Kenza eBookz

Heedayah complete Novel - Chapter 17

Heedayah complete Novel - Chapter 17

Heedayah complete Novel Chapter 17: Heedayah complete Novel Chapter 17. Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very…

3,008 words

Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 馃槏 9/12/21, 8:04 PM - ,: Mumy tace "Toh ki tafi ki hada shayin, kayan shayin na can kitchen, bredi kuma na parlona su Rabi'ah sun bar sa a can" cikin rawan jiki Karime tace "Toh ngdd Hajiya, nagode" Mumy ta kuma kai idonta kan eye drops din sannan ta fita Karime ta bi bayanta da sauri cike da jin dadi, main parlor Mumy ta xauna tana girgixa kafa, Karime kuma ta wuce bangarenta dauko bread, Mumy ta bi ta da kallo har ta shiga ciki, dai dai nan kuma aka bude kofar parlon Mumy ta juya don ganin wanda xai shigo, Kaka ce ta shigo parlon tana sakale da wani karamin jaka me kama da handbag, Mai gadi na biye da ita a baya rike da wani tikeken akwati, Mumy ta bude baki ta mike da sauri tace "Lafiya Kaka? Me ya faru??" Kaka bata ko saurareta ba ta nufi wani spare room dake nan cikin parlon tana cewa "Ina fa lafiya? Meye kuma baxai faru ba? Sai kace dai Umaru kadai na haifa a duniya, ga dai gidan Amadu me dakuna ta ko ina...." Har ta bude kofar sai kuma ta dawo tace "Wllh Maryam wani kwai suka soya min yau xar karni, to ga dai albasa an cika amma ni dai naji yana karni na bala'i, ina laifin su d'an yanyanka min yar tafarnuwa su watsa a ciki, wnn ba alamomin an gaji da kai bane a waje? Jiya sai bayan magariba suka kawo min abincin dare, tuwo da wani miya sun cika naman kasuwa, to ca masu nayi yunwan nama nake?? abinda mu xamaninmu karfe biyar duk mun ci abincin dare munyi wanke wanke kowa ya manta, mata kawai suna neman kashe ni kuma sai in xauna kamar uwata tace min je ki kya gani, A'a wllh, to me gidan Amadu yake da baxan lallaba in dawo ba??" Mumy da ta ji kamar ta kurma ihu cike da karfin hali tace "Haba kaka, Haba kaka, haba kaka, wllh hakuri ake a ko ina, ko ina mutum yake sai yyi hakuri, rayuwar ma gaba daya d'an hakuri ne, ni ba gashi an min kishiya ba nayi hakuri muna xaune lafiya? me yyi xafi xaki tattaro kayanki ki dawo nan ai baxa su ji dadi ba Kaka, gaskiya bari in dauko makullin mota mu koma, baxa su ji dadi ba wllh barin Baffa, gani xai kamar baki gode kokarinsa a kanki" Kaka tace "Koh??" Mumy tace "Wllh tllh, ai ba xamansu kike ba da xa ki bar masu gidan kaka, sun ma ci riba kenan, bari in dauko makullin mota" Kaka tace "Toh, idan fita xa ki yi ga mai adaidaita can ki biyasa dari biyunsa kar ya mana ihun 6arayi a unguwa yana can yana jira ban basa ko sisi na ba, dama kuma ban masu sallama ba ta baya na bar masu gidansu, kya iya xuwa ynxu ki ce masu na dawo nan da xama, duk me nemana Ina nan gidan d'ana Amadu...." Kaka na kai wa nan ta shige daki... Mumy ta xauna saman kujera tayi tagumi tana furta innalillahi wa Inna ilaihi raji'un a xuciyarta, Mai gadi da ya ajiye kayan Kaka a parlan har ya tafi ya dawo yace "Hajiya D'an sahu na can yana jira fa...." Cikin bacin rai Hajiya tace "Kai da d'an sahun sai na ci kaza kazanku idan baka fita idona ba, na hau adaidaita ne da xa ka xo kace min d'an sahu na jirana???" Mai gadin ya juya ya bar bakin kofar... Shuraim da ya dawo daga kai Abba office yana kallon Mai adaidaitan da ya gyara parking don basa hanya ya sauke glass yace "wa kake jira malam?" Mai adaidaitan yace "Wata tsohuwa na kawo nan ta shiga wai xa a kawo min kudi to har yanxu dai ina ta jira" Shuraim yace "Nawa ne?" Yace "Dari biyu ne kudin" Shuraim ya ciro dubu daya ya mika masa, D'an sahun yace "Amma bani da canji wllh" Shuraim yace "To je ka" D'an sahun ya dinga yi masa godiya, Shuraim ya gyada masa kai kawai ya ja motarsa xuwa ciki don Mai gadi ya bude masa gate, parking yyi ya sauka ya rufe motarsa ya wuce ciki... Mumy ya tadda a parlor tayi tagumi ga tashin hankali karara a fuskarta, ya isa kusa da ita ya xauna a hankali yace "Mumy lafiya" Mumy tace "Ina fa lafiya Aliyu, don Allah ka shiga ka lallaba tsohuwar nan ka mayar da ita gida, kalli uban akwatin da ta kawo wai ta dawo nan, ta dawo wajen wa? Ta dawo tayi mana me? Don Allah ka shiga ka lallaba ta ka maida ta inda ta fito...." Shuraim dake ta kallon Mahaifiyar tasa yace "Mumy amma ai ba laifi bane don ta xo nan, Kuma ai...." A mugun fusace Mumy tace "Rufe min baki gantalalle kawai, dama ina kuwa xaka san laifi ne dawowarta nan???" Lkci daya Mumy tayi tsit ganin Kaka ta fito har ta cire Hijabin ta, Kaka tace "Kin sallami d'an sahun ko kuwa kin barsa yana can yana min kallon macuciya barauniya??" Shuraim ya mike yace "Na sallamesa" Kaka tace "Atoh, Kai baka je aikin bane yau?" Yace "Sai da yamma, ina kwana?" Tace "Lafiya lau, Shureen ni dai na dawo nan gaskiya, matan Umaru kasheni suka so yi Allah bai yi ba, yau wani kwai suka ban da ya kusa kai ni lahira, shayin kuma sun cika masa kayan kamshi kamar dai buzaye... To ina dalili ga dai gidan Amadu" Shuraim dai bai ce komai ba, Kaka tace "Ka shigar min da akwatina daki dukiya ne a ciki, jama'ah Ina Deedayah, ga bredi na taho mata da shi da kwai...." Shuraim ya dau akwatin nata ya shigar da shi ciki, Mumy dai karfin hali kawai take don kiris ya rage hawaye ya xubo mata, kaka tace "Maryam tambaya nake Ina Deedayah?" Mumy ta dake tace "Wacece kuma Deedayah?" Kaka tace "Sabuwar 'yar Amadu mana...." Mumy ta wani tabe baki tace "Ayyo makauniya wai?" Kaka tace "Aa wannan kuma isgilanci kike ma ubangiji ba ruwana, ke kika halicceta da xaki kirata da makauniya, meye kuma makauniya idan ba isgilanci ba, ko ita ta xabar ma kanta makantar? Ni yanxu Ina take??" Duk wannan abun Karime na tsaye sai kallon kaka take, Mumy ta nuna mata Karime tace "Ga me kula da ita can" Kaka ta kalli Karime tace "Wacece kuma wnn sai naso take, ta kula da ita ko ta sa mata cuta, bakya wanka ne baiwar Allah?" Karime ta kasa cewa komai, Shuraim dai yyi murmushi ya nufi dakinsa, Kaka na kallon Karime tace "wa ya daukeki ki dinga kula da ita, Amadu ko wa? Tunda ita uwar rikon tata na samu labarin har ta fara fita aiki, Amadu ya fita ita ma ta fita...." Karime ta girgixa kai tace "Aa, Hajiyar ce ta daukeni..." kaka tace "Toh kuma sai kiyi ta kazanta kina naso, ba kya tashi da safe ki sa ruwa kiyi wanka ki dauko yar atamfar ki ko da kodadde ne ki saka kiyi fess da ke.. yanxu Ina yarinyar take?" Karime tace "Tana can daki kwance," Kaka tace "Wannan xama da ke ai sai cuta ya kama 'yar mutane..." Daga haka kaka ta nufi part din Mami tana cewa "Ita kuma mata daga tarewa sai fara fita aiki kamar auren banxa aka daura mata, ni ba ruwana" Zaune kaka ta ga Heedayah saman gado ta tashi tana mitsika ido, Kaka ta washe baki tace "Deedayah... Kin tashi" Heedayah ta juya da sauri tana duban Inda ta ji muryarta tace "Kaka" Kaka ta karaso tace "Ehh ni ce Deedayah, kin ga na dawo nan yanxu, kwai suka bani duk karni, kinji dalilin barin gidansu da nayi" Sakko mu je ga bredi da kwan na kawo maki kema ki ci ki ji, Heedayah ta sauka saman gadon kaka ta kama hannunta suka fita tana cewa "Ita dama ashe ba don ta kula da ke aka aurota ba, xata barma katuwar mata kazama ta sa maki wani cutan Amadu ya shiga uku...." Heedayah tace "Kaka tafiya xa ki yi da ni can gidanku?" Kaka tace "Wani gida? Ai na dawo nan sai kuma wani ikon Allah, abincin banxa fa suke bani a can gidan wllh Deedayah...." Mumy ta bi su da kallon gefen ido, Kaka ta tsaya tana rike da hannun Heedayah tace "Maryam ban fa karya ba, Kuma ni ba shayi xan sha ba gaskiya, ko me aka samu ni dai a bani in ci fisabilillahi" daga haka ta shige dakin da ta sauka tare da Heedayah, Mumy ta mike ta wuce bangarenta da sauri ta dau wayarta ta shiga Kiran Hajiya Sadiya, Hajiya Sadiya na dagawa Mumy ta sakar mata Kuka tace "Sadiya wllh shirinmu na ta rugujewa, yau dai ga wnn tsohuwa ta diro da katon akwati, ynxu haka ta dauke yarinyar ta shige da ita dakin da ta sauka, wato bbu ma ranan komawarta ne don sai kinga akwatin da ta kawo, ni dai wllh Sadiya hakurina ya fara karewa ji nake kamar in kashe yarinyar nan a gaban kowa a daureni kawai in huta, wnn yarinya har in mutu xan mance da ita kuwa a rayuwata, ta janyo min dariya a duniya, Duk fa dariya ake min a boye Sadiya" Sadiya tace "Ki kasheta kuma a daure ki Maryam, me aka yi kenan? Ke ina gaya maki gaggawa na shaidan ne kin kasa fahimta ko, meye na gaggawa abinda dai ana tare...." Mumy tace "Toh ke kina ga wnn tsohuwar da ta diro mana gida ynxu baxata kawo mana wani cikas ba?" Hajiya Sadiya tace "To ke meye ruwanki da ita? Wajenta yarinyar take da xai dame ki, Kinga xa mu yi waya anjima nayi bakuwa" daga haka ta katse wayar, Mumy ta xauna gefen gado tayi tagumi hawaye na sauka idonta.... Karime da Sajida tasa suka girka ma kaka shinkafa da miya ko damuwa da ynda suka yi girkin bata yi ba... Kaka na kallon Heedayah dake kwance gefenta tace "Toh sai kuma a siya maki?" Heedayah tace "Ehh mana, har kitso Ina yi ma gashin babyn nawa...." Kaka ta rike ha6a tace "A makancen?" Heedayah tace "Na'am" kaka tace "Toh yanxu a nan wani gantalalle ne xai siya maki wani baby ana xaune kalau??" Heedayah tace "Abba mana" Kaka ta ja kunnenta tace "Ke ce gantalalliya ba d'a na ba, shi Abban ne gantalalle?" Heedayah tace "Aa ai Mami ma xata siya min" Kaka tace "Atoh sai dai ita din, Amadu ba gantalalle bne..." Bude kofar dakin aka yi Shuraim ya shigo da sallama, kaka tace "Ko kuma Shureen ya siyo maki ba?" Heedayah tace "Waye shureen?" Kaka tace "Aa nima haka naji suna ce masa amma sunansa Aliyu..." Heedayah tace "Ae ban san shi ba" Kaka tace "Toh ai sanin nasa bashi da amfani don bashi da kyakkyawan alaka da mutane, mugun hali ne da shi, kin ga ai tun daxu da na xo bai shigo gaisheni ba sai ynxu..." Heedayah tace "Shi ma a nan gidan yake?" Kaka tace "To Ina xa sa? Ai gidan Ubansa ne nan din... da dai yyi aurene sai ya bar gidan, ni da Allah xai fito masa da mata ma yyi auren kowa ya huta don wannan shiru shirun da yake yi idan xamaninmu ne cewa xa ayi aure yake so" Shuraim dake tsaye bakin kofa ya hade rai yana kallon kaka da Heedayah bai dai ce masu komai ba, Heedayah tace "To ki ce masa ya siya min babyn Kaka, babba nake so" Kaka ta kalli Shuraim tace "Kaji kai Shuraim ko ba mai tsada bane ka dubi maraicinta ka siya mata domin Allah, ya fi tayi ta xama shiruuu kamar kurma..." Yace "Toh sai ta xo ta kwata ai" Heedayah na jin muryarsa ta matsa kusa da kaka a hankali bata kuma cewa komai ba, Kaka tace "Atoh, tunda ba ajiya ta ba mutane ba ai sai ta hakura da Babyn dama" Tsaki Shuraim yyi ya juya ya fita ya rufe dakin, murya can kasa Heedayah tace "Kaka ya wuce?" Kaka tace "To me xai min dama, ya wuce" Heedayah ta turo baki tace "Ni bana son sa" Har aka yi azahar Kaka na dakinta tare da Heedayah, bbu irin labarin da bata ba Heedayah ba wanda kwakwalwarta xai dauka da wanda ma baxai dauka ba, Tun tulin shinkafa da miyan da aka kawo mata da safe ba a sake kawo mata wani abincin ba.... Karfe uku da yan mintuna Mami ta dawo gida daga office, Karime na xaune kasan carpet a main parlor tana kallo, tun kiran da Mumy tayi mata dakinta bayan sun gama yi ma Kaka girki ita da Sajida sai lkcn ta sauko kasa ganin lkcn dawowar Mami yyi, ta mike da sauri daga xaunen da take tana yi ma Mami sannu da xuwa xata amshi jakar hannunta, Mami ta ki bata jakar tace "Ina Heedayan take?" Karime tace "Ai kina fita Hajiya sai ga wata da naji suna ce ma kaka ta xo gidan, to tun safe da ta shigo ta fita da ita xuwa wancan dakin bata yadda na je gunsu ba ma, ynxu haka suna ciki" Mami tace "Kaka?" Karime tace "Ehh haka naji suka kirata, kuma Sajida tace min Baabar Alhaji ce" Mami ta nufi dakin da kaka take ta yi sallama sannan ta bude ta shiga, Heedayah na xaune tana cin shinkafar da kaka ta xuba mata, ita kuma kaka na kara gyara kayan akwatinta don a birkice ta jerasu sbda sauri, Mami ta xauna nan kasa da murmushi fuskarta tace "Sannu Kaka" kaka tace "Yauwa sai yanxu kike dawowa kenan" Mami tace "Ehh yanxu na dawo" Kaka tace "Toh sannu da xuwa...." Heedayah dake washe baki jin muryar Mami tace "Mami kin siyo min Babyn" Kaka tace "Wani baby? Ki samu ma a samu lkcn kula da ke ba wani shegen baby ba, ke yanxu fisabilillahi Rakiya da kika hadata da wannan yar aiki duk wari ta kula da ita idan cuta ya kamata wa aka kai aka baro??" Mami bata ce komai ba tayi shiru tana kallonta, kaka tace "Kice min Amadu, to wllh xuwa nayi na samu mai aikin duk wari wai ita ce me kula da Deedayah, ki fa bar ganinta makauniya ki xata bata da galihu Rakiya, ke kina ganin fatan jikinta kinsan ba daga cikin wahala ta fito ba, gashi har abincin banxa na ga bata yrda ta ci sai na yan gayu, jikinta kwata kwata bai son wahala, wa ya sani ma ko daga kasar waje wani axxalumin ya sato ta ya wullota nan Nigeria da mugun abu yyi yawa?? Allah kadai yasan me yasa ya hadata da Amadu a titi, kema gashi ta albarkacin ta ya aure ki, wa yasani ko kin dade kina jin son sa a xuciyar ki sai gashi ta dalilin Deedayah ya aure ki..." Mami dai tayi murmushi tace "Ai nayi mata komai kafin in fita kaka, abincin rana kawai take bata sai abinda ba ka rasa ba, kuma baxai yiwu in dinga fita da ita aiki bane da tare xa mu dinga xuwa" Kaka tace "Toh ni dai na dawo da ita nan ba ruwana, sai in ga uban da xai dinga cutarta, mace duk wari kice ita xata kula da cin ta da shan ta, kishiyar ki kuma tun xuwana da safe har ynxu ban ga keyarta ba, duk wannan bai dameni ba tunda ke kin shigo, ynxu abinda nake so dake ga wayata ki kira min Junaidu don mun yi da shi xai xo yau kar yaje can bana nan, ba komai yasa na bar gidan ba sai kwai da suka kawo min duk karni" Mami ta amshi wayarta ta sa number Junaid sannan ta kira sa ta mika ma kaka, kaka na jin ya dauka ta washe baki tace "Junaidu... to yau dai gidan Amadu xaka taho na tattaro gaba daya na dawo nan" Junaid ya gaisheta yace "Toh shkkn kaka sai na xo" tace "Allah ya maka albarka ya kare ka sharrin makiya, ni ai ka fi min kowa" Murmushi kawai Junaid yyi ya amsa da Ameen sannan yyi mata sallama ya katse wayar, Mami na kallon Heedayah ta kama hannunta tace "Mu je ki canxa kaya" Kaka ta kalleta da sauri amma bata ce komai ba, Mami ta mike rike da Heedayah tace "Sai na shigo anjima kaka" Kaka ta bi su da kallo a hankali tace "Yauwa" Suna fita kaka ta mike ta fita ita ma ta nufi dakin Shuraim da sauri, yana fesa turare ta samesa a dakinsa da yake a gyara kamar dakin mace, ko ina fesss sai sanyin Ac, kaka ta xauna gefen gado ta fashe da kuka sosai, ya juya yana kallonta da mamaki, ganin irin kukan da take ya nufeta yace "Lafiya kaka? Me ya faru" Tana Shessheka tace "Mata ki fita tun safe ki bar yarinya Ina wahala da ita daga dawowa sai ki dauketa, Halan ita ta tsinto ma Amadu ita bani da labari ko kuma kanwar uwar yarinyar ce ita bamu sani ba, Yarinya muna xaune lafiya banda hira babu abinda muke yi tun safe ba irin labarin da bata bani ba, bbu irin labarin da ban bata ba kawai mata ta xo ta dauketa su wuce sbda bakin ciki...." Ta fashe da wani sabon kukan tana mika masa wayarta tace "Kira min Junaidu...."

Heedayah isn't free, you read for free 馃し馃徎鈥嶁檧锔忦煠佛煆烩€嶁檧锔�

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....

Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096.....

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull