Heedayah complete Novel - Chapter 28
Heedayah complete Novel Chapter 28: Heedayah complete Novel Chapter 28. *pls fans masu son min magana su dinga typing instead of voice note, cox listening…
3,263 words
*pls fans masu son min magana su dinga typing instead of voice note, cox listening to voice note is stressful wllh, idan typing ne cikin few seconds mutum xai karanta yyi replying nn take, but voice note yana cin time when they are other messages to reply to, thanks for understanding*
Heedayah isn't free, you read for free 馃し馃徎鈥嶁檧锔忦煠佛煆烩€嶁檧锔�
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... 9/12/21, 8:04 PM - ,: Shuraim bai yi wani nisa ba ya kula da motar bayansa dake bin sa, slowly ya dinga tafiya to see idan motar xai yi overtaking dinsa ya wuce, but sai ya ga motar ya ki yin hakan sae ma rage nasa tafiyar da yyi shi ma, Shuraim ya samu waje yyi parking har sannan yana kallon motar ta madubi, Mutumin dake cikin motar dake ta lura da Shuraim shi ma kuma ya san Shuraim ya gano yana bin sa ne kawai yyi wucewarsa bai tsaya ba, Shuraim ya bi motar da kallo har da plate number din motar, juyawa yyi ya kalli Heedayah dake xaune bayan motar, she looks so sad kiris ya rage ta fashe da kuka daga ynda tayi da fuskarta, dauke kansa yyi ga mamakinsa har sannan motar bai bace masa ba, sbda a hankali me motar ke tafiya kan less busy road din, Shuraim ya kalli layin dake gefensa kawai ya karya kan motar ya shiga layin.... Sai kusan Magrib Shuraim ya isa gida, a hankali yake tafiya ganin motar Mumy dake tsaye bakin gate tana jiran me gadi ya bude gate din, sae da ta shiga snn yyi parking gefen flowers dake gaban gate din ya kashe motarsa, Mai gadi na ganin baxai shiga gidan da motarsa ba ya kulle gate din, Shuraim ya juya yana kallon Heedayah dake bacci bayan motar, sauka yyi motar ya kulle ya nufi cikin gidan, tsaye ya ga Mumy alamar shigowarsa take jira, ya karasa Inda take ya gaisheta tace "Daga ina kke da magariban nan" Yace "Asibiti" tace "Ohk, goben xaka tafi Zarian?" Yace "In sha Allah" tace "Toh nima xan je Zarian gobe, amma bance ka gaya ma kowa ba, karfe nawa xaka fita?" Yace "Takwas..." Tace "Toh kayi hakuri ka bari karfe tara, kafin nan Abbanku ya fita" Shi dai kallonta kawai yake don ya san basu da 'yan uwa a Zaria, can yace "Me xaki je ki yi a Zaria Mumy?" Mumy tace "Yar Hajiya Sadiya ba can take aure ba, to ta haihu gobe suna, ko barka ban je ba, kuma idan na gaya ma Barrister ba lallai ya yrda ba, ni ko Sadiya ai ta wuce haka a wajena" Shuraim yace "Aa da dai ki fara sanar ma Abba Mumy" Mumy ta daure fuska tace "Toh ban yi niyya ba" Bai kuma cewa komai ba ta juya ta nufi cikin gidan ya bi ta da kallo har ta shiga parlon snn ya juya ya koma waje, Bude back seat yyi Heedayah ta bude ido da sauri, hannunta ya kama ya saukar da ita daga cikin motar ya kulle motarsa, har da xai mika ma Mai gadi hannunta ya kai ta ciki sai kuma kalli cikin compound din ya shiga yana rike da hannunta, yana isa balcony ya bude kofar parlon yana kallon ciki, bbu kowa hakan yasa ya shiga parlon da ita ya kai ta har kofar dakin kaka sannan ya juya ya fita xuwa masallaci, Kaka da ta fito daga bandaki tayi alwala tace "Waye wnn?" Heedayah tace "Ni ce" Kaka tace "Toh ai na ganki, sai yanxu ku ka dawo kai faridan makaranta?" Heedayah ta gyada mata kai, Kaka tace "To ina Shureen din?" Heedayah tace "Nima ban sani ba, ya wuce" Kaka ta ta6e baki tace "Toh me yasa kika yo min nan, Rakiyar bata nan ne" Heedayah ta turo baki tace "Toh ai shine ya kawo ni" Kaka tace "Toh ni dai na gyara dakina na share, na sa turaren wuta, gadon ma yau ko hawa ban yi ba tun da garin Allah ya waye" Heedayah ta turo baki ta juya tana laluba hanya da hannunta ta fice daga dakin, Kaka tace "Haka kawai ba kya ma mutum taimakon komai sai dai ki lalata waje gantalalliya" Mumy da fitowar ta kitchen kenan ta bi Heedayah da ido har sai da ta isa kofar parlon Mami, Dai dai fitowar Sajida dakinsu ganin Heedayah ta karasa don ta bude mata kofar, juyawa Mumy tayi ta wuce parlonta kafin Sajidan ma ta ganta... Sai da Heedayah ta shiga ciki sannan Sajida ta kulle kofar ta wuce. Karfe tara da rabi Mumy ta kira wayar Shuraim, yana xaune dinning da cup din shayi a gabansa, Ya daga kiran Mumy tace "Abbanka fa ya fita, baka gama shiryawa bane ko in tafi in hau motar haya kawai?" Yace "Na gama" katse wayarta tayi, ya mike ya tafi dakin kaka, Heedayah ce kwance saman gadon tana ma Doll din da Junaid ya siya mata kitso, Kaka kuma na bandaki tana wankewa, Heedayah ta dakatar da kitson da take ba Doll din jin an bude kofa tace "Waye?" Ya kalleta ya dauke kai, bata kuma cewa komai ba sbda kamshin da ta ji, Ya xauna yana jiran fitowar kaka, sai ga ta ta fito tana cewa "Masu aikin jaraba kawai sun bari bandakina xai dafe in shiga uku in lalace, Banda dai ma lalacewa ta sameni ina ni ina bar masu bandakina su dinga wanke min...." Shuraim dake ta kallonta yace "Xan wuce Zaria" Kaka tace "Tohhh da sassafe haka shureen" Yace "Eh" Tace "Toh Allah ya kiyaye hanya, ni dai ko kwandala bani da shi a dakin nan, dama Umaru ne me bani, gashi yau kwana daya bai xo ba" Mikewa yyi ya mayar da wayarsa aljihu, tace "Toh ko dari biyar baxa ka d'an bani ba Shureen, bani da ko sisi fa" Yace "Ni da bana maki komai kuma yau xa ki ce in baki kudi?" Kaka tace "Toh ai dama idan ba kai ba waye me min, shi Sudess yan matan da ya tara gabansa ma sun ishesa, Amadu kuma kaga ynxu ta kudin da xai kai makauniyar nan gyaran ido yake, da kyar idan ba sai an kashe kusan miliyan biyar ba tunda India ne, ai kaga ta kassara min d'a na kawai, wa gareni dama banda shi, shi din kuma ga uban abinda ke gabansa ba dangin iya balle na baba, Umaru dama yau sati rabona da kudinsa, sae dai ya xo ya karaci xamansa ya fice, toh ya ake son inyi da raina" Shuraim ya tabe baki yace "Toh nima bani da shi" Daga haka ya fita daga daki, kaka ta bude baki ta bi sa da kallo, can kuma tace "Toh kada Allah ya sa ka samu, marowacin banxa kawai solobiyo" Ko saurarenta bai yi ba, yana fita sai ga Mumy ta shigo dakin, Ta xauna ta gaida kaka, kaka ta amsa xata koma bandaki, Mumy tace "Kaka xanje gidanmu ne Salima bbu lafiya" Kaka ta dawo tace "Toh ba dole ba, yarinya sai gantalin duniya take an rasa me gaya mata gaskiya, kamar abun arxiki Amadu ya daukota kusan shekara sha biyu da suka wuce amma uwarki ta amshe ta wai autarta, to yau ina uwar taki take, ba gashi ta tafi ta barta ba, yarinya duk ta lalace wa yasani ma ko bin maxa take, da ynxu tana wajen Amadu har ya aurar da ita ta haifi 'ya yanta...." Mumy dai bata ce ma Kaka komai ba, Kaka tace "Amma wnn ai tafi karfin kowa ynxu, ta xama abar tsoro, na samu labarin ma ba kullum take kwana gida ba wai koh??" Mikewa Mumy tayi tace "Toh sai na dawo" daga haka ta nufi kofa ta fita, kaka tace "Toh Allah ma dai ya sa ba ciki ne da ita ba, tunda cewa kika yi bata da lfya, toh a dawo lfya Maryam" Mumy dai tayi wucewarta bata tanka ta ba Karfe Goma da rabi suka isa Zaria, Shuraim na kallon Mumy dake ta danne dannen waya yace "Ina ne gidan?" Tace "A'a kawai ka samu waje ka ajiyeni xan nemi adaidaita sahu, kilan kana da lectures kar in shiga hakkin ka" yace "Sai goma lectures din" Mumy tace "Ba dai ni nace ka ajiyeni ba wai" Bai kuma cewa komai ba yyi parking, Mumy ta sauka motar tace "Toh Allah ya bada sa'a" yace "Ameen, amma wani anguwar xa ki?" Tace "Saboda ga ka ubana?" Yace "A'a I was thinking ko anjima xan xo in maida ke kaduna ne" Tace "A'a, xan samu motar haya" Daga haka ta tsayar da adaidaita ta shige, ya tada motarsa ya wuce... A cikin adaidaitan Mumy tayi dialing number Sadiya tace "Toh ga fa ni na shigo Zarian Sadiya" Hajiya Sadiya ta gaya mata sunan wani filling station wai ta jirata a nan, Suna isa gidan man Mumy ta sauka ta ba Mai adaidaitan kudinsa tana jiran Hajiya Sadiya, bayan kusan minti ashirin sai ga Hajiya Sadiya, Mumy tace "Kin fa ce min kin fito gida ashe baki fito ba" Hajiya Sadiya tace "Wllh hatsari me Muni aka yi kafin Jaji, shine ya haddasa go slow" Mumy tace "Toh Allah ya ji k'an musulmi, ynxu ina muka nufa?" Hajiya Sadiya tace "Tashan da xa mu je mu hau motar garin mana" Wani adaidaitan suka samu ya kai su tashan, Mumy sae cewa take ni dai Allah ya sa kafin karfe hudu xa mu koma Kaduna, gidanmu nayi ma Barrister karya nace xan je" Hajiya Sadiya tace "Gwara ke an san baki gida, to ni Alhaji bai ma san na fito ba" Mumy ta biya masu kudin motar suka shiga suna jiran ya cika a tashi..... Tagumi Mumy tayi tana kallon katon Mutumin dake gabansu, Hajiya Sadiya na xaune gefenta ita ma tana kallonsa, bayan kusan minti goma Mutumin yyi gyaran murya yace "Toh ga dai abubuwa da yawa na gani, masu kyau da mara su kyau, da farko dai da fatan a shirye kike Hajiya Maryam don nan ba da dadewa ba babban d'an ki xai yi aure...." Mumy ta kalli Hajiya Sadiya da sauri, sannan ta kara kallonsa tace "Aure kuma Malam?" Yace"Kwarai kuwa gashi na gani" Tace "Toh ni dai bai ta6a ce min komai ba...." Mutumin yace "Ita kuma wnn yarinya Makauniya naga abubuwa da yawa tattare da ita da nake kan ganewa har ynxu, sai dai a sarari na ga har Mai gidan ki na shirin fita da ita kasar waje gyaran ido, haka ne ko ba haka ba?" Mumy ta marairaice tace "Haka ne wllh" yace "Toh nan da kwanaki kadan xa su fita, kuma idanuwanta kam xa su bude in dai an fita... Sannan ita wannan kishiyar ta ki, naga a gaba xata xama ita ce kan komai a gidanki, don ynxu ma maganar da nake maki sonki ya ragu sosai a xuciyar mijin ki, kawai dai yana xaune ne da ke ko sbda rabon tsakanin ku, amma ynxu wnn kishiya ta ki ita ce gabansa, ita kadai yake gani, sannan ita salonta xa a iya kiransa da na makirci don bata wani nuna ta damu da shi, nan kuwa duk karya ne" Mumy da hankalinta yyi mugun tashi tace "Allah Malam???" Shiru yyi yana kallonta da tikeken hancinsa, Hajiya Sadiya ta dinga bugeta alamar me yasa tace haka, da sauri Mumy tace "Tuba nake malam ayi hakuri" Mutumin yace "Ku fita ku dawo nan da minti ashirin" Hajiya Sadiya ta mike da sauri tace "Toh Malam, ayi hakuri...." Mumy ma ta mike suka fita waje da sauri, saukowa suka yi daga kan rock din suka samu karamin rock suka xauna Mumy ta fashe da kuka sosai tace "Kin ji ko Sadiya, dama ba na gaya maki har yau ni da Barrister ba kamar da ba, tun da yayi auren nan dama ko nemana baya yi, Kin dai ga abinda wnn makauniyar tayi ma rayuwata koh? Ta dalilinta ne fa dukka wannan abubuwan ke faruwa, ita fa ta lalata min gida na, ita ta sa kishiya ta shigo gidana har xa a kwace gidan a hannuna, ni ynxu me xan ma yarinyar nn in ji dadi???" Hajiya Sadiya ta sauke ajiyar xuciya tace "Ba tuntuni nake ta bin ki mu xo nan ba kinki, yo ai Allah ma cewa yyi tashi in taimake ka, ga dai shi kin jiye ma kunnenki komai, Amma bari mu koma ciki tukun mu ji sauran bayanin, shi kuma Shuraim duk rashin maganan nan nasa har wani neman aure yake yi dama baki sani ba" Mumy ta share idonta tace "Toh ae sai yyi auren mu ga, xae ma ajiye xancen auren nan ne, ce masa nayi ina son yyi aure yanxu" Hajiya Sadiya tace "Toh ai shi na gani, duka duka nawa yake da xai tsiri son yin aure" Mumy tayi tagumi bata ce komai ba don ba batun auren Shuraim ya fi damunta ba ita yanxu, suna nan xaune har minti ashirin din yyi sannan suka mike suka sake gurgurawa can sama, Hajiya Sadiya tayi kasa da murya tace "Toh ga mu mun dawo Malam, da fatan ka huce" Bai ce komai ba sai bayan kusan minti biyar yace "Tohh, yanxu me ku ke son ayi a kan lamarin, ita dai wnn makauniya naga xata warke nan ba da dadewa ba, sannan xata xame maki ciwon ido nan gaba ke Maryam...." Mumy ta marairaice tace "Toh Malam ya kaga ya kamata ayi, ni so nake gaba daya ta bace bat na har abada kuwa, in son samu ne ma ni kada idon ya bude malam ta dauwama a makance, Kai idan ma duniyar xata bari gaba daya ni dai oho in daina ganinta kawai, sannan shi kuma wnn yaro nawa ayi kokarin ganin an dakatar da batun auren nasa don ni ban shirya aurar da shi ba yanxu, ita kuma kishiyar ayi duk abinda xa ayi ta bar min gidana da mijina, in xama ni kadai ce a gidan, Kuma maigidana na da uwa fitinanniya, duk ta gallabe mu, so nake ita ma a rabata da d'an nata, ko biyayya ya daina yi mata, snn a rufe bakinta gumm ta xama kamar kurma ko bebiye, taji kuma bata son xaman gidan namu ta koma can gidan wansa har abada" Mutumin yace "Toh an gama...." Hajiya Sadiya ta gyara xama tace "Ni kuma Malam a kara rufe min bakin mijina a kan na da, duk da dai bbu wata matsala ynxu bai jin batun kowa sai nawa tun aikin da kayi min kwanaki, amma a kara min wani sabo ynxu dai" Mutumin yace "Toh a bani minti sha biyar a waje" Mikewa duk suka yi suka gungura kasa. Sai kusan magariba Mumy ta isa gida don ma ba ita bace da girki, a dar dar ta shiga parlon tana boye jakarta a Hijab, ganin bbu kowa kusan da gudu tayi bangarenta ta kulle kofar, ganin su Rabi'ah da Khadijah xaune suna kallo parlonta ta shige bedroom tana amsa sannu da xuwan da suke mata... Karfe goma saura na dare Mumy ta fito, Mami ce ta fito bangaren Abba, Mumy ta dauke kai kamar bata ganta ba ta shiga dakinsu Sajida, tana daga tsaye bakin kofa tace "Sajida me ya hanaki wanke min bandaki yau?" Sajida ta mike da sauri tace "Wllh Hajiya na wanke tun da safe" Mumy tace "Toh tafi ki ga bandakin da kika wanke ki dawo ki sameni yanxu" Sajida ta fita dakin xuwa bangaren Mumy, Mumy na kallon Karime tayi kasa da murya tace "Xuwa sha daya ko sha biyu ki taho bangarena ki sameni" Karime tace "Toh Hajiya" Daga haka Mumy ta juya ta wuce da sauri. Mumy na parlonta xaune tana ta jiran Karime sai ga ta kuwa karfe sha daya da rabi, Karime ta kulle kofar ta iso kusa da ita ta durkusa tace "Ga ni Hajiya" Mumy tace "Yanxu ita makauniyar gun Rahinar take ko gun Kaka?" Karime ta tabe baki ta gyara xama tace "Ehh toh, yau ta kwana dakin kaka, gobe ta kwana bangaren Rahinar, amma dai ta fi dai xama wajen kaka" Mumy tace "Ba naga tana yawan shan shayi da, ko ta daina?" Karime tace "Har yau tana sha, gwangwanin kayan shayin nata ma na dakin kaka, ta sha da safe wani lkcn har da rana sannan ta sha da daddare" Mumy tace "toh wani aiki xan baki Allah ya sa xa ki iya Karime" Karime tace "Haba me xai hana, ai bbu abinda baxan iya maki ba Hajiya, ke da kika rike ni tamkar 'yar ki, Ina xan samu haka banda wajen ki" Mumy tace "Toh, ba wani abu bane garin magani ne nake son ki juye a gwangwanin milon gaba daya sai ki gauraya, don idan an sa a madara xa a gane" Karime tace "Hajiya amma dakin kaka fa kayan shayin suke ba dakin uwa rikonta ba" Mumy tace "Toh sai me?? Ba tana sa ki share share ba?" Karime tace "Ta fi sa Sajida, komai Sajida take kira tayi mata" Mumy tayi shiru sai kuma tace "Wani aikin take sa Sajida?" Karime tace "Irin su Shara, goge gogen waje sai wankin bandaki" Mumy tace "Da yaushe take sa ta?" Karime tace "Da safe haka take kiranta ta saka ta" Mumy tace "Toh gobe kafin ma ta kirata xan aiki Sajidar, tana kiranta sai ki je kice bata nan, nan kuma xa ki tambayeta me xa ki yi mata" Karime tace "Toh shkkn, xan yi iya bakin kokari na Hajiya" Mumy ta mike ta tafi cikin dakinta sai ga ta ta fito da Kullin magani a kyallen atamfa tace "Gaba daya xaki juye kuma kiyi a hankali kar ki bari ya xuba" Karime ta amshe ta tura cikin rigan mamanta tace "Toh Hajiya in sha Allahu" daga haka ta fice daga parlon da sauri, Mumy ta sauke ajiyar xuciya ta kashe wutan parlon ta wuce cikin dakinta. Washegari da safe bayan Abba da Mami sun fita, kaka ta kwalo ma Sajida kira, Karime ta mike da sauri tana ta6a mamanta don ta tabbatar kullin na nan don Mumy tun safe ta sa Sajida ta bar gidan, Tana shiga dakin kaka da sallama tace "Gani kaka, Sajida an aiketa" Kaka ta dinga kallonta daga sama har kasa sannan tace "Ni dai na ga jaraba, wai ke baki wanka ne, kullum cikin naso kike kamar d'an wake, mata kazama kawai duk wari, me xa ki min to da kika taho toh?" Karime tayi kasa da kai tace "Na xata aiki Sajidar xata maki shine na xo in yi" Kaka tace "Ehh lallai, da kuwa lalacewa ta sameni, a hakan xaki kama min aiki inje wata cutar ta kama ni a banxa a hofi, wai ma daga wani kauyen kike??" Karime tayi kasa da kai tace "Doguwa" Kaka tace "Ko da na ji, to yi tafiyar ki, kar ki sake shigo min daki da sunan xa ki min aiki ni ba gantalalliya bace, bari Rakiyar ma ta dawo xan ji ko meye sauran amfanin ki a gidan nan tunda dai ga ni nan ina ma Deedayah komai, ke kuma ba sai a sallame ki ba" Karime ta juya da sauri ta fita tana waigo kaka a tsorace, Kaka tace "Ni naga jaraba, mata duk naso kullum fisabilillahi tayi ta shigo min daki" Heedayah dake kwance saman gado tace "Kaka to aiki fa xata taya ki..." Kaka ta kalli Heedayah da sauri tace "Ta je can ta taya uwarki Rakiya aiki, ni ba ruwana cewa ma xanyi a sallameta ko xan daina ganin fuskarta"
Heedayah isn't free, you read for free 馃し馃徎鈥嶁檧锔忦煠佛煆烩€嶁檧锔�
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah