..." Ya mike still smiling yace "In sha Allah kaka, bari in je in dawo" Kaka tace "Allah maka albarka, ni dai gwara min kai a kan kowa ma a gidan nan" Kaka ta kalli Khadijah da sauri tace "Ke 'yar banxa kin gaishe sa ma kuwa da ya shigo? Ku dai 'ya yan Amadu baku da hali tirrr" turo baki Khadijah tayi tana ci gaba da abinda take, shi dai Junaid tuni ya fita ya rufe mata kofa, part din Mami ya nufa ya sameta xaune parlor ta daura kan Heedayah a cinyarta tana mata gyaran gashi, Heedayah ta mike xaune da sauri jin muryarsa, ya xauna saman kujera ya gaida Mami, Mami ta amsa tace "Na xata da Farida xa ku xo" yana kallon Heedayah yace "Aa, Uncle said she should stay" Mami tace "Okay, how are you" yace "Alhmdllh, ya aiki" tace "Mun gode Allah" Ya mike ya koma kujeran da suke ya xauna gefen Heedayah yana kallonta yace "How are you Heedayah" Ta wara ido tace "Fine, me yasa baka xo ba jiya har da shekaranjiya" Yace "Ae gani na xo yanxu" Ta laluba fuskarsa tace "To ka dinga xuwa kullum ka ji?" Mami dai ta tabe baki tana harhada kayan gyaran gashinta, Junaid na murmushi yace "Mami kaka tace a maido mata da Heedayah" Mami na kallonsa kafin tace komai ya kara da cewa "She wants her to be staying with her, bata ji dadin xuwa da kika yi kika dauketa ba daxu" Mami ta rike ha6a tace "Tohhh, ikon Allah" Junaid yace "Yess allow her ta koma wajen ta Mami, since ita ta bukata" Mami tace "Toh ai naga kamar wani nauyin Heedayah xata xame mata, baxata iya da tsirfan Heedayah ba" Junaid tace "Tunda ita ke son hakan ki bar mata kawai Mami" Mami tace "kai yaushe ta gaya maka haka?" Yace "Yanxu, har da kukan ta" Mami ta bude ido tace "Ahh to dauketa ka kai mata ita" Heedayah dake jin su tace "Mami wajen kaka xai kai ni?" Mami tace "Ehh" Heedayah tace "Amma xan dawo koh?" Mami tace "Ehh xa ki dawo" Junaid ya mike ya kama hannunta suka fita parlon, Mami ta bi su da kallo.... Mumy dake xaune parlor kamar dai ko da yaushe ta bi su da kallon gefen ido har suka wuce dakin kaka, Kaka na ganin Heedayah ta washe baki tace "Deedayah, ga kaza Junaidu ya kawo min, ai kin iya cin kai da kafar kaza koh?" Heedayah tace "A'a ni lap na iya ci" Kaka ta kalli Junaid tace "Meye lam kuma?" Yyi yar dariya yace "Cinya" Kaka ta kalli Heedayah da sauri tace "To sai ki kwata ai, ka ji min dai" Ya xaunar da ita gefen kaka yace "Kaka xan je Masallaci in dawo" Kaka tace "Toh yi maxa gashi can an fara kira" a hankali Heedayah tace "Are you coming back?" Ya juya yana kallonta yace "Yess" Yana fadin haka ya juya ya fita, Kaka tace "Toh ko wnn lafiyayyen turancin da kike ai ya ci kowa ma ya san ba daga gidan gantalallu kika fito ba, da kyar idan baki fi Shureen iya turancin ba don ni tunda nake ban ta6a jin ma yyi turancin ba, ga dai makaranta me tsada uban ya sa shi yana karami amma bai jin turanci, ko wnn kwam din da kowa ya sani baya ji" Heedayah ta kyalkyale da dariya tace "Kaka to sai in dinga koya masa mana" Kaka tace "Atoh, bari dai Allah ya shigo da shi mu ga ko xai yadda" Heedayah tace "Kaman ni yake?" Kaka tace "Ka ji ki wannan a haihuwar kaji ai yyi jika da ke, Shureen fa nace maki" Heedayah tace "Ni ban san shi ba" Kaka tace "Idan ya shigo xan Kai ki ki tattabasa ki ji" Heedayah tace "Toh" Tare Junaid ya shigo cikin gidan da Baffa, Baffa ya xauna parlor shi kuma ya shiga wajen kaka yace "Kaka Baffa ya xo" Kaka tace "Waye kuma Baffa, uban wa yace masa Ina nan, Kai ni dai gaskiya ana shiga hakkina, to me ya xo min kuma kamar dai wata yar karamar yarinya" Junaid na murmushi yace "Ya xo ne ya tabbatar nan din kika xo" Kaka ta tabe baki tace "Ni dai ba ruwana wllh" Bude kofar dakin aka yi sai ga Hajiya Amina da Hajiya Hauwa sun shigo da sallama, Kaka tace "Su waye wannan kuma" Hajiya Hauwa tace "Sannu kaka" Kaka tace "Yauwa, daga ina haka kamar an koro ku, ko daga anguwa ku ke?" Hajiya Amina tace "Daga gida muke kaka, mun xo biko...." Kaka tace "Yaji Maryam din ta kara yi ina gidan bani da labari??" Hajiya Hauwa tayi dariya tace "A'a kaka, kawai sai mu ka ga ba ki a gida" dai dai nan Mumy ta shigo dakin, kaka tace "Wllh na so shiga in maku sallama amma sai nayi tunanin bacci ku ke don na San ku da baccin safe, tashi nayi yau da tunanin Amadu a raina shine nace bari dai in je shi ma ya sami lada na...." Baffa ne ya shigo da sallama, kaka tace "Ikon Allah, har da kai Umaru, to me ya faru ne wai? Ba fa kai kadai na haifa ba da xanyi ta xama gidanka, shkkn kuma shi Amadu ba mutum bne da baxan dinga xuwa nasa gidan ba, Kar ka xama me son kanka mana Umaru, ka so ma d'an uwanka abinda kake so ma kanka, shima ka barsa ya dinga samun ladan uwarsa" Baffa yace "Nayi tunanin ko an 6ata maki rai ne ai Baaba" Da sauri kaka tace "Aa wllh, baku ta6a min komai ba, idan nace ma kun mun sai Allah ya kamani, matan ka ai mutanen kirki ne tun ma ba Mai jidda ba, tamkar ynda xa su yi ma iyayen su suke min, to sae in masu sharri ince sun min wani abu?? Aa kawai ni dai na xo gidan Amadu ne shi ma ya samu lada...." Kallonta kawai junaid yake with surprise, Mumy da hawaye ya cika idonta tace "Amma fa kaka cewa kika yi kwai suka soya maki duk karni sannan basa baki abinci da wuri kawai sun gaji da ke ne...." Kaka ta saki salati tace "Yau naga abinda ya isheni jama'a, Maryam ke da wa ku ka yi haka??? Lalacewar ta ki ta kai haka bani da labari? To ke ina ruwanki ko danyen kwai suka kawo min, ba gwara su sun kawo min kwan duk karni ba, ke me barina da yunwa fa??" Baffa yace "Toh kaka tunda dai bbu wani matsala shkkn sai dai mun yi waya" Kaka tace "Bbu ko wani matsala Umaru Allah yyi ma kai da matanka albarka..." Baffa ya amsa da Ameen ya fita....Mumy dai hawaye ya ki tsaya mata, Hajiya Hauwa sai danne dariyar ta take, daga karshe ita ma tayi ma Kaka sallama ta fita haka ma Hajiya Amina, Mumy ta bi bayansu xuciyarta na tafarfasa, Junaid dai kansa na kasa, kaka tace "Ka ji min mata dai xata min sharri da rai na" Tuwo da miyar egusi Sajida ta kawo ma kaka, Kaka tace "To ba gwara ke ba kan wannan mata da Rakiya ta dauka aiki duk wari.... Tafi ki kawo min flet da cokali" Mai aikin ta fita sae gashi ta dawo, Kaka ta amsa ta bude warmer din tuwon ta diba, ta ajiye ma Junaid, Junaid yace "Kaka ni fa a koshe nake" Kaka tace "Aa ni ba ruwana gashi nan ka ci, kana da Inda xaka je ka ci abinci ne da ya fi nan...." Ta kalli Heedayah tace "In xuba maki kema" Heedayah tace "Na koshi" Kaka tace "To wlh baxan baki Kai da kafar Kazan ba ma" Heedayah ta mike xaune kamar xata yi kuka tace "Toh in ci da Yaya" Kaka ta kalli junaid, Tashi yyi ya koma kusa da ita da plate din tuwon yace "Toh mu ci" Kaka ta ta6e baki tana xuba nata, Heedayah ta d'an fincili tuwon bayan ta laluba plate din ta kai baki, Kaka tace "Wllh haramta maka tuwon xata yi, meye kuma na mintsilin tuwo kamar kaza??" Dariya junaid yyi ya deba a cokali kadan ya tabbatar ya huce sannan ya kai bakin Heedayah, Jin cokali a lips dinta ta bude bakin ta amshi tuwon, a haka suka dinga cin tuwon, aka bude kofa sai ga Shuraim ya shigo, kaka tace "Shureen wai xaka dinga koyon turanci gun Deedayah" Shuraim ya kalli Heedayah da ta tankwashe kafa a gaban Junaid, ajiye ledan hannunsa yyi nan gefe ya fita dakin, kaka ta kalli Junaid tace "Kila kunya ya ji, da ban masa magana a gabanka ba" Dariya sosai Junaid yyi... Sai kusan karfe tara yayi ma Kaka sallama Heedayah har da kukanta wai xata bi sa, ya samu dai ya lallabata ya fita, Kaka tayi tagumi tace "Toh wai a gidan ubanwa kika ta6a sanin Junaidun idan ba gulma ba?? Sai kace shine Amadu? Ai ni da Amadu ne dolen ki..." Wajen karfe sha daya Mami ta shigo da eye drops din Heedayah, Kaka da har ta kashe wuta tace "Kinga Rakiya, abinda xai faru ba sai kin dinga ba kanki wahalan shigo mana tsakar dare ba mun fara bacci, kawai ki nuna min ynda xan dinga sa mata a idon, Amadu fa ya fi awa daya a dakin nan sannan ya fita, tun daxu ya kamata ki xo ai, ni na xata kin gaji kin kwanta ne" Mami tace "Aa ban kwanta ba" kaka tace "To nuna min ynda abun yake in dinga yi mata da kai na" Mami ta nuna ma kaka ta tabbatar ta gane din tana kuma tsaye ta diga ma Heedayah dake bacci drops din dare sannan tayi masu sai da safe ta fita... Har kaka ta kashe wuta aka sake bude kofa, Mumy ce ta shigo kaka ta kunna wuta tace "Amma dai bakwa tsoron Allah matan gidan nan, bakin cikin baccin ake mani cikin daren ma" Mumy tace "Yi hakuri kaka, naga baki bacci da wuri ne ban san kin kwanta ba, kankana na yanka ma Barrister shine na dibar maki" kaka tace "Ki sa min a firiji, amma wnn ae shiga hakki ne, meye kuma kankana tsakar dare jama'ah kamar ana yunwa" Mumy ta bude fridge dake dakin ta ajiye tana kallon eye drops dake ajiye saman fridge din, lkci daya ta kwashe su tace "Toh sae da safe kaka" bata jira cewarta ba ta fice daga dakin, kaka ta ja tsaki ta kashe switch din wutan.... Har wani murmushi Mumy take ta wuce dakinta da sauri, bandaki ta shiga da wayarta ta doka ma Sadiya kira, Sadiya na dagawa tace "Toh ga dai eye drops din na samo Sadiya... Kin yarda Allah na tare da ni?? Wllh cikin ruwan sanyi na samu, ban ta6a xaton hka ba...."

Heedayah isn't free, do not read for free, subscribe and read happily....

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....

Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096.....

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull