Heedayah complete Novel - Chapter 29
Heedayah complete Novel Chapter 29: Heedayah complete Novel Chapter 29. Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... 9/12/21, 8:04 PM - ,: Junaid…
2,928 words
Heedayah isn't free, you read for free 馃し馃徎鈥嶁檧锔忦煠佛煆烩€嶁檧锔�
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Chapter notes and social links
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... 9/12/21, 8:04 PM - ,: Junaid dai ba ce ma kaka komai ba sai murmushin da yayi, ko minti goma ba ayi ba sai ga Salima ta fito, Kaka ta bude baki tace "Har kinyi me??" Tace "Na gama" Kaka tace "Tohh ai ya fi babu, Allah yayi maki albarka" Salima na kallon Junaid tace "Ba a kawo masa ruwa ba?" Kaka tace "Au, duba friji ki dauko, akwai mantina ma ki hado" Ta tafi fridge din ta bude ta dau bottle water da malt ta iso ta ajiye gefen Junaid tana kallonsa tace "A dauko maka cup ne?" Ya d'an kalleta kafin yace komai kaka tace "Tafi ki dauko kofi a kitchen" Tace "Toh" sannan ta nufi kofa tana rangwada, Sai da ta fita kaka ta fashe da dariya har da kyakyatawa tace "Wllh wnn dai da kke gani ta fi shaidan shakiyanci, ni dai albarkacin ka an wanke min bandaki" Junaid yace "Toh ita bata yi aure bane?" Kaka tace "Wani aure, matar da ke kan cin duniyar ta, wnn fa da kake gani tafi karfin kowa, garurruka take bi tana sheka ayarta, kasan ba uwa ba uba...." Junaid ya girgixa kai yace "Toh Allah ya kyauta" Kaka tace "Ameen, Amadu ma bai fiye son tana xuwa gidansa ba kar ta lalata masa yaransa, kasan fa kwanaki...." Tsit kaka tayi ganin Salima, kaka tace "Sannu Salima, Allah yyi maki albarka" Ta duka kusa da Junaid tace "A xuba maka ne" yace "No thanks bar shi" Ta mike ta nemi kujera ta xauna tana kallon Heedayah tace "Kaka yarinyar nan ce ta girma haka?" Kaka tace "A'a ba wani girma tana nan yanda take, yarinyar da ko kirgan dangi da kyar idan ta fara xa ki ce ta girma" Salima tace "Duk da hka ae ta fi ynda na santa, lkcn da Abba ya kawota ae bata kai haka tsayi ba" Kaka tace "Ehh to nima na lura da tsayin, to ta ci me kyau ta sha me kyau ba dole tayi tsayi ba, ae Allah kawai ya shi ma Amadu albarka, ko biyansa iyayenta suka ce xa su yi wataran ma ba lallai su iya ba, duk da Ina ma xa a gansu, wa ya sani ma ko sun mace" Junaid ya ajiye nail cutter din hannunsa yace "Kaka xan d'an je wani waje ne kika kirani" kaka tace "Aa ba wani abu bane dama kayan shayi xaka siyo ma Deedayah, me aiki ta sace wanda Amadu ya siya mata, Kuma a gaskiya bai kamata a takurasa ba ynxu ta kudin fitarmu India yake" ya mike yace "Toh anjima da daddare xan kawo in sha Allah" Kaka tace "Har xaka tafi kenan?" Yace "Ehh sae na dawo anjima" Heedayah tace "Yayana baxan raka ka ba?" Kaka ta mata wani kallo ta cikin sigar irin ynda tayi maganan tace "Yeyeyeyen, toh baxa a je da ke din ba" Heedayah ta fashe da kuka sosai, Junaid ya kalli kaka bai dai ce komai ba ya kama hannun Heedayar ta mike da sauri tana Shessheka, kaka tace "Kaiii wnn da ku ke gani fa algunguma munafuka ce wllh, Wai wani ina mata da xafi kamar warce nake guntule ma hannu, Banda ni din waye xai xaunar dake ya cire maki rubabbun faratan ki, kawai yarinya kiyi min sharri a gaban kowa ayi min kallon macuciya" Junaid ya fita daga dakin yana rike da hannunta, Salima ta bi su da kallo, kaka tace "Haka nan take hada kowa fada tunda aka kawota gidan, mu dai ba sae dai Allah ya biya mu dawainiyar da muke da ita ba, ae baxa mu biye ta nata ba" Salima tace "Toh kaka dole ne xama da ita, ba sai a kai ta gidan marayu ba kawai" Kaka ta kalli Salima da sauri tace "Anya kina son gamawa da duniya lafiya kuwa Salima, me yarinyar ta maki xaki mata wnn mugun fata hka, ce maki aka yi marainiya ce xa mu kwasheta xuwa gidan marayu? Ke ma da kike marainiya ba a kai ki can ba balle ita, to wllh ki iya bakin ki...." Mikewa Salima tayi tana yatsine baki ta fita daga dakin, main parlor ta tadda Junaid yana lallashin Heedayah dake kuka a hankali, lkci daya Salima ta hade rai tana kallonsu, Cikin rawar murya Heedayah tace "I am not going back to her room" Murmushi yyi yace "Toh ae Mami bata dawo ba" tace "Ehh xan je inyi bacci dakin Mami" Yana rike da hannunta xuwa bangaren Mami ya murda kofar yaji a rufe, muryar kaka yaji tana cewa "Junaidu kar fa ka je da ita Amadu xai min fada wllh, ka kawota ga fura nan xan dama mata, ga kuma biscuit Rakiya ta bani in bata" Bata jira cewarsa ba ta karaso ta kama hannun Heedayah ta wuce dakinta, Yana rike da makullin motarsa ya fita, tsaye ya tadda Salima a balcony ta jingina da pillar ta rungume hannu, kallo daya yyi mata xai wuce, cikin sanyin muryarta tace "Do you mind sharing ur digit with me?" Rasa me xai ce yyi da farko, can kuma ya tsaya ya juyo ya mika mata wayarsa yace "Alright" ta saka number tayi saving sannan tayi dialing number, bayan ya shigo wayarta ta dawo gabansa ta tsaya ta mika masa tana kallonsa tace "Nayi maka saving da Beauty haka frnds dina ke kirana.... How should I save urs?" Yace "Junaid...." Ta wara manyan idonta tace "Xan iya saving as Jayyy?" Yace "As you wish" ta basa hanya tana wani murmushi tace "Alright, sai ka dawo Jayy" Wucewa yyi bai ce mata komai ba ta bi sa da kallo ko kiftawa bbu... Da daddare bayan isha Mami na xaune parlorn Abba da Mumy dake ta danna wayarta ta dalilin kiransu da yayi gaba daya, Abba ya gama abinda yake yyi gyaran murya yace "Kilan Maryam ke ce kadai baki san xa a fitar da Heedayah xuwa India nan da 'yan kwanaki ba a gidan nan...." Ta katse sa tace "Toh dama ta ya xa ayi in sani, an maida ni wani abu ne a gidan da xa a sanar min??" Yace "Look idan xaki saurareni ki saurareni bana son wani maganan banxa da hofi" Mami dai kallonta kawai take a Tv, Mumy ta tabe baki ta dauke kai, Abba yace "Idan ma baki sani ba ynxu ai kin sani koh?" Mumy bata kuma cewa komai ba, Abba ya ci gaba da maganarsa "So jiya Dr ke sanar min xa a tafi ne before the schedule time, probably she will be placed under diet or anything of such ban dai sani ba, a tafiyar nan kuma da xa ayi mutum biyu kadai xa su je da ita can kasar.... It's a very good thing ace i am among the two pple going out with her amma sbda uxururruka ina ga baxan samu damar bin su, though I didn't even plan going from the beginning sbda nasan yanayin aiki na, sai dai definitely Rahinah xata je..." Mumy ta mike ta fashe da kuka tace "To ba dole kace Rahinah xata je ba tunda Rahinah ce a gabanka yanxu, ni ai ynxu ba bakin komai nake a wajen ka ba barrister, amma ina son tunasar da kai cewar ka ajiye wani akidar banxa ta boko ko makamancinsa, baxa a ta6a canxa ma tuwo suna ba, ina nan a matsayin matarka ta farko, ko ka ki ko ka so, idan ma kayi respecting dina as that or not ni din dai ce kan gaba, kuma kai da Allahn ka wllh" Yace "Wait pls, what are u insinuating Maryam.... Kina nufin banyi adalci ba don nace Rahinah xata bi Heedayah India?? Wacece marikiyar Heedayah?" A kufule ta baxa hannu tace "Ohon maku, Wnn ya rage naku, idan ma kayi adalcin kafi kowa sani idan baka yi ba ma kafi kowa sani wllh..." Yace "Noo amma na yanke wnn hukuncin ne bayan nayi la'akari da cewar Heedayar wajen Rahinah take tun xuwanta gidan nan, so ban ga ma'anar cewa ke ki je India da Heedayah ba, for what reason? Ko kin ta6a involving kanki a lamarin yarinyar ne a gidan nan?" Mumy ta wani tabe baki tace "Uhnn, Ai dama baxa ka ga ma'anar hakan ba tunda Rahinah ce matarka ta fari, to ni kuwa da na shigo daga baya ai bai kamata inyi presenting dinka a ko ina ba, sai dai ita da take uwar gidan ka" Kallonta kawai Abba yake with surprise, Mami kam sai tabe baki take tana murmushi idonta a kan TV, Abba ya jingina da kujera yace "Ikon Allah, anyway if you view it from perspective shkkn sai Rahinah su je tare da Shuraim duk da ba tare nayi niyyar su je ba, na so Rahinah taje ne tare da either Junaid or Sudais, tunda they are free now shi kuma Shuraim yana makaranta" Mumy na huci tace "In har baxa a je da ni ba to bbu inda d'a na xai tafi wllh wllh anji rantsuwar musulmi, su je can da Junaid din ko Sudais amma in dai ni ban cancanci tafiya indiar da su ba Shuraim ma bai cancanta ba don ni nayi Shuraim..." Abba yace "Tashin hankalin da baki yi kwana biyu ba kike sha'awar yi ynxu ko Maryam" Tayi masa wani kallo tace "Duk yanda ka daukesa haka ne, ba shafata yyi ba" Mami ta kalli Abba tace "Barrister sorry.... but I have meaningful things to do now, xan fara hada abubuwan da xa a bukata na tafiya, da kayan Heedayah sannan xan karasa wani aikin da nake yi ka kirani, so duk decision din da aka yanke yayi min bbu damuwa a wajena, afterward sai ka sanar min, as for now I am out...." Yace "Alright Rahinah" daga haka ta mike ta nufi kofa, Mumy ta bi ta da wani irin kallo xuciyarta na tafarfasa har ta fita parlon, Abba ya jawo laptop dinsa ya ci gaba da abinda yake yi shi ma, Juyawa Mumy tayi a fusace ta nufi kofa tana cewa "In har ni baxan je ba to Shuraim ma bbu inda xa shi wllh, Kuma mutum ya ci gaba ranan lahira shi xai tashi da shanyayyen barin jiki al-qur'an" Abba ya bi ta da ido har ta fita sannan ya girgixa kai, tana komawa parlonta ta dau wayarta ta shiga daki ta kira Hajiya Amina don ta sanar mata ance xa aje da Sudais, Umma na dagawa bayan sun gaisa tace "Ke ki ji Amina wai xa a kai makauniyar nan gyaran ido Ina matsayin uwargida a gidan nan wai ba da ni xa a ba" Umma tace "Kai haba, da 'yar gaban goshi xa a tafi kenan, ke kam kina cikin jarabawa wllh mata ta shigo kamar wasa xata kwace gida a hannunki, to sai aka yi yaya, sai ke kuma kika yarda??" Mumy tace "In yarda, Ashe ma ba Maryam bane sunana, ae wllh tayi kadan, muna nan da ke ba da ita xa ayi tafiyar nan ba" Umma tace "Toh wai jira, ke Maryam da kike tada jijiyoyin wuya aje dake wato har farin cikin gyaran idon da xa ayi ma yarinyar kike knn" Mumy tayi wani dariya ta xauna gefen gado tace "Haka kike tunani Amina, ke ai tun da kika ga na dage sai da ni xa aje india kema ai ya kamata ki fahimci wani abu ko" dariya sosai Umma tayi tace "Gaskiya ne ta wajena, toh kuwa sai kin yi da gaske sannan xa ayi tafiyar nan da ke ga dukkan alama" Mumy tace "Gasken gaske ma kuwa, wai wani dama shi ya shirya cewar Rahinah ce xata fita tare da yarinyar sai ko D'an ta Junaid ko Sudais" Da sauri Umma tace "Wani Sudais din?" Mumy tayi wani dariya tace "Naki mana" Umma tace "Ikon Allah, Toh sai mu gani ai idan wani ya haifar min shi, xan ga ta ynda xai bi su din...." Mumy ta tabe baki tace "Ni dama nasan baki da labari shi yasa nace bari in kira ki in sanar maki" Umma tace "Wllh gwara ko da kika gaya min tun wuri Maryam, nagode..." Mumy tace "Ynxu duk abinda ake ciki xan kira ki dai" daga haka suka yi sallama Mumy ta shiga kiran Hajiya Sadiya.... Kaka na xaune dakinta sai Abba da ke mata bayanin yanda suka yi da Mumy daxu, Kaka tace "Kai ni fa ban gane kan labarin nan naka ba Amadu, Wai bata da labarin tare xa aje da ni ne da Rakiyar take tada jijiyoyin wuya sai anje da ita, ita a wa Allah na tuba" Abba bai ce komai ba, Kaka tace "Ikon Allah, to wai ita a su wa? Uban me ta ta6a yi ma Deedayar da take kwadayin xuwa India ta dalilin Deedayah?? Matar da idan ta samu sarari cutarta xata yi ina kuma xancen tace sai ta bi mu India, ni dai naga abinda ya isheni, Anya Maryam na da saiti kuwa? Ta bi mu India ayi me da ita a can, ga dai ni ga Rakiya, Ita har wani ilimi gareta da xata ce sai ta bi mu India mu je can ni ba turanci ba ita ba turanci ba, ni dai naga abinda ya isheni ni Binta, matar da ko boko bata yi ba xata bi mu India da Deedayah" Abba ya kara kallon kaka bai ce komai ba, Kaka tace "Ni dai ba ruwana wllh, wa ya sani ma ko da tsafi take son bin mu don kar 'yan idanuwan su gyaru, da kyar ma idan ba haka bane, to wllh in har Rakiya xata fasa tafiyar ace mu je da Maryam to gwara ni ma kawai in hakura... hka kawai mu je da ita idanuwa su ki gyaruwa mu dawo duk kunya ta ishe mu?? Aa wllh ba da ni ba, gwara in fasa tafiyar kawai" Abba ya rungume hannunsa daga xaunen da yake yana kallonta yana tunanin ta inda xa a fara gaya mata ai fa tafiya banda ita, Kaka ta mike tace "Kaji min mata dai, waye bai san bata son Deedayah ba, to wai abinda ban gane ba.... kai yanxu Amadu da ta tsiri cewa sae ta bi ni da Deedayah india me kace mata?" Abba ya sauke ajiyar xuciya yace "Aa ban ce komai ba" kaka tace "To yanxu ka tashi ka koma kace mata ni kaka nace baxa aje da ita ba, daga ni sai Rakiya xa mu je kai Deedayah gyaren idon, sai kuma Wanda yyi niyyar biyo mu daga baya idan idanuwa sun budu" Ya mike yace "Toh" daga haka ya fita parlon, ta koma ta xauna tana huci tace "Kaji min gantalalliyyar mata dai yar tasha" Washegari da safe Abba ya tafi har parlon Mumy, ta fito daga dakinta tana wani ciccijewa ta xauna bbu ko gaisuwa, yace "Kina ji na Maryam, in sha Allah ranan asabar Rahinah da Shuraim xa su tafi can India tare da Heedayah, nace su je da Shuraim ne sbda dole Rahinah baxata iya komai ita daya ba abubuwan xa su yi mata yawa, Kuma don kar ki ga kamar ai ba a san involving dinki, ynxu idan nace duk mata su je...." Tsam Mumy ta mike ta dakatar da shi tace "Bbu inda Shuraim xa sa in har ni baxan je ba" Yace "To ni kuma nace tare da Shuraim din xa su tafi ke baxa ki je ba" yana fadin haka ya mike ya fice daga parlon ta bi sa da kallo kamar xata kurma ihu tace "Wllh wllh bbu Inda xa shi tunda ba wani shegen ya haifar min shi ba...." Ana gobe tafiyar da yamma Baffa ya xo sanar ma Kaka fa ba da ita xa aje india ba don Abba yace shi dai baxai iya sanar mata ba, Baffa na shiga dakinta ya sameta tana ta kokuwar rufe akwati da ta cika da kaya, Heedayah na bacci saman gado, kaka tace "Aa Umaru kai ne da yamman nan, na xata gobe xaka xo muyi sallaman ai" Baffa ya xauna yace "Aa, gyara kike Baaba?" Tace "Ka ji wata magana, gyaran me kuma, ba gobe ne tafiyar ta mu ba ko an daga ne bani da labari? So kake sai goben inyi ta kokuwar rufe akwati, ynxun ma kawai budewa nayi in tabbatar ban mance komai ba, har ararrabi na da sa6ara duk suna ciki" Baffa dai bai ce komai ba, tace "Ynxu ma na aiki Sajida ta siyo min goro a kasuwa kasan bana tafiya bbu shi sai inji tashin xuciya a hanya" Kaka ta karasa xuge jakar tace "Toh sai a kira min su Shafi'u, da D'an Ladi in yi masu sallama kada su ce na tafi bbu sanarwa, kawun ku Lawali ma ku kira min shi in sanar masa, bbu ruwana da kananan maganan dangin uban ku" Baffa ya gyara xama yace "Da mutane biyu fa nake jin tafiyar xai kasance ma" kaka tace "Ehh na sani, da ni da Rakiya ba, dama Maryam ce xata ja mana bala'i wai sai ta bi mu, amma daxu naje har parlonta nayi mata wankin soso da sabulu wllh...." Baffa ya kasa cewa komai sai kallonta yake.... Shuraim ne ya shigo parlon da sallama, kaka tace "Ae na xata baxa ka xo muyi sallama ba" gaida Baffa ya fara yi Baffa ya amsa masa, Shuraim na kallon jakarta yace "Ina xa ki?" Tace "India da Deedayah da Rakiya, ko baka da labari?" Yace "Ke wa yace maki da ke xa a je?" Tace "Ubanka ya tsara hka, ko xaka hana??"